Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kiran gidan su kenan domin duk mallaman dake garin ya banbanta dasu ta shigan shi,mu'amala da jama'a da kuma biyan buƙata nan take.


Ki buɗe baki kiyi magana domin koda mahaifin ki ya rasu aƙalla kina da shekaru ashirin da biyar a duniya bare kice baki da wayau na sanin shi.

Jiki a sanyaye ta furta,"eh duka kayan mallam ne",murmushi ya sake yi tare da ɗago babban hoton nan mai kama da cardburn paper na black and white ya miƙa mata,"duba ki gane idan akwai mallam a ciki sai kiyi magana".


Ai kuwa shine sanye da jan riga mai ratsin baƙi da rawanin nan a kanshi yana murmushi, zaune saman kujerar ƙarfe na azurfa,gefe kuwa ƙarama cephalopods(shugabar ƙungiyar su na KKK KU KLUX KLAN).,sai sauran mutane na wanan
*ƘUNGIYAR ASIRI* suna taya shi murmar sarauta da aka bashi a matsayin mataimakin shugaban
*ƘUNGIYAR SU* ,yanzu kin yadda ko kina neman wasu hujjuji masu ƙarfi?

Kuka ta shiga rairawa mai cin zuciya...,domin har mallam ya rasu basu taɓa sanin ɗan
*ƘUNGIYAR ASIRI* bane,bata san ko maman su ta sani ba ta ɓoye masu!,cikin zafin nama ta rinƙa kece hoton tana watsarwa tana faɗin,baba ka cuce mu ka bar mana gadon mugun abu Allah ya isa tsakani na da kai,sai an mana hisabi ba zan taɓa yafe mka haƙƙi naba,ka zama sanadin gurɓata mun zuria da mugun iri...

A gadarance hajiya mariya tace,don Allah rufe mana baki saraka shashasha kawai!,ai baki ji komi ba ma tukun sai an faɗa maki dalilin da yasa mallam ya laƙaba wa mijina auren ki lokacin zaki ƙara tsanar iyayenki da tushe domin duk shine ya janyo muka kasance cikin
*ƘUNGIYAR ASIRI* ,dama ƙyale ki kawai nake da kike ci mun mutunci kina ganin kamar ni ce sillar shigar ki wanan musiba!,baki san ni ceton ki kawai nayi ta hanyar ƙara maki ƙarfi da baki kariya baa.
Amma da kika zama mutum baki da wata maƙiyi ya data wuce hajia mariya!.

Cikin yaran hajia lanti muhammad yafi kowa shiga baƙin ciki saboda yasa ya zama dole ya rabu da zainab kawai tunda zargin ta ya tabbata duk iyayen nashi yan*ƘUNGIYAR ASIRI NE*

Sai jan majina yake yan kuka,sauran yan uwanshi ma dai suna cikin tashin hankali amma ba kamar nashi baa.

Zainab dai ambato Allah take yi cikin zuciyarta wanda ke daf da tarwatsewa saboda tsabar tsoro,mamak,fargaba da kuma shiga ruɗani!,ta matso a gama bada wanan labari nasu mai kama da al'mara a bata takardan sakinta!,idan so samu ne ma a bata saki uku zai fiye mata tunda babu wani zuri'a a tsakanin su.
Mami ce,kum ba jininta bace!.


Sai da aka sha kuka da habaice habaice tsakanin matan gidan da yaran, sanan suka natsu don kan su,ya cigaba;


Sai da muka dawo gida da hajia ta zaunar dani domin yi mun nasiha kamar yadda ta saba ko yaushe;

Barau a kullum cikin gode wa Allah nake da ya sa zan zamo uwa a gare ka duk da ba nice na haife ka baa,amma a kullum burina zamo wa uwa ta gari duba da Allah bai bani haihuwar nan ba amma ina matuƙar son yara.SAI dai laifin mijina ne wanda ya mun butulci ya yaudare ni ta hanyar miƙawa ƘARAMA mahaifata amatsayin fansan ranshi!

Cike da tsoro na kalle ta sosai!,ƙwarai nasan zaka yi mamaki idan kaji wanan labari kuma ba wai zan faɗa maka mane don tuna sirrin mijina,sai don ya zama dole kai ma ka sani tunda a ynzu ka zamo ɗaya daga cikin yan wanan
*ƘUNGIYAR ASIRI*

MALLAM nasir da kake gani aminin alhaji ne tun yaranta har samartaka hr tsofa ta kama!,muna zaman mu lafiya da mijina cikin rufin asiri duk da bamu da komi lokacin saukale yake yi(sauke buhuhuwan kaya a babban idan an kawo daga wani gari),ya nuna mashi akwai hanya mai sauƙi da zai bi yayi kuɗi cikin sauri kuma ba mai zargin shi,sanan kuma akwai hanya da zaa bi wurin bashi kariya na musamman daga sharrin mutum,aljan da duk wani mugu a doron ƙatsa idan ya aminta.


Da yake duka basu yi karatun boko ba a lokacin sai na allo kuma yaga mallam nasir nada zurfin ilimin addini ba zai saka shi ya kauce hanya baa,ya aminta suka shirya tare da haɗa komi a ɓoye bada sani na ba yayi duk yadda zai yi har alhaji ya samu shiga cikin
*ƘUNGIYAR ASIRI* ,ba tare da zub da jini ko kashe kuɗi masu ywa baa!,kawai farin ƙyale suka samo aka saka cikin babban akwatin ƙarfe,ko wane kusurwa suka zuba farin kuɗi guda uku uku sai tsakiya uku(a kusurwa huɗu),aka fesa turarai ɗan duwala wai aka tambaye shi wani irin kuɗi yake so?,a farko da bai ɗauka gaskiya bane sai yace sulala!,"mallam nasir yace haɗe da dala na amurka,akace ya rufe akwatin ya tagidashi ya ɓoye sai bayan kwana biyu cikin dare zai buɗe tare da yin kirari kamar yadda aka koya mai....,Ai kuwa yayi yadda aka ce sai ga kuɗi cike da akwati kamar yadda ya faɗa yana su har dalar amurka.! tun daga lokacin ya fara harkokin shi babu wanda ya isa ya tambayi yadda akayi ya samu kuɗi dare ɗaya saboda kariya da suka bashi.

SAI bayan arziki ya bunƙasa kowa yasan ya zama mai kuɗi sai ƘUNGIYA ta buƙaci da a bata mahaifata ya zama fansa akan ranshi da dukiyar shi yadda zai rinƙa bunƙasa koda baya wani kasuwanci.

Bai wani damu ba ya sadaukar da mahaifata ga
*ƘUNGIYAR ASIRI*
ba tare da sani na ba,dukiya nata haɓaka dai har aka share shekaru da auren mu ko ɓatan wata ban taɓa yiba!,tunda a lokacin ma mace na iya shekaru gom a gidan miji ba tare da ta fara haihuwa ba saboda auren sauri ake mana musamman a ƙasar hausa,gashi babu wasu asibitoci manya sai ɗakin shan magani.

Shiru shiru ba haihuwa muna zaman mu lafiya cikin wadata,daga yan uwanshi har nawa suna samun alheri sosai a wurin shi har Allah ya haɗa mu da ku kenan muna zaune lafiya,ƘUNGIYA ta buƙaci a bata jinin namiji nagartace!,lokacin alhaji ya shiga damuwa domin bai taɓa bada kowa ba ya rasa inda zai samo wanda zai bayar.

Sai mallam nasir mahaifin hajia lanti ya bashi shawaara ya bada baffa na tunda ba ɗan gari ne babu mai zargin shi. Suka shirya kuwa ƘARAMA zata turo mutanen su yang
*ƘUNGIYAR ASIRI* a zuwan ɓarayi su kashe baffa nab,nan take ta tafi da kurwan shi(ruhi),sai a binne janjan jiki kawai.

Haka kuwa akayi har suka kora shanayi gudun kada ayi zargin wani abu kuma dalilin da yasa baa gano su ba kenan saboda ba mutane bane.

Bayan shekaru biyar da mutuwar baffan ka,ƘUNGIYA ta sake neman alhaji ya bada mace!.,nan ya shiga damuwa kuma har ya nuna shi arzikin ya ishe shi haka nan ba sai am ƙara mai baa. Suka ce wanan hine ƙa'idan su idan ba haka ba zai tsiyace,kuma sai asirin shi ya tono kaf a duniya kafin yayi mutuwar wulaƙanci!. Nan ma mallam nasir ya bada shawara kawai ya bada innata tunda yana da ƙarfi da kariya da zai iya turawa a ɗauko ruhin koma wanene a duk inda yake a duniya zai tura aljanai.

Ba tareda wata damuwa ba ya tura ƘARAMA da kanta ta ɗauko kurwarta wanda yana kan hanya ne ta kwanta ciwo na kwana biyu amma yana isowa aka rufe a masaki ta mutu!

Rayuwa na cigaba da tafiya arziki yafi na baya zuwa wasu shekaru aka sake neman maceda namiji a takaice dai iyayen alhaji wanda suke rai na ƙarshe da zai bayar!,daga su arzikin shi zai dawama har ƙarshen rayuwar shi babu wani jini da zai sake zubar wa.
Nan fa ɗaya yace ba zai taɓa bada iyayen shi ba duk abunda zai faru sai dai ya faru!,suka ce sun bashi watanni uku idan har wa'adin ya cika bai yi yadda suke soba a bakin rayuwar shi.

Tunda ya bar wurin taron suka rabu baram baram da mallam nasir bai sake waiwayen su ba har ya kwanta ciwo kuma a lokacin ne ya bani wanan labari kafin mutuwar shi.

Barau dalilin da yasa na kai ka wurin mallam nasir bayan na san duk makircin da ya ƙulla muna domjn ɗaukar fansa!,shine sanadin shigar mijina mugun hanya wanda yayi sanadin mutuwar iyayen ka da kuma mijina!,na baka wanan labari ne domin ka shirya yadda zaka ɗauki fansan ran iyayenka akan mallam nasir da iyalen shi.

Bahaushe yace"mugu shi yasan makwancin mugu",dole sai mun san sirrin shi,abunda yake taƙama dashi kafin mu gano hanyar wulaƙanta shi!,kayi mun alƙawari ko bayan rayuwata zaka cika mun wanan buri nawa?


Cikin kuka na amsa mata domin zuciyata tana zugi,nayi dana sanin zuwan mu ƙasar nigeria karo na farko da nayi nadamar sanin alhaji mu'azu!.

Mun daɗe sosai cikin daren nan muna tataunawa wanda da safe zan wuce lagos ta jirgin ƙasa kafin muka yi sallama ta kwanta bacci ashe iya kar numfashin kenan!,koda muka tashi da asuba hajia aisha rai yayi halin sa.

Sai dana ɓata lokaci aka kaita gidanta na gaskiya sanan na ƙara komawa gidan mallam nasir muka yi sallama cike da tsanar shi na tafi....


Hajia lanti kinga kenan mahaifin ki shine sanadin mutuwar iyayena domin cikin wani buri nasu na daban!



Muna isa legos aka tura ni taro na musamman da manyan jami'an tsaro,masu ruwa da tsaki cikin kwamnati sai manyan shuganin jami'oin nigeria a nan cikin lagos watau(EASTERN CONFERENCE),wanda ya haɗa dab;
*university of nigeria(NSUKKA),university of calabar,university of port harcourt,Nnambi azikiwe university(awka),imo state university,owerri university da sauran su*
An fara da bayanin menene *ƘUNGIYAR ASIRI YAKE NUFI?*
Yana nufin taron mutane masu manufofi,ra'ayi da buri ɗaya,masu ɓoye gaskiya,ƙin adalci,damfara,kissa ta wanyar bindiga,yanke wani sassa na jikin ɗan adam,sha ko zubar da jini,faɗa da mutan akan rashin gaskiya su kasance ƙarƙarshin inuwa ɗaya da niyyar ɓoye wani mugun abunda suke aikatawa wala ALLAH abun kunya,abuN Allah wadai na tuzarci ga al'umma wanda basa burin ya bayyana a idanun duniya.
Babban misali su ne"pyrates and Buccaneers"shahararre ƘUNGIYAR ASIRI na yan EUROPEAN wanda sun bunƙasa wurin zama abnun tsoro da hatsari ga al'umma saboda hatsabibancin su.
Abubuwan da yan ƘUNGIYAR ASSIRI ke iya aikatawa sun haɗa da;
Zub da jini da shan jini(shedding and sucking blood)
sata(Armed robbery)
fyade(raped)
kisa(murder)
satar amsa(examination malpractice )
Saka wuta da gangan a gidajen mutane(arson)
Yiwa al'umma ɓarna(vandalisation of property )
Haure gidan mutane suyi satan(Burglary of stealing )
Yiwa wanda suka kama rauni mai munich(maiming of victims)
suna shaye shayen miyagon ƙwayoyi irin suasion(indian hemp,cocaine,heroin and hard alcohol)
tsafi(black magic)
nemawa kai kariya(self defence and security),samun ɗaukaka da suna sosai a duniya(self recognisation).
_Abunda yasa na zayyano wanan bayani a gagauce domin masu karatu su fahimci abunda ake nufi da ƘUNGIYAR ASIRI da kuma manyan dalilan da yasa mutane ke shiga ƘUNGIYAR ASIRI domin wani yana cikin ƘUNGIYAR ASIRI fiye da shekaru ashirin amma bai taɓa shan jini ko zub da jini ba saboda ya danganta da dalilin ka na shiga ƘUNGIYAR shi suke dubawa bayan buƙatar ka ya biya su amshi fansar wanan buƙata naka!,babban misali MAYU"mutum zai iya kai shekaru goma yana maia,yana cin naman mutane ɗanye wasu har yaran cikin su idan lokacin zubin adashe yayi(domin adashin maita da naman mutane ake zubawa)amma sai ka gan shi tsiya tsiya ba cin yau bare na gobe!,babu sutura ko muhalin kirki.Haka wasu yan ƘUNGIYAR ASIRI burin su dai su samu ɗaukaka akan sana'an su,aiki ko duniya ta san su ya zama ana ambatan sunayen su duk inda suka nufa(misali yan film,ma waƙa da sauran su!,wasu kawai dai su samu kariya ne misali (yan siyasa)saboda duk wanda ya nufe su da sharri a koma kan shi,wasu kuma yan fashi da makami near,ɓarayi da mugaye sun shiga ƘUNGIYAR NE kawai don neman sa'a_
Wanan dalili yasa a lokacin yawan ci yan ƘUNGIYAR ASIRI ƊALIBAI NE,sun haɗa ƘUNGIYAR NE.
Amma kuma menene dalilin su nashiga wanan
*ƘUNGIYAR ASIRI?*
Saboda siyasa irin na makaranta(S U G),Samon abun duniya,canjin rayuwa,cin jarabawa,yin suna a makaranta da sauran su.
Wani zai fito takara a makaranta sai yaga idan yaa cikin ƘUNGIYAR ASIRI zai iya samun farin jinin lashe zaɓen a sauƙaƙe!,wani kuma talaka ne liƙis da ƙyar aka haɗa mai ya shig jami'a sai yaga wasu daga cikin ɗalibai na hawa motoci na alfarma,sutura da wasu abubuwa!,nan zaa ja raayin shi ya shiga domin samun irin abubuwan more rayuwa(domin yawancin ƘUNGIYAR ASIRI na jami'a na da haɗin kai sosai wurin taimakawa junan su morally and finacially.(kun ga kenan basa shan jinin kowa sai zub da jini,satan,fyaɗe da sauran rashin ji ta hanyar amfani da bindigogi,wuƙa,gatari da suran su).Domin sai sun yi alƙawarin jini(blood oath) inda zaka yi signing registration foarm da jinin ka cewa ka yadda kuma raayin ka ne shiga ƙungiyar,zaka basu goyon baya kuma zaka rinƙe sirrin su sanan a tsaga babban yatsar ka da raza sabuwa jinin nan zaka dangwala a paper saboda ana ɓoye wanan paper ne koda ka fita ko yi masu taurin kai zaa iya using nashi against you if u decide to reveal what has been done.
Babban makamin yan ƘUNGIYAR ASIRI shine TSORON ABUNDA BAKA SANI BA"fear of unknown"misali ga sabbin shiga zaa tambaye ka "wa ya kawo ka ƙungiyar nan?" Naturally,an initiate responds that its Mr X ,Sai ace Mx X fito domin baa ambatar suna kai tsaye,yana fitowa cikin ɗaga murya zai furt"yaushe na kawo ka?" nan zaimaka dukan tsiya a banza kunga the lesson is very clear,dont answer Questions carelessly!,wanan zai saka ka samu taurin zuciyar da ba wanda ya isa ya saka amsa tambaya akan wanan ƘUNGIYA koda an kama ka cuz all this will determine your"ruggedity".


Nan aka gano yawancin bindigogin da ɗalibai yan
*ƘUNGIYAR ASIRI* ke amfani dasu ana ƙera su ne a wani ƙauye nan cikin garin,kuma idan yaran sun yi kisan suna amfani da jinin wanda suka kashe su rubuta ƙudirinsu a inda akayi kissan.
NAN take nayi tambaya,"ta wani hanya yaran ke samun kuɗaɗen siyan bindigogi?",amsa dai ta hanyar fashi da sata da suke yi nan suke tara kuɗi msu yawa na sayan makami.


An tattauna abubuwa da dama daga ƙarshe ana ɗaura ni matsayin shugaban wanda zai kula da operation ɗin da zamu fara gudanar cikin jami'an legos domin tsafke mssu ruwa da tsaki akan wanan harka nab
*ƘUNGIYAR ASIRI*

A wurin wanan aiki ne ALLAH ya haɗa ni da matata ta farko hajia mariya wace na aure ta tallafa mun wurin cikar burina akan mallam nasir baban hajia lanti.



Follow
vote
Comment
share
[7/1, 15:42] Leema: *🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
       *NA*

          *L££MA*

wattapad
*@leemaMuhammad826*

  _Sadaukarwa gare ku_👇🏻

*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*

*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*


*🅿29-30*

    Tunda aka kawo amina(hajia lanti)gida na babu ranar da bata tayar mana da hankali,saboda ba sona take yi ba nima ban damu da ita baa. Saboda farin cikin hajia mariya kawai nake sauke haƙoƙƙinta da ALLAH ya ɗaura mun amma ba cikin daɗin zuciya baa.

Mallam nasir kuwa ya kwanta rashin lafiya mai tsanani wanda idan ka ganshi duk rashin imanin ka sai ka tausaya mai!,domin ƘARAMA ta sha kawo mana hari domin ɗaukar fansa musamman akan lanti amma bata samu sa'a baa. Ta zo wa mallam da umurni na ƙarshe wanda idan yayi yadda take so zasu rabu lafiya ba zata sake shiga tsabgar shi baa!

Idan lanti ta samu ciki yayi yadda zaa yi ta dawo gidan shi ta haihu suna son abunda zaa haifa!,babban burinta a yanzu tasha jinin jariri sabo dal kuma wanda ya fito daga tsattso na,shine zai ƙara mata ƙarfi na musamman yadda zata ɗauki fansa a kai na.

Mallam kuwa ya amince domin tun kafin ya haɗa auren ta bashi wanan shawara sai ya fake da haɗa ƙarya suna farautar rayuwar lanti ne.Basu san wata aƙalla na auratayya bai taɓa shiga tsakani na da lanti ba duk kuwa ƙoƙarin mariya akan hakan ya faru domin har ga ALLAH tausayin lanti take ji halin da mallam ya saka su rana tsaka.

Wattani uku da auren mu ciwon mallam nata gaba baya iya gane kowa,kullum a kwance yake sai an taimaka mashi ranar mun je duba jikin shi wanda akayita mashi bayanin mune amma bai gane baa!,har sai da zamu tafi sanan ya fara neman gafara wai in riƙe mai amina da abunda ke cikinta amana shi tashi tazo ƙarshe yana so duk runtsi in rufa mai asiri ko bayan ranshi kada in bari a cutar da amina.

Daga ni sai hajia mariya muka fahimci inda maganar shi ta dosa!,ita aminan kuka kawai take yi har yana faɗin idan har namiji ta haifa a saka sunanshi ko baya raye zai matuƙar farin ciki da haka....,mun dawo gida tana ta kuka dama kuma ranar a ɗakinta nake,tausayinta yasa ranar na nemi haƙƙina kuma bata hana ba ALLAH ya sanya wa wanan dare albarka aka samu cikin shafiu!

Saboda tun daga ranar ban sake neman haƙƙi na a wurinta ba sai ta fara ciwo sosai har muka tsorata nan muka nemi father paul,ya faɗa mana tana da shigar ciki ne kuma namiji zaa haifa mu shirya akwa gagarumin yaƙi dake tunkaro mu akan abunda zaa haifa!,kada mu faɗa wa kowa tana da ciki har ita ɗin tunda yarinya ce!.

Tun daga lokacin muke kula da ita sosai,idan aiki zan fita mariya na tare da ita duk da bata ƙaunar mariya ko kaɗan bare yan biyu da basu san komi baa. Bamu sake zuwa duba mallam ba duk da har aike yake mana a bari tazo su gana tashi tazo ƙarshe!,fafur na hana ta fita ko bakin ƙofa sanan na saka ƙana nan yan sanda suna gadin gidana baa bari wani ɗan uwanta ya shiga koma wanene.

Wanan dalili yasa ta tsane ni sosai wanda dama tasha ikirari ita bata sona tana da wanda zaa aura aka mata auren dole,har kwalar rigata taci a lokacin wai sai na saketa tunda baa ƙaunar yan uwanta!.ban taɓa kulata baa.

Gidana ya koma kamar kasuwa kullum haya haya ta hana kowa sake wa gida take son zuwa,sai in ƙyale ta har ciki ya fara bayyana sai kuwa ta daka tsalle sai ta kashe kanta ba zata taɓa haihuwa dani baa!,wanan dalili yasa mariya ta bani shawara in ɗauke ta muje gidan nasu idan har mallam yaga jikin dole zata kwantar da hankalin taa.

Ranara da dare nace ta shirya mu tafi gidan su...,irin farin cikin da ta shiga zan iya cewa ban taɓa ganin shi a fuskantar ba tunda muka yi aure.

Koda muka isa gidan yana kwance yadda muka barshi tun wattani baya babu wani cigaba,yadda matar shi tace sun yi ta zuwa asibiti sai ace ba'a ga komi ba!,kuka dai Amina keta yi da sambatu har ya gane mu ne muka zo.

Buɗan bakin mallam sai cewa yayi"cikin ki wata nawa yanzu?",tace bata sani ba domin a gida ake zuwa dubata kuma baa taɓa faɗa mata komi ba ya tambaye ni!,wata shida na furta a takaice.

Yace dama wata alfarma nake nema a wurin ka barau,inaso idan cikin ya shiga wattani bakwai ta dawo gida har ta haihu tunda kaga ba zama kake yi baa,wahalar zai yiwa matar ka yawa ga hidiman yara da gida.

Nace mashi naji(domin Allah Ya yini mutum mara gardama,koda ba zan yi abu ba bazan taɓa ce maka a'a baa),mun ɗan zaunadaga bisani mukamasu sallama tana kuka mua dawo gida....

Duk abunda ya faru na faɗa wa mariya,tace a bari idan ya shiga wata bakwai a faɗa wa father paul kawai!,nace mata gara ya sani tun yanzu domin mu kasance cikin shiri.

Cikin wanan dare muka gana dashi!,yace ai ya faɗa mana akwai wani gagarumin al'amari  da zai faru damu a dalilin wanana aure da mallam ya haɗa ya zama dole mu zauna cikin shiri,babban mafita shine itama lanti ta shiga wanan ƘUNGIYA domin ta iya gare kanta koda sun yi nasarar sace taa!,idan ba haka ba ana iya rasata koda an samu abunda ke cikin ta.

Nace babu ruwa na da rayuwarta saboda mahaifinta ya ja masu,buri na abunda ke cikintada sauran iyalai na su kasance cikin ƙoshin lafiya!,hajia mariya ta rinƙa magiya domin a samu ceton rayuwarta.

Tana bacci ranar hajia mariya ta taso ta zuwa inda muke ganawa...,ta tsorata da taga father paul a jikin bango wanda tsoho ne tukuf kamar aljan!, zubewa tayi ƙasa tare da riƙe ƙafafun hajia mariya tana kuka tare da magiya kada mu kasheta don Allah a mayar da ita gaban iyayen ta!.

Babu wanda ya saurare ta akayi komi ciikin sa'a  har ya tafi tana zagin mu da aibata ɗabi'un mu da alƙwarin sai nasake ta dole ta koma gidansu ta faɗa ma mallam wanda ya haɗa ta aure dashi ɗan ƘUNGIYAR ASIRI ne!....,cikin ɗakinta muka kulle ta yadda ba zata fita ba kuma akwai masu gadi a ƙofar gida sai lokacin cin abinci yayi a buɗeta...

Ciki ya shiga wattani bakwai mallam ya aiko ɗan aike a tafi da ita,nace yaje da dare zamu zo tare....,dare nayi na tafi ni ɗaya mallam ya tambayi ina amina?,nace mashi tana gida nazo muyi wata magana ne na sirri daga nan zan bashi amina idan har bai aminta da abunda nazo dashi baa.

yace yana saurara;
Na faɗa mai hajia aisha ta sanar dani komi akan makircin shi da yaudarar mijinta da yayi har ya shigo dashi wanan mugun ƘUNGIYA nashi,duk haka bai mashi ba sai da yayi sanadin iyayena!,wanan dalili yasa na shiga ƘUNGIYAR su domin ɗaukar fansa yanzu haka a shirye nake in tona mai asiri duniya tasan wanene shi wanda nasan ba zai so haka baa.

Idan har yana so in cigaba da riƙe sirrin shi har ƙarshen rayuwata ya bani rawani,tasbaha,zobe da hoton nan nashi na naɗin sarauta!,idan yaƙi zan kashe duk ahalin shi bayan na faɗa masu sirrin shi sanan idan amina ta haihu zan saketa yan ƘUNGIYAR shi su cimma burin su a kanta dashi!.

_Abunda yasa nace haka saboda duk ƙarfin shi,sihirin shi da mugun abunda yake aikatawa suna cikin kayan nan!,idan na amsa na gama dashi,hoto kuma a matsayin shaida nekoda nan gaba wani abu ya faru inada hujja mai ƙarfi a kan shi._

Yasan ƘUNGIYAR da nake ciki yanzu tafi nasu ƙarfin sihiri,kuma babban tashin hankalin shi a duniya bai wuce tonon asirin shi ba duba da babban mallami ne da ake alfahari dashi a yankin.

Da kanshi ya nuna mun inda akwatin yake na janyo hoton na ciki,na cire rawanin kanshi,tasbaha dake wuyar shi da zoben hanun shi na zuba ciki sanan na mayar da ƙwaɗon na datse.

Mallam na maka alƙawarin ba zan taɓa bayyana sirrin ka ma kowa ba a duniya ko bayan ranka!,zan riƙe amina amana duk rintsi ba zan bari ta cutu ba wanan alƙawari ne amma ya zama dole ka tafi inda ka tura iyaye na kamar yadda kayi masu na barka lafiya....,kada ka mun haka barau!,ka taimaka ka dawo mun da amina ko don na cika wa ƘARAMA alƙawarin da na ɗauka!

Daga kai har ita ku ɗanɗana irin halin ƙunci  yadda alhaji mu'azu ya shiga lokacin da ku ka tasa shi gaba kuna mashi zagon ƙasa....,ina kai nan na bar gidan.

Koda na iso gida amina tana ta buge bige cikin ɗakin duk ta jimma kanta ciwo sosai wai dole sai na sake taa!.

Banza nayi da ita  nawuce wurin hajia mariya tare da faɗa mata yadda muka yi da mallam!,tace haka yayi kuma tana so in riƙe alƙawari duk rintsi kada in saki lanti ko faɗa mata wani abu dangane da mugun halin mallam.

Tun cikin daren muka fara artabu da mutanen ƘARAMA domin sai kayi wuuuuuuu!,kamar gidan mu zai kwashe saboda ƙarfin su...,wai sun zo tafiya da lanti!,haka zamuta fama dasu har asuba sanan su koma cike da rashin nasara.

Ranar da muka yi faɗan ƙarshe kuwa har da father paul da kanshi,flayers(wizard na ƙungiyar eiye),damu kan mu aka haɗu har muhalin su muka nufa domin ƘARAMA ta sake tara tantiran aljanu mugaye irinta sun saka kafa wata ƘUNGIYA musamman domin cutar da bil adama!,faɗa sosai bana wata ba akayi ashe sun kasu kashi uku ne,"muna tare da manyan,wasu sun nufi gidana wurin lanti,wasu kuma suna wurin mallam domin ɗauƙan kurwan shi"!,mun yi nasara ƙona da yawan su duk da mun jigata matuƙa har wasun mu an samu manyan raunuka,can gida kuma basu iya yin komi da lanti ba saboda kariyan data samu da tun a daren zata rasa ranta da abunda ke cikinta. Mallam kuwa sun cire mashi idanu,zuciya,wurin fitsari da harshe.

Mun fafata sosai har gari ya fara haske sanan muka ci nasarar ƙona ƘARAMA da manyan yaranta yayin da saura suka gudu,wanda suka shiga gida na

Please Login or Register in order to submit comment