Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fada... Kawai sai sukaga feenah ta tashi da gudu ta Shiga daki tana kuka.... Sukabita da kallo suna ikon Allah,

"Maimuna tace Alhaji ka gani ko duk kabi ka shawaba yarinyar nan, ba dama ai mata abu yanzu se tafara kunbura fuska, yanzufa ta girma ba yarinya bace amma tana abu kamar yarinya meye aibu akan makarantar nan haba...

"Adam dai duk tausayinta yakeji dan yasan Ba komai ze sata hakaba se Abun da ya faru tsakaninta da Sags,

kowa yai cirko cirko a tsakar pallown

" Alhajine yaje ya buga mata kofa yana kiran sunanta Akan Ta bude, dakyar ta bude, Yace meya faru tace kantane ke ciwo,

duk haushi yabi ya ishe maimuna tace to shine zaki dinga behaving haka, Wallahi ki shiga hankalinki Nafeesa,

Ta gyada kai Tace Ok mumy,

Dadyne yace kije kisha magani ki huta kinji ko, mumy ta kwasa kayan ta kai mata daki,

Adam ma ya kwasa nashi Ya nufa dakinsa,

mumyne da Abba a Pallow se fada yake mata akan ta dinga bin feenah ahankali, Yarinyace,

maimuna tace bafa yarinya bace kawai ka sangartatane,
"Alhaji yace eh Naji...

Ita ko feenah mumy na ajiye mata kayan ta fita ta tashi tasa key a dakin ta fara kuka tana cewa Na tsana WAYA arayuwata, Ta kara kallon wayan taga Sak irin wanda sags ya siyo mata tace Innalillahi...

tsoro waya ke bata kar yaja mata ta kara aikata abunda tayi a abaya, dan tasan sharrin shaidan ne, kuma waya yaja mata ta fada tarkon mayaudari,
kamar ta fasa wayan kuma seta ajiye tai alwala tai sallah tana kara rokan Allah ya gafarta mata, kuma Allah ya kara hadata da miji nagari, sannnan taci kukanta ta godewa Allah....

ba ita ta fitoba se around 7pm dga daki mumy ta kyalleta ta zo kusa da ita tace feenah wai meke damunki hakane dan Allah, banaso kina kukafa,

'feenah tace mumy bakomai, Sannan maimuna tace ok ga abinci chan jeki kaiwa yayanshi.....

Tana shiga dakin Adam din yace yauwa dama na rasa ta yanda zan ganki muyi magana, emergency.....

Tace ok Gani yaya

Adam, yace feenah farko dai nace miki ki dena damuwa, yanzu me ya saki kuka, nasan komai na rayuwarki fadamun i'm ready to help you, kuma kimun alkawari kome na fada bazakice ah Ah ba...

"feenah tace hmm ya Adam kenan, Inajinka amma kasan wlhi tun abun daya faru tsakanina da sags ne ke damuna,

"Adam yace yeah nasan haka amma idan na baki shawara zaki bi,

tace mezai hana...

Yace ok inasone ki fadawa mumy labarinki na baya, karki boye mata komai ita ta haifeki, kinga ni ba dama na fada mata ni namijine,

Feenah ta kara fashewa da kuka tace i can't ya Adam, da wani ido zan kalleta,

"Adam yace amma kinmun alkawari kome na fada miki zakibi shikkenan tunda abun hakane, ganin ya bata rai ne tace ok Zan sameta in fada mata amma....

yace amma mene tace bakomai, yace yawwa dear,

ki dena damuwa kowa da mukaddirin dake samunsa arayuwa yanzu ba kin tuba ba,

Ta dago kai ta kyalleshi tace haba ya Adam sosai ma na tuba kuma ina kyamar abun...

ganin kar hira yai tsahone yace ok zan tafi masallaci bye... Ta tashi itama ta nufo dakinta
❤❤ *A DALILIN SO*❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

_​​Every one of my fans is so special to me....Much love sosai💋💋_

*_Endless Soyayya to you my Sweet Saaxeey, I so much love and cares_*👄👄👄👄👄👄


© *Ummiey Xeey Abakson*
_+2348164640126_



Page
1⃣3⃣0⃣
Tana shiga time din magrib ne ta nufa toilet tayi alwala sannan tai sallah seda ta tabbatar ta idar da har issha'a tayi addointa Sannan ta tashi,

ta tafi pallow taci abinci bt hankalinta duk yaqi kwanciya dan ta rasa yanda zatai ta bullowa wa mumy da maganar,

"mumy dai se lura da ita takeyi Dan daga gani kasan akwai babban abundake damun feenah,

"Mumy tace kee lafiyanki kuwa,
wai meye hakane kikeyi kamar zararra se kita abu kamar mara lafiya...

"Feenah dai tai karfin hali tace laa mumy rawan sanyi nakeyi sanyi nakeji wallahi,

" mumy tace wuce kisha magani ki kwanta ai kina Sane da abunda kikeyi magani ma se ance kisha....

"Feenah ta tashi jiki duka sanyaye ta shiga daki tace uhm ni ba maganin da zansha lafiyata qalau.....


"Chan ta hango wayanta akan gado tace laaa ni Nama manta da wayan Wallahi taje ta dauka wayan ta kalla wayan ta kara kallon wayan, wata xuciyan tace mezaki da wayan kuma, wata xuciyan kuma tace mata Ki nema maryam kawarki mana tana chan tana missing dinki kuma kin mata alkawarin zaki kirata,

"Haka ko akai tana dubawa taga wayan da chaji full Har sim Dadynta ya siyama mata, batai wani wahala ba tunda dama already ta iya wayan..

" Ta dakko Wani memon data kwafe numbers din frnds dinta na school, ta fara saving,

Tana zuwa kan na sags ne tai wani irin tsaki tace aikin banza. Na tsaneka na tsakake, Allah ya kara mana tsari da irinku...

ta samo biro tai cancel dinshi, seda ta gama saving din numbers din duka hardana ya Adam, Sannan ta fara kiran Adam tace Ya Adam this is my new number...yace inyee manya har wani special number dady ya siyo miki tace yeah... Adam yace koda yake kema special din ce feenah ta kyalkyale da dariya sannan ta kashe wayan,


"ta kashe wayan ta kira maryam kawarta....

Tanata kira ba a daukaba se daga baya maryam din tai calling back.... Bugu daya feenah ta dauka
maryam tace "Hello
"feenah tace you better open ur mouth ba saurayinki bane....

maryam tace hahaha wa nakeji kamar feenah"

"feenah tace itace mana this my new number, hope kowa ya nanan lfiya...ya bayan rabuwa,
"mAryam tace Alhmdlh, inata missing dinki swt frnd,
"feenah tace ba wani ai zangani yanzu inda gske kike kina missing dina,

nan dai suka dan taba hiransu na kawaye. Sukai Sallama, sannan feenah ta fara kiran imfortant frnds dinta na school,

""maryam kuma suna gama waya taje ta sama Sags yayanta ta ce mai yanzu feenah ta kirata,

"Sags ya gwale ido yace feenah nah,
Nidai nace ba nakaba...
"maryam tace yes itafa nafeesanka....

Sags yace amma da gske kike, ba ance tayi aureba....

"Maryam tace huh ni dai she never told me, bandai saniba gaskiya cos this our 1st time da mukai magana da ita buh i'll ask her naji,....

sags yace ok thanks my little Sister, let me have her number.... Tace ok...

Dan tasan yanda yayanta ke mugun son Feenah, ya natsu gaskiya sai yasa ta bashi......

Itako feenah suna gama waya da friends dinta ta kashe wayanta tai bacci dan Gobe mumy tace zasuje unguwa ya kamata taje ta dinga gaishe da yan uwa....

Sags na gama amsan numbern feenah, ya kira frnd dinshi yace Ka tayani murna Na Samo numbernta...,.

frnd dinshi yace huh..congarts amma dai ina mai baka shawara daka rabu da ita,

Sags seda yaji haushi yace enemy of progress,,

ya nufa daki ya kwanta sannan yace lemme call her naji muryanta ko tare da mijinta take i don't care..

Sags ne Kwance gado se dialing numbern feenah yakeyi bt akashe, yanata kira har 1am nadare ko zata bude bt still akashe... Yana ganin haka Ne yace to bari ya fara mata text... Sags ya zauna ya fara tsara text kamar haka....

```What I really want to say is that I'm *sorry, I know
that you didn't deserve to be hurt like that, and I
know that you will find someone who will love
you and treat you right, they will make you happy
and that person won't hurt you like I did_|```
Sannan yayi sending...
Se dubawa yakeyi ko zaiga yyi delivery amma shuru haka har bacci ya kwasheshi tun asuba Sags se dubawa yakeyi ko yayi still shima Shuruuuuuuuuuuuuuuuuuuuu!
❤❤ *A DALILIN SO*❤❤

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

```There is no better friend than A sister, and there is no better sister than you ```

*_Really loves you by blood.. HASSANA SMASHER_*💞💞💞

❣❣❣❣❣❣❣❣❣


© *Ummiey Xeey Abakson*



Page
1⃣3⃣1⃣
Shuru shuru har gari ya waye wayan feenah akashe gashi message bai tafiba....

Da sauri ya kira kanwarshi maryam yace lemme have your phone kodai kin bani numbern ba daidai bane....

"Tace wallahi daidai ne wayan na daki "sags yace shiiiiiiii just go an bring your phone...

Ta tashi ta nufa dakin tace mtsww bayan ka cuceta kuma zaka wani dama mutane da na baka numbern, dama nasani ban fada maba balle ka dameni, da banso ka kiratataba zan Ma fada mane,...

ta shiga room dinta se zuburo baki takeyi ta dakko wayanta ta fito ta kawo mai.....

"Sags ya amsa yai checking numbern yaga iri daya yace ohh...sannan ya mika mata wayan tabar dakin...

"Ita ko feenah ba ita ta tashiba se 8am bayan sallan asuba da tayi ta koma bacci, koda ta tashi batabi takan wayantaba tunda tasan ba wani saurayi garetaba da zai bukaci jin muryanta tun da asuba sai yasa ta manta da yawan....

"tana tashi Tai wanka taje ta gaishe da iyayanta sannan ta zauna sukai having breakfast dan tasan ya adam ya tafi company dinsu sai yasa bata ma wani je room dinshiba...

Sungama ta tattara komai mumy tace taje ta shirya da wuri dan su Dawo da wuri...tace ok mumy....

"Feenah ta shiga daki tai kwalliya ta dakko wani black jallabiya me ratsin red and yellow tasa ta dakko black vail din kayan ta dan yafa akanta, simple make up tayi amma ta hadu ba laifi...

Ta jira mumy itama tazo ta shirya sannan mumy tace muje amma mu fara zuwa gidan su Samira sabd baki taba zuwaba anya feenah kinada zumunci kuwa, gaban feenah taji yayi wani mugun fadi bt she can't say ga abun da yasa gabanta ya fadi, tace uhm mumy kunyar anty samira nakeji wallahi da mun wuce kawai.....

" Maimuna tace baki da kirki feenah,

"feenah dai ba yanda zatai ne dan gabanta wani irin fadi yakeyi tace Ok mumy mu shiga gidan to,,

mumy tace ko keefaa, sannan suka kulle ko ina Mumy ta dakko Car dinta suka shiga sannan suka bar gidan..... Mumy ne ke Tafiya ahankali dan gidan Samira ba nisa, mumy ta sama waje tai parking a waje sannan Suka shiga....



*SAGS* shuru shuru har 10am feenah bata bude wayaba, ya sake tura mata text kamar haka... Still bai tafiyaba nan yaji wani sanyi na shiganshi zazzabiya rufeshi yana cewa *_Feenah plz switch on your phone...i'm missing you, I love you please dont let me die ban sake ganinkiba_*,....

Su Maimuna Suna Shiga gidan Zayyad yazo da sauri yana oyoyo anty Oyoyo Anty, FEENAH ta kama mai hannu sannan suka shiga pallow Anty samira na ganinsu Tace ah ku shugo ciki mana kwa tsaya a fallow kamar Baki,


"ita ko zainab tana ganin feenah ta fara mata tsiya wai yau wace Rana, feenah tazo gidan anya ba ruwa da kankara za ai ba, suka dai shiga sunata hiransu,

Nan ma anty samira se mata tsiya takeyi wai Gimbiya yau anfito,

maimuna tace atoh ki mata fada batason Zumunci wallahi, Anty samira tace ah ah ku kyaleta ko yata ai wata rana zakiyi duk cikin hutune rashin fita, dukansu suka kwashe da dariya.....


Suka dan taba hira kadan suka sha drinks ba da yawaba sannan Sukace zasu tafi dan yau ziyara zasui sosai dan by monday zata fara zuwa school kinsan an mata rejistration idan ba munje yanzuba bazata dinga samun time ba kuma yan'uwa kowa nason ganinta, har kira akeyi ana ce mana mun rike yarinya bazamu koya mata zumunciba..

"Samira tace GOOd JoB ai gwanda a koya mata, kuma Allah ya bada sa'a feenah zainab ma bataci Jamb bane da yanzu tare akai musu rejistaration, ki maida hankali sosai kinsan me yakaiki,

FEENAH TACE insha Allah anty; Thanks Alots.......

Sukace zasu tafi "Su samira suka rakasu har bakin gate tunda dama a waje sukai parking motan sannan suka koma gida su samira,

Ita kuma mumy ta shiga mota, feenah ta tsaya gyara gyalenta adaidai lokacin da *NASEER* yake kokarin shiga gidan ganin Car ne akofar gidansu Ya dago kai ya duba su waye.... Kwallonta da yayine gabanshine yaji yai wani mummunan Fadi, yace subhanallah,

Ya sake kyallonta Ya kara cewa subhanallah, "Feenah ta shiga motan, suka tafi dan duk basusan Naseer na kallansuba tunda basu luraba... Shi dai ya tsaya seda yaga motar tabar kofan gidan sannan ya shiga gida...

Koda ya shiga gidan ba wanda yasan ya shiga ya wuce dakinshi Gabanshi still se dukan uku uku yakeyi, ya rasa me ke mai dadi sannan ya dakko Qur'ani ya karanta, bayan ya gamane ya fara hasubunallahu wani'imal wakeel, yana yine bacci ya kwasheshi,

Su maimuna suna tafiyane Tanama yarta fada sosai akan ta ci gaba da kame kanta, sun isa gidan anty larai, Data gansu taji dadi sosai sannan tai musu fatan alheri, tace tana taso tazo wlhi kwana biyu ciwon kafa ya sata gaba...amma Tananan zuwa, Sukace ba komai sannan sukai biye biyan da zasui Suka koma gida.......

*Naseer* kuma tun 1 ya tashi yai alwala yai azahar bt still ko abinci ya kasa ci dan gabanshi fadi yake sosai..........!
❤❤ *A DALILIN SO*​❤❤

❣❣❣❣❣❣❣❣❣
```My Condelence greetings```

*INA MIKA TA AZIYYATA GA Familyn Late Alhaji Muhammad jajare A bisa rashin Dan Uwa da mukai HAMZA MUHAMMAD JAJARE, ALLAH YAJIKANKA DA RAHAMA ALLAH YAKAI HASKE KABARINKA* *ameen*


*Nanma Ina kara mika gaisuwan ta'aziyya ga Dan AlHAJI DANLAMI ME BREAD Ung rimi a bisa rashi da da sukai... Allah Ubangiji yajikan musulmai baki daya AMEEN*😭


® *HIKIMA WRITER'S ASSOCIATION*

❣❣❣❣❣❣❣❣❣


© *​Ummiey Xeey Abakson​*



Page
1⃣3⃣2⃣
Naseer Ne gabanshi nata fadi Ya rasa me zaiyi gashi zaman gidan ya isheshi.

Shine ya tashi ya nufa wajen friend dinshi, Yake cemai gabanshi fadi yake tayi ya rasa meke damunshi Still dai yace yai ta addua......

*Sags* kuma Zazzabine me zafi ya kamashi Se rawar sanyi yakeyi, Seda Maryam tazo kawo mai abinci taganshi ba shiri tai maza taje ta kira mamansu aka kira doctor yazo ya dubashi harda karin ruwa, Doctorn daya gwadashi Ba karamin tsorata yayiba da yaga BP dinshi yahau,

Doctor Yace please ai Meke saka tinanin haka koma meye u should take it easy, Bp dinka yahau sosai, Sags beyi mamakiba dan yasan abunda yafi hakama sai yaji,

bayan doctorn ya fitane ya lalaubo wayanshi ya duba still dai text be tafiba..... Gabanshi yace *Gam*....

Nan Sags ya fara Ayyanawa a zuciyanshi cewa Shikkenan Adam yaya riga ya aureta,

nan hawaye masu zafi ya zubo mai a fuska.... Wata zuciya kuma tace duk halin da ka tsinta kanka kaine sanadin... *ADALILIN* yarda da yarinya tai da kai ka cuceta ka bata mata rayuwa, Ya gama hawayenshi ya share yana mai rokon Allah yakara nuna mai feenah koda a mafarkine,


*B*angaren feenah kuwa suna komawa gidaN ta samu ta shiga toilet tai refresh up sannan ta zo taci abinci....

Nan Adam ya dawo yanata mata tsiya yana cewa Kaga Special ashe kuna fita unguwa, ai na aza ku manya bakwa zuwa ko Ina...

'feenah ta marairaice fuska taca hardakai ko Ya Adam,

mumy ne ta sako baki a maganarsu tace kaima ka fada, Tun tuni ba yanda Banyi da ita ba akan ta dinga zuwa ziyara, Zumunci nada dadi....

"Adam yace gaskiyane ai yanzu tunda Ta Gane se ta dinga Zuwa, Mumy tace aikuwa dai, intaga dama ba....

"Feenah tace hmm, zan dinga zuwama mumy,

mumy Tace Allah Yasa....

Jin horn din mota ne yasa mumy ta tashi ta je ta hadawa mijinta ruwa a toilet, kafin ya shugo ciki,

Tabar Adam da Feenah se hira sukeyi har yana tsokananta yana ce mata New Student,
tace uhm kai kaji dadi ka gama dama nine....

Yace dont Worry with time kema zaki gama....

" dad ya shugo da sallama sukai mai Sannu da zuwa ya amsa, Yanajin dadin yanda yaga yaran sunayi akwai girmamawa, Shi dai Dad kawai Son Adam yakeyi dan yasan ta *DALILIN* sa ne Feenah ta koya dan ya tabbata da ahannunsa take baice bazatai biyayyaba... Amma ko zatai se an mata da gaske saboda tun tana karama suka sangartata,

Dad ne yace ina mumynku sukace tana daki Shine dad ya wuce dakin......... Yana shiga ya tarar da matarshi tai kwalliya tayi poster a bakin gado yasan yau akwai Harka, Tamai sannu da zuwa tacemai ga ruwan wanka chan abayi yaje yayi

"Alhaji umar yace Ok MY MADAM nan dai na barsu na dawo gun su Feenah, Suna hiransune, Dad suka fito suka samesu suna kallon Wani film a MBC2,

dad dai ya kara kallonsu yaga sun birgeshi....

Adam ne ya Kalla DAD YACE dan Allah daddy gobe insha Allah inaso naje zariya wajen su Baba.... Alhaji yace yauwa Wlhi abun da nakeso nacema kenan yaushe zakuje zariya da feenah ku gaidasu...

Mumy ma tace ai nima Zani hardani, Dad Yace Masha Allah tunda gobe weekend Ba aiki sai muje gaba daya muje mu gaishesu, gaba dayansu sukaji dadi banda feenah dan ta tsana garin ita... Tace axuciyanta wallahi dan kar suce bana bin umarninsune da banjeba..... Suka gama hira Kowa ya tafi makwancinsa..

Adam na shiga Daki dama shi ba bacci yayiba. Dan kudin da yake samu yake boyewa ya tattara waje daya ya sama jakan laptop dinshi ya saka,

Feenah ita kuma tana shiga dakinta ta fada Gado...chan ta tinafa tanada waya...
Shine ta dakko ta kunna sannan kuma ta ajiye....taji alamun text ya shugo bata ma ko damuba dan tasan in banda MTN bawanda zai aiko mata dashi sai yasa ko damuwa bataiba.....

"Sags kuma yana ganin messages ya tafi yaso ya kirata amma ina jikinshi yayi tsanani sosai bazai iya kiraba....
Dan haka dole ya hakura yaci gaba da kwanciyarshi har bacci ya kamashi......















*Ummiey Xeey Abakson*
❤❤ *A DALILIN SO*​❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

*​it's okay to be different​*

_​Much love bby girl ko a mata ke dabance_​ ​
*ZAINAB SHIGA​*💋👄😍


® *HIKAMA WRITER'S ASSOCIATION✍🏼*


© *​Ummiey Xeey Abakson​*


Page
1⃣3⃣3⃣
Washe gari nayi iyalan Alhaji umar da adam suka kama hanyar zariya... Basu tafiya me nisaba suka tsaya a wani babban shago sukai musu siyayyan kayan abinci, su shinkafa,wake taliya, su drinks Etc....

Sannan suka koma cikin motan, suna tafe suna hira basui 2hrs ba suka isa zariya....

Sun isa lafiya Jummai taga ana shugo da kaya nike nike tana dubawa taga ashe su Alhaji Umar ne,
nan ta kira Malan Sani duk aka kama duka aka shugo dasu.......

Nan sukai musu bangajiya ya hanya, sukai godiya sosai sannan aka fara hiran yan uwa abun gwanin sha'awa,

Misalin karfe 2 na rana ne Alhaji Umar yace yau zai koma su zai gobe Sunzo su gaishesu.....

Sukace bakomai suka karamai godiya akan kokarin da yakeyi akansu sosai,

Alhaji Umar yace bakomai ai sun chanchanci hakanne, Nan sukai sallama ya kama hanya,

"Shima malan sani ya fita wajen Da yake zama yake basu labarin dan uwanshi baban wannan yarinyar yazo, sukace ya kyauta...
"Adam shima yace bari yaje ya gaishe da abokanshi da aka kwana biyu ba a haduba.

Nan dai maimuna ta gane feenah bata cikin walwala take tanbayanta ko lafiya, Me ya faru kuma, Feenah dai tace bakomai,

sannan jummai itama ta lura da yanayin feenan take tambayanta ko wani abune ne, nan ma tace bakomai......

Maimuna ta kalla jummai tace wai dan Allah haka take ko da take zaune Anan kullun cikin daure fuska...

"Jummai tace eh to kinsan yau da gobe sE Allah....

Maimuna tace eh hakane amma like da wani abu..
"seda gaban feenah ya fadi..

Suna ta dan hiransu akan ba karamin hakuri maimuna tayiba, Tace hmm Ya zanyi to, yanzu ba gashi Allah ya kawo karshen abun ba...

" Jummai tace hakane kuma..

Sannan maimuna tace bari taje tai fitsari,

tana fita jummai ta matso kusa da feenah tace wai yayane ta ko fada mata abunda ya faru tsakaninsu da sagir...

"Feenah kaman zatai kuka tace whi umma tsoro nakeji dan ta tabamun maganan akan nai hankali da maza mayaudarane....

"Umma jummai tace eh amma ya kamata kisani mahaifiyarkice gwanda tun wuri a fada mata dan komun mun boye wata rana zai fito,

"feenah tace eh hakane zanyi kokari na sanar da ita....

"Suna cikin maganan ne sega Maimuna ta shugo tace maganar me akeyine...

"Umma Tace fada nake mata akan ta dena wannan bata rai haka, be mata kyau,

Maimuna tace hmmm Ina yake mata kyau kuwam, ni na rasa irin wannan halin nata, Dani da babanta duk ba haka mukeba,

jummai tace aikuwa, Sannan suka tashi sukai sallan la'asar suna idarwane Feenah ta dakko wayanta ta nunuwa umma tace abbanta ya sai mata, Umma tace masha Allah yar gidan abba, Yayi kyau

feenah tai smiling tace tagode

chan sai sukaji feenah shuru ba un ba um um....

"Shine Umma ke tambayanta bazata kira kawartataba tazo sui hira ko andena kawance ne,

Sannan maimuna ta bude baki tace kema dai kya fada, wlhi yarinyar nan bata da zumunci kullun sena mata fada akan ta dinga zuwa ziyara na yan uwa da abokan arziki amma ina, Wai jummai dama haka take tuntunci

"Jummai tace ah ah kinsan bata cika son haya niya bane, kuma dama chan bata fita sosai, maimuna tace Allah ya kyauta to

**********************

Feenah ta mike ta shiga dakin yayanta Adam, ta kira kawarta maryam... Bugu daya maryam ta dauka

feenah tace guess what...

"Maryam tace aa just fadamun....

Feenah tace gani a zariya
"wani ihu maryam ta saka ta daka tsalle tace da gske kike

Feenah tace wallahi ina gidan mu,

"maryam tace just give me 5mins ganinan zuwa,

feenah tace ok, Sannan ta koma daki take cewa ai ga maryam din nan zuwa,

"maimuna tace aww sannu yar mulki ke kinzo bazakije ki gaisheta sedai ita tazo ko, wato ita keson ganinki bakeba, feenah dai tace Ah ah mumy,

ita jummai tasan *DALILIN* yin haka sai yasa bata damuba dan tasan komai....

"Suna zaune ne sega maryam ta shugo tazo ta gaishesu cikin ladabi da biyayya suka amsa sannan feenah tace tashi mu shiga dakina.... LOLs Umma nan ta tsokanusu tace kawaye yau za ai hiran da ba ayiba kwana biyu kenan.....

Maimuna tace hka suke ba mazan ba ba matan ba....

Jummai tace sai yasa Adam na zuwa ko zama be yiba, sukai dariya dukansu sudai sukaci gaba da hiransu










*Taku A kullum*


*Ummiey Xeey Abakson*
❤❤❤❤
❤❤ ​A DALILIN SO​​❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

*I ​​​​Dedicated this page to Maman Eeemaan😍 Thanks for the Love*💞💞


® *HIKIMA WRITER'S ASSOCIATION*✍🏼


© *​​​​Ummiey Xeey Abakson​​​​*



Page
1⃣3⃣4⃣
Feenah ne da maryam suka shiga cikin daki, Maryam ta kyalla feenah tace wow.. Kinga yanda kika koma kuwa, Kamar ba yar Naijaba....

Feenah takai mata duka tace frnd banason Iskancifa, ke kinga yanda kikayini, suka kwashe da dariya dukansu...

"Maryam tace swt frnd wlhi i missed you Alots....
Feenah tace me too. Ya labari,

maryam tace labari na wajenku ai inasha an miki aurene da Adam..

" Feenah ta zaro ido tace Huh... Wlhi ko soyayya bamayi balle ai wani aure, ni da school ma zan koma, an mun rejistration a KASU,

"maryam tace ​congrats​ babban yarinya, amma are you serious ba soyayya kuke da Adam ba naga ya koma kd gaba dayane har yaya sags nacewa kunyi aure

"Feenah tace

Please Login or Register in order to submit comment