Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

uhmm Nop transfer akai mai wajen aikinsu bt Ba wani soyayya ina Aure....
Maryam Tace Alhamdulillah,

Feenah tace kefe yaushe zamuzo shan biki,

maryam tace wani Biki, Dad yace sai naga school nima, kinga sai mu maida hankali sosai, Allah ya fito mana da mazaje nagari...

Feenah Tace AMEEN. MARYAM tace frnd dan Allah zaki mun temakon Wani Abu

feenah tace meyeshi
"maryam tace dan Allah kizo muje mu gaishe da Ya sags wlhi beda lafiya kuma duk ta ​ *DALILINKI​* ne

feenah tadan bata rai tace inje inyi mai mene, ya mutu wallahi, ba inda zani, ai kinsan halin daya jefani har yanzu mum bata saniba, tsoron ma yanda zan fada mata nakeyi...

Maryam tadanyi shuru Tace wlhi feenah na sani, Yana chan kamar zai mutu dan Allah kizo muje ki ganshi, ki yafemai, Rai ahannun Allah fa, kiyi hakuri kizo muje...

Feenah tace itafa bazataba, ta tsana garin ma gaba daya, Da tasan zatace dole setaje gaisheshi da bata kirataba, maryam dai se hakuri take ba feenah Akan ta yafemai, Wallahi yanzu ya tuba ya gane kuskuranshi...

Feenah ta bata rai dan just ba yanda zatayi ne tace muje amma wlhi dan Allah zanje gaisheshi badan halinshiba.

Maryam tace eh hakane dan Allah ai nace miki,

Suka fito dakin, feenah ta dakko gyalenta a dakin dasu umma suke, tace musu zataje ta gaishe da su maman maryam ne, su umma sukace dako kin kyauta.... Maimuna tace uhm, kaigaishesu...

Suna fita, gidan suka shiga suka wuce cikin gida feenah taje ta gaishe dasu maman Maryam, Su ka ganta ta yi kyau tA musu kwarjini, seda sukaji kunya dan daga baya gskiya ya fito Sun gane dansune ya yaudareta, Nan suka fara bata hakuri tace uhm Ba komai Ta yafe Allah ya tsara nagaba sukace amee,

suna barin part din Dakin sags suka shiga suka sameshi a kwance da alama bacci yakeyi

Feenah ta kura mai ido tanajin sonshi a xuciyanta; gashi ya bata tausayi, har wani kyau ya kara ga tabon sallah ya bayyana a goshinshi,

shuru be farkaba Har wajen 5pm shine maryam tadan tabashi tace Yaya, yaya ka tashi yamma tayi, kamar a mafarki yaji ana tashinshi ya bude ido ahankali ya Saukar da idonshi Akan FEENAH...

Suna hada ido ya kara kulle ido, shi duk tinaninshi mafarki yakeyi,

Seda Maryam ta kara tabashi tace yaya Ka tashi Yamma yayi shine ya tashi firgigib tana fadin *Hasnunallahu wa ni'emal wakil*....

Ya tashi ya zauna, kanshi a kasa, kamar me tinani,

jin muryan wanda ya dde be jibane ya dawo dashi daga tinanin da yakeyi

" *Tacemai INA WUNI, YA KARFIN JIKIN*,

ya kyalleta cikin natsuwa yace ALHAMDULILLAH...

"Chan kowa yai shuru yace dan Allah feenah ki yafemun abun da nai miki, Wallahi sharrin shaidan ne, kiyi hakuri,
"Itadai feenah batace mai komai ba dan wani haushinshi takeji kuma Sonshi takeyi... Ya kara cewa kiyi hakuri dan Allah.... Tace uhm Allah ya rufa asiri, yace baki yafeba kenan,

ganin batason magana yai tsaho tsakanin ita dashine Yasa tace Sai anjuma maryam zan tafi Allah ya kara sauki,

Nan hawaye yana zubuwa sags yace dan Allah dont go feenah ki tsaya kiji,

"Feenah, ita kuma ina har takai bakin kofa dan xuciyanta tafarfasa yakeyi akan abun da yai mata, ita yanzu me zatacewa wanda zata aura, da wani ido zata kyalleshi, tace a xuciyanta Sags ka *cuceni*.



Tai ficewarta, sedai maryam ta biyota abaya tace haba frnd dan Allah kiyi hakuri mana..

Feenah tace baki da ikon sani wannan, kince nazo na gaisheshi nazo so ki kyaleni da abun dake damuna,
"bake aka ma haka bane sai yasa
maryam tace i'm sorry nasan it pains amma dan Allah ki daukeshi akan kaddara, please

feenah tace uhm Allah dai ya tsara nagaba.... Suna fitowa Adaidai lokacin da Adam yazo wucewa kenan Ya ganta ta fito daga gidan wani harara ya sakar mata, seda gabanta ya fadi *Duuum* tanacewa maryam na shiga uku ya Adam...

Maryam tace kiyi hakuri Allah na gani ba komai kikajeyi ba, nace sonki yakeyi kince ah ah,. Feenah ita inama take sauraran Maryam hankalinta duk yai gida sabd tsoro...

Adam ne ya shiga gida,

feenah da maryam suka biyo bayanshi... Yaje yai musu sannu da hutawa suma sukaje, yana shiga daki feenah tai cirko cirko a tsakiyan gida, su dai su umma basusan meke faruwaba,

maryam ce tabi Adam cikin Dakin take cemai dan Allah yayi hakuri akan maryam ta shiga gidansu,

ko kallon maryam beyiba
Tace nace muku wani abune???? Ko tace miki wani abun ne?? Maryam tace ah ah tacene dai kawai ta shiga Uku shine nazo baka hakuri,

yace Toh. Maryam ta tashi tabar dakin ta fito taiwa su umma sallama ta tafi gida.....
❤❤ *A DALILIN SO*❤❤

❣❣❣❣❣❣❣❣

_Sometimes No Matter how much you want things to happen, all you can do is to *wait*_


*Dedicated to M Khady group* matar sojah💘
❣❣❣❣❣❣❣❣❣


® *HIKIMA WRITER'S ASSOCIATION*


© *Ummiey Xeeyy Abakson*


Page
1⃣3⃣5⃣
Ganin maryam ta tafine, shine Feenah ta shiga daki itama,


Magrib nayi kowa yai alwala yazo yai Sallah aka ci abinci aka dasa wani hiran kuma dukansu, Kowa na lura da feenah akwai abun da ke damunta, se kowa yai banza da ita,

baba sani ne yace feenah ko baki so zuwa bane naga tun dazu ana hira kinyi shuru, Tace ah ah baba, wlhi kaina ke ciwo, shine yace ta tashi taje tasha magani, kowa dai binta da ido yayi,

Around 10pm kowa ya tafi makwancinsa

*WASHE gari* nayi da misalin 12 suka kintsa suka kama hanyar dawowa kaduna.... Maimuna itama taba umma yan kayan sawan data hadu mata da wasu kudade, har sun tafine Adam yace yana zuwa, ya shugo ya basu kudi kasan 20,000 se mamaki sukeyi akarshe dai suka samai albarka sosai sannan yai musu sallama, yazo suka dawo gida

"Bayan isarsu gidane kowa ya huta Feenah ta shiga dakin Adam bashi hakuri beko sauraretaba yace ta fitan mai a daki, tunda ita bataji, har zataje gidan su sags bayan ta manta abun da yai mata,

feenah tace wlhi yaya Ba haka bane, maryam ce tace naje na gaisheshi beda lafiya rai ahannun Allah shine naje....

Yace good inasha dsame maryam din ne ta rudeki har kika biyewa yayanta,

tace hmm Kayi hakuri bazan karaba, yai tsaki yace kima kara......

"Su zainab sunajin sundawo sukazo musu sannu da zuwa, ya hanya sannan suka dan taba hiran kawaye' Har feenah tadan saka Rai ta danyi walwala, nan maryam ke tambayanta ya Adam Fa,
tace yana Daki, tace uhm Gskiya kinyi dacen Yaya nidai kawai burgeni yakeyi, Feenah tace uhmm Kodai kina cikine,

Zainab tace kefa, in miki kwacen karfi da yaji,

"feenah tai smiling tace ah ah ai duk abun da ya Adam yakeso inaso indai yanaso tom,

Zainab tadanji kunya tace muje mu gaisheshi Please,

da kamar feenah bazataba se kuma tace ok muje to,
suna shiga Zainab ta fara Sallama, Adam ya dago kai ya kyalleta, dan a gskiya ta Hadu, ya re mata kallo, sannan tace sunzo gaisheshi yace to nagode.....

Sukabar dakin suka dawo dakin feenah sukadanyi hira kadan, sannan zainab tace zata tafi feenah ta rokata har bakin gate, zainab na fita sega *Naseer* ya kalleta yaga tafito a gidan, be tsaya yaga waye zai biyi bayan zainab ba yai shigewarshi gida.....

Feenah na fitowa zainab ta nuna bayan Naseer tace kinga yayana dinnan *naseer,*
Tace ok,. Har yau dai bansanshiba......

Zeee tace uhm ai baki da kirki taya dama zaki sanshi,

feenah dai tace uhm with time zan sanshi ai,
zee tace hakane ta tafi

feenah kuma tadawo cikin gidan

*********************

"bangaren sags kuma tunda Feenah tazo yaji ya warke, dan har abinci ya samu yaci, Ya dan fito tsakar gida dan yaji karfin jikinshi...

Washe gari seda aka kara kiran doctor din ya gwada Bp dinshi yaga ya sauka....

Yace ya kikaye abun da zai dinga dagamai Hankali......
Ya lalubi wayanshi dai yaga text dai yaje bt besan ko ta karanta ko Ah ah ba...

"Feenah ita kuma dare nayi yau bata tsaya hira ba dan suna dan takon saka da Adam Gashi gobe zata fara zuwa school dan haka ta tafi daki tai kwanciyarta, sannan ta lalubo wayanta tana dan dube dube taga text ta sama, shine ta shiga ta Bude....... LOLz mezata gani tana budewa tafara ganin text din apology na Sags, ta fara karantawa ahankali tana gamawa tai tsaki tace mtswww What!! Me yake nufine,, Beda Hankaline, Yana nufin zan hakurane.... Sbd haushi ta kashe wayan ta kwanta se bacci,

❣washe gari nayi agurguje ta shirya dan daddy yace ta Shirya da wuri ze dinga kaita kafin ya wuce Wajen aiki..... Sbd morning lectures gareta, ta shirya tsab suka wuce har mumy na mata tsiya, ahanyane Dad ya kara mata fada akan Tai hankali da Samari ba ruwanta dasu, tasan me yakaita, indai tai ma haka to zaiji dadi, tace nayima Alkawari Daddy.




















*Love you All*😘
❤❤ *A DALILIN SO*❤❤

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

*Be with some one who is proud to have you*

*Dedicated to Faida simple... Love you bby*

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

® *HIKIMA WRITER'S ASSOCIATION*


© ```Ummiey xeey Abakson```


Page
1⃣3⃣6⃣
Yaje ya sauketa, a bakin gate din school din, tana shigaTa tambaya aka nuna mata department din Su na Microbiology ta shiga ta sama waje ta zauna, sbd da wuri taje bata dde sosaiba aka fara taruwa,

kowa ya sama waje ya zauna, lecturer din su yazo aka fara introduction kowa ya mike ya fada sunansa da state dinshi abun gwanin sha'awa ba karamin birge feenah yayiba,


Anan tai wata kara Me Suna *Ummi*, around 10 ne anje break Feenah da ummi basu fitaba dan ba inda zasu, wayan feenah ya fara Ringing tana dubawa taga Numbern Sags ne Tai tsaki ta kashe, Aka sake kira, ta kara kashewa, Aka sake kira,

Ummi ce tace Haba Frnd ki picking bakisan waye ke kirankiba kuma bakisan mezai fada mikiba,

"feenah dai jin Ummi kawai takeyi dan idan Sanin sags ne sedai tacewa ummi batasan wayeba infact bata ma san waye feenahn ba,


shine feenah ta dauka Tace hello Sags Yace hii, dafatan kinanan lafiya,

feenah tace uhm I'm fine,

se kuma kowa yai shuru, feenah tace kaga in baka da abun fadane sai anjuma ina class ne,

sags yace i'm sorry for disturbing you bakiga text dina bane, Ko reply,

feenah tace nagani sai me, Wai me kkeso danine, Ka barni kajiko tai cutting din call din, ummi ta tsaya kallonta tace haba frnd me yai zafi haka,

Feenah tace uhm bazaki gane bane banaso ina school ana damuna,

ummi tace ohh big girl se ki dena zuwa da phone din, Nan dai suka ci gaba da hira har aka dawo break aka cigaba da lectures,

sags kuma tana yanke wayan a xuciyanshi yace baki laifiba nasan Zaki abun da yafi haka, Ya sake daga hannu ya roka Allah akan Allah ya yafemai.

Lectures suka ci gaba ba ai closing ba se 2pm, Sun fito sun tafiya da ummi tace Bani numbernki, nan sukai exchanging,

Suka fito bakin gate, Se ummi ta hango drivern su tace in bazaki damuba kizo mukaiki gida kinji...

Feenah tace No No thanks, Dad dina zaizo,

Ummi tace inyee yar gidan dady.... Sukai sallama Kowa ya kama gabanshi



*AFTER 2MONTHs* Haka rayuwa taci gaba komai na tafiya normal, Feenah da ummi sun zama aminan juna, ba wanda keji kansu a school,feenah ba karamin yarda da ita taiba Dan har fenah ta fada mata sirrinta,


Ummi ta kwantar mata da hankali akan tunda abun ya wuce tayi hakuri amma tayi kokarin fadawa Mama gskiya, Har ummi na tsokanarta akan in bata fadaba duk randa tazo seta fadawa mumy,

feenah tace huh rufamun asiri plz swt frnd!, shine Ummi tace ta dena daukan numbern Sags kar ya sake yaudaranta again.,

feenah tace nima tsoron da nakeji kenan



"Akwana atashi ba wuya Yau feenah ta tashi da ciwon kai dan a kwanakinan ba wanda ya gane kanta duk ta rame ta kwantsame, aka kaita asibiti, Harda Adam Da ALHAJI umar dasu Anty Samira da Zainab...hankali kowa ya tashi dan ba karamin tsorata sukai ba da sukaga yanda ta Koma..... Alhaji umar ne ya fita yace bari yaje ya dawo,
Sukace Okay,
*SORRY READERS a GURGUJE* Da fitarshi Adam ne ya tsugunna ta yace Dan Allah ku saurareni zanyi magana, Sukace munaji,

Nan ya fara ce musu suyi hakuri ko wani bawa da abun dake samunsa arayuwa, Gaban dai mumy se dukan uku uku yakeyi, Nan ADam ya basu labarin abun daya faru da feenah From *A To Z* amma suyi hakuri, basu sanar dasu tun daga farkoba,

Nan maimuna ta yanke jiki ta fadi se kuka takeyi,

Samirama ta rikice tacewa Zainab ta duba waya zataga numbern anty larai plz ta kira musu,

aiko ana kira bata dde sosai ba tazo, itama ta fara kuka taje ta jijjiga feenah takai mata mari,
maimuna ma ta tashi ta kara kai mata mari,

Dakyar Adam da Samira suka lallasheshu akan sui shuru yanzu idan Alhaji yaji kumafa,

ayi shuru a rufa mata asiri dan Allah,

Nan maimuna kuma ta danyi tinani tace hakane kuma, duk lafinmune, da muka barki, dan duk mace tana bukatar Uwa a kusa,

Anty larai ma Tadanyi jum tace eh hakane kiyi Hakuri feenah, Allah ya baki lafiya, itadai feenah na

kwance ga ciwon kai ga tsoron abun da zata tashi Ai mata duk taji dama ta mutu....

Anan dai suka samu suka fito waje, aka bar feenah da zainab, zainab dai ba karamin tausayi tabata, tana bata hakuri feenah se kuka takeyi, Se anty larai ne suka dan tattauna akan kar abari alhaji Ya ji dan Allah, zasusan yanda za ai,


kwanan feenah 2 aka sallamesu suka dawo gida,

Nan maimuna ta fara nuna mata So da kauna, tana mata nasiha kuma tai mata fada sosai akan a kiyaye gaba,

Anty samira ma tazo ta kara mata fada akan aci gaba dai da hankali da maza...

Feenah Tace *Alhamdulillah* Dama abun dake damunta kenan a rayuwarta,

yanzu bata da wani damuwa bata da matsala, zata ci gaba da rayuwarta cikin Kwanciyar hankali, ta tashi taje tai wa Adam godiya sosai,

2days shuru shuru ba Feenah a school dan haka ummi yau takirata take tambayanta yayane, nan
feenah ke bata labarin abubuwan daya faru Ummi tace wow Masha Allah.... Naji dadi nima....

Yanzu ba wata damuwa ko feenah,

Feenah tace eh Alhamdlh, gobema insha Allah zanzo school sukai sallama,
❤❤ *A DALILIN SO*❤❤

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

*A golden fish has no hiding place*


*I proudly dedicated this page to you my Jinin jiki....Zainab Haruna 🐾Jaamxeey🐾 You mean so much to me*.. ```No One But You```*💋💋💋


® *HIKIMA WRITER'S ASSOCIATION*✍🏼

*© Ummiey Xeey Abakson*



Page
1⃣3⃣7⃣
Washe gari nayi feenah ta tafi school, Tun daga nesa Ummi ke hango feenah ta sauri taje tai hugging dinta ta kamo hannunta suka shiga Lecture Room,

nan dai suka danyi hira kadan, ummi ta kyalla feenah tace har wani kyau kikayi, feenah tace kai Ummi banaso fa, haka dai suka karata suka Gama hiransu har akai closing


feenah ta dawo gida around 4pm taji wayanta na ringing, ta duba taga Maryam

Feenah tai tsalle tace kawata ya kike ya kwana biyu,

"maryam tace lafiya lau se alkhairi,

nan dai sukai hira maryam tace zasu shugo kaduna gobe, kasancewar ranar Saturday ne,

feenah taji dadi sosai taje ta sanar da mumy tace Allah ya kaimu,

"maryam kuma suna gama wayan taje ta sanar da sags tace ta kirata tace Tananan Allah ya kaimu,

sags yace ok sai ki kintsa da wuri muje mu dawo kinjiko
* * * * * * * * * * *

Washe gari nayi feenah ta tashi da wuri tai abincin kala biyu, ta hada drinks, sannan tai kwalliya tana jiran frnd dinta maryam,


har zainab ta kira akan suzo su tarbata kawarta,

Su kuma su sags already sun kama hanya,

"Suna hanyane maryam ta kira feenah akan suna hanya....


Feenah tace Ohk. Basu dde ba suka iso Kaduna garin gwamna,

Maryam tace gatanan feenah tace ki shugo me gadi zai bude miki gate,

maryam ta shugo, da gudu feenah da zainab sukazo tarbeta sukai ciki,

Se murna feenah takeyi, suka rakata sukaje gaishe da Mumy da Adam, Yai tsaki yace Allah ya kyauta,


Nan dai suka shiga ciki su Uku se faman hira sukeyi kamar parrots, chan anjuma Maryam tace suzo waje sudan gaisa da wanda ya kawota,


Zainab tace dama bake kaadai bane, maryam tace Eh...

Suka wuce suka Tafi, Suna fita sags ya fito a motan da sauri kamar zai chafke Feenah,


Gabanta ne ya fadi yace dum!

Sags Yace nazo baki hakurine wallahi ba komai nake nema wajenkiba,

Hawaye suka zubuwa feenah ta kasa cewa koma,
ita dai zainab tana ganinshi tagane shine yai mata aika aika,


maryam dai se kara bata hakuri takeyi, Dakyar dai feenah tace ta hakura,

Sannan sags ya kuma cikin motan,

Ba feenah ba har zainab seda sukaji tausayinsa ya kamasu,

Zainab tace Allah sarki wallahi da alama ya tuba, hope dai kin yafemai har zuciyanki,

feenah tace na yafee, sannan suka shiga gida, Feenah tace dan Allah zainab karki bari kowa Yasan sags ne yazo dan Allah,

zainab tace haba sist wlhi ba wanda zaiji, nan dai suka kara kwantar wa feenah da hankali,

maryam tace zata tafi nan mumy ta hada mata shatara ta arziki, suka rakota har bakin gate,

sukai sallama, su sags suka kama hanya sai gida, Sannan zainab itama ta kara bata hakuri akan yanzu ai komai ya wuce, munawa Allah laifi yana hakura balle kuma mu.....


Feenah tace hakane, Sannan sukai Sallama, zainab ta koma gida,


*feenah* ce ta dakko wayanta tai ma sags Text kamar Haka, _Hello how ar you doing, Allah ya kaiku gida lafiya, thanks for the visit, Kuma inaso na fadamane Na yafema Allah ya kara yafe mana gaba daya, sannan kuma plz karka kara zuwa gidan mu, this will be the 1st and the last, kar ka sani cikin wahala_ Tai sending,


Sags ne yana driving yaje wayanshi yai kara alamun text ya shugo, Ya dauka ya karanta,

bt unfornunate bazai iya yin reply,

Yana gama karantawa Yaji kanshi yayi dum... Bt beyi reply ba, yaci gaba da driving,

ita kuma feenah ta rike waya gam ahannu tana jiran Taga reply shuru, shuru ba reply itama, Ta sake mai text _baka text dina bane ko_,

yasake karantawa bece mata komai ba...

Feenah taga text ya tafi ba reply ta fara wani kumbure kumbure wai wannan ai rainine,

ba sags yai reply ba se da suka koma gida ya huta sannan ya dakko ya sake karantawa nan yai mata reply kamar haka....

_Fatan alheri a gareki, dazu naga text dinki ina driving bt tunda kince haka ba komai... Zan ma chanza sim insha Allah bazan sake kiraba, Thanks for the good time we had when together, na fita hakkinki na baki hakuri bye.. Sai wata Rana Allah Ya kara tsareki, Yana sending ya kashe wayanshi shima da niyyar gobe zaije ya chanza sim_

too faa feenah na gama karantawa tace to ina ruwana dayafi maka......


Se washe gari ta dakko wayanta ko zaataga text ya bata hakuri by shuru,

Ta zauna tana tinanin texts din data mai be kamataba, Shine ta fara dialing numbern sags shuru shuru, be shiga,
taji kuma wani sonshi na shigaNta Azuciyanshi tana cewa Allah yasa dai ba chanza sim din da gaske yayi ba,

Haka tai ta kira shuru, har ta kira maryam akan meyafaru da wayan Sags, Tace naji kamar yana cewa zai saida wani abune?

Feenah tace are you serious,
Maryam tace wallahi da gaske nakeyi ko inmai maganane

feenah Tace No. Shikkenan!

Suna gama waya feenah ta tusa kanta a pillow tana kuka tana Allah yasa ba ba saida wayan yayiba.

Wata xuciya kume na cewa to ina ruwanki da sags kuma





















© *Ummiey Xeey Abakson*
❤❤ *A DALILIN SO*❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

```With all my fans i got a family again!!!, Much love padis```

💞 *Dedicated to Miss Xarah Mansur❤ ILYSM❤*


® *HIKIMA WRITER'S ASSOCIATION*✍🏼

© *Ummiey Xeey Abakson*👄





Page
1⃣3⃣8⃣
2 weeks shuru shuru ba text din sags, Kullun ta kira wayan Sags se taji switch off, Rannan dai ta daure tace bari ta kira Maryam Taji yaya wai da gaskene ya Saida wayanshi,



Tana daki ta kira maryam,
maryam ta daga Suka gaisa,
Feenah tace Frnd wai me yasa ma wayan Sags ne kullun na kirafa baya shiga plz ask him what's wrong tana magana A rude.........

"Maryam tace uhm Ai kinfi kusa da shi, Bari dai nakai Mai Ki tambayeshi da kanki,

Feenah Tace Ohk

maryam ta tashi da sauri ta Shiga Dakin Sags yana kwance Cikinshi namai ciwo Tana Shiga Ya hauta da fada yace ke meye haka, Banace in zaki shugo ki dinga sallamaba me ya faru kuma,


"maryam ta dukar dakai tace i'm sorry Bro, feenah ce tace tana son magana dakai, Kamar bazai amsaba kuma Sai ya amsa,

feenah najin duk abun da suke cewa! Tana mikamai ta fita a dakin,

feenah ce ta fara magana Tace "Hello
Sags ya Ce Wa'alaikis salam
feenah tadanji kunya dan tasan ba sallama tamai ba, ta dai gaisheshi, ya amsa dakyar dan cikinshi ciwo yakemai,

Feenah tace ehmmm Wai please me ya sama wayanki Tun ranar da ku ka koma,

"sags yace oh Bakiga text dina bane,
Feenah tace nagani bt inaso nayi confirming ne da gaske kake,

Sags yace yeah da wasa nakeyi ai zakiji wayan is On.

" Feenah tai shuru

Please Login or Register in order to submit comment