Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lefe abin be wani dameta ba Dan ita gani take ko da Kaya kala daya zata zauna da Omar matukar zata kubuta daga kangin Rayuwar da take ciki na gidansu, zata huta da bala'in Mom da yaranta, a kalla zata samu 'yancin kanta tasan dai a gidan mijinta duk abinda tayi na aiki ladane sabanin gidansu ba lada ba zunubi saima zagi da ake binta dashi.

A bangaren Omar kuwa duk nacin sadeeq d yyi akan dole ayi dinner ko lunch ki yyi, duk wani Abu da zai kawowa bikin armashi fisgewa yyi, domin yasan Ba auren so zaiyi ba sbd me zai batawa kansa lkci? Auren da zaiyi na daukar fansa ne, Saiya tarwatsa Rayuwar Ameera kamar yadda furucin ta ya tarwatsa nasa Rayuwar, da ita da shegen yaron Nan Sageer, har shirya irin muguntar da zaiyi Mata yake idan sunyi aure.
8/15/20, 8:04 PM - Ummi Tandama: *YADDA ZAKI BIYA*
Zaki turo da 200 ta Wannan account din 0030202448 Nusaiba Mustapha Sterling Bank saiki turo da shaidar biya ta Wannan Number 09039118754 ko Katin MTN ta Waccar Number👆🏻


~~~Cinyarta ta kaiwa duka a razane tana mikewa d sauri sbd Jin mugun cizon da sauro yyi Mata, waige2 ta fara Yi Nan taji gidan ya sake Yi Mata shiru tsitt, hankalin tane yadan Fara tashi "Kai Anya lpy kuwa? Har yanzu be iso ba" ta Furta hakan a fili tana mikewa tsaye sbd Jin har Wai Isha tayi, dake akwai Alwala a jikinta kawai ta tada sallar ta. Bayan ta idar ne taji wata irin Hamma ta Kama ta tuni ta hangame baki tana shafa cikinta sbd Jin yadda yake Kara kamar me ulcer, Cije lips dinta tayi tana rintse ido tabbas idan zata iya tunawa yau ko kyakkyawan breakfast Bata samu ba Dan cewa akai ya Kare sai wani guntun tea na dad daya rage data gani lkcn datazo yin wanke2 ta dauka ta kurbe sbd Daren jiya bataci komai ba shiyasa Tasha sbd yunwa, dukda ranar bikinta ne yau din ba'a daga Mata kafa ba Saida tayi aikin gida, Dan numfasawa tayi data tuna tun lkcn Bata samu wani abun takai bakinta ba, Dafe kanta tayi tana nazarin Wai meke Shirin faruwa da ita ne? Tashi tayi tsaye ta fara tattaki tana Dan yawo a gidan ita kadai sai kace Aljana anan fa yunwar ta fara cin karfin ta hakan yasa ta dawo wajen zamanta tana me bude kunnen ta sosai Koda zataji Alamun zuwan Dr. Omar din, juyi ta farayi a wajen data kwanta sbd yadda taji cikin nata shima Yana juyawa yunwace taci karfinta sosai Kai kace zata sheka, a garin juyin nata ta tabo wani Abu me Dan dumi a gefen ta, abinka Dame Jin yunwa zumbur ta Mike tana karewa inda ta taba kallo, "Oh! Ya Salam" Meera ta Furta tana dafe goshi Ledar da Dr. Sadeeq ya Bata ne dazu Akan Omar Idan yazo ta bashi, jawota tayi tace "Bari dai Naga meye a ciki" tana budewa kuwa taga gasassar kaza da fresh milk a ciki sai tashin kamshi take Tasha Hadi, wani irin tsinkewa yawunta yyi Habawa batare da tunanin komai ba hannun ta na rawa ta fisgo Naman tana Bismillah ta afka bakinta, cin Naman take bana Wasa ba tare da kurbar fresh milk, Saida ta kusa cinye fiye da Rabin tsagin kazar kafin ta hakura daci Dan ta koshi, rufe murfin fresh milk din tayi shima kafin taja gefe tana gyatsa hade da hamdala, Wata irin nutsuwa ce ta saukar Mata, sai yanzu tunanin ta ya dawo daidai yyinda gumi ya jike Mata jiki jalab, kallon Naman tayi sai take taji tsoro ya Kama ta, yanzu idan Omar yazo me zatace Masa? Gashi da alama shi kadai zaici tunda komai guda daya ne a gurin, lumshe ido tayi a fili tace, "nayi Masa bayani nasan zai fahimta" da hakan ta sake gyara zamanta tana Dan kishingida sbd yadda taji iskar wajen tana kadawa a hankali, Wasa2 shirun Dr. Omar ya zarta tunanin Meera, kallon Nokia dinta tayi taga 12am Dan har Dan bcci ne ya sureta ta farka a firgice dalilin cizon da wani sauro yyi Mata, koda taga 12am hankalin ta ba karamin sake tashi yyi ba, ba Abinda takeji sai kukan tsuntsaye da haushin karnukan unguwar, Tsoro ne ya Kama ta ainun ta waiga jikin kofar parlon still tana Nan a garkame, "Na Shiga uku kodai Sadeeq mistake yyi banan bane gidan?" Ta Furta hakan a tsorace tana Dan waige2 duk jikinta rawa yake sbd haushin karnukan da suka cika Mata kunnuwa, gaba1 Meera ta rude ba Mafita Dan Haka kawai ta bude akwatin ta Nan ta dauko mayafin ta na kwanciya shima tun na mamanta ne Bata rabuwa dashi Dan Yana tuna Mata mamanta, zama tayi ta fara karanto Addu'ar bcci Dan ta sare da zuwan Omar tana tunanin dole Asubar fari tabar gidan Dan d alama anyi mistake wajen kawota, Saida ta Gama Addu'o'in ta kafin ta tofa gabas da yamma kudu da arewa sanna ta shafe jikinta, duk Wannan abubuna tanayi ne a tsorace yafa mayafin tayi har kanta kafin ta rintse idonta sosai Dan har yanzu jikinta rawa yake sbd tsoro, kafin wani lkci dake dama ba ishashe bcci take samu ba kwanakin Nan tuni bccin yyi awon gaba da ita.
Acan bangaren Dr. Omar kuwa, tunda ya sanarwa Saratu shi bikinsa Babu bidi'a ba wani taro ya dinga Shan Gori da miyagun maganganu, Shidai Abba besan dalilin dayasa Omar yace bayason taro ba sai kace bikin dole dukda Abba baya mgn harda shi akaje daurin auren besan meyasa ba Amma tabbas yyi farinciki da Wannan auren na Omar sosai, a wajen Saratu kuwa cewa take dama tunda kayo gadon talauci yaushe zakaso ayi Taron biki? Da alama yarinyar da zaka aura ma duk kanwar ja ce Banda Haka wacce cikakkiyar budurwar ce zata yadda da biki ba taro kamar bikin mujiya? Shiru Dr. Omar yyi Mata be tanka ba sbd duk yadda Saratu take kushe auren nasa jinsa yake ko a kwalar rigar sa Dan shi kadai yasan wanne irin aure yyi, shirun da yake shi yake karawa Saratu kaimin ci gaba da surfa bala'in ta tace Arziki na binka kana tirjewa Ka mannewa auren da babu riba. Jefar da wayarsa Dr. Omar yyi lkcn da suka Gama Waya da Dr. Sadeeq Akan yakai Meera gidansa, Dan Jan tsaki yyi yana me fitowa a dakinsa Dan yin Alwala sbd Jin Kiran Sallah da yyi, be dawo gidan ba sai Bayan yyi sallar Isha, Koda yazo gidan ma zama yyi wajen Abba, Abba Babu bakin mgn bare ya tmbyeshi yaushe za'a Kai amaryar tasa? Dan ya sanarwa Abba ya Kama haya sbd har yanzu be sanarwa Abba dukkan halin da yake ciki ba daga korar sa a skul har zuwa company din Alhaji Abdullahi, Rike hannun sa Abba yyi Yana Dan jijjigawa hade dayi Masa mgnr kurame da hannu, Dr. Omar dake kallon sa ya gane me yake nufi Sarai, shi duk bayajin dadin Wannan zumudin auren da Abba yakeyi sbd ba auren So yyi ba, Kuma ba wani me lasting bane za'a rabu, Toh Amma ya ya 'iya? Haka dai kamar kullum ya danyi murmushi Yana duban Abba yace, "Sai zuwa gobe za'a kaita" yyi mgnr Yana kawar da idonsa da sauri sbd bayason Abba ya gano Gskyr, binsa da kallo Abba yyi kamar be gamsu da mgnr Omar din ba Dan Haka da mmki ya juyo d fuskar Omar din gareshi yyi Masa Alama da hannu Meya faru? Daidaita yanayin sa Dr. Omar yyi cikin dakiya sosai kamar gske yace, "Eh Abba sai gobe sukace zasu kawota I thought ma yau ne sbd ni dasu din duk ba wani bidi'a akai a bikin ba" girgiza Kai Abba yyi cikin gamsuwa Amma a ransa yanaso yyiwa Omar din mgn ne aure ko a kauye ai Ana shagali bare shi auren birni cikakken Dan boko gashi Dan gayu, saidai ya bar hakan a Matsayin kowa da ra'ayin sa kila shi Kuma nasa ra'ayin kenan, Omar ne ya katse shi da fadin, "Bari na Shiga ciki Abba" ya Furta hakan Yana mikewa tsaye, Saratu data fito daga bayi taja tsaki da karfi tace, "aikin kenan Haka za'a Kare dakai da dangin amarya kowa ba kwabo Tunda ka Musa zabina aurenka bazaiyi Albarka ba" ko kala Dr. Omar bece Mata ba ya wuce ciki abinsa a ransa Fadi yake Toh dama wanne Albarka za'a nema a auren daya zama na wucin gadi? Balle botir din rigar sa yyi ya zame ta kasa sannan ya cire dogon wandon sa, karowa fankar sa gudu yyi kafin ya zauna gefen katifar sa, Yana bude wayarsa yaga misscall din Sadeeq kusan 5, Dan tsaki yyi ya maida wayar gefe Dan yasan dalilin Kiran nasa yanzu zai fara Masa wa'azi be kamata ya zauna yabar 'yar mutane acan ba, dauko system dinsa yyi ya kunna yana me duba ayyukan dazai gabatar a company zuwa gobe Dan ko a company din ma ba'asan yyi aure ba, Shidai auren gashin Nan dai saikace na magulmata, Saida ya Gama nazarin Abinda yakeyi kafin ya tashi yayo wanka, Bayan ya Gama Shirin bccin sa ya dauko heater ya dumama ruwan zafi sharp2 ya hadawa kansa coffee ya kurbe, Bayan ya Gama yyi kwanciyar sa batare da tunanin komai ba, Yana rintse ido kuwa yaga fuskar ta ta bayyana a gareshi lkcn data zabga Masa Mari, cikin kunar zuciya Yaja wani irin mugun tsaki me yaji2 kafin ya sake juyawa dayan barin, Addu'a yyi ya shafa sannan ya rufe Ido ko takan tunanin halin da take ciki beyi ba Kawai bcci yyi awon gaba dashi. A bangaren Ameera kuwa bccin Nan nata rabi da rabi tayi sbd cizon sauron dake damunta, har kwallar takaici Saida tayi sbd cizon d suke Mata gashi haushin karnukan d ake kamar a cikin gidan suke sbd ihu, a daddafe dai taje Asuba a Haka, Wannan ruwan famfo shiya taimaka Mata tayi tsarki da Alwala, Bayan ta idar Bata Dade ba kuwa ta bingere da bcci sbd Rashin samun yinsa a Daren jiya. Shi kuwa Dr. Omar sai 9am ya Gama Shiri cikin Shigar kananan Kaya sunyi matukar Yi Masa kyau dama Shidin ma gwanin kyau ne, laptop dinsa ya dauka zai fito a daki kenan yaga Kiran Dr. Sadeeq, dauka yyi da sallama, Dr. Sadeeq yace, "ah lalle ango kasha kamshi ai tunda na Kira jiya naji shiru nasan cewa Ana tare da madam" ya Furta hakan cikin tsokana Yana dariya, tsaki Dr. Omar yyi yace, "zaka fara iskancin naka Koh?" Dr. Sadeeq Yana dariya yace, "oh Iskanci? Dani dakai waye Dan iskan?" Sake Jan tsaki sosai Dr. Omar yyi kamar zai tsinkewa Dr. Sadeeq kunne sbd ya fahimci inda ya dosa cikin kufula yace, "Amma ka cuceni banza" dariya sosai Dr. Sadeeq yyi yace, "so how far? Ya madam?" Dr. Omar be Amsa Masa ba shima yace, "so ya Shirin exam? Kasan yau zaku Fara" sassauta dariyar sa Dr. Sadeeq yyi yanajin wani irin tausayin Omar din a ransa sun taso tare, burinsu tun suna secondary su zama manyan Doctors yau gashi dalili yasa ya zama GM a company, Dr. Omar ne ya katse Masa Shirun da fadin, "Okay sai kun fito Allah ya bada sa'a" yyi mgnr Yana kashe wayar sbd yadda yakejin wani iri shima, kasa cewa komai Dr. Sadeeq din yyi shiyasa yanaji Yana gani ya yanke wayar, dafe goshin sa yyi Yana Kara Jin tausayin Omar din dukda yasan zuwa yanzu Kam Omar ba abin tausayi bane Allah ya daga darajar sa.
Shikuwa Dr. Omar Aljihu ya maida wayar Yana me bude dakinsa ya fito, lkcn daya fito Saratu harta bar gidan sai Sahabatu yau da Bata fita ba tana kwance lamo a barandar su, Dan kallon ta yyi a kaikaice kamar zai wuce sai Kuma ya fasa da mmki yake binta d kallo yasan dai tunda yarinyar Nan ta budi Ido a sana'a Bata cika zaman gida ba sai zaman Tasha Ana Saida abinci Idan ta dawo gida kuwa wani abincin zatayi Koh bcci, yau kuwa tunda aka ganta a gida har Wannan lkcn da dalili, matsawa yyi jikin rumfar yace, "ke lpy?" Yyi mgnr fuskar sa a hade, Banza tayi Masa batayi mgn ba, ransa ne ya baci sosai cikin tsawa yace, "ke ba mgn nake Miki ba?" Dagowa tayi ta kalleshi cikin tsiwa tace, "Wai ba Ummah ta Hana kamin mgn ba?" Kallon ta yyi shaye da mmki zaiyi mgn kenan yaji an kamo hannun sa ta baya juyowa yyi yaga Abba daga Masa hannu yyi Alamar ya kyaleta, sake juyawa Dr. Omar yyi still mmki bebar shi ba, sai Kare Mata kallo yake, ganin irin kallon da yake binta dashi yasa Sahabatu tayi saurin kauda idonta gefe tana juya musu baya. Sai a lkcn Omar ya kalli Abba, Dan risinawa yyi yace, "barka da safiya Abba da fatan ka tashi lpy" Girgiza Kai Abba yyi Yana murmushi, Dan murmushin Omar yyi kafin yace, "toh zamu fita asa Mana Albarka" kallon mmki Abba yyi Masa a ranar auren ma sai anje aiki? cikin sauri Dr. Omar ya katse Abba Dan ya fahimci inda Abba ya dosa Dan Haka yace, "exam zamuyi Dan Haka ba wani dadewa zamuyi ba asa Mana Albarka" Dan murmushi Abba yyi Yana girgiza Masa kansa, anan dai yyiwa Abba sallama ya tafi. Saida ya fito bakin titi kafin ya tare me napep hade dayi Masa kwatancen gidan sa Dan acan ma motar sa take.
Bayan me napep ya sauke shi ne ya bude gate din gidan, shigowa yyi Yana karewa gidan kallo kamar yau ya fara Shiga, da mmki yake kallon can jikin kofar parlo mutum a kwance an rufe har Kai, Dafe goshin sa yyi sbd tunowa da Meera an kawo ta jiya take haushinta ya dawo Masa, da saurin sa ya Isa Kan barandar ya Rasa dame zai tasheta kawai yasa kafa ya shureta, a figirce Meera ta tashi tana waige2 zaton ma Koh karnukan ne suka hauro gidan, Kanta na kasa ta fara bin sawun takalmin data gani tsaye a gabanta da kallo, a hankali take binsa da kallo tun daga kasa har izuwa can sama, ja baya tayi da sauri tana binsa da kallon mmki, Hade ransa yyi sosai fuskar sa Babu Alamar fara'a a tattare dashi, Wani irin bugawa kirjin Meera yyi sbd yadda taga Yana binta da wani irin matsiyacin kallo, bakinta na rawa Tace, "sa.s..sannu da zuwa barka da safiya" ta Fadi hakan a jere, cikin tsawa yace, "sbd samun waje irin naki har kikai Wannan lkcn kina bcci? Wacce irin malalaciya ce ke?" Darammm, kirjin Meera ya sake bugawa da karfi, hakan yasa ta Mike tsaye tana ja da baya tace, "kodai baka gane ni bane? Ameera ce fah wacce ka Aureta Jiya" wani irin kallon banza yyi Mata Yana sake matsowa inda take yace, "aure?" Girgiza Kai Meera tayi tana kallon sa, Dan ja da baya yyi Yana meyin wani irin tattaki kafin ya dago ya kalleta yace, kinyiwa abin gurguwar fahimta" a tsorace Meera tace, "me kke nufi?" Dr. Omar yace, "me kuwa nake nufi? Dake duk a tunanin ki sai ki Sami namji kamar ni ya aureki? Tatsitsiya dake na aureki ko na Raine ki???" Ya Furta hakan Yana wara Mata manyan idanun sa kanta, zaro nata manyan idanun tayi tana dubansa da mugun mmki, Ci gaba da mgn yyi yace, Koda yake, yes Aurenki nayi Amma bawai irin auren da Kika Saba ji anayi ba, Kai tsaye Zaki iya Kiran auren da auren daukar fansa" zaro ido sosai Meera tayi tace, "me nayi maka da zaka dauki fansa a Kaina?" Ta Fadi hakan bakinta na rawa, "Me kikayi min kike tmby?" Ya Furta hakan da karfi har Saida Meera ta firgita da karar, kasa cewa komai tayi saima sake matsawa can gefe da tayi, Dr. Omar yace, "keda shegen munafukin naki Sageer duk saina koya muku hankali" "Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un" Meera ta Furta hankalin ta na tashi a rikice ta kalli Dr. Omar tace, "Wlhi ba Abinda kke tunani bane, ni Babu ruwana dashi ban sanshi ba, Dan Allah kayi hakuri nayi maka bayanin dalilin dayasa na bada shaida a kanka ranar" wani irin takaicin ta ne ya sake Kama shi, Wai yyi hakuri tayi Masa bayani? Cikin zafin Rai yace, "wannen irin bayani zakiyi min Bayan kin Gama tozarta ni a idon duniya? Me zakice min Bayan kin Gama wargaza min lissafi? Dana San taimakon ki Abinda zai jawo min kenan da tun wuri ban Kai Miki taimako ba..." Meera ce ta katse shi da fadin, "cewa fa yyi...." "Shut up.." Dr. Omar shima ya katseta da tsawa Dan bayajin zai iya tsayawa ya saurari dukkan karerayin ta, Kame bakinta Meera tayi jikinta na rawa, kallon yanayin gidan Dr. Omar yyi yace, "Kinga Nan? Ya nuna Mata farfajiyar girgiza Kai Meera tayi, yace, "Good kisa a ranki kamar Aikatau kikazo Yi gidan Nan idan d kinada hankali ma tun jiya ya kamata ki fara tunanin bakida da wata daraja a idon Wanda Kika aura, Dan Haka ki sani a kullum ta Allah inason Naga field dinnan a share Tass ko kwayar ganyen bishiya bana bukatar gani" bin farfajiyar gidan Meera tayi da kallo hankalin ta a mugun tashe ta dawo da kallon ta Kan Omar taga ya bude kofar parlo, Parlon ba lefi dadan girman sa me dauke da dakuna biyu acan sama da wasu a kasa, "Keee.." ya Furtawa Meera hakan, Meera tace, "Na'am" ta Furta a tsorace Dan ita yanzu gaba1 ma Dr. Omar din tsoro ya fara Bata, Nuna Mata sama da kasa yyi duk Kura sbd be fara using da gidan ba yace, "inaso kafin na dawo ki Tabbatar kin share kinyi mopping idan na dawo na tarar baki gyara ba Zaki fuskanci mummunan hukunci" daga Kai Meera tayi Bata Amsa ba, "Bakyaji ne?" Ya Furta hakan da tsawa a firgice Meera tace, "inaji" Tsaki Yaja me sauti yace, "Toh banason Ana Amsa min da jiki furuci nakeso Understand?" "Yes" Meera ta Furta itama, "Good Dr. Omar ya Furta Yana zube Mata keys din Kan kujera batare daya kalleta ba yace, "your time start Now matukar na dawo na samu ba yadda nace ba you will be in trouble" "Toh" Meera ta Furta, Tsaki yyi ya fice daga parlon Koh sake waiwayen ta beyi ba Yaja motarsa ya fice a gidan Bayan ya janyo gate ya rufe ta ta waje. "Hasbunallahi wani'imal wakil, A'uzubika limatullahi tammat min sharri makalaq..." Abinda Meera ta dinga Furta kenan tana maimaitawa a ranta hade da bin Dr. Omar din da kallo cikin tsoro da firgici "Yau wacce irin rayuwa nake Shirin fuskanta ni marainiyar Allah Ameera??" Ta furta hakan a fili hade da fashewa da kuka.



*Sorry Rashin caji yasa jiya kuka jini shiru*
8/15/20, 8:04 PM - Ummi Tandama: *YADDA ZAKI BIYA*

Zaki turo da 200 ta Wannan Account din 0030202448 Nusaiba Mustapha Sterling Bank saiki turo da shaidar biya ta Wannan Number 09039118754 ko Katin MTN ta waccar number👆🏻



Saida tayi kukanta me isarta kafin ta share hawayen ta cikin Jan zuciya ta fara bin yanayin parlon da kallo, duk wani tunani nata ya kunce Bata da wani zabi a yanzu sama da tayi Abinda yace din, Haka dai jiki ba kwari ta Kama stairs Dan haurawa sama Bayan ta kwaso duk wasu kayan aiki data gani daga can gefen parlon kamar dama Dan ita aka ajiye, tana share kwalla Haka ta Isa gaban dakunan biyu, budesu tayi duka taga duk sunyi kura ba komai a ciki Dan ko furnitures Babu, Haka ta bude toilet din ciki ta cika shi da ruwa kafin ta dawo daki ta fara sharewa, kafin wani lkci harta Gama sharar abinka da an riga an Saba tun a gida, Bayan ta Gama ne ta fara mopping gashi tiles din fari Kal tun daga na toilet har na dakunan na corridor ne ma yadan banbanta, da nishi da komai Haka ta Gama gyaran saman gaba1 harta gangaro izuwa matattalaka ta karshe dake kasa, hatta gefe d gefen matattakalar Suma ta goge, Bayan ta Gama ta rike qugunta cikin wani irin yanayi na wahala sake duba girman Parlon tayi Nan taga lalle fa akwai sauran aiki a gabanta Dan Haka ta daure taci gaba da aikinta tana me Jan zuciya har yanzu.*****
Shigowar Saratu gidan Alhaji Abdullahi kenan ta hango Sageer da Hajjaju a tsaye d alama surfa Masa bala'i take, Karasawa tayi wajen tace, "barkanku da safiya" tayi mgnr tana Dan tsayawa Dan son Jin Akan me suke mgn, ko kallon inda take basuyi ba saima ci gaba da mgn da Hajjaju tayi tace, "Kai sageeru badakai nake ba?" Sageer cikin Rashin kunya yace, "nifa Hajjaju kin fara kaini bango Taya za'ai komai nayi kice banyi daidai ba? Yanzu Shigar Nan tawa ko a birnin London Wlh takai" cikin jin haushi Hajjaju tace, "Bantan ubanka, nace kaci Bantan ubanka kaji Koh? Yanzu ka dubi Shigar Nan taka wando Koh gwiwa be Kai ba wuya nannade da sarkoki sai kace jikan Dan bori Koh Kuma Karen kiwon makwabtan mu..." "habaaa Hajjaju" Sageer ya katse ta Yana saka hannayen sa cikin bujen wandon sa yace, "idan kikace jikan 'yan bori Toh ya tabbata kece dai borin Dan tanan na biyo" tafa hannu Hajjaju tayi hade da salati tace, "nice 'yar borin?" "Atho? Haka dai kikace sa'idawa" ya fada Yana juyawa, juyowar da zaiyi yaga Daddy tsaye bayansa ba tare daya tantance komai ba yaji an dauke shi da Mari, Wannan Marin ya jawo hankalin Saratu kansu Dan duk Basu San da zuwan daddy ba Ada kawai ta tsaya tana dariya ne ta ciki sbd Abinda takeso Sageer keyi wato ya daina ragawa Hajjaju Dan ta cika takura da sa Ido wani abin ma idan ta yunkura zatayi a gidan idan ta tuno da tsohuwar Nan tsoron Yi take.., "Ashe Rashin hankalin naka yakai Nan Sageer ban sani ba?" Daddy ya katse shirun da mgn cikin fada, dafe kumatun sa Sageer yyi Yana huci kamar zai fashe, kamar daga sama tsugul Saratu ta tsoma baki da fadin, "Dan Allah ayi hakuri Alhaji yarinta ne watarana idan ance yyi bazaiyi....." "Dallah kauce" Hajjaju ta katse ta hade da ture ta can gefe saiga Saratu a kasa Tim bin Hajjaju tayi da sauri ganin yadda taji ta sa Mata Kashi, Hajjaju taci gaba da fadin, "munafukar Allah Ina lura dake tunda kikazo Nan kinajin dan banzan yaron Nan yanata zazzaga min Rashin kunya baki dakatar dashi ba sai yanzu shi da ake Masa fada zakice a daina? Kewai meye hadinki da shi ne? Dan na lura kullum akayi Masa fada ranki bayaso" A mugun tsorace Saratu tace, "kiyi hakuri Hajjaju dazun ma Ina Shirin Yi Masa mgn Alhaji yazo" daddy ya katse zancen da fadin, "maza jeka ka canza Shigar Nan idan ba so kke ranka yyi mugun baci ba" juyawa Sageer yyi cikin fushi kamar zai bangaje daddy ya wuce su ko waiwaye bayayi, "ai ka gani koh?" Hajjaju Tayi mgnr tana kallon Alhaji Abdullahi daya bi Sageer da mmki, Hajjaju tace, "bana tunanin Wannan yaron yanada cikakken hankali, Kai nifa hankali na yafi karkata Anya yaron Nan jininmu ne?" A firgice suka maida kallon nasu wajenta, daidai lkcn Safna ta karaso wajen Dan fita zasuyi da daddy zai nuna Mata sabon GM din company dinsa Dan yadda sukeji yabon da daddy yake Masa yasa Safna tace itakam bazata jira sai an kawo shi ba zataje can ta ganewa idonta, Hajjaju ce tace, "Toh meye duk kun wani zubamin Ido? Abinda zuciyata ke rayamin na fada" tayi mgnr tana juyawa Dan barin wajen, Safna na ganin Haka itama taja hannun daddy suka bar wajen ya rage sai Saratu datayi suman zaune, hankalin ta ba karamin tashi yyi dajin furucin Hajjaju ba Anya zata Bari Wannan matar takai lbri kuwa? Domin a hankali dai gashi nema take ta nusar da mutanen data rufe musu Ido zuwa Kan Abinda ta birne shekara da shekaru, Ganin kamar ta fara janyowa kanta kallo agun sauran ma'aikatan gidan yasa kawai ta Mike tana kade zanin ta Nan ta nufi part din Hajia Aisha zuciyar ta na wasu

Please Login or Register in order to submit comment