Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

battery(acid) cikin maƙoshi a gefa a rafi ko rijiya inda har ka mutu ba zaa gano ka baa.

Idan ban manta ba akwai lokacin da yan sanda suka kama wasu ɗalibai yan wata makaranta daga aji ss2-3 kusan su ashirin da biyu lokacin suna meeting na miƙa muƙami(handing over),wasu suka ɓoye cikin ceiling nan take aka watsa masu teargers dole suka fito.

Aka tasa su gaba nan suka rinƙa faɗan abubuwan da suke aikatawa da yadda suke yip...,ashe basu kaɗai bane har yan primay na makarantar suna ciki a cewar shugabar ƙungiyar nasu!.


Lokacin da suke confensing crime na su ne wata ƙaramar yarinya yar shekaru takwas mai suna"sharon"yar primary 3 tace shekarunta uku a cikin ƙungiyar tun tana primary1 wani mutum wanda suke yiwa laƙabi da"one-eyed man", aƙalla tayi sanadin yara sama da ɗari biyu shiga wanan ƘUNGIYA tun daga kan yan primary zuwa secondary!,sanan naman mutane huɗu ta taɓa ciki a cikin ahalinta!,duk da haka har yanzu baa yaye ta baa(she was yet to graduate to eating her family meat) wanda sai ka bada mutane goma cur sanan zaka zama,an exclusive menu preserved for the(upper class) kuma har yanzu she was in the interim drinking human blood.

Wani murmashin jin daɗi tayi domin wanan yarinya sharon ta shiga zuciyarta irn jajircewa da tayi haka.
Wanan ɗan labarin da father ya tsakura mata akan sharon yasa taji ta sake samun ƙwarin guiwa ya zama dole ta zage damtse domin cikar burinta!.

Yawancin yaran dake cikin irin wanan a ƘUNGIYA zaka same su masu taurin kai sosai da rashin tsoro!,bata shakkar kowa kuma suna iya gaya wa kowa magana ba tare da tsoro ba!.

_Iyaye don Allah a rinƙa bibiyan irin rayuwar da yara keyi,irin mutanen da suke mu'amala dasu a makaranta tareda tashi tsaye da addu neman kariya da shiriya wa yara!,wallahi secret cult is real!,especially among teenagers!_

*PINK LADIES*

Ƙungiya ce ta zallar yan mata masu aji,wanda suka isa kuma suke alfahari da kasancewar su yan mata abun kwatance.ƘUNGIYAR nan basa shan jini ko cin naman mutane!,burin su samun farin jini,ɗaukaka!,nasara da ƙarjini a idanun mutane musaman manyan alhazawa da yan siyasa masu kuɗi!.Duk da suna tsafi amma da jini dabbobi bokaye,mallaman tsubbu da matsafa ke masu aiki.abubuwan da suke gabatarwa sun haɗa da maɗigo(lesbian),ana haɗa kai dasu ayi garkuwa da mutane(kidnapping),fashi da makami,damfara,yaudara,bata aure da sauran mugayen abubuwa!.Shi yasa duk wacce ke cikin wanan ƘUNGIYA ƙa'ida ce babu aure a tsarin su kuma babu yadda da namiji sai mata yar uwansu!,yadda ke gane su kuwait;suna saka zobe a babban yatsar hannu na hago,yatsan tsakiya na ƙafa da kuma chain na ƙafa,akwai tattoe mai alamar arrow a gefen wuyar su!,sun kasance yan mata ne masu dukiya da aji sosai zaka gansu da manyan motoci,gidaje har da manyan shaguna na kasuwanci gudun zargi!.


Amma father ya akayi suke samun ɗaukaka haka?,suna sacrifices mana da rituals amma bada mutane baa!,dabbobi ko kuma a basu maganin da zasu yi amfani da mata yan uwansu amma yara wanda basu san komi baa.


zamu dakata haka nan zuwa gobe zan igaba da sauran sanan in koya maki wasu hanyoyi da zaki bi wurin bawa kanki kariya akan su!.


Follow
vote
comment
share.
[7/3, 15:27] Leema: *🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
       *NA*

          *L££MA*

wattapad
*@leemaMuhammad826*

  _Sadaukarwa gare ku_👇🏻

*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*

*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*

*Asmeenart zayyan ina taya ki murnar kamalla littafin ki"BAƘIN DARE" mai cike da ɗumbin darussa da faɗakarwa ALLAH ya bada cikakkiyar ladan faɗakarwa inda aka yi kuskure ALLAH gafarta mana baki ɗaya amine.*

*🅿43-44*

*ABUJA NIGERIA*

   Muhammad zaune saman farar kujera yana riƙe da jaridar daily trust kacokan hankalin shi na kan labarin da yake karantawa na wasu yara yan makarantar sakandari su ashirib da shida da aka kama suna cikin ƘUNGIYAR ASIRI!,mata goma sha tara da maza bakwai.Koda bincike tayi nisa duka yaran manyan masu kuɗi ne wanda iyayen sun shigar da ƙara akan ƙazafi akayiwa yaran su!.

Mami ce ta faɗo mai a zuciya domin yanzu bai san a ina take rayuwa ba kuma cikin wani irin hali?,tana tunawa dasu ko ta manta dasu.Ji yayi an rufe mai idanu da hannaye wanda babu ko tantama na mace ce saboda taushin su da irin ƙamshin hand lotion na mata da yaji.

Who's this please?,tura baki tayi a shagwaɓe tare da sasauta hannayenta...,"ka cinka tau",nan take ya gano muryar ta  saboda yasan baya irin wanan wasan da yaran yayan shi kuma dai ma namiji ne babba sauran matan ƙana na ne!.

Tamke fuska yayi tare da ƙoƙarin cire hannayen nata daga fuskan shi,"MAYAH menene kuma haka?",zagayo wa tayi ta gaban shi ta kwashe waya da goran swam  water sai makulin motar shi dake saman stool na ruba ta zauna daf dashi.

Cikin ido ta kalle shi tareda yin fari dasu sanan ta lumshe kamar mai jin bacci,langwaɓe kai tayi gefe ɗaya a sakalce kamar yarinya ta furta"ba kai bane tun ɗazu nake neman ka mu ci abinci na haɗa maka favorite  naka".

Cikin ɗaga murya yace keee!, hold on don ALLAH bana son shishigi da cusa kai a inda ba'asan kana yi baa ko ni ɗin sa'an ki ne?,yaushe na saba cin abinci tare da ke!, ko yaushe na saki dafa mun abinci?,idan ke mayya ce kya ci kanki ya kwashi tarkacen shi ya nufi motar shi...

Tana zaune wurin kamar wata doluwa har ya fice a motar wanda dama gidan su zashi wurin abban su...,shiru tayi na ɗan lokaci sanan ta gyaɗa kai ta kona ciki inda ta yada zango a palo idanunta sun cika da hawaye!.

Wanan wani irin jarabawa ce ALLAH ya ɗauro mun?,wallahi da nasan haka zata faru dani da ban zo garin abuja baa!.

Ramatu matar shafi'u ce ta fito daga ɗakin baccin su sanye da kayan baccii sai zani data ɗaura saman kayan,saman three seter ta miƙe tana faɗin"wash yau nasha bacci sosai har sha ɗaya tayi!",taga hankalin mayah baya wurin ta alama ma tunani mai zurfi take yi.

Kusa da ita ta koma ta zauna tare da dafa kafaɗanta"menene kuma mayah?",hawayen da take tare wa suka zubo mata tare da kantar da kanta a jikin ƴar uwanta"is not working lovely sis!",har faɗa yamun baya so ina mai shishigi,despite so much effort and hard work i put na girka mai abinci amma ya banni dashi.

Mayah shi yasa tun farko nayi warning  naki domin muhammad  ba irin mazan nan bane da ake samu a sauƙaƙe beside ma baya cikin hayyacin shi a yanzu!,yayi rashin macen da tafi soyuwa a zuciyar shi ZAINAB,ya shiga maraicin uwa wacce a dalilin abunda ta aikata mashi ya kasa amince mata a karo na biyu!,ƴar shi wacce ya ƙallafa rai a kanta she was no where to be found mayah!,har kina tunani muhammad  zai sake buɗe wa wata ƴa mace zuciyar shi nan kusa?,wallahi da maida hankalin ki ko banza shi ba sa'an auren ki bane  ki rufa wa kanki asiri ka kama amir ɗinki wanda ke sonki tun baki san ciwon kanki ba har gashi kin kamala karatu kusan shekaru tara kenan kuna tare da ama maganar saka lokacin aure sai yanzu ki ƙirƙiri wani sabon salo wai muhammad  kike so!

Tun wuri kisan inda kanki ke maki ciwo domin bana cikin shashancin nan ,a farko na ɗauka tausayawa ce kawai saboda halin da yake ciki shi yasa kika ga har na faɗa maki duk abunda yakeso da wanda baya so.

Tana gama magana ta miƙe abunta zuwa kitchen...,kuka mayah ta cigaba dayi tare da tashi ta nufi ɗakin da aka sauke ta nan ta tsaya gaban madubi tana ƙare wa kanta kallo.

_Fara ce siriri ya sosai doguwa amma tana da manyan boobs,babyface ɗinta mai ɗauke da manyan idanu msu haske sai hanci dogo da maki madaidaici,gashin girarta har yana haɗewa saboda yawa wanan ya ƙara ƙawata  fuskarta,ga suman mai mai tsayi ya kwanta lub har gefen fuskanta kamar saje_

Ko dan bani da hips  da ɗuwawu  ne yasa baya kula ni?,fuskata babu maƙusa menene aibu na?,ya zama dole ya soni kamar yadda nake son shi domin ba zan iya rayuwa da ko wane irin namiji ba sai shi!.

_MAYAH kenan ƙanwan ramatu ta biyu haifaffiya kuma mazauna garin lagos,saboda daddyn su air vice marshal  ne suna da dukiya gwargwado irin nasu,bayan tarbiyya da ilimi da suka samu ingantance,lokaci zuwa lokaci takan kawo ziyara wurin ƴar uwarta mafi soyuwa a gareta har ALLAH yasa yanzu ta kamala karatu shine tazo mata hutu mai tsayi karaf ALLAH ya ɗaura mata son muhammad  tun ranar da tafara ganin shi a gidan ai kuwa ta shiga bin didigi har ta gano halin da yke ciki._

   Tunda ya bar gidan ya ke tunanin irin wanan rayuwa wai ace yan mata yanzu ba kunya ƙiri ƙiri suke nuna maitar su a fili!,shi idan ma soyayya zai yi ko wata sharholiya mai zai yi da mayah wacce take kamar one babu shape mace kamar namiji,ga yan mata nan masu kyau da tsari a garin abuja suna neman a kula su da kuɗin su ma bai aminta bare ita yarinya ƙarama ma har tasan seducing  namiji.

Har ya isa gidan tunanin duniya ya cika mai zuciya...,wurin adana motaci ya aje nashi sai ya fara shiga sashin hajia mariya suka gaisa,ya shiga sashin sauran matan abban su kamar yadda ya saba idan ya shigo gidan sanan ya wuce sashin abban su.

Bayan sun gaisa ne ya dube shi sosai sanan a sanyayye abban nasu yace,muhammad  ina horon ka da zama mai hakuri da manta duk abunda ya faru mu tunkari gaba,Allah ya riga ya ƙadara sai hakan ta faru bai kamata ka riƙe wanan a zuciyar ka ba shaiɗan na ingiza ka har kana ƙaurace wa mahaifiyar ka a lokacin data fi buƙatar ka baa.

Abba wani abun akace nayi?,ko ɗaya,"Bismillah mu ci abinci nasan baka karya ba",wanko hannu yayi tare da bismillah suka cigaba da ci a hankali shiru ya biyo baya har suka kamala.Ya dube shi da kyau"yaushe hajiyar ku tace zata dawo ne?".

Kame kame ya shiga yi saboda har ya manta rabon da ya neme ta a waya ba domin wani lokacin ya kan kalli kanshi a matsayin maraya wanda ya rasa kowa nashi a duniya sai uba ya rage mai.Yayi tawakkali sosai duba da abunda ya faru dashi lokaci ɗaya.

Ina neman alfarma daka kira mahaifiyar ka a yanzu!,bai so haka ba amma daure wa yayi kawai ya lalabo lambarta...,bugu ɗaya ta ɗaga da sauri da sallama,"barka dai hajia ya kuka tashi",lafiya lau moha ya kuke duka?,lafiya ya amsa a takaice sanan shiru ya biyo baya,"mana in tambaya yaushe zaki dawo ne?",wani irin daɗi ya ziyarci zuciyarta sosai ɗanta ya yafe mata!,muryarta na rawa tace ko tau kace in dawo moha zan kamo hanya idan har hakan zai sanyayya zuciyarka kuma yasa ka yafe mun.

Hajia dama ni ban ƙullace ki ba,zuciyata ce ke ingiza ni ina aikata abunda bai kamata ba amma ki yafe mun tare da taya ni addu'a Allah ya bani ikon maki biyyaya ya share mun hawaye na.

kullum cikin maka addua nake moha kuma ban riƙe ka ba inaƙara neman yafiyarka...,ya wuce hajia ki shirya a natse idan Allah Ya kai mu ƙarshen sati zan shigo in kwana sai mu dawo tare domin naji kewar kunun gyaɗan nan mai daɗi da kike mun.

Daɗi ya cika mata zuciya ai kuwa dashi zan tarbe ka domin nan sokoto muna da gyaɗa mai kyau da ɗanyen shinkafa,nan a hira irin na ɗa da mahaifi ya ɓarke.



Zainab yanzu hankalinta ya fara dawo wa jikinta domin ranar sunday ya kamata ta koma abuja monday zasu fara leactures,babban matsalarta wurin zama!,inda zata sauka saboda abuja ko hotel zaka kama ba ƙaramin aiki bane bare gidan haya,ga ragistration zata yi kusan dubu hamsin da yan kai wanda take tunani ta inda kuɗin zai fito,idan ba wayarta ko gidan muhammad zata tafi kwasan kayanta tana da yan kunne da zobe na zinari ta sayar dasu baa.

Babban tashin hankalinta yadda tunanin muha ke awan adabarta idan dare yayi,bata iya bacci wani irin sha'awar mijinta ke addabarta,abunka da lafiyayyar mace jini ya ɗauke matad,tana ci ta ƙoshi sai muradin kasancewa da namiji.Wanan lalurar ya matsa mata.

Maman su na lura da yanayinta kuma hakan ya mata daɗi sosaiduk da babu mai adduar nashi ya koma haka.
Da dare ta samu babansu da maganar komawart makaranta.Ya mata nasiha mai ratsa jiki sanan ya ɗauko dubu goma yace ta ƙara.

Mamansu dai tace komi bazata bata ba tunda da gangan ta kashe auren,yanzu ne zta gane miji ma ni'ima ne kuma wani garkuwa na musamman ga mace.



~Kuyi hakuri da wanan ban ban samu zama bane~

FOLLOW
VOTE
COMMENT
SHARE
[7/4, 13:58] LEEMA: *🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
*NA*

*L££MA*

wattapad
*@leemaMuhammad826*

_Sadaukarwa gare ku_👇🏻

*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*

*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*


*SAWDA IDREES ina taya ki murnar kamala littafin ki mai suna"BAƘAR KADDARA",Allah bada ladan faɗakarwa amine*


*MARYA MUHAMMAD HASSAN ina taya ki murnan fara sabon littafi mai suna"BANDA GATA",Allah yasa an fara a sa'a amine*




*🅿45-46*



Ita yanzu babban damuwart auren safiyya da ya matsu daf gashi komi bata shirya ba kuma tun tana gidan muhammad suka yanke shawarar akan itace zata yi set na gado tunda babu abunda mijinta ya raga tadashi ta fanin kulawa,lokaci na tafiya kusan duk kuɗin dake account ɗinta sun kusa ƙarewa saboda lalurar yau da kullum gashi makaranta zata koma.

Mafita ɗaya take dashi ta kwaso kayanta a gidan muhammad domin a sayar da wanda zai sayu da kuɗi sauran ta ajiye wa maman su,amma ta yaya zata fara neman shi tunda ta goge lambar shi da duk wani shaƙiƙin shi!,wata zuciya tace ba sai kin neme shi ba ai kayan ki ne kawai ki kwaso.Da wanan shawara ta samu bacci ya kwashe taa.

Washe garin saturday tun da wuri muhammad ya shirya ya nufi gidan shafi'u domin masu sallama zai wuce sokoto...,koda ya isa mayah ce ke mopping ta gama shara.Bai wani damu ba ya shige ciki da takalman shi masu ƙasa tana gaishe shi ko kallo bata ishe shi ba bare ya amsa.

Sosai ya mata ƙwarjini yana cikin jamfa wacce ta amshi jikin shi yayi kyau matuƙa.Aje mopper tayi ta nufi kitchen don ta haɗa mai coffe tunda da sauran doya data soya wa yara suka ci kafin su wuce islamiyya...,haɗawa tayi ta aje mai gaban shi saman ƙaramin tebur,har ta juya yace"ke zo ki ɗauki abun nan",ɗan jimmm tayi sanan ta ɗauka idanun ta sun ciko da ƙwala wanda tana isa kitchen kuka ya kwace mata sosai.

Shafi'u da ramatu ne suka sauko da alama suna ɗakin baccin su ne,gaisa wa suka sanan ta basu wuri domin su tattauna a tsakanin su.Har ka fito kenan?,Allah tsare hanya ya kai ka lafiya.

Amin yaya dama na shigo in maku sallama ne,zan kama hanya kada nata tayi wuri ba kusa ba ga hanya ba kyau.Haka ne ka gaishe su sosai sai mun yi magana.

Shafi'u ya kwala wa matar shi kira ta fito suyi sallama..,tare da mayah suka fito har wurin mota suka raka shi yana ɗaga masu hannu ya tafi.



*AKURE*


Watan mami ɗaya cur a garin inda take samun horo na musamman a ɓangarorin biyu kuma ta na fahimta sosai saboda cikar burinta ya fiye mata komi yanzu a duniya.

Yau itace rana ta farko da zaa mata jarabawa,shugaban ƘUNGIYA yace abunda ke cikin wata mata suke son kanshi da ƙafa fu a ranar da yazo duniya don haka itace zata yi wanan aiki ba tare da taimakon kowa ba.Bayan an gabatar mata da wanan bayani suka ce yanzu shawara ya rage nata ta gano hayar da zata ɗauko masu abunda ke cikin matar ba tare da taimakon su baa saboda cikin ya isa haihuwa yanzu haka ko wane lokaci tana iya haihuwa.

Nan taro ya watse ta shiga zullumin yadda zata fara wanan aiki wanda bata taɓa aikata wa baa,ai kuwa tana
cikin horon da ta samu a wurin father paul dama akwai littafin siddabaru daya bata idan tana amfani dashi tana iya canza kammanu zuwa dabbba ko wani halitta na dabam.Sosai ta duba sanan tayi murmushi domin ta gano mafita..,dare nayi ta hau saman tsaunin da suke haɗuwa tare da shimfiɗa farar ƙyalle ta ɗauko kurciya da ranshi ta murɗe wuyan shi sai da jinin ya gama tarara a saman ƙyalen sanan ta fige shi,gashin yabi iska naman kuma haka ɗanye ta cinye shi banda kai da ƙafafu wanda ta ɗaura saman ƙyale ta shiga karantu wasu kalmomi marasa ma'ana idanunta a rufe,taba maimaitawa na tsawon lokacin kafi ɓat ƙyalen ya ɓace kamar walƙiya!,wani irin farin ciki ya ziyarceta domin buƙatar ta ya amsu.


Hankalinta kwance ta koma bukar su suka cigaba da sauran darrusan da baa gama baa...

Ai kuwa naƙuda ya taso wa matar nan mai suna"Bishola",suka nufi asibiti bayan wahala data sha sosai a ƙarshe ma aiki aka mata aka ciro yaro wani irin hallita fuskar nan baƙin ƙirin sak kurciya,jiki fari irin na jarirai amma daga kai zuwa ƙafa na dabobi ne!,Ba ƴan uwan mai haihuwa ba har likitotin da suka taru a kanta sun tsorotada ganin wanan abun al'ajabi!,akayi ju

Mijinta yace kawai su yafe shi baya son wanan ba zai taɓa zuwa dashi gida ba a matsayin abunda suka haifa ba duk da shekarun su sha biyar da aure babu haihuwa!,abun mamaki har zuwa ganin ɗan akeyi gashi mai jego bata farfaɗo baa.

Lokacin data dawo cikin hayyacin ta kuka taci saboda ta ƙallafa rai akanabunda zasu haifa sai gashi yadda ta kasance dasu,tace ta ɗauki kaddara zata raini abunda haka nan babu mai raba ta da shi.

Mijin yace ba dai gidan shi ba sai dai ta koma gidan iyayenta...,nan aka yita hayaniya daga ƙarshe ya tafi ya barta a asibiti.

Saboda wanan hasaniy suka nemi alfarma a sallame su daga asibiti suka koma gidan iyayenta.A daren ranar bacci ya ɗaurace wa idon su domin jaririn nan wani irin abu yake mai ban tsoro da rikitarwa wanda ya tashi hankalin kaf kowa a gidan!,yadda suka ga rana haka suka ga dare koda suka tashi da safe jikin shi yayi zafi sosai sai kuka.

maman ta mai suna"iya méjí" tace ya kamata su kai yaron nan wurin baba lawu wani babban harbalist a duka masu idan ba mutun bane kawai su jefa shi a ruwa kowa ya huta!.

Bishola ta fara kuka domin tana son yaronta haka nan,tace ita asibiti zata kai shi a duba shi.Bata tsaya jiran shawarar kowa ba ta nemi abun hawa ta nufi asibiti...,tana sauka bakin gate taga wata tsohuwa zaune kamar almajiri a duƙa har ƙasa ta gaishe taa,sai cewa tayi"ina zaki da tsohon nan dake goye a bayan ki?",murmushi bishola tayi sanan tace ba tsoho bane yaro na ne dana haifa jiya fa.

Wanan ne yaron ki?,tace eh!,tsohuwar tace tau shike nan tafi kawai.

ai kuwa tana shiga cikin asibiti yaro ya ƙara mata nauyi a baya gashi akwai layi sosai haka take ta wahala da ƙyar ta samu ganin likita koda ya duba yaro ya mutu!.

Kuka ta shiga yi d birgima tana faɗin shike nan tsohuwar nan ta kashe mata yaro...,a guje ta fita domin ta same ta amma abun mamaki babu ita ba dalilin taa.
Ba kowa bace wanan tsohuwa sai MAMI!

A daren ranar koda shugaban ƘUNGIYA ya duba tukunyar tsafin su kan jariri da ƙafafu na ciki!,taro na gaggawa ya kira domin murnar samun nasarar mami a karo na farko.

Sun gabatar da sacrifice ɗin nan aka naɗa mami sarauniyar flyers saboda nasarar data samu a karo na farko.



Ranar asabar da tunda safe zainab ta shirya tsaf tare da yin sallama da iyayenta takama hanya zuwa abuja.....

Tana cikin mota sai tunani take yadda zata fara tunkarar gidan muhammad da sunan kwasan kayanta har na sawa da takaddu suna can gidan.

A ɓangaren muhammad kuwa lafiya lau ya isa garin sokoto amma da yamma liƙis,aka tarbe shi da abinci mai kyau har kunun gyaɗan da suka yi magana da hajia tayi mai,zama yayi sunata hira ana sha har aka kira sallah ya tafi masallaci da kawun shi.



Zainab bata isa da wuri ba saboda motar data shiga ya samu matsala a hanya sunata yawan tsayawa.Lokacin da ta fito kowa ya gama fita ne ta fara tunanin inda zata nufa...,yusra ta faɗo mata a rai nan take ta kirata amma akayi rashin sa'a basa gari sun tafi week end garin mijinta.
Kawai ta yanke shawarar zuwa gidan muhammad ta kwashi kayan da zata buƙata na karatu da sawa sai ta kama ko ƙaramin ɗaki ne a hotel ta kwana har da safe idan ta shiga gari taga abunda zata yi..

Abun hawa ta samu ya kai ta har anguwan sanan ta sallame shi ta shiga buga gidan...,mai gadi yazo ya buɗe mata suka gaisa cikin girmamawa da tambayar bayan rabo,saboda ya samu labarin abunda ya faru duba da maganan duniya dai baya ɓoyuwa kuma yayi mamakin zuwanta tunda auren ya mutu.

Tace mai gidan na ciki kuwa?,ayah hajia kinyi rashin sa'a kuwa domin jiya yayi tafiya inaga sai gobe zai dawo!

Kuma bai bar makullan gida ba ko?,eh gaskiya babu a wuri na sai zaki bincika gidan alhaji shafi'u saboda can yake yawan cin al'amuran shi.

Shike nan nagode barin tafi har goben..,addu'arta ɗaya ALLAH yasa akwai makuli a gidan ta amsa da sunan kwashe kayanta sai ta kwana a ciki tunda bayanan zuwa da safe ta haɗa komi nata sanan ta wuce.


Tayi tafiya mai nisa a ƙasa kafun ta samu abun hawa...,koda ta isa gidan lafiya lau suka gaisa da mai gadi saboda yasanta sanan ta wuce ciki.Sallama tayi a lokacin ramatu da mayah sai yara suna zaune palo ana kallo shafi'u ya fita.

Fuskan ramatu ɗauke da mamakin ganin zainab a gidan nasu da daren nan har take tunani ko sun shirya ne ta dawo...,wuri ta samu ta zauna suka gaisa har mayah da bata santa ba sanan ta miƙe ta kawo mata lemu da ruwa.

Zainab daga ina haka da dare?,wallahi daga gida mota ya lalace mana a hanya ban iso da wuri baa,kin san monday zamu koma makaranta kuma kayan karatu na suna cikin gidan muhammad ashe baya gari ma!

Sai lokacin mayah ta kalle ta da kyau,watau itace zainab tsohuwar matar muhammad kenan?,lallai ma wata sabuwa nan take kishi ya turmuƙe taa.

Allah sarki,baku yi waya ba kenan amma ya tafi sokoto yau inaga sai gobe zai dawo tare da hajia...

Kuma bai bar makullin gida a nan baa?,"ta katse ta",gaskiya ban sani ba ko wurin daddyn su gashi bai dawo ba,yanzu dai nasan a gajiye kike bari mayah ta raka ki ɗakinta kiyi wanka da sallah a kawo maki abinci kici kafin ya dawo.

Taso tace a'a domin ba zama ya kawo ta ba amma dai tana buƙatar hakan.

Sai lokacin ta kalli mayah da kyau,amma wanan sister kice naga kuna kama sossai?,murmushi ramatu tayi,eh mayah ce autar mu hutu tazo sun kamala karatu.

Allah sarki,Allah ya taimaka!,mayah ɗauki jakarta ku shiga daga ciki.Cike da ɓacin rai ta ɗauka tana yatsine yatsine domin zainab ta fita diri nesa ba kusa baa da kyau.

Ganin mayah ta tsare ta da idanu yasa ta shiga cire hijab kawai ta toilet ɗin da kayan jikinta nan ta cire sanan tayi wanka tare da ɗauro alwala dama ta mayar da kayan jikinta wanda ya amshe ta sosai haka ya ƙara bawa mayah haushi.

Gidan ba baƙon zainab bane shi yasa ta kabarta sallah abunta...,har ta idar maya na zaune tana kallon ta sanan zainab ta katse shirun ta hanyar gaishe ta suka nufi palo ramatu na lurada yanayin mayah tun zuwan zainab sai abun ya bata dariya ma.


Har zainab ta gama cin abinci suka ɗan taɓa hira da ramatu shafi'u bai shigo gidan baa.Dama da suka shiga ciki ramatu ta kira shi a waya ta tsegunta mai aikuwa yace mai dawowa da wuri sai ta kwana a gidan nan.

Goma ta gota shiru ramatu tace ai da kin kwanta abunki zuwa gobe sai ki amshi makullin idan akwai sai a kai ki hankali kwance ta kwashi abunda kike so.


Dole suka yi sai da safe ta nufi ɗakin mayah ta canza zuwa doguwar riga mara nauyi na bacci ta kwanta kefe ɗaya.
Mayah a kalli ramatu,lovely sis amma dai matar nan ƴar rainin hankali ce!,

Please Login or Register in order to submit comment