Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta wani kwaso jiki wai wai kaya tazo ɗíba,wanda idan bincika zuciyarta suhu take nemaa mijinta"tana kai nan taja tsaki!",mayah bana son haka nan fa,idan sulhun take nema ina ruwanki ko tsarar kice?,ince dai mijinta ne kuma yana son abun shi menene damuwar ki?,bana son sake jin irin wanan magana a bakin ki sanan wanan kallon banzan da kike minta dashi ya tsaya haka nan bana son fitina!

Kiyi hakuri ba zan sake baa,da yafi maki dai ta wuce ɗakinta mayah na nan tsaye kishi ya cika ta tana tunanin yadda zata fara kwana ɗaki ɗaya da matar wanda take so.Gaskiya ba zata iya kwana a ɗakin nan ba domin tana iya shaƙeta cikin dare ta mutu kowa ya huta,kawai ta wce ɗakin yara ta kwanta.


Da safe da wuri zainab ta tashi ta gyara ɗakin data kwana har palo sanan tayi wanka ta zuba lace ɗinkin bubu wanda ya amshi jikinta nan take ta tsinci kanta da zuba kwalliya wanda ta manta rabonta da yin shi ta nemi wuri ta zauna tana chat....

Mayah koda ta fito an gyara wuri kitchen ta nufa kai tsaye domin haɗa abun karin safe ma yara da zasu wuce islamiyya.Kwaramniya zainab taji wanda yasa ta fito a tunaninta ma ramatu ce ta fito.

Har kitchen ɗin ta shiga da sallama wanda mayah ta juyo suka haɗa ido nan take kishi ya taso mata ganin zainab ta chaɓa ado sai data razana a ciki ta gaishe taal,da sakin fuska ta amsa domin dai bata san dalilin wanan ɗaure ɗauren fuska baa,"mumyn nabil bata fito baa?",uhm kawai mayah tace sanan ta cigaba da aikinta zainab ko ɗakin ta koma.

A gagauce mayah ta kamala tana zancen zuci sanan ta shirya ma yaran suka wuce da yake ba nisa da gidan sosai a ƙasa suke zuwa,ta nufi toilet ɗin yara tayi wanka wnda ta ɓata lokaci sosai ta dawo ɗakinda zainab take itama ta ciro duguwar riga na lace ta shirya a ciki duk da ya mata kyau amma bai amshi jikinta baa.

_Mata don ALLAH a daina irin wanan kishi na jahilci wai don abokiyar zaman ki tayi abu ya mata kyau kema kice lallai irin shi zaki yi!,idan da hali kiyi wanda yafi nata ba dai dai yada take ba domin yanayin halluta ba ɗaya bp,ƙarfi ba ɗaya ba haka baiwa kowa da irin wanda ALLAH ya bashing!,abunda zai yiwa wani kyau ba lallai bane ya maka,haka abunda ya maka ba lallai bane yayi wa wani misali ga kayan sawa akwai banbancin a tsakanin guntuwa da doguwa,siririya da mai ƙiba,fara da baƙa yadda mai kiɓa doguqlwa zata saka riga ya amshi jikinta siririya yawo zata rinka yi a ciki ,haka zalika yadda siririya daguwa zata ɗaura zani ko skirt ya amshi jikinta mai ƙiba ba zata sake cikin skirt ba wata ma a takure take dashi,duk wani abu da zaki yi wanda zai faranta zuciyar mijinki shi zaki mayar da hankali a kai ba wai kwaikwayon kishiya va_


Har masu gida suka tashi zaman jugun ake yi tsakanin mayah da zainab domin ko ruwa bata taya mata ba bare shayi.Sun gaisa da shafi'u cikin sakin fuska yake shaida mata baa bar mashi makulli ba amma sun taso suna hanya ta ƙara hakuri idan ba matsala ta zauna a gidan har su iso taje tayi abunda ya kawo ta.

Ba haka taso ba kawai vata iya mashi musu ne domin tana ganin girman shi.Ramatu na kitchen ta same ta a can tana kama mata suna taɓa hira har ta gama haɗa wa mijinta breakfast ta zuba wa zainab nata sanan tasa mayah ta kai mata ɗaki taci. Tayi dariya sosai ganin mayah da lace wanda da dukkan alamu ganin zainab dashi ne ya saka itama ta sa irin shi,lallai akwai drama kenan yau idan muhammad ya dawo.


Follow
vote
comment
share
[7/5, 14:02] LEEMA: *🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
       *NA*

          *L££MA*

wattapad
*@leemaMuhammad826*

  _Sadaukarwa gare ku_👇🏻

*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*

*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*





*🅿47-48*

 
       Ƙarfe shida na yamma a garin abuja tayi wa muhammad  da hajiyar shi,gidan su ya nufa kai tsaya domin ajeta ya gaisa da abban su sanan ya nufi gida...

Zainab kuwa yinin ranar haka ta yishi sukuku saboda ta lura mayah na mata wani gani gani wanda bata san dalili baa,ita ramatu ta kwashe yaranta tunda rana sun wuce can gida zasu jira isowar hajiya wuri yayi shiru daga ita sai mayah wace ke wani yatsine yatsine!,bata da wurin zuwa dama tun zamanta abuja sai gidan yusrah wace itama a sanadin muhammad  ta ƙulla aminta da ita wacce matar abokin shi ne.Yunwa take ji sosai kuma da alama mayah bata girka komi baa.


Sai da suka gama cin abinci sanan shafi'u ke labarta mashi zuwan zainab wace yanzu haka take gidan shi.Wani farin ciki yaji ya mamaye zuciyar shi kenan Allah ya karɓi addu'ar shi matar shi ta dawo gare shi!,yaya gaskia ina matuƙar son zainab saboda haka ba zanyi wasa da wanan daman ba kawai zan mayar da auren mu tunda wata ɗaya kenan da sakin bata gama idda baa.

Dakata moha,kada ka sake zainab ta gano zumuɗin ka a kanta,baa yiwa mata haka nan inaso ka nuna baka ma san Allah yayi ruwanta ba a duniya,idan zaka iya kada ka sake ku haɗu domin dai na tabbatar maka zainab nan da ɗan lokaci zata neme ka da kanta idan taci wuya.

Gaskiya ba haka yaso ba amma dai ba zai iya bijire wa yayan shi bane.Shikenan zanyi ƙoƙarin yin yadda kace.

Sai da suka yi sallar isha'i sanan suka yi sallama da hajia kowa ya nufi gidan shi da alƙawarin ba zasu bari hajia tasan zainab na gari ba saboda zata ɓata masu shirin su.

Da yunwa ya ishi zainab da zanta ta shiga kitchen ta girka ɗan indomie,mayah na zaune palo tana kallon ta har ta gama ta zubo a plate ta kawo wurin mayah"bismillah ga abinci",aciki ta amsa bata ci.

Wuri zainab ta samu gefe ta zauna har ta gama ci tana zancen zuci kawai ita zama gidan ya isheta ba haka ta tsara wa kanta baa,saboda me zata dawo ƙarƙashin ƴan uwan tsohon mijinta tama zama har yariya ƙarama sa'asar ƙanwarta safiyyah na mata rainin wayau!.Ya zama dole a yau ta bar gidan ba zata iya ƙara kwana baa.

Alamar tsayin mota ya dawo da ita daga tunanin da ta shiga yi..,suka shigo har yaran suna yiwa mayah oyoyo,suka gaisheta lokacin iyayen sun shigo nan suka gaisa.Sha'fiu yace kiyi hakur mun jima bamu dawo baa,basu iso da wuri bane amma yanzu yana gida kina iya zuwa zan kai ki tunda dare yayi.


Ba damuwa nagode da ƙoƙarin ku,kawai ka bari zan tafi da kai na daga nan zan wuce masauki na...

Aunty zainab da kin bari yaya ya kai ki tunda dare yayi abun hawa zai maki wuyar samurai,"cewar mayah",da mamaki zainab da ramatu suka kalle ta domin dai tunda zainab ta zo gidan ba wata maganar arziki ke shiga tsakani su ba har gaisuwar ma da kyar take amsa wa.

Ita mayah tayi haka ne saboda kishi,bata so zainab ta tafi ita ɗaya su keɓe da muhammad kada wani abu ya shiga tsakanin su!

Ka barshi kawai zan tafi ba matsala ai.Ɗakin ta koma tare da haɗo kayanta ta fito kenan suna sallama da mutanen gida taji alamar tsayuwar mota....,tana ƙoƙarin fita ne suka yi kiciɓis da muhammad!

Nan take ya ɗauke kanshi yana ƙoƙarin wuceta duk da saboda ita yazo ya ksa haƙuri zuciyar shibta ingiza shi yazo ya ganta ko zai samu sassauci a zuciyar shi.Ramata tace ɗan halas kaƙi ambato yanzu kuwa muke maganar ka.

Wuri ya nema ya zauna saman kujera a gadarance,ai kuwa dai gani nazo hanya ce ta biyo dani nayi mantuwa a motar mijin ki(duk ƙarya ce babu abunda ya manta).Shafi'u wanda ya gano shi yace ai kam dama yanzu zainab take shirin zuwa gidan akan maganar da nayi maka.


A takaice yace,ta jira har in tashi komawa gida saboda na riga na fito....,ba sai najira ka ba saboda ba wurin ka nazo ba kaya na zan ɗauka wanda mallaki nane,"zainab ta katse shi".

Kafaɗa ya ɗaga cikin halin ko in kula sanan ya ɗaura makullan gida saman tebur,gashi nan ki tafi idan kin gama abunda ya kai ki sai kiba mai gadi makullan.

Ɗauka tayi tare da masu sallama ta fice abunta...,mayah da kishi ke cinta amma ganin ydda basu damu da junan su ba sai abun ya mata daɗi sosai.Ramatu taja ta suka nufi ɗaki domin su basu daman tattaunawa.


Muhammad menene kayi kenan?,inace nan muka gama magana da kai bana so yarinyar nan ta ganka ma!,yaya ba zan iya daure wa bane kayi hakuri har yau babu abunda ya ragu na soyayyar da nake yiwa zainab,itama nasan haka taurin kai ne kawai da jan aji irin nasu na mata yasa take basar wa.


Atau tunda kana son matan ka ai sai ka bita kawai ka faɗa mata ka mayar da ita ku cgaba da zaman auren tunda hakane na cire hannu na.



Tashi yayi kuwa zai fice dama ganinta yazo yi kuma ya ganta....,yanzu da gaske moha binta zaka yi?,yaya kaga dare yayi ba lallai bane ta samu abun hawa kuma dai bata da wasu ƴan uwa a garin nan ban san inda zata nufa baa!

Babu ruwan ka sakarai kawai!,ina nema maka ƴanci kana sake mayar da kanka bawa ko?,duk inda zata tafi ruwa gudu amma na tabbatar maka sai a neme mu a cikin kwana kin nan kuwa.

Wuri ya nema ya zauna ba dan yaso baa.

A hankali zainab ke tafiya a ƙasa bata samu abun hawa ba sai sake sake take yi jikinta yayi sanyi sosai,wai ita zainab muhammad zai basar cikin ƴan uwan shi yana nuna halin ko in kula akanta!,wallahi zata yi maganin shi sai dai son shi ya kashe ta amma ba zata taɓa ɗaga mai ƙafa baa.

Da ƙyar ta samu abun hawa akan naira dubu ɗaya zai kaita gidan....,sai da suka gama gaisawa da mai gadi yake ƙoƙarin faɗa mata mai gida ya sake fita!,a hasale tace rufe mun baki don Allah Ba wurin shi nazo ba!

Buɗe gidan tayi tsaf dashi kamar lokacin dake nan,babban elargment ɗin sune manne a bango kamar zaa kira su su amsa ta tsaya kallo idanunta sun kawo ruwa!,tayi saurin share wa ta nufi ɗakin baccin su inda babbam hoton mami ke manne tayi kyau sosai tama dariya....ta jima tana kallon shi abubawa da dama suna dawo mata a kai kawai ta girgiza kai ta buɗe inda tasan tana ajiye abubuwanta msu muhimmanci,ta duba takadunta suna nan yada ta barsu,ɗan kunnen da zobe ma yana nan ta haɗa wuri ɗaya,akwati babban ta haɗa kasan sawanta wanda zai isheta amfani,ƙaramin ta zuba under wears da su hijab har takalma ta haɗa daidai wanda take buƙata kafin ta samu lokaci tazo ta haɗa komi na sayarwa a saya saura ta tura gida.

Har ta gama ta fice sanan taba mai gadi makulli sai dai matsalar abun hawa ga dare nayi kuma kaya sun mata yawa....

Tafiya mai nisa tayi kafin ta samu abun hawa kawai dama ta yanke shawara ba zata taɓa komawa gidan shafiu ba ,tace don Allah ya kaita hotel mai kyau da sauƙi.

Kusa suka isa ta mai godiya ta shiga tare da faɗa masu tana kan hanya ne dare ya mata idan akwai ɗaki mai sauƙi tana so...,list ɗn irin ɗakunan da suke da ya bata tana dubawa wai ƙaramin ɗaki mai sauƙin kuɗi shine dubu goma.

Dubu uku ke hanunta sai na account ɗinta wanda basu haura dubu biyu ba idan ma ta haɗa ta bayar zata tashi ba ko sisi kuma wurin da cikin gari akwai nisa,tana son shiga kasuwa kafin ta shiga makaranta.

Mallam don Allah zan baka wayata ka riƙe har gobe idan na fita zan bada kuɗin saboda na hannu na basu cika ba.
Sama da ƙasa ya kalle taa,hajia bama yin haka a nan gaskiya cash muke amsa sai idan zaki yi transfer yanzu.Kayi hakuri wayata tagi ƙarfin dubu ɗari ma idan kana tunanin zan cuce ka ne har kayana zan bari wanda ko a banza ka sayar zaka samu ninki abunda kuke amsa sosai.

Baki fahimta ba hajia,yanzu duniya ba gaskiya ban sanki baa,bansan inda kika fito ba bani da tabbacin wayar da kayan naki ne domin wasu ma sata suke yi azo neman mafaka saida safe jami'an tsaro su cika mana wuri!,kawai idan baki da hali kiyi hakuri.

Babu irin roƙa da bata yiwa wanan mutum ba yaƙi amincewa tana ji tana gani ta dawo harabar hotel ɗin ta zauna shiru!,Allah yasan ba zata koma wurin yan uwan muhammad baa,bata san kowa cikin gari ba haka makaranta tunda ba hostel take zama ba shi yasa bata shiga tsabgar kowa kullum idan tana da class mijinta zai kaita da kanshi ko ya bata mota ta tafi da an tashi ta dawo gida tana jin kanta a dole ita matar aure ce,yanzu wa yari ya waya?!.

Muryar yaron nan taji a saman kanta,hajia don Allah ki fita daga nan ina ganin mutuncin ki a matsayin ki na musulma ƴar uwata,bana son maki wulaƙanci idan mai wurin ya ganki a nan zan iya rasa aiki na.

Wasu hawaye masu zafi suka taro mata domin data fita daga wurin bata san inda zata nufa baa...,tashi tayi jiki a san yaye ta fice tana waige waige gari yayi shiru saboda har sha ɗaya na dare tayi tsit kake jin wurin ko giftawan komi babu!,a hankali take jan akwatunanta masu nauyitana tafiya bata san inda take zuwa baa,zuciyarta cike da nadama domin ta tabbata da aurenta bai mutu ba a irin wanan lokaci da tana ɗakin mijinta kwace saman babban gado cikin bargo sanyin ac na ratsa taa!

Gajiya da tafiya tayi domin ta iso round about na wani anguwa nan gefen titi wurin wani gidan mai ta samu bakin shago da alama na ɗinki ne akwai tebur a nan ta aje kayanta gefe ta haye saman tebur ɗin ta zauna tana nazari....

Sai da shafi'u ya tabbatar zainab ta bar gidan muhammad sanan ya raka shi ya wuce gida...,koda ya isa ya shiga yiwa mai gadi tambayoyi me ta ɗauka ina yaga ta nufa?,ya bashi amsa iya abunda ya sani sanan ya amshi makullan ya shiga ciki domin ya duba.

Tana zaune saman tebur ɗin sai waige waige take kada wani mugun abu ya faru da ita musamman kayanta kada a ritsata a wurin!,wana dalili yasa ta kasa ko kwantawa ne sai an jima ta duba agogon waya amma taga daren baya gudu.

Muhammad ma ya kasa runtsawa yana tunanin wanan irin taurin kai na zainab yadda ta nuna bata damu dashi baa!,yanzu ma ba wanan ne damuwar shi ba ina ta shige ne da daren nan?

Haka take wurin mayah itama dai ta kasa bacci hankalinta yaƙi kwanciya,hango muhammad da zainab kawai take yi a gida ɗaya suna farantawa juna rai.A takaice su ukun babu wamda ya runtsa ko wanne da damuwar shi har akayi kiran sallar farko a kunnen zainab.

Gidan man ta shiga bayan maza sun gama alwala sun shiga masallaci ta shiga gefen mata ban ɗaki tayi tsarki sanan ta ɗauro alwala ta gabatar da sallah da sauri kafin su fito a ganta a wurin,saboda da dare ƙasan tebur ɗin ta shige babu mai sanin da mutum a wurin.Kwasan kayanta tayi ta cigaba da tafiya a ƙasa har rana ta fito sosai ta fara shiga makaranta sanan ta wuce kasuwa.
Koda ta isa makarantar su bakwai a rabi na safe kuma goma na safe zuwa karfe ɗaya suke da class,tana isa bakin gate ta samu almajirai suka kwashe mata kayan zuwa bakin hostel wanda keda nisa da gate.....,har suka isa ta basu kuɗi su raba sanan ta jingina da itacen dalbejiya tana nazarin ta inda zata fara...,can wata mace wace daga gani ta manyanta ta fito ɗauke da bukiti a hannu jikin riga mara hannu ne da wando mai bin jik nan ta hango zainab dunƙule a wurin.

Sannu ƴar uwa lafiya dai ko sabuwar ɗaliba ce?,wani irin sanyi taji a zuciyarta data samu mai kula taa," yawwa sannu amma ni ba sabuwa bace hasali ma masters nake a faculty of law ina final year ne kasancewa a cikin gari nake zama koda na dawo yanzu gidan da nake sun samu canjin wurin aiki basa garin kuma banda kowa bayan su shine na shigo makarata ko zan samu ɗaki.

Kallon tsaf tayi wa zainab ba laifi tana da kyau a tsari kuma ko daga suturar jikinta zaka gane daga gidan manya ta fito amma dai kuma bata yi zuben budurwa baa...,Allah sarki sannu ai samun hostel ɗin ne da wuya cikin makaranta sai bayan makaranta nima nan apartment ɗiki na yake idan ba laifi kuma mijin ki zai yada mu zauna tare har ki samu naki naga ma dududu bai fi wata uku ya rage ku zana jarabawar ƙarshe ba ko?

Wallahi da kin taimaka mun kuwa saboda ban saba da hayaniyar makaranta baa.(ta kauce wa tambayar data mata ko tana da aure).

Dama na shigo duba wata friend ɗita da bata da lafiya ne cikin hostel shibe zan kai mata ruwan wanka na ciki ya ɗauke amma jira barin zo...,wurin fanfo ta nufa ta cika sanan ta ɗaura wa almajiri ya kai mata ciki tana biye dashi.

Zuwa Ɗan lokaci sai gashi matar ta dawo sanye da abaya saman kayan jikinta ta taimaka wa zainab suka kwashe kayan har wurin wata corola new model da alama nata ne suka zuba kaya a bayan mota sanan taja suka kama hanya....,baki faɗa mun sunan ki ba?,zainab ta bata amsa.Ni kuma Rash(rashida) ina faculty of science shekara ta biyu kenan.Tunda suka kamo hanya aketa kiran wayoyinta har suka iso gidan.

Bayan makaranta jeren gidaje ne masu kyau da tsare gere kamar estate wanda keda gate ɗaya nan ta nufa tayi horn mai gadi ya buɗe har gida na ƙarshe ta aje motar inda wasu motoci biyu suke da yake ko wane gida akwai wurin aje motoci a gefe.

Kayan suka kwasa zuwa barandar gidan ta buɗe ƙofa suka shiga..

_Madaidaicin palo ne mai dauƙe da setin kujeru masu kyau da tsada sai kayan kallo sai kamshi ke tashi,daga gefe ɗakin bacci ne guda biyu da toilet a ciki sai kichen gefe.Yayi kyau tsarin gidan kamar na matar aure._

Karima!....,wata yarinya ta fito wace bata wuce sha huɗu ba har ƙasa ta duƙa sannu da dawo wa aunty,yawwa
karima ya gidan?,ga baƙuwa nan ƴar uwata ce tare zamu zauna sai ki kai kayanta ɗakina a kawo mana abunci idan an gama.


Sannu da zuwa aunty sanan ta kwashi akwatunan zuwa ciki...,zainab sai hankalinta ya kwanta a nata tunani ai matar aure ce.

zube wa suka yi a palo aka kawo masu abinci mai kyau suka ci hankali kwance sai waya ake yiwa rash...,suna gamawa tace ma zainab ta shiga ta watsa ruwa mana kafin lokacin fita.

Nan ta sake tsinkewa da lamarin rash ɗakin ya haɗu sosai komi cif kamar matar aure ta shiga toilet tayi wanka ta shirya abunta cikin shiga mai kyau.

Tana zaune rash ta shigo,har kin shirya?,ni zan fita yanzu akwai komi a cikin gida in case kina buƙata karima tana nan,ga motoci nan zan fia da ɗaya sauran biyu makulli na cikin drawer na mirror ki ɗauka idan zaki fita.

Tau shike nan nagode da kulawa sosai ALLAH bar zumunci.

Tana zaune har rash ta fito wanka ta shirya cikin ƙana nan kaya ta saka madubi baƙi tare da kwasan wayoyinta da aketa faman kira ta fita.


Zainab nata mamakin ikon ALLAH
wanan mata wacce Aƙalla zata kai shekaru talatin da biyar haka,ganin lokaci na tafiya ta ɗauki abunda take so har takaddu da sarƙan da ztasayar ta tsorata da ganin jibga jibgan motocin wanda akwai na kusan million ashirin da a wurin.Makuli ta ɗauka na wata benz baƙa ta fita a tsorace ta hau titi lokacin ta lura ana binta a baya da wasu manyan motoci...



Follow
vote
Comment
share.
[7/6, 14:19] LEEMA: *🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
       *NA*

          *L££MA*

wattapad
*@leemaMuhammad826*

  _Sadaukarwa gare ku_👇🏻

*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*

*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*

*WANAN shafi shine ƙarshen ƘUNGIYAR ASIRI PART 1*

*Masu buƙatar karanta part 2,"cigaban wanan labari" wanda za'a fara posting 30th-7-2020 in shaa ALLAH za su samu akan farashi mai sauƙi*👇🏻

*200 naira MTN recharge card ta wanan number:08164321306*

  *KO*

*transfer 200naira ta wanan account ɗin*
*ACCOUNT DETAILS:sadiya mohammed,access bank:0057431750*

*Sanan a tura screen shot shaidar an biya;08164321306*


*~END OF PART 1~*

*🅿49-50*


    Zainab na kallo ta mirror yadda suke keta motaci da alama ita ɗib dai suke bi!,cikinta ya ɗuri ruwa domin tabbas tasan tana cikin matsala idan har da gaske ita suke bi,wa zai fidda ta?.

Sharara gudu take yi sosai tana ƙara ƙurɗa wa cikin daji domin itama kanta bata san inda take shiga ba,saboda hanyar ya rabu gida uku ne ta miƙe tsaye saboda ba sosai ta iya mota irin haka da zata iya tsere masu baa!.yadda ALLAH ya taimake ta motar nada lafiya sosai kuma sabuwa ce har ta iya bakin wani babban rafi inda ba makara sai an kamata domin bata san inda zata nufa ba sun kawo daf da ita,kashe motar ma tayi gaba ɗaya alamar ta sadakar.

Motaci biyu ne ƙirar jeep prado baƙaƙe suke bayanta nan take suka  fito maza ne masu ji da ƙarfi kusan su shida ne,ko daga ganin yanayin sun sai mutum ya tsorata.Ko wanen su da bindiga a hannu suka nufi motar tare da mata alama ta buɗe.

Babu musu ta buɗe ƙofar motar kanta na ƙasa,hannunta a sam alamar tayi surrender !,wani daga cikin su ya wanka mata mari tare da janyo ta waje  sai data faɗi ya rinƙa janta a cikin yashi har suka isa bakin motar,aka buɗe booth ya jefa ta ciki tare daba sauran umurni su ɗauko motar da take ciki su biyo su...


Kuka take son yi amma yaƙi zuwa,zuciyarta yayi nauyi kamar an ɗaura mata dutse ,kanta ya ɗaure wani irin laifi ta aikata ne da zafi haka aka yi mata wanan horo?,su wanene wanan mutane kuma ina zasu kai ta?

Aƙalla sun yi tafiyar kusan awanni biyu sanan taji alamar tsayuwar mota,aka fito da ita kamar lokacin baya a ƙasa ake janta har cikin babban gida wanda keda bene hawa hawa akayi jefi da ita tsakiyar  palon.

Wani daga cikin su aka nuna,"kai ta ɗakin sama!,gaba yayi tana jan jiki ahankali domin duk ta ƙuƙuje sai jini ke fita...,3rd floor suka hau da ƙyar ta ita duk da akwai lifter saboda tsabar mugunta baa hau baa.

Ɗakin da aka ajeta lafiya lau har gado da akwai,ta waje ya rufe ta ya wuce...,kuka mai cin rai ya kufce mata domin ta rasa dalilin wanan zalinci!,me tayi da zafi haka?,gashi wayarta na cikin motar rash data fito dashi.Tayi kuka sosai taga ba zai fishe ta ba kawai ta haƙura tana roƙon ALLAH ya kuɓtar daita daga sharrin koma wanene.

Rarafawa tayi zuwa toilet dake ɗakin,shima mai kyau tayi fitsari wanda tunda aka yanka mata mari take jin shi amma ta matse saboda tsoro.Shiru shiru bata sake jin motsin kowa ba.

   Tunda safe muhammad  ya shirya zuwa gidan su ya duba iyayen shi...,nan ya ci abinci tare da hajiyar su har rana ta fito yanayi yana duba agogo saboda yana son biyawa makarantar su zainab ya duba ko  a wani hali take ciki kafin y wuce wurin  aiki.

Sallama ya masu sanan ya kama hanyar makarantar har ya isa parking space ya aje mota sanan ya isa faculty su lokacin an fara leacture,sai ya wuce office din wani abokin shi dake aiki a wurin ....,sun gaisa tare da ɗan taɓa hira sanan yace mashi ai matr shi zainab?,yace yanazuwa...

leacture hall ɗin ya nufa suka gaisa da mallamin dake bada darasi ya faɗa mashi wata yake  nema,da yake basu da yawa koda ya duba bata ciki ya dawo ya faɗa mai.

Salama ya mashi ya fita yana tunanin inda ta shige gashi lambarta baya shiga ,ya daɗe  cikin makarantar bai ga kome kama da ita ba haka ya haƙura ya wuce wurin aiki.


Shiru shiru zainab bata sake jin motsin kowa ba har dare ga yunwa tana ji sai ya dameta ,ta shige toilet ta cika cikinta da ruwa sanan ta fito.

akace bacci ɓarawo shine ya sake ta.....,can cikin baccin taji an murje mata ƙafa

Please Login or Register in order to submit comment