Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunda ta saka su kuka har mahaifinta ya mutu da baƙin cikinta,yanzu ina zata nufa?.

Hajia lanti kuwa sai cika take da batse wa,sai me idan kace abar gidan?,idan banda ƙaddara me zanyi da kai?,a dalilin wanan auren naka wani baƙin ciki ne baku ƙunsa mun ba kai da matar ka?.

Ke(haka yake kiran hafiza savoda yƴar fari ce) inaso ki kira duk yan uwanki a waya kice inason ganin su da ƙarfe takwas na dare!,ina nufin duk wani ɗa dana haifa acikina inason ganin shi da uwayen ku mac, har kema zainab halartar ki taron nada muhimmanci"yana kai nan yasa kai ya fice!".

Da ƙyar muhammad yayi nasarar fitar da hajiyar shi daga sashin..,zainab kuwa saboda tsaɓar tsoro da ruɗewa ta rasa inda zata nufa kawai ta koma harabar gidan wurin shuke shuke ta zauna sai waige waige take.

Hajia hafiza ta zauna ƙasa tana kallon maman su ido cike da hawaye,"menene haka mama da girman ku?",a sanyaye tace koma menene zaki ji anjima".

Waya ta fitar ta kira duk wani ƙani/ƙanuwanta da suke uwa ɗaya har na uba ɗaya domin isar da saƙon abban suasion!,duk wanda/wace ta  faɗawa sai ya tambaya lafiya kuwait?,tace idan sun zo kowa yaji.

Bayan ta gama ne ta nuf sashin sauran matan abban su biyu domin faɗa masu saƙon shi.

Hajia hassana itace ta uku wacce bata taɓa haihuwa ba shi yasa ba'a wani sakata cikin tsabgar gidan sai zaman haƙuri take yi,idan yaran sunbawa abban  su wani abu ciki yakeɗan tsakua mata duk da babu rashin ci da sha ko wadaaccen sutura da muhalli gashi bata wani yi boko mai zurfi ba bare a nemi aikin yi.

Lokacin da saƙon ya riske ta sosai tayi mamaki domin ba kasafai ke gayyato ta cikin iirin wanan taro baa,Allah kai mu ta amsa.

Sashin amarya hajia suwaiba wace bata wuce shakaru ashirin da bakwai ba sai zuba rashin kunya da raini,yaranta uku(biyu maza sai mace ɗaya),duk secondary suke,itama da saƙon ya risketa cewa tayi taji kawai.

Yinin ranar ko wanne mutum dake da ruwa da tsaki a gidan a matse yayi shi domin sun matsu suji me zaa faɗa a taron?,banda iyayen dake cikin kiɗma da tashin hankali!,dama dama ma hajia lanti laifin ta ragaggene  a cikin su domin daga sama ta tsinci kanta a ciki kamar yadda mami ta tsinci kanta.

DA ƘYAR da suɗin baki haɗe da jan ido muhammadya samu zainab ta bishi ɗakin samartakan shi tayi wanka cin abinci wanda shima shayi ne ya haɗa a gabanta sana tasha a magunguna domin tayi rantsuwa ko ruwan gidan ba zata sake sha baa.

Baccimai nauyi ya ɗauke ta nan take...,ya jima yana kallonta cike da so da ƙauna,zuciyarshi na raya mashi abubuwa da dama akanta!,duk da yayu alƙawarin sakinta sai dai baya tunanin zai iya rayuwa ba tare da ita baa!,gefe ɗaya kuma maganganun iyayen shi ke mashi yawo a ƙwaƙwalwa wai duk yan
*ƘUNGIYAR ASIRI NE!*

Koda la'asar tayi kusan duk wani jinin ALHAJI BARAUna nesa da kusa yana gidan a sahin hajiyar shi lokaci kawai suke jira cike da duhun kai domin iyayen mata basu faɗa masu komi baa.


  Ƙarfe takwai dai dai a babban palon gidan wanda yake mallakin abban su yayi masu,ko wanne ya samu wuri  ya harɗe an matsu aji zance!,iyayen mata gaba ɗaya suna saman kujera neko wace na zuba wa wacce ta raina harara.

Gyaran murya alhaji barau yayi bayan shiru da ya yi na tsawon lokaci sai ya fara magana;

  Assalamu alaikum ina yiwa kowa fatan alheri tare da kasancewa cikin yarda a amicin ALLAH,duk suka amsa.

Dalilin wanan taro shine domin in warware maku wani ƙulli da baku sani baa,wani babban sirri na rayuwata da mata na biyu na farko(Mariya da amina) wanda baku sanshi ba nasan wasun ku sun daɗe cikin zargi da duhun kai ciki har da surukata zainab.

Da izinn ALLAHa yau zan warware maku duk abunda ya kamata ku sani wanda nasan zai jefawa dukan ku ƙiyayya da tsantsar tsanata a zukatan ku!,koma menene zaku ji azukatan ku bazan ga laifin su ba amma ina mai shawartar ku daku zamo masu yin uzuri da yafiya saboda duk ɗan adam ajizi ne,babu mai wuce ƙaddarar shi domin ku ɗin iyaye ne,sai ƙanan ku da suke jiran lokaci.

Hausawa sun ce ranar wanka ba'a ɓoyon cibi,tabbas kamar yadda kuke zargi ko kuka ji ,ya rutse idanun shi gam sanan ya cigaba,ni alhaji barau da mata na biyu yan
*ƘUNGIYAR ASIRI NE*

Gaba ɗaya palon ya hargitse wasu sun fara kuka,wasu sun miƙe tsaye saboda tsabar tsoro suna neman mafaka,wasu kowa sai kallon iyayen suke da mamaki!.



Hayaniya sosai ya kaure a palon sai da ɗaya daga cikin yaran hajia lanti yayi ƙarfin halin buga tabur da hannu wuri yayi tsit.

Don girman ALLAH ku natsu nayi alkawarin faɗa maku gaskiya yanzu kuwa zan warware komi kamar yadda ya faru a shekarun talatin da suka shuɗe.



Follow
vote
comment
share.

 
[7/1, 15:42] Leema: *🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
*NA*

*L££MA*

wattapad
*@leemaMuhammad826*

_Sadaukarwa gare ku_👇🏻

*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*

*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*


*I am immeasurably grateful to "HUSSAINI ATK" for his willing and generous assistance.I gladly offer my Thanks to him*



*🅿27-28*




UNIVERSITY OF LAGOS,AKOKA akayi posting ɗina a matsayin wanda zai leading"police patrol team zuwa cikin wanan campus ɗin by 6:30 am after all night vigil.

Kayan aiki isassu aka bamu tare da abokan aiki wanda suka san makaman aikin domin ni dai wanan shine karo na farko na. Sai da nayi meetinga da vice-chancellor ,director of student affairs, university administration haɗe da student ashirin da huɗu wa yanda suka kasance shuwagabani daga various constituencies (ULSU,congress,parliament,Hall executives and faculty representatives ) inda muka samo mafita a tare ta yadda zaa magance matsalar ta hanyar;
Zamu aje kwararrun san danda a bakin gate na makarantar

Rarraba jami'an tsaro a ko wane faculty ,Hall and residence.
Duk ɗalibin da zai shigo tun daga gate sai an chaje shi har shiga ɗaukin karatu. Da sauran su

Muna cikin gudanar da aikin ne a washe garin ranar da misalin ƙarfe goma na safe muka tsinci gawar wata ɗaliba bayarba a harabar makaranta ɗalibai sun taru ana kallo!.
Koda akayi bincike muka gano cewa bata wuce shekaru sha takwas ba zasu wurin ɗaukan darasi da safe ita da ƙawayenta sai aka far masu,ƙawaye suka tsere nan akayi mata fyaɗe kace kace tare da harbi da bindiga ta ko ina shine sanadin mutuwar taa!.

Ƙawayen nasa aka nemo mun su biyu domin amsa tambayoyi...,ba wasu bane illa mata ta hajia mariya sai bose wata abokiyar karatun su.

Nan suka tabbatar mana da cewa Ɗaya daga cikin yan ƘUNGIYAR BLACK AXE ne ya gayyato yan uwanshi suka mata wanan aiki domin ya daɗe yana son ita wacce suka kashe bata amince ba.

Tun daga lokacin soyayya mai ƙarfi ya ƙullu a tsakani na da mariya wacce ɗaliba ce a makakantar amma yar arewa ce kasancewa ta kwana biyu a lagos yasa take jin yarbanci sosai kuma ta san mutane a cikin makarantar wanda da taimakonta na samu nasarori sosai wurin kawo ƙarshen yan ƘUNGIYAR ASIRI da dama a makarantar.

Ɓabgaren mallam nasir kuwa muna yawan haɗuwa wurin taron ƘUNGIYAR su wanda bayan wasu wattani akan yi!,basu taɓa neman jinin kowa a wuri na ba sai kayan aiki irin na farko da make saya duk bayan wattni shida a sake mun sabon shiri.

A hankali na fahimci mallam yayi nisa sosai cikin ƘUNGIYAR har shugaba ƘARAMA na ƙoƙarin bashi kujerarta domin shekarunta ya ja sosai,shine mataikamin ta babu abunda bata koya mai ba duk da kasancewarta jinsun al'jan shine mataimakin taa.

Kwanan duniya bani da wani buri da ya wuce inga bayan mallam nasir!,amma ta ina zan fara?.

Na share shekara ɗaya ina aiki a tsakanin lagos,ibada,port harcourt zuwa imo wanda duk ya shafi yaƙi da ƘUNGIYAR ASIRI a manyan makarantu!,duba da irin nasarori da nake da taimakon ƘUNGIYAR su mallam nasir shi yasa duk inda na haɗu da yan ƘUNGIYAR ASIRI nake gane su kuma babu abunda suka isa suyi dani domin nima a shirye nake!.

Lokacin da abubuwan suka lafa sosai na samu ƙarin girma a wurin aikin mu dai dai mariya ta gama karatu soyayyar mu tayi nisa muka tafi wurin iyayenta a bauchi ta gabatar dani. Bayan sun yi bincike ne mahaifinta ya nuna rashin amincewr shi wai bani da cikakken asali ba zai bani auren ta baa.


Munshiga tashin hankali sosai ai kuwa ta bijire masu wanda a ƙarshe ma masallaci muka tafi aka ɗaura mana aure!,haka muka bar bauchi iyayenta na fushi da ita sosai...,na samu canjin wurina aiki zuwa ondo state,akure muka tafi tare.

Rayuwa mai cike da so da ƙauna muke yi kuma ina aiki na sosai har ALLAH Yaba mariya ciki munata farin ciki...,a lokacin ƘUNGIYA ta kira taro na gaugawa domin tana da buƙata!.

Tashin farko mallam nasir ya yanke hukunci akan abunda ke cikin matata suke iso,idan ya isa haihuwa zai turo a cire ruhin jariri koda zafa haihu zai zo babu rai!.

Sai dana gama jin bayanin su tsaf kuma na ƙare masu kallo da kyau sai nace a bani lokaci zanyi shawara,suka aminta nan taro ya watse.

Washe gari sukuku na tashi har na kasa zuwa wurin aiki domin na rasa mafita,idan nace zan bijire masu zasu aikata mummunan abu a kai na,idan nace zan bar ƘUNGIYAR zai iya zama silar rasa rai na gudun asirin su ya bayyana gashi ban samu cika burina akan mallam baa.

Kawai na yanke shawara zan faɗa wa matata gaskiya gudun kada wani abu ya biyo baya taga laifi na!,ranar da dare na zaunar da ita cikin hiƙima na warware mata komi tun daga zaman mu gidan alhaji mu'azu har wanan lokac(dama tasan asalina da kuma zaman mu gidan uban ƙasa).

Tayi kuka sosai na tausaya mun irin zaluncin da aka mana da iyayena tare da alƙawarin taimaka mun dama mashe ce mai fahimta sosai bata tsorata da kasancewa na ɗan ƘUNGIYAR ASIRI baa.

Tace mun hanya ɗaya zamu bi domin cin nasara akan su mallam nasir shine shiga ƘUNGIYAR ASIRI mai taken"EIYE",sai na tambaye ta ya akayi ta san da wanan ƘUNGIYA kuma A Ina yake?.


Tace lokacin da suka shiga makaranta suna sabbin daliɓai sai aka rinƙa tsorata su a ɗakin kwanan su aka hana su sake wa!,sai wata tsohuwar ɗaliba mai suna benita tace idan suna so zata kai su wurin wani ravel father a nan wani ƙauye zai basu taimako.

Kasancewarta musulma sai tace ba zata yi ba kawai zata cigaba da adduce'a ne Sai benita tace gwara dai muje duka yan ɗakin ya mana bayani wanda baya raayi babu dole ai.

Duka mu huɗu muka aminta aka tsaida lokaci muka shirya zuwa ƙauyen nan...,cikin wani church yake zama asali ma shike gadin wanan church ɗin sunan shi"father paul"baya ko jin hausa sai yarbanci.

Benita tayi mashi bayanin abunda ya kawo mu sai yace idan har muna buƙatar kariya har ƙarshen rayuwar mu zamu samu amma sai mun shiga ƘUNGIYAR ASIRI na"EIYE"!,tsoro ya kama mu sai yace zai mana bayani.

_"eiye"kalma ce ta yarbanci wanda ke nufin tsuntsu(bird),"Eiye ko ni isaasun eye nbuta"ma'ana,although the bird has no utensil it has no feeding problem.In yoruba the name also has bone chlling connotation of witchs or wizard and they are believed to fly by night .
Kenan ya ƙunshi abubuwa biyu ne wana ƙungiya bada babban kariya da kuma maita.but mainly the objectives of the EIYE confraternity and the need to protect its upsurge necessitated secrecy.
Suna da ƙarfi sosai wanda har lokacin baa samu wata ƘUNGIYA da zata iya karawa dasu ba kaf faɗin nigeria duba da yadda yarbawa suke da ƙarfin tsafi da sanin kan magungunan gargajiya shi yasa yan ƘUNGIYAR keda masifar yawa a ko wane jaha akwai su amma akure shine madaddalin su,shi father paul yayi retire ne shi yasa ya dawo wanan ƙauye yana kula da church dama baa iya gano su domin suna da ƙafin ibada a adanin su na kirista....

Mariya dai tace bata buƙata sai yace ba zaa mata dole ba amma idan har ta tona asirin wanda suka amince zata rasa ranta ne.

Bayan ta gama bani wanan labari sai naji ina raayin ganawa da wanan dattijo domin samun cikakken bayani daga gare shi.

Lokaci muka saka zuwa lagos wanda da ƙyar muka gano inda yake sai dai aka ce mana ya koma akure da zama!,haka muka sake dawo wa domin lokacin ba wayan hannu sai telphone kuma ba kowa keda halin saya baa.

Inda aka mana kwatance muka same shi cikin wani church,mariya ta sake mashi bayanin kanta. Nan take ya gano tare da faɗa mata ai yana bibiye da lamuranta tunda tasan sirrin su.

Da kaina nayi mashi bayanin abunda ya faru da kuma taimakon shi nake nema.

Nan yayi kirari sosai da harshen yarbanci ssanan ya buga bango tare da nuna mana hoton sauran yan ƘUNGIYAR MU yana tambaya sune wanan?,na amsa.

Ya kece da dariya sanan ya gimtse fuska;wanan ai ba wata ƘUNGIYA bace ila kawai taron mugayen aljanu kafirai wanda basu da wata addini,burin su kawai shan jinin al'umma da ƙuntata masu sune suke haɗa kai da mallaman tsobbu masu amfani da aljanai domin biyan tasu buƙatar!, yayin da mallaminzai rinƙa basu jini suna sha su kuma suna biya mai dukkan buƙatar shi! kun ga kenan babu wanda ya ƙirƙiri wanan ƘUNGIYA na cin amana sai mallam nasir tare da haɗin gwiwar shaiɗaniyar aljanan nan ƘARAMA!.

Hanya mafi sauƙi da zaka iya yaƙar su shineta hanyar shiga wanan ƘUNGIYA TA EIYE kai da matar ka domin samun kariya a gare ka,ita da kuma abunda ke cikinta.

Wanan ƘUNGIYA tamu akwai haɗin kai matuƙa fiye da tunanin ka,muna goya wa juna baya tare da tsakawa juna komin tsanani komin wuya!,bama shan jinin kowa idan har kariya kake buƙata,mayyun dake cikin mu suke cin naman mutane wanda suka zallunce su.

Sanan kana iya fita cikin wanan ƘUNGIYA duk lokacin da ka buƙata muddin dai zaka riƙe sirrin mu babu abunda zai faru da kai har ƙarshen rayuwar ka muna tare da kai.

Ba tare da wani dogon tunani ba na aminta zan shiga wana ƘUNGIYA,itama matata ta aminta zata shiga domin cikar buri na.

_Wa'iyazubillah lallai jahilci babban cuta ne !,domin da munada wadataccen ilimin addini da duk haka bata taso baa!,da zamu kasance masu dogaro ga Allah,masu tawakkali da miƙa lamuran su ga ALLLAH,masu neman zaɓin ALLAH jajircewa wurin ibada da neman tsari wurin ALLAH daga azzalumai da shaiɗanun ajanai_


AN gabatar damu ga sauran yan ƘUNGIYA suka amshe mu da hannu biyu tare da alƙawarin taimaka mana har burin mu ya cika,an mana bayanin yada za muyi idan muna buƙatar taimakon gaugawa a wurinsu domin basa taron meeting sai ya kama dole.


Tunda muka shiga wanan ƘUNGIYA NA EIYE ban sake bita kan su mallam
nasir baa,inata tsabgogin gabana da matata har wa adin da suka ɗiba mun ya cika (watau wattanin haihuwar matata),domint tun kafin lokacin sun yita kiran meeting ban tafi baa.


Ashe suna bibiye da lamuran mu duk da basu san na shiga wata ƘUNGIYA baa,kwatsam naƙuda ta taso mata cikin dare na shiga gidan unguwar zoma dake cikin barrikin mu na yan sanda na faɗa mata,tana zuwa na bar su tare na nufi inda kayan mu yake na buga bango na kira father paul na sanar dashi!....,yace kada in daw komi na hannun"Flayers",wasu manya dga cikin yan ƘUNGIYAR masu kula da irin wanan hayaniya tskanin abokan gaba.

Ai kuwa ina nan zaune cikin ɗakin father paul ya kamo mun hoton abunda ke faruwa;flayers na ƘUNGIYAR EIYE ne a sama suna ta artabu da aljanun da mallam nir da ƘARAMA suka turo su tafi da abunda mata ta zata haifa!,baa ɗauki lokaci ba suka gama dasu ta hanyar ƙona su.

Yace in kwantar da hankali na babu abunda zai faru dani da ahali na...,Allah yasa mata ta ta haihu lafiya Aka samu yan biyu mata.
Ba ƙaramin farin ciki muka kasance ciki ba muna ƙara gode wa yan wana ƘUNGIYA TA EIYE da suka taimaka mana.

Unguwar zoman ke zuwa tana kula da ita har aka kwana bakwai cikin barikin mu akayi taron suna yara suka ci(HAFIZA DA HANAF),ya nuna hajia hafiza babban ɗiyar hajia mariya da abokiyar haihuwarta hajia hanaf,"sune muka haifa a akure".

Ashe wanan ɓarna da akayiwa yan wanan ƘUNGIYA ba ƙaramin tayar masu da hankali yayi baa!,musamman ƘARAMA data rasa manya daga cikn aljanun taa. Suna ta shiri yadda zasu ɓullo mana....


Muna zaune lafiya tare muke rainon yaran mu har suka yi wattani shida yan ƘUNGIYAR su mallam basu samu waa hanya na cutar damu baa,domin dai ko inda muke basu isa su ƙaraso ba bare har su samu ganin su a cutar damu. Duk inda suka ɓullo sai YAN ƘUNGIYAR EIYE sun ci nasara a kan su!

Cikin ikon ALLAH na samu canjin wurin aiki zuwa ainihin gari nab(sokoto) tare da ƙarin girma zuwa matsayin ACP(asistant commissioner of police),raina bai so ba domin nan kudu yafi mun daɗin zama cikn ƙabila ba munafunci,hasada ko ƙyashi sai ma girmamawa da samun alherai iri iri.

Cikin hutun dana samu na sati ɗaya kafin kama aiki a sokoto muka yanke shawara zamu bauchi wurin iyayen hajia mariya mu roƙi gafarar su tare da kai masu yara su gani.
Tayi farin ciki da wanan shawara duk da cewa a tsorace take kada su ƙi amsan mu.


Taro na musaman ƘUNGIYA ta kira aka ƙara tsafe mu tas da bamu wasu powers na musamman tare da mana alƙawarin a duk inda muke a faɗin duniya idan har muna neman taimakon su,muyi amfani da kayan aikin mu a kira su zasu bayana a bango,idan nazuwa ne flayers zasu bi dare su iso.

Mun wuni wurin su sanan muka rabu cike da kewar su..,cikin bariki ma an haɗa mana walimar cin abinci na dare domin nuna godiyar su akan hidimar da nayi da al'umman garin.

Washe gari muka kama hanya zuwa bauchi..,bayan mun tabbatar an tafi da sauran tarkacen mu zuwa sokoto zaa gyara mana gidan da aka bamu.

Da yake gidan su ba mai wahalar gane wa bane muka isa lafiya,ai kuwa jin mariya ce tazo gidan nasu aka kaure da koke koke wanda bamu san dalili baa,wasu yan uwan nata ma ko kallo bata ishe su baa....


Sai da muka natsa ne mamanta ke mana bayani ai bayan tafiyar mu baban su ya kwanta ciwo saboda baƙin cikin ta har ALLAH ya ɗauki ranshi domin itace babba a gidan suasion,da ƙyar ya haɗa mata aka turata jami'a gashi ta dawo ta bijire mashi(dama abunda yan uwanshi suka faɗa mashi kenan duk mace taje jami'a fantarewa take yi gwara ya aurar da ita yaƙi ji).

Nan dai taci kukanta domin an tabbatar mata har ya ar duniya bai yafe mata baa,mamanta ta amshi yan biyu tare da sanya masu albarka kuma tace ta yafe mata duniya da lahira.

Sauran yan uwanta dai sun ɗauki zafi aganin su itace sillar mutuwar baban su. Kwana uku muka yibta zaga dangain su daga nan muka tafi da alƙawarin zata sake zuwa idan an kwana biyu,muka br masu ƙudi sosai a lokacin suna da daraja matuƙa.


Na kama aiki cikin sokota babu wasa,yarana da matata sun samun kulawa kwatsam wata rana mallam nasir yazo gida na bana nan da niyyar cutar da matatada yara!,nan take ya kasa yin komi domin sun fi ƙarfin shi!
HAKA ya tafi yana cizon yatsa amma ya bar mata saƙo ace yazo nema na...

Koda ta faɗa mun ban wani damu ba na cigaba da aiki ne...,wata rana ya same ni wurin aiki wai yazo bani hakuri akan abubuwan da suka faru a baya tsakani na da yan ƘUNGIYA shima yanzu yayi nadama kuma yana son ƙulla zumunci dani idan har zan aure yarinyar shi AMINA(hajia lanti) inzo in ganta sadaki kawai yake buƙata domin yasan ko wane lokaci ya ƘUNGIYA na iya ɗaukar fansa a kanshi.

Nace ya tafi idan nayi shawara zan neme shi....,koda na dawo gida na faɗa wa mariya sai tace ita ta amince in auro amina idan har ba wata mugun abu yake shirin ƙullawa baa...,sai nace sai na tuntubi ƘUNGIYA.

A tare muka kira father paul muka sanar dashi;sai yace tabbas mallam nasir na cikin matsin rayuwa daga shi har iyalan shi domin ƘUNGIYAR su ta tarwatse duk sun halaka a sanadin harin da suka rinƙa kawo wa yan ƘUNGIYAR mu!,yanzu haka daga shi sai ƘARAMA wacce ta lashi takobin ganin bayan shi idan har bai kawo mata yaran da aka haifa nawa baa,jinin Ɗiyar shi amina zai zama fansan ran yaranta aljanu sanan shima ta mashi tonon asiri kafin yabar duniya.

Wanan dalili yasa ya shiga tashin hankali duba da yariyar ta isa aure shi yasa yake so ka aure ta zata fi samun kariya a ƙarƙashinka. Wanan raa yin kane ka aureta idan kuma baka so ba dole.

Mariya tace ta amince in auro amina domin tsiratar da rayuwarta daga shiga hatsari...,duk da na nuna bana raayin ƙarin aure amma ta nace wanda yaso ya shafi auren ta baa!,duba da yadda mallam nasir keta zirya tsakanin gida da wurin aiki ne neman alfarma.

Ba don naso ba muka shirya zuwa gidan shi...,yayi farin cikin ganin mu kwarai!,na gabatar mai da buƙatar nazo neman auren yar shi amina ce.

Nan yasa aka kira mana ita lokacin bata wuce sha takwas ba kuma kyakyawa ce daidai misali doguwa baƙa.

Ban wani damu ba domin bata mun ba haka dai mariya keta ririta magana tana gyara amina wurina wanda itama ta nuna bata so tana da saurayin da mallam ya masu aƙawarin aure dashi.

Ƙiyayya sosai take nunawa amma banda lokacinta cikin sati ɗaya kacal da taimakon mariya muka kai yan kaya aka bada sadaki sai ɗaurin aure....

Kunji yadda akayi na samu kariya daga mugun nufin malam nasir kai na da taimkon ta kuma na auri hajia lanti domin kuɓutar daga ita daga halaka.

Ashe mallam yasan mugun abunda ya shirya mana wanda shine sanadin tilastawa in auri lanti!


Follow
vote
Comment
share.
[7/1, 15:42] Leema: *🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌸🌸🌸 🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
*NA*

*L££MA*

wattapad
*@leemaMuhammad826*

_Sadaukarwa gare ku_👇🏻

*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*

*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*


*To the many persons who have assisted in Inspiring and motivating me,reposting,sharing,following ,voting and comments of this little book of mine,heartfelt thanks are extended much especially;*

*Muhammad Kareem Kd(daddy)*
*Hassan ATK*
*Real hassena oganniya*
*Ummu abdallah*
*Majmiy jumare*
*Siyama Ibrahim*
*Jamila mopol*
*Saratu Musa*
*Aisha Abdullahi gwazawa (Mrs noor)*
*Aisha Isah Adamu(maman noor)*
*Mugirat Musa*
Husna kamshi*
*Aunty Maryam(maman Muslim)*
*Amina aliyu farin wata*
*Queen acid*
*Mrs ganza darling*
*Amira Raji*

*The catalogue of names is so extensive it cannot not be list all here,but I'm deeply greatful to all who have given of their love and time.*






*🅿25-26*


Cike da borin kunya hajia lanti ta zaburo tana faɗin,sharri ne!, sharri yake mun bakin su haɗe da matar shi don a tuzarta Ni a gaban yarana!,amma Ni har mahaifina ya bar duniya bai taɓa shirka ba bare shiga wata
*ƘUNGIYAR ASIRI* ,mutum ne salihi bawan Allah bai riƙo da addini.


Ƙaryar banza kawai,"hajia mariya ta katse ta",ai dama na faɗa maku da kin san wanene tushen wannan mugun abun da baki nemi tonon asiri da ci mana mutunci ba!,ai yanzu kin ji ko?.

Don Allah rufe mun baki muguwar azzaluma ma irin ki!,waya kasa dake?,kai kuma tsohon banza idan har abinda kake faɗa gaskiya ne mene ne hujjar ka?.

Murmushi yayi irin nasu na manya sanan ya janyo wani ƙaramin akwatin ƙarfe irin na zamanin baya a gefen shi,duk yayi ƙura an ƙalgame shi da padlock.


Ina hajia lanti?,gani nan kusa da kai ai!,wanan akwatin na wanene?

Shiru tayi tana nazari...,sake ɗago mata yayi"duba da kyau dai",na mahaifina ne,amma ina ka samo shi?,madallah ya furta yana ƙoƙarin murɗe padlock ɗin da hannu...,buɗewa yayi ya ɗago jan ƙyale mai ratsin baƙi wanda yayi ƙura sosai ,dogon tasbaha mai manya ɗiya wanda komin tsayinka idan ka zura a wuya zai ja maka ƙasa,takalmin jan fata sai wani ƙaton zube na azurfa sai ƙyalli yake daga karshe sai hoto black and white irin na zamanin baya.

Duba da kyau ki gani duka kayan wanene wanan?,shiru ya biyo baya tana mamakin yadda akayi ya samu kayakin domin dai tabbas duk wanda yasan mallam mahaifin su da wanan rawani,tasbaha,takalmi da zuben aka sanshi!,ba zata manta ba har laƙabi ake yiwa baban su da"mallam mai abun al'ajabi",sunan da ake

Please Login or Register in order to submit comment