Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zamu tafi jumaa mu dawo lahadi ya maki?.

Haba wa daddynta aƙalla na kai wata shida banga iyayena ba mai zai hana mu tafi gobe sai mu dawo monday tunda kana hutu wurin aiki,na samu break a makaranta.

Dakata don Allah tafiyar nan ba dake zamu yi baa!,inace ai cewa kika yi mami na son ganin su ko?,zan kai ta nasan kwana biyu ya isheta ganin kowa mu dawo.

Cikin ɗaga murya take magana wn ahin adalcin ya ishe ni fa!, ya zan raini ciki in haifi yarinya a rinƙa ƙoƙarin cusa ƙiyayya a tskanin mu!

Na rantse da ALLAH idan kaga ban tafi kazaure ba sai dai idan kashe ni zaka yi domin nima haihuwa ta akayi kamar kowa ai...

Cikin Ɗaga murya mami ta furta"idan kika tafi kuwa gawar ki za a dawo dashi na maki wanan alƙawarin!"

Dariya ya kece dashi irin abun ya mashi daɗi....

Miƙewa zainab tayi cike da ɓacin rai"gawata zaa dawo dashi mami?"

Ni dana haife ki kike ƙoƙarin ganin baya na?,murguɗa baki tayi eh ɗin na faɗa ai kema rashin kunya kike yiwa daddyna kullum!

BAata san lokacin data finciko ta daga kujerar ba ta sharara mata wsu irin mari masu lafiya guda uku tare da haɗata da tebur ɗin nan taeke goshinta ya fara fitar da jini...

Barin fara kashe ki idan yaso ki dawo daga lahira ki kashe ni nima!

Tsawa ya daka mata yana ƙoƙarin ƙwace mami a hanun taa....,kina hauka ne zainab?,na rantse da Allah idan wani abu ya same ta kotu zata raba mu!

Daidai lokacin daga samu nasarar hankaɗe ta gefe ɗaya.

Sai me?,ai na jima da sanin wanan ba sona kake yiwa,wanan aljanar ƴar taka ta fini muhimmanci a wurin  na!
Da wanan zaman ƙuncin na gwamma ce  ka bani takar data in ƙara gaba sai ka aureta idanzaka iya dama ai ba jini na bane maniyin ka ne dana wacce aka haɗa ku ni kariga ka lalata mun rayuwa saboda a dalilin ka ƙwan haihuwata  ya samu matsala!

Mari mai rai da lafiya ya wanke ta dashi kafin ta ankara ya ƙara mata tare da jan hanunta zuwa ɗakin baccin su ya wurga ya ƙalgame ƙofa.

Huci yake kamar mahaukacin zaki kamar shi zainab zata na yiwa guri da gasa mai baƙaƙƙen maganganu a gaban ƴar shi?,
Ai kuwa sai ya nuna mata shi ka ɗai keda iko da mami!

bugun ƙofar ta shiga yi taba kuka....,banza yayi yace da mami ta ɗauko hijabinta su fita.

Ta window ta hango fitar motar shi daga gidan!

share hawaye tayi ta nufi ban ɗaki ta ɗauro alwala ta gabatar da sallah wandta ɗauki lokaci tana kai kukanta wuri n mahallici.

Taso ta kira Mamansu ta faɗa mata amma bata don tayar masuda hankali a daren amma tabbas tayi alƙawarin sai ta tafi kazaure a gobe goben nan.

Shiru shiru har goma na dare basu dawo gidan baa!,tun tana duba agogo har ta haƙura tayi shirin bacci...


Fitan su daga gidan yawo ya rinƙa yi da ita cikin garin abuja har ya gaji don kanshi ya dawo gidan.

Horn ya rinƙa watsawa kamar wani mahauci domin mai gadi ya fara bacci mac.., da sauri ya buɗe mashi taba tsaye jikin window tana kallon ikon ALLAH"anya kuwa muhammad baya shan wani abun maye kuwait?"shine tambayar da take yawan yiwa kanta idan taga yana wasu abubuwan.

wani irin fincikota taji anyi ta baya tare da haɗa ta da da dressing mirror sai daya tarwatse duk glass ya soke mata baya, tana ƙoƙarin tayi aka sake janta sai banɗaki tayi tayi ƙofa ya buɗe yaƙi!


-Halimatus sadiya muhammad-

vote
comment
share
[6/2, 21:33] LEEMA: *🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
       *NA*

          *L££MA*
wattpad
@leemaMuhammad826

gare ku_👇🏻

*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*

*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*

*🅿5-6*

             Dafe bango tayi da ƙyar tare da riƙe handle na ƙofar tana jijjigaw amma yaƙi buɗe wa!,bayanta inda ta bugu in  banda zugi babu abunda yake mata. Duk da haka ƙarfin hali kawai take domin ta samu mai kawo mata ɗauki.

Sosai ta galaɓaita kafin wani lokaci ta zube ƙasa tana fidda nishi sama sama saboda azaba!, can taji alamar buɗe kofa ana shigowa...,innalillahi zee ina kika shiga near?"muryan mijinta ta jiyo".

Saboda tsabar galaɓaita ko ƙwaƙwarar motsi bata iya wa bare har ta kai ga mashi alama da zai gane tana rufe cikin ban ɗakin.

Wani sabon hauka ne ya kama ki saboda rashin hankali kin yi kache kache da ɗaki haka?,shiru ba amsa, ya shiga duba ko ina cikin ɗakin har cikin closet da ƙasan gado bai ga kowa baa.

Wuri ya samu gefen gado ya zauna yana tunanin ko guduwa tayi ne bayan fitar su?,sosai yake nazarin ɗakin ganin ko ina broken glass mirror near,window a buɗe.

Hankalin shi bai tafi ban ɗaki ba kawai ya fito harabar gidan ranshi a ɓace ya nufi wurin mai gadi...,bubbuga ƙofar ɗan ɗakin yayi a zafafe!

Ganin yanayin mai gidan nashi da yamman nan yasa ya sha jinin jikin shi sai ga bugun ƙofa kuma.

Ranka ya daɗe barka da fitowa!, kai ina matata ta tafi bayan fita na?

Ranka ya daɗe wallahi tunda ka fita babu wanda ya shigo ko fita daga gidan nan...

Maganar banza kenan"ya katse shi cikin ɗaga murya",idan bata fita ba muje ciki ka nuna mun inda take ko?.

Allah huci zuciyar ka mai gida wanan ai ba hurumi na bane shiga turakar gida. Kasan da haka kake wasa da aikin ka?, infact ko ka fitar mun da matata ta ko in hananta wa hukuma kai a yanzu!.

Ranka ya daɗe ka dubi girman ALLAH ka mun rai wallahi banga fitar uwargida ba, tunda ka fita ina bakin aiki banga fitar kowa kamar yadda na faɗa a farko.

Mami ya hango ta nufo inda suke tsaye tana kwasar dariya!...

A hanzarce ya nufi wurin,yana isa ya tsugunna akan gwiwar shi tare da riƙo hanunta"meya hana ki bacci mami nab?".Daddy  me yasa kai ma baka yi bacci baa?.

Banga mummyn ki bane,tunda muka dawo nake dubata shiru!

Ai nasan inda take!, da gaske kike mami?, eh daddy muje ka gani..."ta riƙo hanunshi zuwa suna tafiya".

Basu tsaya ko ina ba sai ɗakin baccin su ta nufi ban ɗaki tare da murɗe handle ɗin ƙofa ya buɗe, zainab ce kwace shame shame kamar matatta!

A hanzarce ya nufe ta tare da rugumo ta yana jijjiga ta..,idanun shi suka sauka kan bayanta daya jiƙe sharaf da jini  ''subhanallah wa nene ya aikata maki wanan ɗanyen aiki zee?,don Allah ki tashi kada ki mutu ki barni ba zan iya rayuwa ba tare dake ba" cikin ɗaga murya yake magana!.

Ko gezau bata yi baa,ya shiga ƙoƙarin ɗaukar ta da nufin zuwa asibiti idanun shi na fitar da ƙwalla!...,mami ta dube shi cike da tausayawa ganin halin da ya shiga"daddy ina zaka kai ta?".

Asibiti zamu tafi mami idan mummyn ki ta mutu asirina ya tono a duniya!.

Bazata mutu ba daddy ka ajiyeta zata buɗe ido kafin safe.

Tsuru tsuru yayi ya rasa mafita domin kanshi ya ƙulle,mutum na cikin jini ko motsi bata yi ace zata tashi ba tare da an bata wani taimakon gaugawa baa?.

Dafa kafaɗan shi tayi,ka yadda dani daddy zata tashi lafiya lau kamar komi bai faru baa!.

A'a mami ba zan iya haƙuri ba saboda idan ta mutu ba zan yafe wa kai na baa,kinga a dalilin abunda muka mata ta shiga wani hali har ta illata kanta.

Cikin ɓacin rai ta daka mashi wani irin tsawa!"bibiyar rayuwar suke yi na rantse da Allah da ka fita da ita daga gidan nan ƙarshenta yazo!,rayuwar suke nema domin cikar burina ya zama dole in nisanta kai na daku daddy!".

Jin wanan maganganu na fita daga bakin ta ai bai san lokacin daya saki zainab a ƙasa ba!,da rarrafe ya nufi gaban mami tare da yin zaman dabas.
Su wanene ke bibiyar rayuwar mumyn kibbutz?,wani buri nake  ne ba zai cika ba idan kina tare damu mami!?, a wahalce yake furta magana saboda tsabar tashin hankali daya shiga.

Juya mai baya tayi tana sharar hawaye..,bana nadamar shigar ɗaya daga cikin ku mawuyancin hali saboda akan cikar buri na babu abunda ba zan iya aikata wa ba lokaci kawai nake jira kuma da yyi zaku nme ni ku rasa!.

Juyo wa tayi tare da murmusawa,mu bar maganar a yanzu daddy dare yayi ka tafi ka kwanta nayi maka alƙawari mummy zata tashi da sauran kwanan ta a gaba."tana kai nan ta wuce ɗakin baccin ta zuciyar ta fal farin ciki burinta na zama shugabar yar
*ƘUNGIYAR ASIRI* ya kusa cika nan bada daɗe wa baa.

Allaahumma 'innee 'abduka, ibnu 'abdika, ibnu 'amatika, naasiyatee biyadika, maadhin fiyya hukmuka, 'adlun fiyya qadhaa'uka, 'as'aluka bikulli ismin huwa laka, sammayta bihi nafsaka, 'aw 'anzaltahu fee kitaabika, 'aw 'allamtahu 'ahadan min khalqika, 'awista'tharta bihi fee 'ilmil-ghaybi 'indaka, 'an taj'alal-Qur'aana rabee'a qalbee, wa noora sadree, wa jalaa'a huznee, wa thahaaba hammee.

Allaahumma 'innee 'a'oothu bika minal-hammi walhazani, wal'ajzi walkasali, walbukhli waljubni, wa dhala'id-dayni wa ghalabatir-rijaal.

Sune addu'oin da ya rinƙa maimaitawa a bayyana...(anaso idan bawa ya shiga cikin wani mawuyancin halibut,ƙuncin rayuwa,damu wa ko wani abu ya shige maka duhu ka rinƙa maimaita wanan addu'a safe da yamma).

Wani irin natsuwa ya shige shi cike da ƙwarin gwiwa ya sake cicciɓan zainab zuwa ban ɗaki a tsanake ya cire rigar dake jikinta wanda ya ɓaci da jini,famfon ruwan zafi ya kunna har ya taru daidai yadda ba zata cutu ba ya shiga watsa mata a hankali yana danna wuraren data samu raunuka da hand towel a hankali...,sai daya kusa gamawa da ruwan taɗan zabura jin raɗaɗi ga ruwa zafi na ratsa jikinta.

Hamdallah yayi tare da gode wa ALLAH cikin zuciyar shi,zubar da ɗan sauran ruwan yayi tare da taro wasu yana yunkurin ƙara wa ta riƙe hanun shi a wahalce ta furta"ciwo nake ji sosai don Allah ka barni haka nan".

Tausayinta yaji dole ya haƙura a hankali suka dawo cikin ɗakin ta kwanta ruf da ciki sai sannu yake mata a jere....
Rub ya ɗauko mai kyau ya shiga shafa mata tana kuka  a wahalce,sai sannu yake mata har ya gama sanan yaja bargo ya rufe mata rabin jikinta inda babu rauni domin ba maganar saka kaya.

Miƙe wa yayi zai sauka daga gadon ta riƙo hanun shi"kada ka tafi ka barni ni ɗaya zasu kashe niagara!".

Dawo wa yayi ya zauna cike da tausayin ta domin tun lokacin data fara bashi labarin abubuwa na faruwa tsakanin ta da mami bai taɓa gasgatawa ba sai a yau!,tabbas wani mumunar al'amari na shirin tunkaro su nan gaba.

Ba inda zan tafi,dama zan tattara ɗakin ne mu kwanta.

Girgiza mai kai tayi,"ka bari kawai har da safe ba kyau sharar dare".

Shike nan barin sauya kayan jikina mu kwanta tau....,don Allah kada ka barni!.

Babu yadda ya iya dole tasaya shiga jero addu'in kafin kwanciya bacci kamar haka;suratul iklas(3x),suratul falaq(3x),suratul nasa(3x),ayatul kursiyyu(1x),amanar rasul(1x) sai;Bismika Rabbee wadha'tu janbee , wa bika 'arfa'uhu, fa'in 'amsakta nafsee farhamhaa, wa 'in 'arsaltahaa fahfadhhaa, bimaa tahfadhu bihi 'ibaadakas-saaliheen(1x),a'uzubikalmaatullahi tammat min sharri ma kalaƙa(3x),Bismillahi ayanaa waa amut.

Bayan ya tufa ya shafe masu jiki duka  ya miƙa hannu ya kashe masu wuta tare da rage ƙarfin fanka.

Chakumar shi tayi tana faɗin,ka kuna wutar tsoro nake ji bana son ganin duhu!.

Hannu ya kai makunin wutar ya kunna,haske ya gauraye ɗakin...,Ya isa haka nan da iznin Allah babu abunda zai faru dake kuma ina tare dake,"yake furta mata ƙasa ƙasa cikin kunen ta,hanun shi na shafa gashin kanta".

Shiru ya biyo baya na ɗan lokaci ko wanne da abunda yake tunani cikin zuciyar shi....., ɗaga kai tayi ta kalli tafkeken agogon dake manne a bangon ɗakin,"ƙarfe goma sha biyu dai dai na dare''.Ina mami?

Nan take yan hanjin shi suka kaɗa,tana bacci ya bata amsa a takaice.

Shiru ya biyo baya babu wanda ya sake magana. Yana son tambayar ta abunda ya faru a gidan bayan fitar su,amma yana jin tsoro kana wani abu ya sake faruwa!.,tana son faɗa mashi abunda ya faru da ita amma bakinta yayi nauyi kamar wacce aka rufe wa baki komi ya ƙwace mata sam ta kasa cewa komi kuma.

Suna a haka hatr bacci ɓarawo ya sace su...,duk abunda ya faru a kan idanun mami domin tana laɓe taba saurare har taji shiru sanan ta buɗe ƙofar a hankali ta tsura masu idanu har zuwa wani lokaci sana ta kaɗa kai tana jin soyayyar iyayen ta na ratsa ko wane sassa na jikinta!. Sai dai kash bakin alƙalami ya riga ya buge ba zata iya haƙuri da cikar wanan buri nata ba akan su,ya zama dole ta nisanta kanta dasu ko don tsiratar da rayuwar mummynta daga shiga haɗari!.

Abun shara ta ɗauko a kitchen a hanzarce ta gyara ko ina sanan ta kashe masu wuta ta kom ɗakinta.

Washe gari basu farka da wuri ba sai kusan takwas na safe saboda rashin bacci da basu yi da wuri baa,haka yasa suka makara sallar asuba.

Cikin ikon Allah koda suka farka jikinta sumul kamar babu abnda ya same ta a jiyan domin ko tambo babu, ga ɗaki a gyare tsaf!

Batawani yi mamaki ba domin ba yau bane rana na farko da irin haka ke faruwa da ita, shi dai yana son yin tambaya akan wanan lamari amma tsoro ya hana haka dai suka gabatar da sallar asuba a gagauce ta nufi hanyar kitchen nan suka yi kichibis da mami a palo."ina kwana mummy,ya daren ki"?, lafiya lau ta furta idanunta ƙur akan koshin mami data buga mata a jiya ya tashi sumbul.

Ina daddyna?"ta katse shirun nasu", muje kitchen zai fito bada jimawa baa.

Har sun kama hanya sai ta tuna da abubuwan da suka faru a jiya kawai ta canza shawara;ahm mami kin gyara ɗakin ki ne?,a'a mummy!.

Amma mena faɗa maki akan gyaran ɗaki idan kin tashi daga bacci?, turo baki tayi,ni mantawa nake yi kuma ai nace ma daddy ya samo maki mai aiki amma kinƙi yadda,kedai mummy komi naki daban dana mutane!.

Cikin rarashi tace,yanzu dai kiyi haƙuri ki gyara kin ji yan mata na,kefa babbar yarinya ce wacce zata shiga jss1 ace bata iya gyara ɗakinta?,ai sai friend naki su maki dariya idan suka ji.

Wuri ta samu saman hanun kujera ta zauna domin anzo inda take muradin ji..,dariya tayi sosai har sai da zainab ta tsorata domin kwata kwata ta tsani taji mami na irin wanan hatsabibin dariyar wani faɗuwar gaba ke ziyartar zuciyar taa.

Riƙo hanun mumynta tayi zauna kiji wsni labari abunda nayi ma yan school namu kowa ke tsoro na;wata yarinya kafila kullum idan muna class sai ta rinƙa kallo na,ai kuwa wata rana muna fita na bita a baya idanun nan nata da take yaan kallo na au na soka mata pencil a ciki!

zaro idanu zainab tayi cike a tsoro domin ta tuna lokacin da abun ya faru,babu yadda baa yida mami ba tace bata san zan cenba.

Sanan kuma ummulkhairi....

Dakata haka nan bana son jice kawai!.

Ji tayi ba zata iya wani dogon girki ba kawai ta ɗaura ruwa zafi da niyyar haɗa shayi....,mijinta ya fito cikin shirinshi tsaf  suka gaisa ya ƙare mata kallo,daga bisani yace idan mun gama breakfast ku shirya zamu wurin su hajia.

Da sauri ta kalle shipl,sanin zata shiga wni hali yasa ya fice daga kitchen din.

Wani tashin hankali ta shigadomin ta tsani zuwa gidan surukanta saboda wani dalili nata wanda ta barwa kanta sani.




vote
comment
share.
[6/3, 13:02] LEEMA: *🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
       *NA*

          *L££MA*

wattapad
*@leemaMuhammad826*

  _Sadaukarwa gare ku_👇🏻

*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*

*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*

*MUGIRAT marubuciyar"LAHANI",ban san da wani irin kalma zan yi amfani wurin nuna matuƙar godiyata a gare ki ba!,haƙiƙa kin nuna mun ƙauna da soyayya,sharhin ki a kan wanan littafin na matuƙar ƙara mun ƙwarin gwiwa. Har kullum ina maki fatar alheri a duk inda kike ALLAH ƙara maki basira da daukaka,Allah yasa ki zarce haka a duniyar marubuta amin❤*



*🅿7-8*


     Ba zata iya buɗe baki ta furta mashi bata son kusantar ahalin shi baa,haka bata jin zata iya zuwa gidan nan.

Zuciya cike da sake sake ta girka ruwan shayi kawai sai bredi ta ɗaura saman tebur sanan ta mashi magana ta kammala...

Wai irin breakfast ne haka ko minti  talatin ba ayi cikakke ba har an gama?.

Haushi ne ya kamata,ta luka kwata kwata muhammad  baya ganin ƙoƙarin ta a gidan nan. Shayi ne idan ba zaku sha ba ai babu dole!,"ta juya fuuuu ta koma ɗaki".

Murmushi yayi a bayyane,sarai yasan neman dalili take da safen nan kawai don kada taje gidan iyayen shi,amma yasan inda zai ɓollu mata.

Mami dake buga vedio game ya kala,wai kin gama gyaran ɗakin da naji tana maki magana ne?,daddy ni ba zan wani iya gyaran ɗaki ba kullum safe tunda ba fitsarin kwance nake yi baa.

Jinjina maganar ta yayi yna nazarin yanyin ta...,watau a gidan kowa shegen kanshi ne,ba wanda ke ragawa wani domin wata rana sai ka rasa gane tsakanin mami dasu waya haifi wa!.

Tashi yayi ya nufi kitchen inda yaji motsin zainab...,koda ya isa kamshi ya maye ko ina tana soya ƙwai ne.

Sannu da aiki uwargida me zan taya ki dashi?, a daƙile ta amshi shi"babu,ka jira na kusa gamawa zan fito yanzu".

Jingina yayi da bango yana ta binta da kallo,a iya zaman da sukayi na shekaru biyar kafin haihuwar mami basu taɓa samun matsalar da zai kai su ga hayaniya ba bare har ya kai mata hannu. Zainab mace ce mai hakuri matuƙa da gudun zuciya,sai dai fa nan da nan ne ta haye wanda idan baka fahinta baka taɓa sanin ta shiga ɓacin rai.

Babu rayuwar auren da zaa ce baa fuskantar ƙalubale a wanan lokaci,amma idan ka samu abokin/abokiyar rayuwa mai haƙuri sai yazo da sauƙi. A iya sanin shi tunda aka haifi mami babu ranar da ba zasu samun saɓani,bashi da kaƙuri ko kaɗan!,zainab ta rikiɗe ta koma wat irin mafaɗaciya,bashi da halin nuna ɓacin ranshi zata haye ta rinƙa jinini kenan bata gajiya har zuws yau ɗin nan da mami keda shekaru goma tana neman na sha ɗaya ya rasa gane inda matsalar su take.

Kwasan kayan tayi bayan ta kashe gas ta nufi hanyar teburin cin abinci...,shauran plate da yaga ta aje zata dawo ta ɗauka y kwashe tare da binta a baya.

Ruwan zafin da ya ji kayan ƙamshi ta tsiyayawa kanta a ƙaramin kofi sanan ta haɗa dai dai yadda take so ta tura mashi flask ɗin gaban shi.

Bredi ta ɗiba tana shafa bota yana kallonta har ta gama tayi bismillah ta fara ci....,mami!.

Na'am daddy!,taso muci abinci.

Babu musu ta aje game ɗin ta nufo inda suke...,tea ya haɗa masu a cup ɗaya sanan ya sama soyayyaen ƙwan tsakiyar slice bread ya rufe da ɗaya ya miƙa mata nata,ya haɗa nashi.

Daddy shike nan breakfast din?,yau mummyn ki bata da lafiya shi yasa bata soya komi baa,kici da sauri ku shirya zamu babban gida(gidan iyayen shi)

Daɗi sosai ya kamata domin idan akwai inda take son zuwa a garin abuja bayan school sai babban gida,saboda akwai yara da yawa zata yi cin zali yau.

Saboda tsabar murna bata wani ci abincin sosai ba ta miƙe...,ina kuma zaki?

Wanka zanyi daddy idan mun isa zan ci abinci wurin su granny.

Duk abunda suke yi tana kallon su ta wutsiyar idanu kiris take jira a sako ta cikin hirar tayi cin mutunci,amma sun shareta kamar ma bata wurin.

Ganin tara na safe ta gota yasa ta hanye ruwan tea kawai ya mike,muje ki taimaka mun da wanka darling.

Wani harara ta watsa mashi kamar manyan idanunta zasu faɗa tare da jab dogon tsaki tana cigaba da kurɓan tea a yangance domin ta ƙudiri niyyr sai tayi abunda zai hana tafiyar da ita.

Dariya yayi sosai tsaf ya gano inda ta dosa ya kaɗa kai ya wuce ɗaki zuciyar shi fal soyayyar matar shi.

Har ya gama ɓata lokaci wurin wanka,ya shirya cikin yaddi brown mai ɗaukar ido ya fito tana zaune inda ya barta,ɗakin mami ya tura a hankali tana zaune saman gado ta baje kayan kwalliya birjiƙ tana fentin fuska!.

Dariya ya mata domin tun tana da shekaru uku haka tare da son kwalliya sai ta taka stool na ɗakin mummyna ta haye saman dressing mirror ta zauna sai tayi kache kache da komi.


MAMI kwalliyar ya isa haka nan rana nayi,idan mun tafi a nan zan barku saboda zan shiga suleja sai da yamma zan dawo mu saboda bana son barin mummynki ita ɗaya a gidan nan.

Tau daddy na. Kayan ta shiga haɗa wa already  ta saka doguwar rigar lace ɗinkin bubu pink,abunka da dogowar mace ya mata kyau duk da siririya ce sosai bata da kauri.

Fitowa suka yi a jere kamar wasu masoya yana kwasar dariyar shirmen taa...,turus yayi ganin har lokacin zainab na wurin tana wasa da kofin da ke hanunta!

Kallon juna suka shiga yi da mami,raɗa mashi tayi ƙasa ƙasa"ba tare da mummy zamu bane naga bata shirya baa?".

Cikin ɗaga murya yadda zata ji ya fara magana,kyale mummyn nan taki ummu yanga kenan amma kada ki damu shawarar da kika bani shi zan ɗauka kawai aure zan ƙara tunda bata son mu!

Kuma bata son zuwa gurin su granny daddy.

An ƙi aje din munafukan banza,wallahi ai anyi lusarin namiji a nan wai duk girmanka baka da abokiyar shawara sai yar mitsitsiyar yarinya!,ba zan tafi gidan naku ba ai ba sona suke yi baa,ka ƙarata can da yan uwanka munafukai irinka.

Ranshi ya ɓaci ainum amma baya so yana biye mata suna samun saɓani a gaban mami gudun sake afkuwar wsni abu makamancin na jiya!

Mami kwashe kayan ki kai kitchen kinji?,tsaki taja tana harhaɗa kayan idan akwai abunda tafi tsana a duniya  bai wuce ɓacin ran daddynta ba duk a takan kasance cikin shauƙi idan taga suna tashin hankali haka,bata ƙaunar ganinsu cikin kwanciyar hankali kawa burinta su rabu kowa ya kama gaban shi domin sun zame mata wani katanga a tsakaninta da cikar burinta.

Mami na shiga kitchen din ya sungumi zainab wacce ke zille zille har cikin ban ɗaki ya sauke ta tare da surin sakar mata shawa sanan ya fice da sauri yaja mata ƙofa!,idan kinga dama kiyi wankar ko ki cigaba da zama ciki har wani abun ya sake faruwa dake kuma.

Jin haka tayi saurin cire kayan ta fara wanka a tsorace tana waige waige har ta gama,towel taja daga inda suke ajewa ta ɗauro ta fito...,baya cikin ɗakin gidn ma gaba ɗaya ya mata shiru nan take gabanta ya faɗi ta shiga tunanin ko sun wuce ne?.


Leƙwa tayi a window,motar shi na nan tayi hamdallah ba wani dogon shafe shafe tayi ba kawai itama ta zura doguwar riga na atamfa sai sarka da yan kunne data saka ta fesa turarai,handbag kalar mayafin da takalmi ta sunguma ta fito...,suna zaune palo hankalin su na kan game din da mami ke bugawa da wayar shi suka ji taku ɗas ɗas ɗas!.

Eyeeee kaga uwargida sarautar matador,takawar ki lafiya uwargida sarautar matador..,"uwargida sarautar banza dai taja tsaki",idan an fasa tafiyar ne ka bani car key zani gwarimfa gidan yusrah(aminiyar ta kuma matar abokin shi).

Key ya wurga matador,zaki gwarinpa wurin gulma da tsegumi dai saboda ance zaa maki kishiya zaki tafi a tsegunta mata Amebo's kawai.

Tana amsan key tayi gaba abunta...,basu wani ɓata lokaci ba ya kashe kayan wuta uka fito tare da mami wacce hankalinta ke kan game na(zombie highway) da take bugawa.
Rufe ƙofar shga ciki yayi ta waje suka nufi mota gimbiya zainab na gaba hakimce,mami ta buɗe gidan baya ta shige,shimaya shiga gaba tayi bismillah tare da ba motar wuta.


Sai da suka hau titi sosai ya tabbatar gwarinpa zata da gaske,bai ce komi ba ya ƙyale ta har suka isa layin sanan yace"juya kan motar zuwa kubwa!".

Kallon shi tayi da kyau taga babu alamar wasa a fuskar shi,itama tayi kichin da rai;ai na faɗa maka ban zuwa kawai ga motar ka zan ƙarasa gidan a ƙasa!.

Allah zainab idan kika fita daga cikin motar nan zan ɓata maki rai tunda na lura bakya son zaman lafiya.

Tsaki taja tana maganganu ƙasa ƙasa...,daga bisani ta ɗaga murya"ni ba zan iya jan mota daga gwarinpa xuwa kubwa ba gaskiya ya mun nisa".

Dama waya saka ki?, fito ki bani wuri
amma inda zuwa kazaure ne zaki iya ja ai shashasha kawai!

Cikeda ɓacin rai ta koma gidan baya saboda tasan baya son zama shi ɗaya gaba,haka baya son zaman mami a gaba saboda mugun bakin taa.

Gudun tashin hankali yasa bai mata magana ba yaja motar shiru babu mai magana har suka isa babban gida wanda yake a kubwa..,mai gadi ya buɗe nasu gate ya shige da motar tare da neman gefe ɗaya ya aje motar.

Fitowa suka yi duka mami ta miƙa mai wayar shi ,suka fara tafiya...,kai nifa

Please Login or Register in order to submit comment