Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai yana kallan sama Cikin tunani Yace HAMEEDA wacce tayi bandaro.
RAMADAN Yace miye bandaro
Yaran ya kalli RAMADAN Yace yanxu bakasan miye bandaro ba
KHAMIS Yace eh miye
Yace bandaro shine abinda yaqi siyuwa a kasuwa
FAWAS Yace ita toh 'Yar tallece da taqi siyuwa
Yaran yayi dariya
Yace aa itafah ba wanda yake Santa ne dan sa'anninta duk sunyi Aure harda yara itako tana gida ba mashin shini
Koda yake tana hannun wata qanwar babanta ne Innah Hansai
Sam bata santa aiki take sata Sosai ba qaramin gana mata axaba take bah........
RAMADAN Yace ya isa haka. Muje karakamu gunta ko itace wacce muke nema
Aiko yaran ya shiga motar tasu yanata murna yau gashi amota har suka iso gidansu HAMEEDA
Yace toh ga gidan
FAWAS Yace jeka kira mana ita
Yace aiko naje innanta baxata bari ta fitoba
RAMADAN ya dafah yaran Yace akwai samari agidan
Yace eh mutum 'daya ne Alo
Yace OK yanxu dai ga wannan. Ya miqa mishi gudar 'dari biyu Yace ka sai littattafai na makaranta kaji
Cikin farin ciki da murna Yace Nagode Yaya Allah yasaka da alkairi ya fitta daga motar
Har yayi nisa ya dawo idanshi nakan RAMADAN Yace ko in shiga in yima innan tata wayo sai in gayama HAMEEDAN xuwanku
FAWAS Yace Yauwa yaran kirki maxa jeka
Aiko ya shige gidan da gudu
A tsakar gidan yasamu HAMEEDA tana tanka'dan masara
Cikin farin ciki Yace HAMEEDA kinyi baqi 'yan gayu 'yan birrni
Tace suna ina Yace suna 'kofar gida
Tace bari toh nayi sauri naje kan innah ta dawo
Yace bata nanne
Tace eh taje gidan jummai
Yace kiyi sauri karsuyi xuciya Su tafi
Tace kafiye surutu Ya'u kace ina xuwa
Yace toh

Da murna yake gayama su FAWAS gatanan xuwa sukace toh mungode ko
Yaran yana barin gun HAMEEDA ta fitoh

Dama RAMADAN da KHAMIS Suna cikin mota ya yinda FAWAS ya fitoh ya jingida da motar
Aiko ya xuba mata ido
Taqarasa gareshi Tace wai da gaske kakeyi
Yayi Murmushi Yace eh kai. Ko baxaki soni bane da gaske in qara gaba
Tayi dariya Tace aitunda kai 'dan birnine baxan qika bah
Sai dai matsalar kai qaramin yaro ne.....
Ya katseta da fa'din. Naji ni qaramin yaro ne Amma xan iya riqe mace ai
Tace kai yanxu kasan me ake kira da Aure
Yace ban sani ba Amma inna aureki saiki sanar dani
Tace aini ba 'Yar iska bace
Yace oho nine 'dan iska
Tace nidai bance ba. kawai kashere batun son da kake min
Yace baxan share ba. Dan kinyi min tako ta ina
Tace me kake so kace
Ya wurga mata wani kallo nan take taji yayi mata wani bala'in kwarjini jikinta kuma ya mutu cikin sauri ta sunkuyar da kanta qasa
Yayi murmushi dan ya hango yanayin data shi
Yace inaso ince ke kyakkyawace kuma abin San kowane 'da namiji
Da sauri ta kallesa Tace da gaske ni kyakkyawace
Kuma abin san kowane 'da namiji
Yace kwarai ma kuwa
Tace shege Iro 'dan iska Yace nafi kowa muni a qauyannan namu
FAWAS ya waro ido😳 kamar gaske Yace wanene shi haka in hukuntashi
Tace wani me satan kajin Mutane ne duk qauyannan sun sanshi Sam bashi da hali me kyau

Dawai yana sona toh danace bana san shi shine ya gayamin baqaqen maganganu har dacewa ni mummunace kuma wai ahaka xan dauwama agidan mu ba mashin shini bare inyi Aure.
Ta qarashe da nuna damuwarta
FAWAS yajah numfashi Yace kalleni. Ahankali takallesa
Yaci gaba da fa'din. kina sona.
Ta lumshe da 'daga mai kai
Yayi Murmushi Yace kin yarda zaki Aunreni Ki nunamin me ake nufi da Aure
Ta rufe fuskarta Tace eh
Yace toh daga yau ko bananan Karki kuskura Ki kula wani saurayi dan ina da kishi xan iya illata duk Wanda naxo nasamu dake

Cikin shagwa6a da daure fuska Tace ni fah banda saurayiπŸ˜”
Yayi Murmushi da fa'din. Shi Iron fah
Tace ainace maka nace bana sanshi ko.
Yace toh naji
Nan sukayi shuru
Xuwa can kuma Kamar an muntsineta takallesa da Murmushi
Tace in kawo muku 'dan malele yana da da'di Wlhi
Da sauri FAWAS Yace aa barshi
Ta 6ata fuska kamar xatayi kuka harda juya mishi wai ita adole ranta ya 6aci kuma tayi fushi
FAWAS yayi Murmushi ya dawo gefan data juyamai bayan ya ha'da hannunsa biyu alamun ban ha'kuri Yace yi hakuri YAYATA jeki kawo min Amma ni 'daya
Da sauri ta kalleshi da dariya Tace da gaske xakaci Yace eh mana. kin san ai baxanqi abin Masoyiyata ba.
Tace naji naqara sanka Yace Allah yasa na mallakeki matsayin matata
Tace AmEEn da shigewa cikin gidan nasu ya bita da kallo

RAMADAN da KHAMIS suka fitoh daga motar suka sakama FAWAS dariya
RAMADAN Yace xakaci 'dan saluhu ko 'dan talatu tace maka ne ko Mene

FAWAS yajah tsaki Yace ban sani ba

KHAMIS Yace katemaki kanka da kace takawo maka kai 'daya.
Kanya bashi amsa harta fitoh da wata tsohuwar robah ta ajiye akan dakalinsu
Kallo 'daya FAWAS yayima robar gabansa ya fa'da
Dan Wlhi ko karansa na gidansu yafi qarfin cin wani a robar
Haka yaje gareta ya xauna a dakalin
Tace kaganshi ko. Yanxu na gama da xafinshi gashi yaji manja
Arayuwar FAWAS bai ta6a ganin irin wannan abun ba
Yace aikuwa gashi nan sai Qamshi yake ya ake cinsa
Tace kai😳 bakasan 'dan 'danlele ba
Ya juya kai Yace tunda yanxu ina tare dake ai Xan sanshi ko
Ta 'dagamai kai Tace aha. Dake kai 'dan birni ne kaga harda cokali na kawoma.
FAWAS ya kalli cokalin wani ko 'dad'de dashi sai dai a tsaftace yake
Ya kar6a da Murmushi Yace Nagode
Nan ya gutsira ya kai bakinsa.......
Aiko cak ya tsaya shi bai ha'diye ba kuma bai xubar bah.....
Yayinda ita kuma ta kafeshi da ido. Ganin haka yasashi ha'diyewa da sakar mata Murmushi
Tayi dariya harda tafah hannu Tace yayi da'di ko
Ya 'daga mata kai cikin murmushin yaqe Yace Sosai mah
Tace Yauwa saika cinye dukka in qaroma kan Innah tadawo
FAWAS ya waro ido Yace in cinye fah kikace. Tace eh ko wani abune
Ya kalli Su RAMADAN cikin damuwa kamar xaiyi kuka Yace aa

RAMADAN ya kalli KHAMIS suka saki dariya
RAMADAN Yace bala'i. Watoh shidai SOO maseefa ne
KHAMIS yayi dariya Yace haka siddan gari banxa wani yaba FAWAS waccan jagwalgwalan sai mutum yasha mari Amma dake SOO daban yake da Komai kaga ko xaiyi kuka sai yayi yanda takeso
RAMADAN yayi Murmushin mugunta Yace bari mugani koxai cinye idan ya cinye insa ta qaro mishin
KHAMIS ya waro ido Yace haba dan Allah ka tausaya mishi aiπŸ˜†




Yace ai tunda yaqi yarda naje ga Auntyna Wlhi saina guma masa.
KHAMIS ya qara yin dariya


Da ace HAMEEDA tasan FAWAS toko da tagane yanacin 'dan malelanta ne tamkar xaiyi kuka....
Cokali hu'du yayi yana tunanin inya qara na biyar toko ba abinda xai hanashi yin amai
Ya kalleta ka'dan. Idanta nakansa. Yayi Murmushi Yace YAYATA.....
Da sauri ta sakar mai murmushi Tace na'am
Yace na koshi
Nan take annurin fuskarta ya 'dauke Tace meyasa ka koshi bayan.......
Saurin katseta yayi dan ganin annurin nata ya 'dauke
Yace wasa nake miki. Da xaki 'daure min fuskar nan taki me kyawun kallo.
Ta saki fuskar tata tare da rufe fuskar da hannu Tace har naji da'di Wlhi.

Ganin da gaske tana Cikin jin da'di shiyasa FAWAS daurewa ya dinga cin 'dan malelannan har ya cinye
Da sauri Tace in qaro maka
Ya kalleta cikin marairai cewa Yace aa
Tace karka damu akwai da yawa
Ya qura mata ido yana kissima abubuwa da dama aransa akanta

RAMADAN ya kalli KHAMIS Yace Wlhi qiris FAWAS yake jira ya saki amai
KHAMIS Yace wlhi kuwa gashi ta kasa ganewa
Yace bara naje na 'dora mishi da nawa
Kan KHAMIS yayi magana RAMADAN ya fito daga mota ya nufusu da Murmushi Yace dan Allah ki daure in akwai da yawa Ki qaro masa dan dama baici abincin rana ba
Haka kawai ya tsinci kansa da qinci. Ashe xaixo ne ya tarar dana masoyiyarsa ne. Baki lura da yanda ya cinye bah pls yi sauri ki qaro masa mana
FAWAS ya maida kallansa qasa da dafe kansa.
HAMEEDA Tatashi da murna Tace aikuwa nayi da yawa
Daqar FAWAS Yace ka'dan xaki qaro pls.....
Bata jishi ba tayi Cikin gidan nasu da sauri burinta yayi ya gama kar innah ta dawo

Dama tana barin gun RAMADAN ya koma mota. FAWAS yabishi da kallan ramuko

Haka ko takawo masa kamar na 'daxo
FAWAS ya rufe ido ya dinga ci batare da yace mata Komai ba. Har yaci rabi
Ya kalleta Cikin wani yanayi Yace da kinada leda da kin sakamin sauran dan anjima incinye.
Taxaro wata leda daga gefan cikinta Tace gashi dama kamar nasan xaka buqata. Dana juye masara naqi yarwa
Yayi Murmushi da kar6a ya juye cikin ledar

Yace toh fa'damin
Tace me fah
Yace kin yarda in dinga xuwa gareki ta'di har Allah yasa Ki xama mata agareni
Tace eh
Yace toh Nagode ga wannan Ki sai abinda kikeso. Ya qarashe da miqa mata dubu biyar
Ta waro ido wajeπŸ‘€ Tace kai kai kai tab😳
Yace wani abune
Tace ko 'Dari biyar ban ta6a riqewa ba bare sama da ita
Idan aka ganni da wannan Wlhi ba qaramin tashin hankali xan shiga ba
Yayi Murmushi Yace Kinga ko bana san tashin hankalinki Sam
Amma Ki kar6a Ki 6oye xai miki ammafani.
Ba xanji da'di ba in baki kar6a ba
Amma idan kika kar6a xanfi yarda da cewa lalle kin yarda in xama miji agareshi tunda nabaki abu kin kar6a batare da gaddama ba

Tayi shuru. Candai ta kar6a Tace Nagode Allah yasaka. Amma miye sana'arka.
Yace ina skull yanxu ina karantar kasuwanci ma'ana nan da Wasu 'Yan shekaru xan xama cikakken 'dan Kasuwa
Tace shima dama kasuwancin karantarsa akeyi Yace eh ai ba abinda ba'a karantarsa
Tace tab ni ban San kasuwancin karantar sa ake ba.
Yace hmm kina karatu kuwa
Tace ban San ilimin boko ba. Nadai sauke alqur'ani da sanin Wasu takaddun musulunci irinsu nahahu kawaqidi adaf hadis da dai sauransu
Yace eh lalle kice da malama nake
Ta kallesa cikin sanyi Tace nasamu wannan iliminne agun BABANA da'ace iyayena sun mutu tun ina yarinya na tabbata baxan samu komai bah

FAWAS Yace 'dan naji labarinki ka'dan.........
Nan tabashi labarin kanta.
Yace yanxu kina nufin duk wani aiki na gidannan ke kikeyi
Tace ba aiki ka'dai ba harda aika xuwa ko ina
Yaqura mata ido tabbas kallo 'daya yayi mata Komai nashi ya kunce yaji maseefar sonta
Cikin wani yanayi yace yanxu xan iya samun matsala wajan xuwa na gareki
Tace indai bana san matsala ta afku Saidai iyayanka suke wajan me gari da maganarmu
Kasan yana hukunci bisa kan Gaskiya
Xai kirani agaban mutane ya tambayeni ina sanka
Idan Nace eh
Toh saiya sakama Innah Hansai Duka akan karta kuskura ta takura min akanka
Sai kuma Yace ma iyayanka Su gaggauta kawo sadaki ayi Aure

Yayi Murmushi Yace daga nan shikenan kin xama tawa saiki koyar sani yanda Aure yake ko.
Ta dariya da rufe fuska cikin shagwa6a da ta6ara Tace toh yaushe xaka dawo
Ya kwai kwa yi muryarta wajan cewa jibi idan kinaso
Ta qarayin dariya danjin yanda ya kwaikwayeta. Tace kaga banaso
Yace toh nadena 'dan bu'demin fuskar ka'dan ko na sami bacci cikin nutsuwa yau.
Tunda Allah yasa nayi gamu da kyakkyawa wacce tafi kyawawa kyau
Ta 'dauke hannunta daga fuskar tata ta kallesa damai fari da ido tana 'daga mai gira irin tasu salan soyayyar ta qauyawa.......

Amai yakeji saboda ba qaramin cika cikin sa yayi bah. xuciyarshi tashi take sobada bai saba da cimar data bashi ba. Burinshi takauce mata ya amayar da shi ko yasamu kanciyar hankali

Yayi Murmushi dan ba qaramin burgeshi tayi ba. damai fari da idan da tayi
Ya tashi yana cewa wannan fari da ido haka. aisai kisa in sume a axaune
Ta rufe fuskarta Tace Allah
Yace kunyarki na burgeni
Tayimai shuru
Yayi Murmushi da cije le6ansa.
Ni xan tafi saikin ganni jibin
Tace kamar karka tafi Wlhi

Ya 'daga mata gira Yace idan bakyaso ai sai in tsaya har Innah tadawo immata gaisuwa
Ta waro ido da cewa tab kace tarabani dakai kenan
Yace aini bamai rabumu sai Allah Ki kulamin da kanki pls bana San wani abu ya sameki
Ta 'dagamai kai cikin Murmushi
Ya shige motar tasu
Ta 'dagamai hannu alamar bye bye
Shiko ya sakar mata wani kallo me kashe jiki
Nan ta'dauke hannunta cikin sanyi dan kallan ya shigeta

KHAMIS ya tada motar sukabarta nan



Suna fitta daga qauyan. FAWAS Yace pls bani minti biyu KHAMIS
Ba musu KHAMIS ya tsaya da motar agefan titi

Sosai FAWAS yadinga sharara amai kamar xai amayar da hanjin cikinsa
Yana gamawa RAMADAN ya bashi ruwan gora ya wanke bakinsa
Kana KHAMIS yajah motar

Banda dariya ba abinda RAMADAN da KHAMIS sukema FAWAS
RAMADAN Yace kaci da yawa fah
KHAMIS Yace Sosai mah kuwa
RAMADAN yasa dariya Yace daga ganinta xatayi da'din Luv dan tana tare da shagwa6a.
KHAMIS Yace nima na lura da hakan Sosai
FAWAS najinsu yayi musu shuru....


Tunda suka sako kan motar tasu layinsu RAMADAN
Gaban RAMADAN ya dinga fa'diwa. Tuni damuwarsa ta dawo masa sabuwa fill
Haka suka saukeshi sukayi gaba KHAMIS na fa'din yasan Aunty XEE na gidansu Aunty LUUVAH bayasan Su ha'da yanxu sai dare..


πŸ‘―: Wanka RAMADAN yayi ya canja Kaya da wadata kansa Qamshi
Sannan ya nufi gun Auntyn tashi




Tana kwance a gado XEE na gefanta ga qawayanta nan sai hira suke
RAMADAN ya shigo 'dakin
XEE ta 6allamai harara Tace ban ta6a ganin qani mesa Auntyn shi cikin damuwa da tashin hankali ba kamarka RAMADAN.......
Da sauri ya katseta da cewa haba Aunty XEE kidena haka. Yanxu xakisa taqara jin haushina bayan KHAMIS ne Babban me lefi dayaqi gaya mata inda nake
Tace eh Gaskiya. dake gaka gata ai dole ka kanemi kare kanka. Karka wani saka KHAMIS dan bashi da lefi
Ya kalleta da Murmushi Yace toh Naji bashi da lefi
Ya maida kallansa ga Auntyn tashi wacce ta kafeshi da ido tun shigowarshi
Yace Barka da yammaci my Aunty
Ta sauke ajiyar xuciya Tace me yasaka ramewa haka
Ya tashi yana cewa tunani da tashin hankali
Tashi itama tayi Tace muje
Ba musu suka jero tare har xuwa gidansu part 'dinsa
Ta xauna gefan gado shi kuma yana kan kujerar da take fuskantarta
Tace wane tunanine haka da tashin hankali yasaka ramewa
Ya kalleta ka'dan Yace kema ai kin rame Sosai
Tace kaban amsata
Yace hmm tunaninki Auntyna mana....
Wai a tunaninki rabuwa dake xai barni na xauna lafiya ne.
Hmm Sam hakan baxai yuhuba
Dan daga ranar da kika bar gidanku xuwa gidan wani toh Ki tabbatar baxan qara samun kwanciyar hankali arayuwata bah
Saban danayi dake ya kai matsayin da in tunaninki yayimin yawa xan iya rasa rayuwata........


Kuka SAILUBAH tasamai Sosai.....
Duk da hankalin RAMADAN ya tashi Amma sai ya share dan yanxu burinshi yayi mata abinda xaisa taji xafi fiye da yanda yakeji axuciyarsa
Nan ya hau 6arar mata da kalamai cikin qara kashe mata xuciya da takaici
Fa'di yake narasa me kika gani ajikin wannan mutumin Sam bai dace dake ba
Ina ganin ma 'dan shan jinine
Dan bashi da fuskar imani
Ki kula dashi Sosai mana
Gashi shi ba wani kyakkyawa bah.
Kawai Kinga ku'di kin yarda yaxama miji agareki
Akan ma wane dalili xaki yanke igiyar shaquwarmu saboda shi
Nayi baqin ciki da takaicin hakan.
Bani da wani buri daya wucce in tayaki neman xabin ranki. Kyakkyawa me aji me ku'di me maseefar kishinki.

Nayi addu'ar istahara nayi Sallah akan Allah ya bani haske akan lamarinki dashi.....
nagani Cikin mafarkina Auran shi nadama ne agareki

Ni fah baxan 6oye miki ba. In bake baxan iya rayuwa sak kamar yanda aka sanni ba

Kuka take Sosai yana qara jefah mata qiyayyar Alhaji Aminu

Can dai dayaga kukan yayi yawa kuma yana maseefar damun xuciyarshi sai ya matso kusa da ita ya kama hannunta
Yace toh kiyi shuru kidena kukan nan tunda kina sanshi baxan qara kushe miki shiba tunda ranki na 6aci kiyi hakuri
Ki dena bana so. inba so kike Ki hanani bacci ba. Yafa'di hakan da leqa fuskarta cikin kusanci dasan qara hargitsa mata kwanya

Aiko ta shaqa
Dan yanda yayi kusanci da ita ka'dan ya rage bakinsu ya ha'du dana juna
Ganin yasami abinda yakeso dan jikinta ya mutu mu'dus. qiris take jira ta xubemai ajiki. Shiyasa ya 'dan janye kansa ka'dan daga gareta tare da jifanta da wani kallo Wanda atake yasan ya gama kunce mata Komai.

Ta lumshe idanta tare da dafe kanta Tace bana sanshi bana sanshi
Na da'de dasanin Kaine kwanciyar hankalina RAMADAN
Ban San me yake damuna ba.

Kina sanshi tunda kike min kuka akansa. Kuma aida bakya sanshi ko kusa baxaji sha'awar kar6ar abin hannunsa bah. RAMADAN Ya fa'da dasan qara harxuqa xuciyarta

Aiko cikin fusata Tace wai kai wane irin 'dan iskane
Nace bana sanshi bana sanshi bana sanshi Amma sai qara Sa xuciyata xafi kakeyi tun kwanaki can da suka wucce nayi dana sanin sanin shi

Yariga da ya samu guri gun Abbana ya hanashi kallan ra'ayina
Ya kakeso nayi ne RAMADAN. So kake na haukace
Naji Komai bana jin da'dinsa aduniyar nan saboda qaurace min da kayi.
Sam nalura bakasan farin cikina
To bara kaji na rantse da Allah ka kara min haka sai mun sami mummunan matsala dakai

Dan narigada na auna na garo ba abinda yake tadamin hankali kamar rashinka kusa dani

Da 6acin rai Tatashi da niyar barin 'dakin.......
Cikin sauri ya Sha gaban da yanayin damuwa......
Yace 6acin ranki tashin hankaline agareni
Ki temaken kisaki ranki ko nasami nutsuwata
Tace matsamin in fitta ko kasha mari.......

Yasan acike take dashi Komai xata iyayi masa
Saidai kash yayima kansa alqawarin baxai barta tatafi awannan yanayin ba
Dan yanasan yau ya bala'in hargitsa mata kwanya

Dan haka cikin yi mata baxata ya rungumeta da kashe murya irinta Wanda yake yin kuka
Yace kimin rai auntyna kiyafemin nasan narabu dake kenan yau har abada. baxan ta6a yafema kaina bah idan har xuciyarki batayi sanyi munyi bankwana cikin farin ciki bah.......

Tundaga tsayar kan SAILUBAH taji wani abu na yawo ajikinta Wanda yasa ta rikice Komai na jikinta ya tsaya cak.....

Cikin wata murya me sanyi Tace toh naji sakeni
Cikin sanyin jiki ya raba kansa daga jikinta idan shi akanta yana San gano wani Abu
Yace kin hakura ta kallesa ka'dan cikin wahalalliyar murya Tace ya xanyi dakai RAMADAN
Pls ina buqatar ka'daita
Ya bu'de 'kofar suka fitoh tare har 'dakin Kakah ya kaita dan nanne ba kowa.
Yace toh Ki huta my Aunty.
Ko kulashi batayi ba
Yayi Murmushi dan yana san ta qara harxuqowa dan bai gaji da maseefar taba
Idan tana magana sam bayaso tadena.
dan haka ya leqa fuskarta Yace toh xan tafi fah Auntyna.....
Kamar xatayi kuka tace wai me xan maka

Ba xaka barni nasamu ka'daicin bane.
Yace da naso kitashi mu'danyi hira ta bankwana
Da maseefa tatashi ta kallesa kamar xata falleshi da mari Tace baxan tashi ba. wai hirar dole ce Nace ina buqatar ka'daici kabarni man
Sai yayi kalar sanyi irin na abin tausayin nan Yace toh shikenan Auntyna Allah ya baki hakuri. Ya nufi hanyar futa
Aiko saita fashe da kuka. Bai tsaya ba ya futa abinsa Yana Murmushi fa'di yake aransa Auntyna kenan duk Sallah idan nayi ina ha'daki da Allah ya xa'ayi Ki xauna cikin kwanciyar hankali akaina. Sam hakan baxai yuhuba

XEE tatareshi a farfajiyar gidan Tace shigowarku 'daxo naga SAILUBAH daga dukkan alamu tayi kuka
Yanxu kuma kafitoh kana Murmushi wai me yasa Sam bakaso kaganta cikin kwanciyar hankaline

Yace Aunty XEE kenan. Wlhi duk duniya bawanda yafini San ganin kwanciyar hankalinta

Kawai batasan Auran wannan shegen ne
Ni kuma dama basan shi nake ba. Saina bata haske akan hakan........

Ta katseshi da fa'din Ka hargitsata dai

meyasa ka tsani ganinta da kowane 'da namiji.
Yace saboda duk wa'yanda take ha'duwa dasu basa dacewa da ita Sam
Ke Kinsan burunta
Auran namiji me aji
Kyakkyawa
Me ku'di over
Me kishinta
Me shakarun da suka xarce nata Sosai
Shin tsakaninki da Allah har yanxu ta ha'da me wannan abubuwan gabaki 'daya

XEE tayi shuru. Can Tace gaskiya aa
Yace hmmm
Kinga Ki share kawai wannan Auran nata ba inda xaije dan xatayi rayuwa ne da Wanda ko kusa bai dace da itaba
Kin santa sarai idan tace ta tsani abu bata sanshi ba tayanda xa'ayi tarayu da wannan abun cikin xaman lafiya
Wlhi ta tsaneshi batasan ha'dinta dashi yanxu
Tayi nadamar saninshi
Ki rubuta Ki ajiye ba'inda Auran sun nan xaije
Idan kin shiga ciki yanxu dan Allah kice tadena kukan ya isa haka
Na barki lafiya. Yana fa'din haka ya wucceta ya ficce daga gidan
XEE tabishi da kallo baki sake
Kana tayi 'dakin khakha.
Har lokacin ko SAILUBAH kuka take ta kalli XEE cikin kukan Tace yaxanyi da RAMADAN XEE yaxanyi dashi
Tace hakuri SAILUBAH hakuri xakiyi dashi
Tace na rasa me yake damuna akansa....
XEE Tace hmm nihar narasa wane tunani Xanyi akanku.......

Wannan dare duk ya rikita mutane hu'du 4 idan ka cire XEE da KHAMIS Wanda yanxu yake tare da ita kusan qarfe tare da rabi na dare.
*Luv*πŸ’” suke xugawa tamkar xasu ha'diye junansu
Sam XEE manta kanta take idan tana tare da KHAMIS
Ya kalleta cikin wani yanayi Yace my Luv
Tace na'am sweetheart
Yace dama ace yanda muke xaunan nan matsayin ma'aurata muke
Tace lokacin na xuwa MENI
Yace kinga mun kusa gama skull ya kamata iyayanmu Susan da xaman soyayyarmu.
Tace mu qara lokaci ka'dan sweetheart
Yace aa fah. nagaji da mafarkan ganinki da yarana inasan inga hakan axahiri
Ta kallesa Tace xaka fara ko
Yace kona fara yanxu dai baxai tabbata ba. Tunda masu ha'dawan basusan da xaman soyayyarmu bah
( *XEE da KHAMIS kenan*)


*RAMADAN*ko Sallah Na dinga ganinshi yanayi ni Rahamat

Addu'a yaketa xabgawa Amma bansan me yake cewa ba
Can ya kwanta ayanda na lura yana cikin farin ciki


*Sa6anin SAILUBAH*
Data kwana kuka da damuwar aranta
Ko wane juyi idan tayi ganinta take rungume da RAMADAN tana shaqar qamshinsa
Wannan abu shiyafi damun xuciyarta
Sam yau bataji Tatashi tayi lafula ba.


*FAWAS ko*
Rasa nutsuwarshi yayi gabaki 'daya
HAMEEDA ta rikitashi
Ta hanashi bacci Sam
Duk juyin da xaiyi hotan fuskarta yake gani tare da jin muryarta tana mishi kurwa akunne



*Ashe itama HAMEEDAN hakan take*
dan har mari tasha agun Innah Hansai dan tafa'da kogin tunanin FAWAS har bata sani bah talgen Innah Hansai ya jinkice daga murhu ya xube bata sani bah
Saida taji saukar mari Tace wayyo FAWAS....
Tace ubanki ne FAWAS 'din xakibar min talge ya xube
Kan HAMEEDA tayi magana Innah Hansai ta rufeta da Duka
(FAWAS kawo magaji)😰







Haka kawai nima Rahamat na tsinci kaina da fa'duwar gaba Ganin yanda mutane suka cika layinsu SAILUBAH dan 'daurin Aure

Na kalli RAMADAN Wanda yayi kyau cikin shigar wani yadi me ruwan madara
Yayi kyau sai Qamshi yake
Haka FAWAS da KHAMIS ma dan anko sukayi
Duk inda kakai da hassadarka saikace yes wa'yannan sun dace da'a kirasu da *~```SAMAREEN BANAH```~*

HAYATUDDEEN ya kallan Yace mutuminki da annuri a fuskarshi banga wani tashin hankali atare dashi bah
Nace hmm wai RAMADAN
Yace eh shi
Nace daran jiya baiyi bacci ba addu'a ya dinga yi
Kasan me yaroqa.
Yace eh gaskiya da walakin goro amiya
πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€



SAILUBAH na kwance akan cinyar XEE xaxxa6i na cafkarta damuwarta taji ance amfasa 'daurin Auran
Dan 'daxo da Asuba tasa Abbanta tayi agaba kan yayi hakuri karya Aura mata Alhaji Aminu
Sai kawai ya kalleta Yace tatashi tabashi guri
Toh shine take cikin wasi-wasi xai Aura mata shine ko aa....

Wasuwasin nata ya katsene lokacin da taji ance an 'daura Auran
*Alhaji Aminu da *FATEEMA SAILUBAH*

Ai SAILUBAH najin haka tasume
RAMADAN Yace innalillahi
FAWAS Yace wa'inna'ilaihirraji'un
KHAMIS Yace shi kenan
Ni Rahamat nace Allah yayi



SAILUBAH Bata samu kanta bah har wajan qarfe biyar na yamma
Lokacin 'yan Uwa da abokan axxiqi suke ta shirin kaita gidan mijinta

Fa'di Take XEE ina RAMADAN. XEE Tace ya shigo 'daxu baki farfa'do ba
Tace xan iya ganinshi yanxu
Tace kai daka mar wiya
Lumshe ido tayi batare da Tace Komai ba

Acikin yamman nan suka 'dauki hanyar Abujah. Basu sami kansu sai qarfe tara na dare

Wani gida ne a maitama Wanda ya hargitsa duk Wanda ya shigeshi
SAILUBAH najin yanda mutane suke santin gidan wai ita dai me sa'ace arayuwarta wannan gida ai aljannar duniyane
Data 'daga kanta taga bet room 'din da take ciki sanda gabanta ya fa'di dan ganin daular da aka narka a 'dakin
XEE ta kalleta tayi Murmushi Tace aha
Bet room ma kenan kije falanki kisha kallo.
Gaskiya xakiyi

Please Login or Register in order to submit comment