Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

BIRNI. sai kin nutsu dakyau Kin kama mijinki dan inbah haka ba wannan ta wajan tana daf da sace xuciyar mijinki ina sanki dashi pls karki sake taxo ta dama miki lissafi kimin alqawari

Murmushi HAMEEDA tayi cikin kuka ta 'daga mishi kai Tace nagode RAMADAN nayi maka alqawari xan nutsu

Qara riqe hannun junior yayi Yace ina San Ganin Auntyna dan lokaci na kusantoni....
Gabansu ne ya fa'di.
Junior Yace pls brother kaika'dai fah nake dashi
Murmushin dai ya qara yi Yace kanada Allah kuma inaso kariqi ibada Sosai kamar yanda nariqe







Ahankali suke tura gadan nasa Suna hawaye har suka kai inda SAILUBAH take kamar gawa dan taqi farfa'dowa

Ahankali RAMADAN yakai hannunsa ga nata ya riqe gam......
Aiko nan take SAILUBAH tajah wani numfashi ta wangale idanta qur yana kallan sama
Al'amarin da yaba likitoci mamaki kenan
Ahankali RAMADAN Yace Auntyna......
Afurgice tajuyo garesa...
Ganin yanda jikinsa yake shiyasa komai ya dawo mata
Wani gigitaccan kuka tasake Tace pls Qanina pls dan Allah pls dan Allah karka min haka
Kamanta kace xan Haifa maka yara da yawa. Meyasa xakacemin dama kayi fatan ka rigani mutuwa. Kamanta kabarni nima baxan iya rayuwa ba....

Murmushi yayi mata Yace Auntyna banda lokaci ga 'dan uwana kiso shi dan Allah...
Kinsan shikadai ya ragemin
Kibama yarana tarbiya ban yarda kisake wani bare ya mallake ki matsayin matarsa ba..........
Yana fa'din hakan Yace la'ilaha'illallah Muhammadur rasulullah. Sallallahu alaihiwasallam.
Rai yayi halinsa ga MUH'MD RAMADAN SENIOR.....

Wan game ido😳 SAILUBAH tayi Da tashi afurgice. Takalli XEE Tace me kenan😳
Shuru ko wannansu yayi mata....😟😟😟😟
Ganin haka yasa ta shafa fuskar RAMADAN na girgixawa Tace Qanina
Ganin da tayi bai motsaba shiyasata sulalewa ta xube a gadan kuma gefan cikinsa
Hakan yayi dai-dai da xubewar junior da XEE asume

Yayinda FAWAS ya kalli KHAMIS a gigice suma suka xube sume

HAMEEDA ta kwalla qala nan take Su Momy sukayo 'dakin........




❌❌❌❌❌ an canceling wani Babban jigo a SAMAREEN BANAH. Wato Senior RAMADAN
Mu fuskanci sabuwar rayuwa da wa'yannan bayin Allah masu karatu...







Cigaba.....
*To wai mexaisa ni Rahamat in tsaya gaya muku irin tashin hankalin da SAILUBAH tashiga akan mutuwar Qaninta kuma mijinta Senior RAMADAN*

*Bayan nasan ku kanku kunsan shaquwa da SOYAYYAR da take tsakaninsu*

*Tsayawa fa'din tashin hankalin da tashiga xaisa in cika shafin bayanan da zan muku agaba*
*Dan haka Ku kimanta da kanku masu karatu......*


🇭ar akayi arba'in 'dinsu RAMADAN SAILUBAH batasan inda kanta yake vah

Abin ne yaxo mata biyu
Ga mutuwar mahaifi gata miji
Da wannan ne xanji ni SAILUBAH.....
Ahankali Junior ya kalleta dan shika'dai ne yaji wannan furucin nata
Girgixa mata kai yayi Yace kidubi Allah shi xaiji dake


Tun Junior KHAMIS FAWAS XEE Suna kallanta suji hawaye ya xubo musu har hawayan ya dena xubowa suka fara binta da addu'a

Duk kwana uku XEE da HAMEEDA sukanje Su 'debe mata kewa da danne xuciyarta
KHAMIS FAWAS ko Kullun sai sun dubata.
Hakanko yana yimata da'di in kuma Sun tafi hawaye ya xubo mata dan tuna Qanin nata.....

Junior shine yake sata a gaba da abinci taci dan samun lafiyarta
Idan takallesa kawai xuciyarta gaya mata takeyi dama Qanin nata ne ya ta rungumesa ko tasamu Sauqi

Bata iya yin bacci dan tasaba da jikin RAMADAN
Saita 'dauki awa a toilet tana tuna yanda takema Qanin nata wanka yake xuba mata shagwa6a

Idan junior yasata gaba akan taci abinci tuno Qanin nata takeyi tana bashi abincin

Idan taxauna kan kujera saitaga kamar xaixo ya 'dane kan cinyarta yana shafata da xuba mata shagwa6a

Idan KHAMIS da FAWAS sukaxo gareta atare saitafa tunanin yanxu Qanin nata xai 6ullo saiko taga junior ne ya 6ollo

Sosai junior yayi nasarai shagwa6ata wajan bata kulawar data dace
Ataqaice dai Junior ya bata lokacinsa wajan 'dauke hankalinta Sosai akan Komai
Ya 6ata tunaninta da bata abinci abaki
Ya 6ata tunaninta dayi mata kalmomi masu da'di
Ya 6ata tunaninta da ganinsa

Komai xatayi shi yake yimata
Damah ita 'yar shagwa6a CE dan haka Komai xatayi agabansa ashagwa6e takeyi
Yayinda yake daurewa dan ba qaramin jefashi takeyi a maseefa bah

Shidai damuwarshi tafuta daga takaba ya bata wata biyu ko uku kafin ya GYARA TUNANINTA




*Al'amuran sunfara faruwa ne kamar haka*

Bayan futarta daga takaba aka rushe gidansu. Nanko take aka tada gini

matsakaici gida akayi meban sha'awa Wanda yaba harabar gidan fili Sosai nashan iska
Wata uku aka 'dauka aka gamah Komai

Kakah Tace xata kuma gidan
Dan haka SAILUBAH Tace dama ita gidan nata ya isheta dan ko'ina tashiga RAMADAN Qaninta take tunowa
Dan haka taroqi Innah Yalwa akan taxo sukomah gidansu gabaki 'daya
Innah tayarda dan Sam bata San rabuwa da SAILUBAH dan Allah ya jarabceta da Santa
Haka suka ha'du da Kakah
xaman nasu gwanin ban da'di

Yayinda hakan yayimah Junior da'di Sosai aransa.
Ga yaransa kusa dashi kuma ga sahibarsa kusa dashi



Sam Junior baifara yimah SAILUBAH iskanci ba saida yaga tayi wata biyu da dawowa gidan😳

Ta "kama. isa. rashin san raini duk yafara nuna mata.


Abinko ya farone da wata rana da yadawo daga office 'dinsa kansa nayi masa ciwo Yace bara ya dawo gida ya huta
Bayan yayi wanka ne yaci abinci ya kira FAWAS Yana cewa aiki ya sami Auntynku tunda tacinye lokutan dana iban mata

Dariya FAWAS yayi Yace xa'a fara buga wasa kenan
Yace Sosai mah
FAWAS yajah numfashi Yace hmm ina tausaya mata da wannan wasan naka kasanfa tasake dakai
Yace abinda ya dace kenan
FAWAS ya gyara xama akan kujeraisa ta office 'dinsa Yace ai 'daxu da safe danaje gaisheta bakaga wankan da tayi bah
Tayi kyau Sosai kamar 'dan uwan mu RAMADAN bai Aureta ba
Har KHAMIS yana cewa yanxu samari xasu mata cahhh aka....
Dan ubansu ko xasu barta dan bata gama warwarewa ba.
Junior ya fa'di hakan ransa amatuqar 6ace
Dariya Sosai FAWAS yayi Yace jimana Malam ai saika tsaya kaji qarashen labari nah
Dan kanna ba KHAMIS amsa
Wani Yaro ya shigo yana cewa wai ana sallamah da SAILUBAH inji Alhj tukur......
Da sauri Junior Yace what😳
FAWAS Yace yah
Wlhi kuka tasa mana wiwi wai yanxu samari xasu sata agaba
Ina gayama sam taqi fita....

Junior yajah numfashi Yace waisu wa'yanne irin mayune daxasu xomah mace daga fitta daga takabah
FAWAS Yace ainaga tada'de da fitta ai
Yace ina wani da'dewa anan. Anaso mace tayi 1 year Amma ko 5 mont batayi ba. Sunfarasa gabah

Murmushi FAWAS yayi Yace kaga malam karkayi wani basaje kawai kashigeta dan idan katsaya sanya kanaji kana gani wani xaiyi maka shigar sauri

Murmushi Junior yayi Yace da'dina daku karantar sO
shine abu nafarko da yayi nasarar sace xuciyarku

Niba Senior bane daxan 6ata lokacina wajan bin ra'ayinta
Nawa umarnine kawai😀

Shege kana wata mubinka fetir jamu muje muga naka SALAN a sO
FAWAS ya fa'da da sheqewa da dariya😆 yana meci gaba da cewa Amma fah kasani Aunty LUUVAH tana dai-dai da tunaninka. Saidai dake mun lura da shagwa6ar da take xubah maka ba mamaki kasameta yanda kakeso. Tunda har yanxu nalura bagane Komai take bah.
Xakaji da'din buga wasan da ita......

Murmushi Junior yayi da kashe wayan dan FAWAS badai xulaya ba

Kiran KHAMIS yayi lokacin wayar bata kusa dashi
Dan haka sai kawai ya miqe yana lumshe ido da takaicin Ganin SAILUBAH dabaiyi da safeba
Yasani tanacan tana tunaninsa ko lafiya dan takira number nasa kusan sau uku Amma yaqi 'dauka haka kawai....
Janyo wayarsa yayi ahankali yafara rubuta mata sa'ko kamar Kullun dan tunda tafita daga takaba yafara damun xuciyarta.

```Assalamu alaiki```
```na gaya miki ni ba'ko ne agareki uwar 'ya'yana.```
```Zanso ki'daure kibani masauki xuciyarki```
```Ina so kisani. Shima so halittarsa akayi```
```Sannan acikin xuciyata samun akayi```
```Na rigada na xubar da ajina gareki nabaki xuciyata ha'de da gangar jikina```
```Kullun mafarkina ganinki nakeyi gani gaki da kyawawan yaranmu muna cikin farin ciki da nusha'di```
```pls kisoni luuuuuuu```
```Dan duk duniya ba wanda yake miki irin san da nake miki```
```Dan Allah kibani xuciyarki mukasance a shinfi'da 'daya```
Wannan shine abinda ya tura mata da wani layinsa
Yana tura mata ya gyara kwanciyarsa danyin baccine.


Saidai kamar yanda yasaba mafarkinta yi yayi gata da yaransa Suna wasa irin na sO da qaunar nan.......
Mafarkin nasa ya katsene dan jin yanda ake jan qafarsa...
Yana bu'de ido yaga KHAMIS ne
Murmushi yayi Yace na Aunty XEE yane
KHAMIS yayi Murmushi Yace muje baranta mu'dan Sha iska kaji
Tashi Junior yayi yana cewa Owkie

Sun haura sama can barandar tasu wanda hakan ya basu damar ganin Komai na gidansu SAILUBAH
Junior yakira Khairat awaya Yana ce mata takawo mai drink.....
Ko minti 'daya batayi bah takawo mai
Yace dts gud my baby
Tayi Murmushi da barin gun..
KHAMIS yaja numfashi Yace Wani abu ne yake damuna
Nafara gayamah FAWAS 'daxo Yace kawai saimun ha'du
Junior ya ture drink 'din gabansa Yace hmmm ina jinka
Yace naga alamun kamar Momy tafara canjamah XEE da sanin danayi musu dah....
Junior ya qara gyara xama. Kamar yaya fah.
Na lura Momy aihuwa kawai takeso shiyasa tafara canja mata

Abin da yaban mamaki dan gani nayi idan kaduba bafawai nakai Aure bane kawai sone yayimin mugun har suka samu sakayi min
Saidai abin takaicin shakaru ka'dan tatada hankalinta akan tanasan jika.
Yanxu Da kumah banyi Auran bafah
Junior Yace da bata damu ba
KHAMIS yajah tsaki Yace toh yanxun mah karta damu mana
Murmushi junior yayi Yace dole tadamu yanxu. Saboda in takalli 'dan FAWAS Ahmad da biyu na nasan xuciyarta xata qara tunxurata akan dama naka ne
Kuma kaga koyaushe Suna kai mata xiyara

Shuru KHAMIS yayi
Can junior yaci gaba da fa'din ga shawara...
Da sauri KHAMIS Yace inajinka
Yace xanso na dubata naji yanayin da takeji ajikinta da sauransu
Kaga saina 'dorata akan magunguna koxa'a dace
duk da dai nasan kunyi na asinitin ko kumama ince kuna kai.
Murmushi KHAMIS yayi Yace hakane kam
Xadai kagammun kawai.......

SAILUBAH CE tafitoh daga cikin falon Su KAULEET da KAULAT Suna biye da ita sunyi kyau Sosai Cikin shigar dogayan riguna da hijabi gayunsu
SAILUBAH ko wani jan les ne ajikinta riga da siket
'Dinkin siket 'din yayi baxar daga qasa
ta saman kuma ya matse mata qugu da futar da tsarin gun
Rigar kuma 'Yar daidai CE
Tayi 'dauran 'dan kwaninta irin na Aisha tsamiya
Gyalanta me shara-shara sai xuba qamshi takeyi
Hannunta maqare da agogo. Haka yatsunta saqale da xubunan xinare.
Batayi wani make-up ba dan daga man baki da fauda ba wani abu afuskarta
Amma dake ita'din me kyau CE bakuga yanda tayi bah

Tsayawa tayi tana qaremah motocin harabar gidan kallo tana ruwan idan Wanda xata hau....

Junior Yace ina xata haka
KHAMIS yayi Murmushi Yace 'daxu dai da safe tacemin tana San xaga gari dan tagaji da xaman haka.
Bata gaya maka bane
Yace dake yau tacinye adadin lokutan dana ibammata shiyasa Sam ban shiga mun gaisa bah

KHAMIS ya miqe ya dafa qarfan gun yana cewa da mamaki kam Amma fah tayi kyau sosai. Dan tafi 'daxu ha'duwa.

Tashi shimah junior yayi Yana wani yatsina fuska Yace baxan bari tayi futannan bah
KHAMIS Yace aisaika hanxarta. Aikine dai yasameka Allah Sarki senior 😀
Tsaki Junior yajah Yace angayama ni shine kawai nawa umarnine da 6atawa
KHAMIS yayi dariya Yace gaka ga ita ai. Jeka ina kallanku daga nan
Junior yayi Murmushi Yace harka tunamin da wata ranah....
Kan KHAMIS yayi magana harya bar gun

Ahankali ya tura "kofar gidan. Karab ko suka ha'da ido da ita
Gaban SAILUBAH ya fa'di kamar koyaushe dan ayanxu idan tayima Junior kallan farko Gani take Qanin nata ne
Saita da'da yimasa kallo na biyu Sannan take yarda Junior ne....

Harara ya watsa mata Bayan yaje daf da ita
Ya wani ya mutsa fuska Cikin raini Yace xuwa ina haka
Kallansa tayi Sosai saitaga yau ya koma mata 'dan iskanta sak😂
Dan haka itamah tawatsa mishi nata hararan Tace inda ka'aikeni
Yace toh baxaki bah...
KAULAT da KAULEET suka rungumesa Suna cewa Dady
Rage tsawansa yayi ya rungumesu yana dariya Yace ina xaku
KHAULAT Tace shan ice-cream Momy tace mana
Yace gud my baby.....

Wlhi baka isa ba saina futa. Ko angayama banda lafiya ne da xan xauna waje 'daya kamar wata mayya
SAILUBAH Tace hakan ranta amutuqar 6ace

Murmushi Junior yayi dan damah so yake tafusata...
Ya shafa kan KAULEET Yace toh maxa kuje gun momyna kujirani yanxu xanxo nakaiku ko.
KHAULAT Tace toh Dady Amma da Momy ko
Yace eh mana
Da gudu suka nufi barin harabar gidan Suna tsalle gwanin ban Sha' awa

Yadawo da kallansa ga SAILUBAH cikin 'daure fuska Yace Kinga malama shige gida
Tace toh ubana
Yace ai basai kinyimin gatse ba
Dan da gaske yanxu kamar uba nake agareki dan Allah ya kar6i abinsa saiya ha'da da masoyinki mijinki me kula dake
gayamin kina da wani Wanda ya wucce nine ayanxu....

Wata muguwar harara tagalla masa xuciyarta tayi mata xafi da amsar daya bata. Saita rasa mema xatace mishi

Ganin dashi kuma yayi tarasa nacewa shiyasa shi kai hannunsa kumatunta ya shafo faudanta yana kallo Yace eh ba shakka kam. harda wanisa pawda Xaki neman mijin Aure tun yanxu ko
Amma kin ban mamaki ko shekara 'daya brother baiyi da mutuwa ba har xuciyarki taraya miki kifita nemo miji 😰
Ki duba wannan wankan da kikayi dan kawai maxa suganki Su biki su yaba
Gaskiya kinci amanar sO
Na tabbatar da ace xai dawo yaganki haka daya tsaneki....

Kuka SAILUBAH tafashemai dashi wiwi tana cewa Allah ya isa tsakanina dakai
An gayama ni 'Yar iska ce da xanje neman Maza

Yace aiko baki fa'da ba. me hankali kallo 'daya xai miki yagane cewa maxa kika fitoh nemah

Ran SAILUBAH ya qara 6aci Tace 'dan iska kawai
Yace baxanji haushi ba idan kince min 'dan iska dan nasan kinji takaicin yanda nagano manufarki ne

Wani kukan ya qara kamata tashige falan nasu tana qara rerawa.

Wanda hakan kuma ya fara damun xuciyar Junior kenan
Dan haka yabita yana cewa kifitoh Ki tafi abinki rayuwace ai. Dan na tabbatar inda kece kika mutu brother bashi ba 'Yan mata har abada😆...

Bata kulasa ba tayi 'dakinta da xama a hannun kujera tana cigaba da kukanta

Kaka takallesa Tace me kamata ne
Yace Bakomai
Innah Tace ya xakace Bakomai bayan yanxu tafuta da dariya
Murmushi yayi Yace bara in lallaso muku ita toh
Yana fa'din hakan yayi 'dakin nata yana cewa haba uwar 'Ya'Yana.....
Wannan Suna da yake kiranta dashi yana tsumah xuciyarta

Ahankali ya durqusa a gabanta Yace kiyi hakuri kinji baxan sake gaya miki magana haka ba Insha Allah....
Ya fa'di yana mai goge mata hawayan Cikin wani yanayi na sO
Suna ha'da ido ya sakar mata wani shegen Murmushi Wanda yasata rintse idanta tana jin wani fa'duwar gaba na shigarta
Ya qara yin Murmushin da tashi ya dafa hannun kujeran yana cewa toh kiyi dariya mana
Tace baxanyi bah
Yace idan bakiyi ba xaki jefani cikin wani hali
Tace me xaisa kashiga halin
Yace saboda ke amanata ce agareni
Idan na 6ata miki wlhi rasa nutsuwata xanyi

Ashagwa6e Tace indai hakane kabarni
Yace nabarki Amma kibari gobe ranar hutuce nakaiku.
Tace hmmmm


Xaxxagar hoda yayi ya shafa mata Yana cewa gwara na 6atar miki da wannan hawayan danna sami nutsuwa
Harararsa tayi Tace Allah karka qara cewamin zanje neman Maza
Yace toh kidena fitta man
Tace baxan dena bah
Yace toh kar kimin rashin kunya mana
Da mamaki Tace nice xan maka rashin kunya ni sa'arkace wai
Yace Amma dai Kinsan Komai qanqantar 'da namiji gaba yake da mace...
Qaryane Wlhi
Tafa'da tana mai danna wayarta da ganin sakwan daya shigo mata tun 'daxo
Naxari tashigayi ka'dan bayan tagama karanta sakwan Tace maye kawai
Junior dake kallanta idansa kan le6anta Yace Waye haka
Takallesa tajan tsaki Tace wani ne yaketa damuna da kalamai
Toh Ki blocking nasa mana inda gaske yana damunki
Tace share kawai dan.....
Dan kalamansa na miki da'di ko
Yayi saurin katseta da fa'din hakan.

Tace eh Amma bai fara birgeni bah
Yace gaba ka'dan dai...
Tace xai fara birgenin Yace kawai na fa'da ne dan nasan ba wanda xai iya burgeki
Tace hmmm meya dawo dakai da wuri haka
Yace ciwo
Meyake samunka
Ciwan sO
Wacece wacce kake Son
Fateemah
A ina take
Fage
Da sauri takallesa kana nufin unguwarmu 'daya
Yace eh Amma bai xama Lalle Ki santa ba.
Tace ko
Yace Yah
Tace tana da kyau
Yace komai naku 'daya.
Tace wane layi take
Kinga malama tsaya haka. Xaki isheni da tambaya kamar wata matata..
Yafa'di hakan da miqewa yana gallah mata harara
Murmushi tayi Tace nidai ban ta6a ganin mara kunya kamarka ba Wlhi.....

Murmushi yayi mata kawai ya futa daga 'dakin itama tabishi abaya
Innah Tace ka lallashetan. Yace gata kin ganta. Kakah Tace aikuwa kam
Haka ya ficcewa xuciyarsa tam farin cikin hanata futan dayayi dan kar maxa Su gane mishi ita😂




(Munga senior RAMADAN mah😆)

KHAMIS ya kallesa Yace meya sata kuka
Yace badai ni bane
Yace amanace dai gareka.
Murmushi junior yayi mai kawai


---------------
Washe gari ko da misalin qarfe biyu tagama shirinta tana Jan tsaki akanma wane dalili Junior xaice saidai sufita tare....
Tana saqar xucinta ya shigo palan yana cewa uwar 'Ya'Yana gani naxo
Tana jinsa tayi bansa dashi
Shiko Jan KAULEET da KHAULAT yayi suka ficce yana yima Su innah sallamah

Tanajin fitarsa itama tafitoh cikin shigar doguwar tayi kyau Sosai
Tace toh Kakah Innah saimun dawo.
Adawo lapia

Tunda tafitoh idansa yake kanta dan baqaramin kyau tayi masa bah
Amma Sam bai bari tagane ita yake kallo ba dan gilashin dake idansa
Duk yaran suna baya dan haka tashiga gaba tana qare mishi kallo dan jin qamshin dake fitta daga jikinsa
Shege ya iya wanka😂...
Abinda Tace kenan aranta
Yace nafiki kyau ko
Ta Kawar da fuskarta tana ya mutsata Tace ko kusa.....
Murmushi yayi da fa'din wannan axahiri yake ai...
KHAULAT Tace Dady kafi Momy kyau
Yace nagode Babyna

KAULEET ko cewa tayi Momy kemah kinyi kyau Ammafah Dady yafiki kyau😀
Murmushi SAILUBAH tayi kawai

Wani wajan shaqatawa sukaje Wanda yasasu jin da'di Sosai
Amma ga Junior abin ba haka yake ba
Dan duk hankalin maxajan wajan Idansu akan SAILUBAH yake
Dan haka Bashiri Suna 'Yan ciye ciyensu Yace sutashi sutafi
Harararsa SAILUBAH tayi Tace asan raina naso nakai qarfe biyar
Amma tunda kace haka muje. Saidai baxan qara fita dakai bah Wlhi
Murmushi yayi Yace Naji dai muje
Da 6acin suka dawo gida Bayan sun biya supermarket sunyi siyayya

Yana yin fakin cikin gidan nasu sukaga wani qatan mutum attajiri xaune akan kujerun harabar gidan
Gabansa cup ne da drink da alama ya 'dan da'de da xama agun.
Kallo 'daya Junior yayi masa yagane nemane ya kawoshi
Nan take kishi ya cika xuciyarsa
SAILUBAH ta kallesa Tace wannan kuma Waye
Yace oho miki. Ai Kinsan batare muka shigo bah
Tace karka nemi ka gayamin magana daga tambaya
Galla mata harara yayi Yace ninace tambayeni ai 'Yar rainin hankali.
Kwafah SAILUBAH tayi tafice daga motar da nufar gun mutumin....

Junior yaja tsaki
KAULEET sarkin surutu Tace Dady Kullun sai kunyi fa'da da Momy ne
Ahankali ya kalleta da Murmushi Yace aa my baby ba fa'da muke bah 😆
Xata qara magana yasa mata sweet abaki. Shuru tayi kamar yanda KAULAT tayi tanata shan nata sweet 'din
Bu'de musu yayi mukayi ciki da murnar dawowarsu
Sannan ya maida kallansa ga SAILUBAH

Ahankali taxauna tana cewa sannu dai
Da Murmushi Alhjn Yace Yauwa sannu SAILUBAH kundawo
Tace eh
Yace madallah. Dama 'daxo naxo kakarki Tace kin fita Amma bada'dewa xakiyi ba
Jin hakan yasa Nace bara in jiraki
Wato SAILUBAH sO da qaunarki CE tayi min mugun kamu dafatan wani be rigani bah....

Kallan Junior SAILUBAH tayi
Aiko karab suka ha'da ido
Gabanta ya fa'di idanta ya fara mata gixo akan anya ba Qaninta bane yake kallanta.......

Nan xuciyarta tafara jagula mata lissafi
Kuma taqi 'dauke idan nata akansa kamar yanda shima yaso dan yasan in tana kallansa baxata iya Komai cikin nutsuwarta bah
Danshi yasan kansa😬......

Bakice Komai ba....
Alhjn ya katseta
A'dan tsorace ta kallesa bakinta na 'dan rawa Tace ban ban banji me kace ba....

Murmushin mugunta junior yayi dan yanda yaga bakinta na rawa yasan tashiga yanayin da yake San tashiga ne


Alhjn Yace cewa nayi sO da qaunarki ne yayi min mugun kamu ina fatandai ba Wanda ya rigani.......

Dake hankalin SAILUBAH nakan junior tanajin bu'de 'kofar motarsa takai kallanta garesa
Aiko ya jingina ajikin motar Yana kallanta da shagwa6e fuskarsa
Yace Auntyna......

Da sauri SAILUBAH tatashi tana cewa Qanina.....
Shuru Junior yayi mata yana aike mata da wani sirrintaccan kallo
Ahankali ahankali tafara nufushi tana xuwa daf dashi Tace kadawo gareni ko
Wani shegen Murmushi yasakar mata tare da ware hannunsa tayi saurin rungumarsa tana cewa I Luv u Qanina
Cikin wani salo Junior ya qara rungumarta yana cewa me 2 my luuuuu......
Agigice SAILUBAH ta 'dago da kanta Cikin mayen sO takama fuskarsa da dukkan hannunta biyu takai bakinta cikin nasa🙈 tafara kissing 'dinsa Sosai afurgice🙊.

cikin nutsuwa ya 'danyi dabarar hanata.

Ganin hakan yasa ta qanqameshi Sosai takwantar da kanta a qirjinsa tana sauke numfashi......
Ahankali ahankali yafara shafa bayanta

Sanda Junior ya tabbatar da futan Alhajin nan daga gidan Sannan ya 'dago da ha6arta ya fara shafa fuskarta ahankali cikin nuna MASEEFAR SONTA.
Duk ya furcitata ta futa a hayyacinta
Ahankali Tace dan Allah karka qara barina RAMADAN
Tafa'di hakan idanta cikin nasa
Murmushi ya sakar mata da rabata da jikinsa a hankali Yace mexaisa na barki.
Amma ai shi nakin ya tafi inda ba'a dawowa.
Kidawo cikin hayyacinka mana
da Junior kike fah😀
Ya kamata muje musauke farali La'asar na jiranmu
ya qarashe da yafa gefan fuskarta cikin kulawa

Yana fa'din hakan ya nufi barin gidan.....

Sororo SAILUBAH tayi sai yanxu hankalinta ya dawo jikinta😳
Tayi saurin dafe kanta da jingina a jikin motar. Ba xatoh ta fashe da kuka 😭

Yana Jin kukan nata ya share da bu'de 'kofar get 'din gidan ya ficce yana dana sanin barinta da yayi tayi kissing 'dinsa
Yauxu tajefashi a maseefa yau yaji lallausar le6anta👄 lips 👄 da yake fatan mallaka🙉


Iuv u❤all


Da kukan tayi falon nasu
Innah tace ikwan Allah wai meyake damunki ne SAILUBAH
Shuru tayi mata da shigewa 'dakinta
KAULEET Tace Dady ne yasata kuka
KHAULAT Tace aa Kullun ai saitayi kuka ko Innah
Murmushi innan tayi

Junior ko Bayan ya idar da Sallah lamo yayi a gadansa yana tuno Al'amarin daya faru
Lumshe ido yayi yanaji aransa damah Su dauwama a wannan yanayin.

Wayarsa ya janyo yafara mata rubutu kamar haka

```Xuciyata na bugawa my Luuuuu. Da alamah baki cikin kwanciyar hankalinki```
```Gaya min Babyna meya faru dake. kinji nutsuwata```

Yana gamawa ya tura mata


Itako kukanta take Sosai dan tuno da Senior da tayi
Tana Cikin kukanne taji shigowar saqo
Bata duba ba. Tatashi tayo Alwala tayi Sallah dayima Senior addu'a
Kafin tamiqe a kujera da niyar kiran XEE
Saidai Ganin sakwan nata yasata dubawa

Shuru tayi tana tambayar xuciyarta wai waye ne wannan
Cikin Takaici tabashi amsa da
```wai kai waye ne```

Junior nagani yayi Murmushi
```Mesan xama miji agareki nahar abada```

Jah numfashi tayi kafin tabashi amsa da.....
```bana San kowa ya xamah miji agareni dan na rufe babin aure arayuwata```

Yace.....
```Xako kiyi kisa inhar baki aureni ba. Dan ina tabbatar miki da cewa mutuwa xanyi```


Dariya tayi da cewa....
```Toh kamutu man. ina ruwana```

Murmushi yayi
```wlhi baxan mutu ba harsai na mallakeki matsayin matata kin haifamin yara kyawawa kamarki. Masu kyan sura da yalwar gashi me santsi da sheqi. Masu fararan ido tamkar madara. Masu lallausar fata me tafiya da ruhin mutum```

Gyara kwanciya SAILUBAH tayi....
```Alamu sunnuna xakayi surutu da yawa```

Murmushi ya qara yi.....
```hmmm Kiyi mafarkina my Luuuuu. Tunda na fara damunki. Saidai Ki share hawayanki kafin kiyi mafarkin nawa```

Tashi SAILUBAH tayi da mamakinsa wayace mishi tayi kuka da sauri ta fara typing.....
```Wayace maka nayi kuka```


Murmushi dai ya qara yi ganin tambayar tata.
Bai bata amsa ba ya ture wayan yana tuno lips 'dinta👄 da lumshe ido cikin son ya qara jinsu
Ahaka baccin yamma yayi awan gaba dashi


Itako SAILUBAH ganin bai bata amsa ba saitaja tsaki da Neman layin XEE. Ringing ko biyu wayan tayi XEE dake falanta tana chatin ta'dauka da cewa 'Yar Uwa yadai
Tace hmm kedai bari. Wlhi XEE banta6a ganin 'dan iska irin junior ba
Dariya😀 XEE tayi Tace a'iya sanina dai tunda RAMADAN yarasu junior bai miki Komai bah
Tace toh ya fara yanxu. Dan yadawo da rashin kunyar da yake min. kinsan ma me yayimin 'daxo
XEE Tace meya miki.......
Kwashe Komai SAILUBAH tayi tagaya mata taqara da cewa dake 'dan iska ne barina yayi nadinga aika masa da sakwannni 😀
Sanda yajini dakyau kafin ya ankarai dani 🙈

Waro ido😳 XEE tayi da cewa tab😊
Eh ya tabbata 'dan iska
Yanxu kun qara ha'duwa ne
Tace inafah yana can ina gida
Saidai kinsan dake ya kware a iskanci baxai wani nunamin komai bah
Murmushi XEE

Please Login or Register in order to submit comment