Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

harda su wani irin gashi a dunkule, dasu allurai da sauransu,

BASU Wani tsaya bata lokaciba se suka hau motan Anty larai suka tafi inda rabee tace musu zata kaisu a karya asirin, basui tafiya me nisaba suka isa....

"suna zuwa sukai Sa'a ba kowa a wajen, nan sukai mai bayanin abunda ya faru, yace wacece a cikinsu aka nuna maimuna,

"yace su hada ido taqi kallonshi, Yace Akwai aljanune ajikinta sai yasa take tsoranshi,

Amma zai mata rukayya yanzu a asamu sui magana, in yaso maganin sai a konasu daga Baya,

Nan take Malan Ya fara mata rukiyya, yana tufa mata, sukaqi magana,, Still dai addua yake mata chan dai sukai magana waiπŸ‘ΉπŸ‘Ή *ammmm aehhhmm eeehmmwoo* Kadena kunamu,, Zamui magana turomu Akai,

" Malan yace bazan denaba se kunmun alkawari zaku fita, Sukace to zamu fita amma ai turomu akai,

idan mun fita ina zamu koma, Malan yace ku kuma jikin wacce ta turoku, Toofaa, malan dai yaci gaba da addua sai Bayan minti Kadan

Saiga maimuna garau ta fara magana, *IKON ALLAH​* se kuka da shima malan albarka suke tayi, Anty larai da samira se kukan murna sukeyi abun yazo musu basui tsammaniba, Nan dai suka ba malan sadaka, Sannan ya basu wasu tilare da magunguna wasu tadinga wanka dashi, tilaren kuma a hada a hayaki ana mata,

"Sukai mai godiya yace kar ku damu, munsha samun cases haka da wanda ya fishi, Da izinin Allah mutun na warkewa, ba komai....sukai Sallama se gidan Anty larai suka koma..**********************

*Bangaren Alhaji* Umar kuma yana shago yaji kaman wani abu ya fitar mai a kwakwalwarshi, nan take ya mike tsaye yana tambayar kanshi ina Beloved wife dita, Ina Yarinyata, Ina yayana malan SanI, Ganin bame amsa mai ne ya kulle shago Ko gida be jeba ya wuce Zaria gidan dan uwanshi Mal Sani..........!


*Ummiey Xeey Abakson*
❀❀ *A DALILIN SON*❀❀

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

_There is nothing on this earth more to be prized than TRUE FRIENDSHIP_


*_I DEDICATED THIS PAGE TO MY BEST PALS MARYAM ABDULLAHI AND AMINA M AUWAL...ONE LOVE_*

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

Β© *Ummiey Xeey Abakson*
08164640126


Page
1⃣2⃣0⃣
Yana hanya se ji yakeyi Kamar ya rufe ido ya ganshi gidan Yayanshi Mal Sani,

yana tafiya cikin gudu Befi 2hours ba se gashi a gidan, yaga komai na duniyan ya chanza mai kamar a mafarki, yaji gabanshi se matsanancin fadi yakeyi......

"Yai sauri ya shiga gidan, A zaurene ya hadu da wata yar mata shiyar yarinya, ya kyalleta yace ke Mal Sani nanan, suna hada ido dukan su gabansune ya fadi *GHAMM*

"tace eh tai wucewarta,

"shiko Alhaji umar a xuciyanshi yana cewa Ikon Allah kamar maimunah Sak, kawai yasa kanshi se cikin gidan,

a tsakar gida ya tarar da umma da Mal Sani jin muryan wanda yai sallamane ya dawo da idonsu inda sukaji sallaman, Aiko wazasu Gani Se *ALHAJI UMAR*, ba shiri suka mike, Alhj umar yazo kusa da yayanshi ya rungumeshi yace dan uwa kaimun aikin gafara,

"Mal Sani Yace Haba Umar, ya zakai mana haka dama haka aure yake, _sai yasa da yawa mu maza muke jawowa kanmu abundayafi karfinmu, idan muna zaune da matanmu bazamui hakuriba, sai munje mun dakkowa kanmu abunda yafi karfin mu sannan zamui hankali haba, Mtswwww, ya kamata ku wani namiji yasan wazai aura, daga ina take ya halinta yake, Idan ma bazawarace sai mu nema babban dalilin da yasa ta fito bawai da munga mace ba muce munaso_ *NASIHACE*

_sannan muma mata please we should be a Good Woman to our husband, Sannan mu zama uwa ta gari ga yayayanmu, akwai masu mugun hali cikin mu to plz dan Allah mu rage, rayuwan guda nawane, Idan har ka kuntatama wani baka tinanin da kaine ya zakayi haba sisters....mace fa yar uwan muce ba wani abu daban ba, Ballema kishiya da idan kika dauketa yar uwa ba karamin dadi zakujiba, kuma sannan hadin kanku, mijinku zan sama kwanciyar hankali, Allah zai kara budemai sosai wallahi, Allah dai yasa mu dace mufi karfin xukatan mu AmIN_

"Alhaji umar yace Nasan ban kyautaba, walhi maganarka gaskiya, Se ayanzu na gane,ku gafarceni dai please ina maimunah da yata feenah suke yanzu, su nakeson Gani,

"Jummai ta kalla mijinta mal Sani suka hada ido tace wata sabuwa

"mal sani yace magace mai tsaho gaskiya dan ba nan ya kamata ayitaba, Sedai muje chan gidan mamanta larai ayi maganar, amma feenah nanan Jin maganganun da akeyine kamar daga sama yaba *Adam* damar fitowa dan ya gasgatawa kunnanshi abun da yakeji, Ana hakane sega Feenah ta dawo da aiken da Umma tai mata, Alhaji umar ya kai idonshi kan nafeesa yace badai kece Yata ba kika girma Haka, Nan taji gabanta ya fadi taji Baba Sani na cewa Itace Alhaji, da gudu feenah ta shige daki ta kulle ta fara kuka,

"Tana cewa Why did you do this to me daddy, ka jefani da mumyna cikin wahala, Nan dai gida kowa ya fara kuka, se yan kuke kuke akeyi don a gskiya Mal umar be kyautaba,

"Dakyar dai Alh umar yaje gaban dakin da feenah ta kulle ya tsugunna yana cewa open d door plz..i'm your father, yanzu na dawo gareku kiyi hakuri,

" feenah najin haka ta bude Se kuke koke dai akeyi kowa abun yazomai kamar a mafarki, dakyar dai mal Sani yace to Alhamdulillah, Yanzu kuka ya kare tunda ka zo da kafarka, Munawa Allah godiya, Aka dan ba uba da ya waje suka dan yi maganganunsu.....

"Mal Sani kuma beyi kasa a gwiwaba ya kira anty maimuna dan ya sanar da ita ga Alhj umar yazo,

"Aiko maimuna najin haka tace Alhamdulillah, Dama abunda nakeson ji kenan,

Mal sani yace be ganeba
Tace eh Dama bazaka ganeba,
Mal sani yai dariya yace masha Allah munanan zuwa gobe dan Ya damu yazo yaga maimuna, Dan ba karamin laifi yayiba, Anty larai tace Allah ya kaimu gobe,

Nan dai suna gama waya Anty Larai ta kira Samira akan Alhaji Ya dawo hayyacinsa har yana neman Maimuna,

Samira taji dadi sosai Tace Sai sanine wallahi.......

"Su malan sani dai haka suka kwana suna hiran abubuwan da ya faru shekara da shekaru da dan uwansa Umar........



❀❀ *A DALILIN SO*❀❀

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

_If two heartsπŸ’ž are meant to be together, No matter how long it takes, how far they go, how tough it seems, fate will bring them together to share their LOVE FOREVER_

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

Β© *Ummiey Xeey Abakson*


Page
1⃣2⃣1⃣
Washe Gari nayi Samira tun safe tazo gidan Anty larai aka gyara ko ina akai wa manyan baki abinci,

" Samira tace Ikon Allah anty, Lallai duk wanda ya dage da addua zai ci riba sosai, Kuma mahakurci mawadaci,

Anty larai tace sosai Ma samira, nifa ganin abun nakeyi kamar a mafarki, nan dai sukaci hiransu

" *Misalin karfe 8am*
su FEENAH, adam, Umma, Mal sani da Alhaji Umar suka taho kaduna, Basu ddeba Wajen 10:30 ne motar Alhaji umar ne a bakin gate din Gidan Anty larai, ya gane gidan sosai, Yayi horn aka bude ya sama wajen parking yayi,

"akai musu iso se babban polloWn Anty Larai.

"Jin motsin bakine yasa Anty larai tace ina maimuna, Wallahi karki kuskura naga kafarki a fallown nan duk da nasan kinason mijinki, bazaki kuma gidanshiba,

'maimuna tasa kanta cikin pillow tanata kuka mara kara

"Su Umar suna shugowa suka samu waje suka zauna sannan aka gaggaisa, Samira da Anty larai suka kawo musu ruwa, aka dan huta sannan anty larai tace Nafeesa keda ADAM KU dan shiga nan gidan kuje ku gaishe da matar gidan kawatace, zamui magana kunga ba maganar yara bane, sukace Toh,

"suka tashi suka fita Adam nadan mata nasiha Akan ta kara hakuri, Duk tsanani yana tare da sauki, Ba gshiba yanzu mahaifinta yazo ganin mamanta, tace eh hakane nagode suka shiga gidan,

" Anty Larai dai tace to Madallah, ina jinku mal sani dame kukaso,
Seda gaban Alhj Umar ya fadi dan yasan waye Larai,

"nan dai sukace sunzo bada hakurine game da abun da ya faru, ayi hakuri bayin kansa bane,

"Anty larai ta nunfasa tace ai hakuri ya kare kuma, meye gamun Kare da doki, tunda ya zaba matar shi akanta meye a ciki kuma, Nan har mahaifiyarta ta rasu ko yaje, haka ake rayuwa, anty larai ta inda ta shiga batanan take fitaba fada tayi sosai

"Nan dai ana tabada hakuri tace ita sam bazata hakuraba
"sabd tasha zuwa gidan har mai magana takeyi akan ya dinga adalci amma yaqi, sai yaje chan ya kama matarshi suci gaba da rayuwa,

"Nafee kuma zata dawo hannunsu tunda yanzu ya gane ya dawo hankalinsa, Dama chan abunda yasa basu riketaba sabd wulaqancin da yaiwa maimunane, nan dai aka ci gaba da bata hakuri,

"abun har ya ba su Mal Sani haushi, Gida ya kachame da fada, Se koke koke akeyi,

Ganin maimuna shuru ne yasa Alhaji umar yankan jiki ya fadi yace kodai ta mutune ko fadamun, tun dazu bangantaba,

jin salatine yasa maimuna ta fito da gudu tazo wajenshi, Aiko Kowa se kallo ya koma kansu, Tana jijjigashi tana cewa ban mutuba Ganinan ka tashi kar ka mutu dan Allah.....LOLz,

yanajin haka ya mike,

Anty larai kuwa taga haka ba karamin tausayawa maimuna tayiba, lalle tayi kokari a yan shekarun nan, Haka aka basu waje dan MATA DA MIJI SAI ALLAH.

Suka dan yi hira kadan, Sannan aka fito aka sasanta magana, Wai maimuna zata dawo gidan mijinta,

kowa yai murna sosai, amma anty larai tace abari nan da sati biyu haka, Mal Sani dai ya roka arziki aka barshi nan Da 1 week,

"su feenah suka dawo dan yamma tayi tanajin labarin zata koma gidan mamanta dadi duk yabi ya isheta, tace ita ai kawai abarta gidan Anty larai,

"Samirane taja feenah daki tace ba haka akeyiba, idan kinyi hakuri sati mai zuwa kina tare da iyayanki, kinga su suka rikeki har kika girma, tace hakane,

"Aka daidaita komai akan next week za adawo da maimuna dama saki 1 ne, sukai sallama suka Kama hanya zuwa zariya,

Adam kuwa tun da yaji feenah zata koma yace shikkenan, Nasan ba rabo na bane, na hakura kawai tausayin kanshi ya kamashi, bt be nunawa kowaba.

*bangaren beeBAH zama da kishiya sai dole* se up an down takeyi a gida, Shuru ba alhaji ba labarinshi, an kwana an tashi amma ko ta kira wayanshi be shiga, ta shiga damuwa sosai, Tace to ina Alhaji yaje, har shagonshi taje taga akulle, ta daga waya ta kira wata kawarta akan fa bataga alhajiba, Tace to meye tunda be dawoba ina ruwanki, Kici kudi kawai....... Kafin ya dawo kisan me kika samu,

Su Umar kuma tun ahanya yaketa wa jummaaaaai Godiya yace yace washe gari zai koma gida

Haka suka isa zariya lafiya kowa se mamakin abun yake lokaci daya komai ya dawo normal




Kuci gaba da kasancewa Dani
❀❀ *A DALILIN SO*❀❀

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

_Some make us cry on the things that we have never done While some others ignored all our Fault Just to see our sweet SMILE_ *It's care*

❣❣❣❣❣❣❣❣❣
_Wannan page din nasadaukar dashine Akan Rashin Dan Uwa da mukayi *NASEER ADAM* JIkan Alhaji Ibrahim mai kalanzir Kawo.... Allah ya jikanka Naseer... We missed you_

Β© *Ummiey Xeey Abakson*

Page
1⃣2⃣2⃣
Bayan sun isane, around 8 na dare Alhaji umar yake sanar da yayanshi akan cewa gobe zai koma yaje ya kara shirye shirye duk sauran bayani zasuyi a waya

"Mal sani yace masha Allah dan Allah ka karabi a hankali, azkhar dinnan da yawon ambaton Allah kar ka manta, idan bamayi shine abubuwa zaita faruwa damu dan Allah.

Alhaji yace insha Allah, Nan ya kira nafeesa, suka dai kara bata hakuri akan abun nan da ya faru ba yin kanshi bane Asirine da har ya manta dasu,

feenah tace bakomai Allah ya kara tsaremu duka sukace ameen.

"" Washe gari nayi Alh umar ya dawo kaduna gidan matarshi Beebah,
yana shiga ko kallon arziki be mata ba, tadai gaisheshi ya amsa, ya shiga daki ya dakko wasu kudade, ya kara fita,

"Nan hankalin beebah yatashi tace alhaji kuwa lafiya..... Nan dai ta tsaya sokoko da ita,

Shiko alh umar na fita ya kira wani amininshi wanda yake yawan mai fada akan ya duba hali da Ya jefa maimuna,se umar yai burus,
sai yau gashi yanaba babban amininshi labarin abunda ya faru tun daga farko har karshe,

"Mal garba yai mamaki sosai yace ikon Allah ina fatan yanzu dai ka gane kuskuranka, indai kasan bazaka kyautata mataba kar ka sake ka dawo da ita,

"Alhj Umar yace haba, Ae insha Allah nothing will happen again, Yanzumafa zuwa nayi ka rakani kasuwa muje mudanyi siyayyan abubuwan kayan gida inyaso gobe sai mu kira wanda zai kara gyara komai na gidan,

"Mal garba Yace Ah Masha Allah hakan yyi daidai, Allah ya barku tare, A dai dinga kiyayewa,

"Alhaji umar yace Ameen

"Sunje sunyi siyayyan kaya da yawa su abinci, drinks, akwatuna, Sababbun kaya, kai Etc yanda kukasan dai kayan Amarya, komai sabo, haka akai mata siyayyan komai, Suka dawo gida

" sunyi sallama beebah taga kaya nike nike se washe baki takeyi tanasha natane, tundaga Gate take daka ma masu shugo da kayan tsawa tana cewa kai Nan zaku shugo dashi,

SaiGa Alhaji yace ita ta aiko ku ko ni, sukace kaine Ranka ya dde, Yace To Nan Part din zaku shiga da kayan, yai musu nuni da sasan maimuna
" Sukace angama Alhaji,

beebah kuwa tsayawa tayi kamar ta nitse kasa dan kunya da bakin Ciki, taga ba wanda yai ta ganta shine ta shiga daki da Gudu, tana wayyo Allah na shiga uku, Ba shiri ta dakko wayanta ta kira makiran Kawarnan tata, take bata labari,

"Kawarta tace tabdijam, ai tunda kikaga haka matarshi zai dawo da ita, Beebah tace meye kike fada hakane

aminiyata, Tace yanda kikaji matarshi zai dawo da ita, ai ke yanzu sunanki sorry wlhi, Kinyi sake dan zaki ya girma....

beebah tace na shiga uku can you help me now... Kawarta tace WA! It's too late yanzu, ai aikin gama ya riga ya gama, sedai musa ido mugani tukunna kafin mu aikata next Action.

"Beebah tace hakane. Jiki a sanyaye ta Sulale a kasa tana kuka,

ba Alhaji umar ya shuga side dintaba se Around 10pm yana shugowa ya shiga bayi yai wanka, ya kira matarshi MAIMUNA,

" Nan Beebah taji dawa yake waya ta yi kukan kura ta kwasce wayan ta fasa tace badai anan gidan ba,
Tai jarking din Alhaji Umar tace ya fada mata uban wa zai dawo gidan....

"Alhaji Umar ya daga Hannu ya sharara mata mari gudu 3 lafiyayyyu,

jin marin ne yasa beebah ta fara ganin stars a idonta ta fadi Kasa, Ya tsallekata yaje pallow Ya dakko biro da pepper ya rubuta *NI ALHAJI UMAR NA SAKEKI SAKI UKU; ba ni bake Har abada......*

Bangaren Maimuna kuma tana jin Faduwar waya tace ta shiga uku tasan bame aikin nan se mahaukaciyar matanshi beeBa, tai tsaki tace Allah ya kyauta, se kuma tsoron komawa gidan Taji a xuciyanta, Taga shaidan na neman Zigata akan karta komai shine ta shiga bayi tai alwala tai Sallah raka'a biyu akan in Alherine Allah yasa ta koma in ba alheri bane Allah yasa kar ta koma......LOLZ

_lols kunsan bana gajiya da Dan mana nasiha...sister koda ana gobe ne daurin aurenki kar ki fasa rokan Allah akan in alherine Allah ya tabbatar, Dan Wasu daga ansa rana kuma shikkenan sunyi bye bye da addua, Matan aure kuma da anyi auran burinsu ya cika shikkenan suma NO.....Ya kamata aduk halin da muke ciki MU YAWAITA ADDUA Yan uwa Allah yasa mu dace ameen_

TAKU A KULLUN
*Ummiey Xeey Abakson*
❣❣❣❣❣❣❣❣❣
❀❀ *A DALILIN SO*❀❀

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

❀ _Being deeply loved by someone gives you strength, while loving someone deeply gives you Courage_❀

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

*I DEDICATED THIS PAGE TO YOU MY ONE ONE ONLY, APPLE OF MY EYES, _ZAINAB SHIGA_*πŸ’ž _YOU REALLY MEAN ALOT TO ME.. MUCH LOVE MUMY XEEY_
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

Β© *Ummiey Xeey Abakson*
_+2348164640126_

Page
1⃣2⃣3⃣
LOLZ beebah na tashi Kaman ance jeki pallow ta ga wani dan karamun pepper akan Dining,

Taje ta bude...Mezata Gani Taga short note din da Alhaj umar ya rubuta mata, Ta karanta Tace Tabdijam....

In kaga nabar gidan nan To mutuwa nayi ba inda zani, dan matarka zata dawo, Taja tsaki tace ni natsana maimuna bazan taba sontaba,

"A gurguje....Ana saura kwana biyu maimuna ta koma gidan Mijinta, Anty larai sukaje kasuwa itama tai mata siyayya da yarinta feenah,

Ansai musu kaya masu kyau.

" Wajen gyara koma ba acewa komai dan Samira da Anty larai sun mata wani gyaran da ake ma lakabi da *MAIDA TSOHUWA* yarinya,

idan kunga maimuna bazaku gane taba se kace ba itaba, Tayi kyau tayi jajir fuskan nan yasha gyara se kyalli yakeyi, abun se Wanda ya Gani, MASHA Allah.

"Ana gobe maida auran maimuna da ALHAJI UMAR aka dawo da feenah gidan Anty Larai.....

Kafin su taho kadunan ne Feenah ta shiga gidan su maryam dan tai mata sallama,

ta tarar da sags a kofar gida ko kallanshi batai ba, ta shiga cikin gidan,

Shi ko duk kunya yabi ya isheshi dan yasan kwata kwata yai ma kanshi Asara...dan feenah ta hadu iya haduwa,

"ta shiga ta sanar da maryam akan cewa yau zata koma gidan mahaifiyarta komai ya gyaru,

"maryam ta rungumeta tana kukan murna ga kukan bakin ciki zasu rabu, feenah ta roketa gafara akan inma ta mata abu ta yafe,

"maryam tace bakomai wallahi, kiban numbernki mana, feenah tace sedai kiban naki dan na saida wayana yanzu, idan naje gida zan amsa wayan mumy na kiraki,

"maryam ta bata numbern har kofar gida maryam ta rako feenah,


Sags ko kamar yaje yai hugging dinta dan ba karamin chanzawa tayiba,

"suna kuka har suka rabu, Maryam zata shiga gidane Sags yakirata yake tambayanta wai me sukewa Kuka....

";maryam tace zata koma kadunane wajen mamanta,

Sags ya zare ido yace what!!!
Ar you serious?

Maryam tace yes

Sags gumi ya keto mai yace ok tafi gida,

"Nan sags ya tsaya kamar wani soko yana hawaye shima, yace Na cuce kaina, _YACE SAI NA AUREKI YANZU DA GASKE NAKE TOO FAA_

Feenah na shiga Jummai tace kefa muke jira maza ki zo mu Tafi kar yamma tayi,

Aiko ta dakko kayanta, *Adam* yace a a kibari na daukan miki, Muje kawai,

Jummai tace inyee Ashe dai yaya naji da kanwarshi,

ita dai feenah tace uhmm dan aranta ita duk ta kosa ma su tafi dan dama tun abun da yafaru ita da Sags Ta tsana garin.....

Sun fito kenan Still feenah ta kara haduwa da sags, taje kallonshi, shima Ya kyalleta,

yai mata wani irin murmushi, Ita kuma duk ta tsargu dan tasan Adam na Kallonsu,

Haka ta wuce da sauri da sauri, har tana hardewa, suka dai samu suka bar layin, Suka wuce Tasha suje su Hau Mota.....

aiko suna Zuwa dama mutane Uku ake Jira suka shige *SAI KADUNA GARIN GWAMNA*......
Basu dde sosaiba suka isa kadunan....

Akai musu maraba gidan ya kaure da ihu anata oyoyo nafeesa dan rabansu da ganinta tun tana karama...

yan uwa da abokan arziki sai murna sukeyi ga maimuna ta warke Ga shi zata koma gidan mijinta......

Kowa yai mamakin feenah yan Uwa sai cewa akeyi ta girma gashi komai tubarkallah.


Ita dai suk kunya yabi ya isheta, Dan Batason aitacewa ta girma this and That Dai Haka....

Around 5Pm ne na yamma Adam yace zai koma akai akai ya tsaya yace aa zedai biyo Baba gobe;
nan gidan matane,

Nan feenah ta fara kuka dan batai tsammanin wata rana zasu rabu da dan uwantaba....

Ana ta bata hakuri akan ai yanzuma suna tare, karta damu ita ko ina se kuka takeyi kamar yarinya....

dakyar Adam ya lallasheta yace to zai dinga zuwa inta koma gidan Mamanta duk bayan 2weeks taji dadi sosai sannan ta dena Kuka....SHAKUWA KENAN.......

zai tafi ta rokoshi har waje tadan takamai kafin ya sama adaidaita sahu ya kaishi Garrage na Kawo....

Yace feenah tace na'am Ta kyalleshi taga idonshi yayi ja kamar zaiyi kuka, Tace ya Adam whats Wrong....

"be ce mata komai ba....
Yace Amsa ya miko muta wani envelope, yace kar ki bude a gaban kowa,

Sannan kuma please ki kulamun Da KANKI Sai NAZo,

Jikinta duk yai sanyi tace ok I prms You...Suna tsaye ne adaidaita sahu yazo ya tsaya gabansu...

Yahau ita kuma ta tsaya tsak Dan tasan tayi missing dinshi
❀❀ *A DALILIN SO*❀❀

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

_We are often deceived by the most trusted person And Loved by the most unexpected person_ *That's LIFE*

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

*Much love Norayyah*

Β© *Ummiey Xeey Abakson*


Page
1⃣2⃣4⃣
Adam na cikin Napep se juyawa yakeyi yana Hangota a inda ya barta a tsaye,

Gabanshine keta dukan uku uku, Ba abun da yakeyi a cikin Napel in banda tinanin feenah har aka kawo besan Ma ankawoba......

Ita kuwa feenah tana shiga gidan taje ta ajiye lettern a cikin Hand bag dinta sannan ta shiga cikin yan mata sa'anta aketa Hira,

Yan uwa se mata congrats akeyi wai she's lucky, Gata da kyau, gata da natsuwa, ga babanta me kudi,

Ba karamin hakuri tayiba, ita dai sedai ta kyallesu tai murmushi....,

Yan matan kuwa se iyayi sukeyi, daga wanchan saurayinta ya kirata, se wanchan ta koma gefe tana chating,

sedai Ta kyallesu kawai tace A zUciyanta race Allah ya rabaku da Sharrin Maza mayaudara.....

Zainab ce me dan hankalin cikinsu yarinyar Kishiyar Anty Samira da itace suketa hira akan school,

abun gwanin sha'awa, nan zainab ke bata labarin ai mamanta neigbour din Sune idan sun dawo dan haka sai yasa feenah tafi natsuwa da ita suke hira........

Bayan isha'i Manyan mata na pallow yan mata kuma suna cikin bed room Se rawar kai akeyi LOLz,

Kowa na abun da yasa gaba, Feenah tare da zainab suka kwanta sunata hiransu, chan har kowa yai bacci, itadai feenah duk ta matsu ta dakkon lettern da ADAM YA BATA.....

"ganin dakin shurune yasa feenah ta tashi ta dakko lettern Ta shiga Toilet ta kunna wutan bayin dan kar yan dakin wata taga haske ta Tashi.......

Ta bude lettern ahankali gabanta se bugun uku uku yakeyi fara karantawa kamar Haka.....
*Hello Sister How are you doing i hope u're doing Well*

_FEENAH i dont even know where to start cos i Surely Missed you_

*_Feenah Naso tun farko na bayyana Miki abun dake Raina amma Ina...A Tinanina Ina ganin kinyi karama, Dan Ko alokacin Da nake tsananin Sonki, A lokacin na gane bakisan me meye SO ba kinga ba dama nafada Miki.......haka Nake ta Rainon SONKI A xuciyata, Kafin Na ankara; Naga sags ya riga da yamun kafa...Bt karki damu bakomai......Just Inaso ki ganeni ni yanzu nafi karfin masoyinki na Soyayya sedai Dan uwanki na jini, I'm ready to help you ko wani Hali kike ki kirani....Sai mun hadu goben, Thanks for your time....I Love You...I'll never stop loving you feenah....Take care bye...._*

Tana gama karantawa wani waye masu zafi suka zubo mata tana cewa WHY YA ADAm me yasa baka furta mun ba..... Nima Ina sonka,
Haka ta gama kukunta ta wanke fuska ta dawo ta kwanta kamar ba itaba Dan kar a gane halin da take ciki.......

bacci ya kwasheta....Washe gari nayi Akai Taron maida auran *MAIMUNA DA ALHAJI UMAR*. Abun gwanin sha'awa Maimuna ba karamin farin ciki tayi sosaiba, Yan uwa da Abokan arziki kowa yai murna, Anci

Please Login or Register in order to submit comment