Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Compiled By Umar Dalha Funtua.





🏕 *RUMFAR BAYI* 🏕
Na Afrah bhai
Page 1
Wattpad @afreey101

'bismillahil'rahmanil'rahim

****************
"A Shekara ta alif sha tara da sittin da tara 1969 a masarautar 'daura' dake cikin jihar katsina.

'A lokacin ne Sarki 'MUHAMMADU ABDUL-JABBAR UMAR' ya amshi mulki daga wajen mahaifinsa wato SARKI UMAR NA BIYU bayan wata sarka'kiya da fadace fadacen da suka wakana a cikin wannan yan shekarun' bayan rasuwar tsohon sarki Abdul-samadu kenan,a inda jama'a da yawa ne suka rasa rayukansu acikin masarautar da ma garuruwan dake kusa dasu'

A cikin wannan karni ne na sarki Abdul-Jabbar ya saka dokiki masu tsauri da yawan gaske ga alummar sa dan samun cikakken kwanciyar hankali a cikin kasar ta sa.

"Babu wani mahaluki dake zaune a kasar ta daura ko ince a cikin masarautar ta daura" da bai san da zaman RUMFAR BAYI ba ,waje ne da zan iya cewa DUNIYAR BAYI ,wato a nan ne gaba daya bayin dake masarautar daura suke Rayuwarsu a ciki.

'RUMFAR BAYI na tattare da tahiri da kuma labarai na bayin da suka gabata..
RUMFAR BAYI wajene inda bayi suka maida a matsayin tasu duniyar' dan ko wacce baiwa nada nata irin rawar da ta taka..

******wannan kenan******

"Gudu takeyi kamar ranta zai fita' bata ko sanin in'da take saka kafarta,macece mai kimanin shekaru goma sha takwas da haihuwa.

'Wani dogon lumfashin taja....sannan naga ta Dafe katoton cikinta, tana zubar da hawaye masu ciwo'kafafunta gaba daya rubar da jini sukeyi duk sun fashe sun kumbura tsabar gudun da take sha..ina zataje?ya zatayi da dan dake cikin cikin ta?dole ne ko bata rayu ba ta haifar da shi...wannan tunanin ne kawai yake yawo cikin kwakwal'warta..

'Dare ne ya tsala sosai dan babu wani bil adama dake yawo a cikin garin data sami kanta..
' juye'juye take tayi dan samun wajen da zata boya..can ta jiyo muryoyin kattin mazan dake binta suna neman raba ta da rayuwarta..

'Wata tsohowar kofa ce ta hango tayi saurin karasawa ta boye a bayan kofar tana jin dan cikinta na masifar juya mata tamkar zai fito dan kansa.

'Tana jinsu suna ta zagaye zagaye a wajen suna faman nemanta' tayi saurin saka hannunta dake rawa ta dafe bakinta ta kulle shi gam jikinta na ba'ri,sbd azabar nishin da takeyi tanajin wata masifaffiyar gajiya na fita a gaba daya jikinta...

'kusan Shudewar minti goma taji shiru hakan ne yake nuna mata sun wuce kenan,ta saki wata irin ajiyar zuciya..
'Tana kokarin mikewa ne daga durkushen da take taji an fada mata kafadarta..

"Zaro jajayen idanuwanta tayi bugun kirjinta kamar zai fito sbd tsabar tsorata da tayi..

Lafiya baiwar Allah...
Taji wata murya mai cike da nutsuwa ta furta daga bayanta..
Da sauri ta juyo suka hada ido da wata mata mai kimanin shekaru 29,sauke ajiyar zuciya tayi..
Lafiya me kike yi anan haka?
Matar ta sake tambayar ta..ganin tayi shiru..

'Tana kokarin bude bakinta ne tayi magana taji marar ta na wani azababben ciwo a take kuma taji wani sanyi a ya ratsa tsakiyar cinyoyinta,ihuu ta saki da bakinta dake a bushi da kyar ta kalli matar tace ki.... ki ki taimaka min......dan darajar ....Allah....

Cikin rawar jiki da tausayawa matar ta juya da gudu tana kwala kiran laure......! Laure....!

Cikin sakanni da basu wuce uku ba sai gata tare da wasu mata su biyu sun karaso wajen'ba bata lokaci suka kamata suna mata sannu gaba daya ta gama galabaita ko lumfashinta ma da kyar yake fita..

wani daki suka kaita suna ta yan leke leke...kamar wasu marasa gaskiya..
Laure ta kalli wannan matar tace, JAKADIYA kina ganin abunda muke shirinyi daidai ne kuwa?

Jakadiya Taja lumfashi,laure kina tunanin mu barta ne ta mutu ita da dan dake cikinta sbd kawai wata doka ta sarki?
(dokar sarki Abdul-Jabbar ta farko itace-kada wanda ya taimaki wani bakuwar fuska a cikin kasar sa)

'Da'yar dake ri'ke da wannan yarinyar me ciki ta girgiza kai,nidai a nawa ganin mu taimaka mata ko ba komi babu wanda zamu bari yasan wannan abun da muka aikata bare har a hukuntamu..ko ya kuka ce?

Gyada kai sukayi du'ka sannan jakadiya ta kalli laure,ki fita kisa mana ido a waje sbd tsaro,bana son kowa yasan halin da muke ciki,laure tace hakane sannan ta fita da saurinta..

Shiru ba'ka jin komai sai nishin wahalar da wannan yarinyar takeyi tamkar ranta ze fita..
Cikin min'ti da baifi ashirin da bakwai ba sai ga kukan jariri laure dake waje ta sauke ajiyar zuciya sannan ta leko dakin cikin zumu'din ta..

'Ganin jakadiya da HANSAI sunyi jugudum jugudum dasu yasa ta fadawa cikin dakin hankalinta a tashe,lafiya ? Ta tambayesu..

" Jakadiya ta kalli yarinyar jiririya dake hannunta sannan ta kalli uwar dake kwance bata lumfashi tace ALLAH YA JIKANKI DA RAHAMA baiwar Allah..
laure ta dafe kirji ban fahimce ku ba?,hansai na goge kwalla tace, Allah yayi wa uwar rasuwa,zaman yan bori laure tayi take jikinta ya hau ba'ri,cikin tashin hankali tace yau mun shiga uku mun lalace shi kenan mu kam Allah yayi kwanan mu ya kare a wannan daren....

"Jakadiya ta watsa mata harara,sannan ta kalli hansai ta mika mata yarinyar dake ta wutsir wutsir a hannunta..
'tace ungo karbi diyarnan bari nayi wa sarkin kofa magana yazo sai muyi wa uwar abunda ya kamata a kaita makwancinta..dan shine kawai na aminta dashi..
Da sauri laure ta mike tace,me kike nufi jakadiya yanzu fi sabilillahi ya zamuyi da wannan diyar?bamu san daga wacce duniyar yarinyar nan ta fito ba shine zamu rike diyarta?ni dai a nawa tunanin kawai mu kai diyar nan can wajen gari mu barta acan sbd dai ajiyeta a nan wani tonan asirin mu ne..

" Hansai ta girgiza kai,haba laure me yasa ne baki da ko digon tausayi acikin zuciyarki ,yanzu kawai sai mukai jaririyar nan wajen gari mu ajiye ta?

'Jakadiya ta kallesu duka tace,yarda aka haifi wannan jaririyar a cikin RUMFAR BAYI to tabbas ne a cikin RUMFAR BAYI zatayi rayuwa kuma tabbas dolene mu zamu rike ta....tana gama fadar haka ta fice cikin saurinta...

'Sunyi mata wanka sannan jakadiya ta kira su sarkin kofa suka kaita makwancinta cike da addu'o'i da kuma tausayi suka dawo cikin masarautar bakin su alekum...

'Washe gari tunda sassafe kamar ko da yaushe a al'adun su na Rumfar bayi dukkan baiwar dake karkashin Rumfar dole ne zasu tashi duk su hallara a gaban dakin UWAR BAYI DUBU (head maid)'
'Itace mai kula da dukkan harkokin bayi mata da kuma kuyangin dake karkashin inuwar rumfar bayi..

'Cikin kamala da kuma daurewar fuska DU'BU (uwar bayi ) ta fito daga cikin dakin nata,jakadiya na kusa da ita..
Gaba daya a tare suka gaishe da ita cike da girmamawa kamar yarda suka saba.
'Ta kallesu tana shirin magana ne sukaji kukan jiriri ya karade wajen gaba daya..
Cikin tashin hankali du'bu ta shiga tambayar su,a ina aka samo jiriri a cikin wanann Rumfar bayin da masaniyar ku akai?
Jakadiya gaban ta ya fadi hakama laure dake da gefenta..
Shiru kakeji kowannen su ya kasa magana kamar ruwa ya cinye su..

Du'bu tace,ba da ku nake magana ba!
Jamila ce tayi karfin hali tace,ina tunanin hansai ce ta haihu a daren jiya tunda ita kadai ce me ciki a duk fadin wannan rumfar..
du'bu cike da mamaki tace hansai dai?
Jakadiya tayi saurin cewa,eh! Dan a jiya ni da kaina na amshi haihuwar tata kinsan tunda ta dawo daga rakiyar GIMBIYA KILISHI kasar Rano ta dawo da laulayin haihuwa..

du'bu tace in ko hakane ina taya malam kamilu murna kwarai da gaske (shima bawa ne kuma mijin hansai)
Gaba daya wajen suka hau murna,du'bu ta saka laure tayi mata kiran hansai..
" ita kuwa Hansai dama tana fama da wani ciwo ne cikin yan watannin, cikinta se ya kumbura sun'tum tamkar wata me juna biyu,toh a daren jiya ne mijinta kamilu ya samo mata magani daga kasar zazzau tana sha kuma se Allah yasa ta warke..'wannan kenan'

'Laure ce tayi kiran ta bayan ta sanar da ita duk shirin da sukayi wa du'bu a waje.
Tana fitowa dauke da jaririyar a hannunta ba'yi suka dau shewa dan kuwa yaune kawai aka taba haihuwa acikin RUMFAR BAYI...

"Wannan kenan"

"Wattpadians ya kuka ji shi?
A ci gaba ko kuwa?

It depends on ur comments ooh..😉
[9/18, 3:01 PM] Aysha Galadima:   🏕 *RUMFAR BAYI* 🏕
Na Afrah bhai
Page 2
Wattpad @afreey101               

****************

           "Du'bu da kan'ta ta sa'wa jaririyar suna JUWAIRIYA a take rumfar bayi ta hau shewa da murna, dan'yen dabino suka kwaso daga rumbu suka hau rabawa junan su cike da tsantsar farin ciki dan a ganin su tamkar wata babbar kyauta ce Allah ya kawo musu..

              "A haka Rayuwa taci gaba da tafiya a inda jakadiya da hansai har ma da du'bu da laure suka ci gaba da kula da JUWAIRIYA dukkanin baiwar dake cikin rumfar bayi tana mutukar son'ta,a haka  labari dai har yaje kunnen GIMBIYA KILISHI wato uwar gidan mai martaba kenan.

'Macece mai shegen son milki da kuma son a girgirmama ta,gata shu'unar mace dan kuwa gaba daya masarautar ta daura babu mahalukin da ake bawa girma kamar ta idan aka cire sarki Abdul-Jabbaru, yaran'su biyu kacal da mai martaba' akwai dan ta yarima JALALLUDEEN shine me jiran kujerar mulki  wato heir apparent to the throne kenan, sai HAMZA kaninsa,ganin gimbiya kilishi ita kadai ce Allah ya bawa kyautar ya'ya maza a kaf duka matayen sarki idan ma an hada har da kwarkwarorinsa (concubines )'gimbiyata kilishi kawai ce bata da diya mace'
shiyasa rashin mutumcin nata ya kara girma sannan tsanar sabowar amaryar mai martaba ya shigeta sosai'
dan kuwa itama FULANI DIYYA  wato amaryar mai martabar kenan daya auro daga masarautar bauchi tana di'ra ta santalo dan yaron ta namiji daya dilo wato TURAKI (ABDULLAH )sai diyarta ZAINABA.

ita kam macece mai son jama'ar ta,indai har kina cikin rumfar ta toh fa lallai ne dole ki so ta dan tana mutukar kyautatawa na kasa da ita balle ga bayin ta,shiyasa kaf masarautar tafi dukkanin matar sarki farin jini da kuma karbowa a wajen Bayi..
    ****wannan kenan *****

"Shekaru nata tafiya a inda yanzu JUWAIRIYA na da shekara goma da haihuwa.

   'Yarinya ce mai karanbani sosai bata ji,sai dai tasan iyakarta,dan kuwa kullum zaka ganta tana guje gujenta a cikin rumfar bayi wanda hakan yake saka  bayin dake ciki annashuwa.
ummanta wato hansai tana kokarin bata tarbiyya irin tasu ta bayi marassa ga'lihu,haka kuma kamilu na mutakar son JUWAIRIYA dan dama ya dade yana neman haihuwa Allah bai basa ba.
(kamilu da hansai bayin Allah ne da kaddara ta fado musu aka siyar dasu a matsayin bayi ga masarautar ta daura)

     "Tunda juwairiya ta ta'so bata taba ko da lekawa ne cikin masarautar ba dan kullum tana cikin rumfar bayi' gashi bata da abokin wasa dan duk bayin dake ciki da safiya tayi suke ficewa zuwa wajajen uwayen gidansu. .

   Kamar kullum yau ma hansai ta gama shiryawarta dan tafiya wajen uwar dakinta wato GIMBIYA KILISHI,ta kalli juwairiya dake zaune ta kura mata idanuwanta masu haske,kamo hannun ta hansai tayi tace kici gaba da hakuri juwairiya kinji abbanki zai zo miki da halawa anjima,juwairiya ta saki dan murmushi sannan tace,umma muje na miki rakiya,hansai ta murmusa sannan ta kamo hannunta, suna kaiwa bakin kofa ta sake hannun juwairiya sannan ta shafa kanta kafin ta fice.
     Hansai na tafiya juwairiya tayi saurin karasawa gaban babban kofar ta leka abunda bata taba yi ba kenan sbd gargadin da ummanta tayi mata..

    Ware ido tayi ganin jama'a da yawa nata zurga zurgar su ga wani haske da har kashe mata ido yakeyi ga kuma iska me dadi dake kadawa..

Da sauri ta karasa cikin dakinsu ta dauko mayafin ummanta,ta boye shi a cikin doguwar rigar dake jikinta .
    A hankali ta karasa madafa waton inda ake shirya wa sarki abincinsa, ta leka nan ta tarar da bayin dake dahuwa suna ta aikinsu,ta juya da sauri ta lulluba mayafin a kanta sannan da gudu ta saka kafa ta fice daga rumfar bayi..

**********
     "Tafiya kawai takeyi tana kalle kalle sai washe baki takeyi dan bata taba ganin mutane masu yawa haka ba balle jinsin maza dan kuwa a rumfar bayi babu namiji a ciki.
"wani dan zomo ne ta hango fari dashi tas,ba karamin burgeta yayi ba,ta shiga binsa da gudu batayi aune ba taji tayi karo da mutum bum!
Da sauri taja da baya...

  "Baki da hankali ne?ina kika bar idanuwanki da har zaki taremin hanya ta!!

Taji an fada da wata murya me cike da isa da iko..
   Dagowa tayi da sauri dan son ganin waye wannan me muryar..yake magana kamar yana kirga lafuzan sa.

  Caraf idanunsu suka sarke dana juna..
Wani dan saurayi ne da kalla zai kai shekara sha biyar..
   Juwairiya ta kafe shi da ido dan tunda take bata taba ganin me kyau irin nasa ba,ahankali ta fara fahimtar irin kallon kyama da kaskancin da yakeyi mata..
hakan yasa ta shiga bin shigar shi da kallo..

Sanye yake da kayan alfarma kayane masu tsada ga zinari ta ko ina sai kyalli yake..
  Ta kalli yaron dake kusa dashi at least shi ze kai 11 years,shima din cikin kayan alfarma yake..

    Bakya jina?

Tayi saurin ja da baya kadan sannan tace,a tunani na mu biyune da laifin..

'tunda idan ni bani da ido ai kai kana dashi ba sai ka kauce min ba?

   Cike da tsantsar mamaki suke kallonta..
Wacece ita da har zata ringa maida masa magana haka?

   Juyawa yayi cike da fusata..cikin daga murya yace,wai ina sarkin Lumbu ne! Sallama kana ina!
wayace musu su ringa barin ya'yan bayi masara galihu suna shigowa nan!

Cikin sauri wani mutune yazo ya zube a gaban sa,Allah ya huci zuciyar YARIMA ayi min afuwa ayi min gafara!nayi laifi ka yafewa wannan bawan naka...

    Wanda aka kira da Yarima ya yamutse fuska sannan ya kalli na gefensa,HAMZA me kake ganin zamuyi dasu?
   Hamzan ya tabe baki,kawai mu kaita ga GIMBIYA  tunda dai kowa ya sani BAYI basu da ikon shigowa cikin lumbun TAKAWA (wato sarki)..

    RANKA SHI dade ayi musu afuwa..
Sukaji an fada daga bayan su..

'A tare duk suka juyo suna kallon shi..
Saurayi ne dan shekara 12 kyakkyawa ne sosai rike da hannun yar budurwa da bazata wuci sa'ar juwairiya ba..

  Yarima ya daure fuska, saboda me zaka neman musu gafara TURAKI?

Turaki yai murmushi sbd a tare muke da ita kulangar ZAINABA ce..
     Hamza da yarima suka ja tsaki sannan suka zo zasu wuce ta gefen juwairiya ta dago suka hada ido da yarima ya banka mata harara, ta bi shi da kallon mamaki har ya fice yana jin zafin halayen ta a garesa ....

"Da sauri juwairiya ta karasa wajensu turaki ta dukar da kai tace,na gode ranka shi dade..

  Da kallo yabi fuskarta,daga ina kike?dan ban taba ganinki a cikin masarautar nan ba..
  RUMFAR BAYI ta bashi amsa,ya jinjina kai,zainaba ta  kalli yayanta,yaya turaki ina sonta!
Da sauri suka kalli zainaba cike da mamakin furucinta ..

Turaki yace,zainaba ke da kika ki amincewa da kowacce baiwa?zainaba tayi murmushi sannan ta juya da gudu tayi tafiyarta..
  Turaki ya juya ga juwairiya data bi bayan zainaba da kallo..

Kiyi gaggawar komawa inda kika fito dan na lura ba ki gama fahimtar wasu dokokin masarautar nan ba,yana gama fadar haka yayi ficewarsa...

A sanyaye juwairiya ta koma cikin rumfar bayi gaba daya taji bata ma kwadayin sake fita dan kuwa duk mutanen da ke waje basu da mutumci ita kam zaman ta a Rumfar bayi yafi mata dadi inda kowa yake da same rights dinsa.......

Wannan kenan!

🏕 *RUMFAR BAYI* 🏕
Na Afrah bhai
Page 3


********************

"DAN SARKI JIKAN SARKI !!
"DAN SARKIN DA BASHI BA SARAUTA!!
"AAH LAFIYA TORON GIYA...
UWAR SORO"taci gaba da da yiwa yarima jalal kirari..wanda ke kokarin shigewa falon mahaifiyar sa..ko kallon inda take bayyi ba bata ..
"Sai Hannu kawai da ya da'ga mata fuskar nan a tamke..

"Gimbiya kilishi na zaune akan kilisarta tasha gayu cikin kayan alfarma zinari ne ba'a mgnr sa..
ga bayi nan sai yi mata hidima suke,hansai na gefe rike da tiren fruits kala'kala..

    Kilishi na kallon dan nata ta fahimci cewa ransa a bace yake...
Hansai ta kalla tayi mata alama da su fice daga falon..

'Hansai ta mike sannan tayi wa bayin dake cikin falon mgn akan su fice..

   "Kilishi ta kalle sa,yarima lafiya?
Yarima jalal ya dauke kansa gefe..
Tasan bazai yi mata mgn ba dan haka sai ta kalli hamza..

  Hamza me ya samu yayan naka?
  Hamza yaja tsaki,wai fa umma dan..........nan ya fada mata komai..

A fusace ta mike tana huci,wacce baiwa ce da har take da wannan ikon na maida wa yarima mgn!dole ne na hukunta ta dole ne tasan matsayin ta.!!!..
  Yarima ya mike da sauri...
Kada ki damu umma na lura gidahuma ce dan bata gama sanin matsayinta ba..
Kilishi taja tsaki,dolene ta fuskanci hukuncin abunda tayi!..
Yarima ta riko hannun umman nasa,kada ki damu umma ya sakar mata murmushi..
Da kyal da so'din goshi yarima ya samu ya lallaba kilishi ta hakura..

**********
"Da gudu zainaba ta shiga makeken falon FULANI diyya dake tsare tsab cikin kwaliya ta gargajiya..
   'Fulani diyya na zaune a kilisarta ga bayin ta nan duk sun zagaye ta sai hidima suke mata..

"Ganin zainaba ta shigo da gudu cike da murna yasa ta fadada murmushin ta..
   Laure dake gefen fulani ta shiga fadin,yar sarki diyar FULANI wannan murna taki dole ta farantawa dukkanin wanda ya kalli wannan kyakkyawar fuskarki rai..

Zainaba tace Allah ko laure?
Laure tace kwarai kuwa ranki shi dade..
Fulani ta murmusa,me ya sakaki wannan farin cikin zainaba?

  'Ta zauna tana lankwashe kafafunta,fulani na canja ra'ayina ina so a yau din nan nima a bani baiwata..

  Fulani ta kalli laure cike da murna,laure tace Yanda kike so ai haka za'ayi gimbiyata..

Laure ta mike da sauri tayi waje..
Cikin minti goma sai gata da wasu yan matan bayi su biyar..

    Ta kalli zainaba dake kishingedi tana cin tufa (apple )
  Gasu nan ki zaba wacce ta mike gimbiyata..
    Zainaba ta kwabe fuska sannan ta kalli fulani,umma duk bani son su..

Fulani ta kalli laure tayi mata nuni da ta koma ta canzo wasu..
Laure ta sake fita ta shigo da wasu yan matan har su shidda..

Still zainaba a shagwabe tace suma haka..
Laure cike da gajiya da wulakancin zainaba ta fice ta sake dauko wasu dan saida ma ta zabo su sannan ta zo dasu..

Zainaba ta girgiza kai tana turo baki..

Fulani ta sauke ajiyar zuciya dan ba yau bane zainaba ta fara wannan fitinar..
    Toh wai zainaba wacce irin baiwa ce kike so ne haka?ina tunanin sai dai a kai ki can kasuwar bayi ki siyo da kanki..

  Zainaba tayi saurin cewa ah ah RUMFAR BAYI  zaku kaini umma..

Cike da mamaki bayin dake wajen suke kallonta dan kuwa babban kaskanci ne ace jinin sarauta ya shiga rumfar bayi..

   Kina da hankali kuwa!

Fulani ta fada cike da daga murya..
   Zainaba ta turo baki,umma ni wacce nake so tana can a RUMFAR BAYI..

  Laure ta hadiye yawu kut amma sanin kuma juwairiya bata fita ko ina.. da wuyane a san da ita a cikin masarautar ma,sai ta sauke ajiyar zuciya tace,ranki shi dade wacece ita yanzun nan na kawo miki ita?

   Zainaba ta langwabar da kai..
Sannan tace..

  Wata yarinya ce kamar ni haka..
   Laure taji kafafunta sunyi sanyi..
Fulani tace,me kike fada haka,kin taba jin a Rumfar bayi akwai yara ne?

Zainaba tace wlh umma da bakinta tace mana a Rumfar bayi take..kima tambayi yaya..
   Fulani zatayi magana sukaji ana sanar da shigowar turaki..

    Sai daya zauna ya gaisar da fulani sannan tace..
Wai turaki wane shirme ne zainaba ke fada,tace min akwai yarinya baiwa dake rumfar bayi kuma ita take so a matsayin baiwar ta ..

   Laure ta cije baki...a ina zainaba ta gano juwairiya kuma?

  Turaki ya kalli zainaba, ke dama da gaske kike?

Zainaba ta gyada kai ni ita nake so ta zama BAIWA ta ..
Ya kalli fulani eh mun hadu da wata yarinya dazu tace mana a Rumfar bayi take..

  Fulani cike da tsananin mamaki ta kalli laure..
Wai haka?
Laure ta kakalo murmushi..
A...eh..eh....kam..anyi haka..akwai diyar hansai ina tunanin itace suka gani din...

Fulani ta ce cike da kasaita a kawo min ita nan!

Laure ta mike da sauri tace toh ranki ya dade..
  Laure na fita ta shiga buga sauri bata zarce ko ina ba se sashen gimbiya kilishi tayi tsaye tana tunanin yarda zata samu mgn da hansai...

  Can ta hango wata baiwa ta fito da tire a hannunta,laure ta tare ta da sauri..
  ke Yimin mgn da hansai kice mata ina mata neman gaggawa..

   Laure na nan jingine da kango sai ga hansai kamar an jeho ta, ta kalli laure ya akayine laure?

   Laure tace ina jakadiya?
Hansai tace tana can fadar mai martaba ,laure taja lumfashi sannan ta sanar ma hansai yarda ake ciki,hansai ta dafe kirji yau mun shiga uku yaushe juwairiya ta fito daga rumfar bayi?

Laure tace ba wannan ba yanzu ya zamuyi?dan fulani ta nemi dana kawo ta..
  Hansai tace a gaskiya bana son juwairiya ko kadan tayi irin rayuwar da muke ciki,bamu san asalinta ba bamu san daga wace duniyar ta fito ba amma laure wlh bana son ganin juwairiya cikin damuwa ko kadan,kuma kinsan halinta kwarai bata ji  kada taje tayi wani laifin...... kuka ne yaci karfin ta..

  Laure ta dafa ta bari na saka wani bafaden yayi mana kiran jakadiya se mu san nayi.

Cikin tashin hankali jakadiya ta karaso wajen su,lafiya naji kira haka,shamaki yake ce sanar min ana nema na bayan kunsan yau ina fa'da ne da kyal na samu waziri yamin alfarmar tahowa..

   Hansai na hawaye ta sanar mata da komai,jakadiya taja lumfashi toh miye a ciki?dole ne kun san watarana hakan zata faru,laure tace bari dai na je na kai ta wajen fulani nasan dole ne a gobe zata fara aikinta na BAUTA...

Laure ce ta shigo rumfar bayi can ta hango juwairiya tana ta tsalle tsalle

Please Login or Register in order to submit comment