Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin damuwa Yace yaxo garin Abujah yau kwanansa uku bana San Su ha'du
Momy tayi saurin cewa bafah ni ka'dai bace
Cikin sauri Dadyn yanemi gyara kansa da cewa Nace wani abu ko
RAMADAN ya kallesa da mamaki Yace kace mana dad
Waye shi da bakasan na ha'du dashi
Dadyn Yace ba dakai nake nufi ba
RAMADAN ya ta6e baki Yace Owkie yanxu dai afara min shiri dad

Dadyn ya kalli momy Yace afara mishi shiri
Cikin damuwa Momy Tace toh
RAMADAN Yace ina buqatan ku'di dad na hannuna sun qare Yace kaje 'dakina ka 'dauka
RAMADAN ya manna mishi kiss a goshi Yace tnx my Dady. Yayi shashin Dadyn da murna
Momy ta gya'da kai Tace akwai matsala Dadyn RAMADAN
Yace babbama kuwa


Washe gari RAMADAN ya cale garin na Abujah dake jirgi yabi

Baiyi mamakin ganin direban Su Yusra yana xaune xaman saukar shi ba
Dan haka suka tafah da Adam direba Yace mutumina ka ha'du fah. Kaga yanda ka girma
RAMADAN yayi Murmushi Yace Yaya Adam kenan har yanxu kananan da barkwancin ka
Yace toh yaxanyi RAMADAN bayan gaskiya nake fa'da
RAMADAN Yace kaga Malam muje daga nan ka 'dorani akan inda katsaya
Da dariya Adam ya tada motar


Ayanda RAMADAN ya fuskanta gidan Auntyn nashi bayi da wani nisa da gidan kawun nasa

Sun isa gidan babban gida murna ta cika gidan Wlcm Ya RAMADAN Wlcm
Baiyi mamakin farin cikinsu ba dan yasan masu qaunarsa ne

Su uku ne yaran gidan
Amar shine saran RAMADAN watanni RAMADAN ya bashi
Sai Yusra wacce take maseefar son RAMADAN tun tana qarama take sanshi sai Ameer qaraminsu yaro me hankali

Cikin Murmushi Amar Yace sannu dai brother.
RAMADAN yayi Murmushi Yace Yauwa na sameku lafiya
Yace lpy lau Wlhi

Toh Madallah. RAMADAN ya fa'da da maida kallansa ga Yusra Yace qanwata yadai rufe bakin mana Tace Ya RAMADAN kenan nayi farin ciki Sosai da wannan xuwan baxatan da kamana
Yace naji da'di da kika ji da'din hakan

Dady da momynsu sai Murmushi suke dan Allah ya 'dora musu san RAMADAN Suna sanshi Sosai
Dady Yace jiya ai Dadyn naka yake gayamin wai haka kawai kace kanasan xuwa garemu
Yace eh Dady kuma inasan Ganin Auntyna mah
Momy Tace SAILUBAH ko
Yace eh Momy ita
Yusra Tace xan rakaka in xakaje gareta
Yayi Murmushi Yace ai kuma tunda naxo shikenan fah na shiga uku agunki
Duk sukayi dariya ya tashi yana kallan Amar Yace toh brother muje inyi wanka in huta...
Dady Yace badai har ka qoshi ba
Yace ai naci da yawa
Yusra tayi dariya Tace nifah na dafa maka
Yace hmm ban yarda ba dan nasan baki iya girki bah
Tace Allah nice nayi Yace na yarda dama nasan qanwar tawa ta iya girki wasa nakeyi
tayi dariya....
Ya tasa Amar agaba sukayi shashinsa

Bayan RAMADAN yayi wanka ya miqe a gado yana san yin tunanin Auntyn tashi da yanda xaije gareta gobe. Kiran wayan shi ya katseshi
Yana dubawa yaga shahuda.....
Da jan tsaki ya picking da Alo
Tace haba RAMADAN lefin menayi kadena 'daukar wayata
Yace wane ke da lefi ai bakya lefi
'Dan jini ka'dan kiji
Tace ina ji
Yace kwana biyu ban riqe wayar bane shi yasa naketa kar6ar hukunci agun mutane pls kar kema Ki hukuntani dan Allah
Tace wane ni
Kana ina ne yanxu
Yace bu'de kunanki kiji dakyau
Tace aha na bu'de
Yace ina garinku kuma inda yake shashinku
Tace dan Allah fah
Yace fa'di abinda xan miki ya tabbatar miki da hakan
Tace yanxu naganka
Yace wa'yanda nake gidansu baxa su barni fitta yau ba
Tace toh gobe na ganka Yace Allah ya karmu
Tace bara na barka ka huta gajiya ko
Yace Saidai ban gaji da jin dad'dar muryarki bah
Tace hmm baka da dama Wlhi
Yace Gaskiya


👯 wata sabowa inji 'yan caca👯

Al'amarin tafaru ne a ranar
Misalin qarfe goma na dare
'Yan fashin suka shiga gidansu shahuda bayan sun buge kawukan masu tsaran gidan da ma'aikata suka shiga cikin babban falan gidan.

Duk Suna falan Suna hira
Shahuda. Dadynta da momynta sai wani 'dan uwanta 'dan Qanin Dadyn nata

'Yan Fashin nan suka musu dirar makiya Su biyar
Nan suka kwanta da tashin hankali
'Daya daga cikinsu Yace ku'di ko rai
Shahuda ta kalli Wanda yayi maganar cikin sauri jikinta na rawa Tace RAMADAN😳
Saurayin ya kalleta da mamaki Yace a ina kika sanni
Tace nice shahuda da mukayi magana 'daxo dakai
Ya 'dauke kallansa daga kanta xuwa ga mahaifinta cikin 6acin rai Yace bakaji me Nace bah
Yace Naji samarii ku'din Suna cikin 'daki. Yafa'da cikin matuqar tsoro..
Saurayin da shahuda takira da RAMADAN ya kalli Wasu maxaje biyu yayi musu nuni da 'dakin
Nan suka shiga cikin gaggawa suka binkico ku'din suka fitoh da direwa a gabansa
Saurayin yayi Murmushi Yace ba wa'yannan bane
Cikin tashin hankali Dadyn shahuda yanuna wani 'daki Yace Suna can
Saurayin Yace kaqara yin kuskuran nan Wlhi saina 'dauke ka

Cikin sauri mutane Biyun nan sukayi 'dakin da yayi nuni
Aiko saigasu da kinki memiyar jaka
Saurayin Yace dakyau Alhaji. Katara da yawa ka qara Tarawa sufi haka xai qara turomu muqara amshewa mun barka lpy
Har sun kai qofa.....
Shahuda Tace Allah ya isa tsakanina dakai RAMADAN
Duk samarin suka juyo da sauri
Saurayin ya dawo kusa da ita Yace mai maita abinda kikace.....
Xatayi magana Dadyn nata Yace ina neman mata afuwa
Saurayin ya 'daga mishi hannu Yace ke agidan uban wah ma kika san sunana
Shahuda tayi shuru.....
Yako daka mata tsawa.
Cikin rikicewa Tace a supermarket 'din jifatu na garin Kano mana. Har kayimin 6ari kaban hakuri nabaka number na kaban taka.
Ko 'daxo ma ai munyi waya kacemin kana cikin garin nan xakaxo gareni gobe Ashe kaxo yashe mahaifina ne.

Ya durqusa ya kama fuskarta yakai bakinsa cikin nata yabata wani make✔ kiss me tsayawa arai
Yace shegiya Kinga 'dan saurayi ko.
Nafi qarfinki Wlhi
Haka kawai kin shirya magana dan kinaso nayi kissing 'dinki ko

Ta girgixa kai cikin matuqar 6acin ran abunda yayi mata
Yace sunana RAMADAN kamar yanda kika fa'da Amma ni ban ha'du dake bah. Dan ban ta6a xuwa wani gari waishi Kano ba
Dan haka ki kula idan muka sake ha'duwa kika nuna kin sanni Wlhi saina bundige kanki
Yana fa'din haka suka bar falan. Iyayanta suka fashe da kuka danjin tashin motar SAMAREEN......


Tofah😳.


Fa'di shahuda take Wlhi na sanshi Dady Wlhi na sanshi
Ya daka mata tsawa da cewa in baki rufemin baki ba saina dan daqaki Wlhi
Tayi shuru
Shima shurun yayi ya tashi yana safah da Marwa......
Can Yace nasan Wanda ya turoshi hmmm xamu ha'du dan ba abin da xai hanani ramawa
Momynta Tace wai har yaushe zaku dena irin wannan abinne
Cikin fusata yace ban sani bah.
Kina kallan uban dukiyar da suka tafi da ita Amma kina San cewa in bari
Tace hmm Allah ya baka hakuri ya kuma ganar daku Yace Amiien
Shahuda tabisu da kallo tanasan fahimtar wani.........



Yusra CE ta shigo 'dakin da RAMADAN yake tana tafiya ahankali ahankali har taxo gareshi
Dake ya juya mata baya Sam baisan da shigowarta ba
Sanda yaji qashin turare ya doki hancinsa yayi Murmushi dan yasan Yusran CE
Yace Wlcm my qanwa
Tayi dariya Tace naso na baka tsoro Yace ahaa
Me ya kawoki da wannan lokacin 10:37pm
Tace gani nayi Ya Amar yana can ga budurwarshi kai kuma ya barka kanata aikin tunani. Shine Nace bara naxo na tayaka hira
Yayi Murmushi Yace hmm qanwata kenan
Ai baije ko ina ba yana toilet
Yama xa'ayi yabarni ni 'daya haka...
Tayi saurin rufe bakinta tana dariya Tace Allah naxata ya tafi garetane Kasan fah ba qaramin Santa yake ba
Banyi tunanin xai iya in xuwa gareta yau ba.
Kan RAMADAN yayi magana Amar ya fitoh daga toilet Yace toh munafuka brother yafimin ita....
Xan iya hakurin ganin har tsawan lokacin daxai tafi
Tace La......
Ya katseta da fa'din. Jeki pls kafin im mangareki
Yusra sanin halin yayan nata yatasa kallan RAMADAN Tace sai da safe
Da murmushi Yace mutashi lpy my qanwa
Nanfa ta fucce

Amar ya kalli RAMADAN Yace brother naga kamar kanada damuwa
Yace kabari kawai. Ina neman wata mafutace tun 'daxo
Yace koxan iya sanin matsalar
Yace gidan Auntyna nakesan shiga Saidai megidan nata 'dan group ne
Tunda akayi Auran ya rabata da wayanta bayasan kowa yaje gareta dan yasan tasan sirrinsa meyake yi
Ina fatan kagane yaran nawa ka fahimceni
Amar yayi Murmushi Yace hmm na fahimceka man. Ina garin nan ban fahimci wannan yaranba ai banyi ba
tashiga hannun 'dan iska
Dan agarin nan kam irinsu Su kukafi Yawa
Ko ina kashiga Wlhi sune.
Sunfi masu gaskiyan yawa

RAMADAN Yace mafuta.....
Amar ya tashi Yace 'daya CE
Shine kafara siye me gadin gidan da maqudan ku'da'de
RAMADAN yatashi Yace eh nima nayi tunanin hakan
Shiyasa dana tashi xuwa ban dawo da ku'di ka'dan ba
Amar Yace idan basuyi ba akwaisu guna
RAMADAN yayi Murmushi Yace xama suyi........


😰😰😰
Washe gari?
SAILUBAH tana kwance afalanta sai saqa da warwara take tasan tunda RAMADAN Yace mata xaixo toko insha Allah xata gansa ko dako xata qara kwana 'Dari tasan duk inda hankalinsa yake yana kanta
Sai dai gabanta na fa'duwa idan ta'daga kanta takalli makeken gidan nata da kuma masu tsaran nasa.
sai taji gabanta ya fa'di. Takuma shiga tunanin ta'ina xai shigo har tafi da ita batare da an'ankare dasu ba.

Tun shekaran jiya rabanta da wanka. Dan afurgice take da Komai.
Tayi nadamar burinta nasan Auran Alhazawan garin Abujah. Masu ku'di meyawan gaske

Ashe kallansu kawai takeyi dan yanke kan mutane suke susha jini. Ku'din bana Allah da Annabi bane
Duk saitaji tatsani kanta da duk wani 'dan garin Abujah
(SAILUBAH kenan ba dukka bane aka ha'du aka xama)

Da qar dai yanxu Tatashi tayi wanka tagyara kanta
Jirine yake ibanta dan tamanta rabanta da abinci
Duk Komai na gidan tsanarsu ta dirshi aranta
Da kanta tashiga kitchen tayi farfesun kifi ha'de da indomie
Tabaje taci taqoshi kana tadinga kiran sunan Allah da salati ga manxansa manxanmu.....


Da qarfe biyu RAMADAN yanufi gidan Auntyn tashi batare da 'dan rakiya bah

Cikin sa'a yaga megadin gidan ya fitoh yana Alwala akofar gidan
Cikin girmamawa RAMADAN ya gaisheshi dayin yunqurin shiga gidan...
Amma sai megadin ya katseshi da fa'din samaree wa kake nema
RAMADAN ya dawo gareshi Yace gun YAYATA naxo
Yace me sunanta Yace SAILUBAH
Shuru me gadin yayi da tsaida Alwalar tasa can Yace kayi hakuri samaree banan bane
Cikin damuwa RAMADAN ya kalli gidan xuciyarshi tana gaya mishi Wlhi gidan ne kuma Auntyn shi na ciki
Yace dan Allah BABAH kamin rai inganta....
Da sauri me gadin ya katseshi da fa'din baxan maka qaryaba samaree kaje gidan gaba qila shine
RAMADAN ya rausayar da kai yanemi guri kusa dame gadin ya xauna Yace xan baka tsabar ku'di daga naira 'daya har million indai xakamin hanyar daxan ganta
Megadin ya waro ido Yace million 😳
RAMADAN ya gya'da mishi kai
Cikin sanyin yanayi Yace axahirin Gaskiya samaree nan ne gidan. Saidai baxan iya temakwanka ba. Gashi naji kwa'dayin ku'din daka ambata baxan 6oye maka ba
RAMADAN Yace me yasa baxaka iya temako na ba
Megadin ya numfasa Yace xan gaya maka ne dan naji qaunarka araina
RAMADAN ya gyara xama Yace ina jinka baba

Megadin Yace megidan nan Alhaji Aminu ya garga'di duk Wanda yake cikin wannan gidan akan duk wanda yaxo akan dangin Matarsa ne SAILUBAH kar'a barshi ya shiga dan tagano koshi Waye
Duk wanda ko yayi gangancin barin wani nata yashigar masa gida toko Wlhi saiya kashe shi
In yana da iyali takansu xai fara
Kagako samaree ni inada mata da yara aqauye inajin da'din aiki dashi dan baya tauyemin hakkina. Kaga ya dace in barka kashiga
RAMADAN ya girgixa kai
Yace Gaskiya bai dace kabarni ba
Amma inaso kamin temako 'daya shine ga wannan.....
Ya miqa mishi wata takadda yaci gaba da fa'din
kasan yanda xakayi ka bata dan Allah
Cikin tsoro megadin Yace baxan kar6aba samaree dan duk abinda xai jawomin matsala da me gidana bana san kusantarshi
RAMADAN ya karkace ya xaro mishi bandin 'din 'yan dubu dubu guda 'daya ya dire mishi kan cinyarsa Yace kamin rai babah itace farin ciki na

Cikin sauri me gadin ya saka ku'din a ajjihu da kar6ar takaddar ya saka ta a ajjihun itama Yace jirani yanxu xan kai mata in dawo....
Bai jira cewar RAMADAN ba yashige cikin gidan da turo qofar da qarfi

RAMADAN yayi Murmushi abayyane Yace shegu masu gadi....
Wata motace tayi parking a gaban RAMADAN
Wani saurayi ya fito yana Sosa qeya Cikin girmamawa Yace Allah yajah da xamaninka oga👏🏻
Me kakeyi anan
Abin yaba RAMADAN mamaki dan baisan saurayin bah
Cikin tuhuma Yace kai Waye a ina kasanni
Saurayin ya kallesa da sauri Yace nine isma'il fah😳
Cikin raini RAMADAN Yace da xaka shiga motarka kaqara gaba da kayima kanka gata.

Ba musu saurayin yashige motar tasa yanata kallan RAMADAN harya tada motar ya tafi

Acikin gidan ko
Megadi yayi nasarar yin shashin SAILUBAH batare da wani ya gansa ba
Yayi mamakin hakan dan yasan mutum sunfi goma wa'yanda suke tsaranta

Ahankali ya bu'de kofar falan yashiga
ananko ya tarar da ita tayi cikin tagumi tabishi da kallo
Yayi saurin durqusawa Yace Allah ya temakeki wani ne ya bani wannan nabaki yana....
Kan ya qarasa SAILUBAH ta kar6i takaddan. Cikin sauri tabu'de kuwa

_Ameenci ya tabbata agareki ya Auntyna. Da fatan kinci abinci dan shine abinda yafi damuna_

_Nasan bai ta6amin lafiyarki bah_
_Dan haka kicire damuwa dan har'abada bawanda xai ta6amin lafiyarki_
_ina tabbatar miki xan fitoh dake daga wannan qaxamin gidan_
_Ki sake kiyi warwalarki dan banaso nayi toxali dake arame cikin damuwa. *Den I Luv u my Aunty*_

Cikin murna SAILUBAH Tace a'ina xan samu bairo megadi
Yace kifa'di Komai da baki dan xuciyata tafara bugawa kar aganoni
SAILUBAH tayi Murmushi Tace toh kace mai inyana Son ya ganni cikin walwala batare da na rame ba. toya gaggauta yin duk yanda xaiyi ya fuddani
Kuma ya dinga turomin kai.
Sannan kace ina son shi ya kulamin da kansa. kuma ya daure ya dinga cin abinci bana San nima nayi toxali dashi arame.
Megadin Yace toh. Ya fitta
SAILUBAH tabishi da kallan jin da'di


Yanda yabar RAMADAN haka yasame shi. Ya gayamai duk abinda SAILUBAH Tace mai

Murmushi kawai RAMADAN yayi Yace toh sai gobe babah

Megadin Yace toh Amma in xakaxo ka qaramin farashi
RAMADAN yayi Murmushi Yace karka damu fatana in sameka daidai wannan lokacin
Yace kan lokacin ma yayi xan xauna jiranka
RAMADAN dai ya shige mota ya tadata yana murmushi....
Megadin ya koma gidan da farin ciki


Daga nan RAMADAN direct gidansu shahuda ya wucce
Sanda ya shiga gidan cikin harabar gidan ya kirata awaya

Lokacin ko tana kwance tana tunanin abin da yafaru jiya
Sai taji wayanta na ringing
Gabanta yafa'di ganin RAMADAN ne
Ta'dauka a tsorace
Cikin san wasa RAMADAN Yace toh shahuda Allah ya kawoni ina cikin gidanku yanxu
Ki sani in kika wucce minti biyu xan 6ace 6at in koma gidanmu
Cikin mamaki shahuda ta kalli wayan nata taqara karawa akunne Tace hmm kana nufin kaine wanda naji shigowar shi yanxu Yace eh

Da sauri tayi cilli da wayan tanufi 'dakin Dadynta tana kwala mishi kira
Fa'di Tace Dady gasu nan sun dawo suna harabar gidan nan fitoh da bindiganka
Cikin tashin hankali Dadyn nata ya waro ido shida momynta Yace da gaske tace Wlhi
Cikin burkicewa ko bindigar bai 'dauka bah. tunaninshi ya 'dauka suka nufu harabar gidan ita dashi da momynta

Lokacin RAMADAN ya fitto daga motar yana jingine ajikinta.....
Sai ganinsu yayi a burkice
Dad 'din nata ya 'daga hannu wai shi xaiyi harbi sai yaga ba bundigar
Shahuda tafashe da kuka tace Ashe baka 'dauko ba Dady
Yace na burkice da yawa ne
Sannan ya kalli RAMADAN Yace kadawo ka kashemu ne
Cikin mamaki RAMADAN Yace ban gane bah
Nan Dadyn nata ya qare mishi kallo yaga ba wani makami ajikinsa
Cikin sauri ya kwallama masu tsaransa kira....
Nanko sukayo kanshi da gaggawa
Ya nuna musu RAMADAN Yace Ku nanna mishi bindiga idan ya motsa Ku harbeshi
Aiko nan suka sassakama RAMADAN bindiga tako ta ina
Dad 'din nata yajah numfashi Yace Alhamdulillah yau xakaci ubanka kai da uban naka
Dan Wlhi in ba'a dawomin da ku'dina ba saina kashe ka
Shegen yaro da aikin manya yau qaryarka ta qare. Bara na 'daukeka video sai in kira uban naka in turama masa.



👯〰👯
*New RAMADAN*

Wani Babban gidane wanda ya amsa sunansa
A cikin gidan cikin babban falan gidan Alhaji Jibiril ne da New RAMADAN da yaran aikinsa Suna ta6a hira cikin farin ciki
New RAMADAN ya kalli Alhaji Jibiril Yace Dad yarinyarsa shahuda cewa tayi ta sanni wai agarin Kano harda ambatan sunana........
Agigice Dad 'din ya kallesa Cikin tsoro Yace tace tasanka kuma ta ambaci sunanka
Shuru New RAMADAN yayi
Can Yace eh
Amma me yasa hankalinka yatashi haka
Cikin San gyara kansa Dad 'din yayi yunkurin yin magana Saidai wayanshi ta katse shi dan kira daya shigo
[9:50PM, 01/12/2016] Rahamat Nalele 👯: Ya kafe wayan da ido dan ganin Dadyn shahuda ne
Sai yaqi 'dauka

Junior RAMADAN ya danna wajan 'dauka ya qara volume dan yaga kamar Dad 'din nasa yana jin qiwar 'dauka ne
Aiko Dadyn shahuda ya fashe da dariya Yace Alhaji Jibiril kenan
Kaga kamun Allah ko
Saiya dawo min da 'danka ba makami ba komai
Yanxu haka gashi a hannuna.
Alhaji Jibiril Yace wane yaran nawa
Yace kanada wani 'dane banda RAMADAN
Shinake nufi
Yanxu xan turo maka da video nasa narantse da Allah in baka dawomin da ku'dina yanxu ba Wlhi saina kasheshi kuma nasa akawo maka gawarsa...
Yana fa'din haka ya kashe wayan

Iya gigicewa Alhaji Jibiril ya gigice ya kalli 'dan nasa RAMADAN ya maida kallansa ga wayan yana addu'a axuciyarsa Allah yasa kar asirinsa ya tonu yau.....
Kanya tattaro tunaninsa videon ya shigo
Aiko da sauri junior RAMADAN ya 'dauki wayan ya duba videon
Abin mamaki sai yaga saurayi kamarsa ba abunda ya rabashi da wannan saurayin an sassaka mishi bindiga yana yin motsi Komai xai iya faruwa
Cikin tsoro da mamaki yaba Dad 'din nasa waya Yace Waye shi Dad

Alhaji Jibiril ya murgina kai ya kalli videon Yace bansan Waye shiba

Qare ma mahaifin nashi kallo yayi junior RAMADAN na'dan wani lokaci yana naxarinsa
Kana ya tashi yana Murmushi yaxuba drink a cup Yace ko Dad
Amma da mamaki
Dan Kallo 'dayan nan dana masa na gane 'dan uwa nane fa'damin ya abin yake dan naji qaunarshi Sosai araina
Cikin wani hali Alhaji Jibiril Yace ban San ko Waye shiba kashare kawai......

Yayi saurin katseshi da cewa baxan iya sharewa ba
Ina San inji Waye shi
Kafa'damin Dad. Idan har nayi bincike da kaina nagano Gaskiya Komai baxaiyi da'di ba
Cikin tsoron shi dan yafi kowa sanin 'dan nasa
Alhaji Jibiril Yace eh 'dan uwanka ne
Ku 'yan biyu ne

Kaine kuma ka haifemu. Jinior RAMADAN ya fa'da da San abashi amsa da sauri

Yace bani bane mahaifinku.....

Junior RAMADAN ya saki cup 'din hannunsa da wani murmushi wanda yaqara Alhaji Jibiril tsoro
Yace hmm ai dama nasan qarshen furucinka gareni kenan kace ni ba 'danka bane.
Alhaji Jibiril ya kallesa da sauri

Junior RAMADAN ya juya kai Yace eh
Ba Uba na gari da xaisa 'dansa akan haiyar daka 'dorani akai
Wane ubane nagari ne xaisa 'dan yin fashi da makami.
Ko kana tunanin banajin ciwan abinda nakeyi
To ina ji
Alhaji Jibiril Yace ka saurareni

Yace bana buqatar jinta bakinka. Dan ban hango gaskiya a tattare dakai bah.
Ya fa'da dasan barin falan xuwa part 'dinsa

Alhaji Jibiril Yace RAMADAN.....
Cikin wani yanayi junior RAMADAN yajuyo Yace karka qara kirana haka daga yau.....
'dan iskan mutum kawai
Cikin fusata Alhaji Jibiril ya tashi yana nunasa da yatsa Yace ni wan Mahaifinka ne

Da 6acin rai junior RAMADAN ya kallesa Yace narantse da Allah kabari mahaifin yarinyar can ya ta6a min lafiyar 'dan Uwa Wlhi ba abinda xai hanani 'daukar mummunar mataki akanka.....

Cikin tsoranaa Alhaji Jibiril ya xauna jagwab kan kujera
Yayinda junior RAMADAN ya kalli abokanayan aikin nasa yace ina san sanin meya kawoshi garin Abujah miye tushanshi ayau nakesan jin Komai...
Cikin girmamawa sukace toh
Kana yayi tafiyarsa part 'dinsa cikin halin ko in kula

Goge xufah Alhaji Jibiril yahau yi Cikin tashin hankali shima ya kallesu Yace dole Ku kashe min shi
Atare sukace wah😳
Yace RAMADAN.....
Sukace wannan na nan gidan ko nacan hannun Babban yarinyar can
Yace nanan gidan.

Suka kalli junansu a hargitse.....
Kuma daidai nan junior RAMADAN ya dawo falan
Duk sai suka bishi da kallo
Yayi Murmushi da 'daukar wayarsa Yace lokaci na tafiya kasan fah yanda xakayi ka ku6utarmin da 'dan uwana
Sai ya qara barin falan
Direct part 'din shi Alhaji Jibiril 'din yayi ya 'dauki Wasu diaries biyu da duk lokacin dayaxo 'daukar su dan karantawa Dadyn nashi yake hanashi gashi xuciyarshi nasan yaji me suka 'kunsa
Cikin sauri yayi shashinsa yana murmushin mugunta





Senior RAMADAN ko mamaki ne fal Cikin ransa.
Me yayima shahuda da Dadynta da xaisa Su qaqaba mishi bindigogi haka

Ya kalli shahuda Cikin wani hali Yace wai me nayima Dad 'dinki ne daxai qaqabamin bindigogi haka
Ta qura mishi ido takasa bashi amsa dan rasama me xatace mishi tayi....
Bata idda tunaninta ba taji Dadyn nata yana bashi amsa
Yace Lalle kacika 'dan iska xahiri
Ko Mantawa kayi in tuna maka
Kuxo jiya kumin fashi yanxu kafara tambayar me kayi
RAMADAN Yace fashi😳.....
Wlhi bani bane. Yafa'da cike da tsoro da kallan shahuda
Tayaya Xanyi fashi
Me nake nema haka dana rasa dahar xanyi fashi.....
Cikin fusata shahuda Tace Amma kai dai kacika 'dan rainin hankali....
Dadynta ya amshe da cewa bar 'dan iska yaudai qaryarka taqare kai da uban naka
Wlhi kaji narantse indan har uban naka bai dawomin da ku'dina ba na rantse saina kasheka natura mishi da gawarka kuma........
Bai qarasa furucinsa ba
Saiga wasu samari biyu sun shigo gidan da manya manyan jakunkuna sun dire agabansa da fa'din wai xaka iya qirgawa ko daidai suke
Dadyn shahuda ya washare baki da murmushin jin da'di Ganin ku'dinsa sun dawo
Yace shege Jibiril yaji anta6o farin cikinsa
Ya fa'da yana mai bu'de jakunkunan. Aiko saiga ku'dinsa nan muraran
Ayanda yalura ko 'daya baiyi ciwan kai ba.

Ya kalli wa'yanda suka takura RAMADAN da bindigogi Yace kusake shi ya tafi.
Nan ko suka bar gun.
RAMADAN yajah numfashi yana kallan ikwan Allah da mamakin abin....
Cikin sanyin yanayi ya shige motarsa shahuda tabishi da kallan harara
Shidai ya fitta yana hamdala ga Allah daya ku6urar dashi
Da wannan tunanin ya iso gidan kawun nasa

Wanka yayi yayo alwala yayi sallah dake lokacin La'asar ta gabatoh
Saiya kwanta yana tuna lamarin
Har bacci ya 'dauke shi bai gane me lamarin yake nufi ba.



Junior RAMADAN ko bajewa yayi agadansa da niyar karantawa
Sai kuma ya tsaya tunanin 'dan uwan nasa. dan tunda yagansa yaji qaunarsa aransa Sosai
Yaji yanasan ya qara ganinsa
Yasan tunda yacema Dad 'din nasa yasan yanda xaiyi tabbas xaisan yanda xaiyin ya ku6utar mai da 'dan uwan nasa.
Yin tunanin nan dayayi shine yabashi qarfin gwiwar fara karanta diaries 'din......





*Asaninsu*

Malam habibu wani shahararran malamine acikin garin kano awata unguwa da ake kira bacirawa
Yana da mata biyu Hauwa da Asabe.
Hauwa itace wacce ta Haifa mishi yara uku wato Jibiril da Naziru da Auwal
Sai Asabe ta Haifa mishi Jabiru
Yaransa sun kama hu'du kenan
Jibiril shine Babba sai Naziru sai Auwal sai autansu Jabiru

Bayan sun girma sun mallaki hankalin kansu Allah yayima iyayan nasu rasuwa
Farko Asabe mahaifitar Jabiru CE tafara rasuwa sai Hauwa tabi bayanta sai megidan nasu Malam Habibu

Haka suka taso gurin kawunsu wato qanin mahaifinsu Wanda yayi musu rikwan tsakani da Allah yabasu tarbiya da ilimi

Duk cikinsu jabiru yafisu ku'di nesa ba kusa ba
Ga shi yanada NASIBI dan duk abinda ya ta6a daniyar kasuwanci sai kaga Allah yasamai albarka aciki
Mahaifinsu Malam Habibu ya mutu yabar musu dukiya me tarin yawa
Dan haka aka raba musu gado dan kowa yaje ya juya kayansa dan sun mallaki hankalin kansu

Jabiru yana ma Yayun nasa ladabi da biyayya Sosai
Kowa ya shaida hakan
Sam jabiru bayasan 6acin ran 'yan uwansa Sam

Lamarin yafarune lokacin daya farayin ku'di duk saiya doke yayun nasa aku'di

Abinda yasa Jibiril kenan yafara mishi hassada da Baqin ciki
Tun baya ganewa har yaxo yafara ganewa

Yaje ga sauran yayun nasa yana nuna musu baidace yaya Jibiril yadinga nuna masa Hakka ba

Ha'kuri suka bashi dan dukkansu tsoran shi Jibiril 'din suke

Ahaka Naziru yayi Aure yatare da amaryarsa nan cikin Fage

Please Login or Register in order to submit comment