Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nasa ya baiyana kan fuskarsa ba. Saima Murmushi da yayi da cewa kamanni kawai mukayi dashi. Amma maganar hali kowa da nasa....
Harararsa dai taqara yi da cewa indai hali na gari ne kasan dai ya fika
Yace ai haka Allah yake bayinsa kiga wani yafi wani.....

Bu'dar bakinta sai cewa tayi dama kai Allah ya 'dauke ya barni da Ramadan😬.....

Dariyar takaici ce ta kwacema Junior yayi Sosai yana kallan kwayar idan da aika mata da wani shu'umin kallo Yace ai dake ba yanda kika iya da ikwan Allah sai kiyi hakuri da rashin masoyinki

Kuma shi yasan me yake nufu daya 'daukeshi yabarki dani 'dan iskan naki

Yanxu dai ba wannan ba. tunda kukan ya 'dauke. Nasamu nutsuwa ka'dan.....
Hau in dubaki pls
Wlhi tun jiya ban samu bacci cikin hankalina ba dan wannan ciwan nakin
Pls my baby tashi kinji yi hakuri👏🏻...

Bayanda ta'iya dashi haka takwanta ya fara mata scanning 'din tana binshi da harara dan gani take da gaiya yake juya mata abun scanning 'din

Batasan shi damuwarsa yaga meyasa mishi ita agaba bane...😬

Yana gamawa ya aika mata da muguwar harara
Bata kulasa ba sanda taxauna a kan kujera tamayar mai da tata hararar kana Tace kaga yaro. yanxu dai kayimin aiko. saika gayamin matsalata kaban maganin naqara gaba....

Karki qara cemin yaro dan yanxu nadoshi 26 years

Ta6e baki tayi cikin raini Tace toh ina ruwana dan kadoshi 26
Agirme dai kasan ba girmata kayi ba. Ko makawo ya shafamu yasan na girme maka nesa ba kusa ba.
Kaga ni ba wannan ba kagayamin matsalata dan gabana ya fara fa'duwa😳.....
Badai ciki bane dani ko
Kasan ko cikin Su KAULEET banji Komai ba sai kwa'dayi da.....

Saurin katseta yayi cikin takaici Yace idan bakimin shuru ba. Wlhi saina tsinka miki mari...
Kona tambayeki ki gayamin ne..
Yarinya sai surutun tsiya kika ajiye...
Ya qarashe maganar da jan tsaki

Shuru SAILUBAH tayi tana kallansa tana tunani aranta meyasa Junior ya gama rainata ne haka.....
Tana cikin tunaninne ya katseta da cewa ya akayi kika kamu da cutar appendix

Appendix😳....
Ta maimaita da waro ido tare da tashi kana tayi narai narai da ido😟
Yanxu yankani xa'ayi acire ko😳
Wayyo ni SAILUBAH...
Kaban amsa katsaya kana kallona......

Murmushi yayi Yace eh yankaki xanyi kuma gobe in Allah ya kaimu.....
Da kuka tafitta daga office din

Murmushi yayi da girgixa kansa ya 'dauki laptop dinsa da wayoyinsa da kulle office din

Lokacin daya fito hartaja motarta ya 'dagama maryam hannu alamar sai Allah ya kaimu. Ta gya'da mishi kai da Murmushi

SAILUBAH ko saka Kakah da Innah tayi agaba tana musu kuka wai gobe xa'a cire mata appendix

Lallashinta suka dinga yi abin tausayi abin dariya.....

KHAULEET Tace kiyi shuru Momy.....
KHAULAT Tace wai Kullun ne sai kinyi kuka Momy
Shuru SAILUBAH tayi musu
Dan Sosai tatsorata da ciwan da kuma fargabar xa'a farke mata ciki 😳

Shiko Junior baibi takanta ba. Sai washe gari daya shiga gidan dankai Su KHAULAT skull
Ya kalleta ka'dan ganin tana Cikin damuwa sai yayi Murmushi dasan ya ta6ota
Yace baki iya gaisuwa bane....
Gallamai harara tayi batare datace mai Komai ba......
Khairat CE tashigo tana cewa LA Ya Junior kawosu na kaisu. Yace taki skull 'din fah
Murmushi da cewa ai muna da walimar skull 'din yau kuma mah sai anjima.
Yace haka nefah
Toh sai kisa dareba ya kaiku yanxu Maza...
Tace toh
Haka tagama hannunsu sukabar falan

Junior ya dawo da kallansa kan SAILUBAH Yace karfah kisa wani damuwa aranki danna shirya wasu dabaru daxan miki wanda xaisa baxa kiji xafin komai ba

Da sauri tasaki fuskarta Tace Allah da gaske😀.....
Murmushi yayi Yace Allah my baby
Tace toh yanxu ya Xa'ayi Yace yanda xa'ayin kenan Kishirya keda Kakah ko Innah muje yanxu dan ayi da wuri. Kinga yanxu 7:30am kafin 9:00 nasan ankagama komai...
Tace anamin xan dawo gida
Yace aa
Tace xan kwana kenan 😳
Yace bama kwana 'daya ba kuma ba biyu ba. Sannan ba uku ba

Tace taf kace aikin babba ne
Kuma xansha jinya
Murmushi yayi yana danna waya batare da yace mata Komai ba

Kiran XEE tayi tagaya mata ita da FAWAS....

******

Dake aikinsu ne Sam bai samu matsala ba
Yayi mata aikin cikin sa'a da nasara.....


Yau satinta 'daya a sibitin

D'akin da take tamkar a 'dakinta take
XEE CE da HAMEEDA suke mata sannu

XEE Tace gaskiya SAILUBAH Junior yana baki kulawa sosai
HAMEEDA Tace wlhi kuwa kamar RAMADAN...
Murmushi SAILUBAH tayi Tace Karki ha'dashi da RAMADAN HAMEEDA danba halinsu 'daya ba
Junior fa bashida kunya idansa atsaye yake. Duk duniya ba wacce ya raina kamarni. Kunafah kallo Haka xai qaraci min rashin kunyarsa ina kallansa in kasa mai komai......
Shigowarsa ne yasata yin shuru tana harararsa dan haushinsa takeji sosai saboda yayi mata qarya akan baxataji Komai ba game da aikin da yayi mata.
Xama yayi kusa da ita Yace har yanxu baxa'a dena fushin dani bane

Kawar da fuskar tata tayi daga kansa tare da qara 'daure fuskarta....
Kumawa yayi inda tajuya fuskar tata Yace kitemaken kidena wannan fushin dani dan ba'abinda yake tayarmin da hankali kamar shi
Kallansa tayi ka'dan Tace ina dabarun naka suke
Murmushi yayi Yana qarema fuskarta kallo Yace duk nayi miki Su
Tace toh naji xaman ya isheni haka pls asallameni naqara gaba
Harararta yayi Yace bayanxu ba
Da sauri Tace yaufah satina 'daya
Kuma nasamu lafiya
Akan me xaisa na xauna
Ta6e baki yayi Yace nace baxa'a sallameki yanxu ba saikin qara sati 'daya...
Ahakan mah in bai mun ba saina qara miki kwanaki
Yafa'da hakan yana me xuba mata abinci a plate
Harararsa tayi Tace Wlhi gobe xan tafi abina dan baxan xauna in qara iban kwanaki haka ba
Murmushi yayi Yace taurin kanki yanada yawa my baby
Amma baxan hanakin ba Allah ya kaimu goben sai kije in gani.....
xata qara magana ya katseta da cigaba da cewa kinga malama ni ba wannan bane agabana gyara nabaki dan kinfara shigar lokacin wasu. Yaqarashe da kallan abincin dake hannunsa

Mugun kallo tawurga mishi da cewa baxanci ba....
Yace idan har bakici yanxu ba aikinki warwarewa xaiyi
Murmushi tayi ganin xai mata wayo....
Tace shekaran jiya bai warware ba jiya bai warware ba sai yau
'Daure fuska yayi kamar gaske Yace Allah idan bakici ba ina tabbatar miki yau Xaki kwana da cigawan ciki
Ya qarashe da kallan XEE dayi mata nuni akan tasa baki

Murmushi tayi Tace kici SAILUBAH dan aikinsa ne tunda yace kici kici kawai mudai lafiyarki muke nema

Xanci Amma da kaina
Kiyi hakuri kibari in baki pls
Wai da raina da lafiyata saika dinga maidani baby
Eh dan ni har yanxu baki wucce wannan wajan aguna ba
Yaqarashe da matsawa kusa da ita Sosai ya kafeta da ido badan tasoba tafara kar6a tana ciki shiko yana bin kwayar idanta da kallo
Wanda hakan ke qara narkar da zuciyarta
Jitake kamar tashige jikinsa dan qamshinsa ya isheta
Gawani shegen sweet dayake tsotsa Sosai takejin San tajishi itama abakinta
dan qamshin ya gauraye bakinsa...
Murmushi yayi da kwantar da murya qasa-qasa yanda ita kawai xataji maixaice mata
Yace kwa'dayayyiya baxan sam miki ba
Ashagwa6e Tace Amma Kasan qamshin yana damuna ko
Murmushi ya qarayi da cewa in sammiki kenan
Da sauri ta'daga mishi kai
Sosai ya qurama bakinta ido da ciro sweet 'din daga bakinsa yasaka mata abaki........

Jan numfashi XEE tayi tana rayawa aranta anyi 'dan iska anan😂. Sai burkita mata 'Yar Uwa kuma qawa yake gashi ba 'digwan kunya a idanshi

HAMEEDA ko burgeta yayi saibinsu take da Murmushi dan Allah yayi HAMEEDA da San Luv

Ahaka FAWAS da KHAMIS suka shigo
Sanda gabansu Yafa'di tunaninsu Senior RAMADAN ne ya dawo....

KHAMIS ya daki fa'darsa yana cewa kashiga da yawa fah
Ba kunya Yace idan ba hakan CE takasance ba baxata bani ha'dinkai bah
FAWAS Yace hmm bi asannu dai dan Auntynmu
Ya qarashe da kallan SAILUBAH yana mai cigaba da cewa am sorry Aunty LUUVAH ya jikin dai
Tace da Sauqi FAWAS kace ya sallameni
Murmushi yayi da maida kallansa ga Junior Wanda ya dage sai bata abinci yake. Kuma kallo 'daya xaka mata Kasan aladole take cin abincin.....
Yace kaga malam sallamemu mutafi
KHAMIS Yace haba kaduba fa bata gama warwarewa ba
Yace ai ita taji ajikinta normal take ko Aunty LUUVAH
Murmushi tayi Tace Wlhi ba abinda baxan iyaba FAWAS kaika'dai ne kake fahimtata Amma KHAMIS bakin shi 'daya yake da wannan....
Taqarashe da kallan junior
D'aga mata gira yayi Yace banda sunah ko.
Tace bansani bah.........



*** ****
Yanda tasashi agaba da mita ita ya sallameta kotatafi abinta
Shiyasashi sallamarta tadawo gida
Wanda hakan yabashi damar cusa mata manufarsa cikin hikima da aiki da hankali
Saiya fake da wai yana bata kulawa ne dan rashin lafiyar tata
Su Kakah dai kallansu suke kawai
Yanxu kijisu suna fa'da anjima kuma kijisu Suna dariya.
Sosai suka gano son SAILUBAH Junior yake Wanda hakan yayi musu da'di Sosai




*Bayan wasu Lokuta*

Junior fa ya shagwa6a SAILUBAH Sosai dan indai yana waje tana waje bawanta yake xama dan bata kulawa
A online ko tun tana jamishi aji hardai tabada kai yadinga 6ata mata tunaninta
Soyayya Sosai sukeyi...
Saidai baita6a kiranta ba
Tunaninsa yana kiranta xata gane shi
Shiyasa yaqi kiranta
Kuma yaqi yarda tasan Waye shi da inda yake
Haka itama Sam bata ta6a kiransa ba
Dan aganinta xai rainata
Yanda yake 6ata tunaninta haka itama take 6ata tunaninsa

Sai su'dauki lokaci metsawo Suna chating batare dasun damu ba

Amma duk da haka idan suka ha'du baya 'daukar raininta
Toh dama ita batasan dashi take chating ba
Shiyasa wani xubin saiyata kallanta yana Murmushi

Nashi salan kenan
(Allah yaji qan Senior Ramadan😭)

*****
Sam SAILUBAH bata kula samari koka'dan
Dan abin ya qara maimaita kansa.
Wani baxawarinta yaxo gareta attajiri dashi yayi ko rashin sa'a dan akan idan Junior yaxo.
Ko cikakkiyar gaisuwa basuyi ba Junior ya 6ata musu Komai ta wajan wasa da hankalin SAILUBAH
Haka shima ya ficce Sam batasan ya akayi ba

(Allah Sarki😰
Karki damu SAILUBAH xamu gyara tuninsa)

Ganin hakan yasa Tace tabar kula samari kenan har abada.......



**********

Yau takama lahadi ranar Hutu ga 'Yan boko

Ruwa ake xabgawa shiyasa duk tauraran nawa Suna nad'e a gado
XEE tana kwance agadanta cikinta ya dameta da motsi tajuyo da kallanta ga 'dan mijin nata Tace gobe ne birthday nasu KHAULAT ko
Yace eh........
Tashi tayi agigice saboda wani naushi da cikin nata yayi mata
KHAMIS wanda yake tura saqo a laptop ya kalleta ka'dan da cewa ina fatan dai lafiya
Tace naushi na yayi
Gaskiya nagaji
Allah katemakeni na aihu yau na huta.....
Murmushi KHAMIS yayi Yace Aunty XEE kenan
Tace yau kuma katuna RAMADAN ne
Yace Wlhi kuwa
Banda haka kinsan kina watan takwas ina ke ina aihuwa yau
Tace ai ana haifar bakwaini
Sai kuma aka gaya miki ana haifar takwasni
Murmushi tayi da cewa baka sani ba.....
Waro KHAMIS yayi 😳 da cewa aa fah😳. Ina addu'ar Allah ya kaiki watan tara kafin Ki haifamin Babyna
Tace oho dan ba.....
Katse yayi wajan saurin cewa gaya min wani abu pls mubar wannan haka
Murmushi tayi da aikamai hararar wasa Tace toh zanci farfesun ganda...

Kallanta yayi da tashi da Murmushi akan fuskarsa Yace muguwa kawai
Kinsan Dady bayaci haka Momy haka ni
Kuma Kinga ana ruwa kawai danki tadamin da hankali shine xakice farfesun ganda xakici ko
D'agamai kai tayi da shagwa6e fuska Tace Allah da gaske nake
Yace ko
Tace eh
Yace toh albishirinki
Tace goro
Yace 'daxo daxan dawo gida
naga gandar me kyau gun wani mutum
haka kawai naji araina inasan in siya
Dan haka nasiya
dana dawo nabama Momy nace tayi farfesu dashi
Batayi mamaki ba dan tayi tunanin koke kikeso
Dan haka yanxu bara inje in kar6o miki. Kinga muguntarki takoma kanki ko😀....
Turo baki XEE tayi Tace toh baxanci bama nafasa
Ta6e baki yayi Yace toh saime😏 dama aina mugunta ne

Haka yakoma yaci gaba da aikinsa itako tasamai ido lokaci lokaci tana aika masa da hararar wasa
Shiko binta yake da murmushin mugunta irin burinta dai bai cika innan ba. Na bashi wahala.....



FAWAS ko futuna yakeji musamman yanda yakejin yanda ake sheqa ruwa dan haka yana maqale da Matarsa yana lalla6ata dan ahannu yake Saura ka'dan Komai ya wanxo sukaji kukan Ahmad
Awahale Yace my boy menene
Yace Dady kabu'de xan 'dauki chokulet 'dina ne
Yace ina na 'dakin Momy
Yace ya qare.
HAMEEDA taxare jikinta daga nasa tabu'de wata durowa ta'dauko mishi kana ta gyara kanta da bu'de qofar Tace gashi.....
Kallan hannunta yayi yana yatsina fuska da cewa toh ina Dadyn nawa
Tace xaka kar6a ne ko xaka tsaya yimin surutu.....
Kar6a yayi yana cewa toh Momy kimatsamin naganshi mana......
FAWAS najin haka yayi saurin gyara kansa.... HAMEEDA ko Murmushi tayi da matsamai ya shigeta......
aiko yana Ganinsa ya 'dane gadan yana cewa Dady tashi muyi wasa.....
A wahale FAWAS Yace banajin da'di my son kaje gun momyna kuyi
Murmushi yayi Yace aa naka bake so....
Duk yanda yaso da yayi masa wayo 'ki Ahmed yayi
Ba yanda FAWAS ya iya dashi dan Sosai 'dan nasa yasamai gaba haka yasauka ya biyemai sukadinga buga boll
HAMEEDA na kallansu tana bin mijin nata da murmushin mugunta
Shiko yana maida mata dana xaki gane kuranki.....



Mutumin nawa ko yana kwance shima a nalla'de kan gadansa yana tunanin mutuniyar tasa
Ganinta online yasa yafara bata kalamai kamar haka

```Nayi tunanin baxaki hau yanxu bah```

SAILUBAH dake kwance afalo tana chatin da wata qawarsu taga shigowa nashi sakwan
Dama tagaji da hirar da ita dan haka tayi saurin kar6ar sakwan nasa da bashi amsa kamar haka.....

```Na haune ko Allah xaisa naganka akai```

``` hmm kinada wayo my Luuuuu. nasan badanni aka hau ba. karkiyi wani alaye```

```Xanso kayarda da abinda nace```

```Na yarda```

```Yauwa dama ina so yau nasan kai Waye. Ina San jin muryarka. Ina San ganinka.```

````Da gaske kike babyna```


```wlhi da gaske. Kuma in ban ganka yau ba. ka tabbatar nadena kulaka```
```farkoma awane gari kake kuma wacce unguwa```


Shuru Junior yayi
Can ya fara bata amsa da cewa a kano yake a unguwar Fage dayi mata kwatancan nayin da yake....


Da mamaki SAILUBAH Tatashi tana bashi amsa cike da al'ajabi

```Toh ai unguwarmu 'daya```
```Gayamin awane gida kake```

Murmushi Junior yayi kafin yaja numfasa.....

```Kinga masoyiyata kar kimin qarya. Taya xa'ayi muna layi 'daya nakasa ganeki```

Afusace Tace.....

```kaga Malam kafitoh k'ofar gidanku nima in fitoh kaga saimu tabbatar da gaskiyar xan xanmu```

```Ana ruwa a uguwarmu sosai😳. Dan haka kibari a'dauke```

```Ai ruwan ya tsagaita yanxu. dan haka kafitoh nima ganinan```

Toh Yace mata tare da tashi yana gyara kansa da rayawa aransa yau xai cika burinsa na farko.


SAILUBAH ko dake agyaranta take dan haka gyalanta kawai ta'dauka tafitoh waje
A'kofar gidan nasu tatsaya tana tana wulla ido ta'ina masoyin nata xai 6ullo
Junior ne yafitoh da shigar sanyi a jikinsa kallo 'daya xaka masa yabaka sha'awa dan yayi kyau Sosai
Suna ha'da ido ta hararare shi

Sanda ya qaraso gareta Yace wow kinga inda kikayi kyau kuwa
Tace nagode
Yace Wlcm
Garin bai baki sha'awa ba. Kiduba yanda yayi wani lublub dashi. Sai qamshin qasa ne ketashi
Tace eh yayi kyau Sosai pls karka cikani da surutu
Yace to fushin namiye
Tace kasan ka 6atani da bani abinci shine yau naqi ganinka ko

Murmushi yayi da cewa ke soyayya nakeyi yau
Kinsan in ina yinda manta kowa da Komai nakeyi.....
Ya qarashe maganar yana mai kallan saman layin da qasan nayin. Kallo 'daya xakamai Kasan wani abu yake nemah.....

Tsaki SAILUBAH tajah cikin 6acin rai Tace yanxu har soyayyarka tafini muhimmanci...
Ka tuna fah ni amanace agareka...

Wai dan ke amanace agareni sai karna fifita soyayyata saboda ke
Inaaa baxai yuhu ba
Inasanta over
Wlhi akanta xan'iya barin kowa da Komai
Xan iya barin Komai
Ina MASEEFAR SONTA
Gwarama kicire wannan dan tayimin illa da yawa

Ki dai yi hakuri kawai naganta yanxu saina baki ko my baby
Ya qarashe da sakar mata shu'umin Murmushi

Itako mugun kallo ta wurga mishi Tace bana so Wlhi In saika ganta xaka ban abincin kabarshi nagode

Yace hmmm
Xama kici ne
Am dan Allah ban shawara
Kinsan ban ta6a ganinta ba
Kawai dai muna catin ne
Kuma wani iko na Allah ahakan tatafiyar da xuciyata
Ina Santa da yawa my baby pls ban shawara yanxu idan tafitoh mexance mata

Dariya SAILUBAH tayi Tace hmm Lalle nemah
Kana nufin duk wannan xagewar da kake akanta baka Santa ba
Yace Wlhi ko waya bamu ta6a yiba
Tace toh ya'akayi kasamu Num nata
Yace ina tunanin KHAULAT CE ko Khairat tsakaninsu wata taha'damin as love Kinsan Suna 'dauka

Tace Lalle sunha'daka da wahala
Kuma baka ta6a ganinta ko'a dp nata bah
Yace bata SA photo Sam
Tace kace taha'du........

Kanya bata amsa wata 'yar makwaftansu tafito dana wullah ido da alama yaran aike take nemah.....
Aiko da sauri junior ya kuma bayan SAILUBAH yana salati qasa qasa yake cewa nashiga uku my baby kodai itace wannan
Kut gaskiya mummunace dan Allah da'da kareni karta 'dauka nine😳

Da sauri SAILUBAH Tace bangane ba kana nufin kunyi da ita Xaku ha'du yanxu ne

Eh mana. Wai tace alayi 'daya muke da ita.
Shine Tace nafitoh yanxu itama gatanan fitowa

Juyowa SAILUBAH tayi tana kallansa gabanta na fa'duwa tafara kiran numbar da suke catin da saurayin nata

Aiko sai gashi taji ringing a ajjihunsa
Da kanta tasa hannu tajiro wayan tana dubawa taga sabowar waya dal
Kuma ba wacce tasanshi da ita bace
Ga Num nata na yawo akai
ahankali ta kallesa Tace wannan wayar fah
ta6e baki yayi da cewa baki sanni da itaba
Tace ina wacce nasankan da ita
Yace tana gida mana
Yafa'da yana mai kar6ar wayan dacigaba da cewa Kinga kuma tana kira....
Ya dace na amsa daji muryata yanxu


Shuru tamai tana qare mai kallo tundaga sama har qasa
Kana Tace nice wacce kake fa'da junior😰.....

Kamar gaske ya waro ido 😳 yana cewa kut keeee

Amma kin bala'in rainani
Kirasa Wanda xaki yaudara saini
Kinsan lokacin dana 6ata akanki

Hawaye ne ya xuboma SAILUBAH Tace Junior kana cutar dani
Nice na yaudareka ko kai

Afusace Yace saiki gayamin ta'inda na yaudareki
Ina da Num naki akan wannan wayanne
Ko kina saka hoto a dp naki ne daxan gane kece..

Tace toh nima ai bakasa hotanka a dp kuma bada aynihin Num naka kake chatin dani ba

Mugu kawai. Wlhi Allah saiya sakamin wasa da hankalin da kakemin

Kinga malama. kar kiyi wani alaye dama can sonah kikeyi shine yasaki yaudarata tawannan Hanyar

Toh bari kiji Wlhi banta6a yaudarar kowa ba. Haka nima bamai yaudarata
Wlhi tallahi saikin Aureni

Afusace tanunashi da yatsa Tace Wlhi baxan Aureka ba
Bana sanka bana sanka

To dama angaya miki nima sanki nake
Maixanyi dake tsohuwa dake
Kawai Xan aureki ne dan in nuna miki ba'a yaudarata

Da kuka wiwi tashige gida.....
Murmushi yayi yabi bayanta

Ajikin Innah taxube tana cigaba da kukanta
Innah Tace toh yanxu kuma menene
Tace kuduba Junior Innah sai wasa yake da hankalina ashe shine wanda nake CE muku yana damuna a waya da sakwanni.......

Katseta yayi da cewa qarya Tace Innah ita take damuna
Yanxu kukan da takeyi 'daya ne
Shine wai dan nace baxan Aureta ba
Toh kiyi shuru Xan aureki danba qaramin illa kikamin wajan yaudarata da soyayyarki ba

Kakah saiku saida xan Aureta
Ku tattauna da Dady cewa minshirya kammu muna San juna da Aure

Saidai kuja kunnanta ba ita ba wani 'da namiji

Murmushi Su Kakah sukayi atare sukace Madallah
Toke kidena kuka tunda Yace xai Aureki mana....
Yauma xamu tattauna da Dadyn naku akan hakan.......

Wani baqin Cikine ya tokari SAILUBAH a qirji.
Watoh junior ya tabbata 'dan iska kuma makiri maqaryaci
A gabanta yanxu ya sharara mata qarya bayan raina mata hankalin da yayi

Tayi mamakin yanda takasa cewa Komai harsuka qarashi xancikan nasu suka barta dashi agun

Yana ganin Su innan sun barshi da ita yayi saurin matsowa gareta yana mata murmushin mugunta
Yace am so sorry my Baby
ina tare da sanki araina
Sosai nake sanki...

Toni bana sanka Junior

Yace meyasa

Saboda kai 'dan iska ne
Kuma mugu Mara tausayi
Daka kasance RAMADAN dana soka...

Kama fuskarta yayi Yana shafawa cikin wani salo na Luv Yace kisoni Ki huta my baby dan xan baki duk wani farinci da kike nima arayuwarki
Wlhi in kikaqi tsaida tunaninki akaina ina tabbatar miki ni ina dai-dai da in gyara miki shi
Ina sanki ina sanki ina sanki
Kuma inada mummunan kishi akanki
Dan haka Ki kiyaye....
Yana kaiwa nan yasakar mata kiss da sakin fuskar tata ya ficce daga falan

a bakin get yaci karo da Khairat dasu KAULEET a hannunta
Aiko suka cukukuyeshi Yace kun gama mah Momy 6arna ko
Khairat Tace aiko Ya Junior bakaga 6arnar dako sukayi ba.....
Yace ai daga ganin wannan dawowar bata shiri bace
KHAULAT Tace Dady gobe ne birthday ko 😀
Murmushi yayi Yace eh....
Khairat Tace yanxuma xanje kar6o musu wasu kayansu ne gun Aunty xema
Yace dare yayi banaso kije ko ina yanxu
Tace yamma ne fah Ya Junior....
Harara ya gallamata da cewa barnan..
Aiko ba shiri tayi ciki
Shiko yaja mutanan nasa sukayi gidansu..


Shigowar Khairat ne yasa SAILUBAH dawowa daga duniyar data fa'da
Khairat na qara gaisheta Amma Sam bata San tanayi bah. Kwakwalwarta tatsaya cak wajan tuno xancikan da Junior yayi mata....

Toh Aunty nina tafi tunda kinqi cemin Komai
Khairat Tace da SAILUBAH hakan cikin gajiyawa....

A 'dan furgice takalleta da cewa Sowie mashiga wani yanayi ne
Tace dama Momy ce tace inkin gama hutawa kixo kiga yanda aka shirya Komai Tace OK.....



Har kwanciyar bacci SAILUBAH bata dena jin xancikan Junior suna mata kurwa a kunne bah
Dan haka sai takasa hakuri sanda takira XEE tagaya mata tana kuka
XEE dai lalla6ata tadingayi dan tada'de tana mamakin me Junior yake jira dahar ya'ibi lokaci me tsawo haka bai nuna mata manufar tasa ba......



*Kishin Maza*

Haka ko akayi
Washe gari takama birthday 'dinsu KAULEET da KHAULAT

Da misalin 2:30pm wajan shaqatawar ya cika Sosai Amma ba irin wannan cikar ta hausawa ba
Dan kowa yana teburinsa da abun ta6awarsa
Sosai wajan ya qawatu
'Yan mata da samari sunfi cika gun
Harda manya manyan attajirai wa'yanda sukaje gun dan kawai su gwa'da sa'arsu agun SAILUBAH ko xasu dace
Sai qawayanta da 'Yan Uwa da abokanayan arxiqi
XEE da HAMEEDA sune ahannun damanta

KAULEET da KHAULAT da AHMAD da wasu yaraku ne xagaye awani ha'daddan gu Wanda yake fidda wutta
Ba qarya mutane sunga birthday 'din yara 'Yan gata
Sosai jama'ar gun shagalin ya burgesu gefe guda kuma Suna yagar kaxa da kora drink abin sai wanda yagani

Ankashe ku'di Sosai bana wasa bah
Dan wannan birthday ya bambanta da Wanda jama'a dadama suka sani

Toh😳
Al'amarin ya faru ne lokacin da wani matashin saurayi Wanda baxai wucce shekara talatin da biyu ba. Sai yajah kujerar da take fuskantar SAILUBAH ya xauna yana aika mata da kallan Luv... Tunkan yayi mata magana Junior ya kalli FAWAS Yace wancan yashiga gonata fah😌
KHAMIS Yace toh miye...
Ka share kawai dan Kasan Auntyn tamu ba kulasa xatayi bah

Yace da sake fah😳
Kaduba yanda suke fesin 'din juna kamar wasu tsofaffin masoya
Murmushi FAWAS yayi da cewa karfa kishi ya tona asirinka yau....
da sauri Yace na yaushe kuma....
Bayan jiya tafaru taqare....
Kan FAWAS ya qara yin wata magana tuni junior yatashi ya nufi inda SAILUBAH take.....
[8:38AM, 11/03/2017] R🇦HAⓂ🇦T Nalele: Daga yanayin yanda yake tafiyar tasa kaxasan yanajin iskanci
Sai tafiyar tashi tabada wani salo da ki'dan da yake tashi
Duk illahirin matan da maxan dake gun idansu komawa yayi gareshi
Dan sak komansa komawa yayi irin na 'yan iskan nigoginnan
Ga madarar kyansa da take 'daukar hankalin duk wanda yayi gigin yimishi kallo 'daya

KHAMIS ya kalli FAWAS Yace gaskiya junior 'dan iska ne kaduba yanda yake tafiya
FAWAS yayi Murmushi Yace hmm kakula mana. kishi ne ya kusan ceshi da yawa.....

Saurayin ko qara kafe SAILUBAH yayi da ido Yace ina sanki SAILUBAH
Murmushi tayi da cemai dan Allah kayi hakuri malam Da sadakina ahannu
Ma'ana wani ya rigaka

Yace toh ai sadaki ba Aure bane.....

Koh....
Junior yafa'di hakan yana mai qarasowa gun da dafa table 'din gaban nasu....
Kallo 'daya SAILUBAH tayi masa gabanta ya tsinke ya fa'di dan ganin yanda ya sauya kamanni

Haba malam. Waye kai da xaka shiga xancanmu batare da neman ixini ba
Saurayin yace da Junior haka

Murmushi yayi Yace sanin koni Waye ba abu bane me mahimmanci agareka
Fa'dar abinda nakeso shine me mahimmanci agareka
tace kayi hakuri da sadakinta ahannu
Bata Barka haka ba sanda taqara maka dacewa ma'ana wani ya rigaka
Amma dake kune irin 'Yan iskan nan wa'yanda basu'daukar fa'dakarwar muslinci abakin Komai shine kike cewa ai sadaki ba Aure bane ko....


Toh ya'isa haka....
Ka bari....
Dan ita 'din bata kowa bace face ta SADEEQ......
Qaddarar Auranta akansa

Please Login or Register in order to submit comment