Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Alhaji Aminu
Wannan wane irin hatsabibanci ne.....

Cikin sanyin rai yace maganar auransu ya ummi akwai matsala ne
Tace basaika ganar dasu axahiri bah
Kawai ka kwantar da yaro baccin ba gaira ba dalili
Waikai saika fahimtar dashi cikin baccinsa
Bakayi tunanin ibadun da suke kanshi ba.
Ka wani sashi kallan wasu bankwan matane......
Tana fa'din hakan ta bigi SAILUBAH da maryam nan take suka xagwanye suka xama toka alamar babusu duk alaye ne
Sannan tacigaba da cewa kacire fuskarsa kasaka taka danya temaki matarka bashi xai baka shiga rayuwarsa yanda kake so bah......

(Meke faruwa ne💁🏼 sisters)

Qara sunkuyar dakai Junior yayi Yace bin umarninki farillane gareni kauce miki matsalane ga rayuwata
Damuwata Ki sauka daga wannan fushin da kikeyi dani
Dan yana sani shiga tashin hankali
Nasan nayi kuskure ya ummi Kiyafemin
Baxan qara maimai irin hakan ba.....
Cikin sanyin rai tace kasan kai ka'dai muka haifa nida mahaifinka
Baxan iya juya maka baya wajan in yafe maka ba
Ina sanka yarona. Amma kacanja hali abunnan da kayi yayi matuqar ta6a xuciyata
Ka sani bana san wasa da ibada
Bana san wasa da alkin Allah
Qara sunkuyar da kansa yayi cikin nadama yace wlhi ya ummi Sam nashagala akan ibadarsa
Kinsan ba haka nake ba
Kiyafe min
Shafa kansa tayi Tace nayafe maka allah yai maka albarka....
Jeka kagyara komai. Sannan kagaishe min da RAMADAN 'din kace injini yayafe maka duk nasan yana ganina kuma yana jina.......
Angama ummina

Nan yatashi ya 6ace cikin nadamar abinda ya aikata.....




****** ****** ****** ******

Yana kwance a asibitin aminu kano yana sauke numfashi ahankali ahankali alamar baccin kwanciyar hankali yakeyi
Gashi ansaka mishi ruwa me sinadarin abinci aciki....

Gefe guda tawaje SAILUBAH ce da XEE FAWAS da KHAMIS Momy da Dady da Khairat
Dukkaninsu damuwace 6ace 6ace afuskokinsu
SAILUBAH tarame duk tafice daga hayyacinta
Kallo 'daya xaka mata kasan tayi kuka dan ga sheda nan yanda idanta ya kumbure
Momy mah haka
XEE sarkin tausayi ba'a barta abayaba wajan taya SAILUBAH kuka
Ba'a maganar FAWAS da KHAMIS dan sunfi kowa shiga tashin hankalin halin da 'dan uwan nasu yake ciki

Cikin sanyin rai Momy Tace SAILUBAH kisaki ranki kinji abinda doctor yace ai
Tace Momy naji jinake tamkar baxai tashi bah
Musamman idan natuna xancikan da mukayi dashi anar daran daxai kwanta
Ina san RAMADAN Momy pls kuyi wani abu akai Dady
Wlhi narasashi nima rasani xakuyi......
Tana fa'din hakan taje taxube ajikin Abbanta tana cigaba da cewa kana gani Abba ko. yau ina qirgawa kwanansa hu'du
Baci ba Sha Abba. Sannan ba magana. Haka kuma ba motsi......

Shafa kanta yahauyi cikin tausayawa
Allah yana qaunar yaran nan RAMADAN dan jiyake tamkar shiya haifeshi.....

Kan yayi mata magana Dady ya kalli SAILUBAN cikin damuwa Yace kiyi hakuri 'Yata xai tashi
Munsan yanda kike da RAMADAN
Kinfi kowa shaquwa dashi. Ina tabbatar miki da cewa xai tashi insha Allah

Shuru SAILUBAH tayi kawai
KHAMIS ya girgixa kai hawaye na xubo mishi yace allah ya tabbatar da alkairi
Duk sukace Ameein

FAWAS yamiqa mah XEE ruwa yace Aunty XEE wanke fuskarki ta6a
Murmushi yaqe tayi takar6a ruwan batare da tayi yunkurin wankewa bah
Shi kam yayi nasa kukan dan RAMADAN wani 6arene na rayuwarsu
Tabbas idan sukayi rashinsa sunyi babban rashi arayuwarsu.........


Murmushi junior yayi bayan gajin abinda suke cewa
Can ya shige ta gabansu batare da sungansa ba ya shiga 'dakin da RAMADAN yake

Sanda ya xuba mishi ido na tsawan minti biyu kana yayi murmushi shidai yana San yaran
Ga nutsuwa ga ibada ga hankali ga tausayi uwa uba ga shegen wayo a soyayya

Cikin nutsuwa ya shafi gefan fuskarsa.....

Ahankali RAMADAN ya bu'de fuskarsa yana me tsaida ganinsa ga Junior
Can ya tashi afurgice ya dafe kansa dayaji yana baraxanar tarwatsewa
Cikin wani hali ya nuna Junior da yatsa yace Junior
Murmushi yayi yace na'am
Ashe dai xaka shaidani
Yace meke faruwa dani
Yace abinda kagani cikin baccinka
Yace da gaske bacci nake ko idona biyu.
Yace da axahirine aida kafi ganin bala'in dayafi haka
Yace na mutu acikin baccina Amma bandena ganin Rayuwar da KHAMIS FAWAS Auntyna suke bah
Yace dake bacci komai mah xaka gani
Yace me yasa hakan tafaru afareni.
Yace saboda nine
Duk surkullena ne
Duk shirina ne
Duk ba gaskiya bane
Sannan rayuwarku baxata kasance hakan ba

Kayafemin RAMADAN nashiga rayuwarka dan nafahimtar dakai wani abu. Saidai ban kaiga cinma burina bah aika gani ummina tanemi da indawo dakai daga waccan duniyar

Da 6acin rai RAMADAN yace gayamin tun yaushe nafara wannan baccin
Yace yau kwananka hu'du
Yace akwana hu'du duk naga wannan rayuwar dana gani...
Yace kawai da gaske
Yace toh da wane buri nakwana acikin daran da wannan bacci yayi awan gaba dani

Shuru Junior yayi....
Shima RAMADAN din shurun yayi kawai yana kallan Junior wanda mamaki ya hanasa sakewa
Gashi kamar shi dan ba abinda ya rabashi da Junior
Can Junior yace awannan daran kayi sallah karoqi allah daya hana auran SAILUBAH da Alhaji Aminu.......

Amatuqar raxane RAMADAN ya tashi Yace kana nufin kwanciyata acikin wannan dare shiyabaka damar shiga cikin mafarkina kashirya min wannan surkullan wanda naga kabayyana a 'dan uwana jinina. Ka 6ullo lokacin da akayi auran auntyna. Kakawo min xancan wai wani wan mahaifinmu wai shiya kashe mana mahaifinmu kan dukiya. Kuma mahaifiyarmu tamutu wajan haihuwarmu. Kadawo kana rayuwa damu cikin gidanmu. Har kakoma karatu waje. Naxo na auri Auntyna sailuba tahaife min yara biyu. Naga rayuwar Aunty xee da khamis rayuwar fawas da hameeda. Bayan na mutu ban dena ganin rayuwarka da auntyna ba dasu dukkansu. Da irin wahalar da kake bata da rainin hankalinka. Daga qarshe ka aureta ita da wata maryam asannan ne kafara bayyana musu ainihin kokai waye.
Kajasu dan kanuna musu yanda waje take saika kaisu garinku gun mahaifiyarka
Nan tanuna 6acin ranta kan abin daka 'aikata agareni....

Wannan shine film 'din daka sakama memoryna acikin baccina ko

Junior ya hararesa yace hmm qaramin yaro dakai sai riqe abubuwa
Ji yanda ka lissafo komai baka manta komai bah

Harararsa shima RAMADAN yayi ya tafe kansa wanda yake masa ciwo da gaske
Tunani ya shiga kan meyafaru dashi wannan ranar da har wannan aljanin ya shiga cikin rayuwarsa........

Yauwa ya tuna da abinda ya faru a ranar... Cewar bakinsa...

(Muje zuwa sisters 😀)


Yeeee🤣🤣 RAMADAN yaga rayuwa

*Dama kyan karatu waiwaye........ Inji hausawa sukace adan tafiya.....*

*Me karatu kaima tuno wannan Page 'din. Dan tun daga shi junior ya d'ora lamarinsa a baccin da RAMADAN yayi wannan daran da komai ya fara gudana*


*Ni dakai dake mun karanta wannan page 'din amma bamu ta6a kawowa daga shine baccin RAMADAN yasomah ba.... gaskiyane Junior hatsabibine inji Aunty Rahamat Nalele

*Page d'in baya

*Shidai RAMADAN ya tuna lokacin da suka dawo daga qauyen takai wajan gaisuwar rasuwar abokin wanda har FAWAS yayi wata budurwa HAMEEDAH 'Yar QAUYE. Ya tuna lokacin daya dawo yayi wanka nufar gun Auntyn tasa SAILUBAH yayi ga abinda suka xanta ita dashi*

Tana kwance a gado XEE na gefanta ga qawayanta nan sai hira suke
Saiya shigo 'dakin
XEE ta 6allamai harara Tace ban ta6a ganin qani mesa Auntyn shi cikin damuwa da tashin hankali ba kamarka RAMADAN.......
Da sauri ya katseta da cewa haba Aunty XEE kidena haka. Yanxu xakisa taqara jin haushina bayan KHAMIS ne Babban me lefi dayaqi gaya mata inda nake
Tace eh Gaskiya. dake gaka gata ai dole ka kanemi kare kanka. Karka wani saka KHAMIS dan bashi da lefi
Ya kalleta da Murmushi Yace toh Naji bashi da lefi
Ya maida kallansa ga Auntyn tashi wacce ta kafeshi da ido tun shigowarshi
Yace Barka da yammaci my Aunty
Ta sauke ajiyar xuciya Tace me yasaka ramewa haka
Ya tashi yana cewa tunani da tashin hankali
Tashi itama tayi Tace muje
Ba musu suka jero tare har xuwa gidansu part 'dinsa
Ta xauna gefan gado shi kuma yana kan kujerar da take fuskantarta
Tace wane tunanine haka da tashin hankali yasaka ramewa
Ya kalleta ka'dan Yace kema ai kin rame Sosai
Tace kaban amsata
Yace hmm tunaninki Auntyna mana....
Wai a tunaninki rabuwa dake xai barni na xauna lafiya ne.
Hmm Sam hakan baxai yuhuba
Dan daga ranar da kika bar gidanku xuwa gidan wani toh Ki tabbatar baxan qara samun kwanciyar hankali arayuwata bah
Saban danayi dake ya kai matsayin da in tunaninki yayimin yawa xan iya rasa rayuwata........


Kuka SAILUBAH tasamai Sosai.....
Duk da hankalin RAMADAN ya tashi Amma sai ya share dan yanxu burinshi yayi mata abinda xaisa taji xafi fiye da yanda yakeji axuciyarsa
Nan ya hau 6arar mata da kalamai cikin qara kashe mata xuciya da takaici
Fa'di yake narasa me kika gani ajikin wannan mutumin Sam bai dace dake ba
Ina ganin ma 'dan shan jinine
Dan bashi da fuskar imani
Ki kula dashi Sosai mana
Gashi shi ba wani kyakkyawa bah.
Kawai Kinga ku'di kin yarda yaxama miji agareki
Akan ma wane dalili xaki yanke igiyar shaquwarmu saboda shi
Nayi baqin ciki da takaicin hakan.
Bani da wani buri daya wucce in tayaki neman xabin ranki. Kyakkyawa me aji me ku'di me maseefar kishinki.

Nayi addu'ar istahara nayi Sallah akan Allah ya bani haske akan lamarinki dashi.....
nagani Cikin mafarkina Auran shi nadama ne agareki

Ni fah baxan 6oye miki ba. In bake baxan iya rayuwa sak kamar yanda aka sanni ba

Kuka take Sosai yana qara jefah mata qiyayyar Alhaji Aminu

Can dai dayaga kukan yayi yawa kuma yana maseefar damun xuciyarshi sai ya matso kusa da ita ya kama hannunta
Yace toh kiyi shuru kidena kukan nan tunda kina sanshi baxan qara kushe miki shiba tunda ranki na 6aci kiyi hakuri
Ki dena bana so. inba so kike Ki hanani bacci ba. Yafa'di hakan da leqa fuskarta cikin kusanci dasan qara hargitsa mata kwanya

Aiko ta shaqa
Dan yanda yayi kusanci da ita ka'dan ya rage bakinsu ya ha'du dana juna
Ganin yasami abinda yakeso dan jikinta ya mutu mu'dus. qiris take jira ta xubemai ajiki. Shiyasa ya 'dan janye kansa ka'dan daga gareta tare da jifanta da wani kallo Wanda atake yasan ya gama kunce mata Komai.

Ta lumshe idanta tare da dafe kanta Tace bana sanshi bana sanshi
Na da'de dasanin Kaine kwanciyar hankalina RAMADAN
Ban San me yake damuna ba.

Kina sanshi tunda kike min kuka akansa. Kuma aida bakya sanshi ko kusa baxaji sha'awar kar6ar abin hannunsa bah. RAMADAN Ya fa'da dasan qara harxuqa xuciyarta

Aiko cikin fusata Tace wai kai wane irin 'dan iskane
Nace bana sanshi bana sanshi bana sanshi Amma sai qara Sa xuciyata xafi kakeyi tun kwanaki can da suka wucce nayi dana sanin sanin shi

Yariga da ya samu guri gun Abbana ya hanashi kallan ra'ayina
Ya kakeso nayi ne RAMADAN. So kake na haukace
Naji Komai bana jin da'dinsa aduniyar nan saboda qaurace min da kayi.
Sam nalura bakasan farin cikina
To bara kaji na rantse da Allah ka kara min haka sai mun sami mummunan matsala dakai

Dan narigada na auna na garo ba abinda yake tadamin hankali kamar rashinka kusa dani

Da 6acin rai Tatashi da niyar barin 'dakin.......
Cikin sauri ya Sha gaban da yanayin damuwa......
Yace 6acin ranki tashin hankaline agareni
Ki temaken kisaki ranki ko nasami nutsuwata
Tace matsamin in fitta ko kasha mari.......

Yasan acike take dashi Komai xata iyayi masa
Saidai kash yayima kansa alqawarin baxai barta tatafi awannan yanayin ba
Dan yanasan yau ya bala'in hargitsa mata kwanya

Dan haka cikin yi mata baxata ya rungumeta da kashe murya irinta Wanda yake yin kuka
Yace kimin rai auntyna kiyafemin nasan narabu dake kenan yau har abada. baxan ta6a yafema kaina bah idan har xuciyarki batayi sanyi munyi bankwana cikin farin ciki bah.......

Tundaga tsayar kan SAILUBAH taji wani abu na yawo ajikinta Wanda yasa ta rikice Komai na jikinta ya tsaya cak.....

Cikin wata murya me sanyi Tace toh naji sakeni
Cikin sanyin jiki ya raba kansa daga jikinta idan shi akanta yana San gano wani Abu
Yace kin hakura ta kallesa ka'dan cikin wahalalliyar murya Tace ya xanyi dakai RAMADAN
Pls ina buqatar ka'daita
Ya bu'de 'kofar suka fitoh tare har 'dakin Kakah ya kaita dan nanne ba kowa.
Yace toh Ki huta my Aunty.
Ko kulashi batayi ba
Yayi Murmushi dan yana san ta qara harxuqowa dan bai gaji da maseefar taba
Idan tana magana sam bayaso tadena.
dan haka ya leqa fuskarta Yace toh xan tafi fah Auntyna.....
Kamar xatayi kuka tace wai me xan maka

Ba xaka barni nasamu ka'daicin bane.
Yace da naso kitashi mu'danyi hira ta bankwana
Da maseefa tatashi ta kallesa kamar xata falleshi da mari Tace baxan tashi ba. wai hirar dole ce Nace ina buqatar ka'daici kabarni man
Sai yayi kalar sanyi irin na abin tausayin nan Yace toh shikenan Auntyna Allah ya baki hakuri. Ya nufi hanyar futa
Aiko saita fashe da kuka. Bai tsaya ba ya futa abinsa Yana Murmushi fa'di yake aransa Auntyna kenan duk Sallah idan nayi ina ha'daki da Allah ya xa'ayi Ki xauna cikin kwanciyar hankali akaina. Sam hakan baxai yuhuba

XEE tatareshi a farfajiyar gidan Tace shigowarku 'daxo naga SAILUBAH daga dukkan alamu tayi kuka
Yanxu kuma kafitoh kana Murmushi wai me yasa Sam bakaso kaganta cikin kwanciyar hankaline

Yace Aunty XEE kenan. Wlhi duk duniya bawanda yafini San ganin kwanciyar hankalinta

Kawai batasan Auran wannan shegen ne
Ni kuma dama basan shi nake ba. Saina bata haske akan hakan........

Ta katseshi da fa'din Ka hargitsata dai

meyasa ka tsani ganinta da kowane 'da namiji.
Yace saboda duk wa'yanda take ha'duwa dasu basa dacewa da ita Sam
Ke Kinsan burunta
Auran namiji me aji
Kyakkyawa
Me ku'di over
Me kishinta
Me shakarun da suka xarce nata Sosai
Shin tsakaninki da Allah har yanxu ta ha'da me wannan abubuwan gabaki 'daya

XEE tayi shuru. Can Tace gaskiya aa
Yace hmmm
Kinga Ki share kawai wannan Auran nata ba inda xaije dan xatayi rayuwa ne da Wanda ko kusa bai dace da itaba
Kin santa sarai idan tace ta tsani abu bata sanshi ba tayanda xa'ayi tarayu da wannan abun cikin xaman lafiya
Wlhi ta tsaneshi batasan ha'dinta dashi yanxu
Tayi nadamar saninshi
Ki rubuta Ki ajiye ba'inda Auran sun nan xaije
Idan kin shiga ciki yanxu dan Allah kice tadena kukan ya isa haka
Na barki lafiya. Yana fa'din haka ya wucceta ya ficce daga gidan
XEE tabishi da kallo baki sake
Kana tayi 'dakin khakha.
Har lokacin ko SAILUBAH kuka take ta kalli XEE cikin kukan Tace yaxanyi da RAMADAN XEE yaxanyi dashi
Tace hakuri SAILUBAH hakuri xakiyi dashi
Tace na rasa me yake damuna akansa....
XEE Tace hmm nihar narasa wane tunani Xanyi akanku.......

Katse tunaninsa junior yayi wajan cewa bayan fitarka daga gidan
Dukkan Ku kunshiga tashin hankali a wanannan daran
Inda kai kakwanta da tunanin mexai faru gobe da auran Auntynka SAILUBAH
Shin Auranta xai yuhu kuwa

Ganin da kayi bacci baida alamar saceka awannan dare shiyasa katashi kadinga Sallah kana kaima Allah kukan ka yayi maka maganin damuwarka

Bayan ka idar saika kwanta ayanda na lura kana cikin farin ciki baka kwanta da damuwa bah


Hakan yasa nayi amfani da wannan kwanciyar taka na d'ora surkullena akanka

Tundaga lokacin baka tashi ba sai yanxu da Allah yayi ikwansa akanka....

Da sanyi sanyi RAMADAN yace acikin surkullanka naga gari ya waye har munsaka ankwanmu ni da FAWAS da KHAMIS na auran nata
Anyi mata auran ankaita garin abujah

Idan nayi tunani dakyau mijin data auran me kisa ne d'an mad'igone

Ta kira ni wata ranah a waya hankalinta tashe take shaidamin mijin nata meshan jinine
Kuma 'dan ma'digone
Sannan me kisa ne
Zai kasheta inbanxo gareta bah......

Junior yayi Murmushi yace anyi haka dan hankalinka ya tashi washe gari kanemi dady daya barka kaje garin abujah
Ya tambayeka dalilin xuwanka kabashi tabbacin kanaso ne kawai kaje gidan Dady Auwal.....

Da sauri RAMADAN ya katseshi da cewa yauwa ya akayi Dady Auwal ya koma garin abujah bayan a jos yake nasan acan na ta6a rayuwa ka'dan

Junior yasheqe da dariya yace shiyasa nace maka surkullan nawa kenan

In banyi hakan bah tayaya surkullan xaitafi yanda nakeso
Tayaya xan baiyana matsayin 'dan uwana......

Harararsa RAMADAN yayi da dafe kansa alamarin damuwa

Dariya Juniorn ya qarayi
Yace sainayi amfani da ha'duwarka da Shahuda da kayi a jifatu
Na fara 6ullowa ta gidansu.
Katuna garqama maka bindigogi da mahaifinta yayi akan abinda na aikata masu yayi tunanin kaine

Shuru RAMADAN yayi kawai yana kallan Junior
Gaskiya aljanu hatsabibaine she'danu

Musamman yanxu daya ke qara tuna yanda amafarkin junior yaxama 'dan uwansa
Da yanda yanuna mishi suna da wani wan mahaifinsu mugun mutum Wanda yake rike dashi Junior
Wai shine ya kashe musu mahaifinsu
Harda yanda shi kansa ya auri Auntynsa SAILUBAH da rayuwar da yaga sunyi shida ita. Rayuwa me tsayawa arai
Har wai ya haihu
Ya haifi 'yan biyu
KHAULAT da KHAULEET
Yaxo kuma ya mutu
Baidane ganin rayuwar dasu FAWAS da KHAMIS XEE da Auntyn tasa ha'di da HAMEEDAH sukeyi ba fannin auratayya da sauransu
Ya kuma mutu saka makwan gobara
Wai har XEE tasamu matsalar haihuwa bata haihu da wuri bah
HAMEEDAH kuma ta haifi Ahmad
Shima ogan Junior sai rainama Auntynsa hankali yake

Toh abin tambayar RAMADAN anan shine miye dalilin dayasa Junior ya shirya mishi wannan surkullan cikin baccinsa har ya ibi kwana uku yana yi......

Dakyau yake Kallan junior yace yanxu naji komai ina so ka gayamin dalilinka nayi min wannan surkullan cikin bacci NAH

Murmushi yayi yace dalilan nawa guda uku ne..........







Na Farko SAILUBAH tasaka buri a rayuwarta nasan namiji me ku'di over
Namiji me kyau 'dan gaye
Namijin da xai sota ya qaunaceta har qarshen rayuwarta
Namijin daya fita shekaru ya girme mata nesa ba kusa ba

Sannan yanayin shigar da takeyi ita da XEE tasa6a ma addinin muslinci
Duk wani namiji me lafiya idan yayi ido biyu da ita da XEE sai yaso ya mallakesu a matsayin matansa

Hakan mu aljanu munada kwa'dayi sosai munasan mata masu irin wannan shigar

Na da'de ina sha'awar SAILUBAH
Na da'de inasan auranta
Amma tsoran mahaifiyata ya dakatar dani

Kana qoqari sosai wajan yima SAILUBAH Addu'a

Kana qoqari sosai wajan ganar da ita abubuwa

Xan gaya maka dalilina na 3 wanda xaisa kagamsu lallal saka baccin da nayi bana banxa bane

Haqiqa akwai cakwakiya arayuwarku dukkanku

Kai RAMADAN FAWAS KHAMIS HAMEEDAH SAILUBAH XEE

Zaku samu abinda kukeso Amma zakusha wahala arayuwar taku

Shin kasan wacece HAMEEDAH wacce FAWAS yayi mata ganin Farko a qauyan takai kafin ka kwanta baccinka

Shin kana da sanin cewa mahaifiyar KHAMIS qaddarar allah ce kawai xatasa tasota musamman idan kaga mummunar tsana da xata nuna agareta

Baxa ka ta6a sanin SAILUBAH tana MASEEFAR qaunarka ba har sai nan gaba saidai ita 'din wawiyace agurinka kai ka'dai ne xaka iya da ita

Xaka San kokai waye ne ta sanadin KHAMIS
Banda haka ikwan Allah ne kawai xaisa kasan kokai waye
Wannan Sirrin Dadynka ne.....

Matsowa yayi ga RAMADAN ka'dan yaciga da cewa.
Hmmm HAMEEDAH bala'i ce futunace
FAWAS ya fa'da tarkwanta

XEE alkairi ce ga KHAMIS Amma iyayen nasu baxasu so ha'din ba ko misqala zairatin. Saidai bayanda suka iya da ikwan Allah

Karigada ka 6ata tunanin SAILUBAH tuni. Kai baxa kasha wahala akanta canba


Abokana yanka FAWAS KHAMIS qaunarka suke da gaske
Tabbas San junanku kuke da gaskiya

Haka XEE qaunar SAILUBAH take da gaske
Kamar yanda yake ita qawar alxiqi ce

Nasan xaka xargeni kamar yanda naga tsanata akwayar idanka yanxu
Meye dalilina nayi maka hakan. Duk wannan baxai gamsar dakai ba. Ko Kuma ince bai gamsar dakai 'dinba
Ina sanka RAMADAN saboda ibadarka
Ina sanka saboda kyakkyawan halinka
Ina sanka saboda wayanka da dabararka


Nasan kaji abinda mahaifiyata tace kagani kuma da idanka
Xanso ka yafeni kamar yanda kagaya taruqi arxiqin hakan
Kamar kuma yanda kaga nadamata axahiri


*Xan tafi baxaka sake ganina bah har sai randa kuka sami abinda kuke so komai yaxo muku qarshe*
*Aranar xan qara baiyana agareka in gaya maka dalilina na uku. Dana saka yin wannan baccin....*

Zan qara gaya maka maka HAMEEDAH bala'i ce. Saidai qarshen wasan nata nadama ne. Ammafah ba wani can bah
Qaddarar da zatasa kusami sauqin wasu abubuwan shine kar6ar uxirin mahaifanku na fitta waje dan qarasa karatunku

Na tafi RAMADAN
Kayi abu me amfani ga rayuwarka
Ba akanka aka fara irin wannan baccin da mafarkan bah dan haka karkasa wata damuwa aranka

Ina muku fatan alkairi....

Dakata.... RAMADAN ya katseshi wajan fa'din hakan
Cikin nutsuwa yaciga da fa'din Ku aljanu maqaryata ne tataya xa'ayi in yarda da abin daka gayamin yanxu
Ko kanaso kaxama bokana ne. me bani sarrin abinda yake gaba
Na yafe maka abinda kamin
Amma kasani bansa duk abinda kafa'da dangane da rayuwar da xamuyi a gaba ba cikin xuciyata
Saboda ni sani irin wannan nema nake agun allah bani nema agun wani
Ban yarda da abinda kace bah. kawai nafi yarda da cemin da kayi in yafe maka sannan baxaka qara bayyana agareni bah har sai kaga cikar burinmu.....

Murmushi Aljani Junior yayi yace lallene kwa xanka na fa'din gaskiyarka yana burgeni
Hakan kake. tun kana yaro. tabbas akan gado hali
Ba shakka mahaifinka babban mutum ne. me gaskiya da rukwan amana da riqe alqawari
Banda haka dabaxai bar kintsattsan 'da kamarka ba
Tabbas mahaifinka me girma ne
Wanda yayi ilimi mexurfi
Harya kaishi da aikata abinda ya dace me kyau
Na tabbatar xaka iya xama kamarsa

Rashin yarda da abinda nace maka yana 'daya daga cikin abinda mahaifinka bai yarda dashi bah
Wato neman sani agun aljan
Hakan ba lefi bane
Saidai ni musulmine
Wanda yasan abinda Musulinci ya yarda dashi

Idan kaso kayarda dani wannan ruwanka yayana. Idan kaso kaqi yarda dama ban gaya maka da wata manufah. Bare naji xafi

Kamar yanda nace maka abaya baxan qara bayyana a gareka ba harsai can gaba. Tabbas kasa aranka haka abin xai kasance
Na barka lafiya allah ya sadamu da alkairinsa.....
Yana fa'din hakan ya 6ace 6at

Dafe kansa RAMADAN yayi yana ji kamar yana bara xanar tarwatsewa. Cikin wannan hali dadynsa yashigo dan yaji kamar motsi a 'dakin.....
Ganin RAMADAN axaune shiyasa shi saurin qarasawa gareshi ya riqe hannunsa cike da matuqar Farin Ciki ya kwallamah Momy......
Aiba Momy bace kawai tasheqo da gudu ba dukkansu ne sukayo 'dakin banda SAILUBAH data tokare a bakin k'ofah tana dafe qirjinta da da sauke numfashin farin ciki

Dukkanin su cah suka mishi akai kowa burinshumi yaji yayi magana
Shiko sai binsu kawai yake da kallo
Can Abban SAILUBAH yaje ya kira doctor

Bayan yay masa Wasu gwajeje yace toh madallah komai ya tafi yanda akeso. Yanxu me kakeji a jikin naka
Cikin sanyin murya Yace bani jin komai
Yace toh masha Allah sai ko yanxu xa'a iya baku sallama. ya qarashe maganar da kallansu Dady

Da murna sukace aiko hakan yayi....
Sai kallan FAWAS KHAMIS XEE RAMADAN kawai yana musu Murmushi kamar yanda yake 'dauke akan fuskarsu
Can ya kalli Momy da dady Abba yace Momy ina Auntyna.....
Ai dukkansu kallan qofah suka sai sukaga wayam ba SAILUBAH ba alamarta
FAWAS yace tana waje dan yanxu tagama kuka akanka
Momy Tace hmmm Allah sarki ai mungode mah allah daya tasar mana kai
Da SAILUBAH binka xatayi
Murmushi yayi ya kalli XEE yace Aunty XEE ya naga idanki jawur
Harararsa tayi tace idan muka rasaka RAMADAN ba qaramun rashi zamuyi bah.
Yace idan dai na canko duk kukan nawa ne
Tace ga xahiri
Murmushi ya qara yi cikin jin da'di ya tashi yana cewa Abba bara in 'dan kintsa Kaina ka'dan
Cikin jin da'di yace. Toh RAMADAN

Kintsa kansa yake yi Amma xuciyarsa tanaga Auntynsa dan Allah Allah yake yayi ido biyu da ita
Bayan ya fitoh Momy ta saka masa abinci tana cewa maxa kaci yanxu da safinsa
Murmushi yayi yace xanci Momy Amma girkin Auntyna itama saina sauke nauyin dake kaina na sallaloli
Tace toh shigarka toilet anbamu sallamah muje gida kayi acan
Yace toh
Sun fitoh harabar asibitin ya hangeta cikin motar dady har sun fara gaba
Cikin kallan shagwa6e yace da Momy allah Aunty fushi take dani lefin me namata
Murmushi Momy tayi tace wannan tsakaninku RAMADAN kafi kowa sanin abarka
Atunanina Farin Ciki ne yayi mata yawa shiyasata kasa fuskantarka
Murmushi yayi yana me rayawa aransa gwara da kikace atunaninki momy wannan fushin na wukunci ne.......

Suna ISA harabar gidan KHAMIS da FAWAS sukace bara suje gida dansu fa'dama iyayamsu tashin nasa
Yace ok ya gode da kulawarsu
Dakar kafa'darsa sukayi suna dariya ahaka suka ficce a motar FAWAS

Yarage daga shi sai ita agun dan haka yaje gareta ahankali yana cewa Aunty kiyi hakuri da lefina
Afusace tajuyo rannan amugun 6ace tagalla masa wata muguwar hararar data qara mata kyau

Please Login or Register in order to submit comment