Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi Nan suka bar dakin ita kuma Nurse Ruky ta shiga ciki Dan kula da Abba.


Suna cikin mota Babu Wanda yace wa wani kala sbd shima Dr. Sadeeq din wani lkcin akwai Shan kamshi saidai bekai Dr. Omar din bane especially daya kasance ya fito daga babban gida Wanda Nigeria kaf tasan da zaman mahaifin sa Alhaji Tukur Malami, Dr. Sadeeq Yana matukar ji da kansa Dan ba karya shima karshe ne gwanine wajen kyau da iya kwalisa, saidai daya hadu da Dr. Omar dukda shi ya fito daga karamin karfi sai yaga ya take shi nesa ba kusa ba ( oh ko ya akai suka kasance abokai aminai? Asalin lbrn nasu Yana gaba Insha Allah) a nutse suka fito daga motar Bayan Dr. Sadeeq yyi parking suna kokarin rufe mota suka ga wata irin kura ta taso daga can nesa da su, wani irin wawan tsaki suka ja a take duka su biyun wato Dr. Sadeeq da Dr. Omar, cikin jin haushi suke bin zugar motocin da sukayi convoy suna shigowa cikin University din Ta B.U.K,

Daga can barin wata arniyar mota ce wasu daga cikin bodyguard din me tafiyar suka zo suka bude wa me motar kofar, Cike da izza da takama na cikin motar aka fito da kafa daya waje Ana me karkada ta a hankali wayyo Allah kowa yaga Tsadar takalmin yasan Tabbas an narka Naira wajen siyan shi Dan ba karya takalmin ya hadu Naira tayi kuka a kansa. Dayawa dake harabar makarantar zuba musu ido akai kamar kullum yyinda wasu ke danyin kuskus kamar yadda aka Saba,

Dr. Sadeeq da Dr. Omar kuwa bakinsu ne ya sake haduwa wajen furta Fool.




*Tofah😱😱😱 Ana wata ga wata ko waye a motar? Fans karku damu nasan kun kosa kuji asalin lbrn, toh Yana Nan tafe sannu a hankali, kamar yadda nace Wannan lbrn yasha banban da sauran Wanda kuka Saba ji a hankali zaku fahimci inda na dosa musamman da muke taso muji me mlm sale yaji matar sa Saratu take kullawa ita da Nas? Kuci gaba da bin Nuceeyluv Dan ta warware muku Kullin zaren🏌️‍♂�?*
*ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA...🐓*
( _ko Ana Muzuru Ana Shaho Sai yayi_)





Na
*Nuceeyluv😘*




3....



Hade dayin wani mugun tsaki suka Kama hanyar faculty dinsu, Wanda ke cikin motar ne aka karasa fito da daya kafar cikin tinkaho da takama ya fito daga cikin ta gaba1 *SAGEER ABDULLAHI OMAR MAI FATA* kenan meji da kansa da nuna Isa akan dukiyar mahaifin sa Abdullahi Omar me fata, duk fadin garin kano Babu Wanda besan sunan sageer ba sbd yadda akasan mahaifin sa dattijon arziki kowa ya sani ya shaida za'a iya jera shi a cikin manyan masu kudin Nigeria daga Sageer sai kanwar sa Safna su kadai iyayen suka mallaka a duniya, Sageer Yana Wasa da Naira kwarai da gske Dan duk wasu manyan clubs dake fadin Nigeria Babu Wanda beje ba kazalika be dauki talaka a bakin komai ba face makaskanci marar daraja sometimes yakan kirasu da kaji Dan gani yake da anyi musu watsi zasu sa baki su caccaki abinda aka Watso musu wato Naira, A takaice dai Sageer Abdullahi baida hali kokadan,

Yana final year dinsa ne anan B.U.K bangaren Business Administration yaso fita waje karatu iyayen sa suka Hana sbd sunsan halin sa ba lalle yyi kr2n bama Yana gabansu ma ya yakare bare yyi nesa da su? Su Kuma tunda dadewa suka bar zaman kasar waje suka dawo kasarsu ta haihuwa har suka haifi Sageer dake Allah be Basu haihuwar da wuri ba har na tsawon lkci, toh daga kan Safnah haihuwar ta tsaya tsak.
Direct shima wucewa sukayi department dinsu cikin Takun Isa da nuna iko.



*****
A gurguje take dura sauran chips din da suka rage hade da sauran tea din su kafin su fito tasan da sun zo Tabbas ko Bata koshi ba Dole ta bisu musamman data lura yadda suke dokin shiga University din,

"Meeraaa...."

Taji an kwala Mata Kira daga can saman daki, dakyar ta hadiye dankalin data dura a bakinta har tana shaqewa a Razane tace,

"Na'aam"

tayi mgnr tana mikewa da sauri har tana hada hanya, Kafin wani lkci harta taka matattalakar benen ta Isa ga Wanda ke Kiran nata, tana daga bakin kofa tace,

"jira kike muce Miki kizo ki kwasar Mana files dinmu?"

Meera ta Girgiza Kai da sauri tace,

"srry Aunty Shafa Ina niyyar zuwa kenan kika kirani"

"Mtwsss"

Aunty Shafa taja tsaki hade da juyawa ciki, Meera dake tsaye tabi bayanta da kallo tana mmkin irin shigar da tayi dama idan za'aje University riga da wando ake tsukewa ko kuwa kawai tsabar Rashin sanin darajar Kai ne da wulakanta Addini? Bata samu Wannan amsar ba Kawai ta fada dakin da sauri kar aga Bata shiga ba, tana shiga dakin Ana wurgo Mata wasu takalma da sauri ta kalli gefen da aka jefo Mata Aunty Jamila ce, Kafin tayi wani tunani taji tace,

"Yi sauri ki gogemin takalmin Nan kafin na gama rolling gyalen Kaina"

girgiza Kai Meera tayi sannan ta dauka tana mmkin Shigar Aunty Jamilan itama, kowa ta tsuke kamar Wanda zasu shiga turaka, A gaggauce ta goge sannan ta aje Mata gefe daidai lkcin harsun Gama Shirin su sun Gama fesa turare kafin sukayi nufin fita daga dakin, Basu ce Mata kala ba suka bar dakin gaba daya cikin taku daidai kowa Yana Murza Dan kugun sa,

wata wawiyar ajiyar zuciya Meera ta saki tana me jawo Ghana masgo dinta da sauri, a gurguje ta canja kayan jikinta zuwa wata riga da skirt da suka Dan Jima Basu dai kode can ba, hijab dinta ta saka sannan ta tattare files din da suka baza akan gado kafin ta biyosu dashi cikin sauri, suna tsakiyar parlo tare da Mom, Dan dukawa Meera tayi ta gaishe da mom din, mom na jinta kamar bazata Amsa ba sai can aka Amsa Mata a wulakance, Meera taja gefe ta tsaya tana jiran su Gama sannan su tafi.

Anty Shafa ce tayi juyi gaban mom tace,

"Ya kika ga kwalliyar tawa mom?"

Mom ta washe baki tace,

"ni na yadda daku yarana duk tsiya Dole a saku a sahun First class"

Nan suka kaure da ihun murna kamar yadda suka Saba kullum mom na Koda su da yaba kwalliyar su hakan ke Kara musu ji da Kai da nuna su din isassu ne, Dad ne ya shigo parlon Nan sukayi gunsa suna gaishe shi, Amsa musu yyi da fara'a yace,

"yaran Mom har an shirya kenan"

"eh Dad"

Suka fada a tare, rafar kudi ya zaro ya Basu Yana dafa kansu hade da sa musu Albarka Nan sukayi ta washe baki sunajin Dadi kwarai da gske, Meera dake gefe kuwa Dan karkatar da kanta tayi ta share wata siririyar kwalla dake Shirin sakko Mata, Dad be lura da inda take ba Sam Koda yake dayawan lkci Idan suna tare baima sanin akwai wata Meera a wajen, sallama sukai musu Nan suka tafi mom Dadi duk ya cika ta tanajin Annashuwa idan taga yadda Dad yake yima yaranta, Dan satar kallon ta Meera tayi Aiko suka hada ido Nan ta samu alakoron Harara, da sauri Meera ta fice a parlon kamar zata kifa,

kawu Bala ne yazo daukar su wato driver dinsu, cikin wata kosasshiyar mota Suka shige baya yyinda Meera ta shige gaba rike da files din nasu, an fara tafiya kenan Meera ta zaro nata file din ta fara dubawa a hankali, Su Aunty Jamila kuwa wayarsu Kirar iPhone 11 itace suka fara latsawa cikin gadara.



*****
Acan bangaren su Saratu kuwa, Saida sukayi tafiya Medan tsawo kafin sukaje gun bokan nasu na tsamiya, suna shiga ya daga musu hannu alamar yasan me suke tafe da shi, Saida yyi shiru can ya dubi Saratu yace,

"Abinda kike nema zai samu matukar kika sadu dashi da Wannan mgnin"

Ya nuna Mata shi a kulle a leda, sannan Ya sake nuna Mata wata karamar laya yace,

"Wannan Kuma Kije bakin kofar dakinsa ki binne toh Ina me Tabbatar Miki yadda kika binne layar Nan baxai Kara mgn ba tamkar bakinsa aka manne da gum matukar ba tone layar akai ba, haka saduwar ku xaisa a kasa gano meye silar kurmantan shi"

murna ce ta Kama su duka biyun Nas tace,

"gsky mun gode boka"

Saratu tace,

"saidai akwai matsala fah"

boka yace,

"Tame kenan?"

Saratu tace,

"mutumin dake kwance Shirim Taya Zan Tara da shi?"

Wata irin shedaniyar dariya boka ya saki Yana kada buzun sa kafin can ya hade Rai yace,

"karki bada Mata Mana, Abu me sauki ki Tabbatar cikin dare yadda Babu kowa saiki zaro bindin nasa ki zura a gaban ki daganan ya rage naki kisan yadda abin xai shiga"

"Toh shikenan boka zanyi yadda kace"

"Dakyau"

Ya furta Yana dariya, Nan sukayi Masa sallama Bayan sun bashi kudi Wanda Nas ce tayi guzurin su.

A hanya Saratu da Nas sukaci gaba da tattauna yadda lamarin zai kasance, suna shiga gari kuwa Nas tace,

"Yanzu Ina zakije?"

Saratu tace,

"can gidan Alhaji Mana yaushe zanje gida tun yanzu"

Nas tayi dariya tace,

"haba Ashe kin gane, Nima wucewa zanyi"

"toh shikenan"

Nan suka raba hanya Nas ta wuce gida yyinda Saratu ta wuce gidan *ALHAJI ABDULLAHI OMAR MAI FATA*


••••••••°°°°°••••••••�?

*ASALIN LABARIN*


*ALHAJI ABDULLAHI OMAR MAI FATA*

Rikakken me kudi ne Wanda duniya ta shaida hakan, kamar yadda nace a baya Tabbas Alhaji Abdullahi ya shahara a Nigeria domin kowa yasan shi mutum ne daya rike mukamai dayawa yyi aiki da gsky daga karshe ya fita daga harkar mulki ya koma kasuwanci, dama Shidin asalin Dan kasuwa ne sbd safarar fata da sukeyi kasashen waje inda ake gyara fata ta koma abun ado wato takalma, jaka dadai sauran su, Duk wannan Dunbin DUKIYA daya samu Allah be bashi haihuwa ba shi da matar sa Hajia Aisha, duk wani mgni sunyi amfani dashi abin yaci tura, Dole suka zubawa sarautar Allah ido domin sunsan ba'a yiwa Allah Dole sai lkcin dayaso zai baka, hakan kuwa ta kasance sun dukufa sosai wajen yin Addu'a dakai kukansu game duka, cikin ikon Allah Saiga Hajia Aisha da juna biyu murna a gurin wa'annan bayin Allah ba'ace komai, tun daga lkcn suka fara tattarowa Dan dawowa Nigeria dama akan Shirin hakan suke Dan tuni Alhaji Abdullahi ya tamfatsa musu kerarren gida anan unguwar Tarauni, kowa yaga gidan Tabbas Saiya kyasa Kai kace ba'a kasar Nan yake ba wajen kyau da tsaruwa, a haka suka hawo jirgi Dan zuwa kasarsu ta haihuwa,

saukar su keda wuya driver dinsu da aka sanar masa Yana jiransu a harabar wajen Dan haka suna zuwa suka wuce cikin mota Nan kuwa suka taho gida, Suna daga Bayan mota sai ji sukai driver yyi wani wawan birki kamar su hantsila cikin muguwar tsawa Alhaji Abdullahi ya dakawa driver yace,

"Kai Salmanu are you out of your sense?"

Jiki na rawa Salmanu yace,

"Ka gafarceni Alhaji Wlh wata Mata mukaso kadewa"

"Mtwsss"

Alhji Yaja tsaki cikin takaici yace,

"shiyasa nace kana duba hanya sbd irin haka...."

Be rufe bakinsa ba yaji Ana kwankwasa musu window, Zugewa Hajia Aisha tayi da tun dazu batayi mgn ba, matar da akaso kadewa ne ta fara mgn,

"Dan Allah bayin Allah ku taimaka min da Abinda zanci Wlh yunwa nakeji kamar Zan mutu."

Kallon ta sukayi cikin tausayi Hajia Aisha ta zaro kudi ta Bata tace,

"gashi"

da murna matar ta karba tace,

"Nagode, Nagode Hajia Allah yasa kufi haka Nagode"

Nan dai suka tafi tanata zabga godiya. Suna wucewa itama matar ta koma gefen hanya cikin murna tana jiran mijinta ya dawo, daga bayanta taji ance,

"gashi *SARATU* dakyar na samu kunun Ashirin ki karba Kidan kurba kinji"

Juyowa tayi da murnar ta tace,

*"MALAM SALE* Yaudai Allah ya hadani da mutanen arziki Ashe dama akwai na Allah?"

Mlm sale yace,

"meya faru?"

Nan ta Gaya masa Abinda ya faru tana nuna masa kudin da aka Basu, girgiza Kai mlm sale yyi yace,

"Tabbas akwai na Allah samun su ne yanada wuya Allah ya biyasu"

Ya karasa mgnr cikin jin tausayin kansu, Tabbas idan zai iya tunawa yau kusan kwana uku kenan suna yawon bara titi-titi gida2 Basu samu abincin da zasuci ba bare Inda zasu tsugunna sunje gidan sarki yafi a kirga Babu bayani, sun tsaya a sansanin 'yan gudun hijira Abin gwanin takaici sbd yadda sukaga Ana layi da ture2 wajen karbar sadakar rabon gishiri kamar Wani garin kwaki abin a zubda kwalla ne, ga matarsa na dauke da karamin ciki Dole ne su fito a samu Abinda za'a sawa bakin salati.

Tun daga Wannan ranar Suka samu rufin Asiri sbd kudin da Hajia Aisha ta bawa Saratu yanada tsoka Dan haka suka lallaba suka Kama haya daki daya sauran mlm sale ya fara jari dashi yanabin kasuwar kwari da wambai Yana Saro Kaya ya dinga yawo dashi akai Yana siyarwa, ita kuma Saratu Bata zauna ba taci gaba da neman Aikatau Sam ta kasa samu abin ya dameta gari ya kano ace ta rasa Aikatau,

Sai wata Rana a garin yawon nata Allah ya kaita wani katon gida me masifar kyau da sheki ga security tako Ina Ana safa da marwa, gidan ya birgeta matuka, Nan ta dinga zagayen gidan tana kallo har taji cewa inama zata samu shiga? Tana daga Dan nesa da gate din gidan kenan taga wata mota zata shiga gidan har an zarta ta sai kuma taga motar ta dawo baya, Daidai saitin ta aka tsaya sannan aka zuge glass din window wa zata gani....?



Hajia Aisha ce dake Bayan mota ta leko tana Kare Mata kallo, sosai suka gane juna da sauri Saratu ta matso tana Dan dukawa tace,

"Allahu Akbar Hajia kece? Allah sarki Ashe zamu sake gamuwa, Ina wuni? Ya gida ya iyali"

Hajia Aisha ta danyi murmushin ta na manyan Mata tace,

"Baiwar Allah lpy ko yaushe kike a titi?"

Dan sosa Kai Saratu tayi tace,

"Wlh Hajia neman Aikatau nake ranar Kuma da kika ganni Wlh..."

Daga Mata hannu Hajia Aisha tayi tace,

"Wuce mu shiga daga ciki I'm very tired yanzu sai muyi mgn a nutse"

"Toh, toh, toh Babu damuwa"

Saratu ta furta tana me ja baya hade da karewa falleliyar motar da hajian take ciki kallo ita kam ta samu shiga Wannan motar ai sai tayi sati a ciki Bata gaji ba, bin bayansu tayi Dan sukam tuni driver Yaja harma ya fara Sanya hancin motar cikin gidan, a nan bakin gate Hajia Aisha tayiwa security mgn subar matar dake bayansu ta shigo, Nan suka Amsa Mata cikin girmamawa, da saurinta kuwa taje gaban gate din ganin basuce Mata komai ba yasa ta saki ajiyar zuciya kafin ta nausa cikin gidan.


A falon baki Hajia Aisha tasa aka aje Saratu tare dakai Mata abin motsa baki,

Saratu na ganin haka ta zauna dirshan tana cin kayan itatuwa abinka Dame ciki duk sai ta fara hannu baka hannu kwarya gashi an kwana biyu ba'aci me nauyi ba.


Saida Hajia Aisha ta huta sannan tazo ta samu Saratu a falon baki, Saratu duk tayi daidai a tsakiyar falon tana Shan iska hade da zubawa TV kallo, Ganin Hajia Aisha yasa ta hade kafa tana sunkuyar da Kai, zama Hajia Aisha tayi tace,

"Kozan iya sanin sunan ki?"

Saratu ta gyara zamanta sosai tace,

"Sunana Saratu matar Sale"

Dan zaro ido Hajia Aisha tayi tace,

"kenan bakwa tare da mijin naki?"

Saratu ta girgiza Kai tace,

"Muna tare.."

"Amma ya barki kike yawo titi2 shi meye amfanin sa da bazai nema muku abinci ba?"

Hajia Aisha ta katse Mata mgnr. Saratu ta danyi kasa da kanta cikin muryar kuka tace,

"Wlh Hajia mu ba 'yan garin Nan bane, asalin mu daga kauyen borno muke a dalilin rikicin Nan yasa mukazo Nan garin, gaba1 Dangin mu sun watse wasu sun mutu wasu bamu San inda suke ba, muma lkcn da aka tada rikici a garin bama Nan ne Dan munje babban asibitin cikin garin Borno sbd jinya da nake ta fama da ita sai da mukaje aka Tabbatar Mana da Ashe ciki ne, toh Ashe tafiyar mu keda wuya 'yan boko Haram suka bulla cikin garin na takaice Miki lbri bamu tsira da komai ba sai kayan jikin mu domin lkcn da mukaje kamar anyiwa garin shara yyinda gefe guda garin ya koma kamar matattarar Makabarta, tun daga lkcn ni da mijina bamu sake awa daya ba a garin muka dawo Borno dadan kudin daya rage Mana muka taho kano sbd tunanin mu kano babbar jaha ce da ko bakaje ba zakaji Ana lbrn ta,

musamman yadda akace 'yan kasuwa ne sai muka ga hakan zaizo Mana da sauki tunda kowa zai iya kasa kasuwar sa ya watse idan munzo sai muyi kasuwanci har mu samu rufin Asiri, toh Wlh Hajia ranar da muka fara haduwa dake kwanan mu uku kenan muna garari a titi sai da taimakon Allah da kukazo wucewa kika bamu kudin Nan ni da mijina muka sarrafa shi wajen siyan abinci dayin jari, Dan Baku Dade da wucewa ba shima ya dawo sbd ya tafi ne ya nema min Abinda zanci sbd karamin cikina, ta karashe mgnr cikin Jan majina.


"Hmmmm....!"

Hajia Aisha taja gwauron numfashi ta ajiye Tausayin matar ya shiga ranta kwarai Nan ta zurfafa cikin tunani kafin ta dago kanta a hankali tace....
*ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA...🐓*
( _Ko Ana Muzuru Ana Shaho Sai yayi_)




Na
*Nuceeyluv😘*


*Wannan page din naki ne Mrs Tajudden Tajra, Ina matukar Jin dadin yadda kikemin comments, hakika sai an nutsu an fahimci Asalin lbrn kafin a gane Ina littafin ya dosa, sai gashi kafin nayi nisa kin fara zaro bakin zaren💃🏻 Inayinki❤️❤️ Aci gaba da gashi🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀�?*




4.....


"Zan amince ki zamo 'yar aikina saidai bansan wanne kala Zaki iya ba sbd mu Already munada ma'aikata a gidan Nan Zan taimakeki ne kawai badan mun rasa ba"

Cikin zumudi Saratu tace,

"Wlh kowanne iri ne Hajia Zan iya, daga kan share2 wanke2 da goge2 duk Zan iya Wlh, irin abincin ku ne dai bazan iya ba idan ba irin namu na gargajiya ba"

kallon ta Hajia Aisha tayi tace,

"naji kamar kince kina dauke da karamin ciki?"

Saratu ta girgiza kanta tace,

"sosai kuwa"

Hajia Aisha tace,

"Toh Taya Zan baki aiki Bayan kina da juna biyu? Ki Bari idan kika haife Abinda ke cikin ki saiki dawo muyi mgn"

da sauri Saratu tace,

"Dan Allah Hajia kimin Rai ni Wlh a hakan ma Zan iya inada dauriya sosai ko Dan goge2 Nan ki bani zanyi idan yaso na haife Abinda ke cikina saiki bani aiki me kwari"

Ta karasa mgnr cikin hade hannayen ta Alamar magiya, Shiru Hajia Aisha tayi tana Dan nazari can tace,

"Toh shikenan kiyi shawara da mijinki Zaki dinga gyara min dakina shi kadai ne masu aiki basa zuwa da Kaina nakeyi na barki ne kiyi min sbd Nima Abinda ke tare Dani wahala yake bani ba'aso na dinga Abu me wahala ko yawan zirga-zirga sbd be Gama kwari ba"

baki washe Saratu tace,

"Kai Masha Allah Hajia kema ciki gareki?"

Dan murmushi Hajia Aisha tayi ta girgiza kanta kawai, Nan Saratu tahau murna tana sanyawa cikin Albarka hakan ya karawa Hajia Aisha jin Dadi harta Dan Kara sakewa da saratun.

Can tace,

"mgn ta gaba Saratu Ina tare da uwar mijina muna kiranta da Hajjaju nata bangaren nacan gafe ki tashi muje na gabatar dake wajenta"

Da sauri Saratu ta Mike tace,

"Toh Hajia muje"

Nan Hajia Aisha tayi gaba saratun ta bita a baya.


Tun a hanya Saratu ke ganin ikon Allah ko Ina na gidan gwanin kyau da ban sha'awa haka dai suka karasa part din Hajjaju, Tana kishingide akan lallausan kafet dinta tana Jan carbi yyinda gefe guda wata 'yar aiki ke Mata tausa, da Sallama suka shiga ciki 'yar aikin ta gaishe d Hajia Aisha sannan ta fice a dakin, Hajjaju ta gyara zamanta sosai tana kallon Hajia Aisha da fara'a a fuskar ta tace,

"Shatu kece tafe"

"Eh Hajjaju"

Nan itama ta zauna a hankali, kallon Bayan Hajia Aisha Hajjaju tayi tace,

"Ikon Allah Wannan Kuma wacece a Bayan ki?"

Tayi mgnr tana nuna Saratu data saki baki tana kallon dukiyar da aka narka a falon tsohuwa, Jin Ana nunata tayi saurin dukawa kasa tana kwasar gaisuwa sama2 Hajjaju ta Amsa tana kallon Hajia Aisha Dan jin amsar tmbyr ta, Hajia Aisha tace,

"sunan ta Saratu dama nazo da ita nan ne Dan na shaida Miki komai game da ita"

Nan ta kawashe lbrn Saratu da yadda zasu taimaka Mata ta gayawa Hajjaju, Hajjaju data saki kunne tanajin bayani tadan lankwashe hannun ta tana me kafe Saratu da idonta kurii, Saratu tayi kasa da kanta, Hajjaju ta dawo da kallon ta kan Hajia Aisha tace,

"Ashsha, Ashsha, ta yaro kyau take Bata kargo yanzu Shatu daga Jin Wannan bayanin shikenan harkin yadda da mutum? Meyasa kullum kike da saurin yadda ne? Karki manta yanzu fa duniya ta lalace marasa Imani sun lalata masu neman bukata domin dayawa mugu sai ya shiga rigar mabukaci ya cuceka a banza da wofi dayawa wasu burinsu su rabeka, badan komai ba saidan Wannan ni'imar da Allah ya baka su ture ka daga inuwa su maida ka Rana su Kuma su mamaye gurbin ka"

A sanyaye Hajia Aisha tace,

"kiyi hakuri Hajjaju Naga baiwar Allah Nan tana bukatar a taimaka Mata ne"

Hajjaju tace,

"duka yaushe kuka dawo daga waje har ta manne Miki haka? Aisha Allah fa Abin tsoro ne haka ma mutum"

Saratu dake zaune ta share hawayen dake malala a fuskar ta tace,

"Dan Allah kuyi hakuri bansan haka abin yake b saina je na nema a wani wajen"

tayi mgnr tana kokarin mikewa, da sauri Hajia Aisha ta kalli Hajjaju, Hajjaju tace,

"baiwar Allah ni bazan Hana taimako ba Abinda na sani kawai na fada ki tmbyi kowa a gidan Nan Hajjaju batasan meye munafurci ba duk dacin gsky fada take Dan haka kuje kiyi aikin ki Allah yyi jagora"

Da murna Saratu ta juyo tana kwasar godiya gurin tsohuwa Hajjaju.


.....Kamar yadda Hajia Aisha ta umarci Saratu ta fadawa mlm hakan ne ya kasance badan mlm yaso ba ya amince sbd takurawar da Saratu tayi Masa, shi yasan halin Saratu wajen kwadayi zata iya yin komai sbd kudi, da naci da komai dai ya barta, Anan Saratu ta fara zuwa aiki sai Hajia Aisha ta bada driver guda Yana dauko ta da maida ta sbd tausayin Abinda ke cikin nata itama.



*********
Sannu a hankali Saratu ta fara aikinta a gidan *ALHAJI ABDULLAHI OMAR MAI FATA* Tanada kokari matuka sbd cikin jikinta be hanata yin aiki da Allah ya taimake ta bezo da matsala ba kamar na Hajia Aisha da kullum ake lallaba shi tamkar kwai.

Saratu a zaman da tayi a gidan Tabbas taga yadda ake zaman aure, taga yadda ake tarairaya mace, taga yadda ake nuna kauna dayiwa matar gida bauta, Kai yadda taga Alhaji Abdullahi yake tattalin matar sa har abin Yana daure Mata Kai uwa uba idan taga daular da Hajia Aisha ke ciki abin na Bata mmki, daga Nan ta fara sakar zuci tana ayyana dunbin dukiyar dake tattare da Ahalin Babu magaji ko guda daya sai Wannan cikin da ake ta lallaba shi kamar kwai, daga tunani sai ta fara Jin inama itace? (Karamar hasada ta fara bullowa) daga Wannan tunanin sai kuma ta fara hango kanta a Matsayin Hajia Aisha da itace ita da tayi kaza da kaza, Kai a hankali dai shaidan ya fara tasiri a cikin zuciyar Saratu Saiya kasance tana Jin haushin ni'imar da Allah ya bawa Hajia Aisha, domin ta faraji a ranta inama duk wani Jin Dadi yabar hajian ya dawo gareta? Saiya kasance yanzu duk wani Budi na Alkhairin Hajian bataso, ta tsani ririta cikin da suke musamman Wannan tsohuwar Hajjaju dukda tana mugun tsoron tshowar sbd Hajjaju Bata sake Mata ba Sam Dan kullum suka kebe da Hajia Aisha ce Mata take Shatu hankalina ya kasa kwanciya da Wannan 'yar aikin Taki dandai kin matsa ne Kuma ba'aso a hanaki Abinda kikeso a Wannan yanayin da kike ciki sai Hajia Aisha Tayi murmushi kawai Dan tasan halin uwar mijin nata itama Sarai Bata cika yadda da mutum da wuri ba, toh Saratu idan taga hajjajun nayin Nan Nan da cikin Hajia Aisha sai taji kamar ta make ta kullum tazo bangaren Bata da Abinda take fara fada sai Ina megida na? toh dai mutanen gidan Basu San me take ba Dan fuska biyu ta nuna musu a fili nunawa take tafi kowa kaunar su, a badini kuwa ji take kamar ta harbe su.

Ana Nan haka wata Rana likitar dake zuwa har gida duba Hajia Aisha tazo Bata sameta a parlo ba sai Saratu dake mopping itace ma ta shaida Mata Hajia na sama tare da Alhaji,

Please Login or Register in order to submit comment