Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Haka ma Auwalu shima yayi Auransa yatare da matarsa a garin Abujah dake shi yana ha'dawa da aikin gwannati

Jibiril ko San mata yasa agaba damuwar shi ya aikata xina da 'Yar mutane ya biyata

Anan duk ku'din da yake samu suke qarewa yaqiyin Aure sam

Jabiru ko neman ku'di kawai yasa agaba
Shine siyan filaye gidaje da dai sauransu gashi dasan yasaka hannun jari a garuruwa
Ananan ananan wata rana yaje saudiya dan sauke farali
Anan ya ha'du da Khamsa'u balarabiyar qasar Harif
Kallo 'daya sukama juna sukasan sun kamu da qaunar juna
Dake wayayyune anan kowa yabaiyana kansa ga 'dan uwansa


Khamsa'u dai 'yar Sarkin garin harif ce
Ita ka'dai Allah ya bashi
Baqamin so mahaifinta yake mata ba
Saidai yanada burin samun 'da namiji
Mahaifiyarta mah 'yar sarauta CE kuma itama ita ka'dai agun iyayanta
Lokacin da tasamu Cikin Khamsa'u alokacin ne iyayanta suka mutu sakamakwan wata cuta da tashiga garin iyayan nata wanda takashe rayuka da dama
Hakan yasa dukkan wata dukiyar mahaifanta tadawo hannunta
Ta haifi 'yarta Khamsa'u suka raini abinsu har girmanta Wanda ayanxu take shekara ishirin da uku

Sunxo sauke faraline saudiya shine Jabiru yaga Khamsa'u suka fa'da qaunar juna

Tun aranar iyayan Khamsa'u suka San da Jabiru
Da sun qita dashi Amma ta bijiremusu Sam
Haka suka rabu da ita bayanda suka iya



Soyayya tayi qarfi tsakaninta da jabiru har magana tayi xafi iyaye suka shiga xancan
Dan koyaushe Jabiru yana hanyar garinsu Harif

Daqar magana tayi qarfi har Allah yasa Khamsa'u taxama mata ga Jabiru
Iyayanta sukace baxai kawo musu 'ya Nigeria ba Saidai ya xauna da ita a qasar Saudi dan tafi kusa da qasarsu
Dake Jabiru ya mutu kan Santa haka ya yarda yasai gida aqasar saudiya suka tare da Amaryar tasa.

Tunda Jibiril yaje yaga maxaunin qanin nasa Jabiru yaga sai hankalinsa ya tashi maqin cikinsa yaci karfinsa nan yafara tunanin Hanyar da xaiyi ya kashe Jabiru danya mallaki dukiyarsa

Lokacin ko idan Jabiru yaqara wayewa dan shiga qasashe da yakeyi shida matarsa Khamsa'u
Nan yasa hannun jarinsa a qasar Kuwait yasaka a England yasaka a American
Wa'yannan qasashe uku dayasa hannun jarinsa sune silar qara ha66akar axxiqinsa
Mutum ne me San temako me ibada da San Allah da Manzansa
Hakance tasa yaware kasu mafi tsoka daga dukiyarsa yaba yayun nasa
Naziru da Auwal ne kawai sukayi farin ciki da kyautar suka dinga murna dasama qanin nasu albarka
Jibiril najinsu yajah tsaki Yace wai murnar mesukeyi dan yabasu 'yan ku'din dabai taka kara ya karya bah
Duk da kallan mamaki suka bishi dashi kana suka hango tarin baqin ciki da hassadace take damun yayan nasu


Wata rana iyayan Khamsa'u suka shirya kawo mata xiyara.
Sai dai basuxo gareta ba jinginsu yasami matsala sukayi mummunan hatsari Wanda duk nacikin jirgin yarasa ransa dan babbakewa sukayi


Sanda Khamsa'u tayi shekara kafin mutuwar tasaketa
Alokacin ne kuma tasamu ciki.....
Wai xokuga murna gun Jabiru
Kowa ya tayashi murna da samun wannan cikin musamman da akayi scanning aka gano 'yan biyu kuma Dukka maxa

Lokacin Naziru yana da 'yarsa Saudat
Auwal kuwa Saida cikin Khamsa'u yakai wata hu'du Matarsa tasamu ciki


Hmmmm
Jibiril yasamu qannansa Naziru da Auwal Yace yanaso subashi ha'din kai su kashe Jabiru da matarsa Khamsa'u dan Su mallaki dukiyarsu
Idan suka mallaki dukiyarsu ya tabbatar wani ikwan Allah ne xaisa suyi talauci arayuwarsu

Sam Naziru da Auwal sukaqi yarda da hakan dan sunasan Jabiru abin duniyarsa bai rufe musu ido bah

Yace toh shikenan shi xai aikata kuma Wlhi suka fidda wannan xance saiya hallakasu suma
Naziru Yace ai Yaya bame harnakawa sai Allah haka kuma baxai baka damar cin galaba akansu ba
Auwal Yace hakane kam
Murmushin mugunta Jibiril yayi Yace xaku gani
Da ido suka bishi Suna mai addu'ar Allah yayaye mishi Baqin ciki

Ana saura wata 'daya Khamsa'u ta aihu tadanqama mijinta Jabiru dukiyarta me tarin yawa Tace yajuya mata
Wata qanwar babanta Amme Salima wacce take Aure anan qasar saudiya da Naziru da Auwal Yayun shi jabiru sune suke da shaida akan mallaka mishi dukiyar tata da tayi
Nan yasa mata Su a hannun jari na qasashen da yake harda
Kuma duk dukiyar tashi da tata yasaka musu Suna 'daya dashi ne mutum yake da damar mallakar wannan dukiyoyin ko bayan ransu
Wato wannan sunan shine sunanta Wato ( *Khamsa'u* )
Indai bada wannan sunan kayi amfani ba kaje kar6ar wani ku'di a American England Kuwait toko in aka kamaka 'daurin rai-rai ne dan ansan ba naka bane

Toh Jabiru ya ke6e da 'yan uwansa biyu wa'yanda ya da'de da sanin SOYAYYAR gaskiya suke masa Wato Naziru da Auwal
Dan haka yagaya Komai akan dukiyarsa data matarsa

Sun jinjina masa kuma suntabbatar masa bamaijin wannan sirrin nasa





.


Ranar ta kasance Asabar mummunar ranah ga masoyan Khamsa'u da Jabiru

Dan Jibiril ya samu nasarar harbe Jabiru qiri qiri acikin gidansa lokacin Khamsa'u tafuta tirenin 'din masu cika nan kusa da gidanta
Aiko tana dawowa taga gawar mijinta alamar kasheshi akayi.
Nan tashin hankali ya sata na'kudar dole
'Yan aikin gidannane suka kaita asibiti
Annan ta haifi RAMADAN da RAMADAN junior

Bayan aihuwarsu da tayi da minti biyu tace ga garinmu nan. Rai yayi halinsa

Kuka Sosai Naziru da Auwal sukayi ganin gawar 'dan uwan nasu da matarsa
Abin takaici Jibiril ya tabbatar musu da cewa shiya kashe Jabiru
Basuyi mamaki ba dan sunsan dama tunda Yace saiya kasheshi ikwan Allah ne xai hanashi aikatawa

Amme Salima tanemi da Jibiril da Auwal Naziru subata 'yan biyun nan Amma sukaqi musamman Auwal dayace shixai 'dau 'daya shi kuma Naziru ya 'dau 'daya
Haka tanaji tana gani suka qi batasu Amma sun bata tabbacin xasu dinga kawo mata Su tana Ganinsu
Tayarda da hakan

Bayan sun rabu ne akan hakan Jibiril ya bu'de musu wutta akan Saidai subashi yaran
Sukuma suka mishi Jan wiya akan baxasu bashi suba ya kashesu
Daqar yasamu kansu suka bashi 'daya bayan yayi musu rantsuwa akan baixai cutar da yaran ba
Su temaka mishi xaisamu me shayarwa ta shayar dasu
Sam sukaqi
Daga baya dai suka bashi 'daya Wato junior RAMADAN qaramin ciki kenan


Yaran sunci suna kamar haka
Muhammad da Sadeeq
Muhammad shine RAMADAN 'din SAILUBAH
Sadeeq kuma shine RAMADAN junior


Sai Naziru ya 'dauki RAMADAN nasa ya ha'da shi da 'yarsa Saudat
Daga baya yasamu khairat



Jibiril dama bashi da niyar kuma kashe junior RAMADAN dan Hakka kawai Allah ya jarrabeshi dasan yaran
Abinda yakeso dai yasamu
Danya samu dukiyar Jabiru
Dangin Su gidajan da filiyan da yasiya a nan gida Nigeria sudai ya samu
Dan baisan da wancan hannun jarin da Jabiru yake dashi a American England Kuwait ba


Tafiya tai tafiya har ya cinye komai. To dama hakkin marayuu ina xai kaisa
Ganin haka yasa yayi wani rikakken 'dan fashi
Anan ya shige harkar
Aikowa yaxama wani Babba a harkar

Tunda ya kar6i junior RAMADAN bai ta6a kawoshi kano ba

Haka 'yan uwansa Auwal da Naziru suke mishi nacin ya kawo musu shi Kullun saidai yadinga turo musu da hotansa

Wata ranah Amme Salima taje gidan Jabiru dan tunawa da 'Yar 'dan uwan nata
Tana binciken kayanta sai kawai taga diarys biyu nan ta karanta na farko taga na Khamsa'u ne
Ta karanta nabiyu saitaga na Jabiru ne
Dan haka saita kaima Alhaji Jibiril har garin Abujah Tace ya ajiyema Su RAMADAN xai musu amfani wata ranah

Toh tunda ya kar6a ya bai ta6a tsayawa ya dubawa ya karanta bah
Saidai yana ankare dasu dan yalura junior RAMADAN 'din yanasan karantawa
Gashi kuma yanasan rigashi karantawa shiyasa Sam yake hanashi 'dauko idan yaxo 'dauka
Shima yana mamakin yanda akayi yakasa tsayawa ya karanta kuma xuciyarshi tahanashi barin junior RAMADAN ya karanta



Alhaji Jibiril ya sakama junior RAMADAN sunan RAMADAN 'din SAILUBAH ne dan in rana ta6aci masa a Nigeria aka gano fashin 'dan nasa yabar garin Abujah Sannan ya rubuta leta mah jami'an tsoro ajan suje garin kano wanda suke nema yanacan
Toh sai Allah ya 6abunta al'amarin


Yabama junior RAMADAN ilimi da kulawa shiyasa Sam junior RAMADAN yataso a shagwa6e saidai akwai aiki da hankali da ilimi
Yana karatu a qasar England inda yakesan xama cikakken doctor
Duk lokacin dayaxo hutune Alhaji Jibiril yake turashi yin fashi da makami


Dan ayanxu mah hutune ya kawoshi Abujah shine Alhaji Jibiril "din ya turashi fashi gidan Dadyn shahuda.



πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―
*SAMAREEN BANAH*
πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―
*TASU SALAN SOYAYYAR*


Junior RAMADAN yaja numfashi dan kammala karanta diaries 'din da yayi

Kanshi ya 'dau caji yagano tabbas mahaifinsu ba mutuwar Allah da Annabi yayi Bah.
Kasheshi akayi.....
Kuma yana xargin Alhaji Jibiril da kisan
Dan rubutun mahaifin nasu yatsaya mai a inda ya gayama yayunsa biyu akan hannun jarin da yasa a qasashe uku
sukace bawanda xaiji wannan sirri nasa

Ya qara jan numfashi yana San sanin ya akayi mahaifunsu ya mutu da mahaifiyarsu
Dole yaje ga Dadyn brother 'dinnan nasa yaji ya abin ya kasance


Wanka yayi yayi. Sallah kana yabi lafiyar gado da tunanin Yayan nasa RAMADAN ko yanxu an sake shi ko ba'a sakeshi ba oho
Koma miye yabarma awa 'daya kacal...πŸ‘ŒπŸ»
Idan yatashi yaji komai.....


Yusra CE take yunqurin shiga gidansu
Wani saurari ya tareta yana fa'din sannu 'Yan mata Tace Yauwa
Yace dan Allah dama RAMADAN anan gidan yake
Tayi Murmushi kun san Yusra da surutu nan tafara mai xuba kamar kanya Tace ayya Ya RAMADAN ai 'dan kano ne ya kawoma Momyna da Dadyna da kuma wata Auntynsa SAILUBAH xirayane
Ina sanshi Sosai
Yace ayya haka kawai naji ina sanshi nima inasan inyi abota dashi ko xakiban adireshin Sa na garin kano
Tayi dariya Tace Sosai mah. Ina lefin me sanka
Nan taxage tagaya mai Komai akan RAMADAN Wanda ta'dan sani
Tana cewa Wlhi xakaji da'din abota dashi dan yanada hali mekyau
Yace Allah qanwata
Tace Wlhi da gaske
Yayi Murmushi dayi mata godiya har yana cewa in tashiga tagai sheshi kuma tace mishi zaixo anjima
Ta gya'da kai Tace toh ta shige ciki
Kana ya tafi yana mamakin magana irin nata

Senior RAMADAN na bacci Yusra ta tadashi
Yace matsala ya akayi
Tace hmm wani ne ya tareni daxan shigo gida wai Yana sanka yana San yayi abota dakai
Na bashi bayanai akanka Sosai
Yace me kika sani akaina
Tace abubuwa da yawaπŸ˜€
Yayi Murmushi Yace ko
Tace Sosai mana
Yace angaisheki jeki ha'damin Lipton
Tace aha Yayana
Tafita. Yabita da kallo

Batafi minti uku ba saigata da Lipton 'din
Yace nagode Tace dame fah
Yace haka dai
Tace Allah bana so ka dinga min godiya idan na maka abu
Yace dalili
Tace nima hakka dai
Ya mata Murmushi kawai batare da Yace Komai ba



Junior RAMADAN ko yana tsaka da baccinsa yaransa suka tasheshi

Yace dafatan kun gano min shi
'Daya daga cikinsu Yace eh Amma ba dukkan labaran ba dan wasu sai sunkai gobe
Ayau Inuwa ya tafi garin da yake Kano
Dan ya sami bayanai agun wata yarinyar gidan daya sauka anan Yusra
Ta tabbatar mishi sunansa RAMADAN kuma agarin kano yake da xama awata unguwa Fage
Na tabbatar maka xai gano maka ko shi Waye
Yace gud... Hakka nakesan jiii......
Wani acikinsu Isma'il Yace oga naganshi 'daxu akofar gidan Alhaji Aminu
Junior RAMADAN Yace Waye kuma shi
Yace wani 'dan kwungiya ne ba abinda bayayi
Cikin mamaki junior ya tashi Yace toh meya ha'da 'dan uwana dashi
Yace eh toh. Idan kana buqatar sani yanxu xan binkicuma
Yace dako naji da'di

Haka Isma'il yaje ga megadin gidan Alhaji Aminu
Yacika shi da ku'di akan yanasan yasan me yakawo RAMADAN gunsa 'daxu
Yace aidama sunansa RAMADAN
Isma'il Yace eh
Nan ko megadin ya gayamai Komai akan 'Yar uwarsa Alhaji Aminun yake Aure kuma ya hanata jin kowa nata

Nan dai da Isma'il ya samu abinda yakeso yayima megadin sallama ya tafi
Shiko yanata murna yau sai samun ku'di yake


Direct Isma'il ga junior RAMADAN yaje
Anan yagaya mai Komai

Junior RAMADAN yayi Murmushi Yace aha
Yana San ya futar da ita daga gidan ne
Dan shi da ita sungano ko shi Alhaji Aminun Waye

Isma'il Yace idanko haka ne ya kamata kasa mishi hannu oga dan baxai iya fidda ita daga wannan gidan bah
Yace Hakka Amma ya xanyi in gansa shi Alhaji Aminun

Isma'in yace nasan wani hotel da yake xuwa cin abinci qarfe takwas na dare

Junior Yace gud...βœ”
Ina san gobe da qarfe takwas 'din muyi ram dashi dan wlhi saiya saketa dan ubansa.....
Isma'il Yace angama oga..

Washe gari ko kusan qarfe biyu RAMADAN yayi parking 'din motarsa a 'kofar gidan Auntyn tasa.....
Kamar yanda megadi yace mai xai jira xuwansa hakance ta kasance

Yace Barka da ranah me baba
Yace barka dai samari
RAMADAN yamiqa masa ku'di da wani abu acikin Leda Yace wannan xaka bata Yace Amma ku'din yau yafi na jiya
RAMADAN yayi Murmushi Yace aikai ka buqaci aqara maka farashi
Ya washare baki Yace ashe baka manta ba samari
Yace ai dama bai dace na manta da hakan ba dan ayanxu ba abinda yafika mahimmanci arayuwata kamarka
Dan kaine kake sadani da abinda yafi min Komai arayuwata
Megadi yayi Murmushi Yace kanasan yayarnan taka
Yace fiye da Komai mah
Nan dai megadin ya shige......

SAILUBAH na xaune tana kallo lokaci lokaci tana kallan agogo addu'arta Allah yasa taji qanin nata yanxu
Kamar yanda take fata ko sai ganin megadi tayi
Tace yanxu naketa sake saken xuwanka
Yamiqa mata ledar hannun nasa cikin ladabi
Ta kar6a jiki na rawa
Tana bu'de ledan taga wata qaramar wayar RAMADAN ce
Farin ciki kamar ya kasheta Tace shikenan babah megadi jeka
Yatafi yana Murmushi har yaxo ga RAMADAN.

Yace nabata samari
Yace Yauwa toh sai anjima
Yace gobema xaka dawo
Yace eh toh bandai saniba amman karka damu
Yace toh nidai ina saurare

Murmushi RAMADAN yayi yaja motarsa
Yana tuqi yanata ganin kiran Auntyn tashi
Amma yaqi 'dauka dan yana san sai yakai gidan kawun nasa ya 'dauka yafi jin da'din magana da ita




Yana kaiwa ko ya shige bet room ya baje agado.
Xai kirata kenan Amar ya shigo 'dakin Yace brother ya kamata yau mu 'dan xaga gari
Yace toh bara inji nutsuwata sai muje
Amar yayi dariya Yace toh kafito lafiya
Yace Allah yasa

Kiranta yayi Yace Auntyna
Tace naji dadi Sosai Wlhi
Yace nasan xakiji da'din yanxu bani labari
Tace farkwan labarin shine kaci abinci
Yace eh toh bandaici na yanxu ba Amma naci na safe
Cikin sanyi Tace kaci pls
Yace Wlhi Auntyna konasaka agaba inna tunoki kasaci nake
Tace wayyo Qanina kaci dan Allah kasanfa bana san xamanka da yunwa
Yace nasani
Kinga nasami wata mafuta guda 'daya....
Tace toh fa'di inaji
Yace mexai hana ki'dan roqeshi ya kaiki ko gidan matar abokinsa ne
Kinga daga nan sai musan yanda xamuyi yanda bazaki koma gareshi ba
Tace Yauwa kakawo shawara. Amma matsalar 'dayace ko ganinsa bana san yi natsaneshi bana qaunarsa.
RAMADAN yaja numfashi Yace kidaure my Aunty Wlhi nayi missing 'dinki sosai ina buqatarki kusa dani
Tace nice nake buqatarka RAMADAN. Ka shagwa6a ganina da ganinka. Ba abinda nakeso ayanxu kamar in ganni gani gaka Qanina
Dan Kullun sai nayi mafarkinka.
Yace Allah Auntyna
Tace Wlhi Qanina
Yace toh kiyi abinda nasaki
Tace toh kaci abinci pls
Indai kanaso nasami nutsuwata
Yace angama my Aunty bye-bye den luv u
Tace love you more my futuna.....
Da Murmushi ya waro ido😳 Yace nine futuna ko
Tayi Murmushi cikin sanyi Tace ko yanzu ganin bani kusa ka dena ne
Yace idan kika dawo xan 'dora akan inda natsaya
Tace aha.
Bana gajiya da hira dakai Qanina
Yace nima haka Auntyna
Tace kaci abinci yanxu bayan ka gama muci gaba
Yace Owkie





Da misalin qarfe biyar inuwa ya kawoma junior RAMADAN rahotan Komai na RAMADAN
Da yanda yake dasu KHAMIS da FAWAS da yanda ya shaqu da Auntynsa SAILUBAH
Komai dai sanda junior RAMADAN yaji
Yayi Murmushi kawai

Qarfe takwas ko nayi na dare junior RAMADAN sukama Alhaji Aminu dirar makiya
Yana Cikin 'dakin da Yakama a hotel 'din
Junior RAMADAN da Isma'il suka buqaci ma'aikacin wajan daya gaya musu wane 'daki yake
Da farko Yace dokace ba'a fa'din inda mutum yake a hotel
Amma dayaga ku'di ai bashiri Yace musu yana 'daki mai number goma Sha shidda
Haka ko sukaje gareshi
Kofarma abu'de take
Sai kawai suka shiga suka dannama "kofar key
Alhaji Aminu Wanda yake cin abinci ga wani saurayi najiranshi yagama sufa'da masha'a. Sai kawai yabi junior RAMADAN da kallo
Cikin mamaki Yace RAMADAN meya kawoka nan

Junior RAMADAN yayi Murmushi ya 'dora qafarshi 'daya a table 'din da yake cin abincin yana juya bindiga Yace abu 'daya ne ya kawoni

Cikin tsoran yanda yake juya bindiga Alhaji Aminu Yace miye shi kuma meyasa naganka cikin wannan yanayin bayan nasan kaime nutsuwa ne gashi kamar ba imani atattare dakai

Junior RAMADAN Yace au haba
shege Alhaji dama kasan imani kake kashe qananan yara kake 6ata maxaje da ma'digo
Kake cikin kwingiya shan jini

Alhaji Aminu yayi shuru ya bishi da ido da mamakinsa da kuma tsoran yanayinsa

Junior yaci gaba da fa'din. Toh dan ubanka idan kana iskanci mu asamanka muke
Duk da bama ko 'daya acikin abinda kakeyi Amma nafika iskanci Wlhi

So nake kasaki SAILUUVAH.......
Sai kuma ya kalli Isma'il Yace Hakka sunan yake ko
Da Murmushi Isma'il Yace eh haka yake oga Saidai naji da'din yanda a ambaci sunan da alama kafi kowa iya fa'dar sunan
Ya tabe baki da maida kallan ga Alhaji Aminu Yace nima haka kawai naji sunan yayimin idan na ambaceshi inajin da'dinsa abakina Sosai
Alhaji Aminu Yace baxan iya sakinta ba.............
Aikam ya qarasa furucinsa junior RAMADAN ya sakar masa harsashi 'daya a kafa'da
Nan Alhaji Aminu yasaki wata furgitacciyar qara yadafe gun tare da tashi yajah baya cikin tashin hankali da tsoro
Junior Yace Shege angayama ana yimin musu ne acikin wannan yanayin da nake ciki
Kayi kuskure
Tayaya xa'ayi ka Auri yarinya ka ajiyeta batare da kana mata amfanin Komai ba
Ko An gayama ita 'din bishiyace da xata rayu haka bajin 'dimin mijinta kusa da ita.

Cikin maseefar tsoro Alhaji Aminu Yace na roqeka da Allah karka kasheni inasan rayuwa ban gaji da ita ba.

Yace toh naji
Yanxu so nake kasaketa Cikin daran nan
Gobe kuma kinji barinta gidanka da misalin qarfe goma
Idan ba haka ba Wlhi kaji na rantse yanda nabaka wutta a kafa'darka haka xan qara baka a cikin xuciyarka

Ya fa'din haka ya fitta daga 'dakin Isma'il yabi bayansa

Iya tsorata Alhaji Aminu ya tsorata da junior RAMADAN
Jikinsa na rawa ya sallami wannan saurayin dan badamar aikata abun nasu yana cikin jini.
kana ya 'dora suwaita akan rigarsa shima ya fitoh dan xuwa ga doctor ya cire mashi harsashin

Bayan angama mishi Komai ya xauna hutawa kafin ya nufu gidan nasa.


Junior RAMADAN ko da qarfe goma Sha 'daya ya kwanta dan jiyayi kansa nayi masa ciwo

Baiyi nisa a baccin bah yaran nasa suka tashe shi
Ya qare musu kallo ba Isma'il aciki
Yace kunxo kashe ninne kamar yanda yasaku ranar
Suka kalli junansu
Kana sukace ka yafe mana oga mun amsa mishi da xamu aikata hakan
Saidai baxa mu iyaba musamman idan muka tuna halaccinka garemu
Yace gud ashe Ku 'ya'yan halak ne.
Kunyi kyan tunani
duk da ban ta6a kisa ba. Da ace bakuyi wanna tunanin ba dako nafara kisan akanku

Kuje gareshi kuce mishi baxaku iyaba shi yaxo da kansa ya kashenin

Haka ko suka juya suka fitta
Yabisu da kallo

Alhaji Jibiril 'din yana falansa suka gayamai baxasu iyaba

Yajah numfashi Yace hmm nasani baxaku iyaba. musamman idan kuka tuna alkairan da yakema iyayanku.
Kuje karku damu xansan yanda Xanyi dashi.




Alhaji Aminu Lokacin da ya'isa gidansa qarfe 'daya ne na dare
A bet room yaga SAILUBAH tana Sallah
Ya xauna harta idar
Tabishi da mugun kallo Tace lafiya
Yace itace takawoni
Dama 'dan uwanki Shegen Yaro ne
Tace duk da bansan wa kake nufiba nasan ko kusa bashi da kwatankwacin hali irin naka. Karka qara kiran wani nawa da shege. dan kaine shegen. 'dan iska. Fasiqi. mugu axxalimi. Mara imani me kashe qananun yara batare da tausayawa ba.....

Yace na sakeki saki uku
Da sauri SAILUBAH Tace Alhamdulillah
Nan Tatashi da sauri Tace muje ka fuddani daga wannan qaxamin gidan naka
Ya tashi Yace xaki fitta Amma sai gobe da qarfe goma
Yana fa'din haka ya fitta

SAILUBAH tajah numfashi taxauna takira RAMADAN dan bashi labari
Saidai taji wayan akashe bayan yanxu suka gama waya tata6e baki da tura masa message
Kana takwanta bayan tatufe ko ina da addu'a






Washe gari ko tun qarfe 6:00pm tayi wanka taxauna xaman jiran qarfe gomah
Alokacin ne RAMADAN yaga sakwanta
Cikin farin ciki ya kirata ta'dauka
Yace Auntyna da gaske
Tace Wlhi har yana cewa qarfe goma xai barni na tafi.
Yace alhamdunillah
Yanxu kinga bara nafara shiri sai na musu sallama daga nan sai naxo kawai mu wucce
Tace toh ina jiranka Qanina
Yace Aha my Aunty
Kana ajiye wayan ya kalli Amar Yace yau xantafi fah
Da mamaki Yace mai yau
Yace yah. Da barin 'dakin
Amar ya bishi da kallo

Anan falan ya tarar da Momy da kawun nasa Yace dad mum kumin afuwa yau xan koma gida
Suka CE lafiya Yace Wlhi qalauπŸ˜€
Auntyna CE xata gida yau shine naga dacewar mutafi tare
Sukace Amma bamuji da'di
Yace hmm aixan qara dawowa ne
Dad Yace kan kadawon ai saika ibi shakaru
Mum Tace qilama sai Auransa in munje ma gansa kawai
Yayi Murmushi Yace kai mum
Tace eh ai gaskiya ne
Yace toh bara naje in sharya xuwa 9:30am nakesan tafiya
Mum Tace toh Allah ya nuna mana lokacin
AmEEn dad Yace
Yusra Tace gaskiya banji da'di
Yace Karki damu qanwata ina tare dake ai







Junior RAMADAN da Isma'il ko qarfe 9:00am dai-dai tayi musu ne qofar gidan Alhaji Aminu
junior ya matsar da motar tashi can gaba yanda xaiga fitowar SAILUBAH da xuwan Yayan nasa
Yace naxa'ku naqara ganinsa
Isma'il Yace ai yanxu haka ma qila yana hanya
Yace Wato Isma'il Wlhi kallo 'daya namishi Naji qaunarsa cikin raina
Yace sai shima ya ganka na tabbata saiyaji sanka fiye da yanda kaji nasa
Yace Allah yasa
Haka suka dinga hira har xuwa lokacin da Senior RAMADAN ya iso
Ya fitoh daga motar tashi yana kallan agogo
Junior RAMADAN ya qura masa ido tabbas ya ha'du sai kace ba tashin Nigeria ba ya iya wanka
Isma'il Yace hakane.

Kiran Auntyn tasa senior RAMADAN ya hauyi
SAILUBAH da take xaune xaman jiran lokaci ta'dauka ashagwa6e Tace kaga goman batayi ba ko
Yace xatayi Auntyna fatana kina cikin shiri Tace eh Amma......
Bata qarasa furucin nata bah Alhaji Aminu ya shigo falan ya wulga mata takaddarta Yace asauka lafiya
Tatashi da sauri ta'dauka tabi bayansa. Har xuwa wajan megadi
Inda Alhaji Aminun ya bashi umarnin ya bu'de mata kofa tafitta.
Tana fitowa tayi ido hu'du da qanin nata
Aiko taje da gudu ta rungumeshi..........
Yace Auntyna atiti nefah😳
Tadaki qirjinsa ka'dan da dariya Tace ko a inane yanda nake cikin farin cikin nan Wlhi rungumarka Xanyi
Tace toh sakeji dan najiki da yawa karna shiga wani hali in 'dauka budurwata CE
Ta sake shi da harararsa Tace xamfah jimaka
Yace idan kika jimin sai kiyi jinyata
Tata6e fuska Tace yunwa nakeji Qanina
Yace idan kikamin kuka xaki jefani atashin hankali
plsπŸ‘πŸ» 'dan rage ragwa6ar ka'danπŸ‘ŒπŸ»
Ya fa'da da ha'de hannunsa biyu alamar roqo da kuma rage mata ido 'daya
Tayi Murmushi Tace kaiπŸ‘ˆπŸ» xaka fara kashemin jiki ko
Yayi Murmushi da bu'de mata mota yana cewa abinda ya dace ne my Aunty
Tashiga tana fa'din xanko hukuntaka
Ya tada motan yana cewa ba damuwa ai indai hukuncinki ne nafi kowa buqatarsa
Tace kaji dani pls
Yace ina ji dake Auntyna.
Ga wani dambun nama nan da mum tabani ha'de da cake kamar nasani nafitoh da drink 'daya
Tace yauwa Qanina...
Yanxu can muka nufah ko
Yace eh Kanon dabo timbin giwa ba......
Ta kalleshi da Murmushi tanajin da'di Tace wannan motar fah
Yace Kinsan jirgi nabiyo. Yanxu kuma nace Amar yaban motarsa kawai
Dad Yace na'dau 'daya daga cikin tashi
Tace lallekam motar tayi kyau.....
Ya katseta da fa'din karkisa na riqe fah
Tace ni bance bah
Yace watoh har sake baki kikayi kika qara kyau acanko
Tace toh yaxanyi dakai kaifa kabini qardin gwiwar hakan.....

Dan Allah Auntyna kinutsu kigayamin komai cikin nutsuwarki.
Ba haka kace ba.
Ta qarashe da kallansa tana dariya
Yabita da kallan jin da'di

Yace kin manta da kuka kike cemin dan Allah kaxo ka'daukeni Wlhi kasheni xaiyi dan Allah Ni dai kaxo kawai ka 'daukeni.....
Ya qarashe da kwaikwayan muryanta
Ta kallesa ka'dan suka sheqe da dariya a lokaci 'daya☝🏻

Dai-dai nan suka wucce

Please Login or Register in order to submit comment