Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaisuwa, Alhji Kabir yace, "yanzun Nan nake mgnr ku nace jiya bamuyi exchanging numbers ba" Sadeeq yace, "hakane shiyasa ma mukayi sauri kafin ku fita" Alhji Kabir yace, "Shikenan ku biyo mu muje" Nan sukabi bayansa Yana gaba. Ahmad dake leke ta window ne ya zame a hankali zuciyar sa na harbawa da sauri2, jiya kusan kwana yyi Yana juyi Sam ya kasa yadda da Wai Ameera Tanada aure, yarinyar data sace Masa zuciya tun a karon farko daya ganta gsky batayi Masa Kama dame aure ba Sam, ya Dade Yana wannan tunanin Yana sane ya kulle parlon sa hade da kashe wutar dakinsa jiya kawai Dan kada a dameshi, yanzun ma damuwar ce ta sashi tsayuwa gaban window Yana leke tunda ya hango su Omar kirjinsa ya buga da karfi especially daya gane Omar din lkcn dayake Kiran Meera jiya, rintse idonsa yyi ya koma bakin gado ya zauna hade da dafe kansa. Zamansu keda wuya aka fara kawo musu abin Kari, Alhji Kabir ya dubesu bayan an gama aje musu komai yace, "kuyi breakfast zanje na shirya kafin muzo ayi mgn" gyada Masa Kai sukayi shikuma ya fice waje, Yana fita kuwa Omar ya maida bayansa Yana lumshe Ido, zamowa Sadeeq yyi ya hada tea cup biyu ya dubi Omar da idonsa ke rufe yace, "ya kamata ka rage Wannan damuwar Omar kasan Abinda hakan ke haifarwa ga lpyr mutum" bude idonsa Omar yyi yace, "sadeeq kenan Kaima kasan a tsakankanin kwanakin Nan Ina haduwa da Abubuwane kala2 da farko Rashin sanin Asalina, ga Kuma bacewar Meera ya kke tunanin zan dau lamarin? Na tabbata da wani ne Wlh sai zuciyar sa ta buga sbd dawanne zaiji? Zafi bisa zafi lkci guda?" Sauke numfashi Sadeeq yyi sai yanzu ya lura Ashe har wata 'yar rama Omar din yyi lalle abun ba sauki danma omar din jarumi ne ya iya dauke duk wannan kaddarar data Fado Masa lokaci guda, cikin matukar tausayin sa yace, "Kayi hakuri komai zai zama normal Insha Allah" Dan guntun murmushi yyi kafin yace, "Haka nake fata" Mika Masa cup din yyi yace, "karbi ko kadan ne kasha tunda kaki Bari muyi breakfast acan" karba Omar din yyi ya fara Sha a hankali, ko Rabin cup din beyi ba yaji tea din ya gundure shi hakan yasa shi ajiyewa, shima Sadeeq din be wani Sha sosai ba ya aje Dan shimafa kusan acikin damuwar yake, Suna zaune Haka dad da Alhji Kabir suka shigo, gaishe da dad sukayi har kasa ya Amsa musu da sakin fuska hakan yasa Sukaji Dadi matuka, zaman su dad keda wuya Inna fure d Meera suka shigo, Dagowa Omar yyi da sauri Yana karewa Meera kallo yadda take ta dukar da kanta tana rabewa Bayan Inna fure, ita kuwa Inna fure fuskar Tace a hade dakyar ma su dad suka lallabata tazo akan kawai anaso aji ta bakin yaran kowa yasan Matsayin sa, zama tayi su Omar suka sake zamowa har kasa Suna kwasar gaisuwa kamar bazata Amsa musu ba sai Kuma ta juyo ta Amsa gaisuwar tasu, zamansu kawai sukai a kasa Basu koma kan kujerar ba, Alhji Kabir yace, "toh madallah, dama Abinda yasa nace kowa yazo Nan shine inaso naji dalilin dayasa shi Omar din ya nemi auren Ameera Alhalin baya sonta" shiru Omar yyi Yana dukar da kansa Sam bayason yaji ance baya sonta, Sadeeq ne yyi gyaran murya kafin yace, "idan ban Shiga tsakani ba ko za'a bani Wannan damar na Amsa tmbyr da aka Masa?" Alhji Kabir yace, "eh Babu damuwa ai Amsa mukeso" Sadeeq yace, "Nagode" Nan ya gyara zaman sa yace, "harga Allah a farkon auren da frnd Dina yyi da Ameera ba komai bane a ciki Banda daukar fansa" "fansa??" Duka suka Furta hakan da mmki, shi kuwa Omar kansa na kasa be dago ba, Sadeeq yace, "kwarai kuwa, dalilin Wannan fansar kuwa shine...." Tiryan-tiryan ya fara Basu lbrn yadda abubuwa suka faru tun daga lkcn da Omar yazo ceton Meera da Sageer yaso Yi mata fyade da Kuma son kwatar mata 'yan dayaso Yi a kotu....karshe ya karkare mgnr da fadin..."a maimakon Ameera ta bada shaidar gsky ta Fadi Wanda yaso rusa mata mutuncin ta shine ta maida mgnr akan Omar inda ya jawo Masa zubewar mutuncinsa a idon jama'a dama dukkan 'yan skul dinmu, Cikakken Likita ne shi me Jiran license dinsa a satin zamu Fara zana final exam dinmu Amma sanadiyar shaidar da Meera ta bayar hakan ya jawo Kora daga faculty dinmu shima duk a cikin plan din Sageer ne a takaice dai komai ya lalace game da Omar duk a sanadin furucin Meera shiyasa yyi auren fansa a kanta a ganinsa hakan shi zai rage Masa radadin Abinda tayi Masa....." shiru parlon ya dauka har Ahmad dake jikin window a labe Saida ya girgiza da Wannan lbrin, Inna fure kuwa Kamar wacce ruwa ya cinye ta Tama kasa Dagowa ta kalli Omar din, dad Kam kunyace ta Kama shi kwarai Haka zalika Alhji Kabir duk sunyi tsumu2, Meera kuwa a hankali ta rabe can gefen kujera jikinta na Bari duk Kuma Omar na kallon ta ta Wutsiyar Ido shima kansa a duke, gwauron Numfashi Alhji Kabir Yaja kafin ya dubi bangaren Ameera yace, "duk Abinda ya fada hakane?" A tsorace Meera Tace, "eh Abba" _Hasbunallahi wani'imal wakil_ Suka Furta hakan a ransu shikenan Kuma me zasu ce da Omar? Cikin fada dad yaso Yi mata mgn Alhji Kabir ya dakatar dashi, kafin a kunyace yace, "Omar shine dalilin aurenka da Meera?" Omar ya girgiza Kai be dago ba, Numfashi Alhji Kabir Yaja toh duk idea ta kwance Meera ai ta kunce musu zani a kasuwa, saidai a hankali ya dubi meeran da jikinta keta rawa Yana Dan kausasa muryar sa yace, "Ameera mutumin dayaso kwatar Miki 'yancin ki irin sakayyar da Zaki Masa kenan?" Girgiza Kai Meera tayi hawaye na cika mata Ido, a tsawace dad yace, "Amma meyasa Kika bada Wannan shaidar?" A rude Meera ta fashe da kuka hade da fadin, "kashe shi zaiyi dad, Wlh kashe shi zasuyi da idona Naga Bindigar" ta karasa mgnr hade da kifa kanta jikin hannun kujera dama a kasan carpet take, wani shirun ne ya sake game parlon yyinda Dr. Omar ya dago a firgice Yana binta da kallo, a nutse Alhji Kabir yace, "bamu gane kashe shi zasuyi ba, su waye? ki Mana bayanin yadda zamu fahimta." Bakin Meera na rawa Tace, "Sa...Sageer da su Anty shafa" Nan ta fara Basu lbrn yadda suka tsoratar da ita Akan matukar Bata bada Wannan shaidar ba saisun kashe shi,...ta karkare zancen da fadin, "ni Kuma Banda wata idea dazan ceci ya Omar daga hannu azzaluman Nan, Banda number sa Kuma lkcn da muka hadu kafin a Shiga kotu idan zai tuna Saida nace Masa inada mgn ya dakatar Dani da fadin dole sai an fito daga shari'a kafin nace komai, be Barni nayi mgn ba shiyasa tunani na ya sake kwancewa a cikin Kotun ma Saida na hango Bindigar a satin bayan Omar mutumin daya zauna a bayansa dauke yake da ita hakan ya Tabbatar min d lalle zasu iya Abinda sukace, bani da wani zabi ne domin tseratar da Rayuwar sa na zabi kare shi ta Wannan shedar bansan Abinda zai juye ba kenan w....l...h...." Ta Ida mgnr a rarrabe sbd yadda kuka yaci karfin ta.


*Littafin na kudi ne, 200 Zaki turo account din Nan 0030202448 Nusaiba Mustapha Sterling Bank saiki turo da shaidar biya ta Wannan Number 09039118754 ko Katin MTN ta waccar number👆🏻*
8/22/20, 8:44 PM - Ummi Tandama: Nan parlon ya sake yin shiru Banda kukan Meera ba Abinda akeji, ba Kamar bangaren Omar daya daskare a wajen idonsa Akan Meera Yana mata wani irin kallo Wanda ya banbanta da duk wani irin kallo daya taba Yi mata a baya, Wannan kallon da yake mata kallo ne dayake haskowa daga can Fadar zuciyar sa, a take ya dinga Jin wasu irin kibiyar so da kaunar Meera na rige-rigen dira a hadaddiyar Fadar zuciyar sa, yanzu ne asalin zuciya da gangar jikinsa suke yiwa Meera kallon kauna badan ya kwashi Ni'ima a jikinta ba, jinta yake har cikin bargo da jijiya, tausayinta da Kuma zazzafar kaunar ta na safara a dukkanin magudanar jininsa, ya kasa daina kallon ta domin ya manta da wasu a wajen...Abban Ahmad ne yyi gyaran murya kafin yace, "tabbas mgnr Ibrahim Haka take akwai Rashin fahimta a tsakanin su duka biyun a kowanne bangare kowa yanada laifi mgnr gsky ko waye akace anyi sanadin barinsa karatu Yana matakin karshe na gamawa bazaiji Dadi ba especially medicine dinnan da a Nigeria ba karamin cin kwakwa suke ba yajin aiki da duk Abubuwan su Yana Jan su lkci me tsawo kafin ka kammala, Suna Shan gwagwarmayar rayuwa kafin su kawo Wannan stage din na matakin karshe, kaii dolene ma mutum yaji haushi Toh Amma inda matsalar take Dr. Omar beyi dogon bincike ba kafin ya yanke hukunci akan Ameera, Haka zalika Ameera shaidar data bayar tayi wauta kwarai dgske ba lalle saita Amsa hakan ba da ace tayi dogon tunani da tun a lkcn tayi hanzarin sanar dashi Koda ace yaki sauraranta ko Kuma take ta nuna mutumin dake rike da gun a Kotun gsky tayi kuruciya sosai" gyada Kai dukansu sukayi Banda Omar da har yanzu keta kallon Meera Sam besan ma me suke tattaunawa akai ba, dubansa Abba yyi yaga dai kamar baya tare dasu hakan yasa ya dubi dad, mgn sukayi kasa2 kafin Abba ya dubi Inna fure da duk tausayin yaran biyun ya kamata yace, "Mama tunda abin nasu yazo da Haka to sasanci Yana a tsakanin su saidai mu matsa dan Basu waje" kafin ma ya Ida mgnr Inna fure ta Mike zuciyar ta na fatan ace sun shirya, mikewa su dad sukayi suka fice Sadeeq dayaga Omar din har yanzu Yana wata duniyar yadan zungure shi, firgigit ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi Yana waigen Sadeeq bakinsa na rawa be Furta Masa komai ba yyi Kan Meera da take share hawaye, ganin hakan yasa shima Sadeeq din ya fice, Tashi Omar yyi ya matsa gaban Meera a hankali, Zama yyi dab da ita zuwa lkcn Meera Jan zuciyar d take ya ragu sai zuciyar ta dake harbawa da sauri duk tanajin motsin sa kusa da ita, dago hannu yyi zai jawota jikinsa ya kasa ya gwada hakan kusan sau uku Ana hudun ne ya samu kwarin gwiwar jawota jikinsa zuwa saman faffadan kirjinsa ya rungume ta tsam take kuwa suka sauke ajiyar zuciya a tare, habarsa na bisa Kan lallausan dogon gashinta sbd rolling din da tayi ya warware Yana shakar kamshin man kitson data saka sunyi kusan 5secs a Haka kafin a hankali yace, "i'm sorry Meeraaa.." ya Fadi sunan Yana Jan shi a hankali, har cikin ranta taji sunan nata Amma dai ta maze ta dago daga rungumar da yyi mata tana kallon kwayar idonsa da suke a lumshe Tace, "nice ya dace na baka hakuri sbd nayi maka asarar Rasa karatun ka daka Dade kana fama akai Kuma..." "Shiiiii...." yasa yatsan sa daya akan tattausan lips dinta yace, "it's okay Meera mu manta baya kawai" riko yatsan nasa tayi hakan yasa ya zuba mata Ido sosai, Dan sauke numfashi tayi kafin Tace, "dole ne na baka hakuri ya Omar domin kaidin na daban ne I mean ba kowane zai iya daukar Wannan abun daya same ka ba ka godewa Allah kanada kwarin zuciya" Dan murmushi yyi kafin yace, "shiyasa nace mu manta baya Meera kisa a ranki tamkar Babu Abinda kikamin a baya Nima Ina neman afuwar ki plss" ya Ida mgnr Yana hade hannayen sa biyu, hannayen ta biyu tasa ta rike hannun nasa tana Dan dubanshi a hankali Tace, "ni wacece da bazan yafe maka Dan karamin Abinda kamin ba? Abinda nakeso tun wuri shine ka fahimci gskyr Kuma Alhamdulillah anzo wajen Ina fatan Allah ya yafe mana gaba1" "Ameen" Dr. Omar ya furta hakan da murmushi Meera Tace, "Toh tunda...tunda.." sai Kuma tayi shiru, Wara mata idonsa yyi yace, "tunda me?" Meera nayin kasa da kanta Tace, "tun..da dalilin dayasa ka aureni kenan har yanzu kana iya bani takarda na Allah ya hadaka da Zabin ranka Koda yake ma ai ka samu tunda tana gida...." Ta Ida mgnr a rarrabe, shiru taji yyi bece komai ba hakan yasa ta dago tana dubansa sai taga Ashe itan yake kallo, "Ya Omarr.." ta ambaci sunan sa tana Dan girgiza shi zaton ta beji me Tace ba dazun, Dan cije lips yyi kafin ya Kama duka kafafun ta biyu Yana duban kwayar idonta yace, "tunda...tunda..tunda.. me hakan yake nufi Meera?" Zaro idonta tayi a hankali Tace, "bafa Haka nace ba" ta Ida mgnr tana Dan tura baki, "Oh Toh wacce takarda kike nufi? Takardar tsire ko balangu?" Girgiza Kai tayi da sauri tace, "No ya Omar.." "yess Meera" shima ya katse ta d mgn kafin yaci gaba da fadin, "toh idan ma takardar tsiren ne ko balangu meye a ciki? Tunda nasan unborn ke bukata" ya karasa mgnr Yana kallon saitin marar ta kasa2 zaro idonta tayi a firgice tana kokarin matsawa baya ya rikota ta Fado jikinsa, dago Kanta tayi tana kallon sa dab da fuskar sa domin har hancin su ya hade Dana juna sunajin fitar Numfashi juna Tace, "Ka daina Wannan tunanin ya Omar ni Abinda nake nufi shine takardar sak...." Bata Ida mgnr ba kuwa ya manne bakinsu tare, anan ya Shiga tsote tattausan lips dinta zuwa cikin harshen ta, dakyar Meera ta kwace tana maida Numfashi Tace, "Ya Omar mgn muke ta fahimta Amma kana kawar da zancen meyasa Haka ne?" Dubanta yyi na tsanaki kafin a takaice yace, "Karen hauka ne ya cijeni dazan sake ki Ameera?" Zaro Ido tayi dan batayi tsammanin hakan daga gareshi ba, bakinta na rawa Tace, "Toh amma ya Omarr auren namu fa..." "Ya Isa Haka Ameera" ya Fadi hakan Yana Dan
Hade fuska, ja baya ta fara Yi yayi saurin tallafo fuskar ta Yana sassauta hade fuskar da yyi kafin yace, "look Meera Koda ace bansan gskyr ba bana tunanin zan sake ki bare yanzu Dana San gskyr Abinda ya faru" lumshe idonta tayi tanajin wani irin Abu na yawo a tsakankanin zuciyar ta, hakan yasa Dr. Omar yaci gaba da fadin, "mgnr gsky shine Raina na baci a duk lkcn da Kika ambaci sakin Nan Meeraaaa..." Bude idonta tayi ta zube shi a cikin nasa cikin wani irin yanayi sai yanzu ta fahimci Abinda ke yawo a tsakankanin zuciyar tata ba komai bane face kaunar Omar da tun fil'izal take Masa, ba ko shakka ta fara sonsa a lkcn da shi din baima San tanayi ba daga ranar daya nuna fushinsa akan Abinda Sageer yaso Yi Mata daga Wannan ranar ya samu gurbi a zuciyar ta, shirun nasu shiya bawa dukkanin zuciyoyin su damar da Isar da sako ta cikin idanun su da suka kafe da juna, wayar Omar ce tayi ringing hakan ya dawo dasu duniyar kallon kaunar da suke ma juna, firgigit kuwa suka farka Meera na Sunkuyar da kanta sbd kunya, shi Kuma Omar din na zaro wayar sa a pocket, ganin Mummy yasa shi daga wayar Yana amsawa da ladabi, Mummy Tace, "yauwa Ameer akwai wani Abu da za'a Kara ne bayan Abubuwan daka lissafa?" Dan kallon Meera yyi kafin yace, "no Mummy I think Abinda nace ma ya Isa saidai Kuma ki tmbyi Safna tunda kusan komai zaizo daya" Mummy Tace, "oh Toh da sauki ma Amma dai dukda Haka wa yafi wani?" Ya fahimci me tmbyr Mummy ke nufi hakan yasa shi sake duban Meera sosai, tana zaune ne kanta a kasa matsawa yyi gefenta ya mikar da ita Meera na Masa kallon mmki, Mummy na fadin, "hello, hello kanajina kuwa?" Omar daya Gama karewa Ameera kallo yace, "hello Mummy Kamar ntwrk mgnr yasa shi daukewa" Mummy Tace, "eh bani answer tmby na" Dan cije lips dinsa yyi Kamar Yana gabanta a hankali yace, "tafi" yyi mgnr a hankali, badan Allah yasa Mummy naji sosai bama bazata ji me yace ba, "Alright" ta Fadi hakan tana kashe wayar, dama hannun sa a bisa kuqun Meera yake ya mayar da wayar cikin Aljihun sa sai a lkcn Meera ta janye rikon da yyi Mata tace, "ni zan wuce ciki" "kina tare da mijin naki Zaki wuce ciki?" Ya mata mgnr Yana rungume hannu a kirji, Dan juya manyan idonta tayi kafin Tace, "Wai bakasan Nan parlon Abba bane?" "Oh! Really?" Dan hararar sa tayi tana sauke Kai, "It's okay yanzu ma saimu koma kano ai" kallon sa tayi da sauri Dr. Omar ya girgiza Kai yace, "yess". Acan bangaren su dad da Abban Ahmad kuwa Suna barin parlon Sadeeq na bayansu Inna fure kuwa tana fitowa ta dubi Sadeeq Tace, "Wai waye ne Wannan Dan iskan Sageer da Kuma waccar 'yar banzan Shafa?" Sosa Kai Sadeeq yyi yace, "ehto gsky sanin waye Sageer lbri ne me tsawo ita Kuma wacce ta Kira da Anty shafa tare nake ganinsu saidai bansan hadinsu ba" Inna fure Tace, "yanzu Haka cikin kawayenta ne masu bakin ciki sukai mata Wannan cin mutuncin Koh?" Dad ne yace, "Mama ba kawayenta bane" kallon sa sukai da mmki, Inna fure Tace, "ka sansu kenan?" Cikin takaicin zuciya dad yace, "yaran matar da nake aure ne da" Salati Inna fure taja ta dire tana tafa hannu tace, "yau Naga debabbun 'ya'ya Kai Wannan mata sadeeya Allah ya Isa tsakaninmu da ita, saidai kayi hakuri Ibrahim Amma Wlh sadiya ta cutar da jinin ameena" Dan Numfashi dad Yaja hakan yasa Abban Ahmad yace, "Mama muje can dayan parlon ayi mgnr a nutse" Nan suka Diba zuwa dayan parlon gidan, Shidai Sadeeq mmkin furucin Dad kawai yake a Haka suka Isa Bayan sun zauna ne dad yace, "Kamar yadda na fada Miki ne tun farko mama Abubuwan daya faru da Ameera tun tana Karama bayin Kaina bane lkcn da kikaje gidana na karshe banji dadin yadda muka rabu ba tun a lkcn naso zuwa baki hakuri har nake sanar da sadiya(Mom) ta nuna min a fuska ta bani goyon baya Amma Wlh bansan ya akai na manta d mgnr ba kwata2 har mancewa nake da Ameera Tanada Dangin mahaifiya...." Nan ya fara Basu lbrn kuncin Rayuwar da Meera ta taso da yadda yyi ta nuna halin ko in kula Kan Meera da fada musu asalin su waye Shafa'atu da Jamila ya dauki kauna d son duniya ya Dora musu kamar shi ya haife su ba Abinda suka nema suka Rasa daga wajen sa sai bayan bikin yaran hankalin sa ya dawo jikinsa, soyayyar Ameera ta dawo Masa, ya fahimci zaman cin Amana mom take dashi, daga karshe yace, "a ranar da abin ya kasance shine cikin bcci na nake mafarkin Aminatu tazo min tana tunatar Dani hakkin Ameera da akaci, sai Kuma fuskar Ameera Dana gani tana kuka sosai ba karamin girgiza nayi d Wannan mafarkin ba da Allah yaso Asirin zai karye Ina farkawa da salati a bakina Abinda ya biyo baya shine Ameera Dama a kwanakin Inajin canji a jikina shiyasa komai sadiya tamin nakejin haushin ta, Koda na fito a dakina ba Abinda nake Fadi sai Kiran sunan Ameera, Sadiya na fitowa a kitchen Jin na ambaci Ameera ta saki plate din dake hannun ta cikin firgici, na matso kusa da ita Ina fadin Ina kuka kaimin Ameera...? A takaice dai duk yadda naso ta bani Amsa kasawa tayi sai cemin take Bata sani ba. A zahirin gsky naji takaici kwarai a lkcn tunanin yadda Ameera tabar gidan ya dawo min, ba Bata lkci na rabu da Wannan annobar Sadiya nasa tabar min gidana ko kwana daya Bata Kara ba dukda taso na barta na rufe idona, tun daga Wannan lkcn na bazama neman Ameera Ina takaicin kalar auren da nayi mata ba bincike ba sanin inda take zaune, Toh da Allah ya taimake ni Ina fitowa ranar da safe muka hadu da ita bakin gate." Abban Ahmad da shi kansa Ahmad daya shigo parlon da Sadeeq ba Wanda be tausayawa Ameera ba, lalle Ameera taga rayuwa Sadeeq Kuma tunani ne ya shige shi kenan idan bazai manta bafa Wannan shafar itace ta auri Sageer? Tab lalle anyi gwarama ya Fadi hakan a ransa, Inna fure na goge hawayen takaici da tausayin Meera Tace, "Insha Allahu sai Allah ya saka wa yarinyar Nan, ace tun tana Karama ake cutar ta? Kai Allah ya Isa Wlh sai sun gani a kwaryar su matsiyata" Sadeeq yace, "ai Inna fure kusan Lbrn Ameera yaso yyi Kama Dana Omar" Nan suka zuba Masa ido da mmki, gyada Kai yyi Yana gyara Zama Nan ya fada musu sauyin da akayiwa Omar lalle sun firgita dajin Wannan lbri Inna fure jikinta har rawa yake sbd firgita cewa take, "duniya Ina Zaki damu? Yanzu wa gari ya waya? Kaii Hasbunallahi wani'imal wakil...." Abban Ahmad kuwa Fadi yake, "Allahu Akbar Lalle inda ranka kasha kallo Abu sai kace a film? Koda yake ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA....." Dad kuwa tsabar tausayin Omar din ma kasa Furta komai yyi Ashe na Meera Nafila ne tunda tasan iyayenta shi kuwa dungurungun aka dauke shi daga wajen su tun besan kansa ba kaii duniya akwai macuta dayawa, duk Wanda ka jawo shi inuwa daga rana sai kaga wata Rana shike kokarin turaka ranar, shi kansa Ahmad ba karamin tausayi suka bashi dukansu ba hakan yasa a ransa lalle sun cancanci su mallaki junansu domin sun dace da juna kowa yaga rayuwa.
Matsawa Meera tayi baya tana kada kanta Tace, "no ya Omar duka yaushe nazo garin? Ko sati fa banyi ba Kuma rabona da garin Nan tun Ina Karama" matsawa yyi dab da ita zai kamota ta zame tanayin hanyar kofa hakan ya sashi binta da sauri Dan yaga kamar zata gudu Aiko kafin ya karaso harta fece, dafe kansa yyi Yana takowa a hankali zuwa wajen daidai lkcn Sadeeq ya fito waje Yana Amsa Kira ya hango Omar din ya fito ita Kuma Meera tabi wata hanyar, Dan murmushi yyi Yana matsawo gun Omar din wayarsa a kunne zuwan sa wajen yyi daidai da Gama wayar tashi ya dubi Omar daya zube hannayen sa cikin Aljihun wando sa Yana bin hanyar da Meera tabi da kallo, ganin kamar baida niyar kulashi yasa shi Shan gabansa Yana tare inda yake kallon, dubansa Omar yyi Yana Dan yatsina fuska yace, "mlm lpy kke keta tsakanin mata da miji?" Gwalalo ido Sadeeq din yyi yace, "Amma Wlh Omar ka dinga Jin tsoron Allah" Omar na Dan hararar sa yace, "toh da Kai zanji tsoro? Haka kawai ka katse ni" "kuttt Amma Kai Dan iskane Wlh kaga ni duk ka maido da nutsuwar ka Nan muyi mgn" sai a lkcn Omar ya danyi murmushi yace, "Inajin ka" Sadeeq yace, "Kun daidaita ne?" Omar yace, "Eh Insha Allah" "Kai Alhamdulillah gsky naji Dadi" kallon sa Omar yyi yace, "tun dazu tare kke dasu ne?" Sadeeq yace, "hmmm kaidai Bari kawai frnd" Omar yace, "meya faru?" Sadeeq na sake sauke ajiyar zuciya yace, "Rayuwar Nan gaba dayanta cike take da Abubuwan tsoro" yanzu Kam da mmki yace, "wani Abu ne ya faru?" Dubansa Sadeeq yyi kafin yace, "ai ya Dade da faruwa ma saidai Allah ya kiyaye gaba yasa iyakar wahalar Taku kenan" Omar Adan tsorace yace, "kamin bayani yadda zan fahimta mana" Sadeeq ya Buda baki zayyi mgn kenan yaga fitowar su dad harda Ahmad dake bayansu hakan yasa ya hadiye Abinda yaso Fadi dukansu suka Isa garesu, Abban Ahmad ne yace, "toh Omar mu zamu fita saiku Kai kayanku can part din Ahmad ku zauna, gyada Kai yyi da murmushi yace, "Mun gode Allah ya saka da Alkhairi" "ba komai Omar mune da godiya" Nan sukayi masu sallama suka tafi, bayan tafiyar su ne Ahmad yace, "muje na nuna muku wajen" Amsa Masa sukai da Toh daidai zasu wuce inda Meera tabi Omar ya juya wajen yanata kallo kamar Wanda zai hango ta, kayansu suka kwashe Nan suka wuce dashi part din Ahmad da yanzu ya ware Yana musu Hira. Inna fure na

Please Login or Register in order to submit comment