Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Butulci ga Allah lokacin Daya Jarabceka da Wata Jarabawa Godiya zaki ma Allah, kar in sake jin kin aibata 'yarki.." Ya faɗa cikin Sanyin Murya gyaɗa kai Inna Fulera Tayi tana Kuka Lokaci Ɗaya Jikinta yayi sanyi Ta kalli Mufeeda Dake Durƙushe Tana Kuka Lokaci Ɗaya tace "Na..yafe miki Mufeeda...Allah ya bamu ikon Cin Jarabawarsa Haƙiƙa na Shaida ke yarinya ce mai Tarbiya Hakama Alhaji na yarda da Ƙaddara ne ta Faɗa muku Domin Dattakonsa Data iyayensa Shike Riƙe damu Har yanzu... Amma Ina Roƙon ku don Allah kada ku Zubar da Cikin ku barma Mufeeda Shi ƙila Wata rana Shi zaiji kanta ko kuma ƙila Shi kaɗai ne ƙwanta a nan Duniya.." Farida dake Jikin Umma ta ɗago Tana Faɗin "Wallahi sai yabi Rariya Uban Wa zata Haifa ma Shege..? Ba anan gidan ba Wallahi sai an Zubar Dashi..."

Ta faɗa Cikin ƙaraji Da Kuka Abba ne ya mata Daƙuwa yana Faɗin "Kinci Ubanki, Farida In na Sake jin bakinki Anan Wajen Wallahi sai naci Mutumcinki mutuniyar Banza da Wofi.." Ya faɗa yana Hararanta Umma dai ƙwallah Take Sharewa Duk Jikinta yayi Sanyi Su Goggo Abu kuwa An Shiga ƙwaryar Nadama.

Baba Hakimi ne yace "Dama waya ce miki za'a Zubar..? Haba kamar ba masu Hankali ba kenan bamu yarda da Ƙaddara ba, taya zamu aikata Wani Zunubin kan Wani Zunubin kuma..? Mufeeda zata Cigaba da Rainan Cikinta kuma ta Haifeshi da Ikon Allah Acikin gidan nan Saboda Lura, Ɗanbatta ƙauye ne In Muka Tafi da Ita labarin zai yi Tambari Gwara abarta anan Ɗin Harta Haihu muga Abunda Allah zaiyi..."

Zabura Farida Tayi Tana Faɗin "Awani gidan..? Wallahi ba a nan gidan ba..? Bata isa ta haifamin Ɗan Shege a gida ba.." Tahir Dake Duƙe ya Ɗago da Jajayen idanuwansa yace "Toh sai dai ke ki bar gidan, Amma Babu fashi kamar Yadda Hakimi yace Mufeeda zata Haihu anan gidan Insha Allahu..." Ya faɗa yana mata wani kallon Tsana Baba Hakimi ya saki Murmushin Takaici Amma ƙasan Ransa yaji Daɗin Amsan da Tahir yabama Farida.

Kuka ta ƙara sakawa kafin tace "Haka kace..? Toh Wallahi sai dai na bar gidan ni ban zauna ba...Bazan zauna gida Ɗaya da karuwarka wacce kama Ciki ba.." Umma ce ta Make mata baki Tana Faɗin "Rufema mutane baki Mara Kunya Gaban iyayenshi kike gaya mai magana Haka Irin Tarbiyar da muka baki kenan..?"

Ta faɗa Tana kallonta Cikin ɓacin Rai Durƙushewa Farida Tayi Tana Cigaba da Gunjin kuka, Abba yace "Saurareni Da kyau Farida kinga matuƙar naji labarin kinbar gidan Mijinki Wallahi sai na Saɓa miki Sakarya mara Hankali Wacce iliminta da shekarunta basu amfana mata komai ba..Wallahi in baki Shiga Taitayinki ba Naji labarin kinyi ma Tahir ko ita yarinyar Wani Abu sai nazo Har gida nan gaban 'ya'yanki na barki Kwance ja'ira kawai.." Ya faɗa Cikin Fushi da Sauri Farida Ta Miƙe ta Haura sama Tana Gunjin kuka gaba ɗaya Aka bita da kallo kafin Baba Hakimi ya kaɗa kai yana Faɗin "Ayyah Ibrahim ga Wacce Girmanta da Shekarunta basu mata amfanin komai ba nan Zainabu..ai ko banza ta Haifi Farida Tsakani ga Allah bata Fita Hankali ba..?" Ya faɗa Cike da Takaici Goggo Abu Dake kuka ta Buɗe baki zatayi magana Baba Hakimi ya ɗaga mata hannu yana Faɗin "Karma ki ɓata bakinki...Yanzu Maganarki banda ɓata min rai Babu Abunda Zatayi Gwara ma ki rufe bakinki zai fi alheri agaremu Gabaki Ɗaya.." Goggo Abu Tayi ƙasa Dakai Hawaye na Zubar mata tace "Attahiru ka yafemin...Mufeeda kema ki yafemin.." Daga Haka ta miƙe ta Fita Zuwa Haraban Gidan Tana Kuka.

Baba Hakimi ne yace "Fulera kama Ɗiyarki ku Shiga Ciki ki ƙara lallashinta kinji itama ba laifinta bane.." Jiki ba ƙwari Inna ta Miƙe ta Kama Mufeeda Da ƙyar Dake kuka Suka Nufi Ɗakinta Iya Dake gefe sai Lokacin itama ta Miƙe tana Sharan Ƙwallah na Tausayin Waɗannan Ahalin Innaro Ta miƙe Ta Bita tana Faɗin "Kai ni Ɗakinki Iya na kama Ruwa nayi sallah.." Da Toh Iya ta karɓa kafin su Nufi Ɗakinta Kowa Zuciyarsa ba Daɗi.

Umma ma Miƙewa Tayi tana Faɗin "Bari naga Farida.." Kai Abba ya gyaɗa mata kafin Ta Haura sama tabar Baba Hakimi da Abba da Tahir da Ishaq Suna ƙara Jajanta lamarin.

Umma Kwance Taga Farida na Kuka, gefenta ta Zauna Tana Faɗin "Farida...Bai kamata kiyi kuka ba kamata yayi ki zauna kima kanki karatun ta Natsu ki gyara Kuskuranki, ki kama Allah ki kuma Roƙi gafaran Mijinki ki Rungumi 'ya'yanki kinga Abunda ya Faru..? Izina ne gareki da Kuma mata masu irin Halinki Daga ƙarshe ina Ja miki kunne da ki Natsu In ba Haka ba Wallahi Dagani Har Abbanki zamu Ɗauki mummanan mataki Akanki.."


Daga Haka ta miƙe ta Fice Daga Ɗakin Tana Fitowa su Baba Hakimi na Miƙewa, nan Suka ce kowa ya Fito zasu Wuce Inna Fulera Data kai Mufeeda Ɗaki ta saka Gefen Hijabinta tana Share mata ƙwallah Mufeeda na kallon Inna Fulera Take Fadin "Inna ki yafemin...Ba laifina bane.." Murmushi Inna Fulera ta mata kafin tace "Na yafe miki 'Yata..Allah yayi miki albarka ya kuma Saukeki lafiya.." Jin Haka yasa Mufeeda Ta Rungume Inna Fulera Suka Fashe da Kuka Lokaci Ɗaya, Iya Data leƙo kiran Inna Fulera itama sai dai taji ƙwallar Sun kawo mata, muryan Iya ce ta saka suka saki juna Nan take sanar da ita ta Fito zasu Koma.

Kumatun Mufeeda ta Shafa kafim tace "Ki kula da kanki kinji ko Mufeeda..? Allah na Tare Dake..." Daga Haka ta saki Hannunta ta Fice Daga Ɗakin Tana Sharan ƙwallah kan gado Mufeeda ta zame tana kuka mai Cin Rai tana jin kamar Bazata ƙara ganin Innar ta ta ba kenan.

A waje Suka samu Goggo Abu bayan Dukkansu Sun Fito Innaro ce kaɗai ta samu yin Sallah Sauran Baba Hakimi yace in Sun Isa gida kowa sai yayi..Abinci kuwa Da Iya Ta jera ba Wanda ya kalleshi Motar Su Abba da Umma ce Ta fara Fita Daga gidan sai ta Baba Hakimi Wanda Garzali zai Maidasu bayan Baba Hakimi yaja Tahir gefe ya ƙara mai Nasiha sosai ya kuma Nusar dashi ya barma Allah komai Da Haka Suka rabu Bayan Motar Ta Fice Daga Haraban Gidan

Ishaq ma bai koma gidan ba, Daga nan Sukayi sallama da Tahir ya Shiga Motarshi ya Fice Daga gidan Bayan shima ya ƙara bama Tahir ɗin baki sosai...Ya Daɗe Tsaye yana Sauke Tagwayen Ajiyar Zuciya Lokaci Ɗaya yana Goge Siririyar ƙwallar data Siraro mai ya Juya ya tunkari Cikin Falon gidan.





*Anitha..*
*Aisha Alto..*
*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Alkaluman:*✍️

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty*💕

_*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_


_*Muna Mika sakon godiya bisa ga masoyanmu na nesa Dana kusa,Bisa ga yadda suka yi ta aikomana da sakon gaisuwa kama daga Masoyanmu na Whattapp da kuma Wattpad munga tarin sakonninku na Ta"aziya muna godiya Sosai Allah ya bar zumunci Muna Fatan Allah ya Sa Dukkanmu Fatima Binafa tazama mai Cetonmu Ranar gobe Kiyama Ameen..*_🤲


     *BABI NA GOMA SHA HUDU*

""""Cikin Sanyin Jiki Da Takun Jarumta ya Shigo Falon,Babu Kowa ya Tsayawa yayi Shuru yana Bin Dakin Mufeeda da kallo Wani Zuciya yana Tambayanshi Ko Wani Hali Take Ciki..? Ganin bashi da Amsa ne ya sanya ya Kada kai ya Fara Kokarin Haura Steps yaji Muryan Basma Tana Fadin"Daddy... "..

Da Sauri ya Juyo yana Kallonsu Ita da Bassam da Laila da Madu Sun Kuramai Ido Fuskokinsu Cikin Damuwa da alamun ma Basma Tayi Kuka ne,Gabansa ne ya Fadi Kunya Ta kamashi Yama manta Sam da yaran Da wani Ido Zai kallesu bayan Sunji Abunda ya Aikata..? Cikin Karfin Hali ya Furta.."Basma Wht hpped....? Yafada Cikin karfin Hali.

Kuka ne ya Kwace mata Da Gudu Ta Isa gareshi Ta Fada Jikinsa Ta kara Sakin Kuka Kamar Wacce Aka Daka,Hakama Bassam Ya Rugo Shima ya Fada bayan Basma Shima yana Kuka Tahir ya Rutse Ido kafin ya Dora Duka Hannuwansa bayan Yaran Nashi yana Bubbugawa alaman Lallashi Idanuwansa ya Bude da Suka kara kadawa Sukayi Jajir ya Sauke kan Muda da Laila Dake Tsaye Suma Suna Share Kwallar..

Hannu ya Mika Musu Alaman Su Taho Suma Da Gudu Suka Taho Suka Fada Jikinshi Yahadasu ya Rumgume Cikin Kuka Basma Ke Fadin"We Relly Srry Daddy.,Momy Ta Cuceka Daddy Mun yadda Muna Son Cikin Mufeeda Ta Haifama kani.."Take Fada kamar Wata Babba Wani Yam Tahir Yaji Cikin karfi Hali ya Sakesu yana kallon Cikin Idanuwan Basma ya Dafa kanta yana Fadin"Nothing To be Worry My Dota,Stop craying and Kar nakara Jin Sunan Momy ku Abakinki balle kice ta Cuceni koma Menene She is my Wife Ku ma,Kuma Mahaifiyarku ce So Stop All dis Kinji ko..?.
 
Gyada kai Tayi Tana Share Kwallarta Kafin ya Saki Kanta yana kallonsu  Dukkansu Cikin Karfin Hali yace"And All Dis..Don't let Anyone Know abount It kunji Ko  Amkaranta Karku Sake Kuyi Zencen da Wani Kuma Laila Koda Kun Koma Gida ko Mamanku karku Fadamwa Kunji.."Kai Suka gyada Kafin Su Hada baki Suka ce"Insha Allahu Daddy We are going To Hide Dis Secret.."

Mirmishin Dayafi Kuka Ciwo ya Hadiye kafin yace"Ok..Muda da Bassam Kuje kuyo  Alwala naji  Ana Kiran Sallar Mangarib,ku kuma Ku Koma Daki Kiyi Taku sai Mun Dawo ."Da kai Suka amsa kafin Kowannensu Ya Juya Basma da Laila Suka Nufi Dakin Basma Hakama Bassam da Muda Suka Nufi Dakin Bassam Din Ko bakomai Zuciyarsu Ta Warware ba kamar Dazu ba....
 

  Sai da Suka bacemai kana ya Kada kai ya Fara Taka Steps Cikin Sanyi Jiki,ya Dade Tsaye Kofar Bedroom Din Farida yana Nazarin Wani Abu kafin ya Cije Lebe ya karisa Cikin Bedroom Dinshi Tiolet ya Fada agurguje yayi Wanka yazo ya saka Wata bakaer Jallabiya da Hula ya Dau Carbinsa ya Fito,Afalo Suka Hadu dasu Muda Suma Sun Fito nan da Nan ya Rike Hannayensu Suka Fita Zuwa Masallaci.

***

Mufeeda Kuwa Bayan Fitan Inna Fulera Kan Gadonta Ta Fada Tana Gunjin Kuka Wani Tsausayin Kanta Dana Tahir na Kara Kamata Zuciyarta Tana mata Rawa In Ta Runtse Ido Ta Tuno Sanda yake Mgana yana Zubar Hawaye bazata Jura ganin Hawayen Tahir ba Tana Jin Abun Acikin Ranta Bata da yarda Da Zatayi ne.

Tana Cikin Wannan Halin ne Iyya Tazo ta Sameta,Zama Tayi Gefen Gado kafin Ta Dagota Tana Fadin"Mufeeda...Mufeeda..."Tafada Tana Dago Fuskarta Wacce Tayi Faca Faca Da Hawaye Sosai Cikin Mutuwar Jiki da Tsausaya Iyya Ta Fara Fadin"Mufeeda,Kibar Wannan Kukan Kinji ko..? Bashi da Wani Amfani Tunda Mai Afkuwa ta Afkuwa...'Tafada Tana Share mata Hawaye Da Hannunta Duka Biyu.

Kuka ya kara Ciyo Mufeeda Sai ta Sulale kan Cinyar Iyya Tana Yi Tana Fadin"Ya zanyi iya..? Na batama Kowa Rai Ba laifina ba..Bansan Haka zata Faru ba Kuma Shima Daddy ba Laifinshi bane Iyya,Momy zata Kasheni ina Jin Tsoro.."Idon Iyya ya Kawo Kwallah Cikin Lallashi Take"Ayyah Bar Fadin Haka Mufeeda Babu Abunda Hajiya Zata Miki Alhaji bazai barta Kibar Kuka babu Abunda zai Faru Kinji ko.."

Tafada Tana Dago Kan Mufeeda Lokaci Daya Tana Share mata Kwallah Mirmishin Yake Mufeeda Tayi kafin tace"Nagode Iyya Akullum Ina kallonki Tamkar Inna tace..Nagode Sosai.."Kumatunta Iyya Ta Shafa kafin Tace"karki Damu Mufeeda duk Abunda Ke Damunki karki Boyemin ki Sanar dani Kinga yanzu bake kadai bane Kina da Yaronki Ciki Toh yakamata Ki Kula da kanki kinji ko.."Kai Ta gyada mata Tana Mirmishi kafin Tace"Insha Allahu.."
.

Mikewa Iyya Tayi Tana Fadin"Maza Ki Tashi Kiyi Sallah Nima bari naje nayi alwala,Kafin Na Idar da Sallah Abincin ya Karisa.."Mufeeda Ta Mike Tana Fadin"Toh Iyyah..."Har Iyya Ta Juya Zata Fita Mufeeda Tace"ahm  Iyyah.."Iyyah Ta Waigo Tana Fadin"Na"am Kina mgana ne Mufeeda..? Kai ta gyada mata kafin Tace"Eh nace Ina Naila Take ne banganta ba..?

Iyyah Tayi Mirmishi Tace"Tayi barci Ammh Itama Tayi Ragimar Rashinki Tana Dakina In Kin Idar da Sallah Kije ki Dauki Yarki  "Tafada Tana Dariya Kafin Ta Fice,Mufeeda Dake Tsaye ta Murmusa kafin ta Saki Ajiyan Zuciya Ta Shige Tiolet Din Dake Dakinta Domin Dauro Alwala.

****
Farida Kwance Take Ruf da Ciki Tana Rafzan Kuka Ji Take kamar Zuciyarta zai Fashe da Bakinciki Da Kishi Sun Taru Sun Mata Yawa Tana Ji kamar Tatashi Taje ta Shake Mufeeda Ta Mutu Daga Ita Har Abunda Ke Cikinta.

  In Ta Tuna Wai Tahir ya Hada Shimfida da Mufeeda Sai Taji Tafita Hayyacinta babban Abunda Ke Kara Ruguza mata Zuciya Sai Cewan Datayi Mufeeda ta bar Gidan Ammh Ko Kunya Tahir ya bude baki yace Bazata Tafi ba Kenan awannan Gidan Zata Reni Ciikin Kuma Ta Haifeshi Tana Gani Ina Hakan Bazai Taba Yuyuwa ba Wlh bazata Iya zama da Mufeeda Acikin gidan nan ba Duk Abunda Zai Faru Sai dai ya Faru

  Hawayen Idonta ta Share Kafin Ta Sauko Daga Kan gadon Wayarta Dake Gefe Ta Dau Tsuwa,Jawota Tayi Ta Duba Taga Daya Daga Cikin Kawayensu Tasan Kan mganar Bikin kanin Bilkisu ne,Tsaki Taja ta Kife Wayar Acikin Ranta Tana Fadin Bata da Lokacin Wannan Bala"in daya Tunkarota ya Isheta Tiolet Ta Fada Domin Dauro Alwala Tanayi Tana Kuka Kamar Wata Karamar yarinya.

Gabadaya Ranar gidan Babu Sukuni Su Basma ne kadai Sukayi Dinner,Tahir Coffea Kadai Yasha ya Koma Dakinsa,Mufeeeda ko Takasa Fitowa Falo Iyyah ce Ta Dauki  Abincin Ta kaimata Dakyar Ta Lallasheta Ta Iya ci Ta Kwanta Tana Ajiyar Zuciya,Ita ko Farida Kofarta ma Arufe ne Kuma ba Wanda yama yabi Ta Kanta Duka Zukatan Haka Suka Kwana Zuciyoyi ba Dadi,Hatta da Umma da Abba Suma Haka Suka Kwana Cikin Zullumi balle Goggo Abu Wacce Tunda Suka Dawo Hakimi bai kara mata Mgana ba Domin yanaganin Duk Itace Silan Faruwan Komai....

Bangaren Inna Fulera Kuwa Kwana Tayi Kuka Cikin Damuwa Gefe Daya na Zuciyarta na Tsausayin Yarta yarinya karama Ta Shiga Cikin Jarabawar Rayuwa,Haka Tatashi ta Dauro Alwala Tana ta kaima Allah Kukanta Kamar yadda Tahir ya Kwana Salloli yana Neman Gafaran Allah kafin Safe yaji Zuciyarsa Tamai Sanyi Duk Nauyin Dadade Tanayi Tun bayan Faruwar Lamarin Yaji ya Washr ko banza ya Rage kaso 74 daga Cikin Damuwarsa.

***

Washegari Tun Karfe 8 na Safe Tahir ya Fita ko Breafsat bai Tsaya Yi ba,Domin baki na Jiransu Ishaq Tun 7 ya Isa Shima ya Tadashi Daga barcin Daya Kwasheshi bayan Sun dawo Daga Sallar Asuba Shida su Bassam da Muda.

Farida najin Fitar Tahir Tayi Zumbur Ta Mike Daga Kwancen Datake Domin Tana Ta saman Steps Din Ta Hangeshi suna gaisawa da Iyya kafin ya Fice Da Sassarfa,Tana ganin Haka ta Fara Saukowa Daga Steps Din Benen Tana Hada Hanya Bibbiyu Sanye Take da Riga da Sikat Din Atamfa Tun na Daran Jiya,sai Wani Hijabinta Red Colour Wanda Tayi Sallar Asuba Dashi,Iyyah na Kichen Tana kokarin Soya Kwan da Za"ayi Breafsat Dashi Taga Wucewar Farida Da Sauri Kamar Ta Kifa Zuwa Dakin Mufeeda,Iyya Tayi Tsam da Sauri kamar Ta Bita sai Wata Zuciyar Tace Bazata saba Mganar Iyayenta ba.

Mufeeda na Kwance Kan Gado Tana barci Gefenta Naila ce Itama barcinta Yadda Naila ta Riketa Kamar Wasu Uwa da yarta Tsaye Farida Tayi Tana Binsu da Kallo Wani Takaichi mai Hade da bakin ciki da Kuma Kishi Suka Taru Suka kara Tunzurata Cikin Fitan Hayyaci Ta Karisa ga Mufeeda Daga Tsayen Ta Saka Hannu Ta Daka mata Duka Abayanta Cikin Masifa tace"Tashi...Tashi Don Ubanki Yau zaki bar gidan nan Tunda Bana Ubanki bane.."Take Fada Tana Kara Sakarma ta Duka Abaya

  Kamar Amafarki Taji Saukan Dukan Tayi Firgigi Ta Farka Tana gyara zaman Doguwar Rigar Barcin Dake Jikinta Cikin Fargaba da Faduwan gaba Ta kara Ware Ido ganin Farida Tsaye Akanta tana Huci kamar Wata Macen Zakayan,Da Sauri Mufeeda ta Sauko Daga kan Gadon Ko"ina na Jikinta na Rawa Tace"Ina..ina..kwa...kwana Momy.."Rankwashi Farida ta Sauke mata akanta kafin Tace"Karki kara Kirana Mommy Domin Ni ba Uwarki bane,Da"ace Kin Dauki ne Amatsayin Uwa da baki Hada Shimfida Da Mijina ba,Mufeeda Kin Cuceni Mijina fa Kika Sani kuma Har yayi miki Ciki Kuma Shikenan Don Ina Sakarya sai na barki Ki cigaba da zamamin Agida..? Tafada Tana Nuna kanta Lokaci Daya Hawaye Duka Wankrmata Fuska.

Mufeeda da Hannunta Guda Daya ke bisa kanta Daya kuma yana Kan Bakinta tana Danne Kukanta Cikin Wani yanayi da Firgici Take Fadin"Don Allah Mommy Ki..."Bata karisa ba Farida Ta Wani ,mugun Dauketa da Wani Lafiyayyan mari sai da Ta Kife Bisa gado Ta Fashe da Kuka wanda Hakan ya Tashi Naila Daga barci ganin Mufeeda na Kuka sai Itama ta Canyara Kuka.

Iyya na Kichen Tana Kokarin Hada Kayan Karyawan Taji Kuka Daga Dakin Mufeeda Ga Naila Taji Kukanta Da Hanzari ta bar Abunda Takeyi ta Fito,Da Gudu Zuwa Dakin Mufeeda Daidai Lokacin Da Farida Takema Mufeeda Watsi da kayanta Dake Cikin Wardrope Tana Fadin"Tashi..Maza Ki Hada Kayanki Cikin Jakarki yanzu zaki Barmin Gida Bazaki Haifan Dan Shege Agida ba Kije Cutar da Kikamin Allah ya Sakamin.."Take Fada Ta kara Watso mata kayanta Wasu Har kan Jikinta,Itako Mufeedan Sai Kuka Take Kamar Ranta zai Fita tama Kasa Mgana,Naila Kuwa Rarrafowa Tayi Zuwa Wajen Mufeeda Ta lafe Ajikinta Daukanta Tayi Ta Rumgume Tana lallashinta Tana Kuka.

Iyya Dake Tsaye Taji kwallar Tsausayin Mufeeda Sun Cika mata Ido,domin Farida ba Abar Tsausayin Bane Duk Abunda ya Faru Tsakanin Alhaji da Mufeeda Itake da Alhakin Kaso mafi Girma Aciki,Cikin Hanzari Ta Karisa Dakin Tana Fadin"Ashh...Hajiya me yayi Zafi kuma..? Take Fada Tana Rikota Daga Rikito kayan Mufeedan Datakeyi Daga Cikin Wardrope.

Cikin Hargagi Farida ta Fizge Jikinta Daga Na Iyya Tana Fadin"Babu Ruwanki Dani,Wlh kinjima Na Rantse Sai Mufeeda Ta bar gidan yanzu.."Tafada Tana Zaro mata Jajayen Idanuwanta Jin Haka yasa Iyya Tayi baya tana kallon Ikon Allah Farida tana Juyowa Ta Saka Hannu Ta Fizge Naila Hannun Mufeeda Tana Fadin"U get me Right ko..? Toh maza Tashi Tashi ko kuma na Watsaki keda Kayanki Zuwa Waje.."Tafada Tana Rike Naila Wacce Ke kuka Tana Zille zille Ita Asaketa ta koma Wajen Mufeeda.

Mufeeda na Kuka Tana Tattara kayanta Tana Tusawa Cikin Babban Akwatunta Wanda Faridan Ta Siya mata,Ita kuka Farida Kuwa Hawaye ke Zubarmata Saboda Fitina Mufeeda na Zage Akwatin Farida ta Mikama Iyya Naila Tana Fadin"Rikemin Ita Iyyah.."Tafada Tana Tunkaran Mufeeda Wacce Ke Tsaye Tana Kokarim Sanya Hijabin Dake Hannunta Fizagar Hannunta Farida Tayi Lokaci Daya da Akwatin Kayan nataTafara Janta Zuwa Falo Tana Fadin"Fito Muje Mufuka Macuciya Allah ya Isa Tsakani na Dake Mufeeda Wlh bazan Taba yafemiki ba.."Take Fada Tana Kuka Lokaci Daya Tana Faman Jan Mufeedan Har Tsakiyar Falon,inda Taci karo dasu Basma da laila da Bassam da Muda dake Tsaye suna kallon Ikon Allah Domin Hayaniyar Faridan Ya Tadasu Daga barci.

Cikin Mamaki Basma Ta kalli Bassam shima ya kalleta Kafin Su maida Kallonsa kan Farida Wacce Ke Jaye da Hannun Mufeeda Tana Kuka ga akwatunta,Cikin Siririyar Murya "Mommy Ina zaki kai Mufeeda..?
Cikin Tsawa da Fada Farida tace"Gidan Ubanta zata Koma basma Ai nan ba gidan su bane.."

Tafada Tana kara Jan Mufeedan Iyya Dake Biye da Ita Dauke da Naila Dake Kuka Cikin Ranta Addu"a Take Allah ka Jeho Tahir yanzu Kowani babba Wanda zai iya Dakatar da Farida Daga Kudurinta,Basma da Abun ya bata Haushi Kawai sai Tasha Gaban Faridan Tana Fadin"A"a Mommy Kin manta Abunda Su Baba Hakimi Sukace Mufeeda zata Cigaba da zama tare damu ko Bassam..? tafada Tana kallonshi Da Sauri ya Gyada mata kai ..

Farida Dake binsu da kallo Cikin Mamaki da Fushi Tace"Au..Allah Haka Sukace kenan..? Tafada Cikin Salon Rainin Hankali Basma Tace"Eh mommy Harda Daddy ma Haka yace.."Kafin Basma Ta kara Motsi Farida tace"Naji Masu Daddy ban Hanya na Wuce ko naci Ubanki yanzu nan.."Basma Takura ma Farida Ido,idanuwanta Sun Cika da Kwallah batasan Sanda Bakinta ya Furta"Haba Mommy meyasa Zaki yi haka..? Duk Abunda ya Faru da Daddy KE CE SILA,domin da baki banzatar Dashi ba,Kuma baki Banzatar damu da yanzu Muna Cikin Farincikin mu,Saboda Haka bazan Matsa ba Wlh bazaki Kori Mufeeda ba.."Ran Farida ya baci Ta Saki Hannun Mufeeda Ta Dauke Basma da Wasu Tawagen Maruka Tana Fadin"Ni ne zaki Fadama Wannan Mganar Basma.."

Bata Dauke Numfashi ba Taji Itama an Wanketa da Maruka Har Biyu Sai da Tayi Taga Taga Zata Fadi kafin Ta iya Tsayuwa da Kafafunta Cikin mamaki Take bin Wanda ya mareta da Kallo Tahir ne Tagani Tsaye Akanta yana Huci Gefe Daya yana Binta da Wani Matsayin kallo Domin Tun Mganar Basma na Farko yake Tsaye bakin Kofar Shigowa Falon,Ya Dawo Daukan Wasu Fayels ne Daya manta Dasu yau Bai Fita Dasu Shine yana Shigowa Falon yaci karo da Abunda Farida Keyi nan da nan Fushinsa ya Dawo Sabo kusan Mai Hakuri bai iya Fushi ba.

Cikin Nunata da Yatsa ya Furta.."Eh Din ta Fadamiki..? Zaki yi Wani Abu ne .? Ko Abunda Ta Fadamiki ba Gaskiya bane..? Tir dake Farida Kinyi Asara Tunda Har ya'r dakika Haifa Daga Cikinki Tafi ki Sanin Abunda yadace Dake Wlh Kinji Kunya Kuma Kinyi Asara Duniya da Lahira.."Yafada yana Huci kamar zai Daketa.

Baya Taja tana Tsiyayan Hawaye Tana kallonshi Cikin Tsoro Domin Batasaba ganin Tahir Cikin Wannan yanayi ba Cikin Kuka tace"Ni ce nayi Asara Tahir...? Ni Farida ni ka mara gaban ya"ya da Yan Aiki.."Ya Taso mata yana Fadin"Amm mareki Di n ko zaki Rama ne..? Bari ki ji na gaya miki na Fada Kuma zan Kara Fada Wlh Baki isa Ki kori Mufeeda Daga gidan nan ba Sai Dai ke in kin ga bazaki iya ba ga Hanya nan ba Wanda ya Rikeki Dama Banga Uwar Da kike Tsinana mana ba Dake da babu Ke Zamu Rayu So in Kin Fita wlh zanfi Kowa Jin Dadin Hakan.."Yafada Duka Jijiyon Kansa na Tashi Saboda Bacin Rai.

Farida Dake Kuka Jin Kalaman Tahir sai ta kara Volume din kukanta Cikin Firgici Take kallom Tahir Tana Girgiza kai ko kallonta Baiyi ba yace"Basma Dauki Akwatun Mufeeda ki kaimata Daki.."yafada Lokaci Daya yana Wucewa Ta gaban Farida ba zato kawai Mufeeda Taji ya kama Hannunta zuwa Dakinta yana Fadin"Naga Uban da zai sake yunkurin Koronki Tunda Shima ba Gidan Ubanshi bane Domin Da Gumin Aikin Danikeyi Aka sakamin Dashi Kinga ko baki da Iko Akanshi.."Yafada yana Rike da Mufeeda Zuwa Cikin Dakinta Basma na Biye dasu Abaya da Akwatun Mufeedan Tana Mirmishin Jin Dadi.

Farida Dake Binsu da kallo Wani Bakinciki Da Kishi Suka Kusa Kada Ita Cikin Kuka ta Zura da Gudu Zuwa saman Tana Haura Steps Tana kuka,Har Ta Shige Cikin Dakinta ta banko Kofa,Bassam da Muda da Laila Suka Bita da kallo Iyya kuma Dake Rumgume da Naila Wacce Tayi Barcin Wahala Ranta ya mata Dadi ko Banza yau Alhaji ya Burgeta Sosai,Ta tabbata Farida zata kara Dawowa Cikin Hayyacinta.


*One love*😍💝


*SHAKIRA..*
*AISHA ALTO*
*NANNY...!*
      (Mai Reno..)

*Alƙaluman:*✍🏻

*AISHA ALTO💞*
*JAMILA UMAR (Janafty💕*

_Follow us on wattpad:Janafnancy13 or Aisha Alto Alto_


*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔*
*KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

    *BABI NA GOMA SHA BIYAR*

.....""Har kan Gadonta ya Zaunar da ita,Dagowa Tayi Tana kallonsa Da Jajayen Idanuwanta Tana Zubar da kwallah Cikin Siririyar Muryanta ta Furta"Kayi hakuri Daddy..."Tsam ya Tsaya yana kallonta gefe Daya na Zuciyarsa Tsausayinta na Ratsashi,Basma Dake gefe Tsaye ya kallah kafin yace"Ku kula da Ita sai na Dawo..'

Yafada Haka kafin ya kai ya Fice Daga Dakin da Sassarfa,basma Dake Tsaye ta Kariso Kusa da Ita Tana lallashinta Tahir yana Fita yaci karo da Iya Tsayawa yayi yana Fadin"Iya don Allah ki kula da Mufeeda..."Iya Ta gyada kai Tana Fadin"Insha Allahu Alhaji.."

   Sama ya haye Cikin Dakinsa ya Shiga Daga ganin yadda yake Komai Cikin Hanzari zaka Fahinci yana Cikin bacin Rai,Cikin Sauri ya Dauki Duka Fayels din ya Fito Garzali Dake Waje yana Jiransa ya Shiga Mota Suka koma Campany Wanda Tunda ya Dawo Ishaq ya lura kamar Ranshi abace yake ba Haka ya Fita ba bai mai mgana ba Sai da Suka Dawo Masallaci Sun Shigo Office Din Tahir din

Kan Wata Kujera Dake Cikin Office din Ishaq ya zauna yana Fadin"Kai inaga fa zan Koma gida cikina yana ta Kiran Ciroma.."Tahir Dake zaune kan Kujeran gaban Tuburansa Ya Dago yana Fadin"Allah Sarki kuda Kukayi Dace kenan Mu ko Mun koma muda banza Duk Daya While sai ka Dawo ni kila sai la"asar in zan Koma gida na Biya na Siya Fura ."

Ishaq ya gyara zama yana Fadin"Tahir meya Faru ne..? Dazu Bayan kaje gida Dauko Wadanan Fayels din ka Dawo Ranka bace.."Ajiyar Zuciyar Tahir ya Sauke kafin ya Mike yana Fadin"Nida Farida ce Wato Ishaq Farida Muguwar Yar Rainin Hankali ce Ayadda nakeji yanzu kamar na kamata nayi ta Duka Gabadaya na Doramata kaso mai girma na Abunda ya Faru Domin Data Kiyaye Hakokina na aure da Duka Haka bata Faru ba.."Yafada yana Saka Duka Hannuwansa Ciki  Aljihun Wandonsa.

Ishaq yace"Me kuma ta Sakeyi..? Tahir ya waigo yana Fadin"Zuwa nayi na tarar da Ita

Please Login or Register in order to submit comment