Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kowa ake yiwa Alfarma ba sai Wanda ya Isa kazo Kanata wani fusfusgewa kamar kanada Wanda zai tsaye maka"

Tafa hannu Dr. Omar yyi Yana Isa gaban Table din Prof yace,

"That's is d main point, yanzu ka Fadi gskyr abin, yanzu kayi mgnr da tun dazu ya kamata ace ita ka fada straight"

cikin Dan kidima Prof ya fara kame-kame Ashe yyi sakin layi be sani ba, Dan haka yace,

"Kai Wai Toh me kke nufi?"

Duk yadda Dr. Omar yaso controlling anger dinsa kasawa yyi Dan haka cikin kaushin murya yace,

"Abinda nake nufi shine Abinda kuka taru kuka shirya a Kaina kaida sauran munafukan da kuke Jin haushina tun fil'izal Hanya kuke nema kuma kun samu then What?????"

yyi mgnr Yana buga table din da karfi hade da juyawa ya fice a office din gaba1. A tsorace Prof Akilu yabi Bayan Dr. Omar da kallo Yana Dan goge gumin daya tsatsafo Masa a saman goshi sbd firgita Wai a hakan ma cikin mutanen da suka shirya korar Dr. Omar shine ma me karfin Hali a cikinsu.

Cikin fusata yafito office din ko kadan be daga Kai ya kalli mutanen dake kallon sa ba kamar dazu harya bar skul din gaba1, Dan napep ya tare kawai Wanda zai kaishi gidansu, lkcn dayaje gida mlm sale ne kawai zaune kamar kullum, Dan daidaita nutsuwar sa yyi sbd bayason Abba ya gano ko akwai wata matsalar yafiso yyi handling komai d kansa Dan haka ya Isa gaban mlm da Dan sakin fuska kadan, mlm sale ya zuba Masa ido a nutse sosai ya hango tsagwaron damuwa da bacin Rai a idon Dr. Omar din, Amma dake Babu halin mgn haka yake ta binsa da ido gwanin tausayi, ganin irin kallon da mlm sale yake binsa dashi yasa ya kwakulo murmushin Dole yace,

"sannu Abba"

kada Kai Abba yyi Alamar ya Amsa, Dr. Omar yadan shafa sumar kansa cikin dauriya da danne bacin Rai sosai yace,

"Yau Abba a gida zansha karatu sosai Dan haka idan na shige daki sai an ganni kasan jarabawar tamu befi kwana uku ba"

yyi mgnr Yana Dada matso murmushin Dole duk Yana yin hakan ne kada Abba ya fahimci Yana cikin damuwa shima ya damu, mlm sale yyi murmushi sbd yadda yaga Dr. Omar din na murmushi sai hankalin sa yadan kwanta sabanin ganin farko d yyi Masa sai yaga kamar Yana cikin damuwa, Murmushin da yyi ya bawa Dr. Omar damar tashi hade da shigewa daki, yyinda mlm sale ya bishi da kallon tausayi duba da yadda yaga dan tsukukun dakin daya Shiga Kai kace na masu gadi ne oh mutum da gatansa a maida shi marar Gata, Allah ya fishsheka Ameen mlm sale ya Fadi hakan a ransa.


###
Koda Dr. Omar ya shige daki sakata yasa ta ciki kawai ya koma kan katifar sa ya kwanta ruf da ciki idanun sa take suka fara canja launi daga fari zuwa ja, juyi yake kwarai cikin tsananin Zafin Rai da Takaici, yasan tun ba yau ba dayawan wasu malaman su suke matukar Jin haushin sa sbd kokarin da Allah ya bashi duk yadda kaso kada shi Yana da zarrar tunkarar ka matukar yanada gsky sai ya karbarwa kansa 'yanci baya Bari ko Kai waye ka tauye Masa Abinda ya samu Akan exam, test, da sauran su, Abinda ya Kara Masa bakin jinin shine duk yadda mlmi ya koyar zakaji Ana Bari Dr. Omar yazo yyi Mana fashin baki domin suna Jin dadin tutorial dinsa, sunfi gane nasa fiye Dana kowa, Wannan Abu na bakanta musu Rai kwarai kazalika duk wacce suke so sai su fahimci Dr. Omar takeso Wannan ma Yana Kara tunzura su shiyasa suka tsane shi basa nunawa ne sbd abin na gulma ne,

Saidai Basu sani ba Dr. Omar karrr yake kallon su Yana sane da duk wani gulmace-gulmacen su Abinda ya yadda dashi shine Babu yadda suka iya dashi domin ya zame musu tamkar ciwon Ido, shiyasa Wannan damar tana zuwar musu batare da Bata lkci ba sukayi amfani da ita musamman da suka samu sa bakin Sageer a ciki sai suka samu nutsuwar yin komai sbd Sageer din Dan kowa yasan waye ubansa.

Juyi ya sake Yi yyinda tunani kala2 ke Masa yawo a zuciya tsabar yadda yakejin ransa na Kuna ma har wani hucin zafi yake fitarwa ta bakinsa, ya cije lips dinsa yafi a kirga, dukan pillow dinsa yake sosai tamkar ya samu mutum, daidai lkcn yaji wayarsa na ringing can gefe Ashe ta Fadi daga Aljihun sa ma be sani ba, Ko kallon inda wayar take beyi ba harta tsinke again yaji wani Kiran ya sake shigowa wani irin wawan tsaki yaja cikin fada2 yace,

"Wai wanne jarabab..."

Mgnr sa ce ta makale daidai lkcn dayaga sunan Alhajin Abdullahi na yawo Akan screen dinsa, Kasa share Kiran yyi sai ma samun kansa da yyi Yana daidaita nutsuwar sa hade da daukar Kiran ya Kara a kunne,

"Assalamu Alaykum"

yaji muryar Alhaji Abdullahi ta doki dodon kunnen sa, sosai yaji mgnr har cikin kansa besan ya akayi ba Amma samun zuciyar sa yyi dajin wani Sanyi na kwaranya a hankali,

"Hello kanaji kuwa?"

Yaji an katse Masa tunani, da sauri ya sake saita muryar sa kafin ya Amsa Masa sallamar cikin nutsuwa, daga dayan Bangaren Alhaji Yyi murmushi yace,

"Omar da fatan ka gane me mgnr"

Dr. Omar yace,

"kwarai kuwa da fatan an Isa gida lpy jiya"

"lpy lao Alhamdulillah"

Alhaji Abdullahi ya furta hakan, Shiru Dr. Omar yyi ya rasa mezai ce Masa daidai lkcn Alhaji Abdullahi ya katse shirun da fadin,

"idan bazaka damu ba Omar inason haduwa dakai akwai wani muhimmin zancen da nakeson Yi dakai"

shiru Dr. Omar yyi ya kasa furta komai, Alhaji Abdullahi yace,

"don't worry ba Dole sai yau ba zaka iya zabar time din da kke free"

Wani irin nauyinsa Dr. Omar yaji Sam ya kasa musawa Wannan mutumin musamman idan yyi Masa mgn sai yaji kamar da kankansa yake mgn sbd sautin yanayin muryar sa, a nutse yace,

"A'ina kkeson nazo na sameka?"

Dadi ne ya Kama Alhaji Abdullahi har hakoran sa Saida suka fito waje sbd murmushi yace,

"Zan turo maka address din ta message saika zo"

"to shikenan sai nazo"

Dr. Omar ya furta hakan cikin girmamawa, Alhaji Abdullahi yace,

"Toh Allah ya kawo ka lpy"

"Ameen"

Dr. Omar ya furta shima, katse wayar Alhaji Abdullahi yyi yyinda Dr. Omar yabi wayar hannun sa da kallo cikin matukar tsananin mamaki, Wai Anya lpy kuwa? Toh meye hadinsa da Wannan mutumin da yake kasa Musa Masa? Shifa abin na daure Masa Kai kwarai, shafa sumar kansa yyi yana tunanin tabbas duk abinka wata Rana saika samu Wanda yake maka kwarjini, Karar text message yaji Dan haka ya zaro wayarsa Dan ganin Address din inda zashi, Sosai ya ware Ido Yana bin Address din da aka turo Masa da kallo.


°°°°°°
Acan bangaren Alhaji Abdullahi kuwa koda ya Gama wayar uwargidan sa Hajia Aisha ya kalla data tsare shi da ido tun dazu, Ganin batace komai ba yace,

"Uwargidan Abdallah nayi Miki kyau ne?"

Dan murmushi Hajia Aisha tayi kafin tace,

"tun jiya na kasa daina mmkin irin zumudin Dana fahimta Akan fuskar ka Anya dai ba Gamon kayi ba?"

Dariya Alhaji Abdullahi ya fara Yi kafin yace,

"Kin cika tsoro Wlh, Ina Tabbatar Miki matukar Kika ganshi zakice tabbas ya dace ayi zumudin shi"

Hajia Aisha tace,

"Ai tunda naji kana bayanin Nan, yaron Nan ba karamin sa'a ya taka ba Wlh"

Alhaji Abdullahi yace,

"kwarai kuwa kinsan Wannan company din nawa na Nan kano?"

Hajia Aisha tace,

"kwarai kuwa ai shine mafi girma da daukaka Akan dukkan companies dinka na Nigeria"

Alhaji Abdullahi ya girgiza Kai kafin ya fara mgn cikin damuwa yace,

"tun kafin Danmu Sageer ya fado duniya nake da burin Mallaka Masa company dinnan, Naso kwarai ace ya kasance cikin masu nutsuwa da hankali sbd kula da Wannan dukiyar tamu Toh Amma saidai kashhh.. a kullum nakan rasa gane Ina Sageer yasa gaba? Sam be damu da kishin kansa ba, be damu da Gina future dinsa ba, Be damu da damuwar Wanda yake tare dashi ba, Abinda ya sani kawai shine yaci, ya batar, yahau latest mota, yasai expensive abubuwa, ya Shana, ya hole, aikin kenan, kina ganin mutumin dabe san ciwon kansa ba ya cancanci a bashi Ragamar wannan company din?"

Cikin matukar damuwa Hajia Aisha ta girgiza Kai duk kwalla ta cika Mata Ido sbd tuno da halayen danta Sageer a fili tace,

"Allah shine shaida na bashi dukkan tarbiyar daya kamata da na gari ya kasance, Kullum Addu'a ta shine Allah ya shiryamin yarona aduk inda yake, Amma abin Sageer sai Kara tabarbarewa yake na rasa ta inda Zan kamo bakin zaren"

Dan jawota Alhaji Abdullahi yyi Yana Dan buga bayanta yace,

"calm down it's okay kisan dama Dan Adam Tara yake be cika goma ba Koh? So kisa a ranki Wannan itace tamu jarabawar mu Kuma gode da Allah yasa shi kadai ne Dan Safna ta fishi hankali nesa ba kusa ba"

girgiza Kai Hajia Aisha tayi tace,

"Allah ya shirye su gaba daya"

"Ameen summa Ameen"

Alhaji Abdullahi ya Amsa kafin yaci gaba da fadin,

"Wannan company din da ya bunkasa Yana nema ya tabarbare sbd zagon kasa da ake min"

Tasowa Hajia Aisha tayi tana dubansa tace,

"meya faru?"

Alhaji Abdullahi yace,

"Manager dina baya min aiki bisa gsky da Amana, haka sauran ma'aikatan Kowa ya zama malalaci yanzu sun maida abin kamar business sbd bana Nan Saiya kasance mafi akasarin masu aikin hanyace ta kawo su ba kokarin su ko son aikin ba, kowa ya maida office dinsa matattarar Chatting, hutawa, Hira batare da sunyi Abinda ya kamance su ba, Shiyasa nakeson ayiwa company din operation a zare duk wasu Bata garin ciki asa masu nagarta a Debi ma'aikata Wanda suke Naman aiki musamman talakawan mu da duk suka rasa aikin Yi Bayan wahalar karatun da suka Sha aiki ya gagaresu"

Cikin gamsuwa da hukuncin da Alhaji Abdullahi ya yanke Hajia Aisha tace,

"Wannan shawarar tayi sosai yanzu Wa kke tunanin zaiyi maka Wannan aikin ka'in da na'in batare da an samu matsala ko an raina sa ba?"

Murmushi Alhaji Abdullahi yyi kafin yace,

"Idan na Tabbatar da Abinda nake hasashe Zan Gaya Miki koma wanene"

Hajia Aisha tace,

"Toh Ina fatan Allah ya hadaka Dana gari me tsoron Allah"

"Ameen summa Ameen"

Alhaji Abdullahi ya furta Yana Shirin tashi Dan zuwa yiwa Hajjaju sallama kafin ya fita, kamar koyaushe kuwa Hajia Aisha ta rako shi har zuwa parlon kasa,

karar zubewar Plate sukaji hakan Yaja hankalin su Kan Saratu data riko su zata Kai dining table Dan tunda tazo d sassafe take raba Ido taji bayanin mutuwar Alhaji Abdullahi bataji komai ba, gashi kowa sai harkar gabansa yake Babu damar tayi tmbyr ta jawowa kanta bala'i Dan Banda mahaukaci waye zai tmby me gida Yana raye koya mutu? Rashin ganin Hajia Aisha tun dazun yasa ta kasa nutsuwa shiyasa yanzu tana ganinsu ta saki plate din hannun ta cikin matukar firgita da tsoro.
8/15/20, 8:02 PM - Ummi Tandama: *200 ne kacal👌🏻 ba yawa Domin sanin yadda Zaki biya ki nemi Wannan number 09039118754*


......🐓🐓🐓



Na
*Nuceeyluv😘*


21.....



Kallon mmki suka bita dashi kafin Daddy ya kawar da kansa Daga wajen, Hajia Aisha ce tace,

"lpy Saratu?"

Saratu na daidaita nutsuwar ta tace,

"Eh lpy ban rikesu dakyau bane shiyasa suka zube"

girgiza Kai Hajia Aisha tayi kafin ta dauke kanta zuwa Kan mijinta da suke tare Nan sukaci gaba da tafiya Dan zuwa wajen Hajjaju, fitarsu keda wuya Saratu ta koma kitchen da sauri kafin ta zaro wayarta hade da lalumen Number Nas, Bugu daya ta dauka cikin sauri Saratu ta fara mgn Tace,

"Nas Abu fa ya baci"

Nas tace,

"me kike nufi?"

Nan Saratu ta sanar Mata Alhaji Abdullahi dai ya dawo Babu ko kwarzane a jikinsa, Cikin takaici Nas tace,

"da alama mutanen Dana tura Basu je ba shiyasa ba'a kaddamar da aikin Nan ba"

Saratu tace,

"Toh ki sake kiransu muji dalilin Rashin aikin su?"

Nas taja tsaki tace,

"Share su ai Abinda muke gudu shine kada mlm sale ya samu bakin mgn yanzu kuwa da akasa zancen mgnin nasa yasha ruwa ai Kinga shikenan"

Saratu tace,

"Wannan haka yake Amma fa ni na kosa na fara dandanar Arzikin da Dana yake ciki"

Nas tace,

"kefa kinada gaggawa Wlh ki Bari komai ayi a sannu Mana ko so kike muyi Abinda za'azo Ana zargin mu?"

Saratu ta girgiza Kai tamkar tana gabanta, kafin tace,

"shikenan Zan Dan jira"

"Mtwss.."

Nas taja tsaki tace,

"Idan ma baki jira ba yanzu sai kije ki sanar musu danki ne a gunsu"

Saratu tace,

"haba abin baikai har haka ba ai"

Nas tace,

"ke Kika sani"

ta karasa mgnr tana yanke wayar ta, Shiru Saratu tayi kafin ta fara wani tunanin a ranta gsky zataci gaba da shigewa Sageer Koda zaiyi ta Mata wulakanci ne ai jini ba Wasa bane Kila wata Rana ya fara jiyo kamshin jinin jikinsa a jikinta, da Wannan shawarar ta kinkimi abincin Hajjaju zata Kai Mata, fitowar ta daga part din Hajia kenan ta hango Sageer Yana waya Yana dariya sosai, daidai zata wuce shi Kuma lkcn ya Gama ya dago kansa, kallon ta yyi yace,

"yauwa ke Yama sunan ki?"

Zaro Ido Saratu tayi
Sageer ya bita da kallo irin na kaskanci yace mmki kike Koh me?"

Girgiza Kai Saratu tayi da sauri kafin tace,

"Saratu"

Dan tsaki Sageer yyi yace,

"Toh Saratutu idan kin Gama kisan yadda zakiyi ki fito zansa driver ya kaiki gidana dake Bayan gari akwai wasu ayyuka da zakiyi a Matsayin ki name aiki"

Sakin baki Saratu tayi d mmki a ranta tace dama Dana Sageer yanada gidan kansa?

"Kinyi shiru ko bazaki bane?"

ya Fadi hakan cikin fada2, Jiki na rawa Saratu tace,

"ayi hakuri yallabai Zanzo Amma meyasa bazan nemi izini daga wajen Hajia ba?"

Wani irin muguwar Harara ya bita dashi yace,

"meye Matsayin ki a gidan Nan?"

Saratu na hadiye wani mugun yawu tace,

" 'yar aiki"

"Good then karki Shiga hurumin masu gida kin gane?"

Saratu ta girgiza Kai, yace,

"oya maza ware"

yyi mgnr Yana nuna Mata hanya, kamar jira kuwa take ta fara tafiya da sauri shima juyawa yyi zai fara tafiya kenan ya waiga yace,

"ke Saratutu"

a firgice Saratu ta juyo Jin irin Kiran da yake Mata, Dan kasa da murya yyi cikin nuna Alamar gargadi yace,

"matukar Kika Bari su Mummy suka San inada wani gida a waje saina sa an koreki a gidan kin gane?"

Yyi mgnr Yana rike kunne, kamar wata kadangaruwa Saratu ta kada Kai Alamar taji, hakan yasa Sageer ya juya yaci gaba da tafiya batare daya sake Mata mgn ba, ganin haka itama saratun ta juya da sauri Dan barin wajen, daidai zata Shiga parlon Hajjaju taji Hajjaju nata surfa fada, Fadi take,

"meyasa baka sa an kamasu ba? Bayan kaji da bakinsu cewa sukayi turo su akayi?"

Take kirjin Saratu da Take bakin kofar ya buga da karfi dammm, Ji tayi ance,

"karaso Mana"

Hajia Aisha tayi mgnr Ashe ta ganta lkcn data zo, A firgice ta karasa Shiga dakin sumsum kamar ace Cass ta zura a guje, shiru parlon ya dauka sbd Hajjaju ta daina fadan saidai kawai mita data farayi kasa2 tana fadin,

"Dakai da matar taka bansan meyasa kuka cika yadda da mutane ba Wlh, Kuna mantawa da cewar makashin ka Yana tare dakai ku rike Wannan mgnr dakyau yanzu duniya ta canja Wanda ka yarda dashi shi yake cin amanar ka"

daddy ne yace,

"Toh Hajjaju Addu'ar da kike binmu dashi koyaushe ta Isa ta zama makami a garemu Kuma ni Abinda na sani shine duk Wanda yake Shirin haka Ramin mugunta to ya ginashi daidai kansa kada yyi tunanin Abinda yakeyi Allah baya kallon sa Dan wata Rana Wannan Ramin zai rufta dashi"

"wufff... ma kuwa"

Hajjaju ta furta hakan da karfi Alamar me Gina Ramin muguntar saidai ya tsinci kansa wuff a ciki, kadan ya rage Saratu ta Antaya Mata tea din data hada Mata sbd yadda taji mgnr har cikin zuciyar ta dama kuwa tun dazu kamar ta zura a guje haka takeji duk tsoro ya Kama ta gani take kamar sunsan me tayi shiyasa suke Mata jirwaye,

"ha'a ke lfiyr ki?"

Hajjaju ta furta tana matsawa baya, Saratu ta washe bakin Dole tace,

"ayi hakuri ban lura bane"

"Mtwss..."

Hajjaju taja tsaki tana fadin,

"kai ni na gaji da Wannan shayin jeki damo kin kunu shi nakeson Sha"

Da sauri Saratu tace,

"Toh"

ta Fadi hakan da sauri kafin tabar parlon, Hajjaju ta bita da kallo sosai sannan ta dubi su daddy tace,

"Wannan Mata tun ranar datazo gidan Nan ban taba Mata kallon mutuniyar Arziki ba"

daddy ne yace,

"tofah Hajjaju wani Abu tayi Miki?"

Hajjaju tace,

"ba Abinda tamin Amma kullum ganinta nake a firgice cikin yanayi irin na mutane marasa gsky"

Dan murmushi Hajia Aisha tayi tace,

"Ai inaga ta kasa sakewa dake ne shiyasa Amma acan bangaren mu Hira ake da ita sosai"

tabe baki Hajjaju tayi tace,

"ai shikenan tunda jinina be hadu da nata ba sai ta karata"

Dariya dukkansu sukayi kafin Daddy yyi musu sallama Akan zaidan fita, Nan dukkansu suka rakashi da Addu'a da fatan Alkahiri hade da fatan Allah ya tsare shi aduk inda yake, sosai daddy yaji dadin Addu'ar Dan haka ya fita Yana murmushi.


*****
Acan bangaren Sageer kuwa koda suka rabu da Saratu part dinsa ya koma, Yana Shiga ya fara cire kayansa Yana tuntsura dariya sbd tunowa da wayar da yyi dazu, Prof Akilu ne ya kirashi ya sanar masa duk yadda sukayi da Dr. Omar, sosai Sageer yyi farinciki at least burinsa ya cika na korar Dr. Omar a school din, Kai Gsky yaji dadin zuwan Meera skul din Dan ta kawo Masa solution mafi girma daya dauka Kan Dr. Omar, sbd murna da tsananin farinciki daya kasance ya sanarwa yaransa dole ayi gagarumin party acan boyayyen gidansa daba kowane ya sani ba, za'a gayyaci duk wani Wanda yake farinciki da hakan harda su Anty shafa sune iyayen Kan gaba a Wannan party za'asha Dj. Ayi rawa a cashe, ayi shaye-shaye da zuqe-zuqe Kai Abubuwan da suka shirya yanada yawa kwarai Kai kace Wani ne yake aure a cikinsu., Yanzun ma wanka zaiyi ya fice can zuwa gidan nasa Dan tun safe ake shirye2 yanaso yaga Abinda ke gudana, sannan sun sanar masa suna bukatar 'yar aiki shiyasa ya zabi ya tura Saratu Dan yaga tafi Kama da zubin karuwai sabanin sauran 'yan aikin gidan da suke matukar Kama kansu basa shishige Masa matukar bashi ya sasu aiki ko wani Abu ba basa nace Masa, Yana Gama cire kayan ya shige toilet dinsa hade da sakarma kansa ruwa.


~~~~~
Kallon yanayin company din yake da mmki Yana Kara duba Address din, sosai yyi mmkin meyasa sai a Wannan katon company din zasu hadu? Dan dube2 ya fara sbd yace a bakin gate zasu hadu, juyowar Nan da zaiyi ya hango shi ya fito a mota Yana takowa a hankali, kafe shi yyi da ido sbd yadda yaga yana tafiya a dake irinta zaratan maza kamar ba Wanda ya kwana biyu ba, ganin Yana tunkaro shi yasa Shidin ma ya Isa gareshi Dan su hadu, Alhaji Abdullahi da yake tafiya shima zuba Masa ido yyi Yana ganin yanayin tafiyar sa irinta jarumai masu matukar cikar haiba da mazantaka, Haduwar su yyi daidai da Mika hannun su tare Dan suyi musabaha, kowanne su murmushi ne dauke Akan fuskar sa, bisa ga mmkin Dr. Omar sai ji yyi Alhaji Abdullahi ya rungume shi kamar yadda larabawa keyi, wani irin sarawa kirjinsu yyi a tare hakan yasa suka rabu da juna suna kallon kansu, Dr. Omar ne yyi azamar furta mgn yana fadin,

"barka da Wannan lokaci Alhaji da fatan kazo lpy"

da murmushi Daddy yace,

"Omar muje office Sai muyi gaisuwar a tsanake"

yyi mgnr Yana kamo hannun sa su tafi, Omar samun kansa yyi da binsa kamar jela duk Wannan abun dake faruwa Yana daure Masa Kaine matuka musamman idan Daddy yyi Masa mgn sai yaga yyi Masa Kwarjinin da bazai iya musawa ba, haka suka Isa cikin company din, tun daga gate har izuwansu office din Alhaji Abdullahi dake can sama mutane ke zube musu Ana kwasar gaisuwa, Zuwa yanzu brain din Dr. Omar ya fara aiki ya fara fahimtar mutumin da yake tare dashi ba karamin mutum bane, yadda yaga manya da matasa ana dukawa wajen Alhaji Abdullahi yasa yaji yasha jinin jikinsa anan ya fara tunanin Toh me Alhajin ke nufi dashi ne? Daga haduwar farko? Haka kawai ya jawo shi gashi baya iya Masa musu Toh Wai meke Shirin faruwa ne?

"Bismillah zauna"

yaji Alhaji Abdullahi ya katse Masa tunanin dayake tun dazu, zama yyi a nutse sannan ya dago kansa Yana jiran me Alhaji Abdullahi zaice, ji sukayi anyi knocking manager ne ya shigo batare daya Bari an bashi izinin Shigar ba jikinsa na rawa besan da zuwan Alhaji Abdullahi ba shiyasa duk ya rude sbd yasan ya tabka barna, Kallon sa Alhaji Abdullahi yyi cikin matukar hade gira ya dawo Alhaji Abdullahin sa na Asali Wanda baya daukar raini yace,

"daga knocking sai fadowa a office na baka izinin hakan ne?"

Baki na rawa Manager Habibu yace,

"I'm so sorry sir"

Alhaji Abdullahi ya daga Masa hannu still fuskar sa a hade yace,

"abeg get outtt..."

Ko minti daya manager be Kara ba ya fece daga wajen, Tunda Alhaji Abdullahi ya fara mgnr Dr. Omar ya kafeshi da ido sosai cikin birgewa be taba ganin mutumin da yyi mgnr data ja hankalin sa ba sai Akan Alhaji Abdullahi, kwarai yaji mutumin ya birgeshi sbd shi mutum ne da baya daukar raini ko kadan, sannan yanada ka'idar da idan ka keta zaka fuskanci bacin ransa, hakan yasa yaji Alhji Abdullahi ya birgeshi sosai sbd yaga Shidin ma jarumine.

"Sorry fah kasan mutanen mu wasu sai a hankali"

yaji Alhaji Abdullahi ya katse Masa tunanin daya fada, Dan murmushi Dr. Omar yyi Kai kace ba yau dinnan aka Gama ci Masa mutunci a school ba yace,

"it's okay"

murmushi shima Alhaji Abdullahi yyi yace,

"Nasan tunda na kiraka zakayi ta tunanin wacce mgnce me muhimmancin nakeson Yi maka Koh?"

Dr. Omar ya kada Kai yace,

"hakane"

Alhaji Abdullahi yace,

"kayi hakuri da dukkan irin tambayoyin da zanyi maka shin Kana aiki ne yanzu ko karatun ake?"

Dan dukar da Kai Dr. Omar yyi yanajin wani irin Abu na taso Masa a zuciya musamman daya tuno yanzu kwata2 baya sama baya kasa, ba aikin, ba karatu, abun dai gashi Nan dai saidai bayason ya sarewa kansa gwiwa ya dago Kai dadan guntun murmushin sa yace,

"karatun nake"

ya Fadi hakan a takaice, girgiza Kai Alhaji Abdullahi yyi cikin gamsuwa yace,

"Ko wanne irin karatu kkeyi yanzu?"

Dr. Omar yace,

"Medicine nake karanta anan B.U.K"

Da fara'a sosai Alhaji Abdullahi yace,

"Kai Masha Allah, kace tare nake da babban Likita ban sani ba"

Dan guntun murmushi Dr. Omar yyi bece komai ba, Alhaji Abdullahi yace,

"sorry fah Amma kana wanne lvel ne?"

"final year saidai kuma...."

Dan shiru Dr. Omar yyi ya rasa wacce irin Amsa zai bashi, Alhaji Abdullahi yace,

"ka saki jikinka Dani Dan Allah ka gayamin gskyr ka bana nufinka da sharri sai Alkhairi"

Dan Jan zuciya yyi can kasan zuciyar sa yana mmkin ya akayi ya sake da Wannan mutumin har yake fada Masa komai Abinda ya dangance shi batare dayaji tmbyr ta gundureshi ba?

"Please saidai me?"

Alhaji Abdullahi ya sake katse shi, Dan sake dukar da kansa yyi harga Allah bazai iya duban mutumin Nan dake gabansa ya fada Masa asalin Abinda ke faruwa dashi yanzu ba, Dan haka yace,

"Nabar school din yesterday I mean yanzu bana daya daga cikin daliban skul din sbd wani dalili, Amma na rokeka Dan Allah karkace na fada maka meye dalilin"

yyi mgnr Yana hade hannayen sa biyu, binsa da kallo sosai Alhaji Abdullahi yyi, Kafin yadan sauke ajiyar zuciya sannan yace,

"it's okay kamar yadda ka bukata I won't ask you, Amma Ina jiran duk ranar da kaji ka gamsu Dani kayimin bayanin meyasa kabar skul din?"

Dr. Omar Yaja ajiyar zuciya sosai a ransa Yana Kara hango girman mutumin da baya cikin masu sa Ido da takura, Dan haka yace,

"Thanks you"

Dan murmushi Alhaji Abdullahi yyi yace,

"Then What next? I mean what is your next plan? Tunda yanzu Babu school"

Dan cije lips dinsa Dr. Omar yyi kafin yace,

"Ban yanke komai ba yanzu Amma Insha Allahu komai zai tafi daidai sbd hanyar Allah yawa gareta idan ka rasa ta wani wajen zaka samu ta wani wajen"

Cikin matukar gamsuwa Alhaji Abdullahi yace,

"Wannan zancen naka haka yake"

kafin yaci gaba da fadin,

"shin zaka iya aiki a company?"

A firgice Dr. Omar ya dago kansa Yana duban Alhaji Abdullahi da mmki, Abdullahi ya girgiza Kai yace,

"yes nasan ba field dinka bane but a yadda na tattauna dakai na Kuma fahimceka nasan zaka iya Abune me sauki cikin 1mthns

Please Login or Register in order to submit comment