Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sani farin ciki ayanxu
Ta girgikai alamar aa
Yace ki'danyi min kiss
SAILUBAH tayi Murmushi Tace na lura kwanan nan iskanci kakeji ko dai junior ya koya maka ne
Yayi Murmushi Yace aa nidai kimin in tafi

Takama fuskarsa tamai agoshi
Tace toh shikenan
Ya 'daga mata kai.
Kama hannunsa tayi takaishi har bakin get 'dinsu Tace toh saida safe
Yabi bakinta da kallo Yace pls Aunty
Tace miye kuma ko wani........

Bai bari ta qarasa ba taji bakin shi cikin nata ya sakar mata kiss.....

Kanta tattaro nutsuwarta sai ganinsa tayi a'kofar gidansu yana 'daga mata hannu alamar bye bye
Ta gallamai harara da juyawa cikin gidan nasu tana tunanin waye iskanci ne yake damun RAMADAN ne yanxu nasan yadinga kissing 'dinta

Har takwanta tunanin bai barta ba
Can xuciyarta tafara hararo mata wani abu saidai tsoro da fargaba sun hanata kar6ar abin Amma tasa aranta zata nutsu dakyau dan ta hararo abinda xuciyar tata ta hararo mata.........




Wayarta CE tayi qara tana dubawa taga shine
Cikin mutuwar jiki ta 'dauka da cewa ina jinka
Yace ina miki addu'ar yin tunani me kyau da samun bacci me tattare da samun cikakkiyar nutsuwa
Tace nagode Amma meyasa kake san kissing 'dina

Yayi mata shuru yana tuno lallausar le6anta

Ina jinka. Takatsemai tunani

Yajah numfashi cikin sanyayyiyar murya Yace Aunty Allah yayi miki baki me kyau
Akowane lokaci idanuna akansa suke

Nima xuciyata CE take tinxorani akan namiki kiss 'din

Nasha gwada qin bin umarninta ina daurewa. Amma ayanxu abin yaci qarfina Auntyna....
Idan bam miki ba hankakina baxai kwanta bah.
Pls kayi hakuri Xan gaba da 'daurewa kamar da. wayan ganin banqara yi miki bah

SAILUBAH tajah numfashi jikinta yayi sanyi
Saita kashe wayar kawai batare da Tace mai Komai bah

Senior yayi murmushin jin da'di dan yasa aranta yanxu yadena barin abubuwa aransa xai dinga gaya mata dan yagaji 6oye mata kansa tunda ita takasa ganewa

Cikin qarasan jin muryarta ya qara kiranta

SAILUBAH data fa'da tunani taqara ganin kiransa
Ta 'dauka a sanyaye
Yace Aunty kinyi shuru bakice Komai ba kuma kin kashe waya.
Tace toh mexance maka
Yace toh inxo in gaya miki abinda xakice min.
Tace aa saida safe
Yace Aunty......
Tayi saurin katseshi da cewa plx kabarni nayi tunani dan Allah
Yayi Murmushi Yace tunanina xakiyi xakiyi ko Aunty

Tace ban sani bah
Yace Allah ya baki hakuri saikin ganni cikin mafarkin ki...
Yana fa'din hakan ya kashe wayar da gyara kwanciyarsa

Junior yiyi Murmushi shidai baisan yaxaiyi da ransa akan Yayan nasa da SAILUBAH bah
Yasani baxai ta6a samunta bah.....
Shiyasa ya fara yakiceta aransa
Amma kamar tinxira xuciyar tashi ake akanta
Allah kabani mafuta
Yafa'di hakan a bayyane
Senior Yace meyake damunka Yace SOO
Yace nawa
Yace nawata CE
A ina take
Nima bansani ba
Toh Allah ya baiyana maka ita
Yace AmEEn



Washe gari bawani jin Komai
Da Senior yagama xubama SAILUBAH shagwa6a kala kala. Saiya qare da manna mata kiss
Binshi da kallo tayi dan kwakwalwarta ta tushe tarasa wane tunani xatayi akansa. Tana kallo ya fice cikin jin da'din yanda ya daskarar da ita



FAWAS KHAMIS Senior RAMADAN
Sun ha'du dan tattauna yanda sukayi da iyayan nasu


Sosai KHAMIS ya nutsu a qawataccen ofishin nashi yana jin yanda mahaifin nashi yake gaya mishi yanda xai tafiyar da harkokin kasuwancin nasu

Haka ma FAWAS....

RAMADAN ma mah kallo 'daya yayima masana'antar Dadyn nasu yasan baxaisha wahalar da yake tunani ba
Sosai ofishin nasa ya burgesa
Yace Dady ina ganin jibi xan fara xuwa aiki
Junior dashima ya rakosu
Yace xan dinga rakoka kan lokacin tafiyata yayi
Sosai Dadyn nasu yaji da'di
Yace Allah yayi musu albarka
AmEEn sukace



XEE da KHAMIS da suka ke6e ba qaramin murna ga junansu suka nuna bah
Dan ganin sunkusa xama mallakin juna

A washe garin ranar Senior RAMADAN da KHAMIS suka raka FAWAS qauyan takai

Sosai HAMEEDA tanunamai jin da'dinta na suma sun kusa zama mallakin juna



Dadyn RAMADAN da Qaninsa Dady Auwal sunsami nasarar kar6oma Senior RAMADAN da junior RAMADAN dukiyarsu tagadan mahaifansu na qasashe biyu Wato Dubai da Kuwait


Dake junior RAMADAN yasan kan ku'da'de ba qaramin mamakin jin wayan ku'din da yayi ba

Senior ko baiji Komai bah
Dan shi Sam harkar ku'di bata dameshi bah
Damuwarsa ya mallaki Auntynsa yabata kulawa ya kuma cika mata burinta nasan Auran me ku'di 👯




Sosai FAWAS da Senior RAMADAN da KHAMIS suka qara xama manyan yara
Dan Komai nasu namasu aji sukeyi

Ku'di da qarin nutsuwa da sanin rayuwa yafara ratsasu


*** *** *** ***

Rayuwa kenan. Yau taxo maka da da'di gobe sa6anin haka...


SOYAYYA tsakanin KHAMIS da XEE sai wacce taqara bunqasa

Haka tsakanin FAWAS da HAMEEDA sai wanda yagani


Junior ko Sosai yake jinyar kansa
Dan SOYAYYAR SAILUBAH taxamemai MASEEFAR SOO
Kullun a baccinsa ganin shi da ita yake a wannan birnin na BIRNIN MASOYA
Toh ya xaiyi da wacce ya temaka kwanakin baya ahannunsu Mubarak
Wacce tanace mishi da kira da magiyar soyayyarta
bayan yagano itadin 'Yar qauye CE 'dan xama ne ya kawota gun yayarta birni
Shin 'yan DUNIYAR MARUBUTA ya dace ya ha'da SOYAYYAR 'YAR QAUYE DA 'YAR BIRNI
Ma'ana ya ha'da soyayyarta data SAILUBAH
Kai baxai yuhuba agareshi shidai SADEEQ abin da kamar wiyu ya ha'da son da yakema SAILUBAH da wata 'diya mace duk dako yasan baxai sameta matsayin matarsa ba
Saidai yana addu'ar Allah ya bashi me kama da ita koma wacce tafita
Dan gaskiya baxai iya da MAKIRCIN 'dan uwansa ba
Toh kodai yanemi shawara agun HAYATUDDEEN ne
Hmmmmmmmmmm

Yaja numfashi Yace Allah yasa naxama LEEKITAN ZUCIYAH dan nagyra tunanina
Tare da cire soyayar SAILUVAH araina

Ni Rahamat Nace AmEEn my RAMADAN😰

Sam kuma junior bai dena tsugama SAILUBAH rashin kunya bah
Danko bata kulashi bah saiya kulata......











😀😀😀😀

Tam😀 inji yara suka tam... Memakwan toh

Komai yayi daidai dan yanxu qiri qiri senior RAMADAN yake nunamah SAILUBAH iskancinsa

Itadai tagaji da kissing 'dinta da yakeyi na baxata
Dan kullun cikin tunaninsa take
Gashi baya shakkar gaya mata duk kalmar data fitoh daga bakinsa
SAILUBAH ta lura daga cikin xuciyar kalaman suke fitowa
Ya mai da ita tamkar *budurwarsa*

Wannan abu na damunta
Tayima XEE maganar
XEE dai shuru tamata
duk da tasan me Senior yake nufi dayi mata hakan.
Amma tashareta taqi CE mata Komai

Kamar yau junior ne yagama shirinsa tsaf na tafiya England dan kumawa karatu. Hutunsa ya qare

Yanxu haka Suna airport Dady da Momy da FAWAS KHAMIS
Senior harda SAILUBAH
dan Momy tanemi rakiyarta
Tace itafah baxata bah junior yayi Murmushi Yace dan Allah Aunty idan kikaqi xuwa brother baxaiji da'di
Ta harareshi Tace hmmm kaci darajar Momy da Yayan naka
Murmushi kowa yayi ahaka suka tawo


Hawaye Senior yake tayi danya saba da 'dan uwan nasa 'dan xaman da sukayi ba qaramin sabu yayi da 'dan uwan nasa ba

Murmushi junior yayi Yace haba brother kaxama jarimi mana.
Dan namiji kamarka baidace ace yana hawaye bah
Bayan ina tare dakai
Yafa'di hakan da bugar kafa'darsa
Murmushi Senior yayi Yace dole nayi hawaye 'dan uwa. Nasaba dakai
Pls karka tafi
Junior ya dafashi tare da bashi kiss a hannu Yace tafiya taxama dole brother

Nidai fatana kadinga kawomin xiraya
Yace Insha Allah

Kama kumatunsa junior yayi Yace tab kumatunka sunfi nawa girmah ashe😳
Dole senior yayi dariya dama haka junior yake son gani
Senior ya lakuce mai hanci Yace qaryane Bayan nagano mah nafika kyau nesa ba kusa bah
Yayi dariya Yace tab kafini kyau aina dinga xuwa gun Auntyna Rahamat tanamin gyara dan nafika kyen Kasan tafi'sona
Yace hmmm ruwan ido ne da ita ai da farko ni tace tafiso
Momy Tace wacece Rahamat
Dady Yace wata Auntynsu CE
Tace shine bansanta bah
SAILUBAH Tace Karki damu Momy xan baki labarinta
Tace ya kamata kam 'yata

Rungumar juna Senior da junior sukayi dan jin ankira sunan junior

FAWAS da KHAMIS suka tafah har Suna ha'da baki wajan cewa abin sha'awa

Haka sunaji Suna gani junior yatafi ya barsu kamar yanda yaxo ya samesu

Haka KHAMIS yashige motarsa
FAWAS mah yashige tasa
Momy da Dady mah suka shiga tasu
SAILUBAH takama hannun RAMADAN suka shige motarsa
Yace AUNTY ki iya mota pls
Tace toh xan iya.

A haka suka dawo tare da hirar junior RAMADAN
Dady ya kalli momy Yace nan da sati biyu xan kai mishi xiyara
Tace Allah ya kaimu saina rakaka ai....



RAMADAN na parking SAILUBAH tanemi fitta
Da sauri RAMADAN Yace Aunty......
Tace miye
Yace yanxu haka Xaki tafi kibarni cikin wannan halin. Baxaki tsaya Ki samarmin nutsuwa ba.
Yafa'da da tsaida idanshi qir akan bakinta dan yasan ya tsokanota.
Kuma kallan bakin nata xai mishi da'di idan tafara sauke mishi maseefa

Aiko gallamai wata muguwar harara tayi Tace iskancinka Yafara isata RAMADAN wai me kakeso na xama maka ne
*_MATATA KUMA UWAR 'Ya'Yana_*





Bai bari furucin nasa ya fitoh fili bah
Dan haka ganin yamata shuru shiya sata cigaba da fa'din
Kamai dani 'Yar iskar ka
Saina dinga maka kiss kamar wata matar ka
In 'iskanci kakeji kafudda 'daya daga Cikin 'yan matarka mana amaka Aure da ita mana. Amma dake ni........








Cak tatsaya da maganarta ganin duk maseefar da take masa bakinta kawai yake bii da kallo
Tajah numfashi dasan ficcewa daga motar dan yanxu tatabbatar RAMADAN yaxama 'dan iska. Gawani shegen kwarjini da yake qara yimata
Kuma yarasa wacce xai saukema iskancin nashi sai ita...

Gam taji 'kofar motar akulle taqi bu'duwa
Ta juyo da kallanta gareshi afusace Tace kabu'demin in fitta

Cikin sanyi da shagwa6a Yace Wlhi baxan iyaba Auntyna
Dan xuciyata bugawa take fat fat fat akanki....

Tace toh ina ruwana

Yayi Murmushi Yace da ruwanki mana dan kika bari ta fashe Wlhi kamaki xa'ayi dan kinyi kisa aSO❤
Ta gallamai harara tare da Jan tsaki Tace mukwana ahaka
Dan Wlhi na dena maka kiss har abada
Yace Wlhi baki isa bah....
Ta kallesa da sauri
Ya watsa mata wani narkakken kallo Wanda ya tabbatar ya gabama da duk wani ruwa da jini na jikinta

Tum ba yau ba SAILUBAH tasan wannan kallan nasa
Ta tabbatar idan ya aika mata dashi gamawa yake da ita

Yace Auntyna Kiyi hakuri baxan iya kwana a haka dakeba
Idan kin matsa lallle sai hakan. Toh ba mamaki in'miki abinda harki mutu baxaki dena jin tsanata aranki
Ina sanki Auntyna banaso hakan ta kasance
Pls kiyi abinda Nace miki kawai.....

Cikin wahalalliyar murya
Tace kana cutar da xuciyata RAMADAN.
Har takai yanxu nadena gane kaina.
Kanajin da'din tarwatsamin tunanina
Me kake nufi danine

Yayi murmushi Yace nima ban sani bah Auntyna
Abinda nasani ayanxu kawai shine kimin kiss nasami nutsuwata

Dan tun farko ke kika shagwa6ani akan kiss
Bini bini duk abinda namiki kikaji da'dinsa saiki kaimin kiss

Toh yanxu lefine danna nuna ba abinda xakimin in samu nutsuwata sai shi......
Ya qarashe da matsowa kusa da ita ya kama fuskarta idanshi cikin nata Yace 'Yan mata da yawa masu kyau da aji da wayewa 'yan yara masuji da quriciya Suna bina Suna Sona Amma me yasa wawiyar xuciyata bata ta6a ganin kyawunsu da ajinsu ba saike Auntyna
Me yasa me yasa Auntyna
Yana maganar idanshi akanta lokaci lokaci yana kallan bakinta

Inasan rayuwa dake Auntyna
Ina San nasami farin ciki agunki Auntyna
Inasan nasamu 'Ya.....
Bai bari ya qarasa ba yakai bakinsa cikin nata ya sakar mata da shock kiss 'din da ayanxu ya sabar mata
Yanayi kuma ya sake mata fuskartata

Sam baiyi gigin qara ha'da ido da itaba


Ixuwa yanxu RAMADAN yafara ba SAILUBAH tsoro
Kamarya asirceta san indai yakai hannunsa jikinta toh Komai nata ya dena aiki kenan harsai yagama yimata kalaman iskancinsa acewarta yasaketa Sannan qarfinta ka'dan xai dawo👌🏻

Yau tahango bala'i😳 a idan RAMADAN
Tabbas San Aure tagani a igadanshi
Hankalinta ya tashi

Dan haka Tace me kakeso RAMADAN
Cikin sauri Yace *Aure*....
Tace toh xansa Momy da Dady su maka
Sai kadena sauke isakancinka akaina
Yace Yauwa. Dako kin temaken dan in baki sasu sun min bah Wlhi NI DAKE a hakka xamu qare rayuwarmu

SAILUBAH tawaro ido 😳 Tace wai yaushe kaima ka xama 'dan iska ne.

Yayi Murmushi tare da bu'de motar ya fitta.
Sannan ya xaga ya bu'de mata motar tah fitoh
Suka ha'da ido ya sakar wannan kallan nan nasa dan yanaso ya barta da tunaninsa
Yace dama a 'dan iska nake Auntyna bana nuna mikine da dan wani ra'ayi nawa.
Amma yanxu baxan iya bah 6oyewa ba dan nalura ke'din bagane Komai kike bah.......

Bata kulasa ba. Tayi cikin falansu dan tasan in tatsaya bashi amsa ba makawa saiya qara kaima bakinta wani kiss 'din
Dan talura da yanda yake qarema bakin nata kallo


Shiko RAMADAN Murmushi yayi Yace Xanyi maganinki ne.....
Ya shige motar tasa yayi office xuciyarsa cike da tunaninta dana junior


SAILUBAH Sallah tayi ta'daga hannu xata roqi Allah akansa Amma saita mance memah xatace
Dan haka sai tatashi kawai tanufi gidansu
Afalo tatarar da momynsa
Tace Momy naxo miki da wata magana ne
Tace ina jinki SAILUBAH fa'di
Tace Wlhi Momy ayima RAMADAN Aure yanxu
Dan na lura akwai abinda yake damunsa

Momy tayi Murmushi Tace ya fara nuna miki ko
Shuru SAILUBAH tayi tafa'da tunanin yanda yake nuna mata iskancinsa


Momy ko bin SAILUBAH tayi da ido. tana tunanin itadai tana hango soyayyar SAILUBAH a idan RAMADAN
Gashi ita SAILUBAN har yanxu bata gane soyayyar da yake yi mata ba.

Cikin nutsuwa Momy tacigaba da fa'din. Inaso Ki lallasheshi cikin nutsuwa harya gaya miki wacce yake so
Dan munan munyi munyi dashi ya gayama mana wacce yake so Yaqi fa'da
Kinga in ke kika lallasheshi qila ya gaya miki
Shikenan saimu masa Aure
Toh SAILUBAH Tace


____

Dare nayi ta nemeshi.

Suna ha'duwa takama hannayansa Tace plx RAMADAN ka gayamin acikin 'yan matanka waccece wacce takwanta maka arai
Yayi Murmushi idan shi cikin nata
Yace wani abune
Tace eh mana
Toh gayamin
Ya fa'da hakan cikin muryar ra'da
Taji hakan har cikin ranta
Tace idan nasani sai ingayama Su Momy kaga sai amaka Auran ko

Yace Allah Auntyna
Ta gallamai harara
Tace ban sani bah
Yayi Murmushin da yake qara masa kyau Yace ni ba wacce nake so a 'yan mata nah
SAILUBAH tawaro ido cikin sanyin kuka
Tace wai meyake damunka ne
Ya sakar mata mata kiss Yace ke kike damuna Auntyna.
Hmmm karki min kuka ki hanani mafarkinki yau in shiga uku.
Ya fa'di hakan da ficewa daga falan yana cewa bye bye rikitacciyar Auntyna

Kuka SAILUBAH tasa tayi San ranta
Can tayi shuru tasa aranta yadena ganinta kenan
Tunda itace take damunsa har yake sauke mata iskancinsa

**** **** ****


Yau kusan sati biyu kenan SAILUBAH na 6oyema RAMADAN kanta
Duk tabi ta rame dan rashin ganinsan da batayi
XEE ta kalleta Tace yau ni naga ikwan Allah
Kin hana xuciyarki taxauna lpy dan kawai bakisan ganin RAMADAN akusa dake
Na tambayeki me yasaki yin hakan kinqi gayamin

Cikin damuwa SAILUBAH tajah numfashi Tace ya xanyi ne XEE ya kike san nayi

Har Saina fitoh naga miki cewa yanxu RAMADAN yaxama 'dan iska. Bayan kina gani da idanki

Inya ibo iskancinsa sai yaxo ya sauke aguna
Ni sa'arsa CE daxai dinga yimin kiss tamkar wata matarsa
Idan na kwanta bacci sai indinga ganina dashi cikin wata rayuwa irinta ma'Aurata

Duk yabi ya birkita kwakwal wata wajan tunaninsa dasan kasan cewa dashi.

Kullun natashi daniyar cimai mutunci muna ha'duwa yana jefamin shegen kallansa xan rasa nutsuwata
Me kikeso nayi anan bayan in ne santa kan nawa dashi

XEE tayi kalar tausayi dariya fam cikin ranta da jin da'di
Amma ko kusa baxata iya nuna hakan bah

Tace toh ai naga hanashi ganin kanki da kikayin. Damuwar kanki take komawa
Dan gashi kin rame sai uban haske da kika qarayi
Ga damuwa nan da tashin hankali da suka baiyana kansu agareki.

Tace ni ban damu da ramar da nayi bah. Ko tashin hankalin daya baiyana agareni ba
Fatana Allah ya yayemin tunaninsa
XEE RAMADAN haukatani yake sanyi

Dan yanxu wani tsoran shi da kwarjininsa ne suke kamani......

Kan XEE tayi magana wayarta ta'dau ringing
Tayi Murmushi dan Ganin KHAMIS ne nanta 'dauka tana cewa sai yanxu

Yace ya xanyi my Luv tashina kenan fah FAWAS yaxo har office ya 'daukeni
Shine fah nace bara in kiraki nasamu nutsuwa
Tace toh xan iya ganinka yanxu
Yace naso dai namiyo miki wanka nacanja Kaya dan kiganni da kyau Sosai.
Tace ai kai kobakayi wanka bah kyanka karuwa yake agareni
Yace Naji dai
Dan nalura wayo kike san kiyi min
xamuje qauye ne ni da RAMADAN da FAWAS yanxu haka
Idan muka dawo na'dan huta xaki ganni.
Ta shagwa6e murya Tace ni dai yanxu nakesan ganinka.

Kallan FAWAS KHAMIS yayi Yace toh Aunty XEE nasan ganina kuma nima ina buqatar ganinta
RAMADAN Yace tambayar min ita Auntyna tana gidan ne
KHAMIS Yace my Luv Aunty LUUVAH na tare dake ne
Tace eh gatanan.
KHAMIS ya 'dagama RAMADAN kai
Murmushi yayi Yace toh kuyi shawara pls lokaci na tafiya kunsan ahakan mah sai munyi dare Sosai yau.
KHAMIS Yace toh my Luv ganinan xuwa
XEE tayi Murmushi Tace ina jira.... Da kashe wayan

SAILUBAH Tace tambayarki yayi ina tare dake
XEE tayi Murmushi dan tanaso ne RAMADAN ya ganta
Tace aa mamah yake tambaya
Tace toh ai bata nan
XEE tadafe goshi kamar gaske Tace Kinga na manta

Tsaki SAILUBAH tajah Tace nixan tafi gida
Wlhi gabaki 'daya banajin da'din rayuwar
XEE tafara lallashinta da tsokalo hira dan dai RAMADAN yaxo ya sameta agidan.....


FAWAS natsaida motar Yace pls minti biyar na baku
RAMADAN yayi Murmushi Yace niba Luv xan tsaya yiba
Kallanta kawai ya isheni
KHAMIS Yace ni dai saina 'dan ta6a
Da harara FAWAS yabishi. Sukamai dariya da shigewa gidan

Saijin sallamar RAMADAN SAILUBAH kawai tayi
Aiko gabanta ya tsinke ya fa'di.....
Da sauri tatashi ko kallansa batayi bah dan ita tasan qarin maseefar da kallan nasa suke qara haifar mata dashi

Da wani gudu ta tafalle da shi xuwa 'dakin XEE........

XEE da KHAMIS baqaramin mamaki sukayi ba wajan ganin RAMADAN ya Sha gabanta
Dan basu san wane irin gudu yayi bah

Yace Auntyna kuliya kika gani haka....
Tace ayanxu ganinka yafi kuliya ban tsoro arayuwata RAMADAN
pls ban hanya in wucce.

Yayi Murmushi Yace abin har yakaimu da haka
Ta 'dagamai kai Cikin damuwa
Ya kalleta sama da qasa Yace meya ramar dake haka.
Cikin gajiyawa da maganar tasa Tace ciwo nayi
Yace narashin ganina ko
Ta kalle ka'dan Tace aa
Yace fa'di dai gaskiya dan gata tana yawo akan fuskarki kuma....
A shagwa6e ta katseshi danjin yanda qamshinsa yake bugarta Tace RAMADAN......
Yace AUNTYNA..........



Bani hanya in wucce
Yace xan baki Amma saikin gayamin...
Tace nace maka aa ko
Yace toh Naji
Yanxo gayamin mexan tawo miki dashi in xan dawo
Ta girgirxa kai Tace ni banasan Komai
Ya waro ido Yace harda ice-cream
Ta 'dagamai
Ya kama hannunta cikin shagwa6a Yace dan Allah dan Annabi Auntyna Karki qara 6oyemin kanki
Kinsan maseefar da kika jefani kuwa...

Ta. Juya da nufin ganin XEE
Amma taga wayam ba kowa daga ita sai shi
Ta kallesa Tace toh Naji jeka
Ya xubama bakinta ido
Ta gallamai harara Tace Allah kamin kiss kadena ganina kenan
Yayi Murmushi dan ya hango tsoranshi Sosai atare da ita Yace baxan miki bah
Dan ganinki yafimin Komai da'di aduniya
Kinga idan najama kaina ai nashiga uku
Tayi Murmushi Tace jeka
Ya shagwa6e fuska Yace toh kimin kiss tunda ni kin hanani inyi miki
Dafe goshi SAILUBAH kafin takama fuskarsa tayi masa agoshi
Tace shi kenan
Ya 'daga mata gira da cewa eh
Amma gaya min me xan tawo miki dashi pls👏🏻
Tace ice-cream
Yace dame kuma
Tace hmm🤔 sai kakulamin da kanka
Yace toh idan na dawo xakiban abinci abaki

Cikin gajiyawa Tace Eh. yanxu mah xanje in dafamah

Yace Yauwa my Aunty bye bye
Ta 'damai hannu ya ficce

Jan numfashi SAILUBAH tayi dan ganin San nan da tayi
Da 'Yar maganar nan da sukayi har ta'danji sanyi aranta

FAWAS yajah tsaki Yace ina shi wancan 'dan iskan
RAMADAN yayi Murmushi Yace wai KHAMIS
Yace eh mana
Ta6e baki RAMADAN yayi Yace na ganshi ya sata agaba yanata aika mata da sakwanni
Wlhi bakaga yanda tasakar mai da imaninta bah.
Dan ko shigewata basuji bah

FAWAS yafara neman KHAMIS awaya

XEE Tace ana kiran numbarka fah
Yace nasani FAWAS ne
Zan tafi. yanxu sai dare
Tace eh katawo min da kayan da'di 😬
Yace angama matata....



HAMEEDA da Qawarta Mero suna xaune a kofar gidan nasu HAMEEDA
Fa'di HAMEEDA takeyi yanxu Mero yaranki hu'du
Tace eh Wlhi naxama babba
Dan yanxu baki isa Ki rainani bah
HAMEEDA Tace hmm nima nadai kusa Auran nan nima in tara yara Lodi Lodi
Mero takalleta ta kwashe da dariya dan tasan san yara irin na HAMEEDA Sam baxataga Yaro ta wucce batace miki yaranki yayi mata kyau bah dan halinta 'daya☝🏻 da (Rahamat)
Tace angaya miki aihuwar cin tuwo ce da xaki haifah lodi lodi.
Wlhi ina tabbatar miki ranar daxaki aihu ji xakiyi tamkar xaki mutu dan axabah

HAMEEDA Tace dallah dena tsoratar dani
Mero Tace nadena
HAMEEDA tayi shuru can Tace Kinga dare yayi Amma banga idansu bah

Mero Tace Wlhi kam
Ai daba dan inaso in gansu bah aida tuni nayi gida
O ikwan Allah yanxu kin kusa shiga birni kiyi rayuwa tahar abada.......
Kan HAMEEDA tabata amsa saigasu FAWAS

Nan farin ciki yacika xuciyar HAMEEDA
Tadinga xungurin Mero cikin muryar qasa qasa Tace gasunan shine Wanda xai fitoh yanxu
Mero da ba'a xancan sirri da ita Tace lah ia'ilahaillallahu Ashe qaramin Yaro ne
HAMEEDA tatake mata qafah
Tace haka nake sanshi😬

FAWAS ya qaraso garesu Yace Aminci ya tabbata agareki YAYATA kuma wacce takusa xama mata agareni...

Tace tare da naka hasken idanuna
Yace kinyi kyau Sosai. Dafatan ba wani namijina daya ganemin wankan nan
Tace wane wani da gane maka HAMEEDA aikoya kallan ina tabbatar maka baxai qara kuskuran yi akaro na biyu bah
Dan munina xai gani. Ina tabbatar maka kai ka'dai ne Wanda aka lamuncema ganin kyawuna ....

FAWAS yayi murmushi dan yanxu yadena mamakin Yayar tasa wajan 6arar da kalamai
Na soyayya dana shirme dana abin dariya
Yace Naji da'din furucin nan naki. Saidai naga baquwar fuska agareki abinda ban ta6a gani ba kenan

HAMEEDA tayi Murmushi Tace ita ka'daice wacce na 'dauketa 'Yar Uwa a qawayena

Yayi kyau hakan. Yafa'da da kallan Mero. Tare da qarawa da cewa. Toh sannu qawar YAYATA
Mero tawashe yalan haquranta Tace Barka da xuwa dai 'dan birni

FAWAS yayi dariya Yace Barka 'Yar qauye......
Dariya sukasa atare dukkansu

Ya kalli HAMEEDA Yace toh Kinga kayan kwa'dayi nasiya miki yau
Dafatan sun isheki cika cikinki yanxu ame makwan kici abincin dare
HAMEEDA takar6i ledar xata bu'de.....
Yayi saurin katseta da fa'din aa karki bu'de yanxu harsai na tafi

Tace darkar namaka godiya me yawa.
Yace ko guda 'dayace bana santa
Yafa'di hakan da ajiyema Mero dubu uku agefanta yana cigaba da cewa
Ga wannan Ki siyama babyn bayanki sweet Qawarmu
Mero tafara godiya
Yakalli HAMEEDA Yace toh Amaryata sai munyi waya
dama damuwata naganki yanxu
Toh Allah yayi ina miki fatan alkairi

Da kallo HAMEEDA tabishi har yashige motar tasu ya tadata
Sannan tadawo duniyarta
Mero tadinga dariya tana fa'din tunda uwata tahaifan ban ta6a riqe dubu uku bah gashi yau sanadinki nasamu
HAMEEDA Tace xomuje ciki muci kayan da'di dan naga harda kaxa


Sun dawo gida lafiya inda kowa yafara cikiniyar wanka da Sallah suci abinci Sannan suhuta

Sanda RAMADAN yayi sallar Isha'i ya huta
Can kusan qarfe tara Sannan ya nufu gun Auntyn tasa
Yasa meta afalo tana karatun al qur'ani megirma

Yace Auntyna takallesa da sauri
Ya sakar mata Murmushinsa da xama kusa da ita. yana cewa ina ummah
Tace tana 'dakin Abbah
Kakah fah
Itama tana can inaga wata magana suke tattaunawa
Yace toh xomuje haraba
Tace aa
Yace dan Allah
Tace me xakamin
Yace ciyar dake Xanyi
Tace dame
Yace da ice-cream da sauransu
Ai fah jin ice-cream Tatashi
Shima tashin yayi ya kama hannunta suka fitoh
Kujerun robar wajan yaja musu can gefe suka xauna kusa da juna
ya tura mata ledan kayan gabanta
Nan tabu'de taga gasassiyar kaxa ce da ice-cream sai danginsu chocolate

Jan ice-cream 'din yayi
Ya dinga bata tana Sha tana ha'dawa ta kaxar ahaka harta qushi
Tace toh bara in 'dauko mah abincinka kaci ko
Yace kidai ban naci ko
Murmushi SAILUBAH tayi
Dan tun 'daxu tasa aranta tadena damuwa da duk abinda xaixo daga gareshi
Tunda talura ayanxu baya shakkar gaya mata Komai.

Nisanta kanta dashi bashine

Please Login or Register in order to submit comment