Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta samu ta wuce gida, yau duk a tsorace take Dan jikinta ma sai rawa yake Yana sake gyara zamanta cikin napep din.




****
A bangaren Sageer kuwa Bayan sun Gama yiwa Ameera dariyar wulakanci suka koma gun zaman su, Sageer ya dubi gun data cije shi ya kalli sauran yaran shi yace,

"kar kuga Ina dariya toh Wlh ta ciki na ciki"

ya fada fuskar sa a hade, ganin haka Suma sauran suka hade fuska sbd oga baya dariya, Sageer yace,

"Ko 'yar gidan uban wacece yarinyar Nan Wlh saina kekketata"

Faisal yace,

"Oga kanaso Abi bayanta ne yanzu?"

Sageer ya hura hanci Yana kallon hannun sa dayake Masa zafi yace,

"Wannan ciwon shi zai determining tsawon lkcn dazan dauka Ina amfani da ita, sbd ba'a taba tozartani ba irin yau sosai ta bani kunya a gaban mutanen tsabar ita din lower class ce ba aji Sam"

Faisal yace,

"ai oga da alama sabuwar zuwa ce batasan dawa take tsaye ba Banda haka ai abin tayi murna ne Dan ba kowa ke samun irin damarta ba"

Wanda aka tura ya Kira Meera ya tsoma baki da fadin,

"ba irin yadda bance Mata ba Danna nusar da ita irin Arzikin da zata dangwala Amma yarinyar Nan tayi kememe kamar za'a yanki Naman jikinta."

Hura iskar bakinsa Sageer yyi Yana tunano yadda mazaunan yarinyar suke da laushi haka ma kirjinta har yanzu jinta yake kamar dazu daya rungume ta gaba1 ta tafi da imanin sa kawai so yake ya kwashi romon ni'imar dake jikin yarinyar can yac,

"just ku sa Mata ido aga wanne department take? So that muji saukin Kama ta duk sanda na bukaci hakan"

Nan suka Gama yanke shawarar su game da mugun nufin su kan Ameera.



°°°°°°
Su Anty shafa iyayen iyayi, lkcn da suka fahimci Sageer ta Ameera yake Bata su ba a take sukaji wani marurun takaici ya Kama zuciyar su, Ashe Wannan dariyar da sukayi duk yake ne, ransu ne yyi mummunan baci da suka ga har wani rungumo ta yake ta baya, Surry cikin jin haushi tace,

"kut**r uban can kayyasa Shafna 'yar aikin naku Sageer yake bi?"

Jamila data Gama kumewa sbd takaici tace,

"Wlh bazata yiyu ba yau dukmai maitar yarinyar Nan Wlh Bata Isa ta kwace Mana wannan ba haba yarinya sai kace Dangin mayu duk wasu masu hannu da shuni ita suke rububi ba mu ba Dan haka fa bama Barinta tayi kwalliya"

Anty shafa tace,

"ni na Tabbata akwai Abinda shegiyar nan ta kulla Mana kinsan mayyace idan ta Kama mutum sai Allah duk zantukan da muke kan samarin mu tana ji shiyasa tayi Mana Shigar sauri ta kame Masa kurwa Banda haka me zaiyi da 'yar aiki?"

Ta karasa mgnr cikin tsananin bakin ciki, Afra tace,

"haba Koda naji duk manyan matan Nan Sageer ya tantance akan Wannan 'yar aikin naku? Toh me ya gani a jikinta Wanda bamuda shi? Nonon ku duwawun?"

Surry tace,

"bar Dan dur*n uwa billahillazi Shafna kusan yadda zakuyi da Wannan 'yar aikin naku Dan bazai yiyu ta kashe Mana kasuwa ba Gata Nan cikin tsumma ko wacce jarabace yasa ya kwadaitu da Itan oho"

Anty shafa tace,

"ku barmu da ita yau tsabar bakin ciki ma bazan karasa cikin skul din ba ke Jamila zo mu juya yau saimun ci kut*r uban yarinyar Nan"

Jamila da take huci tace,

"kamar kin Shiga Raina wlh ai hankali na bazai kwanta ba idan ba gani nayi munci ubanta ba"

Surry da Afra suka sake zugasu suna Basu shawarar yadda zasuyi da Ameera anan gayyar ta watse kowa ya koma gida cikin jin haushi.



•••••••�?
Har zuwa la'asar su Dr. Omar na hospital haka ma Saratu tayi Kane-kane kamar gske, zuwa lkcn mlm sale ya farka Yana kallon kowa tun Yana hawaye Yana sharewa harma hawayen suka kafe, Shidai be taba takaicin Rashin karatu ba sai yau, Dan yau ya gane muhimmancin makaranta da ko da hannu Saiya rubutawa Dr. Omar halin da ake ciki to abin ya faskara Dan be iya rubutu da karatu ba.


Prof Sa'idu ne ya dubi Dr. Omar daya zauna Yana jiran me zaice, Prof Sa'idu yace,

"Omar"

Dr. Omar ya dago ya Amsa Masa a nutse, Prof Sa'idu yace,

"ni na sani kaima ka sani ciwon Abbanka bana hospital bane Dan Abinda zamu iya shine raunin da yaji toh Wannan tun jiya an gama da matsalar sa Rashin mgn kuwa gsky baida alaka da asibiti saidai a gwada na gida"

Dr. Omar yace,

"Tabbas nayi Wannan tunanin Insha Allahu Anjima zamu koma gida sai asan ta inda za'a fara"

Prof Sa'idu yace,

"hakane Allah ya sauwake"

"Ameen"

Dr. Omar ya Amsa Yana shirin tashi kafin yyi Masa sallama yabar office din, Koda yaje inda aka kwantar da Abba Dr. Sadeeq Yana tare dashi sai mgn me Dadi yake masa Yana nuna masa ya rungumi kaddarar data same shi Dan Allah baya bcci shizai yaye Masa, Saratu na jinsu ji take kamar ta make Sadeeq din Dan gani take kamar jirwaye yake Mata, a haka Dr. Omar ya same su ya sanar dasu halin da ake ciki, Dr. Sadeeq yace,

"shikenan saimu fara shirin tafiyar Koh kafin ma Daren yyi"

Dr. Omar yace,

"hakan za'ayi"

Nan suka fara shiryawa murna fal cikin Saratu Dan duk a takure take dama ta qagu ta labartawa Nas halin da ake ciki sannan ta koma gidan aikinta Dan ganin yaronta Sageer.

Dake ba wani shirgine dasu ba cikin kankanin lkci suka Gama Shirin nasu Nan aka Kai kayan motar Sadeeq, Bayan sun Gama Suka riko hannun Mlm sale suka Sanya shi cikin mota, Shidai mlm sale duk kunyar Dr. Omar din ma yakeji hade da tausayin sa bashi yyi abun ba Amma gaba daya ji yyi Yana Masa kwarjini musamman idan ya tuno da Matsayin Asalin iyayen sa, A haka Sadeeq Yaja musu motar suka bar harabar hospital din.
8/15/20, 8:01 PM - Ummi Tandama: *ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA...🐓*
( _Ko Ana Muzuru Ana Shaho Sai yayi_)





Na
*Nuceeyluv😘*




*Wannan page din kyauta ce ga duk wani me bibiyar littafin Nan Inayinku a duk inda kuke😘😘*



11...



Har lokacin da Meera ta Isa gida jikinta be daina rawa ba Kai yau taga tashin hankali a skul, a gurguje ta mikawa me napep kudinsa ta wuce cikin gidansu, hamdala tayi tun daga compound din gidansu data ji shiru Alamar ba kowa kenan, domin Mom Bata cika zama gida ba tana harkar business na dogayen riguna tana kaiwa manyan Mata tallen su,

"yau da alama Zan huta sosai kafin jarababbun Nan su dawo"

Meera ta fada tana tattare hijab dinta zuwa sama tunda tasan Babu kowa yasa kawai ta tura kofar parlon nasu, wani irin wawan birki taja ta tsaya sbd mugun ganin da tayi, Binsun da kallon mmki tayi kowacce Tasha 3quater da T-shirt hannun su rike da USB fuskar su kuwa hade take tamkar an Aiko musu da sakon mutuwa, a Dan tsorace ta aro jarumta tace,

"Ah Ashe Kuna nan sannun ku da gida"

tayi mgnr tana kokarin wucewa, zuuu......' taji an zabga Mata charger a baya a gigice ta juyo tana kallon Anty Jamila dake Bayan nata, cikin rawar murya tace,

"Anty Jamila me na muku?"

Zuuuu....' taji an sake zuga Mata wani dukan a dayan Barinta, Wannan karon kasa daurewa tayi Saida ta zube kasa Dan ba karamin Shigarta dukan yyi ba, Anty shafa cikin masifa tace,

"wato har kina da bakin tmbyr mu me kikai Mana Koh? Dake kinma Raina Mana wayo"

tayi mgnr tana Kai Mata kyakkyawan mari a fuska, Anty Jamila ta amshe da fadin,

"barta yau me rabamu da ita sai Allah shegiya Dangin mayu"

Itama ta Kai Mata kafa, kafin kace me sun rufarwa Ameera sai dukanta suke kamar Allah ya Aiko su, duka kuwa bana Wasa ba Meera Kam tun tana Basu hakuri har mgnr ma ta kasa fita sbd mugun dukan da suke Mata, sosai suka farfasa Mata jiki saida suka gaji Dan kansu suka koma kan kujera suna huci, Meera na tsakiyar falon tana fitar da numfashin wahala tausayin Rayuwar ta kurum takeyi ita batasan lefin me tayi ba Amma haka kawai an kamata da duka saikace jaka....,

"Kinsan lefin ki?"

Taji muryar Anty Jamila ta doki dodon kunnen ta, Meera dake kwance ta girgiza Kai batare data kallesu ba,

"Mtwsss.."

Anty shafa taja tsaki itama cikin zafin Rai tace,

"Toh da ki sani da karki sani ki bude kunnen ki da kyau Wallahi kinji na rantse matukar Kika sake Shiga tsakanin mu da samarin mu billahillazi saimun illataki ke kikai Wasa saimun watsa Miki acid a fuska ta kone muga da fuskar da Zaki yaudare su"

Dagowa Kai Meera tayi da sauri tana kallon su da mmki toh ita yaushe ta hadu da samarin nasu? Anty Jamila ta sake katse Mata tunanin da fadin,

"ke Wlh duk yadda kika Kai ga maitar ki toh ki kiyayi kurwar Sageer domin tafi karfin ki Dan ba sa'an Yinki bane kaf Dangin uwarki sai an lalumo an daure su matukar baki saki kurwar sa ba"

gwalalo ido Meera tayi da kunburarren bakinta tace,

"waye Kuma Sageer?"

"Ubanki ne"

Anty shafa ta furta tana zaginta da hannu, Anty Jamila tace,

"au har yanzu bazaki daina Raina Mana wayon ba?"

Meera tace,

"Kuyi hakuri Wlh bansan Akan wa kuke mgn ba"

"Mtwsss..."

Anty Jamila taja tsaki kafin tace,

"Toh da ki sani da karki sani duk uwarsu daya ubansu daya Wannan gayen daya rungume ki a skul yau shi muke buga Miki warning akai"

Girgiza Kai Meera tayi cikin takaici tace,

"dama duk a kansa kukamin Wannan dukan? Sbd Allah ni me zanyi da Wannan Dan iskan?"

Wani wawan Mari Anty shafa ta dauke ta dashi tana huci a kanta tace,

"Naga alama baki daddara da dukan da mukai Miki bane"

ta karasa mgnr tana haurin kafarta, daidai lkcn mom ta shigo parlon, Mom ta karaso da sauri tana fadin,

"yau Kuma me tayi?"

Tayi mgnr tana hararar Meera, Anty Jamila ta matso kusa da mom tace,

"Yauwa mom gwara da Allah ya kawo ki"

mom ta zauna tana fadin,

"ku gayamin meta muku yanzu na sassaba Mata"

Anty Jamila ta kwashe komai ta gayawa Mom, mom Rai bace tace,

"toh har zaku tsaya ma Bata lkcn ku wajen Mata gargadi? Ai Abu me sauki shine tabar skul din"

"Alhamdulillah"

Anty shafa ta furta da murna tace,

"Wlh shiyasa nakeson ki mom domin kinyi a rayuwa, the best solution shine ta fasa karatun kawai Dan na tabbata matukar tana tare damu bazata barmu muyi kasuwa ba"

Mom tace,

"Ai dole ma Dad dinku na dawowa na sanar masa Aure za'ayi Mata mu huta ni duk na gaji da rikon ta"

"Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un"

Ameera ta furta da karfi tana kallon mom tace,

"Mom na rokeki da girman Allah karku rabani da farinciki na Wlh ni banyi musu komai ba, idan ma zamu daina hada tafiya ne na amince ni ko hostel saina koma Kinga bamu hadu bama bare na kashe musu kasuwa"

Mom tayi Mata mugun kallon tsana tace,

"idan ma Zaki shirya ki shirya Auren ki Nan kusa zansa ayi min tallar ki a masallaci ko Allah zaisa a samu me son ki acan"

Kuka me radadi Ameera ta fashe dashi tace,

"ku dubi girman Allah karku rabani da farinciki na Dan Allah"

mom ta Kare kunnen ta tana fadin,

"Tashi kibar Mana waje kin cikani da ihunki banason ji"

Meera ta Mike a hankali tana share hawaye harta Yi nisa da bakin kofa ta juyo tace,

"mom ki duba maraicin da nake ciki na Rashin iyaye Dan yanzu ni da wacce Bata da uba daya muke karku rabani da dayan farinciki da nake gani naji Dadi Banda wani abokin Hira sai karatuna Dan Allah karku tagayyara min rayuwa"

ta karasa mgnr kuka na cinta kawai ta fice musu a falon, Mom taja wani mugun tsaki tace,

"toh dama wa yake son taci gaba? Ai Banda Abinda nakeso sama da Naga Rayuwar shegiyar 'yar Nan ta lalace"

Anty Jamila na dariya tace,

"yoh mom barta kawai ai tunda Kika samo solution an wuce wajen bakiji yadda Raina yyi fari Tass ba"

mom tana dariyar itama tace,

"ai tunda naji kunce yaron Alhaji Abdullahi Omar Mai fata ne na gigice Kai toh wa yaki arziki? Sai Wanda be samu ba"

Anty shafa tace,

"Shiyasa mukaci ubanta dazu Dan nema take ta Mana asara munaji muna gani."

Nan dai sukaci gaba da tattaunawar su.



~~`
Da dare kuwa Dad ne tare da Mom Bayan ya huta tace,

"Alhji inada mgn"

dad yace,

"inajinki"

Mom tace,

"akan Ameera ne"

Fadar sunan Ameera yasa fuskar dad da take a washe ta dawo ta hade bacin Rai ya bayyana kanta, mom ta danyi munafukin murmushi tace,

"Yarinyar Nan inaga aurenta zamuyi sbd abin kunyar da take neman jawo Mana"

cikin bacin Rai dad yace,

"wani mgnr ta jawo Koh?"

Mom tace,

"samari take tarawa toh dama ta Dade tana Wannan halin da farko na dauka yarinta ne shiyasa ban maka mgnr ba Amma yanzu abin yaci tura Ameera Bata da niyyar karatu samarin banza sune a gabanta shiyasa nace toh gwara na baka shawara a aurar da ita tun kafin ta jawo Mana abin kunya"

zumbur dad ya Mike Yana kokarin zura jallabiya cikin fada-fada yace,

"Ameerar ce duk take Wannan halin baki gayamin ba? Yau kuwa zancin ubanta a gidan Nan"

yyi mgnr jikinsa na rawa tsanar yarinyar na Kara tasiri a ransa, da sauri mom ta Mike ta rike shi tace,

"haba Alhji abin ai bekai har haka ba shawara fa muke? Kawai yanzu ka amince shine bukatar Amma bawai kaje ka sameta ba da girman ka da komai Bayan ni na dace na sametan"

fasa tafiyar dad yyi ya zauna yace,

"aure Kam Babu fashi dama Alhji buba ya taba min mgnr yaran Nan cikin shafa ko Jamila nace karatu suke toh yanzu Abinda yafi sai na bashi Ameera idan yanada bukatar hakan"

dariyace taso kwacewa Mom Amma ta danne sbd tuno waye Alhji buban me Mata uku ga katon ciki Kuma kowa ya sani auri saki ne dashi yaransa sun haura arba'in kowa da uwarsa wasu a daki biyu, wani daya, wani uku gashi Nan dai ko a wajen be kyale ba bunsuru ne na gske ba kowa yasan halinsa ba sbd fuska biyu gareshi, Cikin tsananin farinciki mom tace,

"Kai Masha Allah kayi Mata zabi mekyau kuwa kaga kenan abun bazai ja lkci ba tunda a shirye yake"

"kwarai kuwa"

Dad ya furta Yana murmushi, Itama murmushin tayi Amma na munafurci tana kissima yadda take shiryawa Ameera mugunta.



°°°°°°°°°
A bangaren Dr Omar kuwa koda suka koma tun daga bakin kofar gida ake musu sannu har suka Shiga gidan Amma da kowa yaji yadda abin ya juye sai ahau sallallami Ana tausayawa mlm sale, Ba kowa ke Basu lbrn ba sai Saratu Bata gajiya da fadawa mutane mlm sale baya mgn, abin na yiwa Dr. Omar ciwo Amma Babu halin ya nuna Mata hakan Dan shi bega dalilin da zaisa tayita yadawa ba kamar abin be dameta ba, oho ko a kwalar rigarta haka taci gaba da harkokin ta na gida.


Da sassafe kuwa Saratu ta shirya da nufin zuwa gidan Aikatau din ta, Dr. Omar na tare da mlm sale a daki ya kalleta lkcn tazo dakin tace,

"Maru idan Sahabatu ta dawo kace basai tayi abincin dare ba Zan taho dashi"

Maru ya kalleta da mmki, kasa shiru yyi yace,

"ummah nace jikin Abba fah?"

Saratu ta wurgo Masa Harara tace,

"toh Dadi uba so kke ka nunamin bansan meye tausayi ba? Inace tun jiya nake tare dashi har kawo yanzu? Shikenan a gindinsa Zan tare bazan nemi na Kaina ba?"

Girgiza Kai Omar yyi yace,

"kiyi hakuri ba nufina kenan ba"

"Mtwsss..."

Saratu taja tsaki tace,

"Kai ka sani kowa ya sani mlm bazai iya mgn ba Toh me ya rage ayi Masa? Kaima lalaci da Rashin sanin darajar nema yasa ka zauna har yanzu baka fita ba Banda haka me zakaji agun Wanda dashi da dutse duk daya?"

Rai bace ya dago Yana kallon umman zuciyar sa na suya Yana dannewa Tabbas Wannan mgnr da aka fada kan mahaifin sa badan Allah yasa Umma bace Babu me hanashi yiwa mutumin dukar fitar hankali, huci kawai yake kasa-kasa batare da yace komai ba, a hankali mlm sale dake hawayen takaici ya lalumo hannun Dr. Omar ya fara matsa Masa a hankali yasan yaron Yana da zuciya sosai Amma Kan Saratu Yana hakuri matuka har tsoro yake kar watarana ya hadiyi zuciya kan Abinda take masa, Saratu kuwa na Gama balbalin masifar ta tawuce tabar gidan.


Shiru dakin ya dauka idon Dr. Omar yyi Jajir shi gaba daya gani yake baida sa'a a Rayuwar sa, dukda zurfin ciki irin nasa yakan kasance cikin Nishadi da walwala aduk lkcn da suke Hira da mlm sale toh Dan farinciki ma dayake ji babushi yanzu sai zaman kurame, hawayen da yake gani fuskar mlm salen ba karamin daga Masa hankali yake ba Dole ya fita Dan neman Masa mgni bazai iya jurar kallon sa cikin Wannan halin ba,

Dan gyaran murya yyi ya kalli mlm sale, mlm sale yyi murmushi Dan zuwa lkcn ya goge hawayen fuskar sa ya kalli Dr. Omar din ya girgiza Kai, Dr. Omar ya fara mgn cikin nutsuwa yace,

"Abba kayi hakuri da duk Abubuwan da suke faruwa, sannan inaso ka rungumi Abinda ya sameka a Matsayin kaddara Insha Allahu zaka samu sauki duk inda mgnin yake zanyi kokari na Nemo maka shi Insha Allahu kada halin da kke ciki ya saka a damuwa ko wani halin muna tare dakai Babu Abinda zai faru d izinin Allah"

murmushi me ciwo Abba yyi a ransa Fadi yake ni na dace na Gaya maka Wannan kalaman Omar, Wannan kalaman dakai sukafi cancanta Omar, Kaine ya dace a tausayawa Omar, Rayuwar ka na cikin garari Omar, Omar da gatan ka, Omar Kai ba karamin mutum bane, inama inada yadda zanyi kaji zantukan zuciyata Omar?

Mlm sale ya karasa mgnr a ransa yanajin zafi da kuncin halin da yake ciki, a fili kuwa Dr. Omar saidai yaga mlm sale Yana murmushi da hawaye zaton sa yanajin dadin tausar zuciyar sa da yake ne besan cewa murmushi me ciwo mlm sale yake ba. Kusan dai Dr. Omar shiya kasance da mlm sale a Wannan ranar, saidai Dr. Omar yyita zance shi kadai mlm sale na murmushin takaicin halin daya samu kansa silar matarsa Saratu.



*****
A bangaren Ameera kuwa yadda taga rana haka taga dare gaba1 hankalin ta a mugun tashe yake sbd yadda mom tazo ta Tabbatar Mata yadda sukayi da dad kenan aure Babu fashi, babban bacin ranta kuwa yadda su Anty Jamila suke ta Mata dariya suna siffanto yanayin Alhji buba sai taji tamkar duniyar ta juye Mata a haka sukayi bcci suka barta hakan ya Bata damar tashi cikin dare tana kaiwa Allah kukanta.

Washe gari kuwa Ameera naji na gani taga su Anty shafa suka tafi makaranta tsabar Basu damu da kr2n ba ko files din nasu Basu dauka ba haka suka tafi,

Dad yyiwa Alhji buba mgnr Ameera kamar kuwa dama jira yake take ya amince yace idan Babu damuwa zaizo da yamma dad yace sai yazo, mom tana gida haka tayi ta sa Ameera aiki da gyare2 gaba1 sai Ameeran ta fita hayyacin ta, toh dama ba cikin kwanciyar hankali take ba wani tashin hankali ya sake samunta duk sai ta birkice kamar figaggiyar kaza.



*****
A bangaren Sageer kuwa ya Dade Yana takaicin cizon Meera a hannun sa, a Jima ya duba karshe ya Kira mutanen sa ya Tabbatar musu da su fara sawa Meera ido Dan gani yake idan be kekketata ba bazai huce ba Sam. Washe garin ranar kuwa da wuri zugar motocin nasa sukayi convoy zuwa B.U.K, suna barin gidan Saratu na zuwa sai kurar wucewar su ta gani, washe baki tayi tace,

"Dana kenan kanajin dadinka Nima dab nake da a dangwali Arzikin Nan Dani"

tayi mgnr tana shigewa cikin gidan itama.



••••�?
Dr. Omar na Shirin zama Bayan ya Gama shirya mlm sale da safe mlm Sale ya riko hannun sa, Dr. Omar yace,

"da mgn?"

Mlm sale ya girgiza Kai, Dr. Omar ya zuba Masa ido yace,

"toh Abba Inajin ka"

mlm sale yyi murmushi ya tashi tsaye hade da riko hannun sa suka fito, binsa kawai Dr. Omar yyi Yana jira yaga me yake nufi, sai gani yyi sun nufi dakinsa, Laptop dinsa ya dauko ya bashi yyi alama da hannunsa zuwa waje sannan ya girgiza Kai, Dr. Omar da sharp brain dinsa ya hango Abinda yake nufi yace,

"Wai na tafi hospital?"

Mlm sale ya girgiza Kai Yana washe baki, Dan murmushi Dr. Omar yyi Yana girgiza Kai yace,

"Abba ai ni Ina Nan tare dakai Zan dinga tayaka Hira"

mlm sale ya fara Girgiza Kai Yana hade fuska ya nuna kirjinsa da hannunsa sannan ya nuna bakin kofa Yana kallon Dr. Omar, Dr. Omar ya lumshe ido Yana shafa sumar kansa tabbas ya fahimci me Abba yake nufi wato idan ya Isa dashi toh ya tafi hospital din kenan, bazai iya musu da Abban ba Kawai yace,

"toh shikenan Abba duk yadda kace hakan za'ai"

Murmushi Abba yyi Yana Dan bubbuga kafadar Dr. Omar din, shima murmushin Dr. Omar yyi kafin ya karbi jakar laptop din nasa, sallama yyiwa Abba ya tafi dama cikin shirinsa yake tsaf, Yana dagawa Abban hannu harya bar gidan Bayan ya rufo kofa.

Tsaye Abba yyi Yana goge hawayen dayake ta rikewa tun dazu, shi gaba1 tausayin Dr Omar din yake, ya rasa dame zai taimaka masa ya gano asalin sa, Addu'a ya fara yi a ransa Yana fatan Allah ya kawo wata mafitar dazai tona Asirin Saratu.
8/15/20, 8:01 PM - Ummi Tandama: *ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA...🐓*
( _Ko Ana Muzuru Ana Shaho Sai yayi_)





Na
*Nuceeyluv😘*




12...



Kamar yadda Alhji buba yace hakan ce ta faru da yamma sai gashi cikin gidan su Meera yazo ganin ta, Meera na daki ta hada Kai da gwiwa sai kuka take ta rasa inda zata dura ranta taji Sanyi,

"Ke taso Yana jiranki a parlon baki"

Taji muryar mom ta daki dodon kunnen ta, a tsorace ta dago tana kallon mom tace,

"Dan Allah kuce ya tafi Wlh bana sonsa"

mom ta saki wata muguwar dariya tana tafi tace,

"Au Ashe? Lallefa 'yarnan wuyanki ya Isa yanka kin tashi a wajen Nan kuwa ko saina zo na harbe ki da kafa?"

Ta karasa mgnr cikin tsawa, jiki na rawa Meera ta tashi tana jawo hijab dinta zata saka Kan doguwar rigar ta, da sauri mom ta fisge hijab din tana kallon jikin meera yadda rigar tabi ta lafe jikin meeran sai ya fito da shape dinta karara tsaki Mom taja Dan tun ba yauba itama takejin haushin Kirar Meera da ace 'yarta ce ba karamin jari zatayi da ita ba, wani siririn gyale data gani Kan gado ta Miko Mata tace,

"karbi Wannan Zaki sa"

Zaro ido Ameera tayi tace,

"kiyi hakuri mom bazan iya sawa ba"

mom ta wurgo Mata Harara a tsawace tace,

"Kin saka ko saina watsa Miki Mari yanzu?"

Ta karasa mgnr tana zaro ido, karba Meera tayi da sauri jikinta na Bari, dakyar ya rufe Mata jelar gashinta haka ma dai Saida gashin ya fito ta baya sbd tsawon d yake da shi kallon kanta tayi ko mazaunan ta ma besan da zaman gyalen ba ko Ina na jikinta ya manne da rigar, ta dago a hankali da nufin ta roki mom ko zata barta sai kuma taga an bita da mugun kallo, haka ta hadiye mgnr Tata tayi hanyar kofa, tsaki Mom ta sake ja tabi bayanta itama, a parlo mom ta Mika Mata Tray me cike da snacks da drinks Akan takai masa har bakin kofar parlon bakin mom taje Saida ta Tabbatar Meera ta Shiga sannan ta juya duk Wannan Abubuwan mom tanayi ne sbd tasan halin Alhji buba akwai sakin hannu, haka taci gaba da harkokin ta tana dariyar mugunta lokaci zuwa lkci, Koda Meera ta Shiga parlon bakin kasa motsawa tayi daga jikin kofar,

Yana Nan zaune shirim kamar kayan wanki sai latsa wayar hannun sa yake besan da shigowar Tata ba sbd wasu hotunan banza da yake gani na Mata tsirara, ganin tsayuwar bazata amfanar da ita da komai ba Meera tayi shahada kawai ta karasa ciki hade dayin sallama, har lkcn hankalin sa na bisa Kan wayar beji shigowar Tata ba, mmki ne ya Kama Meera tace a ranta ko bayaji sosai ne? Haka ta karasa a hankali ta aje tire din hannun ta gaban glass din dake gaban Alhaji buba, karar Ajewar tiren ya ankarar da Alhji buba daidai lkcn ya dago da kansa take kuwa idanun sa suka sauka Kan Albarkatun Meera data sunkuya wajen aje abin hannun ta, wani irin Abu yaji ya ziyarci kansa Yana washe baki,

Meera tayi saurin gyara gyalen kanta tana Kare kirjinta ta koma kan kujera tadan dosana sai gyarawa take ta kasa sakewa musamman data ga yadda yake kallon ta, Alhj buba dake zaune

Please Login or Register in order to submit comment