Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya bashi shawara ya Kara aure kodan ita ameeran tunda mace ce sai a samu me kula da ita, sosai Dad ya gamsu da Wannan shawarar harya Shiga sahun zawarawa Dan neman aure,

Ana haka Allah ya hadashi da Sadiya(Mom) Sadiya bazawara ce Dan tayi aure harta haihu Yara Mata biyu Shafa'atu da Jamila, Karshe auren ya mutu ta dawo gida zawarci, Cikin ikon Allah dad ya nemi auren Sadiya batare da Bata lkci ba ta amince musamman data ganshi da maiko, kafin auren ya shaida Mata yanada yarinya me suna Ameera Sadiya tace ai kar yaji komai da na kowa ne zata rike Ameera da Amana, dad yaji Dadi kwarai da Wannan kalaman nata batare da Bata lkci ba aka daura aurensu cikin aminci, a kwana a tashi Sadiya tayi renon Ameera na marmari da ganin ido Bayan wata guda kuwa ta fara yunkurin fadar qudurin ta wajen Dad,

Wata Rana suna tare ta nemi Alfarmar dad akan tanaso ta dawo yaranta gabanta sbd Yara Mata ne rikesu Dole sai uwa sbd tarbiya, Dad ya amince Mata sbd yaga yadda take nuna kulawa akan Ameeran sa, a takaice dai yaranta sun dawo sannu a hankali Ameera ta fara ganin banbanci a gidan, kafin wani lkci har an fara janye hankalin Dad akanta Saiya kasance Shafa'atu da Jamila sun fita nuna Isa da gidan ubanta akanta, Saiya kasance zuwa yanzu Ameera itace meyi musu duk wata wahala ta gida Dad Yana kallo bazaice komai ba saima hantarar ta da yake idan tayi lefi Ameera dai sai gani tayi kamar Wanda aka canja Mata Dad dinta me tsananin sonta zuwa wani can daban kamar besan wacece itadin agareshi ba. A kwana a tashi Babu wuya a wajen Allah sai gashi Ameera dakinta ya koma shine nasu Aunty Shafa haka wardrobe dinta shine nasu kayanta ya zama nasu sbd da kadan suka fita a shekara a surar jiki kuwa ta fisu shape saima ragewa da sukayi, ita Kuma me daki kayanta ya koma Ghana masgo me cike da kodaddun kaya, Kuma wajen kwanciyar ta shine dandanin kasa komai Sanyi kuwa.

A haka Ameera ke rayuwa a gidan mahaifin nata tamkar Bora, inda Allah ya rufa Mata Asiri tana zuwa school har yanzu tare suka fita a secondary yanzu kuma zasu Shiga B.U.K.


*CIGABAN LABARI*

.....✍�?
8/15/20, 8:00 PM - Ummi Tandama: *ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA....🐓*
( _Ko Ana Muzuru Ana Shaho Sai yayi_)





Na
*Nuceeyluv😘*






6...�?




*CIGABAN LABARI*


�?..Lokacin da Saratu suka rabu da Nas direct gidan Alhaji Abdullahi ta tafi Dan karma wani ya zargeta a unguwar su, tun daga bakin gate din gidan take kallon part din Sageer so take taje Amma tana tsoro sbd idan akwai mutumin da Sageer ya tsana ya Raina a gidan to ya biyo bayanta hakan ma Yana daga Mata kafa ne sbd Mummy (Hajia Aisha) Dan akwai ranar daya fara ikirarin saita bar gidan sbd shishige masan da takeyi ya tsani hakan shiyasa yaso a koreta, hakan be samu ba sbd Mummy ta Hana takan ce Masa itama tamkar uwace a wajen sa Dan ta Dade a gidan uwa uba yadda taga saratun na nuna masa soyayya sai abin yake Mata dadi matuka a zaton ta duk cikin zaman tare ne batasan makarkashiyar dake kasa ba Dan Saratu soyayyar uwa take ma danta cikin dabara.

Tana waige tana kallo haka taci gaba da tafiya sai ji tayi ance,

"kalli gaban ki Mana"

a tsorace ta juyo gabanta Nan taga hajjaju a tsaye gabanta ta rike kugu, Saratu ta danyi yake tana daidaita nutsuwar ta tace,

"sannu Hajjaju an fito Shan iska ne"

Hajjaju tace,

"a'a na fito ran gadi ne"

tayi mgnr tana hararar saratun har yau jininsu be hadu ba Sam, Saratu tadan matsa zata wuce tace,

"Allah ya huci zuciyar ki"

Hajjaju tace,

"me kike leke tun dazu da kika shigo gidan?"

Ta katseta d tmby, a diririce Saratu tace,

"ba...ba komai Hajjaju"

Hajjaju taja tsaki tana kallon saratun tace,

"bansan meyasa Kika nacema Wannan shedanin yaron ba dukda ya fito fili ya nuna baya bukatar ki Amma kamar an rura Miki wutar manne Masa kullum baki da aiki sai shishige Masa da neman duwawun zama na rasa me Kika gani jikin sa yaron da cikakken hankali be Gama isarsa ba bare yasan Annabi ya faku"

duk yadda Saratu taso boye bacin ranta kan yadda Hajjaju ke aibanta Mata da abin ya faskara wani irin kalllon tsana ta dago tana yiwa Hajjaju kamar ta make ta a wajen, wara ido Hajjaju tayi tace,

"ke ni kikema Wannan kallon?"

Da sauri Saratu ta girgiza kanta tana matsawa gefe tace,

"Yi hakuri sauri nake"

tayi mgnr tana barin wajen da sauri cikin kunar zuciya, binta da kallo Hajjaju tayi tana rike haba tace,

"Oh! Yau nake ganin ikon me sama"

tayi mgnr itama tana nufar part dinta.


Saratu na zuwa dakin da take zama idan ta Gama aikin gidan ta fara safa da marwa hade da dunkule hannunta cikin zafin zuciya da takaici, ita kadai ta fara mgn tana fadin,

"Wai harma? Harma Wannan tsohuwar ta Isa ta zagar min yaro? Itadin banza? Toh Wlh bazata Sabu ba, Dole nayi mgnin tsohuwar Nan me Kama da zubin 'yan tauri, shegen kwarin jiki gareta kullum tana Nan a dire kamar Bata tsufa Yasin sai tayi Dana sanin aibatan min yaro da take daga kanta Zan fara tarwatsa farincikin Ahalin Mtwsss..."

Ta karasa mgnr tana Jan tsaki,

'lpy Anty sara?"

Taji anyi Mata mgn a Bayan ta, da sauri Saratu ta juyo Safna ce a bakin kofar tana kallon ta, Dan washe baki Saratu tayi tace,

"Safna har kin dawo? Tun yaushe Kika shigo?"

Safna tayi murmushi tace,

"yanzun Nan na shigo inata sallama bakijini ba shigowata dakin kenan naji kinata tsaki"

wata wawiyar ajiyar zuciya Saratu tayi tace,

"karki damu Safna Raina ne ya baci Amma yanzu ya wuce muje kici abinci na dafa Miki pebarayit(favourite) dinki"

Dariya Safna tayi tana maimaita kalmar da Anty Sara tace, yyinda Saratu take tunanin ya kamata ta koyi sawa bakinta linzami tun kafin ya kaita ya baro ta musamman da ko jimawa ba'ayi ba sbd azarbabin zancen ta mlm sale yajiyo sirrin da suka binne shekara da shekaru,

a haka suka nufi part din Hajia Aisha zuwa yanzu Saratu itace meyin abincin 'yan gidan sbd sawa da Hajian tayi aka koya Mata kala2 shiyasa ta kware wajen iya komai.



*****
Dr. Omar kuwa Saida suka shafe 2hrs suna lecture manyan Doctors d professors ne a cikin hall din sosai suka karu da lecture din da akai musu shiyasa lecture ta zama special Dan Basu cika lecture ba yanzu sunfi zama a hsptl sbd final year dinsu da suke sai time to time suke haduwa a hall, karfe hudu suka fito cikin hall din shi da frnd dinsa Dr. Sadeeq,

Direct Masallacin dake cikin makarantar suka nufa lkcn anata Kiran Sallah, anan suka Shiga ciki Bayan sunyi Alwala Nan aka tada ikama, Bayan sun idar ne suka fito Dan komawa hsptl suga jikin Abba,

Sadeeq ne ya zunguri Dr. Omar dake gyara hannun rigar sa yace,

"gafa mutumin ka can"

Sadeeq ya fada Yana 'yar dariya, Omar yace,

"wa kenan?"

Yyi mgnr Yana dagowa kansa,

"Mtwssss..."

Yaja dogon tsaki Yana ci gaba da gyara hannun rigar sa, dariya ce ta sake Kama Sadeeq kafin shima ya hade fuskar sa sbd kusanto juna da sukayi ba kowa bane a gaban nasu face Sageer hade d mutanen sa suna take masa baya cikin wata irin shiga ta Rashin mutunci kananun Kaya ne a jikinsa wandon jins dinsa da kadan ya wuce gwiwa gashi burgujeje sai wata facing cap daya saka ya juyar da gaban baya keyar Kuma a gaba, wuyansa zagaye yake da sarka haka hannun sa daya saka Dan karfen Abu kamar awarwaro hannayen sa sakale cikin Aljihun wandon nasa Yana taku daidai hade da kwambo Ana bokare baya Kai kace jinsin inyamirai ne,

Yana tsakiyar mutanen nasa wasu Kuma a bayansa, A ka'idar Sageer Abdullahi Omar Mai fata Babu Wanda ya Isa yasha gabansa idan Yana tafiya, sannan Babu Wanda ya Isa ya tanka Masa kokai Dan uban waye yanzu zai yaga maka rigar Rashin mutunci tunda ya shigo skul din aikinsa kenan manyan ciki kowa ya tsuke bakinsa sbd girman Matsayin da mahaifin sa yake dashi ba iya Nigeria ba harta wasu kasashen sunsan da zaman sa babu me iya tunkarar mahaifin sa yakai korafi akan dansa shiyasa yake tsula tsiyarsa yadda ya gadama batare da su iyayen sunsan wacce wainar yake toyawa ba, Amma fa duk Wannan Wulakancin da yake bai taba haduwa da Wanda yaji a duniyar sa Yana mugun shayin sa da shakkar sa ba sama da DR. OMAR SALEES, idan akwai Wanda yake tsoro toh ya biyo bayansa saidai yyi kukari Amman bazai iya yiwa Omar din komai ba hakan yasa duk skul din ake sarawa Omar Mata na rububin sa sbd ya cika gwarzon namiji Kuma Namijin Zaki dake baya bi takansu shiyasa Sam be besan wainar da ake toyawa ba.

Abinda ke kular da Sageer kenan sbd shi yanada son luntsuma luntsuman 'yan Mata da an bincika sai a fada Masa ta Dade da matowa kan soyayyar omar, shiyasa duk kyawun budurwa da surarta yake amfani da kudinsa wajen siye zuciyar su.

Sun iso Dab da dab still Omar Yana gyara hannun rigar sa ko kallon Sageer din beyi ba yyinda Sadeeq Kuma ya zaro wayarsa Yana latsawa Yana jiran yau Kuma wanne wasan za'a buga? Dan shi Dan kallo ne badan Omar din bama Tabbas shima bazai iya ja da Sageer din ba, Sageer Ya kafe Omar cikin matsiyacin kallo hade da muguwar Harara daidai lkcin Omar ya Gama gyaran rigar hannun nasa Ya dago kansa fuskar sa a hade ya harde hannun sa saman kirjin sa bece komai ba, Sageer ya kawar da fuskar sa Yana muzurai ba abin ya karta Rashin mutunci ba ayi Masa Wanda ya fishi Dan haka ya kalli sauran mutanen nasa yace,

"guys let's go"

yyi mgnr Yana rabewa gefen Omar din hade da bouncing kamar zai tashi sama, Nan suka barsu a tsaye, Dan cije lips dinsa Omar yyi kafin ya saki hannun sa sukaci gaba da tafiya Sadeeq kuna ya maida wayarsa Aljihu yace,

"Kai Amma fa ka Gama da gayen nan Duk fadin makarantar Nan Babu Wanda yake dagawa kafa sama da Kai hatta malamai be barsu ba"

Dan kallon sa Omar yyi kamar baxai ce komai ba can Kuma yace,

"lusaraye ne dukansu Banda hakan me suka gani jikin Wannan kazamin suke Jin shakkar sa?"

Sadeeq yace,

"ai ba daga Shidin bane kowa yasan waye ubansa Dole Abi komai a sannu matukar anaso a tsira da mutunci"

cije lips Omar yyi Yana shafa sumar kansa da hannu daya, dayan hannun Kuma ya rike kugun sa cikin takaici yace,

"that's why bazamu taba ci gaba ba a Nigeria cos kowa kansa ya sani da ace muna hada karfi da karfe wajen fadawa manyan mu gsky komai dacinta Tabbas da an rage wulakanta mu a Wannan kasar shiyasa wasu masu kudin Sam Basu dauki talakawa a bakin komai ba sbd sunsan Ana tsoron su sbd kudin su"

Yyi mgnr Yana dunkule hannun sa hade da kaiwa dayan naushi, dafa kafadar sa Sadeeq yyi yace,

"look Dr. Bafa lefin uban bane da ace kasan Alhaji Abdullahi Omar Mai fata da zakace Sam Albasa batayi halin ruwa ba sbd shi mutum ne dayasan Kimar Dan Adam, yasan mutunci da tausayi ga talakawa, mutum ne me kyakkyawar zuciya toh kasan Ba duka Dan Adam ke samun yadda yakeso ba shiyasa nake ganin Allah ya jarabce shi da tantarin yaro ne Dan ya gwada karfin imanin sa dukda dai Rashin mutunci da Sageer yake Yi mafi yawa iyayensa Basu sani ba Dan Babu me iya tunkarar su da zancen"

sauke ajiyar zuciya Dr. Omar yyi yace,

"Allah ya kyauta."

"Ameen"

Dr. Sadeeq ya furta Nan suka shige mota Dan wucewa hospital, Sadeeq na kokarin Jan motar baya yaji an buga Masa glass, Dan tsayawa yyi sannan ya zuge glass din nasa tsaye take jikin window tana kallon su da murmushi Dr. Sadeeq ya Dan saki fuska yace,

"a'a Dr. Amina baki wuce ba?"

Dr. Amina tace,

"Wlh har Zan Shiga mota Naga Kuna Shirin tafiya shine nazo wajen ku Dan tun a hall nake dubaku ban ganku ba"

tayi mgnr tana kallon Dr. Omar daya hade fuska sosai ya juyar da kansa dayan barin, Dr. Sadeeq yayi murmushi Dan yasan kwanan zancen yace,

"Lpy kike ta neman mu?"

Dr. Amina ta Miko Masa wata envelope tace,

"gashi ka bayar"

tayi mgnr tana nuna Dr. Omar da ido wato ya bashi, Dr. Sadeeq Yana 'yar dariya yace,

"no problem Dr."

Dr. Amina tace,

"Tnx u"

Tayi mgnr tana bar musu wajen, Dr. Sadeeq ya fisgi motar da sauri sukabar School din gaba1 batare da kowa yace da Dan uwansa komai ba.


•••••••�?
"Oh my God!"

Anty Shafa ta furta tana sake kallon tsarin makarantar ta B.U.K, Anty Jamila ce ta fito tace,

"kaii Bari na Kira Mana Afra Dan yanzu ta zama 'yar gari itace kadai zata nuna Mana inda zafafan gayu suke"

"Exactly"

Anty shafa ta furta tana murmushi, Meera ce a gefen su itama wara ido kurum tayi tana hamdala ga ubangiji daya kawota Wannan stage din da Dadi da ba Dadi gashi yau dai da izinin Allah zata fara karatu a makarantar, suna tsaye Afra ta iso wajen su cikin iyayi da shewa suka rungume junansu, Afra tace,

"Wlh naji Dadin zuwanku kawaye na yanzu skul din zata fi min Dadi"

tayi mgnr tana gyara skirt dinta daya matseta sosai, Anty shafa ta nuna wacce ke gefenta tace,

"Afra Wannan fa"

Afra tayi dariya tace,

"Wannan da kuke gani surry kenan itama 'yar hannu ce anan muka hadu, surry ga kawayena da nake ta baki lbri Wannan itace Shafa'atu Wannan Kuma Jamila Amma muna kiransu da Shafna da jamcy sbd Dan takaitawa"

tayi mgnr tana dage gira, Dake itama surry 'yar duniya ce tace,

"Kai Amma Nima naji Dadi kwarai Shafna da jamcy hop zamu zama kawaye"

tayi mgnr tana Mika musu hannu,

"sosai ma kuwa"

suka furta a tare, Nan suka sake rungume juna, surry ta kalli Meera dake gefe tace,

"waccar fa? Naga kamar tare kuke?"

Jamila tadan yatsina fuska tace,

"oh 'yar aikin mu ce fah sbd samun guri Dad dinmu har skul ya biya Mata gashi tare zamuyi"

Da mmki Meera ke bin jamcyn da kallo, Anty shafa kuwa dariyace ta Kama ta cikin wayancewa tace,

"Tabbas hakane Zaki iya sata aiki anytime dalilin hadamu ma kenan sbd dad dinmu baison mu wahala"

surry tace,

"wow how I wish Nima Zan kawo 'yar aikina duk inda nake?"

Surry tayi mgnr cikin karya sbd itadin ba kowa bace, Afra tace,

"toh duk wannan a aje gefe mu samu waje mu zauna Dan nuna muku pics din zafafan maza"

"yeeeyy Nan suka hau shewa da tafi suna barin wajen"

a darare Meera ta bi bayansu rike da files din hannun ta, wata kasan bishiya sukaje gun ba mutanen sosai ga kujeru jifa2 a wajen suka samu kujerar data fi nesa da wajen suka zauna Nan Afra ta bude wayarta Dan nuna Musu zafafan maza, Meera data Dan rakube a gefe a Dan tsorace tace,

"Anty shafa ko naje na fara Mana registration din?"

Anty shafa ta juyo tana hararar ta tace,

"tun dazu jira kike ace kiyi? Sai kace remote Mtwsss"

Ta karasa mgnr tana juyawa inda Afra ta Nuno musu hoton wani, Binta da kallo Meera tayi a ranta tace da tayi gaban kanta sai tayi lefi, yanzu kuma data tmby ya zama lefi ita kenan kullum a cikin lefi take...., Tana Wannan sakar zucin ta nausa cikin makarantar Dan lalumen inda Department dinsu yake.
8/15/20, 8:00 PM - Ummi Tandama: *ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA...🐓*




Na
*Nuceeyluv😘*



7..�?


Acan bangaren Saratu kuwa koda suka Isa falo anan suka tarar da Hajia Aisha zaune a falon tadan kishingida tana kallo shigowar su yasa ta dawo da hankalin ta kansu hade da Amsa musu sallamar da sukayi, da gudu Safna ta dale jikin Hajian cikin jin Dadi tace,

"mummy na dawo"

Hajia Aisha tace,

"oh ni Safna saikin ballani zakiji Dadi Koh?"

Tayi mgnr tana gyara zamanta, dariya Safna tayi tace,

"Kai mummy idan ban hau ba waye zai hau? Nice fa Auta"

Tayi mgnr tana juya idonta, Hajia Aisha ta kalli side din Saratu datake dining area tana zubawa Safna abinci Amma haushi ne fal ranta harga Allah ta tsani safnar Nan Kai ita duk Wanda zaisha Mata gaba bataso atho haka kawai tana sa ran yaronta shine zai gaji dukiyar Alhaji sai tashi guda a haifo wata can daban? Mtwsss.. Koda yake Safna karamin Alhaki ce maganin ta cikin sauki zatayi Dan ta batar da ita a duniyar...

"Saratu kinaji kuwa?"

Hajia Aisha ta daga muryar ta sosai sbd tanata mgn saratun bataji ba dalilin kogin tunanin data Afka, da sauri ta dago kanta tana yaken Dole tace,

"Ah Hajia mgn kike?"

Hajia Aisha ta tsare ta da ido tace,

"tun dazu nake Miki mgn kinyi shiru akwai Abinda ke damunki ne?"

Girgiza Kai Saratu tayi d sauri tana washe baki sosai tace,

"Babu komai Wlh ban jiki bane kawai"

ta fada tana tahowa da abincin hannun ta wajen su sbd Safna tace a kasa zataci, Hajia Aisha ta girgiza Kai kafin tace,

"cewa nayi ko baki tafi bane? Sbd dazu kinzo kinmin sallama kin wuce gida sbd Babu aiki yau sosai"

daramm kirjin Saratu ya buga ita Sam ta manta Ashe tayiwa Hajia Aisha sallama, cikin wayancewa tace,

"au ah... Hakane fah Wlh Saida naje gida Naga Ashe na manta key din gidan anan shine na dawo na dauka"

Hajia Aisha tace,

"ai da kinyi waya sai driver ya kawo Miki sbd rage wahala"

dariya Saratu tayi tace,

"haba Hajia ai Babu komai Wlh"

Hajia Aisha tayi murmushi kawai, Saratu tace,

"ko akwai wani aikin nayi?"

Hajia Aisha tace,

"Babu wani aiki dama Wannan uban taurin ne kayan abincin sa gasu can idan Safna ta Gama saita Mika masa"

Da sauri Saratu tace,

"kawo nakai masa"

Hajia Aisha ta bita da kallo kafin tace,

"So kike yauma kuyi drama kenan?"

Saratu tace,

"karki damu Hajia kinsan yaran zamanin Nan haka suke Abinda yaron Alhaji keyi Sam baya damuna sbd nasan watarana zai daina"

kallon ta Hajia Aisha tayi cikin tausayi ta rasa meyasa Saratu ke shanye duk wani wulakanci da Sageer yake Mata tana ganin girman Saratu sosai sbd kaunar da take yima danta Sageer shiyasa take tsayawa tsayin daka sosai Dan kar Sageer ya Raina saratun sosai Dan ta lura Saiya iya zabga Mata Mari a Wannan Rashin mutuncin nasa, a fili kuwa murmushi tayi tace,

"ai shikenan kikai masa"

murnace ta Kama Saratu har Yana bayyana kan fuskar ta, ta nufi dining area da sauri ta dauki basket din da aka sa Masa komai ta fice a falon, fitar ta keda wuya Safna dake Shan drink a hannunta ta kada Kai tana 'yar dariya tace,

"tabdijam"

Hajia Aisha tace,

"Lpy?"

Safna tace,

"Anty Sara Mana ita da Yaya lamarin su kamar Shirin film"

ta fada tana dariya, Hajia Aisha tace,

"banson gulma Safna"

Safna ta Mike tana Mika hade da salati tace,

"Bari naje na watsa ruwa sai naje gun Hajjaju mu rakashe"

Hajia Aisha tace,

"Kunfi kusa itama dazun Nan tabar Nan"

Safna tana taka stairs d sauri tace,

"Aiko nasan tana jirana muyi Hira"

Nan ta wuce dakinta itama.


~~~
Saratu Kam a darare ta wuce part din Sageer tasan a Wannan lkcn Yana makaranta dukda zuwa yanzu Bayan la'asar ne cikin sanda ta Shiga dakin tana waige a hankali ta tura kofar ta Shiga, sauke ajiyar zuciya tayi data ga Babu kowa a falon, tsayawa tayi tana karewa tsaruwar falon kallo ranta fari tas tanajin wani Nishadi a ranta duk fadin gidan Nan Babu inda takejin dadin zuwansa da kasancewa cikin farinciki sama da part din danta Sageer, shiyasa ko bazai Gaya Mata me Dadi ba zatazo taga yadda danta ke rayuwa cikin daula dajin Dadi, har hango kanta take sun mallaki dukiyar Alhaji Abdullahi yyinda ta zamo itace tamkar Hajia Aisha me mulkar gidan da nuna Isa akan komai, takanji takaici idan taga tana musu aiki saidai ta kudurta a ranta na lkci ne sbd d zarar ta shafeta a Bayan kasa ita da dukkan Ahalin gaba1 toh daga ranar ta zama me cikakken iko wani kayataccen murmushi ne ya kwace Mata data hangi hoton Sageer an mannashi jikin bango cikin Shiga ta Alfarma, a fili tace,

"yanzu da Wannan shegen miskilin yaron ne a Wannan daular Koh?"

Tana nufin Dr. Omar,

"Yadda yake da tsinannen isar Nan ace shine a wajen Nan ai da anga yadda ake mulki, Mtws"

tadan ja tsaki,

"haka naso yarona Sageer kayi Amma ka tsaya shiririta Babu me yabon ka sai Fadar aibinka musamman waccar tsohuwar"

wato Hajjaju, tunowa da Abinda ta aikata ga mlm sale yasa tayi saurin ajiye kayan abincin cikin sauri ta fito har tana hada hanya kafin wani lkci harta Isa dakin da take zama jawo Jakarta tayi ta duba mgnin da boka ya Basu Yana Nan a ajiye kamar yadda yake, zuge jakar tayi ta rayata Tabbas Dole ta binne layar Nan da wuri kafin a samu matsala, a gurguje taje tayiwa Hajia Aisha sallama sannan tabar gidan gaba1.



°°°°°°
Koda Saratu taje unguwar su lkcn yamma ce akwai masu zaman kofar gida, tana isowa zata Shiga gida mlm Shamsu ya taso Yana fadin,

"Saratu ya Abinda ya faru Kuma?"

Yyi mgnr cikin sigar jimami, Saratu ji tayi kirjinta ya buga sosai kodai mutuwar mlm sale yyi dgske? Amma sbd kada ta bada kofar a zargeta tayi fuska hade da zaro ido irin batasan meya faru ba dinnan tace,

"me kke cewa mlm Shamsu? Wani Abu ya faru ne?"

Tayi mgnr a jere, mlm Shamsu ya dafa Kai,

"Allahu Akbar Ashe bakya Nan koh, mlm sale ya zame jikin karfen gado jini ya dinga malala kamar an balle kogi abin ba dadin ji Dan suna asibiti tun safe har yanzu shiru"

sauke ajiyar zuciya Saratu tayi a boye Amma a fili kuwa cewa tayi,

"yau na Shiga uku ni Saratu"

ta fada tana Dora hannu akai, mlm Shamsu yace,

"sai hakuri tsautsayi ne"

da sauri Saratu tace,

"Bari na aje kayana na tafi asibitin"

Nan tabar shi tsaye ta wuce gida da sauri, tana Shiga gidan kuwa taja tsaki,

"aikin banza yoh ni daya mutu ma da zanfi kowa murna da hakan Dan har yanzu be tsira daga gareni ba saina toshe bakinsa tunda niyyar sa tana Nan Dole yana samun Dama Saiya tonamin Asiri nikuwa Abinda bazan lamunta ba kenan Sam"

a gurguje ta samo fatanya da mlm sale ya sakale jikin rumfar su, dake gidan dama be wani wadatu da siminti ba sbd farfashewa da yyi Saiya bawa Saratu damar cika burinta, cikin karfi ta dinga Sara kofar dakin nasa a gurguje tayi Rami Medan zurfi kafin ta fiddo layar jakar ta ta binne a ciki, tana maida fatanyar kenan aka shigo gidan a tsorace ta waiga ganin sahabatu ce yasa ta saki ranta, Saratu tace,

"yau kin dawo da wuri kice kasuwa tayi kyau"

Sahabatu na ajiye kula tace,

"ai umma na Gaya Miki Nima na waye zuwa yanzu na daina kwashen abinci"

Saratu ta washe baki batare da tayiwa kalmar fashin baki ba tace,

"shiyasa nakeji dake 'yata maza Shiga kiyi wanka ki huta ga abinci can na taho Miki dashi"

Sahabatu tace,

"yauwa umma me abincin 'yan gayu"

Saratu tace,

"ai nasha fada Miki wata Rana saidai ki bayar indai irin abincin Nan ne"

Sahabatu tace,

"toh umma kullum mgnr kenan yaushe wataran dinnan zatazo ne?"

Ummah tace,

"baki yadda Dani bane?"

Sahabatu tayi 'yar dariya tace,

"Toh ya na iya? na yadda zance"

tayi mgnr tana wucewa bandaki. Kwafa Saratu tayi ta bita da Harara, Wayarta data kunna taji tana Kara da sauri ta dauko ta cikin jaka, dagawa tayi tana fadin,

"Alo"

Shiru akayi ba'ace komai ba, can ta sake fadin,

"waye ke mgn?"

Daga dayan bangaren Omar ne daya zubawa Abba dake kwance ido cikin tausayawa bawai baida abin fada bane kawai Yana tunanin wacce amsar za'a bashi ne, can dai ya daure yace,

"Ummah..!"

Daidai lkcn Saratu na Shirin yanke layin kenan taji muryar sa ta daki dodon kunnen ta, wani kululin takaici ne ya mamaye ta itafa ba komai yake karawa saratun takaici ba sai yadda taga Omar din Yana Abu kamar na asalin mahaifin sa Alhaji Abdullahi muryar su iri daya, tafiyar su iri daya, cikar zarra da mazan taka iri daya banbancin su shine wancan ya manyanta shikuma Wannan matashi, yanzun ma ji tayi kamar Alhajin ke mgn, a harzuqe tace,

"sbd Debewar Albarka da Rashin ganin girman na gaba dama Kaine Dan wulakanci inata mgn kamin shiru?"

Tayi mgnr zuciyar ta na zafi har cikin ranta take jifansa da mugayen kalamai tana fata su tabbata a kansa danya daidaice ya lalace a ganin ta ko ba ita ta haifesa ba ai ta shayar dashi ko saboda Wannan bakinta zai Kama shi.

Rintse

Please Login or Register in order to submit comment