Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Fuskartar juna, Hannu ya sanya yana Share mata Hawaye kafin yajata Jikinsa yana Faɗin "Shiiii..Nace miki ba komai ko? Ki daina Damuwa..." Ya faɗa yana Shafa bayanta Har Zuwa Tudun Hips Ɗinta, ganin Haka ne yasa ta ƙara Narke mai ajiki kafin Ta Ɗago kanta Ta Haɗa Bakinsu Waje Ɗaya Gefe Ɗaya Kuma Hannunta na saman Faffaɗan Ƙirjinsa Tana Shafawa.

Tahir bai da Wata Natsuwa Biye mata kaɗai yayi Saboda Kada Allah ya kamashi da laifin Danne ma Farida Hakki Har Suka Dangana da gadonsu sai gashi yau Abun mamaki Farida bata gaji da Tahir ɗin ba Amma Shi Round ɗaya Sukayi ya Zame Jiki ya Shiga Toilet ya sakarma kanshi Shower, yana Jin kamar ya kurma Ihu, yau shine bayan ya Sadu da Mufeeda kuma ya koma ya Sadu da Farida Abun yamai baƙin ciki Sosai Wanda yasa ya kasa Sakin Jikinsa yayi komai kamar yadda ya saba, Har yayi Wanka ya Fito Farida na Kwance Tana Binshi da kallon Mamaki Aranta tana Faɗin Tabbas Tahir bashi da lafiya don A Tarihin Aurensu bai Taɓa mata Ci Ɗaya Alokaci ɗaya ba sai yau.

********

_BAYAN SATI UKU_

Bayan Sati Uku da Faruwar Haka Abubuwa Suka Fara Sauki, Domin Mufeeda ta Saki Jikinta Sosai ta Koma kamar da, rainon Naila ya Dawo Hanmunta kamar da, kuma Tana Cigaba da Harkarta sai dai Abun na Cikin Ranta Tayi ta Kuka Ita Kaɗai Acikin ɗaki, Sai Abu na Biyu Daya Dameta ganin yadda Daddy yake Ta Rama Atsaye Duk da bata cika ganinshi bane, Shiko Tun bayan Faruwar Haka Mufeeda Ta Zauna Aranshi Komai yake sai ta Faɗo mai tausayi Take bashi yarinya Ƙarama Ta Zama Abun Tausayi, Da ganga yake gujema Haɗuwarsa da Mufeeda Da Zarar Sun Haɗu Abunda ya Faru ke Dawo mai Duk da yanzu Ya fara Maida Natsuwarsa Amma bawai Don Abun yabar Zuciyarsa ba Kwata Kwata...

Tsakaninshi ko da Farida Kadaran kadahan Domin Tagaji Da Tambayarshi meke Damunshi Ta Haƙura ta Zura mai ido Har ƙararshi Takai Wajen Goggo Abu ta Kirashi yaje ta Turkeshi Daga Ƙarshe Kuka ma ya Fashe mata Dashi Abunda ya bata Tsoro kenan Domin Ita ta Haifi Attahiru, tafi kowa saninshi Bai da Rauni, Amma sai gashi yana mata Kuka yana Faɗin Ta tayashi Addu'a ya Aikata Wani Abu Wanda yakejin kunyar Idon Mutane da Allah Wanda ya Halliceshi, kuma tayi tayi Ya Faɗa mata Amma yaƙi sanar da Ita, ko da ya tafi Ɗaki Ta shiga Tana Tunanin meke Faruwa da Tahir ɗin ne Haka Domin Ko Afuska ya Rame Sosai Duk ya Chanza, hakama Hakimi Yayi mamakin Ramar Ɗan nashi Amma sai ya Danganta Hakan da Rashin Lafiyar Dayayi, Kai Ranar Duk Wanda yaga Tahir yasan Cewa ba Lafiya yake ba Hatta Innaro sai da tayi magana, Toh ba Wanda Zaice ga Abunda ke Damunshi Domin bai yarda ya Sanar ma Kowa Abunda ya Aikatama Mufeeda ba.








*Aisha Alto...*
*Shakira...*
*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Alkaluman:*✍️

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty)*💕


_Don't Forget to Follow us On Wattpad: Janafnancy13 or Aisha Alto Alto_

_*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_

    *BABI NA GOMA SHA D'AYA*

Rayuwa Tana ta ganganrawa Da Daɗi ba Daɗi, Har yanzu Tahir bai manta da Abunda ya Faru ba, Amma ya ɗan Saki ba kamar Farkon Abun ba, Amma Tausayin Mufeeda yayi Zaune ɗam Acikin Ranshi Tun bayan Faruwar Abun baya iya Runtse Ido bai tuna ta ba, gashi bai cika yarda Suna Haɗuwa ba Saboda gani yake Tamkar Za'a iya Fahimtar Abunda ya Faru.

Ita ko Mufeeda duk da yarinta na Ɗawainiya da ita Zan iya Cewa Tama Fara Manta Abunda ya Faru Tsakaninta da Tahir Tunda gani Take ta warke Komai ya Riga ya Wuce, babu Wanda zai gane Kuma ba Wanda zai sani bata taba Tunanin nan gaba Wani Abu Zai iya Faruwa ba.

Ɓangarenshi da Farida Kuwa ba laifi yayi ƙoƙarin ɓoye Damuwarshi Saboda Iyayenshi Da Sauran 'yan'uwanshi da Kuma 'ya'yanshi da Hakkin Farida Dake kanshi Amma zancen gaskiya Tun bayan Abunda ya Shiga Tsakaninsa da Mufeeda bai ƙara yin Sex cikin Daɗin Rai ba, sam sam Sha'awar Hakan ya Fita a kanshi ita kanta Farida Tana mamakin Wasu Sauye Sauye Daga Hallayar Tahir kamar An Ɗauke Tahir ɗin baya An kawo musu New One ne.

Ko awajen Aiki Koda yaushe Cikin Danne Damuwarshi yake kada Wasu Su Fahimta, bayan Ishaq baisan Ko kowa kallonshi yake ba Domin Duk Wanda yasan Tahir Abaya in ya ganshi yanzu sai ya Tambayi kanshi Cewa Yaushe Tahir ɗin ya koma Haka...? Ishaq ko Daga baya Daya Gaji Da Tambayar Tahir meke Damunsa yaƙi Sanar Dashi, Sai kawai ya kawo Ido ya Saka mai Gefe Ɗaya yana Tayashi Addu'ar Allah ya warware mai duk Abunda ke Damunshi.

Duk da ƙoƙarinsa na Danne Damuwarsa in ya keɓe kanshi na Wasu Mintina sai Abun ya Faɗo mai nan da nan zai Rasa Natsuwarsa Har idanuwansa Su kama Zubar da Kwallah Wanda ya rasa Dalili Haka Kurum ya keji Acikin Ranshi Komai bai ƙare ba Akwai Wani Babban Lamari da Zai Faru nan gaba.

***********

Yau tun 8 yake Cikin Office ya kasa Aiwatar da Komai ya faɗa Kogin Tunani Hannunsa Dafe da Duka Kuncinsa Zuciyarsa na Harbawa Lokaci Ɗaya, Koda da Rana Ɗaya Abun bai Taɓa Shafe mai Acikin Kwakwalwa ba gani yake Tamkar Akwai Wani Babban Al'amarin da Zai bayyana Komai yana Ji Ajikinsa Asirin sa bai Rufu ba, kuma Koda ya Rufu ina Zai kai Hakkin Marainiyar Allah?

Wannan Tunanin Shike Sanyashi Shiga Wani Hali har ya fara Zubar da Kwallah bai sani ba, Tsawon Lokaci ya Ɗauka yana Shessheƙan kuka Abunda bai sani ba Tunda ya fara Wannan Koken nashi Ishaq ya Shigo Office d'in Bai sani ba Wanda ya Shiga Tashin Hankali ganin Tahir na Kuka Lokaci Ɗaya yana Faɗin Allah na tuba ka yafemin, Abun ya bashi Tsoro matuƙa Shiyasa yayi Tsaye ƙiƙam ya kasa magana yana Ɗauke da Wasu Fayel ne Wanda ya kawoma Tahir ɗin ya Duba sai ya Tarar Dashi Cikin Wannan Halin.

Da ƙyar ya iya ƙarasawa Ga Kujeran da Tahir ke kai ya saka Hannu ya Dafa Kafaɗarshi yana Faɗin "Subhanallahi Tahir mezan Gani Haka...? Kuka fa kake yi Don Allah ka Daure ka sanar dani Abunda Ke Damunka Don Allah...?" Ya faɗa Cikin Alamun Damuwa lokaci Ɗaya yana binsa da kallo, Firfigit Tahir yayi ya ɗago yana kallon Ishaq dake Tsaye kanshi, Saurin Saka Hannu yayi yana Share Kwallarsa kafin ya ƙaƙaro murmushin Dole yana Faɗin "Haba Friend Sau nawa Zan Sanar dakai babu Abunda Ke Damuna meyasa kaƙi yarda dani ne...?"

Wani kallo Ishaq yabishi Dashi kafin yace "Eh Naga alama, na yarda kana da damuwa amma bankai matsayin Dazaka sanar Dani ba..." Ya faɗa kai Tsaye yana Kafeshi da ido, Cikin Fitan Hayyaci Tahir yace "Toh mene ne Damuwar nafada maka bakomai Allah..."

Tsaki Ishaq yaja yana Faɗin "Toh in ba kana Cikin Damuwa ba Uban Me zai Zaunar Dakai kana Kuka kana Faɗin Allah ka Tuba ya yafe maka? Haba Tahir ban zaci Akwai Abunda Zaka iya ɓoye min ba. Amma ba komai Insha Allahu bazan Ƙara Ƙoƙarin naji Abunda Ke Damunka ba Zan Ta Maka Addu'an Koma Menene Allah ya yayemaka Shi.."

Ya fada kafin ya ajiye mishi Fayels Ɗin Agabanshi ya juya zai Fita Daga Office d'in kamar Daga Sama Yaji Muryan Tahir Yana Faɗin "Ba Abun Kirki bane Ishaq zaka Sha mamaki in nace maka Fyaɗe Na Aikatama yarinyar Datake Daukana Tamkar Mahaifinta...." Tahir ya Faɗa Idanuwansa suna Zubar da Kwallah, Cak Ishaq ya Tsaya kafin ya Waigo yana Faɗin "Fyaɗe...? Wani Irin magana ne Haka, Shikenan Kuma Don ba kasan Faɗa min Damuwarka sai kayi ma kanka Irin Wannan Mugun Bakin..? Ya faɗa yana kallonsa Cike da damuwa.

Cikin ƙarfin Hali Tahir ya miƙe ya isa ga Windown office d'in Yana Share Hawayensa Cikin Raunin Murya ya furta..."Dama Nasan bazaka yarda ba Ishaq Ina Jin Kunyar kaina Da Kaina In na Tuna Abunda na Aikata, Ba karya bane Duk Damuwar Daka ga Ina Shiga Saboda Hakane Mufeeda fa nayi ma Fyaɗe Ishaq..." Ya faɗa yana Dafe Kanshi, Zaro Ido Ishaq yayi kafin yace "Mufeeda Nanny dai Ta Gidanka mai Renon Naila Wacce Kuka Ɗaukota Daga Ƙauye..." Ya faɗa Cikin Fitan Hayyaci.

Gyaɗa kai Tahir yayi yana Hawayen Takaichi Da Nadama yana Faɗin "Ita fa Ishaq, ita nayima Fyaɗe Cikin Rashin Hayyaci Amma Duk da Haka na Ɗauki Hakan A Matsayin ƙaddarata..." Nan ya Shiga labarta mai Duk Abunda ya Faru Daga Farko Har ƙarshe, ya ƙara da Faɗin "Ya zanyi Ishaq..? Abun yaƙi barin Raina ina ganin kamar na Cuci 'yar mutane, ina ganin kamar Asirina bai Rufu ba, Kamar Akwai Wani Babban Al'amari da Zai Faru nan gaba, Da Wani ido zan kalli mahaifiyar yarinyar nan...? Da wani ido zan kalli iyayena da 'yan'uwana da kuma 'ya'yana...? Ishaq ka Faɗa min Da Wani Ido Zan Kalli Mutanen Dasuke gani na Da Mutumci da Kima...?" Ya faɗa Ya kasa Control Ɗin kanshi kawai sai ya Rufe Fuskarshi da Tafin Hannunshi ya Saki Wani Marayan Kuka.

Jikin Ishaq ya gama yin Sanyi da labarin da Tahir ya bashi Jikinsa A matuƙar Sanyaye ya ƙarasa ga Tahir ya Dafa Kafaɗarshi yana Faɗin "Ba laifinka bane Tahir...Duk Abunda ya Faru Rubutacce ne Daga Rabbil Izzati, amma babu Shakka Farida da Goggo Abu sune Silan Fadawarka Wannan Halin Ko Nace Wannan Kaddarar..." Da Sauri Tahir ya Ɗago Idanuwansa Jajir yana Faɗin "Sune Sila Wallahi Ishaq Sune Sila da'ace Farida Tana Kula da Duka Hakkina Da Haka bata Faru ba, da kuma Ace Goggo Abu ta karɓi Uzurina ta barni na ƙara Aure Da Haka bai Faru Dani Ba Ishaq, kaicona na Cuci Rayuwata Na Kuma Cuci Rayuwar baiwar Allah..." Ya faɗa Lokaci Ɗaya yana Faɗawa Jikin Ishaq Shi kuma ya Rungumesa yana Bubbuga Bayansa Alamun Lallashi Tausayin Tahir ya Cika mai Ciki Sosai.

Sun Daɗe A haka kafin Ishaq ya Ɗago Tahir ya kuma sanya Hannu yana Share mai Hawaye Lokaci Ɗaya yana Faɗin "Ba girmanka bane ka Dinga Kuka Haka Friend na Tabbata koda labarin nan ya Fita kowa zai bada Sheda Akanka kai Mutumin Kirki ne Kawai ƙaddara ne ta Faɗa maka Wanda baka isa ka Tsallaketa ba..." Ƙura mishi Ido Tahir yayi kafin yace "Hakane Ishaq Amma kai kaɗai ne zaka Fahimci Hakan Sauran Mutane bazasu gane Haka ba..."

Hannunshi Ishaq ya Riƙo Suka Zauna Bisa Doguwar Kujeran Dake Cikin Office d'in, Ƙaramin Fridge d'in dake Office d'in ya Buɗe ya Ɗauko mai Roban Ruwa da Kofi ya Tsiyaya mai Ruwa ya bashi, karɓa yayi yasha Kafin ya miƙa mai, shima Tsiyayawa yayi yasha kafin ya maida Kofin Da Goran Ruwan Saman Fridge d'in, Ya koma ya Zauna kusa da Tahir ɗin yana Faɗin "Suma zasu gane Friend, Karka damu Nidai Roƙona ka Cire Komai Acikin Ranka Tunda Itama yarinyar Ta manta komai, Kuma Tana da Hankali Tunda Har yanzu Bata Sanar Da kowa ba.." Ajiyar Zuciya Tahir ya saki kafin yace "Hakane Tausayin Yarinyar ne yaƙi barina Ishaq, ina Tausayinta yadda na Cuci Rayuwarta Marainiya ce fa bata da Kowa sai ni sai Allah.." Ya faɗa cikin Damuwa...

  Kafaɗarsa ya Bubbuga yana Faɗin "Cool Down karka Damu Insha Allahu Komai zai Wuce Kuma Allah naganin Zuciyarka, Ai tana Karkashinka ne Kuma Kana Ƙoƙarin Kyautata mata, na Tabbata nan gaba Zata inganta Rayuwarta.." Jinjina kai Tahir yayi kafin yace "Insha Allahu" Nan Ishaq ya zauna yana Ta bama Tahir baki Sai da ya Tabbatar da Tahir ya saki Jiki kafin Su gangara maganar Aikin, Tahir ya natsu ya Na Duba Fayels din da Ishaq ya kawo mai, nan Ya barshi Shi kuma ya Tafi Office ɗinshi Cikin Damuwar Halin da Tahir ke Ciki.

******

*After 2 Month...*

Gidan na Tahir A cike yake da 'yan Hutu Domin Satin Daya Gabata 'Ya'yan na Ashe Suka Diro Sun Zo Hutu, Laila da Muda Sakamakon Dogon Hutun da yan Makaranta Suka Samu na Third Tearm Duka yaran na gida Hatta Dasu Bassam Waɗanda Sukaji Daɗin Zuwansu Laila d'in.

  Misalin Ƙarfe 4:50pm na Ranar Asabar Iya ta Shiga Ɗakin Mufeeda Da Niyyar Ɗeboma Naila madararta A cikin Wani ƙaramin Kofin Da'ake Dama mata Har ta Ɗiba Madaran Tana Shirin Fitowa Daga Ɗakin Idonta ya Hango mata Mufeeda Kwance Gefen Gadonta tana Sharar barcinta Jikinta Dogon Hijabin Islamiyansu ne, Daga ƙasa Kuma Ƙaramar Jakar Makarantan nata ne yashe A ƙasa Daga Ganin yadda Ta Kwanta Zaka Fahimci Barcin ya Kwasheta ne ba tare Data Shirya ba.

Baki Iya ta Riƙe Cike da mamakin Mufeeda A yan Kwanakin nan, Bata da Aiki sai barci Wuni Take barci bata gajiya Alhalin Kuma Ada ba Haka Take ba,Da Hanzari Ta Isa gareta ta Hau Tabata Tana Kiran Sunanta.. "Ke Mufeeda..Mufeeda..." Buɗe Ido Tayi Cike da barci da kasala Tana kallon Iya, wacce ke Tsaye Tana kallonta Cikin Mamakinta tace "Tashi Meye Haka Islamiyan Kenan, Su Basma sun Tsufa A Makaranta Ashe Ke Kina nan Kina Shegen barcinki na Fama..." Ta faɗa Tana Binta da kallo.

Miƙa Mufeeda Tayi Tana Banƙaro Ƙirjinta kafin Ta Miƙe Zaune Tana Kwaɓe Hijabin Jikinta, Baƙar Doguwar Rigar Dake Jikinta na kamfanin Armani ta bayyana, Wacce Ta Fito da Ainihin Cikar da Mufeedan Tayi Tunda ga Kugunta Har Zuwa Nonuwanta, Cike da Kasala ta Ɗaga Ido Tana kallon Iya Kafin Tace "Wallahi Iya bansan Barci ya Kwasheni ba na Idar da sallar kenan Basma ta Shigo Ita da Laila Tace na Fito Mu Tafi, nidai na san na Ɗauko Jaka na saka Hijabin Daganan Kuma Ban ƙara Sanin Inda kai na yake ba.." Ta faɗa Tana Hamma.

Tsam da Ido Iya Tayi Tana Ƙarema Mufeeda Kallo Tun daga kan Fuskarta yadda Ta Cika Tayi Wani Fari da kyau ga Jikinta Duk ya Chanza Ta kara Cika Kamar ba Mufeeda mara Jiki ba, Gabanta na Faɗuwa Tace "Mufeeda meke Damunki ne, Na lura Dake a yan Kwanakin nan, Baki cin Abinci sai Kayan Kwalama Kullum Sai kin Soya Wainar Fulawa, kin kuma yi Ɗanwake ga yawan Barci Da kasala kamar kasa, Anya Mufeeda Zuciyata fa Tana Rayamin Wani Abu...?"

Ta faɗa Tana Kurenta da Ido Mufeeda bata bama Tambayar Iya Muhimmanci ba Ta Miƙe Tana Miƙa Tace "Bansani ba Iya Haka Kurum na Tsinci kaina, In ina Sha'awar Abu in banci ba kamar Zan Mutu kuma yawan Barci Kila Don Hutun Da Muka samu ne, Nima Wani Lokacin ina mamakin kaina, na rasa Meke Damuna..." Ta faɗa tana Yamutsa Fuska.

Cike da Faɗuwar gaba Iya ke Bin Ƙugun Mufeeda da kallo yadda ya Cika Sosai Ta Juya Zata Shiga Toilet, Baki Ta kama kafin Ta Fice gabanta na Faɗuwa Zuciyarta na Tsinkewa Ita ba yarinya ba ce, Ta san Alamomin Ciki Sosai da Munafiki da Fallasasshe, Bata son Abunda Take Zargi Kan Mufeeda Ya Tabbata, Bayan Ta gama bama Naila Madaran Ta Goyata tayi Barci sai ta Nufo Babban Falon Gidan Inda Farida ke Zaune Tana Waya da Umma.

Gefenta Iya ta Zauna saman Cafet, Har sai da Ta kammalah Wayar, Ɗagowa Tayi Tana kallon Iya kafin Tace "Hajiya Iya Naila ce Tasha goyo Haka..?" Yake Iya Tayi Kafin Tace "Eh Hajiya..." Daga Haka Ta Sunkuyar Dakai, Ganin Haka yasa Farida tace "Lafiya Iya da Wani Abu ne..?" Kai Ta Ɗago Tana Faɗin "Eh Hajiya nazo Miki da Wata Magana ne Allah yasa Zaki Fahimceni..."

Zama Farida ta gyara kafin ta ajiye Wayarta Tana Faɗin "Karki Damu Iya Ina Jinki" Cikin Muryan Dattako Iya Tace "A gaskiya Hajiya ya kamata Ki saka Likita ya Binciki Mufeeda, domin ina Wani Zargi Akanta Duba da Wasu Alamomi Dana ga Sun bayyana Muraratan Tare Da Ita.." Cike da mamaki Farida Tace "Likita ya Binciki Mufeeda Kuma Iya bata da lafiya ne Ko meye Dalili..?

Iya ta Ɗan Yi Shuru kafin Tace "Maganar Gaskiya Hajiya Ina Zargin Ciki Mufeeda Ke dashi, Amma Ita kanta bata Fahimci Haka ba, ko kuma Tsabar Bariki ne bansani ba..." Zabura Farida Tayi Ta Miƙe Hannunta Dafe A ƙirjinta Tana Faɗin "Ciki Kuma Iya...? Wata magana Kike faɗi Haka? Wazai ma Mufeeda Ciki yarinyar Da bata Fita Daga Makaranta sai gida..?" Iya ta gyaɗa kai kafin Tace "Ƙwarai Kuwa Hajiya Nima Abunda ya Dauremin kai kenan" Nan Ta Shiga gayama Farida Duk Abunda Tagani game da Mufeedan da Alamun Ciki Ta ƙara da Sanar da Ita Halin Data Tarar da Ita yanzu Haka..."

Cikin Farida ya bada Wani Sautin Tashin Hankali, jikinta na Rawa Tace "Na Shiga goma ni Farida Ya Zanyi Iya.? In ya Tabbata yarinyar nan Ciki Tayi Wani Amsa zan bama su Goggo Abu da Mahaifiyar yarinyar nan...? Mezan Cema Abban Basma Iya...?" Ta faɗa Cikin Tashin Hankali, Miƙewa Iya Tayi Tana Faɗin "Hajiya kafin Mu Fara yanke mata Hukunci Ya kamata Likita ya Duba Ta Tukunnah..." jinjina kai Farida Tayi Kafin Tace "Shiga ki Sanar da Ita ta sako Hijabi ko Keke Napep mu Tara ya kaimu Asibiti Tunda Inaga Daga Makarantarsu Basma Garzali ya Wuce Company ne, Hanzarta Iya.." Ta fada tana Ɗaukan Wayarta Ta Nufi Upstairs Da Hanzari Nombar Tahir Take Nema Amma kuma bata Sameshi ba, Ɗakinta ta Shiga Ta Ɗauko Mayafi Tunda Motarta ta samu Matsala tana Wajen gyara, Koda ta Sauko Ƙasa Har Mufeeda Ta Fito Idanuwanta Sun Shige Ciki Saboda barci, don Kwance Iya ta Tarar da ita.

Farida sai Lokacin Take ƙarema Mufeedan kallo gabanta na Faɗuwa Na Irin Kyau da Cikar da Mufeedan Tayi basu Tsaya ba Farida Da Iya Wacce ke goye da Naila Suka Tasa ta Gaba Suka Fice Daga Falon, a haraban Gidan Farida ce ta barma Megadi sallahu Koda Tahir ya Dawo ko yara ya sanar dasu Sun Shiga Asibiti yanzu Zasu Dawo Da Toh ya amsa musu yana Musu Fatan Dawowa Lafiya.

Keke Napep Suka Tara Sai iyali Hospital, Ƙuruciya da Yarinta ke Damun Mufeeda Shiyasa Taji Daɗi Tunda Iya tace Za'a Dubata ne Don Itama Ta Gaji da yawan Barcin Datake Fama Dashi Da Kasala, Suna Zuwa Farida da Mufeeda Suka Shiga Ciki Ganin Dr, saboda Daman Nan Suke da Fayel, ganin Farko yayi mata sai ya Fara Jeho mata Tambayan Yaushe Rabon Data ga Al'adanta tace "Wata Uku kenan." Gaban Farida sai ya ƙara Tsinkewa nan Likitan keta Tambayanta Tana bashi Amsa, nan da nan ya kira Waya sai ga Wata Nurse Tazo Yace Suje da Mufeeda Ta Ɗibi Jininta ta kai lab Agwadashi yanzu yana Jiranta Fita Sukayi Ta tafi da Mufeeda lab D'in Ta Ɗibi Jininta, Office d'in Mufeeda ta Dawo Ta Zauna Farida ko na Zaune Tana Fama da Faɗuwar gaba Tsawon Minti 30 sai ga Sakamako ya Fito An kawoma Likita yana karɓan Takardan Ya Buɗe ya karanta kafin ya kalli Farida yana Faɗin "Wai kun ma yaranku Aure ne ba labari..? Da yake Likitan Asibitin ne ya sansu Fiye da Shekaru Huɗu So Duk yasan Mufeedan Dasu Basma.

Farida Taji miyau mai Kauri ya Tsaya mata da ƙyar tace "A'a Dr meka gani.? Ta faɗa tana Kafeshi Da Ido. Cikin mamaki yace "Ah...Garin ya haka..? Gashi Result Ɗinta ya Nuna Tana Ɗauke da Ciki Har na Tsawon Wata Uku..." Ƙirji Farida ta Dafe Hannunta Akai Suka maimaita kalmar "Ciki.....?" Ita da Mufeeda Wacce Ta Zabura Ta Miƙe bayan Taji Kalmar Kamar Saukar Aradu Akunnenta.






*Janafty...*
*Aisha Alto..*
*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Alkaluman:*✍️

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty)*💕


_Don't Forget to Follow us On Wattpad: Janafnancy13 or Aisha Alto Alto_

_*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_

    *BABI NA GOMA SHA BIYU*

   Da mamaki Likitan ke binsu da kallo, Tun ma Ba Mufeeda ba Wacce Taji Zuciyarta da Jikinta Sun Tsinke Gaba ɗaya, Hannunta Bisa kai Hawaye na Zubo mata Take Faɗin "Na Shiga uku Likita Ni keda Ciki...? Wani Haushi ya kama Farida mai Haɗe da tsantsar baƙin ciki, Cikin Zafin Nama Ta Saka Hannu Ta Kwaɓe mata baki Sai da Jini ya Fito Cikin Taruwan Hawaye tace "Eh Ciki don Ubanki Ai ba ƙarya yayi miki ba, Dama munga Alamu, Son Tabbatarwa ne, kuma yanzu Mun Tabbatar, kin Cucemu Mufeeda Kuma kema kin Cuci kanki..." Ta faɗa Hawayenta Suna Zubowa Lokaci Ɗaya Ta Miƙe Kafin Ta Sanya Hannu Tana Ɗauke Hawayenta Take Faɗin "Mun Gode Dr..." Daga Haka ta Finciki Hannun Mufeeda Dake Kuka Suka Fice Daga Office D'in Kamar Walkiya, Da Ido Likitan ya bisu Abun ya matuƙar Ɗaure mai kai yaran da basu Fita Taya Wannan Abun Zai Kasance.

Suna Fitowa Iya Ta Miƙe ko bata Tambaya ba ganin Yadda Idanuwan Farida Suka kaɗa Sukayi Jajir, ga Mufeeda na Kuka Wurjanjan Ta samu Amsarta Shiyasa bata Tsaya Tambaya ba Sai ma bin bayan Farida Datayi Wacce Ta Saki Hannun Mufeeda Tayi gaba Zuciyarta na Ta fasa da Fargaban Wani bayani Zatama goggo Abu..? Mezatace da Mahaifiyar Mufeeda..? Uwa uba Kuma Tahir Wanda Amanar Mufeeda Ya Damƙashi Ahannunta ya kuma ce Ta Kula da Ita Tamkar yadda Zata Kula dasu Basma..? Abunda yafi Ɗaure mata kai da bata mamaki Wayayi ma Mufeeda Ciki..? Yarinyar da babu Inda Take Zuwa Daga Makaranta sai makaranta kuma Makarantan ma Akaisu Adawo Dasu..? Kai Wannan Al'amari Akwai Ɗaure kai.


Ko Acikin Adaidaita Mufeeda Keta Gunjin Kuka Farida da Iya Kuwa Suka mata banza Kowa na Saka Abubuwan Mamaki Acikin Zuciyarsa Ita Farida Baƙin Ciki ne da Kuma Kunyar Wani bayani Zatama Su Goggo Abu Akan Wannan Baƙin Labarin, ita kuma Mufeeda Kuka take Wanda Ta rasa Dalilinshi Sai Da Akace Tana da Ciki Ta Tuna Malamin Islamiyansu ya sanar Dasu Duk macen Data Fara Jinin Al'ada Akayi Abunda Tahir Daddy yayi Da Ita To Zata iya Samun Ciki, ƙananun Shekarunta bai bata Damar Fahimtar Cewa Akwai Rana mai kama Data yau ba, Kuka Take na Baƙin ciki Bakinta bazai iya Taɓa Furta Wanda ya Aikata haka gareta ba Domin Tayi Alkawarin Ko Za'a Kasheta sai ta Rufama Daddy Asiri Domin Shima ya Rufa mata Asiri Lokacin Da bata da Kowa.

Ita ko iya Cikin Ranta Salati kawai Take, Tana Kuma Hasashe da Tunanin Waye yayi ma Mufeeda Ciki, ita bata ma kai da Nisa ba Tunani Take ko Garzali ne..? Ko maigadi ne..? Domin Iya saninta Gidan Tahir gida ne na Tsaro da Tsantsar Tarbiya, Amma Kuma Taya Hakan Ta kasance..? A iya saninta bata san Mufeeda da Wani Halin banza ba, bata da Saurayi ko Wata Ƙawar Banza Wanda Zai Nuna Alamun Hakan Zai iya Faruwa..? Kai Wannan Abu da Ban Mamaki yake.

Suna gab da Isowa gida Wayar Farida ta fara ƙara Tana Dubawa Taga Tahir ne sai taƙi Ɗaga Kiran Don bata da Abunda Zata iya Sanar Dashi Adaidai Wannan Lokacin Zuciyarta bata da Ƙwarin Gwiwa, suna Dawowa gidan Suka Iske Su Basma Sun Dawo Daga Islamiya Nan Suke Shaidama Farida Daddy ya Dawo Megadi ke sanar Dasu Sun Tafi Asibiti Shine yayi Ta Kiranta bata Ɗaga ba Sun Tafi masallaci Shida Muda da Bassam, Farida batayi magana ba Illah Hayewa Sama Datayi, Ranta Duk ba Daɗi Itama Iya Ɗakinta ta Shiga Tana Sauke Naila Data Farka Mufeeda ko Tana Kuka ta Nufi Ɗakinta Laila da Basma Suka bita Suna Tambayanta Ko lafiya Da ƙyar Ta Iya Cemusu batajin Daɗi ne, Basma tace "Oh dama ke Momy Taje kaiwa Asibiti? Sannu Allah ya baki lafiya" Nan Laila Itama ta mata Sannu Daga nan Suka Fice Daga Ɗakin Suna masu Tausaya mata ganin Kukan Datake Su Azatonsu Ko Ciwon nata yayi Zafi Shiyasa Take Kuka.

Farida ko Da ƙyar ta iya Shiga Toilet ɗinta ta Ɗauro Alwala tazo ta kabarta sallar Magriba ta Idar Kenan Tana Zaune Ta Ƙurama Saitin Makeken Gadonta Ido zuciyarta ba Daɗi Kamar mai Nazarin Wani Abu Amma Azahirin Gaskiya Tunanin Mafita Takeyi, Bata ji Shigowar Tahir ba sai da Taji Tattausan Hannunshi Akan Fuskarta yana Shafa Kumatunta Firgigit ta Dawo Cikin hayyacinta, Ta Ɗago Tana kallonshi Shima kallonta yake Cikin Mamaki yace "Lafiya..? Meyake Faruwa Ki kai nisan Tunani Haka.? Waye ba lafiya mun Dawo Kuna Asibiti..?"

Miyau Farida Ta Haɗiye mai Ɗaci Kafin Ta Tattaro Murmushin Yaƙe Tace "Amh..Umh...ba komai..." Ta faɗa Muryanta na Rawa Kamar zata Fashe da Kuka Tana Tunanin In Tahir yaji labari Ita Zai Ɗorama laifi yace Duk da Laifinta bata Son Zaman Gida Balle ta Fahimci Wani Hali yaran Ke Ciki.

Wani kallo ya mata kafin yace "Ban gane ba komai ba Farida? kinga idonki kuwa..? Kuka kikayi ko menene..? Kuma baki bani Amsa ba Waye ba lafiya Kuka Tafi ganin Likita..?" Ajiyar Zuciya Ta Sauke Kafin Ta Yunƙura Ta Miƙe Tana Zame Hannunta dake Cikin na Tahir Hijabin Jikinta ta Cire Tana Ƙoƙarin

Please Login or Register in order to submit comment