Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan kullun SAILUBA da HAMEEDAH suna tare da ita har ranar suna. Inda yarinya taci sunan momy za`a kirata da RAMAT wannan kuma inkiyar yayar KHAMIS ne.
Ba qaramin shagali akayi ba. kunsan ko dole yarinya taga gata wajan kowa daga iyayan XEE har na KHAMIS. ga `yan uwa da abokan arziqi. Kai abundai sai san barka. [Nagaida Hajjiyan ALLAH dan Junior ya tabbatar da ganinki kina sakama baby albarka ki huta me sonah]

Duk abinda aka sakama lokaci tabbas sai yaxo. Kamar yanda masu magana suke cewa rana bata qarya saidai uwar `diya taji kunya. [wannan karan maganar ZULFAU MUSTAPHA NE ki huta sister]
Ayau aka `daura AURAN JUNIOR SADEEQ DA FATIMA SAILUBAH auran daya tara mutane masu yawan gaske


Amarya SAILUBAH tasha gyara sai lamarin yaxo da ru`darwa dan ana `daura auran da SAILUBA AKA `daura DA MARYAM abokiyar aikin junior. YA ZAMANA JUNIOR YAZAMA MIJIN MACE BIYU A RANA `DAYA KUMA LOKACI `DAYA.
Iya gigicewa SAILUBA da junior sun gigice. Dan tsakani da allah junior basan da ha`din aure tsakaninsa da maryam ba. Tunani mah. Yashiga yi akan ya tuno wacece maryam.
FAWAS yace junior ya haka…. KHAMIS yace tambayar da nima xanyi masa yanxu kenan. Arikice yace wlhi bansan ya abin yake ba.
KHAMIS yayi murmushi yace akwai matsala….. shuru junior yayi shuru can yace hmmm bara dady yagama da baqi inji ta bakinsa dan nasan yafi kowa sanin komai. FAWAS YACE ya kamata kam
SAILUBA ko bayan fa`duwar da gabanta yayi game da xamowa matar junior da tayi. cikinta hautsinewa yayi jin ba ita ka`dai bace dashi
Hawaye ne yaxubo mata nan take kishi da baqin ciki suka far mata. Cikin takaici ta kalli HAMEEDA da duk yanayinta ya canza ita da XEE Tace junior matsalane ga rayuwata banta6a jin wani yanayi akansa ba kamar yau…..rungumarta XEE tayi tace kiyi hakuri SAILUBA komai zaizo miki da sauqi insha allah. Cikin wani hali SAILUBA tazame daga jikin XEE tace inaji ajikina wani abu yana shirin faruwa dani.
Bakomai Auntyna. inaso ki kitsa kyakkyawan zato a zuciyarki saikiga Allah ya dubeki da wannan niyar. HAMEEDAH tafa`di hakan cikin tausayawa


Jinior ya samu dady yace dad ya akayi haka. Dady yayi murmushi irin nasu na manya. Yace zauna kaji komai my son……..

Wata rana ina zaune a office wani abokina yazo shi da wani abokinsa. Bayan mun gaisa dayin barkwanci irin namu na manya yace min yaxo neman wata alfarma ce aguna. Nayi mamakin hakan sosai amma na share ina me tattara hankalina gareshi. Yace `yarsa ce take matuqar sanka gashi ita `daya gareshi bayasan matsala tasameta sanadin hakan. Ya gayamin ita`din abokiyar aikinka ce.
Nayi binkice sosai akan ita yarinyar nagano bata da wani aibi sannan halinta mekyau ne zasu shirya da `yata SAILUBAH. Wannan shine dalilin da yasa naji na gamsu da ita yarinyar musamman dana sami labarin kana kulata fiye da kowa agun aikin naka. Hakan yasa na yarje ma mahaifinta bisa maganar daya xomin da ita.
Na shirya komai batare da saninka bah. Xa`a kawo maka ita anjima kamar yanda xa`a kai maka SAILUBAH.
Kanutsu da kyau my son. Dan na yaba da hankalinka ne shiyasa banji komai game da hakan ba. Pls my son karka bani kunya dan allah…….
Har abada dad baxan ta6a baka kunya ba amma kasa momy ta lallashi `yarka dan allah. Murmushi dad yayi yace tana da sanyi SAILUBA nida kaina xan lallasheta my son. Murmushi shima junior yayi
Bayan ya gama ba su FAWAS labarin yanda lamarin yake murmushi KHAMIS Yayi yace gaskiya banji da`din hakan ba. Sai dai mutun baya wucce qaddararsa…

Dare ko nayi dad yaritsa SAILUBAH Da nasiha. Haka kakah da innah momy duk sun mata fatan alkairi. Haka tana kuka aka `dauke sai gidanta. Ba`afi minti biyar da kaita ba taji ankawo maryam aiko me zatayi imba cigaba da kukanta ba. XEE DA HAMEEDAH sunyi mata lallashin duniya taqi sauraransu da kuka XEE tabar gidan hakama Khairat. HAMEEDAH ce dai me `dan qarfin hali. Innah ce dai taqar6i alqawarin da iyayen maryam suke bah SAILUBA akan `yar tasu dan SAILUBA KO kallansu batayi bah. Maryam ko tasa mata ido tana baqin cikin yanda SAILUBA tazama itace kishiya agareta. Tofah masu karatu kunji fah.
Bayan watsewar kowa ya kasance daga SAILUBA sai maryam ne kawai awannan makeken gida SAILUBAH Tatashi tayo wanka tasaka kayan baccinta tafeshe jikinta da turare tabi lafiyar gadanta bayan ta garqame `kofarta
Hakancema ta kasance da maryam itama. Sai ita ba kulle qofarta bah hasalima bata kwanta ba miqewa tayi ga doguwar kujerarta acewar zuciyarta tana jiran angwanta taga agunta zai kwana ko a gun SAILUBAH…..

To mun kawoka gida lafiya sai kashiga katuro mana matanmu dan cikin ni da FAWAS Ba wanda zai iya ha`da ido da Aunty LUUVAH. Cewar KHAMIS. MURMUSHI junior yayi yace ok… nagode sosai. saidai matanku sun da`de da komawa gida sakamakwan kukan da babyna keyi. Dariya FAWAS Yayi yace kaji `dan rainin hankali ya akayi kasan hakan bayan bamuga kayi waya da `daya daga cikinsu ba. Cikin wani shegen murmushi junior yace ku kirasu awaya mana kuji. Ba musu FAWAS yakira HAMEEDAH yace my luv kina inane… HAMEEDAH Wacce take kwance a gadanta ita da `danta tana tunanin SAILUBAH tajah numfashi tace ina gida my luv kayi hakuri kaje `daukata ko. Cikin mamaki yace eh. Tace toh kayi sauri ka dawo ina buqatar jin `diminka da lallashinka dan hankalina ba a kwance yake ba. Cikin wani hali yace ok me kikesan in tawo miki da shi. Tace komai mah. Yace angama YAYATA MY MEEDAT. Murmushi tayi ya kashe wayan yana kallan KHAMIS Wanda yake magana shima da XEE inda take tabbatar mishi da cewa itama tana gida.
Da mamaki duk suke kallan junior. Shiko yayi murmushi yace yanxu kun tabbatar. FAWAS yace YAH. KHAMIS yace toh abi duk wacce take ahannu yau ahankali danna lura atashe kake. FAWAS Yace aikuwa dan allah abi takan qaramar kar.a takura mana AUNTYNMU YAU.
Murmushi dai junior ya qarayi yace angama abokanayan arziqi ina muku fatan kaiwa gida lpy. Murmushi suma sukayi KHAMIS yaja motar sukabar qofar gidan
Ayanda ni RAHMAT NA LURA GANI NAYI KAMAR JUNIOR 6ACEWA YAYI. HMMMMM komadai miye bara in murza idona dan ganin da gaske 6acewa yayi koko na fara gajiya dayi muku typing ne….. Kodai Sis hajjaju zaki duba min

Sam baibi takan kowa ba cikinsu. Dan part `dinsa yayi, ya sheqo wanka yana me jin sanyi aransa. Yau ya samu SAILUBA Cikin shirinsa shin dama agaske ne dayafi kowa jin da`di.
Sanda yasaka kayan baccinsa ya saka turaransa sannan ya nufi shashin maryam dan yimata sallamah.
Yana turo qofar yayi ido biyu da ita. nan take ya sakar mata murmushi da qarasa shiga cikin falan yana me qare mishi kallo da rayawa aransa lalle dady ya kashe ku`di ba `dan ka`dan ba.
Xama yayi kusa da ita yana shafa fuskarta suka sake ha`da ido yace amarya kinsha qamshi. Tace kai kuma ango kasha takaici ko.
Murmushi yayi da cewa ammafah kinyi min wayo. Tayi wani farr da ido tace name fah. Yace haka kawai saiki maidani mijin mace biyu cikin bazata. Dariya tayi tace hmm dadyna ne baya san 6acin raina. Dan nika`dai ce gareshi kaga bazaiso abinda zaisa na rasa rayuwata ba. Wato doctor sadeeq ina sanka so mai tsanani dan Allah nima kasoni ko ka`danne. Dan nasan baxaka min san da kakema Aunty sailuba ba,
Murmushi ya qarayi… aina soki tunda kika Aureni. Kuma ina tabbatar miki saidai ke ki gujeni amma nibazan ta6a guje miki ba. Da sauri tace da gaske. Yace kwarai mah kuwa.
Murmushi tayi. Amma tunda nice qaramah bazaka barni ni ka`dai bako. Cikin murmushi sosai yace haka kuma kinsan baxan bar Auntynmu itama ta kwana ita ka`dai bako. Cikin basarwa dajin kunya tace toh ya kenan.
Cikin sauri yace abu me sauqi. Tace toh fa`da naji. Yace hakuri xakiyi. nayi kwana ukun nan agunta. tunda kinga ita baxan kai bakwai bah. Murmushin yaqe tayi ha`de da `dan 6ata fuska tace kayi min dai kawai wayo. Yace toh naji saki fuskarki nayi miki alqawari xanxo miki cikin mafarkinki har na amshe haqqinah. Tace wane hakki. Murmushi yayi da tashi yace wanda kika `dau shekara da shekaru kina tanadar min wanda har ummar yaso amshemin cikin satincan daya wucce……..
Arikice ta kallesa. Shiko ya kasha mata ido `daya yana cigaba da murmushinsa tare da qoqarin barin falan…… cikin sauri tace `dan jinni ka`dan man…… bata qarasa furucinta bah. Ya katseta da juyowa yana me cewa wlhi na tabbatar miki xanxo miki cikin mafarkinki. Kuma ga kaza nan da milk kici zasu temaka miki
Shuru tayi tana kallansa. Shiko ya fice ya girgixa kai yana tunanin sankai irin nata dukda ya gano kishine yake `dawainiya da ita.
Mur`dawar farko yaji qofar SAILUBAH a kulle. Murmushi yayi yace nayi miki lefi Auntyn brothe kiyafemin wlhi Allah bansan da maganar aurena da maryam ba.
Tsaki SAILUBAH tajah ha`de da juya kallanta ga kallan bango dan dama ta kasa baccin tarasa me yake mata da`di aduniyar nan yau.
Duk wata amarya tana farin ciki da kasan cewar wannan ranah amma ita takasa jin farin cikin ko ka`dan.
Jini ka`dan……. Arikice SAILUBAH Tajuyo. Aiko sai ganin junior tayi a gabanta yana mata murmushi. Bakinta na rawa tace ta ina kashigo. yace ta qofah mana. Tace aina kulle. Yace da gaske. Tace kwarai ma kuwa. Yace inko hakane burinki baxai ta6a cika ba. Tace kamar yaya. Yace daga yau kika sake kullemin qofah sha Allahu saikin gamu da wani bakwan lamari ha`de da ganin 6acin raina.. Cikin maseefah tace 6acin ranka 6acin ran banxa 6acin ran hofi. Duk 6acin ran da zaka shiga kata6a yin kuka ne……..
Duk da yake da 6acin rai take maganar kallo `daya xaka mata ka tabbatar da cewa ita `din shagwa6a66iyace. Hakan da yagani kamar yanda dama yasan abarsa shiyasa kawai ya `dane gadan ya rungume abarsa yana sauke numfashi ahankali ahankali.
Bayanda ta iya face ta lumshe idanta dan wani da`dine ya xiyarci xuciyarta tamkar an watsa mata rowan sanyi.. ciyafemin babyna wlhi Allah bansan da aure tsakanina da maryam bah.
Bugar qirjinsa tayi tace nayarda da abinda kace ba. Sai dai kasani wlhi bazan ta6a baka zuciyata ba harsai katabbatar min da zaka iya riqeni amana bazaka ta6a ban wahala ba. Xaka soni xaka qaunace ni a duk inda kake. Xakaban farin ciki har qarshen rayuwata, zaka mantar dani maraici. Xaka xamar dani `yar lelanka wacce zakama komai. kuma zaka dinga ba duk wanda ya ra6eni girmansa da matsayinsa. Sannan Ni kuma in har kayimin hakan nayi maka alqawarin baka farin cika gabaki `daya har qarshen rayuwata.
Murmushi yayi yace na`dau alqawari kuma yanxu xan fara tabbatar miki.
Murmushi tayi tace toh ina jinka ina kuma ganinka..
Bakin ki zaki ban kawai ayanxu….. kallansa tayi. Yako camke bakin yana aika mata da wani shu`umin kiss… sanda yakusa shi`dar da tunaninta yace muyi sallah in baki kaxa da madara kibani xuma ko babyna. Harararsa tayi tace sai wani sauri kake bayan bangaji dajin bakin naka bah. Pls qara ban ka`dan….. waro ido yayi yace nakuma baki allah rikicewa xakiyi. Tace daga kiss kawai. Yace eh. Da sauri ya sunkuceta sai ganinta tayi a toilet…. Cikin sauri tace yah akayi na ganmu a toilet bayan ko tashi bamuyi bah. Cikin murmushi yace nidai ba ruwana dan kinsan ba`a Magana anan. Shuru SAILUBA tayi tana tuna wata rana data cema RAMADAN `dinta haka.
Shafar fuskarta yayi yace kin tuno ranar da kika gaya mishi haka ko.
Kallansa tayi da cewa ya akayi kasani. yace kawai dai
tace kawai dai me….. Muyi alwala na gaya miki babyna….
Bayan sun idar da sallar yayi mata addu`o`I tare da bata kazar taci yabi ya kanalna`deta dada`din baki har yakaita gado ya had`ata da qirjinsa. Minti goma ta sakarmai bacci. Saboda wata nutsuwa data saukar mata lokaci `daya.
Ahankali ahankali taji yana shafata da aika mata da wasu wasanni masu bara xanar tarwatsa mata tunani….. arikice tafarka ha`de dabu`de idanta tasauke akan nasa.. aiko cikin tsunuwa yafara kissin `dinta batare da yadena mata wasannin da yake mata ba……. Nishi take sama sama cikin wani hali tafara biye mishi kamar zasu cinye junansu.
Lokacin da labarin ya canja kuka SAILUBA tasa mai da ihu….. 🙊




MARYAM KO ITA TAGA BALA`I A WANNAN DARE…….
Abinko daya faru shine bayan futar junior daga part `dinta tashi tayi tarufe qofarta sannan ta`isa ga bedroom `dinta ta haye ha`de dabu`de kaxarta tafara cin kayanta tana mamakin ya akayi doctor sadeeq yasan saurayinta ummar yaso 6ata mata rayuwa da gaskene. Amma abin mamaki anan ya kayi yasani bayan daga ita sai shi ummar `dinne suka sani. Tasamu ku6uta daga gareshine wajan ganin kamar an makeshi lokacin dayake qoqarin yaga mata riga. Sai ganinsa kawai tayi ya sume. Ganin hakan yasa ta hanka`dashi baya tagyara kanta da tafice daga gidan daya kira da gidan iyayansa. wanda yagama mata da`din baki akan mahaifiyarsace take san taganta shine dalilin da yasa tabishi ashe shi da wata manufa aransa akanta. Saida suka shiga gidan daya kira da sunan na iyayansa ne taga ba kowa. bayan tanemi taga mutan gidan ne ya fito mata da mummunan qudirinsa akanta. ALLAH dai ya temaketa
Bayan tagama cin kaxar tata takora da sanyayyiyar madara saita bama kanta minti biyar kanfin ta kwanta…. Can tayi nisa acikin baccin nata ne saita fara mafarki kamar haka……….
Junior tagani ita dashi cikin wani falo suna wasa irin na ma`aurata. Bata fatan yadena yimata wasan dan yana tafiya da imaninta. Itadai tabu`fe idanta tagansu shida ita akan gado. Da mamaki tace yana ganmu akan gado. Yace lokacin da kika rufe idanki lokacin komai ya faru. Tace kai amma da sauri kake. Murmushi yayi yace ai nawucce nan…….. shuru tamai jin yana san rabata da komai nan tafara nishi tana lumshe ido. Aiko komai yafara gudana. Dake ita budurwace tasha azaba ha`de da kuka… ba ita tasamu kanta agunsa saida aka kira sallar farko………
Amatuqar razane maryam ta farka, lokacinko yayi daidai da kiran sallar azahiri. hankalinta baqamin tashi yayi ba lokacin dataji zafi na ziyartar gabanta…… arikice tahau doba gaban nata. Ganinta kaca/kaca alamun ammaida ita cikakkiyar mace shiyasa kurma ihu tana fa`din na shiga uku ni maryam…. Me yake shirin faruwa dani…. Mafarki nayi gashi yazama gaske…. Ko nayi haukane…. Meke faruwa ne……. duk tabi ta gigice abin tausayi. Sai kallan ko ina takeyi ajikinta tana samfatu. Kuka ko batabar yinsa ba. Musamman idan ta kalli gabanta taga yanda duk ya 6ata xanin gadan da jini. Aiko saita qara rushewa da kuka…..
Haka tayita kukanta harsanda tafuskanci anshiga sallar asuba. Sannan tayi qoqarin tashi daqer tashiga toilet tagya kanta tana me ciga da kuka.
A daddafe tayi sallah kanta na sara mata…. Nan tashiga neman wayarta aiko tarasata sama ko qasa. Taje taduba qofarta taganta arufe kamar yanda tarufe abinta da key daran jiya. Ganin hakan ne yasa tadawo bedroom `din nata tayaye zanin gadan tasa agefe ta shinfi`da wani kana takwanta hawaye na xubar mata tana me tunanin kodai ba mafarki take ba. Kodai azahiri ne. in hakane ai bata manta cewa ita ka`dai ta kwanta ba. Haka kuma bata manta cewa junior yayi mata sallamah akan a`dakin Aunty SAILUBA xai kwana ba. Sannan takwille qofarta kuma yanzuma akullan taganta. Wai meyake faruwa da itane. Kodai har yanxu duk acikin mafarkin take….. girgixa kanta tayi tace wlhi yanxu azahiri nake…..
TOFA MASU KARATU WAI ME YAKE FARUWA NE… TAKU DAI RAHAMAT MUH`MD RUFA`I NALELE. QIRQIRATA CE BAIWATA CE BANYARDA WANI KO WATA YA SARRAFAMIN LABARI NA BA.
Lallashin duniya SAILUBA tashashi agun junior. Lokacin da suka samu kansu. bacci me da`dine yayi awan gaba da SAILUBAH ba ita tafarka ba saida tajita cikin ruwa tsundum sannan ta kwllah qara tare dabu`de idanta ahankali. Karab suka ha`da ido. Tayi saurin kawar da kallanta daga gareshi. Tana qarema inda suke kallo. A toilet suke…..
Haba barwar Allah tsabar jin da`din bacci ya hanaki kifarka dan ki gaisar da ubangijinki. Junior ya katseta da fa`din hakan yana murmushi. Harara ta sakar mai zatayi Magana yayi saurin taran numfashinta wajan cigaba da cewa Na tuna ashefa na wahalar da babyn tawa dole tayi baccin gajiya. … da sauri tahau kare girjinta gabanta na fa`duwa tunowa da tayi da daran nasu na jiya shi da ita. Cikin shagwa6a tace tashi ka futa. Murmushi yayi da cewa wanka zan miki. Afusace tace banaso kaje xanyi abuna. Shuru yayi mata yana qarema kyakkyawar furkarta kallo. Ganin haka yasa ta watsa miki ruwa a fuska tace katafi mana kallan ya isheni haka. Yace xan tafi amma saina cika alqawarin dana `daukar miki. Tace wane irin alqawari. Yace wanda kika nema a daranmu na jiya. Kin manta kince na `daukar miki alqawari xam mai dake `yar lelena wacce zan dingamah komai…. Shuru tayi mai yace toh wannan alqawarin bazan barshi ba. Dan haka oya saki jikinki nayimiki wankan sai kiyi na tsarki. Duk nasan xan shiga wani hali bayanda zanyi dan nasan na kuma ta6aki da safannan sumemin xakiyi raguwa kawai…… aiko jin haka yasa SAILUBA fashewa da kuka tana mai cewa wlhi kafita daga toilet l`din nan.
Kamar gaske yanuna rikicewarsa yana cewa menene kuma nayimin kuka. Tace bansani ba. Yace oho yanxu nagano dalilinki. Hmmm SAILUVAHHHH Kenan. Hmmm xuciyata da taki tarigada taxama `daya a daran jiya nasani ayanxu koyaya na ta6aki sai kinji har cikin ranki. Ayanxu ba wani abu waishi soyayya a cikin xuciyarki na brothe na kona qawa kona yara kona iyaye acikin xuciyarki banda tawa, hakane. Ahankali tadena kukan tace hakane. Junior. Nayi gamo da zazzafar qaunarka adaran jiya, nayi dana sanin baka kaina duk nasan abune wanda da wiya na `ketare hakan awannan lokacin. Nayi tunanin salan RAMADAN na dabanne ashe naka salan ne daban. Nakusa manta kaina ajiya na tabbatar ba daga kaina kafara sanin mace bah. Saboda kayi amfani da salan karuwan maza. Nagano hakanne yanxu wajan yawan karance karancan da nakeyi. Wlhi da gaske kaqara ta6a wani part na jikina ayanxu saika biyamin buqatata. Ina sanka ina sanka amma dan Allah karka qara ta6ani kabarni haka ya isa. Xan iya rayuwa a haka har qarshen rayuwata…….. dariya ya sheqe da ita sanda toilet `din ya amsa. Nan SAILUBA tahau waige waige a tsorace. Cikin nutsuwa yanemi yakai hannunsa ga qirjinta aiko cikin sauri taja da baya cikin bahun wankan hawaye na xubo mata….. tausayinta ya kamashi. Yayi murmushi tare da maida hannunsa jikinsa. Yace kinga bakyau Magana a bayan gida. Baxan dena ta6aki ba. Amma yanxu nabarki kiyi wankanki. Xanxo in `daukeki na shiryaki kiyi sallah dan haka kinutsu sosai ki gyara kanki duk wannan bashi bane na farko nasan kin iya. Yana fa`din hakan yaficce daga toilet `din. Aiko nan tasauke ajiyar zuciya. Tare da shafa inda xuciyarta take tace haba zuciyata me zaisa cikin lokaci qanqani kI shafe soyayyar RAMADAN A CIKINKI. KI TEMAKA KI DAWO MIN DA SOYAYYARSA. Shi mai sanyine xan iya `daukar komai nasa amma banda na junior dan nasa me germane……. Adafe tayi wankan nata tana shirin tashi dan `daukar tawul sai ganin tawul `din tayi yana nufuwa gareta sanda yaxo daf da ita ya tsaya ha`de da warware kansa. SAILUBAH tawaro ido waje. A tsorace takai hannu ta kar6i tawul `din wanda kamar wani ne ya miqo mata. Tana `daura tawul `din sai ganinta tayi tadawo bedroom. A razane ta kwulla qara saiko tazube su qasa sumammiya.😳








Ha ya girgixa kai ha`de da ta6e baki ya watsa mata ruwa. Ta farfa`do. Bai bari ta tsawaita tunaninta ba. Bare ta tuno me ya faru ya miqa mata doguwar riga yace lokaci na wuccewa my baby pls kiyi sallah. Aiko da sauri ta kar6a tasaka das aka hijab tayi sallah tana laximine tatuno abinda ya faru, aiko nan take ta tsaida laximin tafito falo inda taganshi yana danne danne a waya. Tace junior wai me yake faruwa ne. daga toilet naganni a bedroom me kenan h……. bata qarasaba taganta akan cinyarsa. Xata kwalla qara ya ha`de bakinsa da nata sannan Yace kin fiya Magana my baby pls kibarni haka. Komai ya canja gareki daga yau. Komai ganinsa xaki dinga yi kamar me nayar 6ata wannan wani sirrine nawa. Arikice tace kai aljanine. Shuru yayi mata ha`de da rungumeta. Xatayi Magana ya shafi le6anta nan take bakinta yarufe rub kamar ba`a ta6a tsaga mata bakin ba. Shiko yaci gaba da abinda yakeyi da hannu `daya. `dayan hannunko yana rungume da ita, Tayi tayi tayi Magana abin ya gagara aiko saita nemi tasaka ma kuka. Ya bita da wani furgitaccen kallo. Yace ba bakin da zakiyimin kuka dan haka karki batamin fuskarki da hawaye pls. Jin abinda yace mata yasa ta tashi daga jikin nasa ha`de da fusgar wayar tasa hannunta na rawa tashiga typin kamar haka. Pls bu`demin bakina wlhi baxan qara yima Magana ba. Murmushi yayi bayan ya kalli meta rubuta. Yace da bansanki bane da sai in bu`de miki. Bani wayata. Shuru tayi batare da tabashi wayan bah. Can taqa rubuta mishi…. Toh xani gun maryam dan allah bu`demin bakin. Saurin tashi yayi wannan karan ganin meta qara rubutawa. Cikin sauri yace Ya ALLAH kinga na manta da ita… yana fa`din hakan ya 6ace 6at. cikin sauri SAILUBA Ta waro dukkanin idanunta ganin axahiri junior ya 6ace….










Kamar daga sama sai ganinsa tayi ya baiyana a gefan gadanta hannunsa `dauke cup da magani….. Agigice tatashi tana nunashi da yatsa tace doctoh ya haka. Murmushi junior yayi yace ki kirani da junior yanxu ba doctor ba. Ha`diye yawo maryam tayi tace to to to junior ya haka ka bayyana gareni kamar aljani, ta6e baki yayi yace baxaki dena kukannan ba. Tace tayaya kasan ina kuka. Murmushi yayi Yace nayi murna da samunki cikakkiyar mace. Maryam tace mene. Kana nufin mafarkina ya zama gaske. Yace eh aina gaya miki xanxo miki cikin mafarkin naki ko ban gaya miki ba, da sauri ta qara ha`diye yawu tace ai mafarcikine kuma dama ana irin haka. Murmushi shima yaqa yi, Yace ga magani kisha dan ya dace nabaki tun `daxo.
Kar6a maryam tayi tace meke faruwa dani. Yace nima ban sani ba. Kisha pls raina ya fara 6aci.. aida sauri tasha ta miqa mishi cup `din. Bai kar6a ba. Sai gani kawai tayi cup `din yabar hannunta yaje ga kan wani qaramin teble dake kusa dashi. Atare suka ha`da ido ya sakar mata murmushi





yace ammafah kin ban tausayi daran jiya. Kawai dai baxan iya barinki bane shiyasa.
Shuru tamishi. Ganin tayimai shuru yasa yaci gaba da cewa toh bara naje ga Auntynki in bude mata baki. `daga mishi kai maryam tayi. Aiko kamar qif tawa da bismillah saiganinsa tayi ya 6ace. Nan take takoma gado luuuuu sumammiya.
Bayyana ya qarayi gareta ya watsa mata ruwa kafin ya qara 6acewa. Tashi maryam tayi tafito falo a bala`in tsorace tabu`de qofarta akan tana san ficcewa daga gidan tayi gidansu. ko `dankali babu akanta bare takalmi. Tana fitowa harabar gidan taga ba hanyar ficcewa. Kamar yanda aka kawosu jiya. Ba get ba alamarsa. aiko nan take ta `dura hannu aka ta kurma wani uban ihu. NIMA RAHAMAT NA TAYATA DAN NIMA BANSAN TA INA ZAN 6ULLEBA…….


Ne Man kwafkwafina Ya jamin. Gashi bame piddani😒



Nakune masoyana
Tun farko nagaya muku kunutsu da Kyau ku gano kan lbrina

Waye junior
Daga ina ya fitoh
Shin Tun farko ya bayyanar da kansa a SAMAREEN BANAH
Kowa ya bayyanar da kansa tun ranar farko Amma shi meyasa bai bayyanar da kansa ba.

Komadai miye nidai Rahamat ni nasan kan labari nah
Abune mai wiya Nima nayi rashin Ramadan nahhhh

Ihu takeyi sosai me ha'de da kuka....
Na shiga uku ni Maryam make faruwane......
Tafa'di hakan cikin tashin hankali.
Kuka take sosai can taxube aqasa tacigaba da rera abinta batare datayi tunanin SAILUBAH dan kanta ba qaramin bala'in kuncewa yayi ba....

SAILUBAH ko bayan daskare wanta atsaye sai kuma ganinsa tayi ya bayyana gareta da bata kyakkyawar runguma cikin so da kyauna
Yace menene my luv...
Hawaye ne ya xubo mata cikin ka'duwa

Please Login or Register in order to submit comment