Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dedicated this page to you Hannah Aliyu, Maman tasleem, Maman mama_❣❣❣

© *Ummiey Xeey Abakson*


Page
1⃣0⃣8⃣

Sundawo gida *BAYAN KWANA BIYU*

"Anty larai ta kira samira a waya tace haba samira kwana biyu baki nememu ba ko lafiya,

Samira tace dan Allah Anty larai kiyi hakuri wallahi Zayyad ne beda lafiya har mun kwanta asibiti amma an sallamemu, kar in fadamukune hankali ya kara tashi dan nasan halin da muke ciki sai yasa,

"Anty larai tace Allah sarki ai da kin fada mana anzama daya yanzu ya jikin nashi, Samira tace da Sauki Alhamdulillah muna nan zuwa kwanan nan, Ya Jikin maimunan,
Larai tace da sauki har yanzu dai Se Ahankali, mungodewa Allah ma tunda ba makantar da ita sukai ba, tanaji tana gani,

Samira tace eh sosai ma, Alhamdulillah sai mun zo,
Anty larai tace Allah ya kawoki lafiya munje gidan baban maimuna chan senegal din, Samira tace kai Anty larai kice nazo gobe gobe wannan hiran bata waya bace gaskiya, sai nazo goben,
"Anty larai Tace Allah ya kaimu, Mungode Allah yai miki Albarka, tace Ameen sukai Sallama.

*Washe Gari* Sunday suna kan dining table suna break fast Alhaji kamal da iyalansa abun gwanin sha'awa, Naseer shi na kan kujera yana kallon T.V ana wani program a Arewa, Samira ta kalla mijinta cikin kulawa da Tsantsar So Tace Alhaji dan Allah inaso naje Ung ne na manta ban fada maba tun jiya, Alhji kamal yace a inane
"tace nan cikin kadunane,
"yace Ok badai ni zan kaikiba, tadan kalleshi irin na masoyan nan tace in baka kainiba wazai kaini,
Naseer na jinsu yai kamar besan anayiba, Alhaji kamal yace haba A a ga naseer nan yazo ya kaiki, yau hutawa zanyi a gida kinsan gobe zan koma Abuja aiki, Tace To ba komai Alhaji na gode Allah ya saka da alheri, yaran se kallansu sukeyi, zayyad ne karami yace laaa mumy Suna soyayya da abba; mumy samira ta dan bige mai baki,
"Naseer kuwa kamar yai dariya amma ya fuske dan beson susan yana jinsu, Alhaji kamal ne ya kira sunan _Naseer_ Yace zaka kai mumynku ung kaji, yace ok daddy ba komai, idan ta shirya ko yanzune se mu tafi,
Samira taji ta kara son naseer dan yarone me natsuwa da sanin ya kamata ya dauketa tamkar ita ta haifeshi, alhaji Kamal ma ba karamin dadi yajiba dan yasan yayi sa an Da na gari me natsuwa, Yace nagode My Son Allah yayi albarka, Allah ya hadaka da Mata ta gari, suka amsa da Amin dukansu;
shima duk da yanajin kunyar dadynshi seda yaji dadi Sosai aranshi Yace Allah nagodema da ka bani uba nagari me kaunata, me sani ahanya na kwarai.......

_WOW What a lovely and caring Family......._ ❣❣
Sungama cin abinci samira da zainab suka gyara gidan tsab sukai Wanka suka shirya; Alhaji kamal ya kalla matarshi yace kinyi kyau tace Thanks My Boss😍. Ai kwalliyan nakane, yace a a keda zaki fita tadanyi dariya, Yace bari na kira Naseer din nace kin shirya ya kaiki ya jira ya dawo dake tunda ba ddewa zaki ba, ya kirashi yace ok, ina tsakar gida bari na fito da motar, Alhaj kamal se samai albarka yakeyi....ta fito suka kama hanya sai gidan Anty Larai......
Da fitarsu Alhaji kamal ya kira yaranshi zainab da zayyad tunda usman benan yana school yace su dakko books dinsu na school yagani....Great daddy....👍🏻❤
❤❤​ *A DALILIN SO*​❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

"```Anyone who stops learning is old, whether at
twenty or eighty. Anyone who keeps learning
stays young. The greatest thing in life is to
keep your mind young.```

❣❣❣❣❣❣❣❣❣


_​this goes to my darling friend 🐾Jamxee🐾 thanks for d love baby I Luv u to the moon and back​❣❣❣_

© *Ummiey Xeey Abakson*

Page
1⃣0⃣9⃣
Suna tafiya ahankali tunda suka shugo Layin Gaban Naseer se fadi yakeyi, Dakyar yake driving dan shi kadai yasan Abun da yakeji, Anty samira tana sit na baya tana lura da yanda yake driving tace naseer lafiya kuwa ko an takura mane, yai sauri ya ce wallahi mumy a a kainane naji yanadan mun dum dum amma ba wani takura mumy, Har axuciyanta taji dadin amsan daya bata tace Eyya Sorry NASeer, muje gidan sekasha magani yace wa mumy ai ni bazan shigaba in munje zanjiraki a waje, Tace a a naseer gidan fa ba kowa,
kar yai mata musune tace Allah ya kaimu lafiya tace ameen, Sundanyi tafiYa kadan suka karaso gidan, naseer yai horn aka bude gate din, suna shiga ya sama parking space yai parking ya fito da sauri yazo ya bude mata kofa, ta fito se samai albarka takeyi tace ka zo muje yace no mumy kinsan bazan shigaba,
Tai tai dashi aiko yaqi shiga, Tace bari na tafi to,
"yace Ok, ya shiga motan ya zauna a sit din baya ya dakko wayanshi se danne danne yakeyi amma gabanshi se fadi yakeyi *_yana danna waya yana Hasbunallahu wa ni'eemal Wakil_*

tana shiga tai sallama se oyoyo anty larai da maimuna suke mata; sunji dadin ganinta sosai suka zauna suka bata ruwa tasha, suka gaisa, nan hira ta barke sunyi hira sosai, larai ta bata labarin tun randa kwanaki Mal sani ya kawo feenah abun tausayi, har kwana hudu da sukaje senegal, samira tace wallahi nima abun na raina, nace ya kamata muje mu fadawa Baba Alhaji abun dake faruwa, tunda kinje Shikkenan Allah dai ya bata lafiya sukace amin....
Chan samira tace yau nashiga Uku, tare fa muke da dan mijina Naseer, ku bani panadol nakaimai wallahi yace kanshi ke ciwo,

anty larai tace yana ina,
samira tace yana cikin mota wallahi yaron nada kirki kamar ni na haifeshi yakemun tadan basu labarin kirkinshi,
"Anty larai tace haba jeki kirashi mana ai muma iyayanshine, ya shugo mana,
"samira ta fito ta taddashi cikin mota yama dan kwanta a sit din baya ta bubbuga motan ya tashi,
yace mumy kingamane muje, Tace A a sunce suna son ganinkane kaga ya kamata kaje ka gaishesu koda wata rana
be mata musuba yace ok muje mumy, ya fito a motan Gabanshi se wani matsanincin fadi yakeyi ya bita a baya *TOOPAA*
suna Shiga Yai sallama kanshi a duke ya gaishesu yaji Mace daya ta amsa dayan bata amsaba ya dago kai dan ya kara gaisheta Kawai ya sauke idonshi a kan Maimunah yaji gabanshi ya Fadi *Duuummm!!!*

seyai shuru kuma a Zuciyanshi yana cewa _Like nasan me kama da wannan but i can't recall a ina naga fuskan_...

yana cikin tinanine samira ta katse mai tinanin
tace sorry Naseer wannan bata magana amma taji abun da ka fada, Ya kara kallonta at the second time still gabanshi se fadi yakeyi dole ya kara kallonta ya tausaya mata yai mata alamu da hannu Sorry Madam😄, Yace Allah ya kara lafiya......
"sukace Ameeen
Maimunah taji Son naseer ya shigeta dan ya mata sosai, Saurayine me natsuwa ga sanin yakamata, suka sa musu abinci yace bazai iya ciba, dan shi Kadai yasan abun da yakeji axuciyanshi.... Basu ddeba sukace zasu Tafi anty larai tai musu godewa Sosai itama sai samai albarka takeyi
yaji dadina ranshi sosai sukai Sallama suka kama hanya..... Ahanyansu na dawowane mumy samira take cemai Ita wannan da kaga bata magana kishiyace tasata agaba ta maida ita haka
Yace Allah sarki taban tausayi amma ya kamata adage da addua sosai Fa, insha Allah za a dace,
Samira tace *insha Allah*

*Ummiey Xeey Love*
❣❤❣❤❣❤❣❤
❤❤​​ *A DALILIN SO​*​❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

*Each person must live their life as a model for others*

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

_I dedicated this page to world ladies novel groups and African ladies group... Thanks for the love_

*© Ummiey Xeey Abakson*
❣❣❣❣❣❣❣❣

*Page*
1⃣1⃣0⃣

Sundawo gida lafiya, zainab da zayyad sunzo suna musu oyoyo, Alhaji kamal ya fito ya tarbesu, Yana masu sannu da hanya,

"samira tace Alhaji bani zakawa sannuba Naseer zakai mawa, Yana kokari sosai agidan nan Alhaji, suka shiga pallow dukansu suka baje a Pallow

"shi ko Naseer daki ya shiga Ya watsa ruwa ya hada ruwan lipton yasha sannan ya dauko magani Yasha, ya kunna Fanka Ya hau gado, Se tinanin matar da ya gani yakeyi, ya zurfafa acikin tinani sannan ya gane ashe matar daya gani kama take da wannan Nafeesan daya bata 200, Yace Ikon Allah; Gskiya suna kama, anya ba mamanta bane....Wata xuciya tace Ba mamanta bane, wannan matar daka Gani Ai tana cikin Wadata, Wanchan kuma yarinyar ai tana cikin wahala, Ya fada a fili kai ba mamanta bane, Duk uwa bazataso ta Bar danta cikin wahala ba sedai Ita ta wahala danta a cikin wadata...Nace kayi gskiya wannan....lOlz ya kara da cewa Kuma ita a zaria na ganta wannan kuma a kaduna...kai Is hardly ace mamantane......ya dauka waya yahau kan whatsapp bacci ya kamashi.

"Suko su sameera suna pallow suna ta hira da alhaji da yaransu abun gwanin sha'awa Alhaji yace zaiba naseer capital ya fara wani business din dan kar ya tsaya a aiki daya, samira taji dadi sosai, tace alhaji ni zan farawa naseer albishir, Yace aiko dankine sukai dariya

"ba naseer ya tashiba bacci ba se 5pm ya tashi yai alwala yai sallah ya roka Allah, ya azurta kowa dan beso yaga yara suna cikin wahala akwai tausayi.....

"Ya fito kenan Zai fita waje, wajen gidan wani frnd dinshi wanda sukai school tare, yai kicibus da samira a hanyar kitchen, yai mata sannu tace Naseer Albishirinka Yace Goro, Se kuma tace guess What, Yace badai daddy zai mun aureba, Ashe dady na bakin kofa yai dariya yace My SON tsoron aure kkeyi ko meye,

"Naseer yadanji kunya yace No Dady, bangama plans dina bane.....

"Sameera tace kwantar da hankalinka Dady ne zai baka capital ka fara wani business Din,
"naseer Da sauri yaje ya tsugunna wajen dad din ya fara godiya. Yace my Son karkaji komai, samira abun ya burgeta tace Masha Allah...

"Naseer ya fita wajen frnd dinshi *BASH* da yai niyyar zuwa ya bashi labari....

"Yana fita daddy ya shugo kitchen ya rungeme matarshi yace *INa SOnki Sameera*, nayi dace da Allah ya hadani da ke, Kema zan baki jari adinga miki ordern kaya...tai kai mai kiss💋 tace Thanks Alot mijina abun alfaharina, me zan dafa maka Yau, Yai murmushi yace kome kika dafamun Zanci.....
"Life continued, Haka Alhaji kamal suke gudanar da rayuwarsu gwanin sha'awa, magana daya biyu basayi sai an ambato Allah.....

*_yake yar uwa kema ki gwada ki gani, kidingawa mijinki biyayya, kuma kar ki musgunawa yayan kishiyanki, sannan kuma kome zaki kisa tsoron Allah a gaba...wallahi sai kin ban labari..* ALLAH YASA MU DACE_

*Ummiey Xeey Abakson*

*08164640126* ❣❣❣❣❣❣❣❣❣ LOVE YOU ALL
❤❤ *A DALILIN SO​​*​❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

```A blind person who sees is better than
a seeing person who is blind.```

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

_No one but you my drearest sister Hassana smasher thanks for d soyayya_👄👄👄

© *Princess Ummiey xeey*
*08164640126*
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

Page
1⃣1⃣1⃣

Kwanan su biyar *ADAM* be wa feenah magana da tana damuba har tazo abun bedamunta,

"Rannan dare nayi sagir ya kira feenah a waya ta fito sui tadi dama duk ta damu su hadu kullun se dai suyi waya da textx da chat amma basa haduwa, ta tashi ta shirya tasa wani kayan da ya sai Mata wani riga da skirt me tsantsi kusan ana ganin surar halittan mutun,

"Baba sani besan wainan da ake toyawaba tunda yanzu ba gidan yake gwanaba gadi yakeyi, ita kuwa umma abun da takeso kenan Taga feenah na kawo mata kudi duk da batai tinanin Wani abunba, Ta kintsa tayi kyau sosai ta fita ta sameshi a Mota,

"Ashe Adam na wajen, idonshi Na Kanta yana ganin time din data shiga Motan, Innalillahi kawai yake fadi dan ya tsorata yace shikkenan Feenah, Kasa zama a layin yayi yatafi chan saman layinsu ko zai danji relief a xuciyanshi,

"Tana shiga Sags yaganta ta hadu sosai tayi kyau ga lips dinta yasha lisptick👄, gashi tasa perfume Motan yadau kamshi,

"ya kalleta yace wow Bby love kinyi kyau😍 inama ace munyi aure yanzu da.....

"Tace uhm kadameni, Plz ka dena irin wannan maganar gskiya, in bazamui hiranba na Koma *Lolz*

"yace My Rigima baby kawai se bazan yaba kwalliyaba, *A DALILIN SON* da nake mikine fa Yasa Na yabeki ko bakiso na aurekine.......

"Tace Uhm inaso Mana Yace yauwa My Love, Ya yayanki tace lafiya Lau, ya akayine ya labari,
"Yace labari na wajen Yan mata, wai Kinaso na kuwa har yanzu banga alaman kina sonaba,

"Tai murmushi😊 tace ina sonka mana dankai nafitofa kuma nama kwalliya yace yes hakane suka dan taba hira kadan tace zata tafi yace ok Bye...take care sai munyi waya anjuma Tace Ok.....

Ta fito cikin Motar se gida...Shiko nan take ya kira abokinshi dinnan Yace aboki, na kusan yin wining Fa yace Allah ko, Yace ofcourse yace nasan dama baka Wasa......

ya ajiyan wayan sai Gida...

"Chan around 10pm Adam ya dawo da bacin rai ya banko kofar Umma yace Haba umma kuna gidan nan Za a batawa Feenah Rayuwa, umma na bacci tace dannan meya Faru, yace wannan sagir din nan nefa Yazo har suna tadi a mota Umma tace to ba har gida nan yazo yace zai auretaba kai ina ruwanka, Ba mutumin banzane ai bazaizo har gidaba, Shidai Adam yace Umma bakusan mazaba wallahi mu da muke fita munajin halayan mutane ku kuna gida yaushe zaku gani, dan Allah kusan dai yanda zakui ku rabata dashi dan ni ba ruwana, Umma tace to Naji ni ka kyaleni, bacci nakeji,

Haushi ya isheshi Ya koma daki Duk ya kosa safiya tayi babanshi ya dawo ya sanar Dashi, Washe gari nayi Aiko yaje ya sama babanshi ya sanar dashi Komai Hankalinshi ya tashi sosai yace Zaiyi mai magana da kanshi, Baba sani ya kira feenah yace tace wa Sagir yana nemanshi; Ta shiga daki ta kirashi amma yace kar yazo yanzu dan kar ai mamaki taya ta kirashi har yazo yanzu,

Chan anjuma nayi sega sagir yazo, baba sani ya kirawo shi daki shida umma suka nai maganan indai da gske yake tu ya turo, sagir yace baba da gske nake, Zan aura feenah kuma kudan bani lokaci kadan zan turo sukaji dadin maganan da yayi dan ko ba komai hankalinsu ya kwanta.........

sukace sun gode sukai sallama ya tafi gida
❤❤ *A DALILIN SO​​*​❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

*_This page nakune Matan Aljannah group, mu temake juna group na 🐾jamxee🐾, da matan arewa group, INA godiya sosai kwarai_*

© *Ummiey Xeey Abakson*

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

Page
1⃣1⃣2⃣

Yana komawa gida ya kira abokinshi dinnan kabeer Yake cewa Kasan meye,

"Kabeer yace A a

"Sags yace A gidan yarinyar da nakeso wanda nake baka labarinta dinnan, Akwai yayanta yasamun ido, har ya kai gulma wai zan bata musu yarinya ba auranta zanyiba shinefa suka kirani wani da gske nake zan aureta nace eh da gske nake,

" *Abokin sags kabeer* yace to gskiya ka chanza taku dan kar kazo baka cimma burinkaba gashi kana kashe mata kudi a ce baza a bakaba,

"sags yace Nima abunda nake tinani kenan Wallahi yanzu meye abunyi

"kabeer yace abunyi shine kai mata wayau kawai kadinga zuwa tadi da rana nasan zata sake jiki dakai daga nan se kasan yanda zakayi

"sags yace nagode my frnd sai yasa nake Sonka, sukai sallama,


*Adam* kuwa ko kallon feenah beyi yanzu dan ba karamain haushinta yakeyiba, Dan yasan Idan ba abata taba ana gab da bataba, tunda ta shiga tarkon Sags,

*1week letter* tunda su feenah sukai hutu, kullun se sags yazo tadi da rana, idan yazo sesu dade a wajema suke zama dan kar Wani ma yai musu Zargi.....

😜 *_Lolz to masu tadi a mota a dingayi ana lura da kula sosai dan wallahi wani ko bakuyin komai da anganku a ciki za a fara ma kallon dan iska balle ma Tadin dare cikin mota....ALLAH ya kara karemu_*

"haka suka ci gaba da tadin su da rana kullun, Ganin hakane yada Adam yadan rage damuwa kadan har ya farawa feenah magana,

"Rannan yace yan mata yau ba afita bane,

"tace uhm ya Adam kenan irin wannan tsuke fuska ni ai tsoron maka ma magana nakeyi wallahi, Dan naga abun naka azimun

"Ya kyalleta yace eh nasan abunda nakeyi ke macece bakisan yanda maza sukeji bane idan sunga yar uwarsu da namiji mara tarbiya,

ta zare😳 ido tace haba wannan wani irin maganane ya Adam, nidai bama komai Wallahi

"Ya bude baki yace wayasani ma ko kunayi dan ai ba zuwa zaki ki fadaba, nidai be carefull dan nasan yanzu ma maganar da nakeyi haushi nake baki ina zaginshi agabanki ku,

"ita dai feenah tace uhmmm "

yace yes, Dama nasani ai, yanzu duk maganan da zan fada bazaki yardaba, saboda soyayya ya rufe miki ido amma wallahi u should be very carefull, Tace to nagode, Yace Allah Ya kara tsaremu tace ameen, Nan sukai hira sosai kamar ba abun da ya hadasu har tana kawomai abinci,

"Ranar tare suka wuni har jummai na cewa tom and jerry yau ba fada kenan...sukai dariya

"yamma nayi kowa ya kama gabanshi, Ta dawo daki ta kira *Sweet Love dinta* tace dan Allah zata roka wata alfarma yace mene Tace, Ya dena zuwa gidansu Na yan kwanaki,

"Yace ok harda ranar ma tace eh yace bakomai gimbiya nasan matsalar

"tace meye yace Ba yayanki Adam bane ya hanaki,
"tace uhmmm yace yes nasani amma karki damu zamu ci gaba da waya da Text Da Chat tace thanks sukai Sallama,

"Suna gama wayan Sagir ya tashi zaune idonshi yai ja yace i know what to do...ba muna waya da chat ba....anan ne nasan zaki sake jiki dani sosai tunda An hanani zuwa gidansu...ya tashi yai wanka yace bari Anjuma tayi yau zan Plans Dina Zasu Fara Aiki akanki....

yai dariyan mugunta😆
❤❤ *A DALILIN SO*❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

```“All Our Dreams Can Come True If We
Have The Courage To Pursue Them”```
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

_I dedicated this page to duk masoyan novel dinnan A dalilin so❣ I LOVE YOU ALL_

© *Ummiey Xeey Abakson*
08164640126

Page
1⃣1⃣3⃣
Feenah Na daki akan gado taji wani wutan Son Sags se ruruwa yakeyi Axuciyanta

magrib nayi Tayi alwala ta shigo daki

Sags Duk ya kosa dare tayi, after magrib nayi, ya fara mata wasu Zafafan *lOve Text* mesa jikinka yai Sanyi

sedai ta karanta Tai smile, Tace my Swt love kenan,

"shiko yaji shuru batai reply ba ya kirata
"yace hello
tace Hii,
" yace Haba bby love kinga text dina ko reply, kinbarni cikin tinaninki ko,

"Tace i'm sorry ina jirane nagama addua, Nahau whatsapp mui chat tunda Bazuwa zakai ba,

"yace yes hakane, bt at least you hv to reply me nasan kingani ko, Ko ni kadai nake Soyayyata bandake,

"tace a a Hardani dont worry just giv me 30mins nagama komai....kar ka manta i'm yours fa,
"yai murmushi,

"yace Yeah....you re mine.....i'm yours tace haka yake sukai sallama

" Sagir suna gama waya Ya kunna data yasa wayanshi a chaji ya shiga toilet ya watsa ruwa yai alwalan ishai kafin cikon lokacin yayi, Har yaje yai sallaH yahau whatsapp shuru Feenah bata hauba, yai mata text kamar haka,
Hello Bby love,
good Evening,
How are you doing,
i missed you,
"shuru messages basu tafiba, kamar ze kirata kuma seya kyaleta dan tacemai nan da 30minuites ta gama BT yaji shuru,

"se chan after 50 minuites sega feenah *Online*, tana karanta text din tamai reply,
hi sweet love,
I'm fine,
I missed you more n more,

nan dai suka fara hiransu na Masoya dan Kunsan yanda akeyi LOLZ, chat sukeyi sosai,

"Around 10pm tacemai zatai bacci, nan dai ya fara magiyan wai ai ba school take zuwaba ta bari irin 11 haka, tunda ba komai takeyi a gidan ba,

It a ko *ADALILIN SON* da takemai Ta tsaya...

😳What Me zai faru next, Chan taga ya fara turo mata voice note da wani irin murya na sexy voice dinnan, wai dama suna tare, Shi duk ya kosa ai aurannan, this an that Dai,

" taga lokaci daya *Sags* dinta ya chanza yana mata wasu surutai kamar bashiba, da kyar dai Ta samu tace mai saida safe,

"Haushi duk yabi ya dameshi yace wannan yarinyar karfa ta rainamun wayau, Tana sauka ya kirata a waya, ta dauka yace meyasa kika sauka na dameki ko,
"Tace a a bacci nakeji wallahi,

"yace oh Dama in muna tare ashe kinajin bacci, ai inasha soyayyanmu takai matsayin da bazaki iya bacci seda izininaba...

"Tace no ba haka bane i'm sorry, i prms you gobe zan dade online muyi hira sosai,

yace are you sure tace yes sukai sallama,

"Ita Ko feenah hankalinta ba karamin tashi yayiba ta tino da maganar mamanta nacewa kar ta kuskura wani ya bata mata tarbiya, ta dena magana da maza inda san samune,, Nan taci kuka sosai tace bt nasan bazai batamaun tarbiyaba, wata xuciyata tace ya akai kika sani kedai kibi ahankali kawai, nan taci kukanta Ta godewa Allah,

*Washe gari* nayi tun asuba Ya tasheta da kira wai ta tashi Lokacin sallah yayi tayi addua sosai, Allah ya kawo musu ranar auransu, Ranar wuni tayi a daki dan Adam bayanan sun tafi gona da baba Sani, Sunci chat kamar me, Da rana yana ta mata kalaman soyayya harta manta da maganganun da yai mata jiya da darrade, yau Ma sukace 8:30 zasu hau online aiko time nayi kowa yahau suka fara aikawa junansu da texts na masoya,

"chan taji yace bby love kina kwancene ko Zaune,

bata dauka wani abun bane tace Ina kwance....

yace good. What Ar you wearing,

"Tace banganeba,

"yace yap nasan kingane me nake nufi to wani kaya kikasa.....

gabanta ya fadi dum tace Atamfa mana........Ya Kyalkyale da dariya hahahaha Yace bby Da Atamfa kike kwana tace yes meye..... LOLz


*Ku ci gaba da biyoni*

*Princess Ummiey Xeey*

*08164640126*

❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
❤❤ *A DALILIN SO*​❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

••••Move Out Of Your Comfort Zone. You
Can Only Grow If You Are Willing To Feel
Awkward And Uncomfortable When You Try
Something,•••••


❣❣❣❣❣❣❣❣❣

© *Ummiey Xeey Abakson*
_08164640126_

Page
1⃣1⃣4⃣
Sagir Dariya yake tayi harda rike ciki yace haba sweet heart, kinfa girma, kin waye yanzu Kidena kwana da atamfa baki da kayan baccine,

Please Login or Register in order to submit comment