Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zan manta ba Gida ne babba ginin jan laka amma anyi daɓe tare da zanen sarauta da farin ƙasa sai yayi kyau sosai,shiya shiya ne ainun akwai mutane ƙwarai a ciki tun daga kan kakkani, iyaye,yara da jikoki kowa da shiyar shi amma kada kuyi mamaki duk girman gidan nan tukunya ɗaya ake ɗaurawa(ma'ana dai sau ɗaya ake girki a rana).

Yadda akayi na gano haka kuwa shine;an shigar damu ciki har shiyar mahaifiyar uban ƙasa wacce suke kira gwaggo uwa ta amshe mu hannu biyu biyu nan innata tayi wanke a ɗan ban ɗakin shiyar da aka kewaye da zana,ni kuma ta haɗa ni da samarin gida aka kai ni ban ɗakin waje nayi wanka a cewar su nayi girma da wanka cikin gida.

Bayan mun kimtsa duka aka bani taguwa da wando na haladu(ɗaya daga cikin yaran gidan)na canza,innata aka bata taguwa da zani,shima baffa acan garka an bashi taguwa da wanda na uban ƙasa masu kyau ya canza duk mun yi shar aka bamu  abinci tuwon gero da miyar yauƙi muka ci da yake yamma tayi sosai a lokacin babu wutan nemi sai farin wata da fitilar aci bal bal sai fitilar kai da ake kunawa lungu da saƙo ga masu hali.


Ina nan waje laƙe wurin baffa na da ƙyar haladu ya ja ni muka fita dandali kallon wasanni,baffa na kuwa yana nan garka wurin magidanta yan uwan shi,inna tana wurin gwaggo uwa. Sai da dare ya raba aka nuna mana inda zamu kwanta tare da baffana,inna kmam ɗakin gwaggo uwa ta kwana.
Tun da asuba muka tafi sallah wanda ana fitowa masallaci zaka ji matan  na daka tif tif tif!,da manyan taɓare na hatsin da zaa yi dawo,wasu sun hasa wuta ana zazafen sauran tuwon jiya da miya wanda shine abun karin safe,yan mata  na sharada wanke wanke wasu kuna jan ruwa a rigiya,lokcin yan maza zasu nufi gona wasu wurin kiwo.

Kafin su fita ne gwaggo uwa ta saka aka kirani a garka ta haɗa da innata tare da mana jagora cikin gidan inda kowa yake harƙilan gaban shi nan aka higa gaishe gaishe tana gabatar damu a matayin baƙin uban ƙasa!
Matan shi huɗu ne duka an nuna mana su da yaran shi wanda suke nan bayan wa yanda suka fita fatauci wasu garuruwa na maƙwabta.  Cikin faram faram aka mana maraba nan suka zauna cikin matan gwaggo uwa naso ta saba da kowa.
Wurin baffa na waje na koma inda aka gabatardashi ga duk wanda ke zama fadar har zwa takwas na safe inda kowa ya kama gabanshi zuwa wurin biɗa .
Ƙanin uban ƙasa aka umurta daya nuna wa baffa na gari har gidan gonan su dake wajen ƙauyen muka zaga yna mana bayani  daga nan muka nufi gonaki inda aketa aiki ba kama hannun yaro.

Da rana kuwa dawon nan ne da nonon saniya aka dama cike da masaki aza zubawa kowa har ya rage da dama aka juye a babban kwanon sha aka fitar garka. Innata ta saje da yan gida gwanin sha'awa duk da kasancewarta farar buzuwa ce amma tana da hazaƙa sosai,sai nan nan suke da ita musamman gashin kanta mai tsayi yan matan gidan nata mararin shi.

Ba laifi na ɗan saba da yan samarin gidan sa'an nina irin su haladu ina binsu idan aka aike su haka dai har  da yamma aka ɗaura babban tukunya domin tuƙe tuwo wanda zaa raba kaf gidan a kwashe na zazafen safe(wanan dalili yasa nace sau ɗaya ake ɗaura tukunya a gidan).

Dalilin da yasa na kawo maku wanan tarihi domin ku san asalin tushena wanda ba dukan kune kuka sani baa.

Zama yayi zama a gidan uban ƙasa domin baffana ya samu aikin yi;shi aka ɗaura wa alhakin kula da gidan gonan suasion,dabbobi dake ciki harda  wuri aka bashi yana ɗan noma shima. Inata dama ta iya kitso sosai tana yi tana samun ɗan kwabon kashewa,nima ina bin su haladu kasuwaninin ƙauyukan kusa muna ɗan ƙwadago muna samu.

A hankali zama ya miƙe har muka zama cikakkun yan gari,harshen mu ya saje da nasu mun iya hausa sosai,ganin za'a shiga haƙƙin baffana aka basu ɗaki ɗaya a nan gdan shida innata dama ni cikin yaran gidan nake kwana, inata ƙoƙari ga dubarun kasuwanci kala kala ba laifi mun samu.

Bayan kamar shekara ɗaya haka baffana ya yanke shawarar zai shiryawa innata dani mu tafi ganin gida duk da ya taɓa bada saƙo sau biyu wa yan ƙasar mu a kai wa yan uwan su da shaida masu muna cikin ƙoshin lafiya kuma saƙonnin sun isa,amma yaga dacewan tafiyar ta ashe duk lokacin tana da shigar ciki bamu sani baa.

Kwasam sai turawa suka shigo garin aka bana sanarwa ya zama dole ko wane magidanci ya bada ɗan shi namiji a saka shi karatun bako da turawa suka zo dashi kuma daga gidan uban ƙasa zaa fara.

Aka yi rashin asa'a yawancin samarin gidan suna wurin fatauci garuruwa bamu fi mu uku dake gida baa(ni da haladu sai salmanu),ai kuwa aka kwashe mu iyaye mata na kuka baa so dole aka tafi damu masaukin su inda suka kafa makarantar.

Gashi idan an kwashe mu sai yamma ake dawo wa damu,ana isa nida aka gani da gashi cike da kai aka aske shi tas na koma kamar bahaushe aka shiga koya mana karatun boko daƙarfin tsiya duk da bama gane komi har yamma aka dawo damu gida.

Nan innata ta shiga kuka hadda birgima wai an aske mun gashi na koma kaman rago wanan mugun abun yafi komi mata ciwo saboda idan ta tafi garin mu da ni a haka ba ƙaramin abun gori da ALAH wadai bane dole sai an jira gashina ya tofo zamu tafi.

Da ƙyar aka rarasheta akan ta haƙura da tafiya dani ta wuce ita ɗaya wani lokaci idan gashin ya fito a tafi dani...

Tace ba zata iya zuwa ba tare dani ba dole ta haƙura har wani shekara,haka dai muka cigaba da zuwa karatu wurin turawa idan mun yi taurin kai abamu horo mai tsanani dole muke mayar da hankali sosai.

Cikin wattani shida muka iya karatu lissafi,rubutu da karatu masu sauƙi daga nan suka ce zamu shiga mataki na gaba watau aji ɗaya kuma a cikin garin boɗinga zasu kai mu inda suka gina makarantar kwana wanda a yanzu aka mayar (WTC women teaching college). Inata karatu na a makarantar kwana...

Cikin ikon ALLAH baffa na ya samu karɓuwa ALLAH ya haɗa shi da wani attajirin ɗan kasuwa a cikin birnin sokoto mai suna alhaji mu'azu wanda keda matar aure ɗaya amma ALLAH bai basu haihuwa baa.

Mahaifiyata ta kasance mai aikin wanke wanke da shara,baffana kuwa shike kula da gidan gonar su tare da dabbobin su mai tarin yawa saboda ya kasance mutum mai gaskiya da amana.

Zaman mu ya koma cikin gari wanda sai an mana hutu nake zuwa nan ɗin.Har muka shekara muna jin daɗin zama dasu sai baffa na ya nemi alfarma zai kwashe mu zuwa ganin gida tunda an kwana biyu duk da yana yawan yin aike a kai akai. Alhaji ya nuna rashin amincewar shi domin bai san inda zai sake samun mutum mai amana irin baffana baa,nan dai suka yi shawara ni da innata zamu tafi mu yi kwana biyu.

Shirye shirye sosai hajia aisha tayi mana na zuwa gida da yake a gidan gonan su muke kwana an bamu ɗaki biyu ai kuwa cikin daren ranar yan fashi suka shigo gidan gonan nan take suka harbe baffana a gaban mu,suka buga mun gindin bindiga nan take na sume innata ma ta faɗi a sume suka kora shanayen masu yawa sosai.

Abunka da wajen garin ne baa san abunda ya faru ba sai da safe labari ya riski alhaji mu'azu wanda yazo a hargitse aka kwashe mu sai asibiti domin bai kula da ɓarnar da aka mashi baa.

Cikin ikon ALLAH na farfaɗo amma anyi mun ɗinki a goshi,innata kuwa tayi ɓarin ciki yayin da ALLAH ya yiwa baffa na rasuwa.

Sosai aka tausaya wa innata domin kuka take na fitan hankali idan ta koma garin mu bata san e zata faɗa baa,ba lallai bane a yadd mutuwar Allah yayi a wanan lokaci da ilimi yayi ƙaranci!.aka sanar dasu uban ƙasa aka tafi da gawan gidan shi dai aka shirya baffa na zuwa gidan shi na gaskiya muna ji muna gani.

Iya bincike baa gano ɓarayin nan ba,akace inata bata da takaba domin cikin wattani uku ne ya zube mata ,sai hajia Aisha da mijinta suka ɗauki soyayyar duniya suka ɗaura mun suke kula dani innata kullum zugum sai kuka.

Bayan wattani uku da faruwar haka alhaji mu'azu ya shirya da niyyar raka mu gida wurin dangin mu cike da abun arziki,hajia aisha ta ruƙi a bar mata ni ta saka ni a jami'a.Alhaji yace bashi da wanan dama saiya nemi izini wurn dangin baffa na.

Cikin ikon ALLAH muka isa ƙasar yamen har gidan kakkani na wanda suka haifi baffa na,hannu biyu aka amshi alhaji bayan innata ta masu bayanin ko shi wanene. Daga bisani ya masu bayanin abunda ya faru!, dama basa jin hausa sai innata ta sake masu bayani da yaren mu.
Abun ka da mutanen dori babu ilimi ba tawakkali suka  shiga zage zage wai innata ta haɗa kai da alhaji an kashe baffa na don taga mai kuɗi ne tana son auren shi,zagi iri iri daga bisani suka ce sai an fiddo masu da gawan ko a biya diyya.

Ganin rigima ta kasa zuwa ƙarshe ya nemi da a kai shi wurin manyan gari.
MUKA tafi innata nata kuka aka sake mayar da magana,sai suka goyi bayan dangin baffa na,tare da yanke hukunci koda ya biya dole zai aureta domin idan ya barta a garin gudunta zaa rinƙa yi.

Babu yadda ya iya aka kira yan uwan innata da na baffa na suka yi kuɗi na raƙumai bakwai wanda kuɗi ne masu yawa ya biya diyya ,sanan ya biya sadaki aka ɗaura aure nan take.

Gaba ɗaya gidan su innata muka nufa yace dasu zai barta ta kwana biyu daga baya zai dawo su koma tare. Basu ydda dashi ba kamar sun san bazai sake dawo wa ba akace sai ya tafi dani.

Washe gari ina kuka muka rabu da innata muka dawo tare da alhaji,Babban kuskuren da alhaji yayi bayan mun dawo sai ya ɓoyewa matar shi ainihin abunda ya faru,yace mata an basu ni kyauta su riƙe.

Murna wurin hajia ba'a magana ai kuwa ta shiga kula dani daga bisani na fara jami'a.

Cikin sa'a na fara karatuna ina amfani da (barau muazu) babu wata damuwa sai kewar innata wanda idan na tunata nakan yi kuka sosai.
Shiru shiru har aka share shekara alhaji bai da niyyar waiwayar innata a lokcin inada shekaru ashirin a duniya kuwa,mun  samu hutu na yiwa hajia magana inason zuwa ganin gida tace zata yiwa alhaji magana muje duka tare.

Fafur yaƙi amincewa yanata faɗa wai sai na kamala karatu!" da yake a lokacin zuwa aji bakwai ake tsayawa",inada zurfin ciki sosai shi yasa ban taɓa faɗawa hajia mijinta ya auri innata baa,haka naci kuka har na hakura.

Sai dana kamala aji biyu na roƙi alhaji ya barni naje da alƙawarin zan dawo idan hutu ya ƙare sanan ya amince,aka shirya mun na tafi....

Da kyar na gane wuri duba da an samu cigaba sosai a garin.

Yan uwan innata sun yi kuka sosai da naje domin a cewar su bayan tafiyar mu anata zagin innata wai ta sayar da yaro wa alhaji ta amshi kuɗi!, amma tana ƙoƙarin shaida masu alhaji mutumin kirki ne ba zai taɓa cutar da kowa baa.
Sshiru shiru alhaji bai dawo ba har aka shekara taga tsangwamar ya mata yawa ta gudu ta bar garin zuwa shiyoyin agadaz.

Bayan wasu shekaru ta dawo tare da sabon mijinta babban ɗan kasuwa ne wanda suka samu mallamai aka kashe auren alhaji aka ɗaura nashi.

Ta ɗauki lokaci a gida sanan ta koma baa ɗaɗe ba ciwon kwana biyu ta rasu!,nayi kuka sosai naji tsanar alhaji kamar kada na koma amma sai na tuna yadda hajia ke sona zata shiga wani hali dole tasa na koma.

Bayan na dawo na faɗa masu innata ta rasu ai  jikin alhaji yayi sanyi alamar rashin gaskiya,hajia tasha kuka abun tausayi.

Tun daga lokacin na tattara hankali na wuri ɗaya inata karatu har na kamala ,alhaji yaso ɗaura ni a harkar kasuwancin shi tunda bashi da ɗa ko jika. Na ƙi kasacewa ina ƙullace dashi nace aikin ɗan sanda nake so.

Hajia ta mara mun baya na samu aiki kuwa tashin farko aka tura ni garin ibadan inda na shafe shekaru uku ina aiki daga bisani aka dawo dani cikin sokoto. Hajia nata farin ciki duk da ta tsufa sosai lokacin inada shekaru ashirin da bakwai alhaji ya mada aure zai mun in natsu a gidan shi domin bashi da lafiya sosai.

Na nuna ban aminta ba karatu zan cigaba domin an samu cigaba an buɗe jami'a babban a garin legos akwai fanni kala kala lokacin nan ne federal capital.

Ba'a wani daɗe ba ya rasu,yan uwanshi suka taru aka raba abunda ya bari kowa ya kwashi rabon shi aka ba hajia ma nata har gidan da take ciki. tsufa ya kamata sai ta samu yaran dake zama tare da ita cikin yan uwanta.

Cikin wanan shekara aka mai dani aiki lagos domin a lokacin akwai yawan kashe kashen mutane da yan
*ƘUNGIYAR ASIRI*  keyi a kudancin nigeria musammman a yan jami'a.

Kafin in tafi hajia tace in shirya zata kai ni wani wuri ta haɗa ni da wani mallami wanda shike taimakon alhaji lokacin yana da rai. Muka shirya sai wani ƙauyen yabo gidan wani babban mallamin zaure tayi mashi bayani irin aikin da nake yi da kuma inda aka tura ni.

Sai yace wani irin kariya nake so?,tace irin wanda aka ba alhaji!,yace zai bani amma duk abunda ya biyo baya kada a kuka dashi domin shima alhaji rashin cika alƙawari yasa aka ɗauke shi.

Ban fahimci komi ba a lokacin dai tace ayi mun ba matsala. Yace mu dawo gobe da kayan aiki kamar yadda ta sani,sauran a bar mashi zai kula da komi.

Washe gari muka biya kasuwa hajia ta bani kuɗi muka sayi wuri(wanda wasu ke kira da arin kuɗi),farin ƙyale yadi huɗu,turaren binta sudan sai babban masaki muka nufi ƙauye....,cikin wani ɗaki mai duhu muka shiga duka ya amshi abubuwan nan ya baza ƙyalen tare da zuba farin kuɗi ya shiga kirari irin yadda ake yiwa aljanai idan ya kai ya watsa turaren ko wane kusurwa zuwa wani lokaci wata mace ƴyar ƙarama ta bayyana tana faɗin ɗan samari ina maka maraba da shigowa cikin wanan ƙungiya taa(KLU KLUX KLAN) zaka samu kariya har ƙarshen rayuwar ka idan har ka cika mana sharuɗan mu!,zaka samu ɗaukaka kayi suna duniya ta sanka akan aikin ka!,bama kisa,bama shan jini haka bama cutar wa sai bawa yan ƘUNGIYA kariya!. Ka amince?

SHIRU yayi,hajia ta mun alama da na amsa da eh!,haka na amsa aka rantsar

dani bayan an faɗa min duk dokokin babu kisa ba shan jinin kowa zaa bani ƙarfin iko da zan kare kai na a ko ina ,babu mutum ko aljan bare ɗan wani
*ƘUNGIYAR ASIRI*  da yaisa ya cutar dani a doron ƙasa,amma ya zama dole idan lokaci tayi duk abunda ƘUNGIYA ta buƙata zan bayar.

Haka na aminta inaji ina gani aka yi komi tare da bani wani karfe siriri na rinƙa murzawa a damtsen hanu na har ya shige da kan shi.

Kun san wanene wanan mallamin da aka kai ni wurin shi yayi sanadin shiga na
*ƘUNGIYAR ASIRI?*  shiru suka yi kowa ya ƙagu yaji sauran labari!

uhm ba wani bane illah"Mallam Nasir"mahaifin HAJIA LANTI!


Follow
vote
comment
share





 
[7/1, 15:42] Leema: *🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
       *NA*

          *L££MA*

wattapad
*@leemaMuhammad826*

  _Sadaukarwa gare ku_👇🏻

*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*

*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*



*🅿21-22*

        Zainab Wai Ina soyayyar da kike mun ya tafi,har kin manta tsawon shekarun da muka kwashe a tare?,kiji tausayi na mu koma gidan mu zainab!

Tsaki taja a gadarance (irin kanta yayi girma ɗin nan),kai mallam!,ko ka bani takardata ko kada ka bani gidan mu zan wuce daga nan,sanan ka bani wayata tunda ba da kuɗin ka na saya ba ehe.

Dariya abun ya bashi yadda take magana tana kaɗa kai kamar kaɗangare...,wayar ki na cikin mota muje ki amsa,"yana kai nan ya wuce abun shi domin yasan idan ya biye mata ana shiririta ba zata yi yadda yake so ba".

Har ya isa ya zauna cikin motar bata zo ba..., ɗauke kai yayi daga sashin ta yana latse latsen wayar shi amma hankalin shi na kanta,sarai yasan zata zo dama haka take lokacin da kake lalabata ba zata taɓa yin yadda kake so ba saboda tsabar taurin kai da jan aji.

Hangota yayi tana zuwa sai jinini take zubawa...,ya sake tamke fuska babu alamar wasa tare da saurin a wayar nata saman ɗaya sit din!,tana zuwa ta miƙa mai hannu ta window inda yake zaune alamar ya bata,hankalin shi na kan wayar shi yace"zagaya ki ɗauka gashi saman sit!

Bata kawo komi a rai ba kawai ta zagaya har ta ɗaura hanunta saman wayar ya riƙe hanun da wayar sosai,tana dago ido ya watsa mata harara,"zauna ki rufe kofar !",ba shiri  ta shiga  da yi yadda yace,bai tsaya wasa ba kawai yaja motar sai hanyar babban gida...,tana ganin haka ta fashe da kuka,Ni ba zan koma gidan nan ba kawai ka sauke Ni in tafi gidan mu!.

Bai amsa mata ba ya cigaba da kwarara gudu don ranshi..,layin Safiyyah ta kira,tana ɗagawa tace,"kiba wa mama waya don Allah!",mama ta fita,lafiya dai yaya zainab?,babu lafiya Safiyyah Muhammad da yan uwan shi zasu kashe Ni ne kawai,yau kwana uku kenan ina cikin ƙuncin rayuwa sun hanani farin ciki,an salwantar min da mami,cikin dana samu kuma ya lalace har an wanke mara,yanzu haka farautar rayuwata suke yi!,tana magana tana kuka sosai shi kuma bai yi yunkurin dakatar da ita ba domin sai daya yi aure ya kara tabbatar da maganar da abban su ke faɗa akan mata tunanin su ragagge ne,basu da lissafi,duk abinda yazo barin su babu nazari ba tauna harshe suke fitar wa koda hakan zai sanadin ɓacin ran koma wanene. Idan banda rashin lissafi a gaban shi zainab take faɗa wa sister ta ƙarama wai shi mijinta da yan uwansu suna farautar rayuwarta!,Safiyya ɗin guda nawa take?,yanzu ta ɗauki maganar ta saka a zuciya ai ba zata sake kallon shi ko yan uwanshi da mutunci ba.

Kome Safiyyah ta faɗa mata oho,domin ta jima shiru tana saurare daga bisani tace shike nan duk yadda ake ciki zan sake kiran ki kuma idan mama ta dawo kice don Allah ta kira Ni.

Cigaba tayi da maganganun na ɓatanci akan ahalin shi ƙasa ƙasa bayan ta aje wayar,bai kulata har suka isa gidan ta saje buɗe sabon babin kuka wanan karon hadda buge buge cikin motar...,wurin adana motoci ya aje nashi sanan ya fita ko kallo bata isheshi ba  ya wuce har ya isa sashin hajiyar shi zainab na zaune cikin mota tana cika da batse wa!,dawo wa yayi wurin motar.

A sanyayye ya furta,"mu shiga daga ciki kiyi wanka ai kici abinci kisha magana",Allah ya kiyayye awani gidan,so kake su ƙarƙare ni?,ta Allah ba taku ba zuri'ar mugun abu,ni ai da nasan haka kuke da ban aureka baa!,ba babba ba yaro kowa ɗan halibut!.

Idan ranshi yayi dubu ya ɓaci domin yatsani rainin arziki da cin mutunci musamman ma iyayen shi wanda ya lura a kowane lokaci zainab na ƙoƙarin ciwa iyayen shi mutunci.

Tsawa ya daka mata,kada ki sake ambatar iyayena zainab,idan takardan ki kike so nayi alƙawrin zan baki amma sai kin faɗa mun mugun hali da ahali na suke dashi wanda ni ban san dashi baa.

Nan take jikinta yayi sanyi kuma domin ba haka taso ba kawai burinta ranshi ya ɓaci ne...,ina sauraren ki fa?,shiru tayi tana nazari domin magana mara tushe take yi itama bata san me take yiba wani lokaci sai daga baya tayi nadama.

Idan babu amsa ki fito mu shiga domin yanzu lafiyar ki ya fiye mun komi idan kin warware kina da daman zuwa duk inda kike so nayi alƙawarin baki takardan ki!.


Jiki asanyaye ta fito tana bin shi a baya har sashin sashin...,hajia lanti na zaune a palo hankali kwance kwatsam taji shigowar su,ai kuwa ta sake waro idanu da kyau idan ba gizo zainab ke mata baa!,zainab ɗin data bari kwance a jiya kamar gawa itace haka fes?.

Wallahi ƙarya ne kin yi kaɗan ki lalata mun aiki mariya!,sororo suka yi ko wane ɗauke da mamaki a fuskanshi domin basu fahinci inda ta dosa ba!,muhammad na tambaya"lafiya mama?",bata ko tsaya binta kanshi ba ta nufi hanyar waje zuwa sashin hajia mariya ai kuwa suka rufa mata baya...

Tana isa har ɗakin baccint ta dame ta kwancetana ramuwar baccin da bata samu ba jiya..,uban dundu ta zuba mata a baya!,tashi munafuka algungunma yau Asirin ku zai tonu a gidan nan daga ke har mijinki!.

A firgice ta buɗe idanu domin baccin ya mata daɗi,menene haka hajia lanti?,abunda kika shuka be shekarun baya yau zaki girba hajia mariya!.

Sosai ta tashi zaune tana ƙokarin ɗaura ɗan kwali..,hajia lanti ta shaƙe mata wuya da hannunta duka biyu sai data kai kwance tana kakarin amai!

Cikin ikon ALLAH sai ga muhammad  a gaba zainab na bin shi a baya inda suka jiyo hayaniya suka nufa..,da saurin ya riƙe hanun maman shi ganin tana  ƙoƙarin aikata kisan kai.

Da kyar ya ƙwace hanunta a wuyar hajia mariya ,zainab dai na kallon ikon ALLAH..,ka barni in kasheta moha wanan matar annoba ce a cikn wanan zuri'a domin duk abunda ke faruwa itace musabbabi.

Kanshi ya shiga duhu alamar yana neman ƙarin bayani amm ba ta wanan yake ba burin shi hajia tabar sashin sai dai yana janta tana turjewa!,hajia mariya kuwa kanta na ƙasa tasan yau asirin su ya gama tonuwa wanda ba haka taso ba a nata wautar ta zaunar da muhammad da zainab ta faɗa masu hajia lanti yar
*ƘUNGIYAR ASIRI CE.*

Kaga munafukar tayi shiru ko don ALLAH ka sake ni moha zan koya mata hankali ne...,hajia don Allah mu tafi sashin ki kada jama'a su taru a nan ɗin.

Ƙara ɗaga murya tayi,sai me idan sun taru?,ai ba ƙarya na faɗa ba daga ita har uban naka duk yan
*ƘUNGIYAR ASIRI NE* ko ƙarya ne hajia mariya?,shiru ya biyo baya yayin da muhammad  ya ƙara shiga duhu,zainab kam ta fashe da firgitaccen kuka domin a tsorace take wurin nan taji ana ambatar
*ƘUNGIYAR ASIRI*  baki yi kuka ba ke kuma sai lokacin da kika ga takardan sakin ki a hannu domin tunda kika zama sillar tonon asiri na wallahi kin gama zama da ɗana!.

Cikin ɗaga murya zainab tace,wallahi zanfi kowa farin ciki idan haka ta faru dominnadaɗe da gane kaf ahalin nan mushrikai ne basa tsoron ALLAH kowa duniy ya saka a gaba!

MARI mai lafiya muha ya wanka mata!,idan n sake jin bakin ki wallahi ba zan maki abunda kike soba sai dai ki mutu!.

Isowar hafiza babban ɗiyar hajia mariya kenan da mai aikin da aka tura mata taje kwana,ta dawo da ita domin taji dalilin da yasa mamanta take yawan ɓoye mata abubuwa alhalin itace babba a gidan gaba ɗaya!,sai dai suna tunkaro palon hayaniya kawaike tashi har suka isa ɗakin lokacin hajia lanti ta sake rarumo hajia mariya da dambe!,zainab na gefe tana kuka yayin da muhammad  ya ɗaura tagumi domin ya rasa abun yi!.

Hajia hafiza ns ganin abunda ke faruwa tsyi baya tare da ambaton sunan ALLAH,bata tsaya wata wata ba sashin mahaifin su kawai ta nufa a tsorace...,babu ko sallama tafaɗa.

Abba! Abba!! Don ALLAH kawo mama zata kashe hajiyar mu gasu can suna dambe..,gaban shine yayi mumunar faɗuwa!.

Takalmi ya shura tare da yin gaba ta bishi a baya har sashin hajia mariya...,koda ya isa dambe ya kachame a tsakanin su sai tonon asiri ake yiwa juna babu ko daɗin  ji!.

Muhammad  na ganin abban su ya fasheda kuka yana faɗin,don girman Allah abba ku fitar damu daga duhu ko zukatan mu zasu wanke daga zargin da ke cike cikinta!

Wani irin tsawa ya daka ma matan nashi"ya isa haka nancy,idan har haka kuka zaɓa zan maku yadda kuke su bayan nan duk sai kun bar mun gidana wallahi!",jikin hajia mariaya ya mutu domin itace zata shiga wani hali saboda ta rabu da kowa nata akan dukiya data samu a dalilin haka mamanta ta mata mumunar baki akan ƙarshenta ba zai taɓa yin kyau ba

Please Login or Register in order to submit comment