Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai shiga baa.

Haka ko sukayi,sai da suka nufi duk inda ya kamata akayi sanarwa sanan suka nuka sanar da sauran yan uwan su a haɗu a gida akwai taro na gaugawa.

Mami ce duƙe gaban wata mata a wani katafaren gida,sai dai matar ta juya baya baa ganin fuskarta.

shiru ya ratsa wurin daga bisani matar ta furta,ya zama dole ki nisanta  dasu domin cikar burin ki,lokaci da muka ɗiba maki yayi da zaki nisanta kanki da kowa naki mami!

Godiya nake kuma ban manta da alƙawarina a gare ku baa,amma ina neman alfarma a ƙara mun lokaci rayuwar mummyna yana barazanar tarwatse wa,ya zama dole in bata kariya daga azzaluman dake ƙoƙarin ganin bayanta!

Dakata maami!,har sau nawa zaa rinƙa baki dama mahaifiyar ki na wasa da damar ki?,in ce taurin kai ne da ita ko an hanata aikata abu sai tayi?,shike wahalar da rayuwarta ai,abunda baki sani ba kawai suna amfani dake ne wurin tarwasa farin cikin iyayen ki,idan baki nisanta kanki dasu ba sai kin zama ajalin iyayen ki!.

Duk na gare komi fin ƙarfi na akayi,ki sani har yanzu banyi ƙarfin da zan iya bawa iyaye na wani kariya na musamman baa,idan ban bi abunda suke buƙata ba zan rasa iyayena ne!

Zaki rasa mahaifiyar ki ne kawai idan har ta cigaba da yin taurin kai,mudin ta nufi hanyar kazaure sai gawan ta!,yanzun ma da take a cikin gidan nan rayuwarta da abunda ke cikinta na cikin hatsari babba,zama ɗakin mijinta shine babban kariya a gareta ko baki faɗa mata bane?"cikin tsawa ta tambaya",na faɗa mata amma ta kasa fahimta,duk yadda naso hanata fita sai ta bijire,ina neman alfarma a bani dama in kula da ita har ta haifi abunda ke cikin taa,daga nan zan nesanta kai na dasu yadda ko labari na ba rasa taɓa jiba.

Ba zai yiwo ba mami!,ke ɗin yar aiki ke kuma kin isar da saƙon ki a tsakanin su,kin wanzar da farin ciki a zukatan su,lokaci yayi da zaki bar su har abada!,ko kin manta burin ki na son zama shugabar yan
*ƘUNGIYAR ASIRI NE?* ban mata ba ya shugaba na!,shine kike ƙoƙarin wasa da damar ki?,mutane nawa ke neman wanan dama a duniyar
*ƘUNGIYAR ASIRI?* ,amma basu samu baa?.

Lokaci yayi da zaki koma akure wurin mai girma father john domin samun horo na musamman akan wanan buri naki!.

Ina ƙara neman alfarma dai a barni na gana da ahali na kafin tafiya taa!

NA GAMA MAGANATA!,"matar ta faɗa tare da ɓace wa ɓat kamr walƙiya!.


follow
vote
comment
share
[6/8, 14:40] LEEMA: *🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_

       *NA*

          *L££MA*

wattapad
*@leemaMuhammad826*

  _Sadaukarwa gare ku_👇🏻

*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*

*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*

*🅿15-16*

       Ruɗani ta shiga,wani sashi na zuciyar ta na gargaɗinta da bin umurnin shugabanta,yayin da wani sashin ke ƙarfafa mata gwiwa ta koma wurin iyayen ta har sai taga halin da suke ciki sanan ta wuce!,sai dai muddin ta bijire wa umurnin shugabanta rayuwarta zai shiga cikin hatsari wanda zai sanadin rashin cikar burinta.

Idan tayi nisa da iyayenta a wanan lokaci da suka fi buƙatar ta komi zai iya faruwa ciki har da rasa cikin dake jikin mummynta ko rayuwarta.

  Muhammad  da ɗan uwanshi suka garzayo gida bayan sun fi abunda ya kamata a cikin gari,koda suka iso gidan basu wuce ciki ba sashin Abban su nan suka nufa...,da sallama suka shiga cikin babban palon.

_Dattijo ne  fari sol mai matsakaicin jiki,cike da natsuwa da kamala,yana sanye cikin yadi fari da wando ,hanun shi riƙe da babban littafi na addini da alama nazari yake yi_

Wuri suka samu a ƙasa  gefe  suna jira ya kamalla.,sai daya kai aya sanan ya miƙa masu hannu ɗaya bayan ɗaya suka gaisa,"ya iyalen ku?",da sauƙi dai ABBA domin wani al'amari ne ya tunkaro mu a yau ɗin nan..

Ba dai rashin lafiyar zainab ɗin bane"ya tambaya?",cikin jimami shafi'u(babban yayan su muhammad) ya furta,yanzu maganar da ake bamu san inda zainab ɗin take baa,domin dai muhammad  ya barta a nan gidan ya fita hajia ta kira shi a waya wai bata gidan!,gashi ita mamin tun da safe baa ganta ba ,inda ya kamata mun duba bata har wurin yan sanda mun kai rahoto.

Girgiza kai yayi cikin ƙosawa da hali irin na lanti!,kun tabbata ita zainab ɗin basu tare da mami?,A'a ABBA ni da kaina na kawo zainab gidan nan ita ɗaya.

Yanzu me ya kamata ayi?,sanin kan ku ne mahaifiyar ku zaman kanta take yi babu sauran igiyar aure a tsakanin mu,bani da wani iko a kanta yanzu!,tafi jin shawarar mu akan nawa.
Amma ABBA mun riga mun kira sauran yan uwan mu zamu yi zama na gaggawa tare da ita a gaban ka,lokaci yayi da fitar tsabgar muhammad da iyalan shi,iya gwargwado yarinyar nan tana mata biyayya,ranar data gaji fa ba zaa ji daɗinta baa!.

Haka ne shafi'u ALLAH maku albarka,sai ku sanar da ita ai.

Shafi'un ya wuce sashin hajiyar su....,har ɗaki ya same ta,tana ganin shi ta shiga faɗa zainab tayi mata rashin kunya!

Sai da ta kai ƙarshe yace,idan ba damuwa hajia mu haɗu sashin ABBA akwai shawara da zamu yi akan lamarin.

Jimmm ta ɗan yi,shi baban naku ya shirya ko kai?,hajia don Allah ki rinƙa ba ABBA darajar da ALLAH ya bashi ,ko ba komi akwai zuri'a a tsakanin ku an zama ɗaya bai kamata yadda kike ƙoƙarin tuzarta shi cikin jama'a wasu lokutan!

Dataka can wawan banza kawai,duka bunda yake mun bakwa gani ko?,kada ku wuce gona da iri,wallahi wallahi idan ku ka kai ni maƙura sai na bankaɗo wani ƙuli nashi wanda baku sani baa!,idan yaso kowa ma yabar ganin mutuncin shi domin shi da wanan makirar hajia mariya sune musababbin shiga na tashin hankali wanda har yau na kasa fidda kai na,ban san ranar da zai fita baa!.

Ya isa hajia,koma menene Allah yasan gaskiya koma yana bayan mai gaskiya!,kiyi hakuri mu tafi akan ɓatar mami ne dole mu zauna tare a nemi mafita ɗaya.
Mayafi ta ɗauko suka kama hanya zuwa sashin...,koda suka isa sauran yan uwan shi sun iso.

Tunda ta shigo sashin idanun shi fes a kanta domin suna gida ɗaya,sai ya shafe wata mai ganta baa. Duk da haka kullum cikin begenta yake saboda  tana da asalin ɓoyayyen kyau da ba kowa ke gane wa ba kasancewarta baƙa,shekarunta sun ɓoye domin mace ce mai tsafta da kula da kanta,wanan dalili yasa yake matuƙar sonta duk da auren haɗi ne.

Gaisuwar da take amsawa na ɗiyanta ya maido da hankalin shi wurin su,saman kujera mai zaman mutum ɗaya ta zauna ko kallo bai isheta baa.

Shafi'u ya gabatar da addu'a daga bisani ya ɗora;makasu din taruwar mu a nan shine dalilin ɓace war mami da ita kanta zainab a yanzu,mun yanke shawarar taruwa a nan ne domin neman mafita daga iyayen mu.

Allah albarkace ku da zuri'ar ku,"amin ABBA  suka amsa",ina baku haƙuri akan abubuwan da suke faruwa,duk da banda masaniya akan wasu abubuwan dukan ku kun fi kusanshi da mahaifiyar ku,banda laifin da na maku ba?,koma dai menene ku gafarce ni,abunda na sani yarinya kamar mami bata isa barin garin nan ba!,tana cikin garin nan amma a ina?,shine muka kasa gane wa....

Kamar yadda zainab ma tana cikin gidan nan wurin makirar matar ka,kuma dole kayi mata magana ta fito da ita ko wallahi sai na datse igiyar auren su kamar yadda hajia mariyata saka ka datse namu!.

Murmushi yayi irin nasu na manya domin yasan halin lanti sosai tana da matukar kishi mai zafi,musamman akan hajia mariya.

Wanan ba hurumi na bane lanti,ai kin saba yanke hukunci kai tsaye,yanzu ma zaki iya samun ta da maganar.

Huci ta shiga yi,yaran su kan shiga cikin duhu a duk lokacin da iyayen nasu ke irin wanan hatsaniya,kan su na ɗaure wa domin suna hganin kamar akwai  wata ɓoyayyen sirri da basu sani baa!.

Tunda haka ne ku tafi zan ɗauki matakin da ya dace akan ɓatan mami kuma zata dawo...,amma kin san dawo warta a wanan lokaci zai zo da abubuwa na ban al'ajabi?,zai iya kawo tarwatsewar zuri'ar mu!.

Hakan yafi komi mun daɗi dama ni aka bari cikin tashin hankali ku hankalin ku kwance!, gwara asiri ya tono kowa ma ya huta.

Shiru yayi yana jimami,yaran duk an barsu a duhu dai!,haka taron ya tashi babu wani gamsasshiyar mafita.

Tashi tayi  ta nufi sashin hajia mariya har ɗakin baccinta...,lokacin tana ban ɗaki.

Daidai hajia lanti na ƙoƙarin fizgo zainab daga saman gadon,hajia mariya ta fito,"kada ki soma wallahi domin zaa yi kare jini,biri jini!",juyowa tayi suka haɗa ido ko wacce na huci!

Sai me ai ba yau muka fara baa!"cewar hajia lanti",ci goro cikon benci tabarmar kaɗa caca!,sanin kanki ne baki taɓa cin riba a kai na baa!,sai nawa muka kara kina cin ƙasa?

HAJIA mariya kenan!,a baya kenan da  nake ɗaukar darasi a wurin ki,amma yanzu na wuce sanin ki,nayi nisan da kara kaf ɗin ku babu wanda ya isa ya dakatar dani!,ba wanan cikin kike tattali ba saboda tsabar sharri?,burin ki a haife shi in wulaƙanta a idon duniya?,wallahi sai na zubar dashi sanan in lalata mahaifar yadda ko a mafarki ba zata taɓa ɗaukar ciki baa,sanan in dawo da mami ta tona asirin ku daga baya ayi walƙiya ɓoyayyen sirin ko wanne a cikin ku ya bayyana!.

Daga baya kenan lanti!,kada ki manta nice nasa aka auro ki gidan nan domin cikar burin mu,yanzu da burin mu ya cika baki da wata amfani zaman me kike yi?,ince dai da mamin kike taƙama wai zata maye maki gurbin ƴa mace da baki samu ba kamar yadda aka buƙata a haihuwar muhammad ?,yanzu ina take?,taje neman nata burin,tayi maki nisan da ba zaki taɓa iya kamota baa!

NICE nan SHUGABA mariya na tura mami inda tya kamata domin cikar burinta!,domin tarwatsewar naki burin,mu zuba sai na ga bakin ki wallahi lanti!.

Jin wannan hayaniya kamar a cikin bacci yasa zainab ta tashi a razane domin ta gasgata maganganun  da taji daga bakin surukanta!

Yunkuri hajia lanti tayi ta dunkule hannunta na dama gam,ta cije lebenta na ƙasa!,nan take zainab ta fara salati domin mararta ke matukar murɗa mata kamar hanjinta zasu fita.

Ashe hajia lanti abunda ke cikin zainab ta riƙe kam cikin hanunta tana ƙoƙarin ganin bayan shi!,ganin haka hajia mariya ta  yi wani irin gurnani nan take wani haske ya fito daga idanunta kamar wuta ya soki hanun hajia lanti!,

zubewa ƙasa tayi tana gurnani nan a take hanun ya sale kamar wuta ya cinye!

Cikin zafin nama ta sake miƙewa,ba zan taɓa kyale abunda ke cikin zainab yazo duniya ba sai dai yau asirin kowa ya tonu a gidan nan!.

Barin taɓa bari burin ki ya cika ba koda zan rasa raina sai an haifi cikin nan domin shi zai kawo ƙarshen duk wani tashin hankali da rashin jituwa a gidan nan.

Barin kashe ki in kashe zainab ɗin idan yaso zan kashe kai na,wanda ya zamo toshin haddasa komi zai warware.,tsohon ki dake ƙaa shine babban anoba wanda ya ƙirƙiro duk wani mugun abu domin neman suna a duniya,gashi ya mutu ya bar maki gadon mugun abu har ɗiya da jikoki haka zai ta zagaya zur'ar ki!

Cacar baki ya kaure a tsakanin su ko wacce idnunta ya rufe..,a hankali zainab ta sulale daga saman gadon tana dafe da marar ta ta sulale zata bar ɗakin!,hajia lanti ta zabura tare da yin wani irin surkulle wani haske ya bayyana ta watsa shi a cikin zainab!,nan wurin ta zube tana ganin bishi bishi jini mai dubi ya fara bin ƙafafunta a guje kamar an buɗe famfo!

lokaci ɗaya taja dogon numfashi tare da ɗauke wuta.,hajia mariya tayi wani irin yunkuri tare da tattaru duk wani irin bajinta nata da niyyar tunkarar hajia lanti!,a zabure ta buga bangon ɗakin!,hajia mariya ta  hango mami ɗaure saman tsauni a galaɓaice ta fita hayyacinta ai kuwa ta zube a ƙasa cikin mutuwar jiki domin wanan faɗar yafi ƙarfinta.

Dariya mai rikitar wa hajia lanti ta kece dashing!,na faɗa maki wanan ba lantin da kika sani bane?
!,nayi ƙarfin da har abada ba zaki taɓa iya cin galaɓa a kai na baa!

IDAN kika fita a tsabgata zan kyale mami ta tafi inda  take so,amma zainab rayuwarta na cikin hatsari,abunda ke cikinta dai na gama dashi ta hanyar zuba dafi na musamman a jikinta!,kalli nan"bango ta buga wani hoton ya bayyana",zainab ce kwance gefe tana kakarin mutuwa,yayin da zaki na gefe ina cin wani jariri saura kaɗan ya kai ga kaiser...,hajia mariya ta zabura tare da hura iska  wurin wani irin tsawa ya tsarwatsa bangon bat komi ya shafe!.

Daria ta sake yi sosai tana kallon hajia mariya,aikin gama ya gama ai mami na ƙarƙashin iko na sai yadda nayi da rayuwar taal,zainab kuwa awwani ƙalilan uka rage mata a ɗauki gawanta a sashin ki!,kinga alhakin mutuwar ta na kanki ta sake fashe wa da dariya!!!!

~AYI HAKURI DA WANAN~

Follow
vote comment
share.
[6/10, 12:17] LEEMA: *🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
       *NA*

          *L££MA*

wattapad
*@leemaMuhammad826*

  _Sadaukarwa gare ku_👇🏻
*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*

*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*



*Masoya wanan littafi ina ganin saƙonin ku,comments da addu'oi ina maku fatan alheri,Allah saka da alheri ya bamu ikon ɗaukan darussan dake cikin littafin,munanan abubuwan dake ciki Allah bamu ikon ƙyamatar su ya kare musulunci da musulmai a duk inda suke a faɗin duniya amin❤*

*🅿17-18*

  
            Huci hajia Mariya ta shiga yi zuciyarta na tafasa kamar an rura mata wuta a ciki!,tabbas hajia lanti ta gama da ita domin zai wuya ta samu cikar burinta a wanan karo!.

Me kike tunani hajia mariya?,inace ni ɗin ce dai ku ka ɗauki tsawon shekaru talatin kuna musguna wa?,ko kin manta lokacin da na shiga irin wanan hali,a ƙasƙance ina neman agaji a wurin ki,saboda tsabar butulci kika ƙeƙashe ƙasa a ta fau sai kin aiwatar da mugun nufin ki a kai na,wani irin magiya ne ban maki ba a lokacin?.

Yanzu lokaci yayi da zaku girbi abunda ku ka shuka"cikin ɗaga murya take magana",ita zainab ɗin da kike nan nan da ita,wallahi da tasan mugun nufin ki a kanta ba zata taɓa tunkarar inda kike ba,domin kece musababbin shigar wanan ahalin
*QUNGIYAR ASIRI.*

Lokaci yayi da zan fallasa komi kowa ma ya sani idan yaso zuri'ar ta tarwatse kowa ya kama gaban shi!.

Girgiza kai hajia mariya ta shiga yi"kada ki mana haka lanti!,kada ki manta alƙawarin da kika ɗauka zaki riƙe sirrin mu har ƙarshen rayuwar ki".

Ke ɗin nan har kin san ALLAH da girman ALƘAWARI?,babu sauran imani a zuciyar ki domin a bushe ta ke ƙeƙas ,duniya kika saka a gaba,baki tunanin akwai ranar da zaki mutu a saka ki cikin kabarin ki kowa ya watse a barki daga ke sai abunda kika shuka!.

Zaɓi ya rage naki,idan har kin yi alƙawari ba zaki sake shiga tsabgata dana ahali na ba kamar yadda mijin ki ya zuba mun ido,zan cigaba da riƙe maki alƙawarin ki har ƙarshen rayuwata.

Shiru tayi na ɗan lokaci zuciyarta cike  da baƙin ciki akan rashin nasara da tayi a karo na farko tun da suka fara karawa da hajia lanti!,shike nan na aminta amma ki kyale zainab da ranta kada ki cutar da ita,bata maki laifin komi baa.

Mariya barin zainab a raye babban barazana ce a gare mu baki ɗaya,ta riga ta san sirrin mu wanda muka daɗe muna ɓoyewa,shi yasa na zuba guba a jikinta a hankali zai rinƙa cin ta har ta mutu!,shi abunda ke cikinta sai idan ana haihuwa a lahira tayi a can domin na riga na ba dodon tsafi na ya cinye!.

Yadda jariri yake sabon jini fal, haka zan koma kamar wata yar sha shida!,
Wanan shine sirrin kyau na hajia mariya ko kina ƙoƙonto ne?.

Duk naji wanan amma don Allah kiyi wani abu akan zainab ta tashi koda ace zaa daburta ƙwaƙwalwarta ta manta duk abunda ya faru a yau ne ,in har zata tashi babu matsala.

Sanin kanki ne hajia mariya bamu tayar da mutum haka nan dole sai an kawo mana ƙaramin yaro a bawa dodo jinin shi yasha ranshi zai zama fansar a gareta.

Girgiza kai ta shiga yi...,ki duba lamarin nan dai yara suna waje suna jiran fitowar mu,idan aka same ta cikin wanan hali zargin su zai ƙarfafa a kan mu,ina maganar abunda zai yiwu yanzu ne!.

Abu ɗaya zan iya taimaka maki dashi yanzu shine,in bata jini na tasha nan take zata tashi amma ki sani da zarar  jinin yabi jikinta zata iya tsintar kanta a irin halin da nake ciki a yanzu!.

Ban aminta baa!,domin bana burin wanan muugun abu ya cigaba da yaɗuwa a cikin zuri'ar gidan nan.

Ɗaga kafaɗa tayi,yanzu ai ya rage naki duk shawarar da kika yanke ki same ni  a inda ya kamata kuma a lokacin da ya kamata ina fatar kin gane?,shiru tayi mata.

Wasu irin surkule ta shiga yi nan take hanunta ya dawo dai dai har jikinta kamar babu abinda ya faru a sashin sanan ta nufi hanyar fita hajia mariya na zaune a ƙasa tana kallonta.

Tana buɗe ƙofar yaranta suka taso mata fuskokin su ɗauke da alamar tambaya,"ku kwantar da hankalin su zainab na cikin ƙoshin lafiya domin likita yazo ya dubata bacci take yi".

Ajiyar zuciya muhammad  ya sauke,sauran ma suka shiga hamdallah ana faɗin"saura mami".

In shaa Allah itama zaa ganta kada ku ɗaga hankalin ku,muje kuci abinci ko?,muham dai hankalin shi bai kwanta ba tunda bai ga zainab da idanun shi baa.

Sama sama dai suka ci abincin jikin ko wanne a sanyayye baa wani jima ba suka mata sallama banda muhammad  wanda bai san inda zai nufa baa.

Sai da hajia mariya ta tabbatar hajia lanti ta fita sanan ta rufe ƙofar ɗakin gam ta janyo zainab wacce take kwace  kamar matatta zuwa wani  ɗan lungu bayan wardrobe  a cikin ɗakin wanda ba kowa ne yasan dashi a wurin ba. Sai data janye wardrobe  ɗin ta shige da ita lungun wanda ke cike da duhu,kwantar da ita tayi saman wani akwatin katako,gefe ta janyo wani babban riga ja kamar abaya mai hula ta saka yadda ba a ganin fuskarta,wani babban ƙwarya ta ɗauko da ƙahon saniya ta ɗaga sama sanan  ta fara maganganu cikin wani yare a hankali,a hankali har ta fara ɗaga murya!! nan take haske ya bayyana jikin bango nan  hoton mami ya bayyana tana ɗaure jikin tsaunin ta fita hayyacin ta.

Daka mata tsawa tayi"ashe ban faɗa maki kiyi nisa da ahalin ki baa,ya akayi kika zo nan!?",kuka ya kwace mata...,magana zaki yi domin bamu da isasshen lokaci,dubi halin da mahaifiyar ki take ciki a dalilin taurin zuciyar ki!.

Duk maganganun nan da hajia mariya keyi kanta na rufe da hula yadda babu wanda zai iya ganin fuskarta bare a gane itace.

Mami na ɗago fuskarta da ƙyar sai kan mummynta dake kwance kamar gawa!,ihu ta fara tana fizge fizge amma ta kasa kwance wa..,bamu da isashen lokaci ya zama dole ki bar wurin zan kula da mahaifiyar ki amma dole sai an sadaukar da rai domin ya zama fansa akan nata rayuwar da tsiratar dake cikin asiri ta yadda ba zaa taɓa gano inda kike baa,mun rasa cikin dake jikinta ba zan bari ta rasa ranta ba duk da ban taɓa shan jinin kowa ba amma zan fara a kan zainab domin ceto rayuwar taa.

Kuka kawai mami keyi cike da takaicin kanta domin ta ɓata biyu ɗaya bai gyaru baa!.

Ki zauna cikin shiri anjima da dare zan gabatar da duk abunda ya kamata,dana kamala zaki tafi da father john idan kika sake dawo wa rayuwar ki zai kasance cikin hatsari babba babu ruwa na!.

Cikin ƙarfin hali ta furta"godiya nake ya shugabata",ba zan taɓa manta irin dumbin alherin ki agare ni baa duk da har yau ban san ke ɗin mutum ce ko aljan baa,haka ban san dalilin ki na taimaka mun ba.

Wanan ba damuwarki bane kawai ina taimkon ki ne domin cikar nawa burin!.

Tunani mami ta shiga yi yadda ta tsinci kanta a wanan jejin;
_Bayan shugabatarta ta ɓace ta zauna cikin wurin tana saƙa da warwara yadda zata ceci mummynta kafin ta bar garin...,kawai taji anyi wuf da ita idanun ta sun rufe sai duhu take gani kamar makauniya har aka iso jejin aka ɗaure taa!,sai da wurin yayi shiru babu motsin kowa sanan ta iya buɗe idanunta amma wayam ba kowa kuma ta kasa ƙwatar kanta a wurin!_

Surkulle hajia mariya shiga yi bangon ya shafe ta cire kayan sanan ta bar zainab a ciki ta fito tare da rufe wurin yadda babu wanda zai gane akwai wani a ciki.

Cikin ban ɗaki ta ɗauko mopper ta goge wurin da jinin zainab ya ɓata,ta feshe ɗakin da turaren ɗaki sanan ta saka babban hijab ta buɗe kofa ta nufi palo...,mai aikinta ta sama ta gama jera abinci duka.

Ki shirya yanzu driver ya aje ki gidan hafiza zaki kwana can da safe zai dawo ya ɗauko ki!.

Tau hajia ta amsa tana mamakin wanan fita da aka shirya mata da rana tsaka!,barin kai wa maman mami abincin ta ɗaki.

A'a bta tashi daga bacci ba,idan kinci naki kawai ki shirya,"tana gama magana wuri ta samu a palon ta zauna tana daddana waya".

saƙo ta turawa babbar ɗiyarta hafiza kamar haka;
_driver zai kawo mai aikina ta kwana wurin ki kuma bana son dogon bincike sai anjima_ 
tana turawa ta kashe wayar gaba ɗaya.

Zuciyarta cike da saƙe saƙe domin yau zata aikata abunda bata taɓa aikatawa ba a rayuwarta!,ba wai don bata iya bane kawai sai don bata ra'ayi amma ya zama dole ta dubi zainab da mami.

Yau duk wanda ya kalle hajia lanti zai gano tsantsar farin ciki da take ciki domin burinta ya fara cika akan zainab!,bata da wata matsala a rayuwa da ya wuce zainab da abinda ke cikinta,idan har zainab na raye ba zata taɓa samun biyan buƙata ba domin ta kasance mace mai yawan ibada,zai wuya ayi galaba a kanta?,tsatsson zainab zai kasance rufin asiri ne a gareta sai akayi rashin sa'a zainab nada bin ƙwaƙwafi da taurin kai ga ibada wanan dalili yasa namanta da abunda zai fito daga cikin ta zai zamto mai ɗaci a gareta!,cin nama mai ɗaci a gareta na nufin wargajewar duk wani shiri nata!,abunda yasa tayi tasiri akan mami saboda ba jinin zainab bace kuma muhammad  ya sauƙaƙa mata duk wani aikinta ta hanyar sagarta mami ,hakan ya bata daman cusa ƙiyayya mai ƙarfi a zuciyar mami wanda yasa bata burin shan inuwa ɗaya da mahaifiyarta!,bata burin garin farin cikin mahaifiyarta!,burinta kullum ta ganta cikin baƙin ciki da tashin hankali!.

Lokaci yayi da zata rama abunda hajia mariya tayi mata a lokacin baya koda hakan na nufin tonon asirin su gaba ɗayan  ne!.

   Mai aikin hajia mariya ce ta fito cikin shiri..,ƙasa ta zube"na fito hajia",sama da ƙasa ta kalle taa. Idan kin fita ki turo mun driver.

Fita tayi, zuwa can driver ya shigo da sallama.
Gidan hafiza zaka kai ta daga nan ka tafi maraba inda ake gasa kifin nan ka samo wa zainab.

Hajia ai akwai masu yin irin shi a nan bakin kasuwa...,bana son na wurin a maraba zaka tafi ,inace dai nike da mota kuma biyan ka albashi nake yi ko?, Allah huci zuciyar hajia zaa yi yadda kike so.

Tashi yayi ya fita...,sai data tabattar ya wuce an fara kiraye kirayen sallar magrib gidan yayi shiru maza sun nufi masallaci,ta ɗauki niƙab da makulin wata ƙaramar motar ta shiga tare da bata wuta babu kowa a gate don haka a buɗe yake ta fice...

_Motar  data saya wa jikanta na farko nee a nan gidan yake barin shi sai ya shigo yake fita dashi yaron bai wuce sha shida baa,mahaifin shi ya nuna rashin amincewa da kyautar motar a cewar shi yaron yayi ƙarami ina laifi ya kamala secondary school,sai ta aje a wurinta aka mashi tintec idan yazo wurinta yana shiga ya tafi yawo_

Jabi ta nufa har ciki irin  gheto area ɗin nan  ta nufa a guje take sharar gudu yadda zata dawo da wuri...,ba'a jima ba ta isa har cikin wata anguwa da tasan akwai yara sosai,ta samu gefen hanya ta parker tana kallon yara suna wasan su.
Sun fara watse wa ne  ɗaya yazu giftawa ta wurin motar,da sauri ta buɗe ta fito tare da chafko shi sai  cikin motar ta rufe, a zafafe ta zaga gefen driver ta zauna  yaro na ihu amma babu mai ji saboda tintec ce kamar walƙiya ta bar wurin!.

Ganin yaron bai bar kuka ba ta buɗe aljihun motar ta fito da wani mai ta shafa mai a fuska nan take yayi ajiyar zuciya tare da ɓingirewa sai bacci har ta isa gida lafiya ba

Please Login or Register in order to submit comment