Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ansha angodewa Allah,

Maimuna tayi kyau, Kowa yaga feenah zaka rantse ba diyar maimuna bane, dan kamar ta baci sosai, sedai ace ko kanwartace,

Dare nayi akace za a maida mai mata, yan uwa se cece kuce akeyi akace abari zuwa gobe...

Anty larai tace aa Yau dinnan za a maidata, tunda an maida me ya rage ai kawai haka zaifi, Abunka da masu Kudi komai baja baja....

Dare nayi aka maida maimuna dakin mijinta,

su Anty samira da kawayensu a ciki harda Hajiya rabiii tare da Diyarta feenah.....

Ba wanda ya kwana tunda ba budurwa bane.....

*Beebah* najin motsin mutane a gidan ta kwarma Ihu, Ta fito cikin gida se masifa takeyi, Ba wanda yace mata komai a ka wuce Part din Maimunah.....

Kowa yaga gidan masha Allah,

Beebah saboda tsabar masifa Bata bari baki sun wuce ba,

tayo part din Maimuna....Mezai faru, Suna hada ido da maimuna, maimuna ta karantu addu'oi akan Allah yai mata katangar karfe da beebah

*beebah ta kara kwarmu Ihu....wayyo Allah na shiga uku, Dama ni nayi asiri akan Su rabu, wayyo Allah, Maimunah Na bani inji haj Beebah. Ganin ihun bana hankali bane ya maido da hankalin mutanan da ke cikin gidan, se Ihu takeyi tana tuma a kasa.....*

Nan maganar malam me rukiyya yace Abunda tayi zai koma kanta ya fado musu......

ikon Allah Haj beebah ta hau kace dan duk mugayan abubuwan da tayi yau ta fadeshi da bakinta....Dakyar dai aka samu wasu maza suka yaudareta da kida (gangar shaidan) se rawa takeyi tana ta samu tabar Gidan.


"Kowa se Allah ya kara yakeyi Abun mamaki, Wasu matanen se Hankali wlhi, Nan dai akai ma maimuna fada akan ta jajirce da addua sosai bazama zatai ba,

sannan ta sa yarta addua itama, Allah yasa mu dace......

yan rakiya sun watse daga maimuna se Samira da yaransu zainab da feenah....

Suna hira ALHAJI YAI SALLAMA, ya kara godewa Samira sosai dan ba karamar kokari sukai Ba.....

Samira tace bakomai ta komaai duk temakon junane

Sannan danyi hira kadan samira ta koma gida ita da zainab.

Se maimuna da Alhaji da feenah.....nandai ya kara musu fada suma, Akan kowanne a cikinsu ya dage da addua....sannan ya kuma basu hakuri akan abubuwan da ya faru,

Feenah Dai budurwace tasan tabbas Babanta zai bukaci mamanta, sai yasa tai musu saida safe ta barsu,

LOLz, mezai faru, Maimuna suka dan taba hira Kadan Da AlHaji tace ita dai tare da yarda zata kwana, yaushe rabon da suji dumin juna.....

Haka Alhaji umar ya hakura dan ba yanda zaiyi.....LOLZ
❤❤ *A DALILIN SO*❤❤

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

_A Muslim must not hate his wife and if he is displeased with one bad quality in her then let him be pleased with another that is good because no one is perfect._

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

*Na sadaukar da page dinnan ne gareki Fatima Umar farouk....#Baby Xarah I love you plenty*

© *Ummiey Xeey Abakson*


Page
1⃣2⃣5⃣
Bayan Sunyi sallama da Alhaji Umar

HAJIYA MAIMUNA Ne Ta shugo bed room dinta ita da yarta tilo daya....

Feenah ta fada gado tace huh Mumy i'm tired wallahi,

maimuna ne tace ah Ah ki tashi ki nafila raka'a biyu kafin ki kwanta, Nima yi zanyi, dole mu godewa Allah,

" Feenah tace yeah that's my mumy,

Su ka tashi sukai Alwala around 11Pm sukai sallah sukai addua,

Alhaji najinsu ganin sun yi ne shima Ya tashi yayo Alwala yai sallah, bayan ya idar da Sallan ne ya dakko Qur'ani me girma ya fara karantawa yana kara godewa Allah....Sannan ya kwanta.

"Su maimuna kuma tuni bacci yai Awon gaba dasu.

Washe Gari Feenah ta tashi da wuri dan ta saba tashi, Ta tafi kitchen se alokacin ta kara kallon kitchen din ya hadu, Ta kara daga hannu ta godewa Allah sannan ta dakko Irish ta fere daidai na cinsu su Uku,

ta soya ta hada da kwai, sannan ta dafa ruwan Zafi tasa a flask,

jin motsin Mutun ne a kitchen Mumy maimuna tai sauri ta tashi Ta duba bataga feenah ba ta nufa kitchen Din...

Tana shiga ta ganta Tace My doughter ai da kin bari mun tashi muyi tare ba sai kinyi ke kadai ba!

Feenah tace laa mumy ai na sabane wallahi Ban iya komawa bacci harse na gama ayyukan da nasan dole zanyi da safe,

"Mumy maimuna taji dadi sosai tace Kai nagode Amma Allah yasakawa su Ummu jummai albarka, Nasan duk ita ta koya miki,

" ita dai feenah tai murmushi a xuciyanta tace hmm Na bautu da aiki ai dole na iya,

mumy maimuna ta kama mata sukai sauri suka gama suka tattara kitchen din, suka jera komai akan dining table,

Sannan suka shiga wanka,

Maimuna ne ta fara yin wankan tai kwalliya tasa wani Dankararran Ash less me ratsin Pink, An mata doguwar riga ba karamin amsanta yai Ba,

Ta Kalla yarta feenah tace Nayi kyau kuwa,

Feenah tace wow mum kinyi kyau wallahi,
Tace Thanks sannan ta fita a dakin ta nufa dakin Alhaji Umar mijinta....

Ita kuma feenah tana daki tana shiryawa duk Dadi ya isheta tace hmm Lallai wannan duk kayanane,

Ita dai maimuna tana shiga Alhaji yazo yai mata Oyoyo yakai mata kiss a baki, Ya tura kofan dakin, Nan ya fara sarrafata yanda ya kamata yana cewa i missed you my wife,

ganin yana neman Wuce guna da irine tai karfin Hali Tace hmm Alhaji NaFeesah fa nanan nazo gaisheka na fada maka your break fast is ready,

Alhaji ya kusan kaiwa lukuwan dadi dakyar ya saketa yace Ok ki tafi kar taji shuru ganinan zuwa,

maimuna tai maza ta tafi kan dining bataga feenah ba, Itama seda tadan Huta sannan Ta kwallawa feenah kira akan tazo suci Breakfast,

feenah na fitowa tace Mumy where is Dady,

Maimuna tace yana daki gashinan zuwa mu fara ci kawai,

Feenah ta tashi ta hada musu komai Sannan ta zauna suka fara having breakfast,

Chan sega Alhaji yasha wata shadda me launin light blue ya baza turare se kamshi yakeyi Yazo ya zauna,

yace My Beloved daughter morning,
Feenah tadanji kunya tace mrng dady, how was your night
yace fine my daughter
hope kinci abinci baki tsaya jiranaba,
Tace yes dady naci yace good,

Sanan ta hadomai itama ta bashi,

Ganin wani kallo da dadynta ke wulla wa maimuna
"Tace uhmm Bari naje daki nadan huta na gaji.....

Mamanta tace yes my daughter ki huta ai kinyi aiki,

Nan maimuna taba Alhaji umar labarin Ai Feenah tai yawancin girkin break fast din, Yace Masha Allah, Ai ke ta biyo hannunku da Zaki, kun iya abinci,

maimuna tai dariya suka gama break fast dinsu sannan ta raka Alhaji Daki,

ita kuwa feenah Tuni bacci ya kwasheta,

Maimuna ta shugo daki taga feenah na baccine yasa ta koma dakin Alhaji Nan Suka Raya sunnah,

Alhaji umar har sumbatu yakeyi, dan yaji ta dawo kamar amarya, seda suka gama Dakyar ta tashi dan taji jiki na nufa toilet da gyara jikinta

kafin feenah ta tashi, wajen 12 feenah ta tashi daga bacci Tayo kitchen taga tun abincin safe ba a gyara kan dining ba, nan ta fara gyara komai ta maidashi ma ajinshi,

Ranar dai wuni Alhaji yayi da Matarshi, Abun gwanin sha'awa......

*After la'asar ne Maimuna ta kira Anty larai ta gaisheta ta kara mata godiya sosai,

Suna gama waya ta kira Aminiyarta Samira itama tai mata bangajiya.....

Samira Tace la bakomai wallahi, Ya diyata feenah,

" maimuna Tace gatanan wallahi,
Yau ita ma ta hada mana break fast, Yarinyar akwai aiki ba laifi,

Anty Samira taji dadi sosai, Dan Dama bataso Taga mace budurwa bata iya girkiba LOLz mata akoya girki tun wuri, sukai sallama ta kashe wayan............
❤❤ *A DALILIN SO*❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

```At your absolute Best You Still won't be enough for the wrong person At your Worst, You'll Still Be Worth it To The Right Person ```

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

_I dedicated this page to Hadiza Isah...love you_

© *Ummiey Xeey Abakson*


Page
1⃣2⃣6⃣
bangaren su Jummai Kuwa, Sun koma gida Lafiya sedai Adam Be samu yazoba sbd bejin dadin jikinshi,

"hardai Umma jummai ta gane tace kodai duk Rashin Nafesa ne yasaka haka, kwana biyu na rasa gane kanka komai akace gashi se kace ba ka SO,

"Adam dai yace umma ba haka bane wallahi, Ai ni ba soyayya mukeyi da feenah ba, Inma ina son ganintane ai zanje gidansu, Kawai banjin dadin ne as i said...

" Umma tace uhm To naji Allah ya kara lafiya, kadai samu abinci kaci Sbd karka zauna da yunwa; dan wahala zakasha,

" Adam Yace ok Umma yanzu kuwa, Tana fita ya tashi zaune yace Hmmm Garama na cire feenah a xuciyata tunda ni ban furta mata kalmar So Ba, Yanzuma kona furta mata da wuya ta Soni Tunda Ta zama matar manya....bazata saurareniba, Hawayene ya fito a idonshi yace Shikkenan I already Missed her..... She can't be mine!!!

Bangaren Sags Kuma tun ranar da su feenah Suka bar Zaria ya shiga Nadama, se yai ta tambayan kanshi A ina zanga feenah, Feenah inasonki, Karshe dai ya fashe da kuka dan yasan ba karamin missing din feenah yayiba, Ya cuceta ya musguna mata yanaso yaga feenah amma ba dama, Ya rasa wa zai tambaya inda ta Koma, dan kunyar Adam yakeyi yanzu dan yasan Koya tambaya bazai Taba fadamai ga inda feenah takebaa Haka dai rayuwa taci gaba,.......

*1week letter*
Adam Na tashi daga bacci Yaga text a wayanshi na companyn Su, Yana dubawa ya karanta yaga An mai TRANSFER wajen Aikinsu Zuwa Kaduna,

yana gama karantawa.
Naji yayi tsaki mtsww, Yace Ya Salam, Naji dadi banji dadiba gaskiya, kome yasa yace haka ohon mai.........

"Ya tashi ya shirya tsab yaje ya gaishe da umma da baba Sani, yace an turashi wani Companynsu dake KADUNa Yanzu, Nan zai dinga aiki duk weekend zai dinga dawowa nan zariya. Sukaji dadi sosai sukaimai fatan alheri, Sannan sukace ya dinga zuwa yana gaishe da su Alhaji Umar Sbd mahaifinshine,

"Adam yai shuru yace ok baba insha Allah zan dinga zuwa, ya tashi ya nufa dakinshi ya dakko jakanshi.....

suka kara mai fatan alheri sukai mai nasiha akan Kardai Yaci amanarsu, ya rike mutuncinsa, Yasan abun daya kaishi, yace indai wannan ne kar ku sama damuwa bazaku sama matsala daniba, Ya ciro kudi ya basu da yawa sannan ya kama hanya......

"Ya isa Kaduna Around 11, Suka hadu a wani babban 0ffice, duk wanda akai musu transfer zuwa Kaduna Aka shiga meeting akan Yanda za aci gaba da gudanar da ayyukan companyn,

suka gama around 2pm Aka nunawa kowa inda zai zauna, yaje ya gyara dakinshi, Sannan ya shugo cikin Gari yaje gidansu Feenah....

Yana Isa yai knocking gate din maigadi be tsaya mai wasu tambayoyi ba tunda dama yasan kowa waye,

suka gaisa yace suna ciki mai gajd yace eh,

Feenah na kitchen Taji sallaman Namiji bata kawo Adam bane a Ranta dan batai tsammanin Zaizo yanzuba,

*maimunane ta fito daga Daki tana maraba lale, yau kaine a gidan namu, Ya tsugunna ya gaisheta, Sega feenah ta fito daga kitchen ta kalleshi tace Oyoyooo Ya Adam, dama kaine, kayi zuwan bazata, Meyasa kai mana Haka,

Yace hmmm walhi nima emergency tafiya nayo, Yau da safe companyn mu sukai mun transfer zuwa kaduna,

"Tace WOW i'm so Happy wallahi, Itadai maimuna ta zira musu ido dan tasan indai shakuwane ba wanda nafeesa ta shaku dashi kamar Adam dan tun tana karama shidai yaji yana Sonta,

Adam yace yau gani a garinku da Kano fa naso su turani,

Feenah ta harareshi tace uhm su Yaya kenan yanzu aka kaika Kano seka zauna bazaka nema transfer dole ka dawo kadunaba.....

"Yace LOLz Zan nema mana, maimunane ta katse musu hira tace Aww ashe har yanzu kinanan da surutun nan naki, bazakije ki kawo mai ruwaba se kin gama cikashi da surutu,

Ta tashi ta rufe ido tace wlhi mumy na mantane,

Maimuna Tace naga Alama bari na shiga ciki Adam, Amma dai anan zaka zauna ko,

Adam yace walhi Aa sun bamu wajen zama, Tace Ok, Allah ya bada sa'a yace ameen, Feenah ne ta shugo da wani Katon Tray hade da ruwa da drinks da fruts kala kala tazo ta ajiye mai agabanshi, Tace yaya Adam sakko Kaci,

'Yace Lol wannan irin kaya haka ai na manyane, Bari dai na sha ruwan ma is ok,

"Ta fara buga kafa kamar karamar yayinya ita lallai sai yaci duka,

Ya dan mata tsawa yace meye haka kinfa girma yanzu,

"Tace eh nidai kaci please, Yace ok sedai muci tare, Suka zauna Ya fara cin apple sannan ya kalleta yace shikkenan Ko tace Eh.......

Yace baby kawai tai smiling😊
❤❤ *A DALILIN SO*❤❤

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

*JINJINAR BAN GIRMA GAREKU💅🏼💅🏼 SADNAF*💞💞💞

_Allah ya Baku abun da kuke nema duniya da lahira...._

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

© *_Ummiey Xeey Abakson_*
_08164640126_


Page
1⃣2⃣7⃣
Adam ne da feenah a Pallow
Sun gama cin abinci Suna kallo yaga feenah tayi shuru yace dear what's Wrong

"Tace bakomai Wallahi, Sannan tace Ya Adam....Suka hada ido taji wani Karjinta yace gham!!

"Yace menene tell me Tace bakomai Ya Adam,
Yace ar you sure tace Yes....

"Chan dai duk ta kasa sukuni Sabd tun dataganshi take ganin kyanshi ya kara fitowa, yayi kyau sosai, Lolz

Readers ban siffarta muku yanayin Adam Ba! _Adam ba dogo bane sosai, he is Dark in complexion, yanada eyes lashes sosai ga saje da pointed noise, ga Manyan idanu sosai...lips dinshi daidai gwargwado, yanada natsuwa kuma yanada innocent face...a zahirima he's innocent Sabd mutun ne kamili me natsuwa da sanin ya kamata......that's little About Adam._

Ya kyalla feenah yace baki karanta Lettern dana baki bane.... Tadan sunkuyar dakai kasa tace Nakaranta...

Tace but plz why did you said nafi karfin kai soyayya dani, Idan ina Sonka kumafa.....

Ba ita da take maganar ba hatta Shi da yakeji seda yaji wani iri ajikinshi....

"Yace feenah sanin kankine nafi kowa sonki a duniyan nan...but:....
Seyai shuru kuma

"Ta kalleshi tace but what...yace hmmm bazaki ganeba, Na daukeki tamkar uwa daya uba daya, kinga i have to protect you duk abun da zai dameki bazan Soba....

Tace eh hakane...thanks For the cares

Yace never Mind my sister

Suka gama hiransu na soyayya soyayya, yan uwantaka da sauransu,

Anty Maimuna Ta ce Bari na kira Amiyanata ku gaisa,

Ta dauka waya ta kira Anty Samira tace tazo ga Yayan Feenah yazo suzo su Gaisa,

Anty samira ta taho da zayyad da zainab Suzo suma su gaisheshi,

Suna shiga Ya tsugunna ya gaishe da samira, Sannan zu zayyad suka tsugunna suka gaisheshi shima,

"Nan Maimuna take bata labarin ai yasha dawainiya da feenah shine yanzu andawo dashi kadunane a companynsu,

"samira tace naganeshi sosai naga yadan chanza koba dashine ranar akazo ba....

"Maimuna tace hakka ashe kin taba ganinshi, samira tace eh Maimuna....

sukai mai congrats sukace ya maida hankali sosai, Ya tsayar da gaskiyanshi; Kome za ayi indai bana gaskiya bane a companyn kar ya sake ya shiga, Yaji dadi sosai har xuciyanshi yai musu gudeya sosai;

"sannan samira tace zata koma gida gasu Zainab nan idan sungama hiran da feenah sa dawo gida,

Nan dai hira sukai sosai da maimuna, Adam, feenah Zainab da autan samira zayyad,

Sannan around 6pm ne Adam yace zai tafi, maimuna tayi tayi akan ya tsaya babanshi Umar yazo yace ah ah ai ze dawo gidan tace hakane,

Zai tafi kenan feenah ta fashe da kuka wai ba inda zai tafi shi ya zauna gidan, Se kuka takeyi kamar yarinya, Dakyar maimuna tai mata da gske tace tai shuru ai zai dawo bawai yatafi gaba daya bane....

Shiko Adam duk tausayi yabi ya ka mashi dan Yasan *FEENAH* na sonshi, shi kawai bazai iya zama gidan bane, dan yasan kanshi, kar ya zamana abun da ya faru da ita da sags ya sake faruwa akansu, dan yasan kanshi yana da sha'awa sosai.....

Dakyar dai tai shuru har ya samu ya tafi.....

Zainab tace hmmm Wai dan Allah na tambayeki
* feenah tace eh Ki tambayeni.

" Zainab Tace amma saurayinkine Ko,

" FeeNah tace hmm wannan yafi karfin saurayi aguna, Shi yakemun komai tunda naje gidansu,

"zainab tace Allah sarki gskiya da alama yana sonki sosai,

Nandai zainab ta bata hakuri akan cewa ta dena damuwa, Tunda yanzu yana kaduna zata dinga ganinshi akai akai,

feenah tace eh hakane,

zainab ce ta kalla agogo taga 6:20 tace kai Bari muzo mu tafi gida tunda ke bakison zuwa, Feenah tace zanzo wlhi, sukai sallama zainab da zayyad suka wuce gida,

Ita kuma feenah nan ta zauna kamar an shukata tana mai takaicin rabuwa da Adam, Chan kuma se tinatin sags ya fado mata, tace na shiga uka ta shiga Daki da gudu ta fada gado tana kuka,,

zainab kuwa suna shiga gida suka tarar da Naseer a Pallow,
ya daka musu tsawa yace From where,

Zainab na rawan baki tace wallahi tare da mumy muka fita,

"Naseer Ya kara daka mata tsawa yace i said where ar you From...

tace Gidansu feenah

yace who is this feenah
ita kullun sedai ku dinga zuwa se an tambayeku ku wani ce daga gidan su feenah,
" Ita waye sannan me yasa bazata dinga zuwa nan gidanba,

Zayyad ne yace sorry Uncle Nas bazamu kara fitaba Yace kuma kara fita ku gani,

Jikin zainab na rawa ta tafi daki,

mumy ce ta fito tace Naseer ina jinka da yara kayi hakuri tare muka fita, Suka zauna, wannan matar nan da mukaje wannan kurman nan ne ta warke ta dawo gidanta,

Yace Ok Allah ya kara rufa asiri
Tace Ameeen!!
❤❤ *A DALILIN SO*❤❤

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

_Share love, share laughs and share kindness💜_

*_U mean So much to me Farida M Nasir (Maman Amatullah)_*💞💞

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

© *Ummiey Xeey Abakson*


Page
1⃣2⃣8⃣
Bayan Adam ya isa gidane, Ya Zauna sannan ya kira iyayanshi akan ya cika musu Alkawarinsu yaje gidan Alhaji Umar.

"Sunji dadi sosai sukai mai Fatan Alheri, yana kashe wayan Tinanin Feenah Kawai ya fadomai........


Around 9pm na dare ne Alhaji umar Ya dawo cikin iyalansa. Maimuna ta karbeshi yadda ya kamata ta hadamai ruwan wanka ta bashi abinci etc.

Sannan sukazo pallow suka Zauna suna hira nan Maimuna take bashi labarin Zuwan Adam wai anmai transfer Zuwa nan Kaduna,

Alhaji Umar yaji dadi Sosai, Sannan suka dan tattauna da matarsa akan Adam ya musu Halaccci ya rike masu ya Amana, Sannan iyayanshi ma su suka rike Feenah ya kamata gskiya Ya dawo cikin gidan nan tunda Koba Komai Adam DANSHINE tunda dan wan shine....

" Maimuna tace wlhi Alhaji nima abun danaga ya kamata kenan Dole Adam ya dawo gidan nan,

NAN Take Alhaji Umar ya kira Adam akan cewa Ya dawo, meya amfaninsu a garin da zaije wani waje ya zauna, Tunda ba nisa ai kawai ya zauna a gidan,


" ADAM ba damar yace mai A a haka ya hakura ya amince akan gobe Zai dawo

"feenah Najin haka wani murnan dadi duk ya isheta amma bata bari kowa ya gane hakan ban, Dan a tinaninta Adam Zai zama nata dan she realy Loves Him..

"Washe gari" nayi Adam ya dawo Gidan aka bashi Wani room dan madaidaici da toilet da komai a cikin dakin, dan yasha Ado kamar dakin budurwa,

Feenah se Hamdala takeyi a hrt dinta, Yazo ta tayashi gyara komai se dadi takeji tace ya ADAM is Mine....se dai ya kyalleta yai smiling....

Bayan sun gama gyaran dakin ne ya ajiye a ma'jinshi

ya juya ya kalla feenah Yace yauwa inason magana dake feenah,

Tace Ok bros inajinka,
" Yace Please n please, kinsan yanzu ba Da Bane, Ki rage shugowa dakin nan, kinga Kar su mumy sui tinanin wani Abu,

"feenah numfasa tace Uhmm To naji, Se kuma idonta ya cika da kwalla,

yace me ya faru kuma Tace mai bakomai, Alhalin Ita tasan abunda take tinawa...ABUN DA ya shiga tskaninsu da SAGS,

yace ok ke dena damuwa koma menene Ki dinga Addua bawai kina bari abu na damunkiba.

Feenah tace thanks my bros sai yasa nake sonka, Kana da tsoron Allah, ba zaman da zamui ba Baaka ce mu na dinga tsoran Allah ba, Matarka ta huta wallahi.

"ADAM yace LOLz idan kece fa, seta rufe ido tace na huuutaaah..

Yace yauwa, let pray for the best, in nine me alheri Allah ya baki ni tace Ameen
**********************


*2 months LATER* haka komai yaci gaba da wakana Amma tunda feenah suka dawo bata taba zuwa gidan su Anty Samiraba, Tun tana mata korafi har ta gaji, ita ma frnd dinta zainab Ta dena zuwa tunda feenah ba zuwa takeyiba,

Anty larai kuma tana zuwa akai akai tana duba lafiyan Yarta da jikanta feenah:....

*FEENAH* tunda Suka dawo kullun bata wani walwala in kunga tayi to dan uwanta Adam nanan ne, Tun mumy na tambayanta meka faruwa se tace ita Ba komai dan ta rasa yanda zatai ta fadawa mamanta SHE IS NOT VIRGIN...

"Bangaren Sags kuma kullun cikin mafarkin feenah Yake, dan tun bayan tafiyanta ya tuba, Ya zama ustaz din dole, Sedai ya kulle kanshi a daki yaita kuka yana rokan Allah ya yafemai dan ba karamar cutar da feenah yayiba,

Kullun seya kira kanwarshi maryam akan Ko tanada numbern feenah tace wlhi nima nema nakeyi,

Maryam ta tausayawa yayanta Sags dan tasan yayi missing Mata Amma meye Shi yajawa Kanshi:......

Yayi neman Amma har ya gaji, Gashi be ganin ADAM a unguwansu shine ya kara daga mai hankali yana cewa kodai Aure Sukayine, Yaita tinani barkatai abun tausayi,

Alhaji umar ne zaune a daki suka tattauna da matarshi akan Shifa Yarsu Makaranta zata koma ba zaman gida zatai ta yiba,

Maimuna ta bada goyon baya dari bisa Dari tace nima Abunda ke Raina kenan tunda miji bai fitoba se ta koma School,

Aiko washe gari nayi tunda lokacin daukan New student ne akaje akai mata rejistration *A KADUNA STATE UNIVERSITY*, sbd Dad dinta yace ba yanzu zatai aureba karatu zatayi sosai, Kasancewar ita dayace a wajensu, taso tayi aure ita da wuri amma bata samu tayiba,

Feenah tace ita Ba karatun da zatayi, se tirje kafa takeyi akan ita Sam Boko ya isheta Aure za ai mata Adam ne ya kirata ya bata hakuri akan cewa tabi umarnin iyayanta zatajii dadi, ta nuna Yanzu wasu suna chan suna neman wa zai temakesu su samu su shiga makaranta yadai mata nasiha Karshe dai ta amince Tace ta gode yace yawa baby Sister.....
❤❤ *A DALILIN SO*❤❤

❣❣❣❣❣❣❣❣❣

_Keep your hope alive nd never lose your faith_

💗 _Na sadaukar da page dinnan gareki ZAINAB ALIYU(Cutie Xeey)_💗


© *Ummiey Xeey Abakson*



Page
1⃣2⃣9⃣
Misalin Karfe 4 na yammane ALHAJI umar ya dawo gida yau, be dde a wajen aikin shiba,

ya dawo da kaya nike nike, yana shiga ya kira Adam da Feenah sukazo suka kwashe kayan sukakai pallow, Kayan abincine da drinks, da kayan kwalliya a cikin kayan harda Waya,

"Alhji yana zuwa ya ware wa kowa kayanshi yaba Adam wasu shaddoji da riga da wando, Feenah kuma ya bata kayan Kwalliya da Waya kirar Iphone 6,

"Adam ya tsugunna yai wa dady godiya sosai akan kokarin da yakeyi, Ita kuma feenah ganin wayan datai ne yasa gabanta ya fadi seda suka fuskanci ranta adan bace yake

"Mumyne tace me yafaru kuma, Kika bata rai,
"ta kirkiro dariya tace bakomai mumy, Ta juya wajen Dady tace thanks Alot daddy, Allah ya kara bude na alheri yace Amin,

"Maimuna tace ko kefa naga alama kwana biyun nan tunda akai miki rejistration se wani bata rai kikeyi in bakyasone ki fadawa mutane kar ai asaran kudi a banza,

"Feenah ta kalla mumy tace mumy inaso, nagode,

Mumy tai tsaki mara kara,

"Daddy dai na kallanso yace sorry my daughter mamanki zata saki agabako, kiyi hakuri,

"Maimuna tace uhm Alhaji kabarni da ita, muba iyayanta bane setai ta abu tana bata rai waye sa anta Anan,

Adam ne yace haba nafeesa meya faru kuma, ki dena abunda kikeyi ba kyau...

"mumyne ta taba baki tace kaima dai ka

Please Login or Register in order to submit comment