Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

riƙe jaririn tayi sosai tana neman mafita...,wani dubara ya faɗo mata tayi kamar zata afka ramin,ya nufo wurin..,sai ta koma gefe saura ƙiris ya faɗa ya juyo a hasale tare da yin kanta cikin zafin zama ya janyo ƙafar jaririn dake hanunta!

AI kuwa ta riƙe sosai tare da zube wa ƙasa,tana ja yana tana kwance ƙasa ta kasa tashi duk jikinta ya ƙuƙuje!,amma bata saki ba hat ya samu nasarar fizge ƙafar jarinrin ya taune!

Ihuuu ta sake ganin abunda ya faru nan take ta sake rungume sauran jikin  jaririn ai kuwa ALLAH ya bata sa a ta rarumi wani dutse dake gefe da hannu ɗaya ta kwaɗa mai a baki...,ya saki wani irin gurnani saboda azaba,bakin ya tsage yana zubar jini!.

Ƙara zaburowa yayi zai far mata nan take ta farka tare da sakin ihu tana ƙoƙarin tuge ƙarin ruga dake hanunta sai faɗa take;jaririna a kawo mun ɗauki !

A zabure muhammad  ya danne ta tana ƙoƙarin ƙwace wa sai kuka take yi yana ƙoƙarin rarashin taa...,jin ihunta yasa maaikaciyar jinyar dake aikin dare ta shigo da zumar masu gargaɗi suna damun sauran marasa lafiya.

Meke faruwa ne?,farka wa tayi tana ihu bansan abunda ya same ta baa.

sake ta kawai inaga zafin ciwo ne,gefe ya koma tsaye yana kallon yadda take zazzare idanu hannu riƙe da mara!,dafa kafaɗarta maaikaciyar tayi tana mata sannu...,nan ta lura ƙarin ruwan ya kwacce har wurin yayi kumburi.

Canza mata hanun zata yi sai taji ɗigan abu a ƙasa,koda ta duba jini near!,baiwar Allah dama kina da ciki ne ko al'ada kike yi ne?.

Cikin matukar tashin hankali ta dubi jikinta,shima ya nufo wurin hankali a tashe..!,girgiza kai ta shiga yi cike da tsoro"ban sani ba amma lokacin al'ada na ya wuce da sati biyu ma",Allah sarki inaga ɓarin ciki kika yi amma ban tabbatar ba sai likita ya duba ki!

CIKI !?"suka haɗa baki",ku kwantar da hankalin ku barin kira likita...,ta fice a ɗakin.

Kuka zainab ta cigaba da rerawa cikin zuciyarta tana addua ALLAH yasa ba mafarkin da tayi bane ya tabbata a kanta!,muhammad  addua yake Allah yasa cikin ne kuma bai samu matsala baa.

Tare da likita suka dawo tana riƙe da file ɗin zainab...,turo ƙofar da suka yi ya maido da hankalinsu wurin,kallon muhammad  yayi ka ɗan bamu wuri zan duba taa.

Bai furta komi ba ya fita a ɗakin yanata addua  a zuciyar shi.., sannu ko madam ?,likita yace da ita amma bata amsa baa.

Ki kwantar da hankalin ki zamu yi iya ƙoƙari wurin baki cikakken kulawa a nan. Shiru dai tana kallon shi..,bayan ya ɗan dudubata yace da nurse ɗin ta gyara mata jiki ta taimaka mata zuwa ɗakin ganawa da marasa lafiya na musamman zai ƙara duba taa.

Taimaka mata tayi zuwa ban ɗaki tayi tsarki tare da saka pad  sanan ta bata riga dogowa wanda marasa lafiya ke sawa ,ta riƙo hanunta suka fito...,ganin su muhammad  ya miƙe tsaye yana tambaya"lafiya dai?",zaa dubata ne ,nurse din ta bashi amsa suka wuce..,abunka da asibitin kuɗi akwai ƙarancin mutane har suka isa basu haɗu da kowa baa.

Kwantar da ita akayi saman wani gado ya tambaye ta ko tana jin fitsari?,ta girgiza kai!,ruwan gora ya umurci nurse ta bata,ta shanye duba.  Haka ta shanye ya cigaba da rubuce rubucen shi har zuwa wani lokaci ya sake tambayar taa,ta amsa tana ji.

Umurni ya bata data kwanta zaa yi mata hoton mara(pelvic ultra sound scan), domin gano yanayin da take ciki,ba musu ta kwanta ya fara aikin ckin gwane wa ...,ya ɗauki lokaci yana yi daga bisani yace ta tashi ta koma ɗakin da take kwance,da safe idan ta sake samun ƙwarin jiki zai magana da su duka amma a kira mashi mijin.

Muhammad  naji saƙon likita ya shiga da sauri...,wuri ya nuna mashi ya zauna tare da bashi wani takarda,wanan bill nku kenan idan ka biya zaa baka sauran magunguna.

Zan iya biya da credit card ɗina?,sosai ma inaga ba zan shigo da wuri ba gobe da safe saboda akwai marasa lafiya a zan duba a babban asibitin gwagwalada,amma zan yiwa nurse magana ta kula da ita idan na shigo bayan na ƙara dubata zan maku bayanin matsalara taa,yanzu dai bata cikin wani damuwa.

Godiya yayi sanan ya fice zuwa inda zai biya kuɗin likita ya haɗa kayan shi zai wuce..,sai daya biya aka bashi receipt da sauran magunguna ya kawo wa nurse ɗin.

Tana dai kwance shiru ya tsaya gefe yana kallonta cikin tausayawa har nurse din ta mai magana ya basu wuri..,fita yayi sai data gama komi ya dawo tare da zama gefen gadon hanun shi riƙe da nata,yana  kuma yana shafa kanta cikn tsigar rarashi..,kiyi hakuri zee duk abubuwan dake faruwa laifi na near,bana yadda da maganar ka,bana haƙuri dake abubwa suna faruwa dake a dalili na,kuma ba kowa bane sila sai mami!,amma nayi alƙawari zan yi maganin taa.
Rufe mashi baki tayi da hannu,ya isa nayi imani duk abunda ya aru dani daga Allah ne amma dai ya zama dole mu bincika lamarin mami.

Shike nan Allah baki lafiya.

Cikin ikon Allah ciwon marar ya tsagaita mata har ta samu bacci yana zaune,zuwa wani lokaci ya jingina shima sai bacci...,zuwa da asuba aka cire mta ƙarin ruwa nurse tace ya samo mata abunda zata ci mai zafi.

Masallaci ya nufa yayi sallah daga nan ya wuce gidan iyayen shi...,Gidan shiru baa tashi bacci ba ya nufi sashin hajiyar shi,nan ma sai day buga inna mardiyya ta buɗe suka gaisa,ya tambaya ko sun ɗaura abun karyawa?tace ta ɗaura ruwa dai.

Don ALLAH a hanzart idan yayi zafi a samun a babban flask,a soya ko dankali da kwai ne zainab na asibiti barin shiga wurin hajia yanzu zan fito.

Assha ashe jikin ya matsa haka?,Allah bata lafiya yanzu zaa haɗa kuwa..,ɗakin hajia ya shiga da sallama suka gaisa ,lafiya dai da safen nancy?,ya faɗa mata abunda ya faru,"ina mami?",shine tambayar data fara jeho mashi!,mamai na gida na barta saboda cikin dare muka nufi asibitin..,yanzu kai moha don baka da lissafi zaka bar yarinya yar shekaru goma ita ɗaya a gida saboda ɗan ciwon mara na al'ada da ya kama matar ka,babu kunya ka kwashe zuwa asibiti?,banga laifin ka ba ta riga ta gama da kai moha,mace bata da amfanin komi amma ka liƙe mata haka?,Allah ba zan ƙyale ku ba idan wani abu ya faru da mami!.

Hajia kiyi hakuri ciwon ne yaci ƙarfinta kuma dai bata taɓa yin irin shi baa,kinga ma nurse ɗin tace tana tsammanin shigar ciki ne ya fara samun matsala amaa ynzu da sauƙi.

Shigar cikin gidan kurt!,ka taba jitter/ganin inda aka ɗaure wa mace bakin mahaifa sanan ta samu ciki?,inace ta inda ƙwan haihuwar zai shiga aka rufe?,shashasha kawai wanda bai san inda ke mai ciwo baa,ka tsaya lelen ta har ka rasa wacce Allah ya baka tunda ita ba so take ba ko an rasa bata da hasara boko ya fice mata haihuwar.


Ganin faɗan ba zai ƙare ba ya mata sallama zai koma asibitin..,kai zaman asibiti ya kama babu wani nawa da zai biyo kurt,sanan ka tabbatar ka ɗauko mun yarinya a zauna a nan har ku gama shirmen zaman asibitin idan kun shirya kua da ita sai ta koma.

Wuce wa dai yayi zuwa kitchen ruwan ya tausa an zuba a flask da kofuna an soya ƙwai dankali ya rage baa kwace ba...,zama yyi ya jira lokacin har gari ya fara haske hankalin shi na asibiti wurin zainab,ya yiwa inna mardiyya godiya ya tafi.

A hanya ya saya madara,sugar,milo da  bread ya isa tana zaune saman gado shiro ba kowa a ɗakin....,ya jiki naki?,da sauki ta amsa ina mami?,
ba gida na tfi ba wurinsu hajia tana maki ya jiki. Ina amsawa tace duk da tasan ya dai faɗa ne kawai.
Ya shiga haɗa mata shayin da komi yadda take so ya dawo bakin gadon,a hankali take sha har ta ƙoshi shima ya ɗan ci domin hankalin shi ya koma gida wurin mami gashi bai fito da waya baa.

Akwai abunda kike so ne?"ya tambaya cikin kulawa",eh ka tafi gida ku zo da mami,sanan ka ɗauko mun kayan da zan sauya da wayata.

Shike nan sai na dawo!,tana kallo ya fice.

Koda ya isa gida mai gadi ya buɗe mai suka gaisa sanan ya wuce ciki..,yadda ya rufe ƙofar haka ya same shi alamar baa taɓa baa.  Buɗe wa yayi ya shiga shiru bbu kowa a palo ya higa ƙwalawa mami kira shiru...,har ɗakinta ya shiga wayam kuma babu kowa a toilet har ƙasan gado da closet ya duba ba kowa!,kuma ba alama an fita ta window.

Ya nufi ɗakin baccin su...,yadda suka bashi haka yake!,ko ina ya duba a gidan har can baya harabar babu kowa nan hankalin shi ya fara tashi!,ciki ya koma ya ɗauki riga doguwackier,zani da hijab na zainab sai wayoyin su ya nufi wurin mai gadi...,wayar shi na kunne yana kiran hajiyar su.

Ya iso wurin kenan ta ɗaga"am nace ko kin aiko driver ya ɗauki mami ne?",saboda me zan aiko driver?,bayan mun gama magana nace ka kawo mun ita da kanka ko amsa ni kayi?.

innalillah ya furta!,me ya faru near?,ba komi dama na dawo gida ne ban ganta baa!

Baka me baa?,wallahi ƙarya ne duk inda jikata take a cikin garin abuja sai kun fito mun da ita!,ta kashe waya.

Tashin hankali wanda baa sa mashi rana,bai san lokacin daya jingina da jikin ɗakin maigadi ba!,ranka ya daɗe meke faruwa?,kai zan tambaya tunda kai ka kwana a gidan!.

Wallahi ran ka ya daɗe jiya ban yi bacci ba a gidan domin wasu abubuwa na ban al'ajabi ya faru,wasu koke koke kamar na dabbobi ko jinnu dai gashi nan har asuba ,nayi nayi in shiga ciki in dubi halin da yarinyar nan ke ciki wuri a rufe wayar ka dana uwargida bai shiga!.

Shike nan nawa ya ƙare domin bata cikin gidan babu inda ban duba ba wallahi ba kowa!,A'a ran ka ya daɗe a sake duba wa dairy...,ya nufi cikjn gidan yana ƙara duddubawa.

Ya ɗauki lokaci sanan ya dawo cike da tashin hankali domin bai ga kowa baa!,muhammad  yace zama bai ganshi ba bari ya duba maƙwabta duk da estate ne babu wanda ke damuwa da wani,haka ya rimƙa yawo cikin anguwan har cikin gari gidajen yan uwa ace bata zo baa.

Koda ya isa likita ya shigo tafiya na gaugawa ya kamashi zai shiga garin minna saboda su ya shigo,kuma har ya zauna da zainab a office ɗin shi muhammad  ya dawo.

Ya shiga ɗakin babu kowa ya tambayi nurse ta nuna mai office ɗin da ake jiran shi...,da sallama ya shiga suka gaisa ya nuna mashi wurin zama.

Bayan ya kalle su na wani lokaci ya fara magana;kun taba amfani da wata hanya na tsarin iyali ne?,daga sama tambayar yazo masu.

Eh likita a farkon auren mu nayi tubal ligation wanda zaɓin mijina near,a cewar shi sai mun mori rayuwar auren mu zamu fara tara iyali,na goyi bayan shi duk da an faɗa mana illar dake ciki saboda ina da burin komawa makaranta.

Jijina maganar yayi,amma haihuwar ki nawa?,ɗaya!.

Kuma baki samu wata matsala ba tun daga rainon ciki har haihuwa?,gaskiya na wahala matuƙa wanda da kyar na haihu da kai na.

Maganar gaskiya kun tafka babban kuskure domin shi tsarin iyali irin wanda kuka yi bako wace irin mace ake yiwa baa,hasali ma sai wacce tatara iyali sosai kuma ta tabbatar bata buƙatar wani haihuwa har karshen rayuwarta, ko wacce rainon ciki da haihuwa ke zuwa mata a wahalce har wurin haihuwar ta kanyi yunkurin rasa ranta sai an mata aiki,sune irin matan da ya dace su ɗauki wanan tsarin iyali na ɗaure bakin mahaifa(tubal ligation).

Domin idan aka yiwa mace irin ki wanan tsari gaskiya da wuya ta isa ɗaukar wani cikin,saboda an ɗaure bakin mahaifa babu ta yadda maniyyi zai shga ciki,illa ya taruwa ne a saman mahaifa zuwa wani lokaci yabi jikin ɗan adam ko ya fita a lokacin jinin al'ada.

Illolin shi nada matuƙar yawa da hatsari,ciki akwa;
_yana ɓata inda fitsari  ke taruwa a jikin mace(bladder),da magudanan jini(blood vessels)._

_Ciwon mara mai tsanani har ƙarshen rayuwar mace_

_Idan kuma ALLAH ya nufa kin samu ciki zai rayu ne a wajen mahaifa(ectopic pregnancy ),wanda zai zo da matuƙar wahala tare da barazanar tafiya da rayuwar kibbutz,idan ya kai ma lokacin haihuwa sai anyi aiki ko a rasa ki ko abunda ke cikin ki._

wanan ne yasa cikin ki na farko kija wahala sosai Allah ya taimaka kin rayu da abunda ke cikn ki.

Yanzu dai a takaice kina ɗauke da cikina sati shida a wajen mahaifa(ectopic pregnancy ),ciwon mara da kika yi fama dashi yana daga illar tsarin iyali da kika yi shine har yake barazanar lalata cikin!,Allah ya taimaka duk da ya fara zuba mun dakatar dashi ta hanyar wani allura wanda kuka saya dubu talatin da biyar.

Yanzu cikn na lafiya zamu bata hutu na wata biyar(bedrest)idan anan kuke so ko a gida,abunda ake bukata dai ko spoon kada ta ɗauka da hanunta har cikin ya shiga wata shida kenan.

Saboda tsabar farin ciki kuka ta shiga yi na farin ciki,shi kuwa baki ya kasa rufuwa.

Yace da likita a basu sallama zai koma gida da ita zaa kula da ita sosai.

Shawawari ya ƙara basu da magungunada zata yi amfani dashi sai sallama.

Sun fito ne take tambayar shi ina mamin?,ya tsinci bakin shi da cewa tana wurin hajia can zamu yanzu haka!

follow
vote
comment
share.
[6/6, 14:33] LEEMA: *🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
       *NA*

          *L££MA*
wattapad
*@leemaMuhammad826*

  _Sadaukarwa gare ku_👇🏻
*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*

*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*

*Mutane nata tambayar page 9-10,kuyi hakuri mistake nayi wurin numbering nayi page 7-8 sau biyu idan ku ka duba labarin ya tafi dai dai,sai page na ranar Thursday ya kamata ya zama 9-10 na saka mashi 7-8 kuma.Ayita hakuri kuskure ne nagode❤*

TALLAH!!!

_*ƙungiyar brilliant writers na yiwa masu karatu abishir da sabon littafin ɗaya daga cikin haziƙar maruciyar da zai fito bada jimawa ba"RASHIB HAIHUWA(da ciwo)daga alƙalamin OUM FARHANA(habibah shehu)kada ku ku sake a baku labari*_

*🅿13-14*

    Shiru ne ya biyo baya ko wane da abunda yake tunani a cikin zuciyar si har suke isa babban gida ya yi horn mai gadi ya buɗe tare da mashi barka da zuwa.

Tunda suka aje mota ya taimaka mata ta fito,samarin dake haramar gidan suke mata Allah sanya albarka(da yake ya kira kowa a waya ya faɗa masu),sai dai ta murmusa domin tana da alkunya,shike washe baki yana amsa wa har suka wuce inda mutane suke saura ƙiris su isa sashin hajia lanti yace,darling barin ɗauke ki nasan kin gaji da yawa ko?.

Waro idanu tayi waje,don Allah ka rufa mun asiri ina da kunya..,oh ni ne mara kunya ko?,wai naga ko irin ɗan alkunyar nan babu sai washe baki ka ke kana amsa gaisuwa.

Ah zee ALLAH ya amshi addu'ar mu na tsawon shekaru goma ha biyar yau ya azurta mu da samun namu rabon,jinin mu babu sirki!,kinga kuwa ba zan zama butulu ba ko?.

Haka ne,Allah ya inganta mana yasa rabo ne. Yawwa matata amin thumma amine,dai dai ƙofar hajia ya tura da sallama hanun shi ɗauke da kayan zainab....,tana zaune a palon tare da matar umar da yaranta suna karin safe.

Wuri zainab ta nema a ƙasa"ina kwana hajia,ina kwana aunty balki?",hajia bata amsa baa,ita balkin ce ta amsa a ciki bakinta cike da ƙosai ga kofin kunun gyaɗa gaban su,yaran kuwa shayi suke sha.
_wanan ya zama ɗabi'an surukan hajia lanti banda zainab,kusan kullum zasu kwaso yaran su a gidan zaa karya,aci na rana har na dare idan mazajen sun shigo nan zasu ci sanan su kwashi matayensu a tafi gida. Idan lokacin makaranta ne iyayen na wurin aiki daga makaranta aka ɗauko yara gidan zaa zube su sai dare a dawo dasu_

Gaisawa suka yi da muhammad  cikin girmamawa har da addua ALLAH raba lafiya balki tayi.

Hajia ta tsare gida  hankalinta kwance tana karyawa,har ta gama suna zaune mai aiki ta kwashe kayan...,sai lokaci ta ɗago ta kalle su da kyau idanunta kur akan cikin zainab daga bisani tace,"ina mamin?",kallon juna suka shiga yi babu bakin magana domin hajia ta tsare su da ido,zainab ma kallon tuhuma take mashi!.

Cikin inda inda yace,ai na ɗauka tan nan wurin ki ....,da ka kawo ta yaushe?,"ta daka mashi tsawa!",ayi hakuri dai hajia wallahi koda na koma gida mun duba sosai a mai gadi bata nan,inda nasan za'a same ta naje bata.

Ƙarya ne wallahi kun yi kaɗan!,daga matar ka ta samu ciki sai a iza mun jika saboda ba sonta ku ke yi baa?,miƙewa tayi,na baka awa ɗaya duk inda take ka nemo mun ita!,tana kai nan ta wuce ɗakin ta cikin tashin hankali...,zube wa tayi bisa gwiwar ta hanunta duka saman kanta,sosai ta riƙe shi domin yana juya mata!

Mami!,mami ina kika shige ne?,idan kika yi nisa dani asirina zai tonu,kece rufin asirina!,shekaru ashirin ke nan ina ɓoye da wanan sirri don ALLAH kada ki guje ni zan tozarta a idon duniya domin kece maganin matsalata,cikinn nan na jikin zainab ba ƙaramin barazana bane a gare ni!.

Kamar wacce aka tsikara ta miƙe zuwa palo...,daga naya suka jiyo muryar ta,ka tashi ya nemo mun jikata!,zan cigaba da riƙe matar ka a gidan nan har sai ka gano inda mami take!.

Cikin tashin hankali zainab ta kalle ta domin jin abun take kamar wasar kwaikwayo!,ba a ga mami baa?,itace zata zauna a gidan hajia har na tsawon wani lokaci?.

Yana miƙewa itama ta miƙe,ƙafata ƙafar ka wallahi ba zan zauna ba duk inda aka kai mun yarinya sai an fito da ita domin na lura kaf ahalin ka babu mai sona da cigaba,ana ɓakin ciki da farin cik na!

Daakata zainab!,"ya daka mata tsawa",da wanne zan ji ne saboda Allah?,duk wanda ya fi muhimmanci!.

Lallai moha a gaban ka zainab take ci mun mutunci kada kallo?,kiyi hakuri hajia mu yi abunda zai fisshe mu,ya zama dole zainab ta zauna a gidan nan domin bata da lafiya,zan fita neman mami.

Wallahi ba zan zauna ba garin mu zan koma kuma tare da ƴata!,kada kije ko ina Allah zainab zan mumunar saɓa maki idan kika bar gidan nan!,ai ba yau ka fara saɓa mun ba.

Hanyar waje ya nufa ta bishi a baya...,bayan hanunan shi yasa ya bugeta!

Jiri ya kwasheta nan take ta dafe bango tare da yunƙurin sake bin shi...,
ai kuwa ƙafa ya saka ya shure ta a gefen ciki!

Ƙara ta saki tare da dafe wurin nan take ta fita hayyacin ta..,hajia na zaune zuciyarta fal farin ciki burinta zainab ta fice daga rayuwar ɗanta,domin ita ɗin barazana ce a gare su.

Balki dai tausayin zainab ya kamata domin a gaban hajia ne kawai take nuna mata ƙiyayya,cikin zuciyarta tana matuƙar sonta da tausayina gudun ɓacin ran hajia yasa bata nuna wa.

Mai aikin hajia mariya da yanzu driver ya sauke ta sun dawo daga kasuwa tunda suka shigo komi akan idonta ya faru har muhammad  ya shiga mota zai wuce...,ta isa wurin zainab tana mata sannu ta kamata zuwa sashin hajia mariya,lokacin hankalin hajia lanti na kan yaran balki da suka fara kuka ganin abunda ke faruwa(abunka da yaro).

Koda ta duba babu zainab a ƙofar ɗakin,a zabure ta tashi domin a leƙa...,bata nan kuma ba motar muhammad .

Idanu ta rinƙa zarewa kamar mahaukaciya,balki kinga babu zainab a wurin ko tare suka fita ne?,girgiza kai tayi,ban lura ba hajia.

Zirga ya shiga yi ina zainab ta shige nea?,wanan rana yazo mun da rashin sa'a babu zainab ba mami!?.

Waya ta ɗaga ta kira muhammad daya parker mota a gefen titi yana kukan nadamar abunda ya aikata wa zainab,bayan a gaban shi likita ya bada sharuɗan a kula da italy,ta ina ma zai fara neman mami?.

Wayar shi dake ruri ya maido dashi cikin hayyacin shi ya ɗaga"tafi ya kayi da matar ka ko?",xuwa ina kuma hajia?,gidan ubanka lalatacce kawai,idan ba tafiya kayi da ita ba ina ta shiga?,ni ban sani ba domin nan na barta a gidan!,"yana kai nan ya kashe wayar gaba ɗaya",ya shiga tashin hankali.

Balki na zaune cike a mamaki da tsoron hajia,domin sai sambatu take kamar mahaukaciya har ta fara zargib akwai wata a ɗasa!

Mai aikin hajia mariya na isa da zainab sashin,hajia ta taso cike da tsoro"me zan gani haka?",hajia ban san meke faruwa ba kawai na ganta ne duƙe a ƙofar sashin hajiyar su shine na wuto da ita nan.

Riƙo ta tayi meke faruwa dake zainab?,muna farin ciki an samu ƙaruwa kuma!

Ashhaa zainab sannu!,lami kai ta ɗakina saman gado barin kira hafsa a waya tazo a duba taa(matar yaronta ma aikaciyar jinya ce).

Saman gado ta ajeta sai sannu take jero mata..., har lokacin hanunta riƙe da wurin da ya shure ta.

Hajiyata shigo tana yimata sannu har hafsa ta iso gidan daga wurin aiki..,a hanzarce ta shigo suka gaisa hajia na faɗa mata zainab nada shigar ciki ne kuma kamar tana fama da ciwon mara.

Kayan awon cik ta fito dashi tare da duba yanayin cikin,babu wata matsala ta fito da wani alurra kwalba uku ta haɗe wuri ɗaya tayi mata.

Zata yi bacci sosai kada a tashe ta har sai ta tashi don kanta in shaa ALLAH zai bari.

Albarka hajia mariya ta sanyawa surukar ta tare da fatan alheri.

Ba'a daɗe ba bacci ya ɗauke zainab,hajia ta jima tana kallon ta cike da tausayawa domin babu abunda bata sani ba kawai ƙyalewa takebab,amma tayi alƙawari ba zata ƙyale hajia lanti ba idan wani abu ya faru da cikin zainab domin kar ta san kar shi yasa basa shan inuwa ɗaya!.

Bata son kai ƙararta wurin mijin su saboda bashi da cikakken lafiya,nan take ne jinin shi ya hau.

palo ta koma tare da ɗauko wayarta ta shiga neman lambar hajia fatima(mahaifiyar zainab)...,daga ɗaya ɓangaren safiyyah ta ɗaga da sallama,bayan sun gaisa tace taba hajiyar su waya.

Tace ta kashe zaa kira anjima domin tana wurin wanka ne.

Kashewa suka yi safiyyah dai hankalinta ba kwance bp,saboda tun ranar da mami ta kirata akan zasu zo ,zainab ta amsa tace da maman su akwai matsala akan lamarin mami hankalin su ya kasa kwanciya har yau da safe da muhammad  ya kira yaba faɗa masu zainab na ɗauke da shigar ciki.  Sai dai tun lokacin suke kiran layinta baa ɗaga ba a ƙarshe ma wayar a kashe.

Hajiyar su na fitowa tayi saurin kiran hajia mariya..,bata ɗauki lokaci ba ta ɗaga wayar da sallama.

Suka gaisa cikin mutunta juna a matsayin su na manya,hajia mariya
tace hajia fatima magana nake so muyi na fahimta a matsayin mu na many,domin abunda babba ya hango yaro ko ya hau ribi ba zai hango baa.

Tace haka ne hajia mariya,yawwa akan maganar zainab ne,tsakani da Allah yarinyar nan tana cikin damuwa matuƙa,idan da hali ku ɗauke ta kawai ta dawo gaban ki,saboda wata rana fa sai dai a kira ku ɗaukar gawanta.

Subhanallah!,abu bai yi daɗi ba kuwa hajia,kin san sha'anain ɗan yau baka matsa mashi idanba shi  ya kawo maka magana baa,sai ka saka mai idanu lamarin mata da miji sai Allah.

Duk da haka hajia fatima ya kyautu ki jata a jiki,ɗan yau sai da rarashi musamman zainab ba mai yawan surutu bace akwai zurfin ciki.

Tau hajia wallahi babu abunda zan iya yi a kai domin mahaifin su nada tsauri sosai,ba zai goyi bayan a dawo da ita gida ba amma zan turo safiyyah idan ya amince ta ɗan zauna da ita har cikin yayi ƙwari.

Jikin hajia mariya yayi sanyi domin taso su duba lamarin dai da idon basira,rayuwar zainab da abunda ke cikintana cikn hatsari!,bata so aji komi a bakinta ne kada ace ta haddasa fitina.

_Iyaye muji tsoron Allah ku sani yaran nan da Allah ya baku amana ce a gare kurt,akwai hisabi a tsakanin  ku,kuja su a jiki domin sanin damuwar su,ku fi kowa kusance dasu ta hakane kawai zasu sake daku sosai,duk da yawancin mata da suke fuskantar ƙalubale a gidajen auren su gudun ɓacin ran iyayen su yasa suke ɓoye wa,iyayen basa yiwa yaran adalci idan magana ya fito baa taɓa tsayawa a jita bakin mace sai a ɗaura mata laifin gaba ɗaya,kafin ka sani anyi rayuwar ta mummunar illa,Allah yasa mu dace._

Ɗakin ta sake leƙawa,zainab na bacci cikin kwanciyar hankali..,kitchen ta nufa ta bada umurnin abunda zaa dafa wa zainab mai ruwa ruwa.

_Duk data manyanta sosai mace ce mai kazar kazar da motsa jiki shi yasa ba kasafai ake gano ainihin shekarun ta baa._

Muhammad gajiya yayi da yawo ya nufi office ɗin babban yayan shi..,bai ɓata lokaci ba ya zayyane mashi komi,shawara suka yanke kawai zasu kai report wurin yan sanda,gidajen radio da talabijin sanan  su sanar da mahaifin su domin idan yaji daga sama ba zasu ji daɗin halin da

Please Login or Register in order to submit comment