Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masu yafiya da rufawa juna asiri,Allah ya albarkaci zuria gaba ɗaya amin.

Mazajen yanin su mata sukayi wa alhaji sallama suka tafi,matayen mazan kuma dama sun saba yini a gidan amma yau wani abun mamaki ko wacce tace gidan ta zata...,Allah ya ɗaura masu wani irin tsoron hajia lanti a zukatan su,basa ma so yaran su suyi kusa da ita!.

Ko wace ta koma sashinta cike da nadama...,muhammad  na wurin abban su domin yafi samun natsuwa idan yana tare dashing. Ba dan hajia lanti mahaifiyar shi bace,wallahi da sai ya ɗau ƙwaƙwarar mataki a kanta.

      Zainab ta isa kazaure a gajiye duba da yanayin hanya kuma wuri ba kusa baa,abun hawa ta nema da zai kai ta har gidan su...,zuciyarta cike da zulumin yadda baban su zai karɓi wanan magana nata domin bata da matsala da maman su.

Tsayuwar adaidaita a ƙofar gidan su yasa ta dawo cikin hayyacinta,cire da ƙwarin gwiwa ta salame shi tare da tura ƙaramin ƙofar shiga gida...,duba da yanayin gidan su ba zaa kira su dawasu shahararrun masu kuɗi ba,amma suna da rufin asiri da wadata iya gwargwado.

Motsin mutum taji a madaidaicin kitchen ɗin su na zamani dake tsakar gida,koda ta isa safiyya ce ta gama abinci tana kwashe wa....,bata mata magana ba haka bata yi wani alamada zai nuna tana wurin ba har ta kamala ta juyo zata fita!,nan take ta zabura saura kaɗan kular ta suɓuce daga hanunta.

Yaya zainab kece daga ina haka?,"ta watso mata tambayoyi a lokaci ɗaya",kuka kawai ta fashe dashi tare da haɗe kanta da bangon kitchen ɗin!

Mama! Mama......!!,fito ga yaya zainab!!!

Wata farar mata mai matsakaicin jiki ta fito fuskarta ɗauke da alamar mamaki!,ke daga ina haka!,kuka ta cigaba dayi babu amsa.

Idan kuka ya kawo ki kawai ki fice daga gidan nan baa son saunan ci,"tana kai nan ta koma palon",safiyya ta aje kular saman kanta sanan ta riƙo hanunta suka shiga daga ciki har ɗakin baccin su sanan ta zaunar da ita saman gado.

Aunty ki daina kuka haka nan bana son kina shiga tashin hankali,kinga mama ba cikakken lafiya take dashi ba idan ranta ya ɓaci asthma  ta zai tashi ga hawan jini,shi yasa nake tsoron faɗa mata maganar da muka yi dake jiya bayan kin bar asibiti.

Yanzu dai ki shiga ki watsa ruwa zan zuba mana abinci kici sai ki rama sallolin ki daga nan a natse  sai ki mata bayani kafin baba ya dawo daga kasuwa.

Babu musu ta fito harabar gidan domin shiga banɗaki tayi wanka...
,maman su dai na binta da idanu.Bata ɗauki lokaci ba ta fito da yake tana ganin jini bata sallah kawai ta shige ciki dai dai safiyyah ta zubo masu ɗan waken fulawa wanda yaji kayan lambu irin su,"cabbagels,carrot,cucucumber,green pappe,tomamoes,onion har dasu ƙwai,ga yaji mai daɗi"(wayyo daɗi LOL😋).

Cikin kayanta irin wanda ta bari a gida saboda idan tazo haka take amfani dsu ta samu riga da skirt na atamfa ta saka,ƙare wa ɗan waken kallo tayi,ai kuwa miyun ta ya katse domin tana son shi sosai. Ba tare da ɓata lokai ba ta rinƙa shi ba kakautawa da hannu sai ta haɗo uku ta tura.....,cike da tausayawa safiyyah ke kallonta domin har tayi rama ainun idanunta sun zurma.

Tas suka cinye wanda ba wani abun kirki safiyyah taci baa,sai lokacin zainab taji wata irin kunya ta kamata yadda tayi wa ɗan wake cin hauka!,kuma dai bata ga laifin kanta ba domin rabonta da wani abincin kirki tun tea da muhammad  ya kawo masu asibiti tasha.

Safiyyah bata yi magana ba ta ɗauki plate ɗin ta ƙaro masu tare da turawa gaban zainab,"ke nifa na ƙoshi sai sai ke",gaskiya yaya zainab nimana ƙoshi dama ke na ƙara mawa kinga tafiyata....,kitchen ɗin ta dawo tare da fashe wa da kuka domin na baban su ta juyo masu duba da baya dawo wa cin abincin rana ana sawa ne kawai koda an samu akasi ya dawo.

YA ALLAH Ka kawo wa yaya zainab ƙarshen wanan jarabawa na rayuwa!,Ya Allah ka bata ikon cinye wanan jarabawa ka mayar mata da mafi alheri amin.Bata koma ciki ba kawai ta kama wasu aikace aikacen gida gudun kada ta hana yayanta cin abincin yadda take so...., har kusan minti talatin  sanan ta duba taa,ai kuwa koda ta shiga zainab ta cinye tas har ta kishingiɗe bacci ya kwashe ta.

Palo ta dawo wurin maman su dak faman saƙa na engine...,duk da ta manyanta bata wasa da sana'ar hannu irin su(saƙa,ɗunki,bit making,haɗa takalmi,jaka, purse da turaruka na jiki dana ɗaki wanda itama safiyya idan sun samu hutu shi take yi har snacks kala kala da kwalliya na amare  domin maman su ta daɗe tana yi a gida har ya bunƙasa ta buɗe wurin koyar da ɗalibai(vocational training center).

Hankalin ta na kan aikin da take yi ta jeho wa safiyya tambaya"ina fata ba kashe auren tayi baa?",am...mama bata faɗa mun komi ba dai, amma kuma yanzu bacci take yi!,"cikin inda inda safiyya tayi maganar".

Ai kuwa dai gwara ki faɗi gaskiya domin daga ni har mahaifin su ba zaku mayar damu dattijan banza baa!

Cigaba da faɗa maman tayi,ita dai safiyyah sai addua take cikin zuciyarta Allah yasa ba kashe auren yaya zainab tayi baa...

Sai yamma lis ta farka lokacin safiyya na kitchen abincin dare take haɗa masu domin anyi magrib bata so ayi isha'i baban su ya dawo bata haɗa ba sa   sauri take ta gama...,maman su kuwa na zaune saman tabarma a harabar gidan wanda yasha sumunti fes dashi tana jin labarai a rediyo...

Har ƙasa ta duƙa,"ina wuni MA?",lafiya lau ya jikin ki?, da sauƙi sosai madallah. Shiru ya biyo baya na wani lokaci,ki zauna mana baban ku ya dawo kina bacci ni ban ma faɗa mashi kina gidan nan baa,sai ki bari idan ya dawo daga masallaci kya mashi bayanin dalilin da ya kawo ki gida(ita a nata tunani muhammad  ya hanata zuwa ne ta sato hanya).

Bata ce komi ba ta zauna gefen tabarma,safiyyah sai kai da kawo wa take tsakanin kitchen da tsakar gida,tana ta jan zainab da hira ko zata saki jikina...

Bayan sallar isha'i ya shigo lokacin an ɗauke wutar nefa,inda generator yake ya nufa ya tayar dashi sanan ya shigo ciki(dama gate nata bayan gida ne inda yake je mota,domin ta gaba babu hanyar mota shi yasa suka saka ƙaramin ƙofa).


Inda palon shi yake ya nufa wanda an riga an haɗa abinci,mama ta same shi a nan sai data tabbatar ya ci sosai sanan tayi kiran safiyya suzo tare da zainab...,gaishe shi suka yi ya amsa sanan yace,"yaushe kuka zo ne?", baba ni ɗaya nazo yau saboda wata matsala data taso!.

Kallon safiyya yayi,tashi ki bamu wuri za muyi magana....,sai daya tabbatar ta fita sanan yace ina sauraren ki.

Kukan daya taso mata ne ta danne tare da ƙarfin halin kwashe komi ta sanar dasu!,babu abunda ta rage har yadda akayi ta samu cikin mami da abubuwan da suke ta faruwa zuwa wanan ciki da lalata shi da hajia lanti tayi har lokacin da komi ya bayyana!. Ta ƙara da cewa don ALLAH baba ku taimaka mun bazan iya cigana da zaman aure dashi baa,domin koshi abban su yaba matan shi zaɓi kuma nima muhammad  ya mun alƙawarin saki idan har zargi na ya tabbata akan iyayen shi.

Shiru palon ya ɗauka kamar ruwa ya cinye su sai shesheƙan kukanta dake tashi..,ko wanne da abunda yake saƙa wa a zuciya domin wanan magana ba ƙarami bane.

Zainab kin tabbata abunda kika faɗa gaskiya ne ba shirya kika yi ba kawai don kin gaji da zama dashi?,Allah baba gaskiya ne koma kayi waya da abban su zai faɗa maka.

Shike nan jeki ciki zan yi magana dashi zuwa da safe sai muga abunda zai yiwu....,zuciyarta fal farin ciki domi bata yi tsammani baban su zai fahimce ta har haka baa.

Ke kinji wanan irin iftila'i?,ko kina da masaniya a kai?,alhaji kenan ai da na sani ba zan ɓoye maka baa,abunda na sani shine irin matsala da take yawan samu da mijin akan mami har da hajiyar shi kuma ina ƙoƙarin kwantar mata da hankali banyi tunani yayi nisa har haka ba shi yasa ma ban tayar maka da hankali baa.

Shawara ɗaya zan baka alhaji,don Allah kamar ydda ta nemi alfarma a duba lamarin da idanun basira,a tsorace take da lamarin su domin kaji har tsafi akayi da ita Allah y nufa tana da sauran numfashi a gaba!,ka neme shi alhaji barau ɗin aji ta bakin shi,idan da hali su zo tare da muhammad  ɗin abi kom a sannu idan ta nuna ba zata koma yanzu ba a basu haƙuri ta kwana biyu a gida hankalinta ya dawo jikinta,kota koma yanzu matsala zasu rinƙa samu garin neman aljannarta ta faɗa wuta domin ba wani biyyyar aure zata iya mashi baa.

Wanan shawara ce mai kyau maryam ALLAH ya kyauta kawai domin wanan abu akwai ban mamaki da ɗaure kai.


Can ɗakin su kuwa zainab ta kwashe komi ta faɗa wa ƴar ƙanwar ta safiyyyah domin bata da kamarta bayan iyayen su saboda su kenan ALLAH ya basu bayan babban yayan su daya rasu a wurin bautar ƙasa a maiduguri tarzoma ta ritsa dashi shekaru ashirin kenan ko gawan shi baa gani ba.

Kuka sosai suke yi duba babu mai rarashin ɗan uwanshi saboda tausaya wa juna!,tabbas yaya zainab baa kyauta maki baa,duka laifin hajiyar yaya muhammad  ne domin ta cutar dake sosai,ko wacce mace akayi wa irin yadda aka maki ba zata so wani alaƙa ya ƙara shiga tsakaninta da wanan zuri'a baa.

Mu cigaba da addua ALLAH zai kare ki daga sharrinta har ita mami da suka sanya a cikin mugun hali duk da ba jinin ki bace muna sonta sosai kuma zamu tashi tsaye da addua har ALLAH ya bayyanar da ita.

Wayarta ta janyo tare da lalubo wani rubutu kamar haka;
MAGANIN JIFA KAI TSAYE!!!

*SIRRIN ƘAIƘAYI KOMA KAN MASHEƘIYA (BACK TO SENDER)*

_1-Ƙaiƙayi koma kan masheƙiya(ganye ne)_
_2-Farfatsin maƙera_

_NOTE:Farfatsin maƙera daban,kashin maƙera daban, shi farfatsin maƙera za a ganshi ƙanana-ƙanana,kashin maƙera Kuma manya ne ana samunsa a ƙasan maƙerar,farfatsin ƙira kuwa ƙarfe ne in aka sa wuta yayi jah in aka dakeshi Sai yayi farfatsi,to wannan farfatsin shi ake nufi Ba kashin maƙera ba_

Wadannan abubuwa guda Biyu da farfatsin k
ƙira da ganyen ƙaiƙayi koma kan masheƙiya Su za a daka Su dawo gari Sai a hade Su wuri ɗaya ana sha ana wanka kullum, Inshaa Allahu indai wani na cutar da kai ta hanyar jifa, ko maita, ko kambun ido ko Na Baka,ko wata cuta da aka kasa gane kanta Inshaa Allahu Allah zai yaye, game da me jifanka ko sammu ko wani makirci wallahi Allah zai nuna maka shi Kuma Zaka ga sakayya cikin gaggawa domin Allah zai mayar Masa aniyarsa kansa kuma wallahi bai isa ya jefe ka sau uku ba sai ya hallaka!.

Sanan kuma da wata sallah na neman biyan buƙata da kuma na neman gafara wanda baba ya bamu ko zaki tuna?,jimmm taki na ɗan lokaci,kai safiyya gaskiya na manta domin abubuwa sun mun yawa a kai na.

Barin tuna maki shi;

*WA YAKE NEMAN BIYAN BUƘATA A GURIN ALLAH DA GAGGAWA RANAR ALHAMIS AKE WANAN SALLAH MAI DUMBIN SIRRI*

_Duk wanda keda wata muhimmiyar buƙata da kake so Allah ya biya ma ita In kana da wani buri mai muhimmanci da ka ke so Allah ya cika ma shi.In kana da wata damuwa da kake so Allah ya yaye maka ita._

To ga sallar da ake kira; *KIBIYAR BIYAN BUƘATA CIKIN GAGGAWA!*

A cikin yinin Alhamis ake yin sallar, (amma ba taƙamemen lokaci, wato a kowane lokaci a ranar alhamis ɗin.Sallah ce za a yi Raka'a 4 kamar haka:-

Raka'ar Farko:Fatiha 1,sai Qulhuwa 11.Raka'a ta Biyu: Fatiha 1,Qulhuwa 21.Sai a Sallame,sai a ci gaba;-
Raka'a ta Uku:Fatiha 1, Qulhuwa 31.Raka'a ta Hudu:Fatiha 1,Qulhuwa 41.Idan an Sallame, sai a karanta Qulhuwa 51 a zaune, sannan a yi Salatin Annabi (S.A.W)shima 51.
Sai a yi Sujjada,a cikin Sujjadar sai a ce; YAA ALLAHU"sau 100.Sai a roƘi Allah Ta'ala duk bukatar da ake so (a cikin Sujjadar).
Manzon Allah (S) ya ce; Wanda duk ya yi wannan Sallah, ya yi wadannan wuriɗoɗi, to da zai roki Allah a kawar (masa) da dutse,da za a kawar da shi. Da zai roki a sauko da ruwan sama, da an sauko da shi.Babu hijabi tsakanin wanda ya yi wannan aiki da Allah.

"Kuma ku sani, Allah Ta'ala zai yi fushi da wanda ya yi wannan Sallah amma bai roke shi wata bukatarsa ba!". ( A duba;Jamaalul Usbou'i, shafi na 122. Mujarrabatul Imamiyyah, shafi na 188).

_Wanda ya maimaita wannan Sallah Alhamis uku a jere, to zai ga abin mamaki na biyan bukatarsa har da ina ma masu muhimman bukatu za su yi wannan Sallah a cikinsu, da sun ga abin mamaki!,Allah ya amsa mana, ya tausaya mana,ya sa mu dace!_


Ko zaki gwada na
*ƘAIƘAYI KOMA KAN MASHEƘIYA* yaya zainab naga an turo ne kuma mutane da dama suna ta godiya sun jaraba an dace?,tau safiyyah ta inshaa Allah zan jaraba.


*_Abunda yasa na kawo irin wanan magunguna domin sauran yan uwana su amfana saboda wani bawan Allah ya taimaka dashi Kuma wannan mujarrabun ne domin mun jarraba mun ga ikon Allah da taimakon Allah! Yah Allah ka karemu Daga sharrin maƙiya, ka karemu Daga sharrin masharranta, ka ɗora mu a kan maƙiyanmu amin ya ALLAH_*

Allah yasa mu dace dai safiyyah in shaa ALLAH ZAN YI ƘOƘARI!,da haka suka shafa addua suka kwanta bayan dogon tattaunawa.


Washe gari koda ta tashi har safiyyah ta gama haɗa abun kari domin ta samu bacci sosai bata tashi ba saoda fashin sallah.a palon maman su ta samu kowa ana karyawa,gaisawa suka yi itama ta ɗiba abunda zata ya ci.....,sai da suka kammala sanan baban su yace da ita ai alhaji barau ya kira shi a daren jiya don yaji idan ta iso gida?,ya bashi tabbacin tana nan,yace in shaa Allah zai ƙoƙari yazo saboda ba maganar waya bace.

Jinjina maganar tayi tana addua cikin zuciyarta ALLAH ya bata nasara a kan su kada a tilasta mata komawa.



Nasiha da jan hankali ya ɗaura masu tare da gargaɗin su da riƙe ibada,addua,karatu al-Qur'ani mai girma da sadaka kamar yadda suka ɗaura su su akai. Saboda auren safiyyah ya kusa dama karatu take kuma ta kamala sakamako ake jira kawai.


Ɗaki suka koma safiyyah ke tambayarta wayarta?,sai lokacin ta tuna yana kashe tunda ta kamo hanya.Babu chargie koma banzo da abun chargie baa(kasancewa iphone ne ba ko wane abun chargie yake mai ba shi yasa tayi wanan ƙarya don kada ta kunna muhammad ya dame ta da kira).


Ina matuƙar jin daɗin zama da iyayena har na fara manta wata damuwa duk da ina fashin ALLAH amma ina ƙoƙarin azkar na safe da yamma,zama da alwala tre da saka karatun al-Qur'ani mai girma da yawan sadaka.Sanan safiyyah na ƙoƙarin ɗebe mun kewa.

Sati ɗaya cur wayata a kashe kuma a ranar muka tashi da shirye shiryen tarban baƙi daga abuja(gidan su muhammad ). Ban wani tadda hankali na ba,safiyyah ta kula da duk wani girke girke na tarbon baƙi...


Abunka da motar gida neda wuri suka iso...,safiyyah ta shirya masu abinci a barandar gidan mu saman babban darduma inda zasu fi sake wa saboda babu wutar nepa ana zafi. Sunci sosai sanan muka fita aka gaisa lokacin na gane(abba da muhammad sai yaya shafi'u ne suka zo). Baba yace safiyyah ta koma ta kira maman mu tazo.

Ina zaune kaina na ƙasa amma naji a jikina muhammad ni yake kallo....,sallamar mama yasa na ɗago kai muka haɗa ido dashi!,ya idanun shi sun zurma abunka da ƙaƙarfan mutum baa gane ramar shi a jiki sai a fuska.


Bayan gaishe gaishe;alhaji ya bada haƙuri na rashin zuwa da basu yi da wuri baa,hka ya faru ne saboda maganin da suke amfani dashi kuma Alhamdulillah ana samun cigaba domin har zuwa yau babu abu mugun abu da ya faru dasu. Bayani yayi na abubuwanda suka faru kamar yadda zainab tayi cike da natsuwa yana mai kwantar da kai wurin neman afuwa akan abunda aka yiwa zainab.


Baba yace,tabbas zainab tazo mun da magana amma ban gasgata ba nace har sai naji ta bakin ku kafin a yanke hukunci!,mu nan iyayenta a ɓangaren mu wallahi har ga ALLAH babu wata matsala mun yafe domin babu wanda ya wuce ƙaddara sai fatan ALLAH ya tsare gaba kawai.

Mama tace wanan haka yake ALLAH ya gafarta mana baki ɗaya.

Wani daɗi ne ya rufe muhammad gani yake zai samu zainab a sauƙaƙe!.alhaji barau ya sake katse su idan babu damuwa muna so a bamu zainab ta koma ɗakinta.

Baba ya kalle ta sosai tare da nazarin yanayinta,kuma ya duba alfarma data nema a wurin shi da irin hakuri da juriya da tayi a baka duk abunda yake faruwa bata taɓa kawo ƙarar mijinta wurin shi ba har suka shekara goma sha biyar cikin na sha shida da aure.

Alhaji barau watau wanan magana tsakanin zainab ne da muhammad domin ba zan tursasa mata komawa ba haka ba wai ina bata ƙwarin gwiwar zamanta a gida bane!,illa ta tabbatar mana akwai alƙawarin saki a tsakanin su.Dukan su ba yara bane inaga zai fi kyau mu bari su sasanta kan su a natse idan hakan ya yiwu,idan bai yiwu ba dama can adadin zaman da Allah ya ɗiba a tsakanin su kenan. Duba da aure da mutuwar aure,arziki da haihuwa duka lokaci nea.



Muhammad ya ƙara sunkuyar da kai,haka akayi baba nayi alƙawarin sakinta idan har zargin da take akan iyayena ya tabbata kuma ba zan so karya wana alƙawari ba sai idan har itace da kanta ta yafe mun kuma ta aminta dani mu koma gidan mu sanan zan fidda kaffara.


Baba ban aminta ba ina neman alfarma kawai ya cika mun alƙawarin daya ɗauka!

Wuri ya ɗauki shiru kowa jikinshi yai sanyi duba da girman alƙawari!

_wanda yanzu mutane basu ɗauka a bakin komi ba wani zai maka alƙawari fiye da sau gomaa rana amma ko ɗaya ba zai iya cika wa baa._


Shafiu yaso yn magana amma yana jin kunyar zainab matuƙa yadda hajiyar su ta zama sillar rugujewar farin cikinta.


Muhammad da kanshi ya tashi zuwa mota ya ɗauko biro da takarda!,sai daya share wasu hawaye masu zafi dasuka zubo mashi sanan ya dawo ya zauna idanun shi fes a kan zainab wacce ko a jikinta bata jin komi game dashi sai zallar ƙiyayya da tsana!,Hanun shi na rawa sosai ya rubutu yayi kamar haka;
*_NI MUHAMMAD MU'AZU BARAU NA SAKI MATATA ZAINAB SHANONO SAKI ƊAYA A YAU RANA....._*

Ajewa yayi saman carpet ɗin tare da miƙewa da sauri ya koma wurin mota,nan yaduƙe a ƙasa hawayen da yake ɓoyewa suke kwararo kamar an buɗe famfo!


FOLLOW
VOTE
SHARE COMMENT
[7/1, 15:42] Leema: *🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
*NA*

*L££MA*

wattapad
*@leemaMuhammad826*

_Sadaukarwa gare ku_👇🏻

*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*

*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*






*🅿39-40*



*ONDO STATE,AKURE*


Ƙarfe biyu na dare a ƙauyen "ÓHEÍA ",cikin wani dokan jeji,a saman babban tsauni wanda ke malalle da wani zani mai tsantsi jawur, daga tsakiya babban dutse mai kamar falali ne,an jera manyan candle aƙalla sun zagaye dutsen wanda ya haske wurin gwanin sha'awa!.


Mutane ne aƙalla sun kai ashirin maza da mata,sun manyanta sosai a tsaye suke da fararen riguna masu sulɓi har ƙasa sai hula fari shima babu takalmi suna riƙe da ƙananan candle sun zagaye dutsen(FLYERS kenan!,azzalumai a cikin ƘUNGIYAR EIYE). Father paul na zaune saman babban ƙwarya,mami na gurfane a gaban shi.

Cikin ɗaga murya wani mutum baƙin ƙirin mai jiki sosai da tsayi ya fara magana kamar haka;"EIYE KO NI ISAASUN EYE NBUTA!!!",suka amsa da EIYE.......!!!
Wuri ya ɗauki shiru kamar ba kowa,fuska a murtuƙe cike da nuna ɓacin rai ya sake ɗaga murya....

Each and everyone of you knows that we are perhaps the most numerous on the western nigeria!,our methods of recruitment are not as rigorous as some of the other cults,but because of our large number it has become difficult to maintain real disciple,BARAU and his family consider this to cheat on us and display our secret !.They know the EIYE confraternity was born consequent upon a crisis,we are not devoid of violence!.(MANDIA kenan shugaban ƘUNGIYAR EIYE)


Wata mace fara sosai,farinta har ya kuma ja ja kamar jini ya kwanta mata har ana ganin jijiyoyinta green a fili saboda tsabar bleaching!,jabbabatu kenan cikakkiyar bahaushiya ce kuma itace mataimakiyar shugaban wanan ƘUNGIYA.

Tabbas BARAU yayi babban kuskuren ja da ƘUNGIYA!,yana ganin zai tsira ne?,saboda cin amanar ƘUNGIYA shine zai haɗa kai da wanan mallamin suna lalata mana aiki da ayar QUR'ANI!,ni ɗin nan JABBA ba zan taɓa aje makaman yaƙi na akan shi da ahalin shi ba,wanan da kuke gani"ta nuna MAMI",zata zauna hanun father paul har sai ta samu horo na musamman tsawon shekaru goma sanan zamu naɗa ta shugaban wana ƘUNGIYA lokacin ƙarfin mu ya ƙare itace zata yaƙe su gaba ɗaya sai taga bayan su wanan alƙawari ne!
"Eiye ko ni isaasun eye nbuta....!"
EIYEEE........"suka amsa",alamar sun aminta da hukuncin data yankee.


Saboda tunda father paul ya ɗauko mami basu samu daman haɗuwa irin haka ba tana wurin shi a nan cikin ƙauyen a wani bukka,nan yake rayuwa dama a saman bukkan shi tsaunin da suke taro na musammman yake.

Duk yunƙurin da suka yi na kai farmaƙi wa ALHAJI BARAU sai ALLAH ya kare shi bsu iya komi haka zasu gaji da wahala su dawo!,wanan dalili yasa suka yanke shawarar ba zasu taɓa bari mami ta suɓuce masu baa,zasu canza mata suna,addini da akalar rayuwarta sai yadda suka juyata.


Nan take aka mata alama tazo...,tsakiya aka saka ta dama itama tunda tazo farar rigar nan take amfani dashi babu takalmi bare ɗan kune ko wani ƙawa na duniya.

Sabuwar reza aka miƙa mata tare da bata umurni ta tsaga babban yatsanta na hanun hagu,babu musu tayi yadda suka ce kuwa sai ga jini ya ɓalle sai ta tara hanun a saman candle yana ɗiga wutar na ƙara ruruwa sai tashi yake sosai har jinin ya ƙame wurin yayi jawur(wanan shine tambarin yan FLYERS(watches or wizard) NA ƘUNGIYAR EIYE).



Sun tattauna abubuwa masu muhimmanci sosai musamman akan mami da ahalin ALHAJI BARAU daga nan suka watse.

Washe gari ya kama lahadi shi da mami suka nufi cikin garin akure domin mami ta amshi addnin kirista.

Wani babban church ya nufa"THE REDEEMEND CHRISTAIN CHURCH OF GOD AKURE",wanda yake cike da ɗan mutum mabiya addinin krista.Bayan an natsa pastor ya fara gabatar da opening prayer;
_Oh holy Lord,you are worthy of all of our praises,Heavenly father,our provider,our maker and our protector your name is glorious and wanderful so help us Lord._


Father paul ya gabatar da mami a matsayin wacce zata canza adinni!,nan aka shiga praising Lord ana farin ciki.Aka tambaye ta sunan da take so?,tace merry.

Dafa kanta yayi tare da fara kwararo addu'a...

_father in heaven,we thank you today for your blessings that you bestow upon us all.Father,I pray for our congregation today.Lord,may we all give with gladness and sincerity_

Waƙa suka shiga rerawa na nuna godiya wa abun bautan su har zuwa wani lokaci aka tara wa mami abubuwa na ban mamaki tun daga kan kuɗi,kayan sawa,takalma da sauran su sauran su har wanda suka ce zasu ɗauki nauyin karatun taa.

Har aka gama service ɗin sai ɗaukan hotona ake yi da mami daga nan aka bata kyautar bible wanda zata rinƙa zuwa bible study kullum daga safe zuwa yamma,amma da dare kuma zaa fara koya mata al'amuran ƘUNGIYA ne.

Dama daga wani ƙauye makwabtan su ake kawo ma father abinci da duk abunda ya ke buƙata shi yasa yabar mami har yamma ya dawo ya tafi da ita.


Ɓangaren mami kuwa har ta manta da wasu iyayenta ma,zuciyarta ya bushe bata tunanin komi sai cikar burinta na zama shugabar yan ƘUNGIYAR ASIRI!


Da dare suna zaune cikin bukkar su faɗa yace,kamar yadda nayi alƙawari zamu fara darasi akan ƘUNGIYOYIN da muke da su masu girma da ƙarfin iko wanda aƙalla sun kai hamsin!,zan lissafa maki masu muhimmanci wanda idan kin san sirrin su da kyau ne zaki iya yaƙar su har su dawo ƙarƙashin ki!.zamu fra da goma sha biyar sai kin gane su kuma na gwada ki a kan su zamu cigaba.sube wa ƴan nan kamar haka;

Black berrets
Knight cadet
The green berrets
Black pyrates
The black cat
The black scorpions
Royal Queen
Mafia
Dragon
Pink ladies
Death Row
The blood

Please Login or Register in order to submit comment