Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasancewa dani Nice taku Har abada...



















*Ummiey Xeey Abakson*
❤❤ ​​ *A DALILIN SO​*​❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

​​​​​​```We must let go of the life we have planned, so as to accept the one that is waiting for us ``` ​​​


❣ *Jingijar ban girma gareku Exclusive Writer's Association♻...*_​ _Mutanenah Allah yabarmu tare gaba day an mu, Alheri Allah yakai muku I So Much Appreciate All you do.....#ONE LOVE KAWAI_❣


® ♻ *EXCLUSIVE WRITER'S ASSOCIATION​​*✍🏼
♻ *E W A*♻


© *​Ummiey Xeey Abakson*💋



Page
1⃣4⃣6⃣
Naseer ne tsaye agun sunata hiransu,
Naseer ji yake tamkar a mafarki,

feenah taga lokaci na tafiya tace ya barta taje gida in yaso sai suci gaba da magana!

Hakanan naseer Ya barta amma besoba a xuciyanshi, yace tahau mashin din ya kaita gida......

Feenah dai dakyar tahau suna tafe suna hira har suka kawo gida sannan ya sauketa, ta shiga Gida shima yayo gida.


Feenah ce da shigarta gida Kallo daya maimuna tai mata tasan tana cikin farin ciki da walwala,
maimuna tace hmm Yau ya naganki se murna kikeyi, feenah tace wlhi mum ba komai yai mun gama exams se monday kuma,

Tai mata fatan alheri sannan feenah ta shiga daki tai refresh up...


Naseer kuwa yana zuwa gida ya je ya tadda Mumy samira ya gaisheta tace ina ka shiga tun dazu inata nemanka,

naseer yace hmm Mumy Alhamdlh kwanan nan zakui sirika,

maimuna tace Itama Alhamdulillah, ashe wajenta kaje, Naseer dai beyi maganaba,

Zainab na jinsu tace hmmm Su yaya an kusan zama ango a zuciyanta! Dan tasan meke going ita Zeee din...

Samirace tace a ina take
"zainab ce tai kararaf zatai magana Naseer ya harareta shine zainab tai shuru,

Naseer yace mumy very soon zaku ganta still dai muna dan daidaitawane tukunna,

mumy samira tace masha Allah, Allah yasa adace yace ameen Sannan ya shiga daki!


Naseer ne kwance a daki duk dadi ya isheshi Se cewa yake *I found her* shi kadai kamar wani tababbe,

ya lalubo wayanshi Ya kira Bash yake bashi labarin ai ya je...in takai ce makaba she accepted me!

Bash yai ihu yace *woww*

i'm so happy for you abokina, Ka tashi daga naseer ka dawo Ango,

Naseer yace hmm kaima dai ka samu ka lalubo mata mui aure,

"Bash yace inyee tun yanzu har an faramun gori inaga ka aureta..

Naseer yace LOLs na true i dey talk,

Bash yace naji Ya sunan nata, Naseer yace *_Feeeenaah Nah_*

bash yace manya har ta zama naka kenan naseer yace insha Allah sukai sallama!


Feenah ce a daki ta rike waya Gam a hannu se faman aika messages takeyi ana mata reply, Kana gani kasan da Naseer takeyi:.....


Adam ne yace sister inason magana dake, feenah tace ok Ya Adam ina jinka, Adam yace hmmm What's the secret naga kwana biyu kinyi kyau da alama ba damuwa a tare dake me ya sa hakan ne!!

"Feenah tace hmmm Ina wannan abokin naka dinnan wanda randa banda lafiya kukazo tare,

Adam tana fara magana ya tabbatar da Naseer take, Shine adam yace eh,

Feenah tace hmmm wai shine yake sona!

Adam ya zare ido xuciyanshi namai zafi amma hakanan ya daure yace *SO* fa kikace Feenah tace yes yace ma zai turo nice dai nace yadan tsaya tukunna,

Adam da karfin hali yace haba sist why not kice ya turo tunda kinsan problem dinki,

feenah ta dokar da kai tadanji kunya tace ok shikkenan zan fadamai,

Nan dai suka ci gaba da hira amma xuciyan Adam kamar zai fashe dan Yasan ba karamin cutar kanshi yayiba.... Yace mata bari yaje daki kafin Anjuma tayi....


Ya tashi ya shiga Dakin yana shiga ya kulle kofa ya fara kuka kamar karamin yaro yana cewa nashiga uku...l'm a loser, ya fara tuni ranar farkon maganarshi da naseer, yake cemai _he's no body a wajenta Ashe karya yamai he's everything a wajenta yanzu_ nan yaci kukanshi yace bakomai koda yake ni dakaina nace bazan auretaba kuma badan komai ba gani nayi bani na dace da itaba....

Yace kashh Amma na zalunci kaina tunda nasan feenah na Sona! Kiran magrib din da akai ne yasa Adam fitowa a daki ya shiga toilet yai wanka be sama daman zuwa masjid ba saboda kanshi wani irin ciwo yakemai, Dan yasan ya riga da yayi loosing din feenah har Abada sedai wani Ikon Allah!!!

Bayan isha'! Ne feenah taga Adam shuru bezo sunci abinciba yasa ta tashi taje dakinshi taganshi a kwance da alama beda lafiya, Da sauri tazo wajenshi tana tambayanshi yace mata bakomai baijin dadin jikinshine,

Feenah tace ah ah bari naje na fadawa su mumy da umma jummai suzo akaika asibiti gaskiya,

Adam ne yace NO, basai kin kirasu ba zansha magani ma insha Allah,

Feenah ta zauna tana kallonshi ciki da tausayi, Chan ta tina soyayyan dake tsakaninsu Tace Oh i'm sorry ya Adam nice na janyoma ciwon nan ko,

Adam Yai sauri yace NO,

Feenah tace kayi Hakuri na fasa auranshi kai zan aura,

Adam dole ya tashi yace da bakimai adalciba, Bayan kin amsa zaki aureshi, Baki tinanin yace ke mayaudarice ko yace ni na zigaki,

Feenah tace yace din ai kai nakeso tun Farko ba kowa ba!

Adam yace naji dai bt remember our promise nace duk abun da kikeso zan miki, ni yayankine kinga i'v to protect you kuma kinmun alkawarin kome na fada miki Zaki dingaji,

Feenah tace uhm Eh, Adam yace to indai nine ki kwantar da hankalinki insha Allah alherine,

kar ki damu, Nima very soon zanyi auran kinji kanwata,

Feenah dai dakyar ta yarda dan tace indai bazai dena damuwaba to yanzu zatai ma Naseer text akan su rabu,

dan haka dole Adam ya wartsake ya sake jiki sukai hira sosai da feenah duk da yana jin zafi a xuciyanshi bt hakanan ya hakura.........























*Ummiey luff*💋💋
❤❤ *A DALILIN SO​​*​❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

​​​​​```The Best and most beautiful things in the world cannot be seen or even touched they Must be felt with the HEART❤ ```

*I Proudly Dedicate this page To You Again!!! 💞Miss Zarah Mansur* U realy mean a lot to me in this world... ALLAH ya hadaki da alheri Kawar arziki💋💋💋💋


® ♻ *EXCLUSIVE WRITER'S ASSOCIATION​​​* ✍🏼
♻ *E W A*♻


© *Ummiey Xeey Abakson​*💋


Page
1⃣4⃣7⃣

*Washe Gari!!!* Friday Bayan sallah jumma'a Alhaji kamal Ya dawo daga abuja, Ya fita sallan la'asar kenan Suka hadu da Alhaji Umar shima ya dawo daga wajen aikinshi, Nan dai suka gaisa sukacewa junansu basu da kirki ga gida ga gida amma ba wanda ya damu adinga zumunci,

Alhaji Kamal yace kayi hakuri Alhaji Umar wlhi tun abun da ya farune dakai da matarka na tsame Hannu daga Harkokinka,

Alhaji Umar yai dariya yace Alhaji Kamal kenan Ai yanzu alhamdlh komai na tafiyamun dai dai,

Alhaji Kamal yace masha Allah ai haka akeso Nan dai suka dan tattauna akan su dinga zumunci,

ALHAJI kamal yace Ai matanmu sunfimu zumunci gaskiya,

Alhaji Umar yace eh gaskiya To inanan zuwa anjuma agidanka zan ci dinner insha Allah, nan sukai sallama kowa ya kama harkan gabanshi,

Alhaji kamal ne bayan ya dawo daga masallaci yakecewa matarshi ai yanzu ya hadu da Alhaji Umar yananan ma zuwa gidan nan anjuma wai anan zaiyi dinner, Samira tace ok badamuwa Allah ya kaimu anjuma, Alhaji yace ameen, Sai ki san abun da zaki girka mana!
Samira tai dariya dan tasan indai fannin abincine bata da damuwa!!




Su feenah kuwa ranar wuni sukai tare da Adam se bata hakuri yakeyi tun yanajin kishi Har ya hakura yadai ta bata baki akan ai suna tare, sbd ita yar uwanshine ta jini, dakyar dai ta yarda dan itama taso ta aura Adam ko nima naso ta aureshi...LOLz

misalin *7:30* ne Alhaji Umar yai sallama gidan Alhaji Kamal,

Nan Naseer yaje ya budemai kofa yamai iso har babban pallonsu, sannan Naseer ya tsugunna ya gaisheshi,

Kallo daya Alhaji Umar yaiwa naseer shima yaji ya kwantamai, a zuciyanshi, dan yaron yayine, daga gani akwai ladabi da biyayya,

ALHAJI kamal ne ya fito suka gaisa sannan aka kawo musu abinci sun taba hira kadan sannan suka zauna suka ci abinci,

bayan sun gama suka dasa hira daga inda suka tsaya,

Nan Alhaji umar ke cewa dama kanada yaro babba haka, Alhaji kamal yace eh ai yaron matatace data rasu shine babban dana, sunansa naseer,

Alhaji umar yace masha Allah, Allah yaji kanta su kuma Allah ya rayasu,

ALHAJI kamal yace ameen Kai fa yaranka nawa,

Alhaji Umar yace yata dayace tun daga nan ban sake haihuwaba, Sunanta nafeesa,

Alhaji Kamal yace masha Allah, Badan badan ba dana hada auransu, da yarka, Dan inaso Naseer yai aurene kafin azumin nan!

Alhaji Umar yace ah ba matsala indai sunasan junansu ba damuwa ai tunda an riga an zama Daya!

"Alhaji Kamal yace ok bari dai na kira samira matata ai agabanta tukunna!

Kamal ya dauka waya ya kira samira akan cewa tazo,

Samira ta tashi ta dakko hijabinta har kasa sannan ta nufa pallown Alhaji, Tana zuwa ta gaishe da Alhaji Umar ya amsa,

Nan Alhaji Kamal Yace dama inasone a hada auran Naseer da yar gidan kawarki Maimuna wato Nafeesah!!

*SAMIRA* tace to Amma dai ku tsaya mugani wazai dakko, dan jiyan nan mukai magana dashi Akan cewa ya samo mata, dama ina jirane ka dawo mui maganar aje gidan iyayanta a nema izini,

Alhaji Kamal yace au au au hakane, Gaskiya bamu Zauna ba tunda nadawo to shikkenan Bari mugani kafin mu yanke namu hukuncin,

Alhaji Umar yace ah to shikkenan na, Ai mu duk iyayanshine kowaye ya dakko indai ta mana Alhamdlh....

Nan samira ta tashi ta barsu su Alhaji sukaci gaba da maganarsu!


Ba Alhaji Umar yabar gidan ba se 10Pm, Alhaji Kamal ne ya rako Alhaji umar har bakin Gate sannan sukai Sallama!


Alhaji Umar ne ya shiga gida yaga duk sun kwanta, ya shiga dakin matarshi har ta fara bacci ya tasheta,

Maimuna taji haushi sosai dan a tinaninta alhaji neman Aure yakeyi dan be sanar da itaba ga inda zaije,

Alhaji Umar ne yaga fuskar matanshi duk a daure yake tambaya me ya faru,

tace mai bakomai ina kaje Haka,

Nan Alhaji umar ke bata labarin ai gidan Alhaji Kamal yaje sai yasa be dawo da wuriba ya bata labarin duk yanda sukai har alhaji kamal nacewa kodai za a hada auran feenah da naseer ne Samira tace yace ya samo mata mujira muga zabinshi in beyiba se a chanza,


Sannan maimuna ta sakko daga fushin da take, Tace to Allah dai ya ba kowa me alheri, *Nima nace wanda suke neman aure yan mata da zaurawa Ya Allah ka hadau da mazaje nagari* Ameen ya Allah


Sannan yace ba bacci zasui ba, su tashi suje pallow yanaso ya kalla wani news a bbc, hakanan ta tashi taje ta dakko mai abinci yace ai yaci gidan Su Alhaji Kamal

tace eh nasan zakaci ai wannan na matarkane kaci ka samun Albarka,

Alhaji umar yaci yace wow yai Dadi gaksiya, Allah dai ya saka da alheri matata,


Tace ameen Thanks mijina.........!























*Ummiey Xeey Abakson*💋
❤❤ *A DALILIN SO​​*​❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

```​​​​​​​The Best prepation for tomorrow is doing your best Today ```

💞💞💞 ​​_*​Dedicated to Ruksad & Amnoor all for Ummiey xeey Novels group*_​💞💞💞

*We Love you so much cos munajin dadin yanda kuke manah​​*​💞💞💞


® ♻ *​​​EXCLUSIVE WRITER'S ASSOCIATION*​​​✍🏼
♻ *E W A*♻


© *​​Ummiey Xeey Abakson*​​​ 👄


Page
1⃣4⃣8⃣
Bayan kwana biyune Alhaji Kamal yace Samira ya naji shuru bayan kincemun Naseer ya sama mata,

"Samira tace alhaji kenan dadine dakai gaggawa, nima abun da yacemun kenan bt mu jira muka zuwa ending din this week,

Alhaji Kamal Yace Kinsanni idan naso abu,

Samira tace uhm Nasani amma mu samai ido mugani kaji kar ka karamai magana kasan Neman aure is not Easy...


Alhaji Kamal yace oh Hakane kamar yanda nasha wuya wajen nemankiba,

Duka sukai dariya,

"Naseer a daki a kira feenah a waya yace yananan zuwa, batai mai musuba, tunda Adam ya bata hakuri, tace inanan ina jiranka,

Naseer yace ah ah bafa gida zanzoba why not muje bayan layinmu bansan asan nine!

Feenah tace ok duk sanda ka shirya seka kirani,

naseer yace yanzuma a shirye nake,

yace ok sai naganka, yace ok mu hadu akwai awajen yanzu,

suna gama waya feenah ta tashi ta shirya ta dakko hijabinta har kasa tasa,

tacewa mumy bari taje gidan anty samira ta dawo, Mumy tace ok sai kindawo,

Ta fito Allah yasa Adam be tsakar gidan dan tasan ko yayane yaganta he will feel some how! Aiko ta fita bata tsaya ko inaba se inda sukai AP da Naseer su hadu,

Aiko tana zuwa ta sameshi shi already har ma ya rigata zuwa yana zaune yana jiranta, Ta karaso ta gaisheshi kowa dai yayi shuru, chan dai naseer ya kalleta yace kinyi kyau,

tace uhm Thanks, Nan dai naseer ya fara janta da hira kamar bazatai ba, har ta sake jiki sukai hira,

nan ya kara cewa ta bashi labarin rayuwarta,

Gabanta ya fadi a xuciyanta tana cewa huh this is the second time fa daya tambaya kodai yasan Nayi sex da sags ne,

ya katse mata tinanan da takeyi _Yace i'm all ears_

Feenah tace uhm sarkin son labari, Naseer yace eh Naji Dai inajinki, Nan ta kara bashi dsame labarin data bashi kwanaki still ta kara maimai tamai guy din nan da ya bata 200, tace inanan inamai Addua dan ya temake rayuwata, Allah ya hadashi da mata ta gari, dan mutun ne mai hankali!

Tana gamawa Naseer ya sake wani murmushi da it a kanta seda ta tsorata

taji ya tafa hannu yana cewa Clap for ourselves!!!!

Tace what is this kuma!

Yace Lolz Amma kinsan meye Tace ah ah,
Yace kice ALHAMDULLAHI, Tace *ALHAMDULILLAH*,

Yace burinki ya cika Allah ya amsa miki adduanki,

Feenah TACE how? I don't Get you,

Naseer yace idan na fada miki wata magana zaki yarda

Feenah tace why Not, Naseer yace nine guy dinnan dana baki 200 tun kina primary.

Feenah ta mike tsaya tace _NO_
bakai bane!
Bakai bane! !

Naseer yace wallahi I'm the one, kinji na rantse miki,

feenah dai tai shuru taji kamar abun amafarki,

Tace huh...Allah yasa abunda nake mafarki ya zama gaske,

Naseer yace ba mafarki bane dagske ne!!

Feenah ta kulle ido ta bude, ta mintsilan kanta taji zafi tace Ohh ALLAH,

*naseerrrrr* taji ya amsa,

Tace *ALHAMDULILAH*, Walhi bansan me zancemaba!!!

naseer yace hmmm IKON ALLAH KENAN, amma kinsan kafin ma naji daga bakinki seda na aiko zainab!!

Feenah tace hmmm lallema ka cika yawau, Allah dai ya tabbatar mana da alheri.

Nan dai ita feenah duk ba ahayyacinta takeba dan wani murna da nishadi taji kawai tanayi, ji take atasheta ace mata mafarki takeyi! Idan ko ba mafarki bane lelle ta yarda _Adduan da kake ma wani in na alherine tamkar kanka kakemawa!!_

Ganin yamma nayine tace zata tafi gida but ko ya ake ciki zasui waya anjuma

sukai sallama yai da ita tahau kan bike din tace ah ah dan tsoron haduwa Da Ya Adam takeyi...


Bayan minti kadan Naseer ya isa gida yana shiga ya sama zainab kanwarshi Akan tazo daki ta sameshi!

Zainab nata jin tsoro ko wani laifi kuma tayi; taje ta sameshi yace kinsan meye,

Tace ah ah a tsorace yai tsaki yace mtwee wai ke meye haka se kace kinga abun tsoro,

Itadai tace bakomai, Naseer ne yace naje na sama feenah kawarki mun gama magana!

Kuma confirm maganar da kika fadamun akanta gskiyane, Nagode sosai da kika temakeni zainab,

Sannan zainab taji wani sanyi tace bakomai,

zainab na fita ya kira abokinshi Bashir yake bashi labarin duk yanda sukai,

Abokin yace wow, Kaje a sa'a kenan

Naseer yace hmmm Kadai bari sukai sallama,

sannan ya kira Feenahn shi akan cewa Gobe zai turo da manya ai maganar Aure!!!














*Taku A kullun Ummiey Xeey*😘
❤❤ *A DALILIN SO​*​❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

```Put your Heart, Mind And Soul into even your smallest Act This Is the secret of SUCCESS ```


_Dedicated To exclusive writer's Association_♻


® ♻ *​​EXCLUSIVE WRITER'S ASSOCIATION​​*✍🏼
♻ *E W A*

© *Ummiey Xeey Abakson*​​ 👄



Page
1⃣4⃣9⃣
Da daddarane Naseer yaje ya sama mahaifinshi Yake sanar Dashi Ya sama Mata,

Babanshi Yace Alhamdulillah, a ina ne dan So nake Aje da wuri ai musu magana Dan Dama so nak kai Aure Naseer,

"Kan Naseer ne A kasa yake sanar da babanshi ai yar Gidan Alhaji Umar Ne,

"Baban yace me Kace, Naseer ya kara kwantar da murya Yace mai yar Gidan Alhaji Umar Ne,

ALHAJI kamal saboda Jin dadin maganar da ya fada Anan take ya kwalla wa matarshi Sameera Kiya yace tozo Taji mafarkinsa Ya zama Gaske,

" Samira tazo da sauri Ta sama waje ta zauna take cewa Alhaji lafiya Kuwa,

Nan Alhaji Kamal Yke sanar da matarshi cewa Nafeesa Naseer keso,

"Samira tace ALHAMDULILLAH, Amma naji dadi dari bisa Dari wlhi,

Alhaji Kamal yace nafiki Jin dadi...


Naseer kuma na jinsu azuciyanshi Yace hmm Ai nafi kowa jin dadi A rayuwata Wallah!!!

"Nan mahaifinshi ya katse mai tinanin da yake yake cewa Naseer, Nayi farin ciki Sosai, Amma dai da fatan ka sanar da ita cewa ta fadawa iyayanta Gobe zamuzo,

"Naseer yadan kara tsugunar dakai dan dama yasan Babanshi Dan dai dare yayine da sai yace yau dinnan agama komai,

"Dan Haka naseer yace ah ah zan sanar da Itane Dai yanzunan,

Naseer ya tashi Ya shiga Daki, nan babanshi se samai albarka yakeyi dan yayi dacen yaro mai hankali da natsuwa, kuma gashi ya farantamai Rai, zaiyi aure, kuma wacce baban keso zai auro!!


"Yana shiga daki be tsaya yin komai ba waya ya dauka ya fara kiran numbern feenah, Ringing daya ta dauka, yake sanar da ita Ta fadawa su baba gobe insha Allah za'azo maganar Auran su,

Feenah tace ba matsala insha Allah yanzunnan zan sanar dasu,

Naseer Yace ok To badamuwa! Sukai sallama

"feenah ce ta fito daga dakin taje ta sama mamanta take sanar da ita akan ta fadawa abbanta gobe zasui Baki,

amma bata fada musu cewa Naseer bane, Tadai ce mata wanda yakeson aurantane zai turo magabatanshi,

Nan mumy maimuna ta rungumeta, tace i'm very happy my daughter wallahi abun da nakeson Ji kenan! Sai yasa kwana biyun nan duk kikaga na damu So nake ki aure,

Feenah Tace uhm, sannan mumy maimuna tace Bari naje na sanar da mahaifinki dama gobe ba inda zaije weekend ne! Feenah tana dakin mumynta;

maimuna kuma ta tafi dakin baban feenah ta sameshi Kan sallaya yana sallah, Tadan jira ya idar take cemai Alhaji nazo maka da wata albishir, Ya gyara zama yace inajinki beloved,
"Tace in Allah ya kaimu gobe zamui baki, wanda yakeson auran feenah ne zasuzo, Alhaji ya kara gyara zama ya ce Alhamdullilah, Amma naji dadi kwarai A ina ta sama miji, Maimuna tace dan garin nan ne, ai gobe zamu ganshi insha Allah,

"Alhaji yace Allah ya kaimu amma naji dadi kwarai, Allah ya sanya Albarka,

"Maimuna tace Ameen,



"Agurguje Washe gari nayi alhaji Umar ne da abokinshi guda daya se Yayanshi Mal Sani a zaune a gidan suna jiran baki,

ADAM Kuwa tunda yaji labarin za ai baki ya tabbatar dasu naseer ne ba kowaba dan haka shi ko zaman gidan beyiba tun safe yace sunada meeting a office dinshi dan haka tunda yasa kai ya fita ba labarinshi..


Bangeren Naseer kuwa kiran abokinshi yayi, yace yazo Zasuje gidan yarinyar da yakeso tare dasu baba, Bash ko ya shirya ya garzayo, da naseer da bash da alhaji Kamal da Abokanshi guda biyu su 5 kenan

"suka Kama hanya sai gidan su Feenah, Suna shiga Da sallama Alhaji Umar ne yai musu iso har pallow beko lura da Alhaji Kamal ba kawai yasa kai gaba sukai cikin pallow, Aka gagagaisa, aka kawo musu ruwa da drinks, me dumbin yawa,

nan wani abokin Alhaji Kamal ke magana akan cewa dansu Ya gani yanaso, Se a sannan ne Alhaji Umar ya kara kallonsu Sukai ido hudu da Alhaji Kamal
yake cewa aww harda kai a ciki,

sukadai kara gaiswa, Nan wannan mutumin daya fara magana yake cewa yoo Ai Danshine ke neman Yarka,

ALHAJI umar yace badai naseer ba, Akace shine Nan Alhaji Umar ke hamdala yaketa jin dadin abun nan daya faru, Dan abun yamai dadi sosai ne,

sukadai yi hira sosai akace anason auran dan da 3weeks, Alhaji Umar yace badamuwa

Se mamaki Alhaji Umar yake tayi, Dan har ga zuciyanshi yanason naseer fiye da tinanin ku readers dan tun farkon ganinshi yaji kawai shi ya kwantamai a zuciyanshi dan mutun ne me natsuwa, nan dai sukai sallama,t Abun ba karamin dadi yai ma kowa ba!!


"Bayan sun tafine Alhaji yaje ya sama matarshi yake sanar da ita dan Gidan dai Alhaji Kamal ne naseer,

"Maimuna ta mike tsaya ta daga hannu tana kara godewa Allah daya cika musu burinsu,


*Adam* se dare ya dawo feenah tana ganinshi ta shige daki dan bata son taganshi kunya takeji ita gskiya,

Adam ne ya shugo yaje ya sama maimuna nan take ta bashi labarin ai yau wanda zai aura feenah sunzo ansa biki sati Uku,

Adam kawai yake yayi yaji kamar ya kwalla ihu amma ba dama, xuciyanshi wani zafi da kona yake mai, kawai yace Allah sanya Alheri ya tashi ya shiga daki ya zauna yai tagumi kwalla na fitomai yace shikkenan Kuma *A DALILIN* kin Furta mata Ina son ta gashinan zatai aure! Dole ya hakura da wannan kukan xucin da yakeyine haka har bacci ya kasheshi!!!











❤❤
❤❤​​ *A DALILIN SO​*​❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣


``` Happiness is Not Something You Postpone For the Future, It's Something You Design For The Present ```


_Dedicated To_


®♻ *​​EXCLUSIVE WRITER'S ASSOCIATION​​*✍🏼
♻ *E W A*♻


© *Ummiey Xeey Abakson*​​ 👄



Page
1⃣5⃣0⃣
Washe Gari Nayi maimuna ta kira autyn Larai take sanar da ita ansa bikin Feenah nan da 3weeks,

"Anty larai tai murna sosai Tace Allah ya kaimu, Amma hope dai yasan abun da ya faru da ita,

"Maimuna tace ah ah be saniba Wallahi, Nan anty larai tace mata to gaskiya ya kamata a fadamai dan kar Aje ai aure kwana daya biyu ya saketa ko ya aza yar iska ce, Alhalin *A DALILIN* So ne ya rinjayeta,

"MAIMUNA na nunfasa tace To shikkenan Zan sama samirata mui maganar in yaso se asan yanda za ai,

"Anty larai tace to ba matsala nagode, Ki huta lafiya,
maimuna tace Ok,


*Feenah ce a school Allah Allah take ta hadu da ummi ta fesa mata ansa bikinta Nan da sati Uku, aiko suna haduwa feenah tace ma ummi albishirinki,

Ummi tace goro, Feenah tace ansamun Rana da wannan guy din da kika Gani,

"Ummi ta mike tsaye tace Wow ar you serious,

"Feenah tace wlhi i'm da gske nake, Ummie ta dafa kafadar kawarta tace _hmm Bana fada mikiba, Ki manta da wanchan yanzu ba gashi Allah ya miki zabi na gariba? Kici gaba kawai da addua, Kema yanzu gashinan kin sama wanda yafi ma my Number 1 iya soyayya_

"feenah tace kai ummi ya akai kika gane Ummie tace uhm Kedai kawai bari ki shiga daga ciki nasan zakusha soyayya kamar ba gobe,

Feenah tace hmm Ummi kenan nifa tsoro nake ya gane ni

Please Login or Register in order to submit comment