Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jego yace a a Please abarmai matanshi sedai A dakko wata tsoho, dakyar anty larai ta yarda dan ba yanda zatai ne yasa tabarta, Anty larai na zuwa akai akai tana kawo mata kayan gyra ta hade sosai Kamar ba itaba, suka ci gaba daga inda aka tsaya sunata soyayyan gwanin sha'awa hmmm se wanda Yagani..... ```Marasa Aure ya Allah ka fito musu da mazaje na gari, Masu auran kuma ya Allah ka kara dankwan soyayya a tsakaninsu, Masu neman Haihuwama ya Allah ka BASu ```............ *Ameen*👏🏻👏🏻👏🏻
❤❤❤ ​​​ *A DALILIN SO* ​​​❤❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣

*Wannan page nakune, mar'atus saliha da ladies world novel.Allah yabar So da kauna*

© *Ummiey Xeey Abakson*

Page
4⃣6⃣➖5⃣0⃣
Akwana atashi Ba wuya yau *NAFEESAH* ta cika 2years, tayi kiba tayi bul bul don tana samun cikkken kulawa wajen Beloved parent dinta, gata da wayau sosai, Mum dinta da dad Suka shirya mata wani hadaddan Birthday na musamma😘, Dan Dad dinta ya bata gift, anyi inviting yan uwa da abokan arziki duk sunzo na nesa da kusa *Naafeeh* tasha gift kala kala,

Bangaren iyayan Adam Kuma jummai tazo dan sedai Adam bai samo yazoba sbd he was in school akaima little sisternshi B.day Beji dadi Ba amma yace yana dawowa zai zo ya ganta......Adam yana son Yarinyar sbd kanwarshice, yana feelings dinta a heart dinshi, dan tunda aka haifeta Kawai yaji ta shiga Ranshi...... *ALHAJI UMAR MUSA WADA* komai na tafiya normal cikin natsuwa da kulawan Junansu, ga yarsu tayi kyaw gwanan sha'awa,

Alhj umar yana wayan jin faduwan gaba amma ya kasa sanin meke damunshi, dan ya chanza yana tinanan kodai wani abu zai faru ne nace Toofaa.......Akwai Wata Rana yana cikin shago gabanshi nata faduwa sega wasu mata biyu sukazo shagonshi, Dayan ta kyalla👀 taga alhaj, nan take ta kamu da sonshi, suga gama siyayya suka tafi, Ahaka ahaka suna yawan Zuwa shi besan meke ransu Ba, sun zama sosai dan sun zama costomers........

*Su waye wa ennan matan????*

Ba wasu Bane Illa hajiya *Rabi* da *Bibah*, suna fitowa haj bibah ta kalla haj rabi tace kawata wallahi sai na aura wannan mutun, haj rabi tace haba haj biba me zaki da wannan, Ae ance yanada matafa, Anan biba ta zare ido😳 tace To ina ruwana, Ko matanshi *4* ne dole daya ta fita na aureshi...kinsan in inason abu i'll do my possible best na samu ko tawani hanyane.....'A'uzubillah,...tace Rabi tai murmushi tace uhmm Ballema naji ance matarshi daya so kinga shiga ba abune me wahalaba, nan haj biba ta murmusa tace yauwa kawata, sai yasa nake sonki, Nan suka gama hirarsu suka tafi gidan tunda zaman kansu suke...idonsu a yage yake bama a bude ba lolz.....Nidai nace Wata sabuwa............! Yamma nayi alhaj umar ya dawo gida ya tarar da beloved wife dinshi na koyama yarsu karatu nan dai ya kara farin ciki da godewa Allah beyi zabam tomin dareba.....,magrib nayi alh yaje yin salla ya dawo ya siyo musu snacks suka ci suka dan taba hira, nafeesa tai bacci aka kwantar da ita, nan fa Alhaji da beloved dinshi suka baje suka fara sarrafa junansu.........A bangaren Hajiya biba kuma kullun se Tayi mafarkin alhaj umar tanaji idan batayi da gaskebabazata aureshiba, Nanfa itada kawarta sukai shawarar yanda za su bulluwa abun dan....nan dai kawarta tace indai kinaso ki mallekeshi dole fa se kin hada da malamai, yanda za a karkato miki da kanshi....suna gama shawaran suka mike, sai wajen *hatsabibin Bokansu* A tinaninsu ta hanyar zasu mallakeshi.......````Wa'iyazubillah```

*MATA* _Mu rika jin tsoran Allah, ba abun da boka zai maka illa yaci kudinka kuma koda asirin yayi tasiri na wani dan lokacine......_

*Comment Only*
*08164640126*
❤❤❤ *ADALILIN SO*❤❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣

*Love you all masu bin novel dinnan Allah ya cikawa kowa burinsa na Alheri*


© *Ummiey Xeey Abakson*
*08164640126*

Page
5⃣1⃣➖5⃣5⃣
Suna isa wajen *HATSABIBIN BOKANSU☠* yai musu umurni da su zauna suka sama waje suka zauna
yace Me ke tafe daku Haj biba tace Naga wanine kuma Ina son Na aureshi shine nazo ka temaka mun.....
Yai kyakyale😈 da Dariya
"yace aikine me wahala dan Za a cusa mai sonki a zuciyanshi, amma zaki bada kudi me dumbin yawa,
"tace bakomai indai bukata zai biya ba damuwa bane, nan ya fara musu Wani siddabarun su na bokaye, Ya basu wani *Hatsabibin Tilare*
Yace da zaran zakije wajenshi sai ki shafa, ammafa se kin tabbata zaki ganshi in ba hakaba duk wanda kika fara karo dashi To shi zaki aura Nan gabanta ya fadi tace a xuciyanta ta shiga Uku🙆🏻.....
setai tsit yace yaya kikai shuru ko da wahalane;
"Tace a a zan daure yace tooooooo, nandai tace tagode yace kece da godiya.....
"zata mika mai kudin kenan ya daka mata wani tsawa yace ba aban kudi a hannu, idan zaku fita zakuga wani gwangwani babba a ciki zaki ajiye, tsoro duk ya kara kamasu....
suka tashi suka tafi, sunyi yanda ya umurcesu dayi..........

Gidan su jummai kuwa ''Adam Yau ya dawo daga school saboda Sun sama hutu, ya kwana biyu kenan su maimuna da alhj umar da yarsu nafeesa suka kawo musu ziyara, Adam yafi kowa Jin dadi, Jummai ma haka ta hada musu abinci lafiyayye dan murna tayi da ganinsu, Adam ya dauka Nafeesa yaje ya siyo mata Su sweets da ice cream, se dadi takeji sosai cos she realy likes Kayan Zaki.....Ya kama hannunta suka dawo gida...suka gama hira sukace a yau zasu Tafi sbd Nafeesa tana da school gobe balle Su kwana,
Nan dai Adam be soba don *Adalilin Sonda* yake mata seda yaji dan Wani iri a xuciyanshi, Amma ba yanda ya iya, haka suka gama hiransu suka dawo gida Kaduna....🚗🚗



😍😍😍😍😍😍😍😍😍
❤❤❤ *A DALILIN SO*❤❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣


© *Ummiey Xeey Abakson*

_I dedicated this page to you my Twin Sister Faida simple... Much love_💋

Page
5⃣6⃣➖6⃣0⃣

*Alh umar* Yau Yai sallama da beloved wife dinshi zaiyi tafia dubai inda zaije ya siyo wasu kaya, beloved dinshi ta rakoshi har bakin gate ita da nafisat,
"Feenah Tace dady kar ka tafi ka barmu zan bika, yai mata murmushi😊 yace ok baby nah, bazan dadeba zan dawo, ta langwabe kai tacee ok.
Dad yace me zan siyo miki,
"tace kayan dadi da kayan Wasa yace ok my dear
Ya kalla😍 matarshi wandata tai kwalliya tai kyau yace *beloved* to zan wuce, TACE OK *safe trip*, har ya juya zai tafi kuma sai ya dawo, yace mata
*_I LOVE YOU PLEASE TAKE GOOD CARE OF YOURSELF DA SWEET BABYN MU;_*

_TAce never mind my love, take care of urself too_ yai murmushi yai mata kiss a goshinta, Ya fita a harabar gida, *Nafeesa* tace laaa, Mumy dad ya maki kiss a goshi, Tace eh kar na sake jin kin fada Haka......
Yana Hanya seya tina da ya manta wristwatch dinshi a Shago, yai sauri nufa shagon, ya bude da sauri da sauri kar yai missing flight dinshi, 👀Ashe su hajiya bibah suna labe suna jiran isowarsa, suna ganin ya bude hajiya bibah, tai sauri ta ciro *Tilaren da bokanta ya bata,* ta shafa a jikinta, suka nufa shagon da saurinsu, Sukai Sallama ya amsa kanshi na kasa dan yasan muryan masu magana,
"yace aww Hajiyas ne da kansu da safennan "Beebah tai kararaf tace eh wallahi wasu kaya mukeso,
"Alhj umar yace Ok, bari na kira wani yazo ya baku sauri nakeyi, yanzu haka tafiya zanyi,
"Beebah Ta kara sanyaya muryanta tace haba Alhaji muma sauri mukeyi sai yasa muka fito da saurinan,......Dole ya maida kallonshi gareta, kawai sai naji Alhaji na cewa *INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJIUN*.....biba tace lafia kuwa Alhaj yai karfin hali yace ba komai dan shi a xuciyanshi suna hada ido yaji ya fara Sonta se satan kallonta yake itako se wani iyaye takeyi, Nan dai duk jikinshi yai Sanyi yace wani kaya kukeso ta fadamai, ya ciro ya basu, Hajiya rabi dai tana gefe tace Lallai kam, haj beebah bariki, Ji yanda ta maida Alhaj yanzu yanzu,.....sukai sallama suka kama hanyan gida..
❤❤❤ *A DALILIN SO*❤❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣

_Na sadaukar da page Dinnan gareku amina juna..Sadiya da nafisa *SADNAF*_❣

© *Ummiey Xeey Abakson*❣


Page
6⃣1⃣➖6⃣5⃣
*Alhaji* dai suna fita yai wani sokoko dashi a tsaye shi be zaunaba shi be tafiba, ya fara tinanin kawai so yake ya aureta dan tayi mai, amma matsalan daya shine taya zai fadawa beloved wife dinshi, shi ko aranshi ma be san zai kula wata maceba balle ya kara aure, dan maimuna ta gama mai komai, tana bashi kulawa, infact itace farin cikinsa a kodayaushe,
Haka dai har jirginsu ya tashi shi yana shago yama kasa tabuka Komai, yaga rana tayi ne yasa ya kulle shago ya nufa gida duk a a rikice dan So yake ya aura hajiya *beebah*, yana hanya ya kira matarshi gashinan dawowa tai mamaki sosai tace Alhaj meya farune, yace bari na dawo gida ya kashe wayan, Suna gama wayan Ta tashi ta daura mai girki ta hada mai drinks kafin ya dawo, ba'a jima sosai ba se gashinan ya dawo,
Tamai sannu da zuwa takaimai ruwan wanka, yana fitowa ta shafa mai mai, ta bashi abinci sannan take tambayanshi wata matsalarne yasa be tafi ba, nan dai yai mata karya yace bejin dadine, sai yasa be sama tafiyan ba, nan dai tamai sorry yace bari yaje ya kwanta ya huta yana shiga dakin Ya Kunna A.C se bacci, ita ko gabanta se dokan *UKU_UKU* yakeyi tana tinanin me yasama Alhaji be taba dawowa hakaba, hankalinta yadan tashi amma batace mai komai ba, ta tashi tai alwala tai sallah ta rokan ma mijinta Allah yabashi lafia ya yayemai abun dake damunshi,
Nafeesa kuwa time din da babanta ya shugo tana bacci, tana tashi la'asar tayi mamanta ta shirya ta ta tafi islamiya dan batasan ma dad dinta ya dawoba.....
*Bayan Sati Biyu✌,* Beloved wife dinshi dai ta rasa gane kan mijinta, Baya fita office, har yar rama yayi, amma kullun seya fita da dare yana zuwa wajen budurwanshi haji *beebah*, dan yanzu sun saba har exchanging📲 number sukayi suna ta soyayyansu amma a boye, idan beloved ta tambayeshi sai yace, wajen abokanshi yake Zuwa Sai Tace OK bata kawo komai a rantaba dan a tinaninta haka yafi akan yai ta zama gidan yau sui fada gobe ai wasa, Amma ta dage da addua sosai, dan al'amarin alhaj tsoro yake bata Sosai, sedai tai addua tace Allah ya yayemai abun dake damunsa🙏🏻

Love you All💋
❤❤❤ *A DALILIN SO*❤❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣


© *Princess Ummiey Xeey*


Page
6⃣6⃣➖7⃣0⃣
Alhaj umar dai ya chanza yanzu baya ganin kowa se matar da yakeso ya aura wato beebah, Yan uwanshi da abokai ko, kowa ya rasa gane kanshi Har yayanshi *MAL Sani*, idan ya kirashi be dauka balle kuma kanwarshi sadiya, tun abun na damunsu amma har kowa ya Saba, dan Al'amarin Saishi, haka matar dai take ta hakuri bata fadawa kowaba duk yanda take da Anty larai amma bata fada mata ba in banda Mal Sani yayanshi bata fadawa kowaba, sedai yai ta cewa tai hakuri........
wata rana se Labari...tace hakane, Addua ta dukofa Sosai........
wajen su haj kuwa murna sukeyi sosai dan yanzu sunsan sun kama alhaj a hannu, Dan har ya amince zai aureta ba tare da yayi shawara da kowa ba cos *munsan Bayin kanshi bane asirine*.....
```Allah ya kyauta, Allah ya kara tsare mana imaninmu amin``` Akwana atashi ba Wuya yau Watan alhj biyu a gida, maimuna na zaune tana addua, nafeesa already tun 8 tai bacci saboda gobe monday,
Sega alhaj ya shugo da fara'a Yai sallama itama ta amsa, ta gaisheshi yace ina babyna tace tayi sleep kasan gobe monday yace oh Yes..... ba karamin farin ciki ya bayyana a fuskar taba,
"yace beloved wife ki kawomun abinci,
"Tace uhmm Sweetheart wata rana,
" yace eh naji dai ki kawomun kizo ki feeding dina,
"ta tashi cikin natsuwa taje ta dakkomai ta bashi suka gama hiransu a xuciyanta tana mai Godewa Allah daya ya dawo mata da kan Alhaji.....
suna gama hira yace suje su kwanta..............

Suna shiga bedroom alhj umar ya rungumeta ya fara mata wasu maganganu masu kashe jiki, dakyar suka samu suka hau gado, ya kara rungumeta yace mata I missed you,
itadai se uhm take cewa, shi ko se ai ka mata da sakon ni yake, "tace zata kwanta plz ya barta,
yace mata haba beloved rowa kikemun, tace a a, yakai mata kiss💋, Yace ki tashi kiji dama inason mui magana dake, Tace ok ta tashi suka fuskanta juna, Yace beloved inaso na kara Aure, hankalinta a tashe ta mike tsaye hannunta a kirji tace *WHAT* beloved aure fa kace yace yes,
"ki natsu plz mui magana, dakyar ta zauna, baccin da takeji nan take ta nemashi ta rasa, ta kalleshi tace nama laifine da zaka kara aure, ko inama wani abun da bakasone yace ko daya beloved yace nima auran ne yazo mun unexpected banyi tinanan kara aureba kinsan aure nufine na Allah,
Tace hakane, nan wasu hawaye masu zafi suka fito daga idanunta😰,
❤❤❤ *A DALILIN SO*❤❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣


© *Princess Ummiey Xeey*

*Thanks Masoyana INA samun sakonku wasu sun kira wasu sunmun text in godiya Sosai Allah ya hadamu a Aljannah*🙏🏻


Page
7⃣1⃣➖7⃣5⃣
yace kiyi hakuri dan Allah, ita ko ina hankalinta a tashe yake taci kuka ta godewa Allah, Alh se bata hakuri yakeyi amma ina.....
*_​Nace dole ki kuka Ba kishiya bane bamaso, bamusan waye za a auro mana ba se yasa da yawa mata hankalinmu ke tashi in munji bayanin kishiya....lolz kuma kishi wajibine​_*
dakyar ya lallasheta tai shuru, alhj umar kam yakai London wajen bacci dan baccinsa yake ta sha, ita ko ta tashi cikin dare, tai Al'wala tai sallah ta kara rokan Allah, Allah ya hadata da kishiya ta gari, nace Ameen....
Washe gari nayi bayan ta tashi ta hada breakfast Nafeesa ta tashi taga babanta harda tsalle, ta gama cin abinci yakaita school daganan ya wuce shagonshi......
Suna fita ta hada kai da kafa ta sake sabon kuka Sosai, tayi kukanta ma'ishi sannan ta *kira anty Larai da baba Alhaj* da sauran yan uwanta ta basu labarin akan alhj zai kara aure, hankalinsu ya tashi sosai dan sunsan ko yayane se an cuta maimuna dan tanada hakuri sukace tayiwa mijinta biyayya dama ai maza *4* akace mutun ya aura in yanada hali kuma zai iya adalci, suka dai kwantar mata da hankali tace ok to bakomai.......
Nan neighbour dinta ta kira *samira* aminiyarta ta fada mata, ta tausaya mata dan tabata labarin duk daya faru kwanaki tace tayi hakuri ai gwanda kishiyar ciki akan na waje, nace sosai.....Allah dai yasa mudace *Amin*

Life moved on......Akwana a tashi ba wuya dan *YAU NE* take daurin auran *ALHAJI UMAR DA MATARSA TA BIYU HAJIYA BIBAH*..... kawayen maimuna sukazo dannar kirjin uwargida shiko gogan naka nachan ana ta fama da abokai....ita ko amarya bakya laifi, tana nan tare da kayanta gogaggu yan duniya se Chasu akeyi ana mata kirari, amarya bakya laifi, kanta se kara kato yakeyi ana iyayi irin na gogaggun matan nan...gasu ba wasu shekaruba amma idonsu ya riga ya bude, aka gama taro lafia....Dare nayi aka kawo amarya, tare da kawayenta anan suka kwana se kara ziga biba sukeyi akan cewa kar tai mata da wasa,

Hmmmmm Duniya rawa ta yanmata
❤❤❤ *A DALILIN SO*❤❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣



*```Wannan page din nakune, maryam deeyanah💋, Aisha yar amana, da Samira Abdullahi love you all```


© *Ummiey Xeey Abakson*


Page
7⃣6⃣➖8⃣0⃣
Washe gari nayi kawayen amarya dama ansanku da gulma😜 lolz...aka zO ganin part din uwargida, nan dai ta amshesu hannu bibbiyu tare da kawarta samira, suko gogaggun se kallon dakin suke sunga yafi na Amarya kyau ​ *Adalilin son da babanta ke mata ya cika mata kaya da daki*​ suka gama jefa magaganunsu basu ce musu komai fa, suka gama felekensu suka kara gaba.....Samira *tace Ikon* Allah....
Maimuna kuma ta fashe da kuka tace ta shiga uku🙆🏻,
Nafeesa, tace mumy whats wrong wa ennan ne suka saki kuka, samira ta kalla nafeesa tace common keep quite, je daki ki jirani ina zuwa, ta tashi ta tafi,
Samira da dafa kawarta tace Haba maimuna, karkiji komai mui ta addua, Duk tsanani yana tare da sauki, be strong plz kawata, Allah na tare da mu...... *Nace sosai* kam
_dan duk wanda ya rike Allah walhi, Shine me riba a zaman duniya,,_ tace hakane, ta tayata gare garen Gidan yamma nayi ta tafi gidanta tana cewa aranta Lallai se maimuna ta dage da addua dan daga Gani wannan ba kishiyar arziki Bane,.......
😰Ita dai maimuna har ta fara tausayin kanta dan tasan Za ai drama ne ba kadan ba..........👀👀👀👀👀
Kawaye kowa ya kama gabanshi, Alhaji umar ya hadasu waje daya yai musu nasiha akan su zauna lafiya beson wani tashin Hankali, Maimuna tace karkaji komai Alhaji, yace eh maimuna nasan banda matsala dake, bibah kiba maimuna girmanta dan itace gaba dake, Ta wani yatsina fuska tace uhm, Alhaji, nima dole ta girmamani amatsayin Matarka, maimuna tai murmushi😊 tace karki damu anty Amarya, suka dan taba hira kadan amma beebah batace komai ba suka gama yace biba su tashi su tafi......har zasu fita sega feenah ta shugo falour tace *oyoyo dady, *ADALILIN SON* da yakema yarshi nan ya tsaya yai wasa da Beloved Doughter dinshi.......
haj ​Biba​ abun ya bata haushi ta gaji da tsayuwa tai side dinta, tace lalle ma, Har Alhaj na bata lokaci akan yarinya karama inaga mamanta,
nan ta kira rabi tace kinji kinji, tace kawata ki fara aiki da maganin nan a daren yau kar ki sanyafa, Tace ok ngd, Chan se ga alhj ya shugo yana amarya amarya....ahaha😀, tai maza ta shafa abun da *HATSABIBIN BOKANSU YA BATA*....alhaj yana shaqan tilaren yaji wani feelings ya kamashi nan take ya dauke amaryanshi se bedroom, nikam da gudu nabar dakin na jirasu a falour har gari ya waye lolz😜......
Washe gari nayi Alhj har gift yaba amaryanshi, Dan ta sashi farin ciki sosai.....
❤❤❤ *A DALILIN SON*❤❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣


*This page nakune Queen amina college__ my mate thunders Strikers Alherin Allah yakai muku* One Love Kawai💋💋💋

© *Ummiey Xeey Abakson*

Page
8⃣1⃣
Bangaren Maimuna kuma shuru ba alhaji ba alamanshi, 1week shuru, 2weeks ma haka shuru abun ya fara damunta sosai, sedai sui waya amma baya taba zuwa side dinta,
Nafeesa kuma kullun seta tambaya dad dinta sedai beloved tace mata Yazo tana bacci ko tana school Yazo, haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, alhji tun 1st night dinshi baya zuwa wajen maimuna, sedai tai ta addua....
Dan tasan abun nan akwai ​ *ASIRI* a ciki​ bata fadawa kowaba se Aminiyarta *Samira* dan Ko anty larai batasan meke faruba ba...samira itama ta dage da rokawa kawarta Akan Allah ya kawo karshen abunnan,
*Samira* tai tagumi Tace ikon Allah, Ni kingani Banzauna da kishiyata ba uwar gidana Amma nasan bazatai mun Hakaba......

Haka rayuwa ta ci gaban musu, haj *biba* ta riga ta gama asirce Alhj umar, dan kwata kwata yau shekara daya, yadena picking call dinta, ballema ya zao ta ganshi,
tun tana damuwa amma yanzu har ta dena ya bi mata jiki, dan kullun seta tino da *maganar iyayanta ​nabin mijinta sau da kafa​* taci gaba da addua dan tana samun kwanciyar hankali, matsalan ta daya shine, abincin ta ya kare tamai magana amma kamar ba da mutun take magana ba, Abinci kam sedai taje wajen samira, tanaci dan
*Nafeesa* dama already anty samira ta amsheta, dan Alhaj gaba daya ya manta yanada mata balle wata kuma yarinya ​Feenah​ dan tun randa Alhj ya nuna ma feenah so a gaban Haj beebah, taje tai asiri, akan ya manta da ita....
Tayi nasara kam dan ya manta dasu gaba daya.....maimuna kuma Abun yafi karfinta se *INNALILLAHI WA INNAILAIHI RAJIUN* take yawan fada....

Love you All...Readers da writers Allah yai mana albarka💋
❤❤❤ *A DALILIN SO*❤❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣

© *Ummiey Xeey Abakson*❣



Page
8⃣2⃣
*BANGAREN* gidan🏩 Mal Sani Kuma yayan Alhaj umar, Abun ya matukar bashi mamaki dan Rabonshi da dan uwansa harya Manta, Dan yanzu malan sani karayan arziki ta sameshi beda kudi kaman Da yanzu dillalancin da yakeyi Sai aslow, Dan ba wani kudi yake samuba, So Jummai Yau mafisan yau daban na gobe daban gashi badama tace ya saketa, Ko takai kara ba yarda zasuiba dan dama wan babanta ya riga ya mata kashedi karta kuskura ta kawo kara.........''Hmm mata kenan Idan zamuso mutun mu Soshi dan Allah bawai abun hannunshiba ko kyau, dan Komai Allah na chanzawa alokacin da yaso''....haka nan ta hakura dan ba yanda za tai, Yau asamu gobe kuma baza'a samuba, Shi kuma dan tilon dansu daya *Adam* secondary school yake be kawo karfi ba tukunna ko ya samu, na makarantarshi yake tanadawa.....rayuwa kenan...
A kasar senegal kumA Baba Alhaji ya kara tsufa amma kullun da tinanin yarsa yake mafarkai barkatai yakeyi akanta amma koda ya fadawa maman maimuna sai tace alhaji ba komai, tunda mukaji shuru nasan lafia lau, da akwai wani abu ko bata kirabuba zata kira Larai, kuma zata fada mana yace hakane, nan dai suka ci gaba da hiransu irin na tsofaffin Masoya....gwanin sha'awa..true love never end😘.....
nan na barsu bace bari na nayo kaduna na leka dakin *Beebah*😁 me alhaji lolz Ina daga labule naga beebah tasha wani shadda pink ta harda kafa tana latsa waya ta sake wani murmushi naga tayi dialing din numbern aminiyarta haj Rabi, tace hello
ta amsa da madan Ranki ya dade,
suka gaisa tace ya labari kwana biyu,
nan dai tace wlhi kam, Kinsan maganinan nan ba karamin aiki yamun ba dan Alhaji ya manta da wata mata,
tace very good ai nasan baki wasa da abunda kikeso tace yeah ashe kingane.... Sukai sallama,,...haka rayuwa taci gaba dai dan *maimuna* gaba daya ta rame ta kode abunka da hips da boobs duk tai wani iri sbd ba abinci mekyau, Bayan wata *4* kenan aka aiko mata da rasuwar mamanta,.. *kulli nafsin za'akatul maut*😭😭.....
hankalinta ya tashi Sosai tai kuka kamar ranta zai fita, Tazo side din haj biba tace alhj nanan tace eh, yananan...
haj biba ta juya ta kyalkyale da dariyan mugunta, Ta shiga ko kallon arziki be mataba, ta sanar dashi mamantane ta Rasu, yace Allah yajikanta, dan ko alamar damuwa beyiba,
Yace idan taga dama taje danshi ba inda zaije yanada abunyi sosai....
❤❤❤ *​A DALILIN SO​*❤❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣

© ​ *Ummiey Xeey Abakson​*❣


Page
8⃣3⃣
*SUBHANALLAH.......*
maimuna bata damuba dan macece me hakuri, sosai dan tasan bayin kanshi bane harda *asiri* a ciki, ta dawo daki jiki a sanyaye ta kira samira ta fada mata rasuwar mamanta, ta tautsaya mata, ta bata kudi sosai, sannan ta shugo gidanta ta kira Anty Larai ta sanar da ita rasuwar,
Washe gari nayi sega *anty Larai* nan gidan dan ta zone su tafi senegal din Tare,...da isowarta ta kalla👀😳😳 maimuna, ta jijjigata tace *Maimuna* lafiyanki kuwa, meka faruwa dakene, ba abun da maimuna takeyi inba kuka ba, kasancewar
*Da yake Samira* nanan Ne Tace Anty Larai is a long story ki bari kuje ku dawo zan sanar dake duk abun da ke faruwa, Larai ta juya kallon ​ *Samira*​ tace Waye ke Kuma........

*_Thanks for your time sisters...Nagode Sosai_*💞💞💞💞💞

_*SAMIRA* tace agurguje ni sunana Samira iyayena suna garin Katsina, a dalilin aurene Mijina *KaMal* ya kawoni kaduna inda muka zama makota da Maimuna, Alhaj Kamal dan siyasane sosai yanada mata daya amma Ta rasu, Yaran Alhj Kamal hudu, babban danshi, sunansa Naseer sai usman, sai autan dakinsu Zainab, yanzu haka ni yarona Dayane zayyad_,
_Naseer yana Abuja yana karatu don be cika zama anan ba, usman ma boarding school yake be zama sai Autan dakin maringanya Hindatu zainab, Ita munanan tare da ita se yarona kwara daya zayyad......kinji atakaice kenan_, Anty larai kuzo ku tafi dan lokaci na kurewa....Tace ok nagode sosai idan ko nadawo zan nemeki dan dole insan abun dake Damun yata..........nan sukai sallama maimuna se kuka takeyi ga bakin cikin Alhj ga Rashin mahaifiyarta......Sun isa sunyi gaisuwa kwana bakwai sukai agarin kowa dayaga maimuna seya tausaya mata dan tinanainsu rasuwar mahaifiyarta ce yasata haka, nan ko ba wanda yasani dan ko anty larai bazatace ga abun dake damuntaba..... Ana gobe zasu tafi kamar bazasu rabu da mahaifinta ba yace ina *Jikata feenah* duk angama gaisuwan nan ban gantaba tace tana wajen abokiyar zamana sbd school sai yasa banzo da itaba yace ok....ya Alhaji kuma, nan gabanta ya fasi sosai tace yananan zuwa aikine sukai mai yawa da tare zamuzo, yace ok, adai ci gaba damai biyayya ga Larai nan ki riketa tamkar ita ta haifeki dan kinga yanzu baki da uwa nima na kusan mutuwa...anan aka fara sabon koke koke sukai ma'ishinsu sannan suka hakura,.......washe gari suka kama hanya Sai gida nigeria✈..............

*Readers Weldone Allah yabar

Please Login or Register in order to submit comment