Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dawo take a layin ta rasa ya zatai ta shiga gidan Samira se ga _Naseer_ babban dan Alhaji kamal Ya fito daga gidan ya ganta se zirga zirga takeyi a kofar gidan, Ya gaisheta tace yauwa dama dan Allah ina tambayane ko nan ne layin gidan haj samira, yai murmushi yace gama gidan nan, ya kama hanya yai gaba, ita ko tace na shiga uku, yanzu ya zanyi in shiga dama nasan gidan kawai munafunci nane oh ni rabi, dakyar tai karfin hali ta shiga gidan da sallama da hijabinta har kasa,
samira na ganinta ta tsuke fuska tace lafia kika shugo mun gida,
Rabi tace kiyi hakuri dan Allah nazone na tambayeki ina maimuna take yanzu,
samira ta kara hada fuska a xuciyanta tana innalillahi wa inna ialihi rajiun, samira tace nima bansan inda takeba dan bansan meya hadasu da mijinba, kuma ki fitarmun agida yanzunan nan, wato kinzo in fada miki inda take ku bita ko, To bansaniba fitan mun a gida, kuje chan kuita abunku, tace zan fita Allah ya huce xuciyarki tunda bakisan gidan ba shikkenan Sai anjuma...tace agayas, munafukar banza da wufi, Allah yai mana tsari da irinku, Tana shiga daki ta Nema Wayanta ta kira Anty larai, take bata labarin abunda ya faru, Anty larai tace nagode da baki fada mata ba,nan dai suka jajanta ma juna Dan abun tsoro yake basu, ko ina sukaje ace sihirine Babba se anci gaba da addua.........wannan kenan
❤❤❤ *A DALILIN SO*❤❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣

© *Princess Ummiey Xeey*

Page
9⃣4⃣

Har Naseer yaje ya dawo Samira na dakin tai tagumi ta rasa me ke shirin faruwa da maimuna ne, Mutun yabar gidan amma se biyoshi akeyi wannan wani irin bakin kishine irin nasu, Naseer yai sallama, Ta amsa tace kadawo yace eh. Ya sama waje ya zauna, yace kinga bakuwa ko, tai maza tace mai eh, dan batason ta bashi labarin meya faru,
Ya shugo ya Zauna yake cewa mummy, naga jifa, tace ina kaje ina sha kana bakin gate ne dai, yace wallahi a a naje chan kasane siyo card, tace ok, Kaje kan dining table ga abincin ka chan kaci,
Yace na koshi, mumy Kinsan me,
tace a a Naseer,
yace wallahi bansan Ganin yara marasa iyaye, tausayi suke bani, most especially naga yara almajirai suna yawo a rana, mumy Samira tace A xuciyanta Allah sarki, Nan take idonshi ya cika da kwalla mumy tace kayi hakuri, wallahi akwai tausayi, ya tashi ya busar da iska a bakinshi yace Allah ya bani wani babban mukami insha Allah marasa gata zasuji dadi.....
Ya tafi daki yadan huta, da kwanciyarshi ba sai *Feenah* Ta fado mai araiba
yace Oh My God ina zan sake ganinki, beauty wani hali kike, Gashi Kun bar makarantar bari naje na duba...
Ya daga Hannu yace Ya Allah ka hadani da beauty, *SAI NA TEMAKETA*, wai meyasa wasu iyayan basu da tausayine, nan take tinanin marasa gata ya kamashi, harda kwallan shi, Bacci yai awon gaba dashi,....

Washe gari, Alhaji Kamal suna palour dashi da matarshi, da naseer, da zainab da zayyad, suna hira, Alhaji kamal ya kalla dansa yace to Alhamdulillahi, Tunda Ka gama service kana samun aiki aure zan maka dan haka ka fito da mata, da sauri Naseer ya kalla dad dinshi yace Dad zanyi aure amma ba yanzuba _please i'm still young ko Mumy_, Samira tai murmushi tace Alhaji su kake ka sama jika kenan, Alhaji Kamal yace a a, naga ya girmane tunda yanada hankali kamata yayi ya sama mata ya aura, samira tace eh hakane, Dana kaji abunda dadynku yace ko so please kai nemo mata Musha biki, Naseer yadan bata rai yace toh Lolz, suka dan taba hira kenan Dad yace zai tafi office, Naseer ya shiga daki yace tab, dady zai kiramun ruwa fa, aure ni a tsarina ba yanzuba Dan ko mata ban kulawa Dan banso na yaudara kowa, yaga tinanin zai dameshi ya dakko laptop dinshi yanada Dan dube dube.....
❤❤❤ *A DALILIN SO*❤❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣


© *Ummiey Xeey Abakson*


Page
9⃣5⃣
Bangaren Nafeesa Kuwa kullun se maryam ta dameta akan yaya sagir, tace to naji amma dan Allah karki sake damuna ko ana So dolene, nida har yanzu banjin feeling din kowa wai da sunan *SO* Wai ya so yakene, Allah yasa wata rana naji ina son wani naji yanda akeji, I heard mutane da yawa suna So mugun abune bt ni har yanzufa bansan meye *SO* ba, kawai se na fara son mutun, tayaya zan ma fara soyayya,
Maryam dai se kallonta take, tace ji beki awajen ahaka kamar kin waye amma ashe da sauranki, common So ne zakice bakyaji a xuciyanki, nafee tace i told you bansan ya ake Ji faba, Ko zaki iya sani naji,
Maryam ta tsintsire da dariya harda rike Ciki, Tace wane Ni sedai yaya sagir ya koya miki ya So yake, Tace Ok maryam bari naje gida we talk tomorrow tace ok kawata, ko kicemun na gaishe da yaya sagir, tace ohh My regard duk da bansan ya so yakeba, maryam dai ta tsaya tana mamakin kawarta tace ok bye, feenah ta dawo gida, Ta tarar da Baba sani a daki yace feenah jummai batanan kuma Adam ya koma school, dan Allah dauka 100 naira dinnan kije ki Siyomun magani bayana na ciwo, Tace Allah sarki baba Sannu, bari nai sauri na dawo yace To nagode yar baba, Tana fita taci kawo da yaya sagir yasa sport wears (riga da Wando three quater me kalan blue black) yadakko sport car dinshi zai fita da yamma, Tace ina wuni yace lafia lau, ya tsaya yana kallonta yace ina Zaki tace babane ya aikeni, yace ok in bazaki damuba please 2minuite, kaman zata tafi dan sauri takeyi, Se ta tsaya tsak,
Yace Hope kinji sakona wajen kanwata Tace eh naji amma kayi hakuri har yanzu _bansan meye kalmar So Ba, ya so yake_,
yace *huh* a xuciyanshi shima yace wow gskiya she's beautiful ji yanda take magana amma ace batasan meye soba, yace nasan me zanyi, Yace _Feeenah_ cikin wani irin murya, tsigan jikinta ya tashi ya kara cewa _feeenah Look into my eyes_ Ta kyalleshi ido cikin ido kawai se ta tsince kanta a wani yanayi dan har jikinta na rawa dan Wani irin deep kallo sukai, yana ganin jikinta ya fara rawa yace you can go....tai maza tabar wajen, Ya bita da kallo yace yes Sai Na.........Nima banji abun da yace ba..lolz, ya shiga motanshi yasa Wakan blame it on me na *AKON* dan favorite din wakanshi kenan, har ya fara tafiya yaji bazai iyaba, Ya sama waje yai parking yana tina muryanta me dadi tace _Bansan meye SO ba, Bansan ya So yakeba_ yai murmushi yace zakisan meye *S0* With time indai kina tare dani, ya Wuce Wani Shopping Plaza Babba yai siyayyan su perfume, Kayan kwalliya, Yasai Mata waya IPHONE 6...tirkashi yace da wannan zan malleki ki insha Allah, Yai murmushi ya shiga motanshi ya dawo gida......

Ita ko bangaren ta jikinta se rawa yake taje chemist din amma ta kasa cewa komai ta sama waje tai tagumi ta zauna ta sunduma cikin kogin tinani......
❤❤❤ *A DALILIN SO*❤❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣


© *Ummiey Xeey Abakson*


Page
9⃣6⃣

Chan taji ance ke lafiyanki kuwa, ba abu kika zo siyaba ta tashi jikinta asanyaye tace eh, yace to tinanin me kike tadanyi tsaki mtsw azuciyanta tace bansan tambaya, to in ma tinani nakeyi ina ruwanka, Ta mika kudi tace abata maganin ciwon baya na 50 naira, ya amsa yace yan mata ko tinaninshi kikeyi, tace Allah ya kyauta, yai mata dariya yace nasan shine dai zaki zauna kita tinaninshi haka lolz...ta kyalleshi tace Ikon Allah jimun mutun kaman yasan abun dake raina, Itadai ta amsa maganin ta dawo gida, baba Sani yace kin dade ina fatan lafia dai ko, Tace eh baba Layine kasan yamma yayi yace hakane, nagode yar baba Allah yayi albarka tace Amin, Ta shiga daki ta huta, dan yamma tayi taga umma bata dawoba tace uhm bari na tashi na daura abinci kafin umma ta dawo ta cinyeni da fada, Ta tashi ta daura tukunya, Ta dafa taliya yar hausa, Kafin ma tagama umma ta dawo se shi mata albarka take abun yabata mamaki tace wata rana, dare nayi tana waje ita kadai tanashan iska tunda Adam abokin hiranta benan, taji su umma suna hiran mahaifanta, sukace ikon Allah Alhaji umar shuru, Jummai tace tunda kaji shuru ai sekabi dan uwanka Kaji ya labari, baba sani yace bazanjeba, shi ina hankalinshi yake, Tunda yarinyar nan tazo gidan nan ya taba zuwa ya ganta dandai uba ubane Amma wallahi ba ban maida itaba, jummai tace Wallahi nima tausayi take bani, yarinya da gatanta amma ta zama abun tausayi, Feenah naji ta shiga daki se kuka takeyi an tsokanu mata inda yake mata ciwo dan kullun da tinanin mahaifiyarta take kwana Ta tashi, chan sukaji shasshekar kukanta da sauri suka bita dakin suna tambayanta meya faru, tace Kantane ke ciwo,
Da sauri baba yayo kanta yace kiyi hakuri sannu, kodai kinji maganar da mukeyine, Ta kara fashewa da kuka tace banjiba baba, Umma tace yo inma taji ai ba karya bane, abun fa da ciwo Malan, mutun da gatanshi da komai amma Matar uba ta hana mahaifiyarka da kai zama dan sai ta kara fashewa da kuka, Malan Sani se yi wa jummai fada yakeyi don me zata dinga sata kuka, Lallashinta ya kamata tayi bawai tai ta cewa kaza da kazaba, Dakyar dai ta samu ta tsayar da kukan dan ji take gaba daya so take taga mamanta, Ga Malan Sani besan Inda mamanta sukeba Yanzu, Ya bata hakuri yace nima abun na raina yar baba ki bari gobe zan kira Larai inji inda suke sai mu kaiki kinji ko, Nan dadi ya isheta ta kosa gari ya waye yaje taga mamanta, Washe gari nayi taje kofar gate din su Maryam tace baba tsoho maryam nanan, yace eh amma basu tashiba se zuwa anjuma, Hakanan ta hakura ta koma gida.
❤❤ *A DALILIN SO* ❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣

© *Ummiey Xeey Abakson*


Page
9⃣7⃣
Ta Dawo gida, baba sani ya ce yar baba, naga yau tun wuri kika tashi duk zumudin ne tace eh baba, Jummai dai ta sa musu Ido tace yau nagani, ya aiketa siyo card taje ta dawo ya kira numbern Anty larai, bugu daya ta dauka tace Mal sani ashe kana nan yace inanan mana, tace ai munsha anyi zuciya da mune yace wane mu sedai ku, tace ina nafeesa yace gatanan shekara uku shuru har yanzu ba labari, nan dai ta bashi labarin ai maimuna bata magana, hankalinshi ya tashi sosai, Dan ba karamin tausayi ta bashiba, tace Alhaji ko ya nanan, shima yace tun ranar ba abun ya faru ko sashi a ido ban karaba, ko kirana beyi, tace Ikon Allah, mata basu da tausayi, ya jumman fa yace lfia lau gatanan ma ku gaisa, jummai bata soba dan kunyan su takeji, hakanan ta amsa suka gaisa sama sama, ta mikawa mal sani, yace dama inaso ne muzo muganku, nafeesa ta damu, tace eh gaskiyane nima inaso naga jikata, nan tai musu kwatance, maimuna najin abun da take cewa ta fashe da kuka, tausayin Maimuna ya kamata, Nan dai sukai sallama yace a gaishe da maimuna kafin suzo, Suna gama wayan Kenan mal sani ya kalla nafeesa cike da tausayi yace taje ta shirya yau zasuje kaduna su dawo saboda school, murna yabi ya isheta duk batasan abun dake faruwaba, ta kintsa riga da siket na wata atamfa duk ta kode ta dakko hijabinta ta saka, tai kyau daidai gwargwado, mal sani shima ya shirya suka kama hanya se kaduna.... Ba su sha wahala ba sosai tunda suna waya da anty larai akai akai suka gane gidan.... Wani katafaren gidane babba yasha kwalliya irin na manyan masu kudin nan dan ko se kabi layi 10 da wuya kaga irin Gidan se wanda sukaci suka tada Kai, Alhaji yace ikon Allah, Ji gida kamar a out side, ita Ko nafeesa duk ta kosa su shiga taga mamanta Allah sarki, *Uwa Uwace* suna tsaye a bakin gate din wani dan saurayi da alama dan aikine yazo ya bude musu, Yai musu iso har cikin babban Falon....Allahu Akbar, Nafeesa tai steping kafarta Mamanta tazo da gudu ta rungumeta, Nafeesa tai farin cikin sosai Tace mumyna, mumy shuru, mumy, mumy ta kuma shuru, Nan take maimuna, hajiya larai malan sani suka fashe da Kuka, Nafeesa tana ganin sun fara kuka itama ta fashe da kuka, seda malan Sani yai ta maza yace kui shuru Mana, ya zamuyi, Sannan suka dan tsagaita da kukan, Itada dai nafeesa bata san meye silan kukanba, Ta kara cewa _mumy i missed you alot_ maimuna ta kara rungumeta tanajinta har axuciyanta; abun yaba kowa tausayi ba yanda zatai magana, Mal Sani yace Nafeesa, kiyi hakuri ki sauraremu kinjiko, tace ok Baba, yace yauwa yar baBa, nan dai suka bata labarin mamanta bata magana amma tanajin abun da ake cewa, *Nafeesa* ta sake wani razannar Ihu Tace _*INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN*_ beloved Mumy nane bata magana
❤❤ ​ *A DALILIN SO​* ❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣


© *Ummiey Xeey Abakson​*

Page
9⃣8⃣

Ta Kara maimai tawa Beloved mumy nane bata magana cikin shesshekar kuka, tace Mumy Allah ya saka miki, Allah kuma ya baki lafiya, suka amsa da Amin, suna ta hira mal sani da Larai da nafeesa, wajen dariya Maimuna tayi, dan ba karamin farin ciki tai ba dataga Yarta ta girma, Shape dinta ya fara fitowa a matsayinta na Mace, maimuna tai nuni da paper da biro aka miko mata ta rubata wa yarta kamar haka
_*beloved daughter words enough will never explain how happy i'm dana ganki, plz ki kasance mai natsuwa ki rike baba Sani tamkar babanki, Kinga kin fara girma ba kowani namiji zaki bari yana kallonkiba ko yana miki magana, ki daure ki dena kula maza dan nasan yayan ki Adam ma bazai bari ba, please keep your dignity as a pride of a lady dont allow the love of Money to deceive you please yata, Kome kikeso ki tambaya jummai ko baba ko Adam, kar ki yarda da ko wani namiji, naso na kasance tare dake har girmanki amma ba haka Abun yazoba, Please kar ki bani kunya yata I so much love you my dear,*_ ta mika mata, anty larai tace ya da uwa suna soyayya.....dukansu sukai murmushi; ta mika wa yarta, tana gama karantawa hawaye ya zubo mata Tace Allah Sarki tace a xuciyanta *Mumy...........*
ta mata reply itama tace _mumy I love you more, Thanks Alot my beloved mumy, nayi bakin cikin rashin girmana tare dake amma i promise you bazan taba kula wani namijiba kuma su baba sani suna kokari akaina sosai, Ina miki fatan Allah ya baki lafia, mumy Allah ya saka miki, nagde_
ta mika mata itama, sudai su Anty larai da mal sani sunyi Shuru ko wannin su da abun da yake sakawa a xuciya, abun gwanin tausayi, maimuna tana gama karantawa ta taba yarda ta daga ma kai Alamun ta gode, nan sai suka dan taba hira sukaci sukaha sukace zasu tafi amma zasu sake dawowa, sukace ok yanzu an zama daya ai, maimuna ta kara kallon yarta cike da so da kauna taga tayi kyau sosai sedai ta lura yarta tana lacking kayan sawa masu kyau amatsayinta na tafara zama budurwa zata bukaci kaya, ta kira Anty larai daki, tai mata short note Kamar haka
_anty aduba cikin kayana akwai panties da breziers da sauran kayana plz a bata naga tana lacking kaya, maimuna na gama rubutawa ta mika mata_ anty larai ma tace yes na lura da haka bari na har hada mata da kudi na bata extra, koda zata bukaci yaci yabu, maimuna ta mikawa anty larai hannu alamun 👍🏻👍🏻yes..that's Great, sukai murmushi suka hado mata suka dawo falour, maimuna ta mikawa yarta kayan taji dadi sosai dama tanason tambaya amma ta rasa yanda zatai, ta mikawa mal sani shima kudi masu dunbin yawa, yai godia sosai, kamar karsu tafi, a gskiya sunji dadi sosai...sukai sallama sai gida Zaria......
❤❤ *ADALILIN SO*❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

© *Ummiey Xeey Abakson*

_Wannan page din nakune masu kirana musamman..nagode da adduanku Kuma Allah ya biyawa kowa bukatunsa na alheri_


Page
9⃣9⃣
Sundawo gida lafia lau, Mal sani ya labarta ma jummai abun da ya faru da maimuna ta tausaya mata itama, amma yana nunawa jummai kudin da suka bashi nan ta fara washe baki, kai angode, yau zan wanke tukunya se jar miya zamusha, shiko duk takaici yabi ya isheshi ya kalla matarsa kawai ya kauda kai,
_yace azuciyanshi hmmm Rayuwa kenan, inbaka da kudi ka zama banza, yaja tsaki mtsww_
nafeesa kuma tanajin kunyar malan sani sbd kayan da aka bata bazata iya nunawa agabanshi ba seda ta bari mal sani ya fita sannan ta nunawa jummai, tayi farin ciki sosai saboda a tinaninta yanzu hajar feenah zai bude zata dinga samun kudi, sbd dama yan mata seda kayan kyale kyale in baka dashi abarka abaya lolz, _Allah ya tsare mana imani_ *Ameen*,
Tana fita dakin ta je wajen kawarta maryam sbd dama kafin ta tafi tazo akace basu tashiba, tace maryam kizo muje ki gani kayan da mamana ta bani, maryam ta biyota, suka shiga daki ta nuna mata one by one, feenah kuma tana gefe tana tinanin mahaifiyarta, nan dai har feenah taba maryam labarin yanzu mamanta bata magana,
feenah ta fashe da kuka,
maryam tace karki damu insha Allah zata warke muita wa mumy addua, sannan feenah tai shuru,,
Maryam tace wow gskiya kinji dadi, yanzu zaki fito sosai, wannan kaya haka masu kyau da tsada, feenah tace uhm har wani tsada garesu,, maryam tace masu tsadane ina gani mumy na siya tana sawa, nan dai suka barke da hiran kawaye,
maryam tace zaki yaka samarifa kawata, ga kyau da diri,
feenah tace eh naji dai Alhamdullilah, nifa har yanzu banga namijin da yamun ba balle inji sonsa araina,
*maryam* ta kalle feenah tace please can i ask you,
feenah yeah you're free to ask,
maryam tace hmm bakya tinanin yaya sagir,
feenah tace, eh sometimes inayi but ba irin sosai dinnan ba,
mayam tai kyalkyale da dariya tace my frnd kinfara kamuwa fa,
feenah tace god 4 bid, banga wanda zan sobafa, just yanzu nasa karatu a gaba
maryam tace to sannu, Komun dai karatunki se kinyi soyayya, irin ku ma ba a magana, feenah tai murmushi tace we shall see,
maryam tace ok, nan dai sukai sallama, maryam ta tafi gida,

*Yaya sagir* najin labarin feenah ta dawo ya rasa yanda zaiyi, sonta yakeji sosai aranshi, kullun da tinaninta yake kwana ya tashi dashi, dan yarinyar ta riga ta shige mai heart❤ dinshi,, nan dai ya fada kogin tinani se juyi yake agado kamar mara lafiya chan dai naji yace *I LOVE YOU FEENAH*, ni na dace dake, yaga tinanin bana kare bane ya Tashi ya fito ko Zai hadu da Apple of his eyes,...ya fito waje shuru, se leke yakeyi kamar mara gskiya har yamma tayi bata fitoba, ya kuma gida ya kira kanwarshi ina feenah tace tana gida, ya hada rai kar ma ta rainashi ko taga alamun ya kamu sosai yace _can i see her to night_ da sauri maryam ta dago kanta tace walhi dakyar za a barta ta fito,. Ya katse mata magana yace Tafi..it's Ok....shi kuma ya chusa kanshi cikin pillow. Lolz😜 Love one tin tin..
❤❤ *A DALILIN SO* ❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

© *Princess Ummiey Xeey*


Page
1⃣0⃣0⃣
Yau feenah ta tashi da ciwon ciki sosai kamar zata mutu, sukaje asibiti, akace period ne amma please su daure sui mata aure da wuri tunda ta fara ciwon cikin nan mai tsanini, suka ce OK, suna dawowa gida maryam tazo tace lafia ya naganki some how nan ta bata labarin period ne yazo mata, maryam tace inyee _feenah an girma_, feenah tace ke ba wannan ba ki duba cikin jakana zakiga kudi plz kije ki siyomun pad, umma jummai ta bani tsumma wai nayi using dashi kinsan i can't, maryam ta fashe da dariya😆 tace inama dashi a gida bari naje na dakko Miki, tace ok.....

*bayan kwana hudu* yaya sagir shuru basu hadu da feenah ba, hankalinshi ya tashi sosai, kullun seya tambaya maryam ko lafia tace lafia lau, Tunda ba lallai bane yaji abun dake faruwa,
*_(Hakan datai shine daidai ba wai wasuba da anfara period har saurayi sai yaji haba...it's your secret fa, ki kama mutunci wallahi yake yar uwa, saurayi ba mijiba, be kamata ko wani sirri naki yajiba. Mu kiyaye plz)_*

Washe gari yaya sagir ya gagara dan bazai iya bari yau ta wuce ba tare da yaga feenah ba, Haka yai ta maza, duk ya kosa dare yayi, Aiko dare nayi ya aiwa wani yaro yace aje ya kiramai Nafeesa, Umma na tsakar gida da Mal Sani, se ga yaro wai ance nafeesa tazo, Bakuga murna wajen Ummaba, feenah tace bazataba, shidai malan sani bece komai ba dan yasan yanada iko, kuma beda iko akan *FEENAH* umma ta nufo dakin feenah da sauri tace kije ana kiranki awaje, Batai mata musuba tace ok je kace ganinan zuwa, ta dauka hijabinta ta nufi waje, Umma se washe baki take, Wai anfara neman Feenah amma azuciyanta tana cewa *zanci Kudi* umma ta duba malan sani tace Ikon Allah je har anfara nemanta, kamar sunsan ance ai mata aure da wuri, malan sani haushi ya kamashi yace To basai ki aurar da itaba, daga ganin sarkin fawa sai miya ta fara zaki, wai me yasa ku iyaye mata wata sa'in baku da tinanine, Wanna fa ba yar mu bace da zamu aurar da ita, to ke da kiga ance ana nemanta auranta yace zaiyi kome, da kike zumudi haka, Umma tace Allah ya baka hakuri, Nafesa na fita ta hadu da Yaya sagir yasha wani riga da wando na pakistan, yayi kyau sosai sabd farine kyakkyawa gashi bashi da tsayi sosai, Data ganshi seda gabanta ya fadi dan ranar da sukai deep kallo ya fado mata, se kuma ta fara jin kunya, tace ina Wuni yaya sagir, Yace lafia lau amma sunana Swt Love, Ta ji kunya sosai tai shuru, yace da fatan kinanan lafia, hope dai ban takura miki ba, tace eh Bakomai, Yace To dakyau, Abunda ya kawoni shine Nazo da kaina ne dan na aiko maryam baki bata wani _respond_ me karfiba da zai gamsheni, Yana magana irin na kwararrun yan duniyan nan dan Ko dan jin kunyan nan beyi, Tace uhm mezance to
yace ki fadamun kome ra'ayinki yanzu,, tai shuru yace baby love dake nakeyi, nan dai kamar ta nitse dan bata taba dogon hira da namiji kamar yau ba, ishenta da surutun da yayine tace To Naji, yace kinji mene, *_Do you realy love me Yes Or no...Tace yeesss cikin rawar murya_*, Yai murmushi yace that's my girl to yanzu kin yarda na dinga zuwa zance ko a a, tace kaga ina zuwa school amma ba kullunba ko, yai murmushi irin na samarin nan yace *OK* Tace zan tafi, yace bani numbernki tace wallahi banda waya, sukai sallama ya rokata har kofar gidan kamar zai shiga ya koma...lolzz
❤❤ *A DALILIN SO​* ❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣

​© *Princess Ummiey Xeey​*

*_Much love my chocolatey....Marfancy_*❣❣❣

Page
1⃣0⃣1⃣

Shiko gogan naka (Sagir) yana zuwa gida ya kira abokinshi _kabeer_ yace _baaba_ yane, yace kaida baka neman mutane, kota samune yace wallahi kuwa, Nayi beb fa, yace haba dai, sagir yace i'm serious yanzunan nan ma daga wurinta nake, kabeer yace kai ko bazaka nema mace kai aureba, yan matanka sunkai 10 amma kullun se kayi new girl lover,
sagir yace to ya za'ayine,
kabeer yace adai rage
Sagir yace haba dai ai daga wannan ba kari, yarinyace fa, kasan sunfi dadin Mu'amala, amma yan uni nan idonsu👀 a bude yake, kebeer yace hakane, ko zaka barmun itane, sagir yace haba Dai aboki, wannan tawace ni kadai, nandai suka taba hiransu na abokai sukai Sallama, amma dagajin yanayin maganansu akwai (nadi a cikin lauje), Haka suka ci gaba yau inyazo intaga dama ta fita inbata ga damaba taqi fita...., Soyayya dai ana yinta wasa wasa gske gaske,

bayan kwana biyu *YAYA SAGIR*

Please Login or Register in order to submit comment