Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan bata da abun da zatace, Yace shikkenan maganar Tace Eh...
Yace ok Thanks, Sai anjuma ya kashe wayan,

feenah taji haushi wai dan me be tsaya sunyi Hiraba, itafa batason wulaqanci,


chan wata zuciya tace to bake kikace karya sake kirankiba to meye kuma na kiranshi ke, It's better kawai ki hakura da wannan sags din

Sags ya kira maryam ya bata wayanta yace duk randa ta kara kira, kika kawomun se na kusan ballaki,
Tace yaya meyai zafi....
Yai mata alamu da baki shiiiiiiiiii,
maryam ta fita sumi sumi.

feenah suna gama wayan dama in banda kuka ba abun da takeyi wai kamar ita sags ze ma haka, Allah Allah take monday yayi taje ta sanar da kawarta Ummi!

"Bangaren Su Samira kuwa Alhaji Isma'l ne tare da matarsa Samira, Suna zaune suna hira, yake cemata ashe abun daya faru da Makwancinmu kenan shekarun baya dasuka wuce

"Samiiraa Tace uhm eh Wallahi,

Alhaji Ismail yace Hmm ai Alhaji Umar bejin sha'wara ne sai yasa na rabu dashi, nifa rabon da mu hadu na dade gskiya dan most time bana zama,

Samira tace eh
Alhaji ya kamata dai yanzu aci gaba da zumunci

Alhaji yace Uhm Indai yanaso ai za'ayi kinsan ni a rayuwata Bansan mutun me yawan aure aure ahaka kake haduwa da masifaffa, Sai yasa nakeso yarana su biyoni,

Samira tai murmushi dan tasan tayi sa'an Miji kwarai da gaske, suna cikin hiran ne Sega *NASEER* ya shugo ya tsaya ya gaisheshu, Nan Alhaji Umar Yace ya zauna dama nemenshi yakeyi,

Naseer ya tsugunnar dakai Alhaji Isma'l yace Kaga kullun girma mukeyi ko Mumyn yara...

Samira tace eh Hakane Alhaji,




Alhaji yace to Naseer ka fito da mata da wuri kafin azumin nan gaskiya so nake Kai aure, Yoo wai ma me kke jira ne naseer, wanda basu kaika ba duk kowa yayi kokari yana neman aure wasu sunyima to kai me ka tsaya ne, Komai Allah ya wadace mu dashi To me ya hanaka,

Samira tace uhm Alhaji ka barshi mana, Aure lokacine,

Alhaji yace eh amma se kanada niyyar yi,

Naseer dai tunda yasa kanshi a kasa ya kasa daguwa dan yanzu wannan ne karo na biyu da daddynshi kemai maganar aure beso ya kara mai na uku gaskiya, Tunda yanajin maganar babanshi,

Alhajine yace tinanin me kkeyi bazakai maganaba bane, kaji dai na fadama ka nemo matar aure kafin azumi,

se asan nan ne naseer Yace Ok dady, insha Allah zanyi kokari na nemo Amma da zakaban zabinka inaso,

Alhaji yace ah ah, Ka nemo da kanka wacce tai maka,

Samira dai na jinsu dan ta lura da gske Alhaji so yake Naseer yai aure,

Naseer yace ok Insha Allah, yace bari yaje gidan abokinshi ya dawo, sukace ok,

da fitashi samira tace haba Alhaji kabi dan nan ahankali mana,

Alhaji yace yo me nai mai, Aurene Nasan shima yanaso yayi, kinga ai gwanda yayi,

Samira tace eh hakane Allah ya hadashi da mata ta gari dukace amin,



*Naseer* ne ya fita a rude dan yasan this time around babanshi da gaske yakeyi
_Yana tafiya yana tinani yana cewa Ya Salam Cikin wata ukun nan da suka rage ina zan sama mata nifa har yau banga matar datai mun ba_...

yana tinani tinanine har ya samu ya karasa wajen Abokinshi Bash..... Da bash yaganshi yasan dole akwai magana akasa dan ba yanda ya saba ganinshi ya ganshiba, Bashi se tambayanshi yakeyi wai lafiya,

naseer ne yace mu shiga ciki please maganace mai muhimmanci,

suna shiga Nas ya kalla abokinshi yace kasan Meye Wallahi dady ne yace na nema matar aure kafin azumin nan kuma ni bansan wa zan nemaba,

bash ne ya zare ido yace da gaske kke Abokina, *Naseer* yace wlhi yanzu ni ta ina zan fara neman matan aure, Abokinshi yace calm down abune me Sauki, ina wannan yarinyar da kkeban labari kace ka ganta a zariya, why not muje mu nemata in Allah yasa rabonkane zaka Samu,

naseer ya kalla abokinshi Yace haba yanzu kusan 15yrs fa, tun a *L.E.A* zariya fa naganta yanzu ko naje ina zan ganta kaga plz muyi mai yuwuwa...

Frnd din Nas yace eh hakane, Kuma, gashi banda little sister bare na baka....

Naseer yace nasani karka damu, yanzu dai dole na mike,

haka sukaci gaba da hiransu har yamma tayi, Nas ne yace bari naje dare nayi sukai sallama sannan ya tafi,

























*Ummiey Xeey Abakson*❤
❤❤ *A DALILIN SO*​❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

_​​share your smile with the World, It's a symbol of friendship and peace_


*​I proudly dedicated this page to you NAFEESAT ANKA* _Muaahh_❤​❤❤

```Allah ya kara tsareki```


® *HIKIMA WRITER'S ASSOCIATION*​✍🏼


© *Ummiey Xeey Abakson*👄



Page
1⃣3⃣9⃣
Naseer ne kwance a gado se tinani tinani yakeyi, Yaga tinanin nan ba abun da zai mai se dai yasa kanshi yai ciwo dan haka ya tashi yai alwala yai sallah yai addu'o'i sannan yadanji dadi,


ya koma gado be ddeba bacci ya kwasheshi. Yana cikin baccine yai mafarki _wai Gashinan yana zaune a harabar gidansu yana shan Iska, Se ga wannan yarinyar dai da yataba bata 200 naira a school L:E:A tana ganinshi tazo da gudu, Yace keee Dont touch my cloth tace sena taba, Ba kaine...............!_

yana zuwa nan ya tashi firgigib yana subhanallah.

Yadan natsu mafarkin yadawomai yace uhm Shaidan kenan, yarinyar da jiya abokina kemun magana kenanfa, to meyasa nai mafarkinta kodan na sata arainane, wata xuciyan tace eh mana da ita ka kwana axuciyanka dole Kai mafarkinta,

ya sake adduo sannan ya koma bacci be sake farkawaba se washe gari ya tashi da farin ciki da walwala. But besan *dalilin* hakan ba,

ya hada breakfast ya gama komai around 10am yaje wajen dsame frnd dinshi dai yake bashi labarin mafarkin,


Frnd dinshi yace Kai....Anya ba aljana bace daga maganarta har Kayi mafarkinta,,,

Nas yace plz ka dena bani tsoro plz, sukai dariya sukace zasusan abunyi har frnd dinshi na tsokanarshi kodai zasu jarabane suje zariyan....qila rabonshine,


Nass yace ah ah bazan iyaba....zan ci gaba da _searching_ anan nasan zanyi dace Insha Allah.........
* * * * * * * * * * * *




Bangaren Su ADAM kuwa, Akwana a tashi ba wuya, ADAM YA ZAMA babba a companynsu shine *manager* dan An sameshi da zuwa aiki kan lokaci da rike amana sosai, Dan haka kowa yai Na'am dashi gashi young guy ga son addini, kowa sonshi yakeyi.....

Dasu Umma sukaji labari ba karamin farin ciki sukai ba sosai,

Alhaji Umar da Dansu Adam suka hada kudi suka sai musu gida dan madaidaici kusa Dasu but kudin Alhaji Umar yafi yawa, Nan su umma suka dawo abun ba acewa komai Arziki ya wadata,

suma tun da sukaga Adam ya yi kudi suka fara mai fadan akan Ya nema mata gaskiya yai aure ban Baba sani yace bazai yarda ya zauna ahakaba dan yanada kudi, umma ma tace eh gskiyane Shi dai ADAM yace karsu damu indai aurene zaiyi.

*Haka rayuwa* dai ta ci gaba a kowani bangere yanzu Duk da iyayan Adam sun dawo Kaduna, Adam na gidan Alhaji umar dan yace yai zamanshi a gidan ba komai......

yanzu Adam da feenah bamejin kansu, Sun Dena fada bt sedai kusan kullun se tamai maganar Sags Sedai Adam yace to ta bishi mana.,

tun tanajin haushi harta Saba,

yanzu feenah tunda suka shirya da adam Ta rage zuwa gidan frnds dinta dama chan ba zuwa takeyiba,

zainab tayi naci har ta gaji, Frnd dintama Ummi na school tazo gidansu uncountable bt still feenah taqi ita beme son zumunci bane.................

*1 month letter* Feenah ne da ummi zaune a wani dan waje nashan Iska suna hira sega saurayin Ummi yazo, yasha wani riga da wando three quater, a bayan rigan an rubuta *Captain HABEEB* yayi kyau sosai, yazo ya samesu

Ummi na ganinshi ta fara wani yauki, tana shan shan kamshi yazo ya zauna kusa dasu,
Yace My num 1
"tace yes honey nah na saka shugowa school baka shiryaba ko,

"C HABEEB yace ah, ah ai kinsan duk inda kike sedai bansaniba ko baki kiraba sena biyoki,

"Itadai feenah najinsu ta sa musu ido, Se wani nunawa junansu so da kauna sukeyi,

Chan dai yace My num1 frnd dinki bata maganane,

"Ummice Tace LOLz Tanayi,
"yace shine ta zauna shuru ko mun takuratane,

" Ummi tace ah ah haka take batason hayaniyane,

"Yace ohh real Ajeboter kenan,

Ummi tai dariya 😀 tace ka cika tsokana ko Dear,

"Yace LOLz baki fada mata bane inada surutu,

"NAN ummi tace ta sake jikinta fa ba komai, Shi haka yake he's friendly ba ruwanshi wai ke dan frnd ditane,

"Se anan Feenah Ta sa musu baki Akai hira da ita sosai, yace kokefa amma dazu kin zauna kamar ba yar BIRNI.....dukansu suka kwashe da dariya....



Nan yace bari yaje ya samo musu wani abu suci kafin su koma Gida, Ya tashi cikin yanga irin na samarin nan masu jijjidakai yana tafiya kamar bazai taka kasaba yabar wajen.....

Ita dai feenah tace uhm Ikon Allah dama akwai maza haka,

"Ummi tace LOlz akwaisu mana!

Kinsan duniya makarantace sai kaga wanda bakai taba tsammanibe ita dai feenah tace tabbas kuwa,

Anan ne take bata labarin yanda sukai da *Sags*,

"Ummi tace mtsww Haba feenah da kyanki da komai zaki wani damu akan Sags,

Nace miki ki rabu dashi ki sake ranki Wallahi Allah zai kawo miki wanda yafishi


Feenah tace eh hakane, ai just na fada mikine yanzu I'm single, Ba ruwana da kowa,

Ummi tace ah ah, wani irin ba ruwanki da kowa Nasan baki samu bane,

Feenah tace Lolz M serious;

"ummi tai murmushi tace frnd kenan,

Feenah tace Ummi Soyayyan ku na burgeni Wallahi nima ina rokan Allah ya hadani dame sona;

Ummi ta kalleta dan ba karamin Tausayi ta bataba, dan ta lura feenah mace ne Meson Ta sama Caring wajen Guy..

Ummi Tace Ameen, Karki damu my besty nasan zaki samu, mace kamar ki,

Feenah tai dariya tace Ummi banda zolayafa,


suna hakane sega C Habeeb Da ledodi guda biyu daya na drinks daya na snacks, Ya bude bayan motanshi ya dakko wani Dan daddoma babba kamar carpet yace kuzo nan ku zauna....LOLz ummi anata iyayi ita ko feenah duk kunya ya kamata, suka sauka akan kujerun da suke suka zube a kasa suka kwasa gara, suna gamawa ya kaisu gida ya fara sauke Feenah a gida sannan ya wuce da ummi itama ya ajiyeta a bakin gate...... LOLz!
















*Much Love My Lovers*
❤❤ *A DALILIN SO*❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

```Hosnesty is the Best Policy```

*Dedicatad to Dija Waziri and Sadeeya S Adam* 😍❤👄 💞


® *HIKIMA WRITER'S ASSOCIATION*✍🏼


© *Ummiey Xeey Abakson*👄



Page
1⃣4⃣0⃣
Haka rayuwa taci gaba bangaren kowa da kowa, Komai Normal abun sha'awa ko wani family suna cikin kwanciyar hankali da wadata,



*sags* Kuma yanzu yama manta da wata feenah Dan yanzu ya tafi yin wani course a india, dan ya koma school ya dena runs din da yakeyi,


Feenah ma itama tuni ta manta dashi dan Adam na ebe mata kewa sosai dukda dai ba soyayya sukeyiba, bt yana faranta mata rai sosai, Dama Sun saba Sun shaku,



"Yau Saturday. Zainab ce atare da kannanta da yayyinta Naseer Da Usman se kaninta zayyad, suna ta mata tsiya wai duk cikin gidan tafi kowa celebrating birthday duk year, ta kalla yayanta usman tace to ni ba mace bane, ko ya Naseer,

Naseer shidai bece musu komai ba.. zayyad yace ya Usman Bari naje na ebo ruwa na watsa mata gobene birthdayn ta,

usman ya biyemai yace oh yeah daka kyauta kuwa maza katashi ka tafi da sauri mui mata wankan birthday,

zayyad ya fita usman ya bishi shidai Naseer na jinsu,

ganin sun fitane Zainab tace ya Nas bari plz bari naje gidan frnd dina yanzu zan dawo, yace ok a dawo lfiya,

Su Zayyad suna fita suka hadu da daddy yace in suka kuskura suka jikamai Kakanshi Zainab sai sun sani...
Dan haka suka dakata!!





feenah ne zaune a daki tana chating da ummi dan bayan zainab feenah bata da wata kawa da ya wuce ummi,

Tana zaunene sega Zainab ta shugo ta tadda Adam a cikin palour ta tsugunna ta gaisheshi

tace yaya Adam feenah nanan,

Ya dago kai ya kyalleta gabanshine ya fadi Dan shi a gskiya yana Sonta bt tsoron fadawa feenah yakeyi karta shiga damuwa dan yasan feenah bataqi ta aura Adam Ba.....

Yana fada mata ta tashi ta shiga cikin dakin, Adam ne ya kara binta da Kallo.


Tana shiga ta tsaya a bakin kofa tace sister wlhi baki da kirki, yau weekend ko kizo kiji yayane kuma na fada miki gobene birthday dina ko,

feenah ta kyalleta tace to almasifatu ai kya shugo ko kuwa, kin wani tsayawa mutane a bakin kofa,

"zainab tace lallema yarinyar nan kin iya wulakanci dan kina chating da saurayinki shine zaki cemun haka ko,

"feenah ta sakko a gado jin abun da zainab ta fada ne tace uhm Wlhi da ummi ne ba wani saurayi, har zanyi saurayi baki saniba bane,

"Zainab tace eh mana tunda yanzu yaushe rabon da ki shugo gidanmu dan Allah,

"Feenah tace sorry swt sist muje toh bari na kashe data,zainab tace ok muje,

feenah ta dakko hijab dinta ta tsaya gaban dressing mirror tadan shafa huda tasa litstick tai kyau sosai tunda dama ta hadu.......

"Zainab tace uhm Beauty kenan,

"feenah tace LOlz naji dai muje,

"suna fitowa suka tadda Adam a pallow Yace sai ina kuma,

Feenah ce tace Gidan su anty samira zamu Yaya, zamui cake ne da sauran abubuwa kasan gobe Zainab zata cika shekara .............!

"Zainab ta bige mata baki,

tace ya Adam karyane,

"Adam yai smiling yace oh shekarun ne ba'aso muji ko yayane,

"Feenah tace tayi girma sai yasa bataso kaji,

" Adam Yace LOlz, Sai kun dawo a jiyema mana cake dinmu,

sukace ok ai naka daban ne yayai sukai smiling suka wuce,



"feenah na fitowa taji gabanta na fadi har take cewa zainab wlhi kinji gabana se fadi yakeyi,

"Zainab tace matsoraciya ba komai duk rashin son zumuncin ne, sudai suka wuce cikin gidan anty Samira,

suna shiga ita suka fara gaisarwa tunda dady be dde da fitaba, su usman kuma suna waje shida Kaninshi Zayyad,

Sannan suka zauna a palour, Feenah ta gaishe da *Naseer* bt ko kallonta beyiba ya amsa, Suka tsaya kallo,

*Nas* ne ya juya zaiwa Zainab magana akan me sukeyi Anan su wuce ciki mana,


Kawai me zai gani idonshi ne ya sauka Akan *FEENAH* gabanshi ya fadi but ya dake ya kara kwallonta,

A zuciyanshi yace ha'a Ba wannan bane wanda na gani rannan a bakin kofar gidan nan,
Ya dukar dakai ya fara tinanin,

Zainab ce tace yaya Naseer, kaga feenahn da nake baka labari nan, wanda take nan makotarmu, wanda muke yawan zuwa dinnan,

Yace Oh sannufa,

sannan ta juya kan *feenah* tace kinga wannan shine babban yayanmu, sabd rashin zumunci irin naki baki sanshiba, yanzu kin ganshi ai koda wata rana,


"Feenah tadanji kunya ta kara gaisheshi, Duk ita dai taji she is not feeling confortable a wajen tacewa zainab sudai su shiga ciki,

Zainab tace ok, sannan suka shiga,


Suna shiga feenah tace haba *Xeetah* ya zakimun baran barama haka tun yanzu yasan banda zamunci,

xeee tace to kinadashine, Lolz

Ashema ba dadi dazu zaki fadawa ya Adam shakaruna,

"Feenah tai dariya tace oh Kin rama kenan,

' Zeee tace Lolz Eh

Suna barin wajen shidai Naseer gabanshine Yadan lafa da beating, yace Huh.... Bt kamarfa Nasan yarinyan nan, yanata tinani tinaniine shine, suka fito suka wuce kitchen zasu fara shirye shiryen Hada abubuwan Birthdayn xee,

dan haka yana ganinsu ya tashi ta Tafi Daki,

Yaje ya bude laptop dinshi ya fara kyallan wani Film dan Kar tinanin yamai yawa!













































*Muje Zuwa*
❤❤ *A DALILIN SO*❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣


```There is Nothing on earth more to be prized than true friendship... Much love my Fans Allah yabar So da kauna💞💞💞💞
```
❣❣❣

💞💞 *Dedicated to PRINCESS UMMIEY XEEY NOVELS GROUP💞💞*


®✍🏼 *HIKIMA WRITER'S ASSOCIATION*✍🏼


© *Ummiey Xeey Abakson*
_+2348164640126_



Page
1⃣4⃣1⃣
Sun gama hada komai na bithdayn harda cake, tunda dama anty Samira ta iya,......


Sannan feenah ta dawo gida ta kawo ma adam cake din da sukai ta hada mai drinks tace wannan nakane babban yaya kai zaka fara ci kafin kowa Yaci....


Adam yaji dadi sosai dan yasan confirm Feenah na sonshi bt Bazai iya bane kawai! Nima bansan meyasaba.


""Washe gari nayi Tun 8 feenah taje gidan aka gyara komai a kai decorating wani bangare a cikin gidan yayi kyau sosai abun gwanin sha'awa,

Sun gama shirya komai sannan feenah ta dawo gida dan ta dan huta har baccin tayi kafin 3 yayi a fara shagalin birthday...


Ba feenah ta tashiba Sai 2 tana tashi taga time ya tafi haka tai maza tai wanka dama bata sallah so se ta sama time din data zauna tai kyalliya iya kwalliya, na yan matan zamani!

Ta dakko wani Riga nata pink colour da ratsin blue a ciki, rigar duguwace bt kobaka da shape se ya fidda ma ita,

tai kyau iya kyau sannan ta dakko gyalen kayan sky blue ta talalki shima sky blue ta saka tai kyau masha Allah.....


Sannan ta fito taiwa mamanta sallama, Mumy ma tace itama gatanan zuwa yanzunnan,

feenah na fita se kunya takeji dan tasan se an kyalleta se Allah Allah takeyi kar Allah Yasa taga naseer yace da yake bithday ne tazo Amma in zumuncine batason zuwa!

Tana shiga sidif sidif tana tafiya ahankali dan hill ta saka tana tafiya ahankali zata shiga dakin Zainab kenan, Aiko Sega *Naseer* ya fito daga dakin mumy sukai kicibis a hanya,

Duk tabi ta rikice, Shiko naseer se smiling yakeyi dan yaga tai kyau sosai,

sannan ta gaisheshi murya na rawa,

Naseer ya amsa, yai wucewarsa

"ita ko ta nufa dakin zainab se zumburar baki takeyi,

tace zeee bazan kara zuwaba wallahi, kinsan duk inda naga Ya Naseer se naji kunya,

Zeee tace me ya faru, feenah tace ba duk ke bace kin riga kince banda zumunci yanzu yace da yake birthday ne na iya zuwa ko,

zee tai dariya tace ai gskiyane,

"Feenah tace naji dai ai dagayau ma bazan kara zuwa gidan nan ba,

"zeee tace Ahab basai kin fadaba nisani,

zainab tace kinsan meyene,

"Feenah tace ah ah,

zainab tace Wallahi u look so gergeous kinyi kyau sosai,

"feenah tace uhm naji nidai ki shirya time is going,

zee ta shirya shap shap ta sako irin kayan Feenah sak dama Anty Samira tasai musu sukai kyau sosai kamar yan biyu,

suka fito tare tsakar gida ya ciki da yan uwa, se frnds din zeee dai dai, suka fito kowa se daukansu hoto yakeyi,




shidai naseer yana gefe yana kallon ikon
Allah
tunda dama zee mutumiyarshi tace plz kar yayi missing, dan shine birthday dinta na karshe a gidan tace kafin wani year ya zagayo tayi aure,

suka zauna aka fara sa Wakan *Happy b.day to youuu,* yara sai bi sukeyi suna jin dadi,
tunda dama ba haihuwa anty samira keyiba kuma ba aure aka tabayi a gidan ba, Abun yama yara Sugar sosai,

akasa waka da rawa feenah tadan juya taga ba wanda takejin kunya a ciki tadan taka,

ashe ko Naseer nata gefe har vedio yai mata bata saniba se rawanta takeyi.

Akazo yanka cake feenah ta kama mata hannu suka yanka tare, anata daukansu hoto, kowa se cewa yake Like *TWINS*

dago kan da feenah zatai kenan Taga Naserrr ya kashe musu hota,

yana dauka yabar wajen,

"feenah duk kunya yabi ya kara kamata tace O.M.G, wannan guy din lafiya zaizo ya dauke mutane hoto. Tai tsaki

tadai manta da abun se shagali aketayi, akaci akasha aka watse Alhamdulillah,


Feenah ta koma gida da kayan bithday, nan ta tarar da Adam da mumy dan ta rigata komawa gida, tace Adam kanwarka batada kunya har rawa seda tayi....

Adam ya kwashe da dariya yace laa Ashe kin iya rawa, mumy ma tai dariya tace abun kunya........



Itako zainab taji dadi sosai, dan batazata feenah zatasoba
Washe gari monday Feenah taje school takeba ummi labarin birthday da sukai

" ummi taji haushi tace ko a gayyaceni ba komai....

feenah dai ta bata hakuri
* * * * * *

around 4 ne bayan feenah ta dawo daga school xeee tazo mata godiya da ban gajiya, nan dai suka dan taba hiransu sannan sukai sallama!


Bangaren Naseer kuma beda aikin yi se kallan pics din feenah

kamar yaje yabawa abokinshi Bash labari,

wata zuciyan tace kace mai mene, kace kana sontane??? Just kaga yarinya bakasan wayeba ko ansa ma mata rana ko ah ah, zakaje ka fara bada labarinta,

dan haka yaja bakinshi yai shuru amma yanaji a xuciyanshi kamar ya santa a wani *Waje*!



*One week letter* shuru shuru Naseer bega feenah ba a gidan, yake tambayan Xeee ina kawarta mara zumunci,

"xee tace lolz yaya naseer bagashi ka fadaba, *Mara zumunci* ai bata zuwa kwana biyu tun ran bithday dinnan,

"naseer yace ohhhh Lolz, ki dinga mata fada ta dingayi sbd abune me muhimmanci a rayuwa,

"xee tace wlhi har mumy da anty samira sun mata fada rannan bt inatinanin haka take, naseer yace waye mamanta kuma inane gidansu Wai!

Nan xee ke bashi labarin ai gidan hajiya maimuna ne itace ma mamanta....

Naseer ya zaro ido yace what!

Dama tanada yarinyar budurwa,

"Tace eh mana bagatanan ta zo ba, Naseer kamar zaiyi magana kuma se yai shuru yace ok Zan ganki zuwa gobe ko jibi zamui wata magana insha Allah....


Xee tace ok Allah ya kaimu,

xeee ita duk bata kawo ko Naseer na son feenah bane ah ah, tanasha wani maganane daban dan haka ta kosa taji me zai ce mata.......!


























*Taku a kullun Ummiey xeeey Abakon*
❤❤ *A DALILIN SO*❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣


💓💓 *this page goes to You Amina Suleiman.. Ammiey Ayan..Keep on Rolling The

Please Login or Register in order to submit comment