Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

itama dakyar!

Naseer na bude kofan bega kowaba se Kanwarshi da Maryam kawarta! Kamar zai koresu yace bata tashiba amma ganin maryam ne yasa ya barsu suka shiga se wani kumbure kumbure yake!


Ya shiga Daki yai tsaki yace Nifa sai yasa bansan matata da kawaye fa, yanzu muna cikin Jin dadin mu za a wani takuramu!!

Zainab ce ta fara shiga dakin feenah ta hango feenah cikin hijab, dukansu suka kwashe mata da dariya wai Lafiya Suka ganta da hijab ai sunasha zasu ganta taci kwalliyane!


Feenah dai tabisu da Ido tana kallonsu, itadai tasan me take ji kawai!

Maryam ce tace tazo mata sallama dan zuwa anjuma Ya Sagir zaizo ya dauketa ta koma gida, Kuma anan tAi wa feenah ai sun kulla soyayya da Bash!


Feenah ta rungumeta tana zatai missing dinta sosai, Tagaida su mumy da kowa da kowa sannan Tai musu fatan alheri,

"itama maryam din kuka takeyi dan a gaskiya sun saba sosai sosai! Sukaci dai kukansu zainab na basu hakuri Dakyar suka hakura su maryam suka fito,

suka wuce basu hadu da ya Naseer din ba dan haka suka sa kai kawai suka fita,


Naseer na ta leken su ta window yana ganin sun fita yai maza yaje ya cewa me gida kowaye yazo ace basanan,


"Baba Buba Yace to Ba damuwa!

Naseer na komawa ciki ya kara sa key ya nufa dakin matarshi yaga tana kuka,

Nan yake tambayanta me ya faru tace bakomai zatai missing din Kawartace! Nan ya rungumeta ya fara bata hakuri yana lallashinta hade da Salo irin na ma'aurata,

yana aika mata da kiss da su romance tuni Suka fada gado Suka fara sarrafa junansu,

"yi sukeyi ba sauki dan naga alama dukansu harijai ne! Ranar dai basu sukabar Dakinaba se Ana kiran azahar,

"Naseer yacE wa *FOREVER* su tashi sui wanka tace ah ah yaje dai yayi dan tasan suka shiga toilet dinnan se sunja lokaci dan komawa gidan jiya Za ai ba wani wanka zasui ba se sun kara!!

___ Dan haka NAS ya rabu da Ita yai shigewarsh ya fito yasa wani riga red da Wando Black tree Quater, yayi mai matukar kyau sosai,

Itama sannan ta tashi tai wanka ta shirya tsab, ta sako wani english wears nata itama Tasa T_shirt Red da wando black, kallo daya yai mata Yace Wow, Kin ganki kuwa? Tace uhm kaima ka gankane,

Shidai Nas ya kurawa Forever dinshi ido kamar zai cinyeta, motsi daya tayi ya dinga binta da ido kenan kamar be taba ganintaba!!

Haka har 1 week suke gudunar da rayuwar auransu gwanin sha'awa!

_Naseer kwata kwata ya kashe wayanshi dan karma abokai suce zasu dameshi da zuwa irin ganin Amaryan nan.

Dan jinshi yakeyi a wata sabuwar duniya!



_________________________
Bangeren Iyayan NASEER KUWA Alhaji kamal ba karamun farin ciki yai ba da yaji labarin Amaryan Dansa, an sameta me natsuwa a gskiya Alhaji yaji dadi Sosai!

Akwana a tashi ba wuya yau feenah sun koma hutun semester dinsu, Dama ba son karatu takeyi sosai ba tace ita tunda tai aure ba inda zata koma!

Dakyar dai naseer ya shawo kanta akan cewa ta koma plz, duk amfanin kansune. Tace ita wlhi badan karyace tamai gaddamaba itafa atafau bazata komaba zaman aure zatai ko karatu,

yace zaman aure amma kinga saura kadan ki karashe plz kar mui haka dake,

dole feenah ta tashi da wuri ta shirya Nas Yakaita har bakin gate yace kuma zaizo ya dauketa kar ta tafi ita kadai tace mai to.


Tana shiga Lecture room yan class din kowa se Allah sanya alheri ake mata duk kunya yabi ya yasheta tace Ikon Allah kenan, Ummice tace uhm Matan manya Wai duk auran ne yasa kikai kyau haka, har wani Miskilanci kika koya ko?

"Feenah dai sedai tai musu smiling dama ba mace bane me yawan surutu.

Ummi tace lalle kam muma dai auran nan gskiya zamuzo muyishi kinga yanda kikai kyau kuwa,

feenah tace uhm naji dai plz ya isa, haka suka wuni ummi se tsokanar ta takeyi wai Kodai Taji jijiyan mazane yasa ta natsu haka,

itadai feenah sedai tace mata Eh din,


Haka rayuwa tace gaba Tunda akai auran suna zamansu lfiya ba abunda ya taba hadasu, Naseer ko irin anzo ganin amaryan nan yan unguwa be bari sedai yace Tana school,

Adam kuwa tunda akai auran be zo gidan ba, kuma be sake kirantaba dan yanzu ya fara mantawa ma da ita, tunda yasan duk wani abu da zaiyi to yana jifa bayan hari ne....

*2 months* Letter Yau Saturday feenah ce ta tashi da kasala sosai a jikinta bata iya tabukai komai se Amai takeyi jikinta dai yana mata wani iri badai yanda ta saba jiba! Dan haka ko tashi ta daura musu break fast batai Ba. Gashi NAS zai fita da wuri, Yajita dai shuru a daki ya leko yaganta a kwance duk daukanshi bacci takeyi dan haka yaje mai mata peck a goshi yace I love you ni na fita, sannan ya sa Kai ya fita,

ita tananan kwance tanajin motsinshi amma ba yanda zatai ne,


NAS ya Fita office yaji dai gabanshi na fadi like something is wrong a wani waje dan haka yake ji indai wani abu yana faruwa da wani nashi Zai dingaji gabanshi na mugun Fadi dan haka yaketa karanta Hasbunallahu wani'eemal Wakeel,

Feenah ce kwance a daki se Amai takeyi a cikin daki kamar hanjinta zai fito common waya ba bazata iya dauka ta kira wani ba balle asan halin da take ciki!!

*11:00* NAS ne yaji yana missing din matarshi yace wa frnds dinshi bari yaje gida ya dawo Har bash namai tsiya yace zan biki tunda fa akai auran nan ban ganta da kyau ba...

"Naseer ya daure fuska yace kaje kai aure so that seka ganta dakyau badai _FOREVER_ na ba dukansu suka kwashe da dariya shidai Nas yadauka ke ya fito daga office din................








*Ummiey Xeey Abakson*
❤❤ *​​​A DALILIN SO​​*​❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣


``` Sometimes you have to let go of your fear to catch your destiny'```


_Proudly Dedicate This page To you Beebie👄 And neena Cool you guys are just amazing...# ONE LOVE😘_

® ♻ *​​​EXCLUSIVE WRITER'S ASSOCIATION*​​​✍🏼
♻ *​E W A*​♻


© *​Ummiey Xeey Abakson*​​​ 👄


Page
1⃣5⃣5⃣
Yana cikin motan ne yaji gabanshi dai still yana faduwa yace to Mudai Allah gamu gareka duk abun da ka hukunta akanmu dai dai ne!

Yana tafiya yana addua, Hardai ya samu ya shugo cikin gida yana horn yaga matarshi bata leko tazo mai oyoyo ba nan yace to lafiya kuwa,

Yana parking da azamarshi ya shiga cikin pallow tun a pallow yaji ana nishi wayyo Allah, Wayyo Zan mutu,

Da sauri NAS Ya shiga dakin da gudu ya ganta cikin Amai tana yunkuri kamar Zata fado daga gado, Wani Zaranannar Ihu Nas ya sake da ya kara Tsoratar da feenah dan Batasan ma Wani Ya shugo Ba,

" cikin Azama ya dauketa Se cikin Mota ya nufa *GIWA HOSPITAL* suna Zuwa aka kaita Emergency room akai mata gwaje gwaje nan take akasa mata drip Dan ta wahala sosai,

Seda A Ka sa mata ta fara dan dawo wa hayyacinta Sannan NAS ya kira gida Yace Plz zainab taje ta gyarawa feenah daki su suna Asibitine bata da Lafiya,

"Mumy Sameerah Tace subhanallah kuna wani asibitine Naseer

" yace suna Giwa Hospital da Sauri Anty samira tace gasunan Zuwa, Ta shirya suka fito tare da zainab, zainab ta wuce gidan Ya Naseer ita kuma Anty samira ta wuce asibiti.

"Zainab na shiga dakin taga Amai duk a tsakar daki tace subhanallah me ya faru haka, shi Ya naseer din yana ina har haka ta faru, Taga tinani ba shine abunyi ba ta fara gyra dakin ta dakko tsumma ta kwashe sannan ta cire bedsheet din ta jika da ruwan omo, sannan ta dakko Mopper da ruwa ta fara gyara cikin Dakin!

Ita kuma anty sameera Tana shiga Aka nuna mata dakin Da aka kai feenah ta shiga da sauri ta sameta da drip a hannununta, Take tambayar naseer da ya dukar dakai alamaun yana cikin tsananin Damuwa, Anan yake bata labarin yadawo daga Office kenan ya sameta cikin Amai,

Anty Sameera tace Ya salam Amma dai da sauki dai ko Yace yes Alhamdlh, Tace karya damu, Bari ta kira maman feenah din a sanar dasu Kar mui abun mu Kadai dan haka ta dakko waya ta kirata ba a ddeba sega Anty Maimuna tazo ta samesu suka gaisa, tace meke damunta haka, Nan naseer yace wlhi DOCTOR be fadaba tukunna, bt kamar typhoid ne dan naga harda jiri tace tanaji,

Nan dai suka ce Allah ya kara sauki, sukace Ameen,

Suna cikin Hiransu Sega Zainab tazo itama ta shugo da Sallama sannan tai ma feenah ya jiki tace da sauki, sun jima kadan Anty Samira tace zata koma gida ita Zainab din ta zauna tare da feenah zata dawo anjuma da Alhaji idan ya dawo,

Maimuna ma tace muje mu hada hanya, Allah dai ya bata lafiya sukace Ameen,

Duk NaS yabi ya basu tausayi.


Zainab ne a dakin Nas yaje yin Sallah feenah ta farka da alama abinci take bukata, Ta bude ido taganta a asibiti, but batace komai dan Tasan ta sha wahala sosai, Nan feenah ke tambayan Zainab ina Nas, zainab tace yaje sallah amma yanzu zai dawo bari na sako miki abinci kici kinji, sannu,

Feenah kawai tace uhm Ok Thanks,

Zainab na cikin zubawane sega Naseer ya dawo yace yauwa sister nagode, Ya kalle matarshi abun sonshi abun alfari, yace mata sannu yatakeji yanzu, Tai nuni da hannunta ta taba cikinta tace yunwa takeji,

Naseer yaji dadin haka dan dama Beso tamai gaddama akan bazataci abinci ba, dan Haka Ya amsa food din da Zeee ta saka ya fara feeding din feenah, taci sosai sannan tace ta koshi,

Naseer yaji dadi yake tambayanta yanzu meye ke mata ciwo tace ita ba komai Kawai batajin karfin jikintane!

Haka dai suka ci gaba kwanansu biyu asibiti Aka sallemeta,

_________________________

Alhaji Kamal ne yace Ya kamata a nemo mata yar aiki ko yar karamar yarinyace dan Gaskiya baiso a dinga barinta ita kadai, Kaga inda wani abu ai yarinyar zatai hikima ta fadawa ko me gadine inyaso se asan abunyi,

"Dukkansu sukai na'am da wannan shawaran! Alhaji kamal ya dada da cewa ya biya musu Umura idan sundawo Sai a nemo mai Aikin,

Feenah da Naseer ba karamin dadi sukaji ba matuka, Alhaji Umar da anty Maimuna ma sun mai godiya sosai, dan abun ya musu sugar, Alhaji Kamal yace ba komai su shirya zuwa jibi zasu tafi dan international zasu bi dan Haka tunda suka dawo basu koma gidan suba!


Kwanansu Daya gidan Alhaji Kamal kowa ya lura feenah macece bame son Hayaniyaba, in kaga ta sake jiki to Da kawarta Zainab Ce!!

Ranar da daddare ana gobe zasu tafi suna daki feenah da Naseer Yace mata bari ya nuna mata wani abun data manta! Tace ok Nunamun Ina jira!

Aiko naseer ya dakko wayanshi yai playing Wani Vedio yace tazo ta kalla! Mezata gani... Ita ta gani ranar birthday din Zainab se tika rawa takeyi tai maza ta rufe ido tace Plz nidai ka goge dan Allah,

"Naseer ya kyalyale da dariya yace kalleki kamar bakeba! Hahaha nan dai suketa hiransu Har dare yayi yace ta bashi hakkinsa, Tace yayi hakuri fa nan ba gida bane!

Naseer kamar zai mata kuka yace 3days fa kenan rabon da na jini a jikinki nidai ki barni plz,

Nan dai ya fara mata wasu surutun da ya kashe mata jiki har suka manta wai a ina ma suke suke fada kogin soyayya se Sarrafa junansu sukeyi kamar wanda suka shekara basu ji dumin junansuba!

Daren ranar dai haka sukaci Soyayya kamar ba gobe, Asuba nayi feenah ta tureshi tace kagani ko, nidai bari na shiga wanka tun wuri kafin Asan me mukayi!

Naseer yace Lolz. Wace rana! Yau zaki rigani wanka Dan ba gida bane ko?,to Iran ma sunsan me mukayi ke ba mata ta bace?

Feenah tace uhmm nidai bari kagani haka ta nufi toilet tun gari da duhu tai wankanta ta shirya shi kuma naseer se asuba sannan ya tashi yai wanka yai sallah suka kintsa suka fito suka gaida iyayansu

Sannan Alhaji Kamal yace su shirya Jirginsu ya kusa Tashi Fa! Da sauri sukai breakfast,

Alhaji KAmal dasu Su anty samira da Zainab da mumy maimuna suka rakasu airport!!















Ummiey Xeey Abakson!
❤❤ *​​​A DALILIN SO​​*​❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣


```Kindness and faithfulness keep a king safe, through kindness his throne is made secure```.


💝💝 _Dedicated To Zarahn Ms, *I love you so much* thanks for the care and support_💝💝


® ♻ *​​​EXCLUSIVE WRITER'S ASSOCIATION*​​​✍🏼
♻ *​E W A*​♻


© *​Ummiey Xeey Abakson*​​​ 👄


Page
1⃣5⃣6⃣
Suna tsaya wajen Har Jirgin su Feenah ya tashi, Zainab se kuka takeyi, Wai tayi missing din Su!

Anty Maimuna ne tace sorry yata, Baga munan ba kuma suma Zasu Dawo ai,

"Alhaji Kamal ne yace hajiya maimuna rabu da ita se kuka takeyi kamar karamar yarinya batasan ta girma bane? lolz Suka danyi dariya

"Maimuna tace ina ruwan Yara!!
sannan suka kama hanya Suka dawo gida kowa yayi gidanshi!!

"Su feenah kuma Sun isa lafiya suka kira gida suka sanar dasu kowa yai hamdala sukace amaida hankali ayi ibada sosai Allah ya dawo dasu lfiya, Sukace Ameen!!

"Haka dai rayuwa taci gaba kowani gida cike da kulawan junansu, Akwana atashii ba wuya yau Zainab tacewa mumy samira zataje gidan su Anty maimuna ta gaisheta,

"mumy samira tace aiko kin kyauta, Ki gaishemun da ita kinji kici mata ya gajiyan hanya kwana biyu bamu haduba!!

"Zainab tace Insha Allah zan fada mumy sai na dawo, Samira tace adawo lafiya!!

Zainab ta fita cikin natsuwa tasa hijab dinta dan madaidaici ta nufa gidan Maimuna, Ta shiga da Sallama Taji *ADAM* ya amsa ta shiga ta gaisheshi anan take tambayan Mumy Batanan ne yace yap batanan,

"Yanda yake magana tabishi da kallo itadai har xuciyanta tana son Adam but ba yanda za ai ta fadamai ne tana mace! Dan har ta juya zata tafi Adam Yace ah bazaki tsaya mui hiraba, dama kawarki da mumy kawai kika Sani Ko?

Tadan dukar dakai tace ah Ah, Yace ok to mui hira mana! Ta sunkuyar dakai tana wasa da yatsun Hannunta yace is like na takura miki Ko, Just give me your number mudinga zumunci tunda haka kike keda kawarki!

"Tadanji zafi aranta dan tasan wa yake nufi, A xuciyanta tace wato still dai kana son feenah ko, shine har zaka hadani da ita, Tana cikin tinanin ne ya katseta yace bakiji me nace bane Ki bani numbernki!

Nan dadi ya cika mata heart dinta dan dama abun da take jira kenan, Taji Adam ya tambaya numbernta dan A duniyan nan Sonshi Takeyi.


_________________________
Tana bashi numbern ta fita ta tafi gidansu, Nan anty sameera ke tambayanta ko lafiya taga tai saurin dawowane!

Zainab tace Batanan ne mumy sai yasa, Anty samira tace ok badamuwa Anjima Sai ki koma tace ok Mumy,

________________________
Bangaren su Naseer kuwa tun da suka Isa basu wani sama time din soyayyaba amma kana ganinsu kasan masoyane dan ko ina zasu tare suke zuwa! Feenah na makale da Naseer shi kuma yana rige mata jaka! Kowa yagansu se yayi sha'awarsu!


*ADAM* ne zaune a daki da yamma, ya dakko wayanshi kamar zai kira zainab kuma se yaki, dan shi tsoro yakeji ya furta mata Kalmar So tace bata sonshi, Sai yasa yace huh... To ni yanzu tana ina zan farane??? Kawai yahau Wahtsapp Yai Sa a tana online yai Sallama ta amsa!
Tace who am i chating with
Yace its me,
Tace who banfa gane kaba,
Yace wanda dazu kika gaba numbernki,
tace oHh Ya Adam
Yace yeah nine,

nan suka fara hira sosai tunda dukansu suna muradin junansu ba wanda ya sani cikin dan kankanin lokaci suka Shaku:

chat sukeyi kamar bazasu denaba, Anty Samira tace tazo ta koma gidan ko anty maimuna ta dawo.

Zainab tace ah ah mumy ki bari zuwa gobe yanzu fa yamma yayi.
Samira tace ok Allah yakaimu,


Zainab na shiga dakin tace huh Kawai yanzu inje in ganshi da wani ido zan kalleshi nifa kunyarshi nakeji!

Adam ne yaji shuru yanata message ba reply data dawo yace haa meye farune!
Tace a a na dan Duba kitchen ne,
Yace oh Ashe kanwata ta iri girki, Tace uhm

Ranar dai har 10 haka suka kai sunata chat kamar bazasu Rabu ba, Seda suka gama chat dinne zainab ta zauna tai tinani tace too faa kar dai ace ni nakesonshi nake ganin kamar shima yana sona! Wata xuciyan tace hmm To bazai ki fadamai ba meye a ciki, daga gani shima so yake yai aure ya huta! Da wannan tinanin tai bacci,

Shi kuma bayan Sun gama chat din yayi bacci kadan ya farka cikin dare yatashi yai alwala yai nafila yana rokan Allah dai ya hadashi da mata ta gari!

Yana gamawa ya koma bacci be farkaba se asuba...

Tun asuba suka dasa chatS se yi suke tayi har mumy samira nacewa sai ta kwace wayan wai mutun tun safe se danne danne yakeyi,

Tadai cewa mumy sorry tai wa Adam sallama tace zatai aiki amma idan ta gama zata kirashi ta tayashi hira,

"Adam yai dariya yace Wato ni zaki taya hira ko itama tai dariya
Tace eh mana Kai zan taya LOLz

Yace ni dai Ki sauri ki gama aiki kizo muci gaba da hira!

Har xuciyanta taji dadi sosai dan dama burinta ya kusan cika! Dan bata da abun dake so kamar taganta tare da ADAM suna hira dan gskiya tana sonshi kuma tayi alkawari indai yana sonta zata aureshi sbd ta cireshi daga cikin damuwar rashin feenah,



*sannan sukai sallama!!!*









*Ummiey Xeey Abakson*
❤❤ *​​​A DALILIN SO​​*​❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

```sisters are like stars you dont always see them but they re always there for you ```

💞💞💞 *Dedicated to my sisters*💞💞💞


® ♻ *​​​EXCLUSIVE WRITER'S ASSOCIATION*​​​✍🏼
♻ *​E W A* ♻


© *​Ummiey Xeey Abakson*​​​ 👄


Page
1⃣5⃣7⃣
Haka ADAM DA zainab suka wuni suna chat suna waya Dukda dai Adam be furta mata kalmar So ba amma Kana ganinsu Kasan soyayyan gaske sukeyi, dan yanzu zainab bata wuni bataji muryan Adam ba, shima Haka,

Satin Su Naseer Biyu suka dawo, basu sauka ko inaba se gidan babanshi Alhaji Kamal, Nan zainab taketa murna dan taji dadi sosai, Tace Manyan Mata kinga yanda kikai kyau kuwa!

Feenah dai tai dariya tace uhm kema zai zakiyine lokaci kawai ake jira, Ranar tare da zainab suka kwana suka wuni zainab ta bata wasu magunguna tace tasha Wlhi Zai mata aiki tunda dama kwana biyu Tasan yayanta yyi missing dinta,

Feenah tai murmushi tace uhm XEETAH wlhi baki da dama fa, haka dai suka kwana suka wuni kwanansu Biyu sannan aka saman ma Feenah yar aiki dama kafin ta dawo anty Samira taje kauye ta saman mata so tare SUKA tafi..........


Ranar da suka koma gida ji naseer yake kamar sabon maye dan wani matsifan feelings yakeji sosai suna pallow suna kallo yacewa feenah taje ta dakko Mai Wayanshi a gado:

"ita feenah tasan zancen sai tacewa Asma'u (sunan yar aikin su kenan) taje ta dakko mai tai hankali kar Ta fadar mai da wayan,

"Asamu yarinyace karama amma tanada hankali da wayau ta tashi cikin natsuwa ta tafi dakin da sauri Naseer yazo kusa da ita ya fara mata wani irin kallo shifa Yanason kasancewa da ita cikin Daren nan!

Suna cikin hakane sega Asma'u Tana mika mai taga abun da bata saba ganiba naseer a kusa da matarshi jikinta nA Rawa tace sai da safe zata tafi daki,

feenah tace ok Bye kanwata!

"Asmau ta tashi jikinta na rawa se kallonsu takeyi a xuciyanta tana cewa Yan iska, ba ance ba kyau ba: kalle yanda yake ta bata!

Itadai ta shige daki duk tsoro ya kamata!

Feenah ce ta kalla Naseer tace kagani ko ka koreta tana cikin kallonta, Naseer yace ki kika koreta bake nace kije ki dakko mun wayaba ai da a daki zan sameki sai mui abun da zamui.

Feenah tace uhm Naji,
Nan dai ya tashi ya kashe wuta da kayan kallo suka fara aikin da suka Saba se shafata yakeyi kamar besan wacece ba, Dakyar dai tace kaga bamu kadai bane mu tashi mu shiga ciki, ya dauketa be zarce ko inaba se bed room dinshi yana ajiyeta ya cire riga Yahau faman sarrafata, A daren dai gskiya yaji dadin da ya kwana biyu bai jiba!

Asuba nayi dakyar ya banbare jikinshi a nata ya tashi yai wanka sannan yai Alwala yai sallah!

Sannan ya tasheta itama duk a gajiye tai wanka tai sallah sannan suka koma bacci,

Asam'u kuwa tun safe tajisu shuru Tace hmm basu gama iskancin bane, Chan dai ta gyara ko ina,

sega feenah ta pito daure da towel

Asmau Tace laa, asmau kyar idonta akan feenah, Shima sega Naseer din ya fito yace dear ki shiga ciki; tana shiga ya bita;

Asma'u kuma se haushin Naseer takeji wai shine dan iskan Lolz...

Haka dai sukaci gaba da gudanar da rayuwarsu cikin zumudin juna da kaunar juna!

Asma'u ko har ta saba dan ko ta gansu kauda idonta takeyi tana cewa basu da kunya LOLz..

_________________________
Bangaren Adam Kuwa Soyayya suke ruwa ruwa duk da ba wanda yasan sunayi Sai su Kadai! Adam a boye har ya fara hada kayan aure be fadawa kowaba!

Shi kullun idan ya dawo aiki beda abokin hira in ba Zainab ba dan sun wani irin sabo be Balle kuma ace maka SOYAYYA DA SHAKUWA, abun se wanda Yagani

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••
Ummice Zaune a class kowa se tambayanta yake wai ina kawarta kodai mijin Nata ya hanata zuwane!?

'Ummi sedai tace wlhi bansaniba dan Kunsan kowa da ra'ayinshi may be beson tadawone ko kuma kunsan auran yanzu mostly zakuga da anshiga in Allah ya kawo sai ciki may be cikine yakesata laulayi yasa bata zuwa!

Wasu dai daga ciki sukaci haba sedai ciki, Nidai nace ba wani ciki kawai bata zauna bane hidima sun mata yawa!

"Ummi dai tace to bansaniba indai na koma gida yau zanje!

Suna gama magana Ummice ta kira mumynta tace yau bazata sama daman dawowaba saboda zataje gidan frnd dinta feenah tajita shuru may be batada lafiya ne, Mumy tace to sai kindawo Allah ya tsare kardai ki dde ki mata sannu,

Ummi tace thank you mumynah bye,

Aiko anayin closing ummi ta kama hanya sai gidan feenah Ta sameta cikin wani atamfa tayi kyau sosai nan feenah ta runguemata suka shiga daga ciki suna hiran rayuwa!

Chan sai ga asma'u ta kawo mata ruwa,
ummi ta kalleta tace waye wannan!
Gaban Asamu ya fadi,

tana fita feenah tace yar aikine!

Ummi ta zare ido tace what wlhi kar ki yarda da wata yar aiki se ta girma ta kwace miki miji Ko??

Hankalin feenah ya tashi,
ummi tace better kisan abun da kkeyi to wai har ma wani aiki ne agidan de se an nemo miki bakisan lada ko?

Feenah nan take bata labarin dalilin kawota tun wani rashin lafiya datai ne akace a kawo mata yar aiki,

Ummi tace tabdijam... Allah dai ya kyauta nikam bansan yar aiki komin kankantarta!

Haka dai suka ci hira har Naseer yazo ya samesu yaketa mata tsiya wai ashe itama tafiyarsu daya da feenah mean kirkinsu yayi yawa tun biki bai sake ganinta ba se yau,

Nan ummi tace wlhi school tinx ne sai yasa bt zaku dinga ganina akai akai,

NASEER YACE

Please Login or Register in order to submit comment