Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuwa koda hajia mariya ta dawo ta samu nasara ƙone!,na wurin mallam ne dana isa gidan an taro ana kuka domin rai yayi halin sa!,mutuwar wulaƙanci babu wasu sassa na jikin shi,gawan tayi baƙi ta sale kamar an ƙona shi da wuta.

Muna wurin manyan yaran shi maza na ƙoƙarin gyara shi,sai ga lanti ta shigo a guje kamar mahaukaciya da dogon ciki tana kuka....,gaban mamanta ta faɗi tana haƙi!,muna haɗa ido ta shiga nuna ni tana son magana amma nayi wani siddabaru maganar ta kasa fitowa domin nasan arcewa mariya tayi tazo ta faɗa abunda ta gani cikin dare!.

Rungume ta maman su tayi cikin rarashi tana faɗin;mallam lokaci yayi sai mu bishi da addu'a ba kuka zaki yi ba wanan mutuwa nashi mai ban al'ajabi kamar wanda matsafa suka saka a gaba!,nan take ta sake kallo na cike da mamaki!

mallam ya mutu?,mutuwa mai ban al'ajabi!,kenan ni na kashe shi tunda bana son shi ko?,nasan tunanin dake zuciyarta kenan amma ya kasa fitowa kawai ta yanke jiki ta faɗi.

Aka yayafa mata ruwa lokacin ana shirye shiryen sallace mallam,koda ta farfaɗo naƙuda ya taso mata...,yan uwan mallam suka shige da ita ɗaki ana kula da ita.

Maƙabarta muka wuce...,har muka dawo tana fama da naƙuda na nufi gida tare da faɗa wa mariya duk abunda ya faru,ta tausaya mata sosai tace mu koma tare da ita har da unguwar zoba dake cikin barrikin(dama inada mota da kwamnati ta bani),haka muka kwasa har yarana yan shekara ɗaya da wata takwas.

Muna nan gida abu yaƙi gaba yaƙi baya da yake haihuwar fari ne kuma wattani bai kai ba sai da akayi awanni goma sha biyu sanan ta haifi ɗanta namiji ɗan wata bakwai(bakwaini).

Murna da farin ciki dana tsinci kai na ko haihuwar yan biyu ban yishi ba domin ALLAH ya ɗaura mun son yara maza,nan take na mashi kiran sallah a kunne tare da mshi huɗuba da sunan baffa nab(shafi'u).
Da zamu wuce maman su ta nemi alfarma in barta agidan a cigaba da kula da ita sanan idan da hali tana so a cika wa mallam alƙawarin shi(yaro yaci sunan shi).Nace mata tau kawai muka nufi gida.

Washe gari muka haɗa duk abunda ya kamata a kai mata muka tafi har lokacin kuka take bata mana magana yaronta na rungume jikinta,nan nabar mariya da yara na wuce wurin aiki.

Kullum nan mariya da yara ke yini sai dare zan tafi da ita,duk da babu jituwa a tsakanin ta da lanti ko kaɗan amma yan uwanta na yaba mata sosai.
Ranar suna kuwa a massalaci aka raɗa wa yaro suna nan yan uwanta maza sukaji sanarwa sunan yaro shafi'u!,suka dawo gida suka faɗawa maman su wacce bata so haka ba amma tayi shiru dai.
Ita lanti ba irin haukan da bata yi ba wai ba zata sake shayar da yaron ba kuma sai na saketa!,sai da maman su ta tsawata mata sanan tayi shiru amma ta na Ƙullace dani.

Lokacin na kamu da wani irin sonta wanda ban san lokacin da haka ta faru dani baa,kwata kwata ban son ɓacin ranta duk da wulaƙancin datake mun kullum ina laƙe gidan su saboda duk ranar da ban ganta ba babu kwamciyar hankali har mariya ta gano haka sai dai idanu ta sa mun domin tana da kaƙuri kuma tana son duk abunda nake so.

Bayan kwana ki arba'in lanti ta  dawo gida na da sabbin babin cin mutunci kala kala domin bata kula da yaro har shayar dashi ta bari.

Hajia mariya ta haɗa shi da yan biyu tana shayar dasu domin tayi alƙawarin sai sun shekara biyu zata yaye su. Abun ya mata yawa tun da safe zata masu wanka ta gyara gida tayi abinci babu aikin da lanti keyi.

Ranar kwananta da ƙarfin tsiya nake kwatan haƙƙi na....,rayuwa na cigaba da tafiya har aka yaye yan biyu lokacin shafi'u nada wattani shida a duniya kwatsam lanti ta sake samun wani cikin mai laulayi matuƙa,tayi kuka sosai da barazanar zata zubar har na tsorata na kai ƙaranta wurin maman su wacce ta ce bata yafe ba idan har ta sake saɓa mun!,sanan muka samu sauƙinta har ta haihu lafiya aka sake samun namiji wanda yaci jafar shima dai anyi shagali wanda yasa har hajia mariya ta nuna kishinta a fili yadda nake nuna soyayya da kulawa akan lanti da yaranta.

Wanan dalili yasa na miya mana hajji(nida ita),na shirya mata tafiya bauchi wurin yan uwanta domin taga gida  kafin mu tafi aikin hajji saboda hankalinta ya kwanta.

Lokacin data wuce da yara ne ,na ɗauko hadiza yar uwan lanti ta dawo gidan ta taya ta zama saboda hidima zai mata yawa duk da jafar yayi wata biyu amma akwai rigima kuma tafi damuwa dashi akan shafi'u.

Sati biyi na ba hajia mariya amma kwana uku kawai tayi sai gata ta dawo tana kuka.....,koda na tambaya tace ai yan uwanta sun haɗa kai da maman su an ci mata mutunci tare da mata gargaɗi kada ta sake zuwa inda suke tunda mijinta nada dukiya ta zaɓe shi a kan su,bayan a sanadin ta mahaifin su ya mutu da baƙin ciki ta bijire masu!,koda tayi magana maman su tace bata buƙatar ganinta daga yau kuma ƙarshenta ba zai taɓa yin kyau ba tunda ta zaɓe shi a kan su!.

Rarashinta nayi akan idan mun dawo daga aikin hajji zamu tafi tare...,cikin ikon Allah Lokacin zuwa aikin hajji yayi muka tafi aka bar yan biyu wurin lanti.

Tunda muka tafi mariya bata wani yi aikin hajji ba saboda rashin lafiya da tayi fama dashi har muka dawo. Koda aka duba shigan ciki ne wanan dalili yasa bamu samu zuwa bauchi baa.

Lanti ta fara nuna kishi ƙarara da baƙin cikinta a fili yadda taga ina kula da hajia mariya domin na lura ta fara sona.

Cikin ikon ALLAH kuwa hajia mariya ta haifi ɗanta namiji wanda yaci sunan mahaifinta abubakar sadik.Lanti tace ina wuta ta saka hajia mariya!,don me zata haifi namiji?,har ta zaɓi sunan da take so kuma in biye mata bayan ita baa saka sunan nata mahaifin baa!.

Fitinar safe daban,na dare daban sai bala'i,wata rana taci kwala na sai na sake ta ida  na cika haihuwar iyayena!,ba tare da wani tunani ba nayi mata saki  ɗaya.

Ta ɗauki jafar suka wuce gidan iyayenta...,hajia mariya ta shiga tashin hankali tare da tuna mun alƙawarin dana ɗauka wa mallam!,nace babu ruwana duk sonda nake mata ba zan lamunta cin mutuncin iyayena baa.

Maman su tayi tayi inzo a mayar da ita na share da lamarin su har ta gaji ta dawo da ita da kanta tare da kalamai masu tsauri akanta,"muddin ta kashe aurena kada ta kuskure a nufi inda suke,ko bayan ranta bata yafe ba".

Tsakanin mata da miji sai ALLAH ai kuwa muka koma kamar wasu sabbin ma'aurata saboda tsabar soyayya da kula da juna . Shekara ta zagayo  muka koma hajji tare da ita saboda hajiya mariya ta sake samun wani ciki gashi sadik shekaran shi ɗaya

Haka dai muka ci gaba da zama da daɗi ba ɗaɗi har hajia mariya ta haifi marwan(yara huɗu kenan),babu jitowa a tsakanin su zai zafin kishi da habaici duk da bata biye mata.

Muna nan sokoto har hajia lanti tayi haihuwa huɗu itama(shafi'u,jafar,hamza da umar),sanan na samu ƙarin girma zuwa matsayin CP(commisioner of police),aiki na ya dawo abuja a lokacin.

Mun dawo kenan na haɗu da hassana wacce banufa ce abinci suke sayarwa a bakin office ɗin mu,saboda tsabar natuswarta yasa naji ina sha'awar auren taa. Lokacin dana gabatar wa matana da maganar zan ƙara aure ai kuwa hajia lanti tace sai na saketa domin ta wuce ayi mata kishiya kuma tasan makircin hajia mariya ne.

Ban kulata ba rashin mutunci sai gaba yake yi ....,ranar da aka kawo amarya tayi rashin mutunci na fitar hankali ai kuwa na mata saki ɗaya(ya zama biyu kenan),tace bata zuwa ko ina tunda na shiga tsakaninta da yan uwanta nan zata zauna har ta samu miji tayi aure!.
Ashe tana da cikin muhammad,amarya ta tare amma idan ban gida hajia lanti bata bari ta sake!,lokacin ne ban sani ba ta nemi ɗaya daga cikin flayers  na ƘUNGIYAR EIYE tana son shiga cikin su domin ta samu power na musamman!.

Ya nuna mata su na dabam ne a cikin ƘUNGIYAR EIYE domin suna shan jini da cin naman mutane,sanan suna sacrifice na mutum duk wanda ƘUNGIYA ta buƙata dole ta bayar.

Tace ta amince idan har zata samu ƙarfi fiye da wanda muke dashi domin muzguna mana ta ɗauki fansa a kan halin da muka saka ta tare da kashe mahaifin ta(mallam).

Nan take tayi blood oath aka bata matsayi a ƘUNGIYAR kamar yadda suke yi tare da neman abunda ke cikin ta idan har mace ce a matsayin sacri na farko da zata yiwa ƘUNGIYA!,ba tare da shakka ko tsoro ba ta amince.

Bamu sake gane kanta ba har cikin jikinta ya bayyana mugun abu iri iri ke faruwa a gidana a bayyane wani lokaci sai da safe mu gani!,koda na tuntuɓi father paul shine ya sanar dani wanan mugun nufi nata!,kuma bamu da ikon fitar da ita ko hanata ƘUDIRIN ta domin ƘUNGIYA ɗaya ce sai dai ba zasu taɓa aminta ta cutar damu ba sai dai abun yayita bibiyan taa.

A kwana a tashi hasarar mai rai lokacin haihuwa yayi ta sake haifan namiji,baƙin cikin data shiga baa magana kamar zata  yi hauka.

Dama mariya tasan komi sai bata kulata ba lokacin dama gidan nan na sabo dana saya amma ɗakuna ɗaɗaya ne guda huɗu sai babban palo da ɗaki ɗaya wanda yake zaman nawa.

Ranar suna yaro yaci muhammad  kuma duk abunda akeyi nayi mata har mota natura aka zo da yan uwanta don faranta zuciyarta amma bata huce baa.

Koda suka yi meeting da flayers sai suka ce mafita ɗaya ne ta maida aurenta dani ta samu a haifi mace domin ƴa mace suke buƙata daga ɓangarenta shine zai bata daman cikar burinta a kan mu.

Inata lura da ita tayi sanyi matuƙa tana neman shiri gashi dai ta riga ta haihu babu sauran idda a kanta...,wata rana ta samu hajia mariya ta roƙeta ta mun magana a mayar da ita ɗakinta.

Dama nima jira nake yi ban ɗauki lokaci ba muka sake mayar da auren mu,kyautatawa babu irin wanda bata mun!,domin ta bar shiga tsabgar hassana.
Shiru shiru daga ita har hassana babu wacce ta sake samun ciki sai hajia mariya wacce sai data samu sau huɗu yana lalacewa kuma baba ya faɗa mana sharrin hajia lanti ne mafita kawai ta haƙura da haihuwar haka nancy!,ya bamu wani magani da zata yi amfani dashi na tsarin iyali.

Hassana ta shiga damuwa sosai akan rashin haihurta,wanan dalili yasa na biya mata hajji ta tafi domin yin addu'a na musamman ko Allah zai bata ita. Amma shiru har ta dawo aka shekara babu ko ɓatan wata!.

Ana haka hajia lanti ta sake samun ciki,faɗan farin cikin data shiga baa magana wanda duk a sanadin zata bada abunda ta haifa wa matsafa ne asha jini ta samu biyan buƙata!.Ita dai hajia mariya ta rungumi yaranta huɗu wanda duk suna karatun boko a makarantar kuɗi har su shafi'u da yan uwanshi na saka su.

Lokacin haihuwa  yazo da tangarɗa domin yaro baa cikin mahaifa yake ba !,dole sai an mata aiki a cire babyn sanan   likita ya bada shawara tayi tsarin iyali domin samun isashen hutu kafin ɗaukan wani ciki. Ban ɓata lokaci ba da gangan nace a rufe bakin mahaifar kawai idan an cire babyn!.

Ba'a ɓata lokaci ba aka shiga aiki wanda aka dace tare da ciwo ɗa namiji mai lafiya wanda yaci sunan  usman.

Idan nace zan faɗa maku irin  hauka,rashin hankali,cin mutunci da tonon asirin da hajia lanti ta tashi mun a gidan nan palon nan wallahi duk sai kun tsane taa!

Domin tayi ikirari idan ban saketa taje ta aure wanda zai bata ƙwan yara mata ba sai ta tona muna asiri muna cikin ƘUNGIYAN ASIRI sanan ta yi amfani da ƙarfinta duk ta kashe kowa!

Wanan dalili yasa na cike mata sakinta uku!, dama  dai muhammad  bai muhammad  bata damu dashi ba bare kuma usaman wanda yayi sanadin aka rufe mata bakin mahaifa!,da madara ya rayu.

Father paul ke faɗa mun flyers  sun ɗaga mata ƙafa ne akan idan ma bata haifi mace ba duk sanda muhammad  yayi aure ya samu mace ita zasu yi amfani da ita domin biyawa hajia lanti buƙatar ta akan mu.

Har ta gama idda bata tafi gidansu ba duba da bakin da maman su tayi mata tacigaba da zama ɗakinta nima ban koreta ba kuma bana shiga tsabgarta duk da abunda take so take aikatawa a gidan kuma har yau ɗin nan soyayyarta na nan daram cikin zuciyata.

Allah ya mun buɗi sosai na gyara gidana zuwa ginin zamani yadda yake a yanzu,hassana Allah bai bata haihuwa ba sai na basu kuɗaɗe masu kauri suka fara kasuwanci.

Nasan dukan ku babu wanda bai san lokacin dana auri suwaiba baa?,domin yarinya ce ƙarama yar babban gida, tunda ta ganni a TV shike nan ta tashi hankalin ta babu wanda take so sai ni lokacin har na kusa aje aiki duk manyan yarana kun yi aure"banda muhammad   da usman".

Yadda ta shiga damuwa yasa na aure ta haka nan har itama Allah ya bata haihuwanta uku kuma taje aikin hajji kamar sauran,gashi duk suna kasuwanci sosai.

Yanzu dai ya rage tsakanin hajia mariya da hajia lanti su faɗa abunda suke ɓoyewa akan zainab da mami!,domin dai nayi alƙawrin sai sun bar mun gidana tunda har ita hajia mariya ta kasa haƙuri ta biyewa hajia lanti suka janyo wanan tonon!,abunda ake rufewa baa so kowa ya sani domin bamu san hukuncin daƘUNGIYA zata yanke mana baa!

Follow
Vote
Comment
Share.
[7/1, 15:42] Leema: *🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
*NA*

*L££MA*

wattapad
*@leemaMuhammad826*

_Sadaukarwa gare ku_👇🏻
*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*

*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*


*L££MA novel fans group📙I cherish the way you people care,love, respect,honour and admire me.You are indeed a blessing to me, I'm always greatful💖*






*🅿31-32*



Hajia mariya ta rarrafo ƙasa inda mijin su ke zaune tare da riƙe ƙafafun shi da hannayenta duka biyu a ƙasƙance,"Alhaji na haɗa ka da girman ALLAH kayi mun rai,kada ka sake ni a cikin wanan hali ba san inda zan tafi baa,kar ka manta a dalilin auren ka na rabu da kowa nawa,a dalilin cikar burin ka na kasance yar ƘUNGIYAR ASIRI,kada ka mun butulci alhaji!".

Gaba ɗaya duk wanda ke palon sai da ya tausaya mata,domin tayi babban sadaukar wa a soyayya.Yaranta sai harar hawaye suke yi tare da jin tsanar hajia lanti na ratsa zukatan mu,itace sillar faruwar komi tunda mahaifinta baya raye.

Alhaji dai kan shi na ƙasa ,zuciyar shi na raɗaɗi kamar an zuba garwashin wuta!,domin da yasan wanan rana zai riske shi a duniya da wuri haka,da addua zai Allah ya ɗauki ran shi kafin zuwan wanan rana.

Hajia lanti kuk take yi sosai mai suti cike da nadama..,tunda ta saka gaba akan wanan al'amari bata taɓa zama ko sau ɗaya tayi tunani akwai ranar nadama da dana sani baa!,yanzu ita burinta bai wani cika baa,asiri ya tono wanda itace silla!.

Ina sauraren ku,idan kuma babu wani bayani zan sallami kowa dare nayi,"ya ƙatse shirun nasu".


Hajia mariya taja majina tare da saurin goge fuska da bayan hanunta sanan ta fara....

Wallahil azeem kamar yadda ka sani kuma ka faɗi a yanzu bani da wata ɓoyayyar manufa akan lanti da ahalinta,bani da burin cutar da ita ko wani nata!,hasali ba a kullum ƙoƙarina inga na dawo da ita akan hanya ta hanyar ƙoƙarin ruguza mugun nufinta akan mami da zainab!.


Cikin mamaki kowa ke kallon hajia lanti....,tabbas hajia lanti ta shirya ganin bayan zainab ne ta hanyar amfani da mami a matsayin yar aikenta,duk abunda ke faruwa na rashin jituwa a gidan muhammad hajia lanti ce sila!,itace tayi sanadin zubewan cikin zainab ta hanyar zuba guba mai muni a jikinta wanda a hankali zai lalata cikin har itama ta rasa ranta!,sanan itace tayi sanadin ɓacewar mami.

Ke!,kima mutane bayani dalla dalla ba'a son ɓata lokaci,"alhaji ya sake zaburo mata".


Tunda na gano mugun nufin hajia lanti a kan mu,kuma na gano itace tayi sanadin lalacewar duk cikin da nake samu a baya har guda huɗu ,sai na ɗauki alwashin ba zan sake bari ta cutar da wani mahaluƙi baa,ba zan sake shiga tsabgarta baa!,nasan nice sanadin komi,saboda a lokacin da na goyi bayan mijina bai aureta ba da mun zauna lafiya. Sai dai ɗan adam baya taɓa wuce ƙaddarar shi a rayuwa,Allah ya nufa akwai rabon ƴaƴa a tsakanin su duk abunda za muyi sai anyi auren.

Nasan tun lokacin haihuwar muhammad da akace shi akeso idan mace ce,Allah yasa namiji ne,usaman ma yazo a namiji aka ɗaure mahaifar taa!,tayi wa ƘUNGIYA alƙawari idan har muhammad ya haifi ɗiya mace zata sadaukar masu a matsayin jinin shi da suka fi buƙata.


Allah yasa akayi auren zainab lokacin kaman hajia lanti ta zuba ruwa a ƙasa tasha saboda farin ciki,kowa shaida ne a gidan nan babu irin soyayya da ƙauna da bata nuna wa zainab ba bayan auren!,kwasam aka kwashe shekaru bata samu haihuwa baa. Nan ta fara fuskantar tsana da tsangwama daga ɓangaren hajia lanti da sauran surukanta wanda itace ta haddasa wanan fitina.

Abun nan daya faru yasa naji zainab ta shiga raina,tausayinta ya kamani, na ɗauki alwashin janta a jikina ta hanyar nuna mata soyayya da kulawa domin bata kariya daga sharrin hajia lanti!.wallahi wanan kawai shine burina a kan zainab ba cutar wa ba.

Ta fuskanci mugayen hali kala kala a wurin hajia lanti ciki har da son raba auren,amma Allah bai nufa ba. Ana tsaka da haka ne Allah ya bata cikin mami har zuwa lokacin haihuwa inata kula da ita. Cikin ikon Allah aka haifi abinda hajia lanti ke muradi"ƴa mace",bata ɓata lokaci ba ta sanar da ƴan ƘUNGIYA.Bincike mai zurfi da suka yi akan ƴar jaririyar suka gano zata zama babban abun alfahari wa yan ƘUNGIYAR EIYE!

Dalili kenan da yasa basu kashe mami baa,sun faɗawa hajia lanti mami zata zamo masu fitila wurin hasko martaba da darajar wanan ƘUNGIYA ta EIYE a faɗin duniya gaba ɗaya,alfama ɗaya da suka yiwa hajia lani shine bata cikakkiyar iko akan mami,zata iya amfani da ita wurin cimma duk wani mugun buri nata akan koma wanene.

Lokacin da yarinya ta fara girma hajia lanti ta ɗauki soyayyar duniya ta ɗaura mata,baya burin tayi nesa da ita domin tana amfani da ita ne wurin hura wutar tashin hankali da rashin zama lafiya a tsakanin muhammad da zainab. Saboda zainab ta kasance mace mai yawan ibada da tsoron Allah,shi yasa bata ci galaɓa a kanta ba sai wurin muhammad.

_Ta kwashe labarin rikicin daya faru a tsakanin su har hajia lanti tayi nasarar zuba wa zainab guba,da yadda akayi ta ceci rayuwar zainab ta hanyar yin abunda bata taɓa aikatawa ba a rayuwar taa(zub da jini)_

Magana ta ƙarshe nasamu nasarar tsiratar da mami daga sharrin hajia lanti ta hanyar turata akure tare da father paul,saboda hajia lanti na mata barazana akan idan bata muzguwa iyayenta ba zata rasa ranta.



Tunda hajia mariya ta fara bada wanan labari muhammad ke kukan zuci wanda yafi n fili ciwo!,babu makawa Allah ya hallice shi ne daga tsattsun azzaluman iyaye musamman mamanshi!,rayuwar shi tazo ƙarshe muddin zainab ta rabu dashi a wanan lokacin da yafi buƙatar ta fiye da kowa.

Zainab dake kuka iya ƙarfinta a guje ta taso tare da shaƙe hajia lanti da wani irin ƙarfin da bata san tana dashi baa!"sai na kashe ki!,wallahi ba zan taɓa yafe mai hakki na ba sai ALLAH ya saka mun cutar da rayuwata da kika yi....,babu wanda yayi yunƙurin ɓanɓareta daga jikin hajia har tayi mai isarta ta zube ƙasa tana kuka mai tsuma zuciya!

Ke hajia lanti abunda hajia mariya ta faɗa a kan ki haka ne?,"alhaji ya tambaya",gyɗa kai tayi tabbas haka ne alhaji nayi ƙudirin rashe zainab ne domin yan ƘUNGIYA sun faɗa mun itace ce mutum ta farko da zata fara kawo mun cikas a aiki na,kuma zata iya zama sillar tonon asiri na!.

Na fara tsorata da lamarinta ne yayin data fara zuwa ma moha da maganar zargin mami,a lokacin hankali naya tashi matuƙa har nace wa moha ya maido mami wurina da zama suka ƙi. Sai kuma ya zamana duk wani shirina tana gani a mafarki!,tun daga nan na yanke shawarar ganin bayanta,haka ba zai yiwu ba dole sai mami bata tare da ita.Sai na fara ƙoƙarin nisanta ta da mami domin cikar burina amma duk da haka mami na ƙoƙari wurin bata kariya!.

Tana mata hanun ka mai sanda ta hanyar yawan faɗa mata sai ta kasheta ko haka zai saka ta tsorata,amma bata jiba.Na yanke zan kasheta ne a hanyar ta na zuwa kazaure Allah yasa tana da sauran shan ruwa bata samu zuwa baa. Kullum idan suka fita tarage ita ɗaya a gida ina ƙoƙarin ganin bayan zainab amma ayi rashin sa'a mami ta dawo ta taimake ta har lokacin da ta samu ciki yan ƘUNGIYA suka tabbatar mun da wanan ciki namiji za'a haifa wanda zai sanadin shafe tarihi na a doron ƙasa!. Wanan dalili yasa na kama mami na ɗaure har sai na gama da zainab.

Aka yi rashin sa'a hajia mariya ta shiga tsakanin mu duk da nayi nasarar lalata cikin amma tana raye.yanzu dai mami ta kufce mun domin yan ƘUNGIYA sun ɗauki abun su.



Alhaji barau ya nisa tare da sauke gwauron numfashi,matana da yarana kun ji irin halin da muka tsinci kan mu a sanadin son zuciya da neman duniya,rufin asirin duniya da kuma neman suna da ɗaukaka.

Mun manta ALLAH shine mai kare bawan sa,Allah ke rufa wa bawan sa asiri,Allah ke ɗaukaka bawan sa a lokacin da yaso.Sauran matan shi biyu ya kalla,"ina neman gafarar ku akan ɓoye maku wanan babban sirri da muka yi,ku gafarce ni kuma kuna da zaɓi idan har ba zaku iya cigabada zama dani ba zan sawaƙe maku kamar yadda nayi alƙawarin rabuwa da hajia mariya da hajia lanti.



Hajia hassana ta ƙara share hawayen da ya kasa tsaya mata tunda aka fara wanan badaƙala,haƙiƙa alhaji baku kyauta mana ba kwata kwata!,wanan babba sirri ne wanda tabbas sai yan ƘUNGIYAR ASIRI kam domin su ne kaɗai zasu iri rufe wanan sirri mai girma har tsawon shekaru masu yawa!.

Ina tare da kai domin kona tafi yanzu ban san inda zan nufa fa,dama uwar riƙo na nake yiwa aiki har ka tausaya mun ka aure ni duk da ni ɗin ba kowa bace,zan cigaba da zama da kai mu haɗu mu nemi mafita wurin manyan mallaman addini har ta ALLAH ta kasance a gare mu.

Hajia suwaiba da taso neman saki sai tayi tunanin lokacin da iyayenta suka hana ta auren alhaji barau sabodaya manyanta sosai cikin mata uku zata shiga,tace babu wanda ya isa ya hana ta auren shi!,iyayenta na son farin cikinta shi yasa suka amince yanzu ga yara uku a tsakani ina zata dasu.


A sanyayye ta furta"nima na aminta zan zauna",yaran ya kalla akwai mai magana?

Zainab tace,Abba ina neman alfarma don Allah ka saka muhammad ya bani takardata ba zan iya cigaba da zama cikin wanan ahali baa!,mami kuma na yafe maku ita duniya da lahira domin ba jini ta bace son ɗa da soyyyar muhammad ya rufe mun ido na aminta muka aikata babban laifi saboda haka nasan tun a nan duniya ALLAH ya fara nuna mana ishara akan shishigi da muka mashi.


Me kike faɗa ne haka zainab?,"cewar alhaji",gaskiya nake faɗa abba har cikin zuciyata ba zan iya cigaba da zama cikin ku baa.Maganar mami kuma;
_Yadda akayi har ta samu cikin mami ta labarta masu,idan baku yadda ba a nemi dr fa'iza ta gidan nan tasan komi_


Wurin ya sake rikicewa da sabon surutai ƙasa ƙasa kowa na faɗin son ran shi....,Abban su ya dakatar dasu ta hanyar janyo takarda da biro da niyyar rubuta sakin hajia mariya..

Hajia hafiza ta dakatar dashi ta hanyar riƙe biron,abba ka rufa muna asiri idan ka saki hajiyan mu ina zata nufa?,kai ka faɗa mana a sanadin auren ka ta rabo da kowa nata!,saboda soyayyar da take maka ta sadaukar da kanta da imaninta ta shiga mugun hanya domin taimakon ka wurin cika burin ka!,yanzu burin naka ya cika zaka mata butulci abba?

Sauran manyan yaran suka saka baki ana bashi

Please Login or Register in order to submit comment