Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganin yana Kuka Duk da Halin Dayake Ciki Sai da tace "Ka..ka...Da.daina Kuka Daddy...bazan Faɗama Kowa ba.." Ta faɗa Itama tana Sakin Nata marayan Kukan.

Jin Abunda Tace ne yasa ya Ɗago da Sauri ya Riƙo Hannunta yana Faɗin "Da gaske kike Mufeeda bazaki Fadama kowa ba...?" Ganin yadda Yake Rawan Jiki ga Hawaye na bin Fuskarshi yasa Ta ɗaga mai kai kafin tace "Ka..kaini Wajen Innata..Wajenta zani.." Iska ya Furzar kafin yace "Zan kaiki ki kwantar da Hankalinki kibar Wannan Kukan kada gobe su Basma su Fahimci Wani Abu ya Faru, yanzu bari na Shiga nayi Wanka na Fito Hau gado ki Kwanta naji Jikin ki Temperature yayi yawa Kinji ki jirani na Fito.." Ganin yadda ya Ruɗe ne yasa Ta Ɗaga mai kai da Hanzari ya saki Hannunta ya rarumin Zanin gadon daya baci da Jini ya Faɗa Toilet yana jin Tsanar kanshi, da kallo Ta bishi Sai da ta Tabbatar ya Shiga kana ta fara Rarrafe ta jawo Rigarta ta sanya, tana Neman Hanyar Fita Lokaci Ɗaya tana Zubar Ƙwallah Saboda Azaban Dake cinta ta Tsakiyarta kamar Wacce Aka Tusa mata Wani Katon Abu ya Tokareta... 

Da Rarrafe ta Fito Daga bedroom Ɗin ta Kuma gangaro Steps d'in Benen Tanayi tana Kuka Har Ɗakinta, Allah ya Taimaketa Basma ko Bassam ba Wanda ya Fito, Da Rarrafen ta Ƙarisa Cikin banɗakin Dake Ɗakinta ta Haɗa Ruwa Mai Zafi Ta Shiga Ciki Tana Cigaba da Kuka mai Cin Rai Tana Sane Cewa Wannan Abun Tahir yayi Toh sai fa sai tayi Wankan Tsarki Domin A makarantar islamiya an Sanar Dasu Duk Ranar da Namiji ya kwanta Dake sai kinyi Wankan Janaba kuma ko ba Haka ba Lantana Ta Sanar da ita Ranar Daren Farkonta Haka Mijinta yayi mata, Amma ita yau gashi ba Miji ba Saurayi ba Daddy Shi ya Keta mata Budurcinta yau ya maida Ita mace..

Tana Kuka da Komai tayi Wankar Tsarki ta Fito Tana Dafe bango, Lokacin Zazzaɓi ya Rufeta tana Rawan Sanyi, Da Hanzari ta Faɗa kan gado taja bargo Ta Rufe Jikinta tana Rawan Sanyi, Shiko Tahir Wanke Zanin Gadon yayi ya Shanyashi Acikin Bedroom d'in kafin yayi Wankan Tsarki ya Fito sai dai yana Fitowa yaga Wayam ba Mufeeda Hankalinsa Tashe ya Zura Wata baƙar Jallabiya ya Nufo Ɗakinta Ajiyar Zuciya ya Sauke sanda ya ganta Lulluɓe Cikin bargo baya yaja Cike da Damuwa kafin ya koma sama Yana mai Nadama.

Darduma ya Shimfida ya kabarta sallah dama already ya Ɗauro Alwala, Sallah yayi Raka'a goma Sha uku Haɗe da Shafa'i da Wutiri, Kafin ya Ɗaga Hannuwanshi Sama yana Roƙon Gafaran Allah, Yana yi yana Kuka kamar ƙaramin yaro baƙin ciki da Nadama Sunga ma Lulluɓe Tahir, Bayan ya idar karatun Qur'ani ya dasa gabatowar Asuba, kana ya Tashi Daga kan Sallayar ya Sauko Ƙasa Idanuwansa Sun Masa Nauyi, Ɗakin Mufeeda ya Leƙa yarda ya Isketa sai gabansa ya Faɗi Tana Kwance Cikin Bargo Tana Rawan Sanyi Cikin Hanzari ya ƙarisa gareta bayan ya yaye Bargon ya Taɓa Goshinta yaji Zafi Sosai Ruɗewa yayi Cikin Fitan Hayyaci ya koma Ɗaki ya Ɓallo mata Paracetamol da Kuma Pain Killer yazo ya tada Ita tana Rawan Sanyi gefe Ɗaya Kuma Tana Tsiyayan Hawaye, ya bata Tasha Ta Koma ta Kwanta.

Ranar dai Barci baiga idon Tahir ba Shi ya Tashi Bassam Suka Tafi masallaci Koda Suka Dawo Sai da ya leka Dakin Mufeeda ganin Ta samu barci ne yasa Hankalinsa yadan Kwanta sakamakon baya Cikin Natsuwarsa yasa breakfast ɗinsu ma Garzali ya aika yayi musu Takeaway Koda Basma Ta Fito Cikin Shirin kayan makaranta ita da Bassam, Tahir bai bari Sun Tambayi Mufeeda ba yace musu yau bazataje Sch ba batajin Daɗi, Ransu baiyi Daɗi ba Suka Juya Zasu Shiga Ɗakinta Tahir ya hanasu Cikin Wani yanayi nan yace su bari Su Dawo ya bata Magani ta samu barci Inda Ace Zasu lura da Sunga yadda yake Rawan Jiki kamar baya Cikin Hayyacinsa.

Basu kawo komai Aransu ba Suka Fita Zuwa Haraban gidan bayan Sun karya da takeAway d'in Da Garzali yayi musu, ƙarfe 7:30am Garzali ya kwashesu Zuwa Makaranta Shikanshi Da baiga Mufeeda ba sai da ya Tambayesu Suka ce mai batajin Daɗi Fatan Samun Lafiya yayi mata kafin ya kaisu Makaranta ya Ijiyesu ya Kamo Hanyar Gida yana Tunanin Zai kai Tahir Office.

Shi ko baida Cikakkiyar Natsuwa Hankalinsa A tashe yake na Abunda ya Faru kada Kuma Wani ya ɗau sanau, Ganin Jikin Mufeeda Har da Safen Arikice yasa bai Fita Office ba koda Ishaq yajisa Shuru ya kirasa Awaya nan yake Shaida mishi bazai Samu Fitowa ba baya jin Daɗi, Sannu yamai kafin Suyi Sallama, Tahir Wuni yayi Tashin Hankali Domin Zazzaɓi yaƙi barin Mufeeda ko Abincin da Garzali yasiyo ta kasa Ci Komai ya bata sai ta kauda kai Tana Kuka Tana Kiran Sunan Innarta ya rasa yadda Zaiyi Tsoronshi Ɗaya kada Farida Ta Dawo ta Fahimci Abunda ya Faru Domin Ko makaho Ya Shafa yasan Cewa Mufeeda ta Illata ganin ko iya Tafiya ma batayi Tana Kuka Tahir nayin na Zucci Suna Cikin Wannan Halin ne yaji sallamar su Basma sun Dawo Daga Makaranta Koda yayi Wuf ya Fito Daga Ɗakin Mufeedan Sai Suka ci karo da Su, Ganinshi Hankalinshi Tashe sai su ka Tura kai Ɗakin Azatonsu Jikin Mufeedan ne ya Tashi Shiko kasa Komawa Cikin Dakin yayi ya Tsaya anan Yana Kiran Sunan Allah yana Fatan Kada Su basma Su Fahimci Wani Abu.

Toh dai basu Fahimci komai ba, Illah Sun Tausayama Mufeedan Ganin yadda Take kuka Tana Kiran Sunan Innarta, Basma kamar ta mata Ƙwallah Ta Fito Daga Ɗakin Tana Faɗin "Daddy Akai Aunty Mufeeda Asibiti Jikinta kamar Wuta.." Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin yace "Za'a kaita Basma ku Shiga ɗaki ku cire Uniform ɗinku ga Takeaway chan Garzali yayo muku kunji.." Gyaɗa kai suka yi kafin Kowanne ya Nufi Ɗakinsa zuciyarsu ba Daɗi Domin Sun Shaƙu da Mufeedan Sosai.

  Suna gama cin Abinci Sukayi sallah Da Farko Basma taso Ta Zauna da Mufeeda amma Tahir yace maza Ta Shirya ta tafi makaranta Dole Hakanan ta Shirya Ita da Bassam Garzali ya Kwashesu Zuwa Islamiya, Har Suka Taso Daga makaranta Tahir baisamu mafita ba, Sun Shigo Kenan sai ga Iya Ta Dawo Wanda ya Faɗarma da Tahir gaba, Basma da Bassam Suka Rungumeta suna Murna Itama Cikin Farin cikin Ganinsu Take Amsa gaisuwansu kafin Su Dakata ta Rankwafa Tana gaida Tahir ya amsa Cikin Wani yanayi na karaya, yana Ƙara yi mata gaisuwa.

Mufeeda Ta fara Tambaya kafin Farida nan Basma tace Tana Ɗaki Tun Jiya bata da lafiya, Ai kafin Tahir yasamu Mafita Iya da Basma Sun Nufi Ɗakin Mufeeda Zuciyarsa ce ta karye ya Nemi Kujera ya Zauna yana Dafe kai Bassam ne ya katseshi da Faɗin ya Tashi Su Tafi masallaci Shidai Har Aka idar da sallar mangariba baya Cikin Natsuwarsa Saboda Zullumi bai jira Sun Sallaci Issha'i ba kamar yadda Suka saba Ya Riƙo Hannun Bassam Suka Dawo Gida Zuciyarsa na Bugawa Saboda Fargaban kada iya tagano Abunda ya Faru Ta Matsama Mufeeda Har Sai ta gaya mata Abunda ya Faru, Bassam ko tausayin Daddynsa yakeji ganinsa Haka Kamar Wanda ƙwai ya Fashema aciki sai ya yi Tunanin ƙila Jikin Nashi ne Har yanzu.

Suna Shigowa Falon Suka Ci Karo da Iya ta Fito Daga Ɗakin Mufeeda Ɗauke da Ƙaramin Kofi Ahannunta tana ganinsu Tace "Yauwa gama Alhajin nan..." Faɗin Haka da Iya Tayi sai da gaban Tahir ya Tsinke Zufa ta fara Ketomai Tsura mata Ido yayi yana kallonta Domin miyan bakinsa ya ƙafe, bata Lura da Yanayinsa ba tace "Alhaji gaskiya ya kamata Akai Mufeeda Asibiti Zazzaɓin Jikinta yayi Zafi Sosai Inajin Maleria ce Ta Shigeta.." Ɓoyayyiyar Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin yace "Eh dama Dawowar Danayi kenan, Ta fito muje Adubata yanzu..." Ya faɗa Cikin Sanyin Murya Kai Iya ta kaɗa kafin tace "Yadai kamata Alhaji.." Ta faɗa Tana Komawa Ɗakin Mufeedan.

Iya ta Umarci Basma Data Ɗaukoma Mufeeda Hijabinta ita Kuma tana Ƙoƙarin Miƙar Da Ita Noƙewa Mufeeda Tayi Tana Rawan Jiki Tace "Bazan iya Tashi ba Iya ki barni Akwance Don Allah..." Fuskarta Iya Ta kallah Tana Faɗin "Sannu Daurewa zaki yi Alhaji ne zai kai Ki Asibiti Adubaki Mufeda.." Jin Abunda Tace ne yasa Ta ƙara Ruɗewa, Bata da Kwanar Amin Iya ta Tsayar da Ita da ƙafarta tana Cema Basma ta Bata Hijabin Hannunta, Mufeeda Ji Tayi Ƙafarta na Rawa Saboda Wani Hucin Azaba Dake bin Tsakiyar Kafarta Tana Ƙoƙarin Sulalewa Basma da Iya Suka Riƙota Iya ta Sanya mata Hijabi saman Doguwar Rigar Jikinta, Suna mata sannu Duk da Suna Riƙe da Ita amma yanayin Takunta yadda Take Gwale ƙafa sai da ya bama iya mamaki ta kalleta tana Faɗin "Mufeeda meya sameki ne ga kafarki ba Daidai ba Kina Tafiya Wani Iri..?"

  Iya ta Faɗa Tana kallonta Cike da Mamaki daidai Lokacin Da Suka Fito Falon, kuma maganar a kunnan Tahir, wanda Yaji jiri ya Ɗaukesa ya Ɗago yana kallon Mufeeda Zuciyarsa na Harbawa da Sauri Sauri Mufeeda Wacce Iya ta sakama ido, kafin Ta Waiga Tana kallon Tahir yadda ya Sauya cikin Kwana Ɗaya yasa bakinta na Rawa Tace "Ba..ba komai.. ɗazu ne nazo Fitowa Daga banɗaki Shi..shine Santsi ya ɗebeni na Faɗi na Buge ƙafana.." Ta faɗa Tana Runtse Ido Hawaye na Zubo mata, ajiyar Zuciya Daga Tahir har Iya suka Sauke Iya ce tace "Ashha Sannu.. ƙila Targaɗe Kikayi.." Ta faɗa Tana ƙara Riƙota su suka Fita Da Ita Har Haraban Gidan Saboda Tashin Hankali ko Ɗaki Tahir bai koma ba Da Jallabiyan Jikinsa ya Shiga Mota Daidai Lokacin da Iya da Basma Suka Shiga Motar, Gabansa ne ya Faɗi, amma sai ya Danne ya juya yana Ce musu Su bari yanzu zasu dawo su Zauna Su kula da gidan, ba yadda Suka iya Suka Fito Daga Motar Suna ji Suna gani Garzali yaja Motar Suka Fice Daga Haraban gidan..
.

Iyali Hospital iyalanshi Keda Fayel Amma gudun tonon Asirinshi yasa Suka Nufi Garkuwa Hospital, Suna Zuwa Aka karɓeta suka kuma yi sa'a Dr Hadiza ce kan Duty Ranar Haka ta Fito tana Faɗa Lokacin data ci karo Da Mufeeda Office Ɗinta ta Kira Tahir tana Tambayanshi Suwaye suka ketama yarinya ƙarama Mutumci Suka mata Wannan Illar, Fada Take Sosai, Zuciyar Tahir tashi ga Rawa Da ƙyar ya iya Faɗa mata ba'a san ko Suwaye ba, Nan dai Tace Zasu Riƙesu Domin Mufedan Tana buƙatar Kulawa Saboda An Jimata Rauni Sosai So Zasu Riƙeta Har Zuwa nan da Sati Ɗaya Sugani, Tahir yaji Daɗin Haka Sosai ko banza Asirinshi Zai Rufu, bai bar Asibitin ba Sai Wajen 10pm na Dare Har Mufeeda ta samu barci bayan ansaka mata Drip da Wasu Allurai, gida Suka Dawo Shi da Garzali Wanda baisan Abunda Ke Faruwa ba, inda Allah ya Taimakeshi Asibitin basu bukatar masu jinya, koda Ya Dawo su Basma basu Kwanta ba Suna Jiran Dawowarsu nan yake sanar dasu an bata gado, sun janjanta Sosai yace Suje su Kwanta gobe da Safe sai Suje Su Dubata, Iya ma sai Fatan Allah yabama Mufeedan Lafiya Take har Tashiga Ɗakinta.

Tahir ko bedroom ɗinsa ya Shiga Kafin ya Faɗa Toilet ya sakarma kanshi Shower yana kuka zucci jikinsa na Rawa inya Tuna kalaman Dr Hadiza inda Take mai Faɗa bayan yace Shi mariƙin Mufeeda ne, Da Har yayi Sakaci aka keta mata Mutumci Haka..? Yaya zataji in Taji labarin Shine Da Kanshi ya Aikata mata Haka..? Tun yana Kukan Zucci Har ya Fito Sarari, Dakyar yayi Wanka ya Ɗauro Alwala ya Fito ya Saka kayan barcinsa Riga da Wando, Ya Shimfiɗa Darduma ya Tada Sallah, Issha'i yayi kafin yayi Shafa'i da Wuturi ƙaramin Alqur'aninsa ya ɗauko ya Tankwashe ƙafa ya fara karatu Cikin Rawan Murya yanayi yana Kuka, kukan Nadama Da Kaico da Rayuwarsa.






*Anitha*
*Aisha Alto..*
*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Alkaluman:*✍️

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty*💕


_Don't Forget to Follow us On Wattpad: Janafnancy13 or Aisha Alto Alto_

_*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_

       *BABI NA GOMA*

Ranar barci ko ɓarawo bai Sace Tahir ba, kuka kuwa yayishi kamar Ranshi Zai Fita Daga ƙarshe ya Haƙura ya Fauwalama Allah komai ya kuma Ɗaukeshi A Matsayin Ƙaddararshi, Amma yasan Duk Abunda ya Faru Dashi Farida ce Sila kana Goggo Abu Da'ace Sunyi Duba da Lalurarsa da Irin Halittarsa, Da Duk Haka Bata Faru ba Amma yana Ta Neman gafaran Allah, sai dai Kunya da Nauyi Sun Cikamai Ƙirji Sun Hanashi Sukuni.

Shi yazo ya tashi Bassam Suka Tafi masallaci Sallar Asuba basu Dawo ba sai Wajen Bakwai Saura Koda suka Shigo Iya ta gyara Ko'ina Tana Kichen Tana Musu Abun Karyawa Bedroom ɗinsa ya shige ya Zauna Kawai ya Zabga Tagumin Makomar Rayuwarsa yadda ya Cuci Rayuwar Yarinya kamar Mufeeda.

Su Iya ko tana gama Abun karyawa Ta ɗorama Mufeeda Abunda Zata Tafin mata Dashi Asibiti Tunda Tahir yace in Sun karya Garzali zai Tafi Dasu, Shiko yana Cikin ɗaki yama kasa Fitowa Bawai bayajin Yunwa bane A'a yanaji Domin Rabonshi da Abinci Tun Jiya da Dare, Amma Cikinsa ne A Chushe bayajin Akwai Abunda Zai samu Wajen Zama ga bakinsa ba Tes Kwata kwata Ɗaci ɗaci ma yakeji Shikanshi Damuwa ta Saukar mai Da Zazzaɓi mai Zafi kan gado ya Kwanta ya Lulluɓa da bargo Haka Basma da Bassam Suka zo Suka iskeshi ya Dunƙule yana Hawaye, yanajin Muryansu Suna Kiranshi yayi Saurin Share Kwallah ya Fito da kanshi yana Ƙoƙarin Daidaita kansa.

   Basma ce Ta ƙarasa Tana Zama Gefen gadon Lokaci Ɗaya Take faɗin "Daddy jikin ne...? Ta faɗa Cike da Tausayawa, Kai ya girgiza musu kafin yace "No ba sosai bane Basma, nasha magani da nayi barci zan Warware, kun Shirya ne..." Bassam ne ya Ɗaga mai kai yana Zama Shima gefen Basma Fuskarshi ta bayyana Damuwar Dayake Ciki, Cikin Raunin Murya ya Furta..." Daddy What Wrong With you ne? bama jin Daɗin Ganinka A haka in Momy bata sonka Why not ka samo mana Wata Second Mom ko Basma...?" Ya faɗa yana kallonta, Saurin Kuka ne da Ita sai ga Hawaye Shar ta gyaɗa kai tana Faɗin "Eh mana Daddy, Momy tana Barinka kana Wahala bamai kula dakai ka ƙaro Aure plz kasamu Wacce Zata Dinga Zama dakai kullum muma Mu samu Mommy Wacce Zataso mu sosai Fiye da Momy.." Ta faɗa Kuka na Ƙwace mata ta Kifa kanta Jikin Tahir tanayi, Hannu ya saka yana Shafa kanta Dake Cikin Hijabin yanajin Ƙaunar 'ya'yansa Har Cikin Ranshi Duk da ƙananan Shekarunsu Sun Fahimci Damuwar nashi Acikin Ranshi Faɗi yake dama dama ace bai Aikata Abunda ya Aikata ba, Amma yanzu da Wani ido Zai kalli 'ya'yansa yace Shine ya Ketama Mufeeda Mutumci.

  Cikin Sigan Lallashi yake Faɗin "Shiii..Is Ok karku damu Kunji na samu Sauƙi Sosai Ku Tashi Ku Tafi Garzali zai kaiku Room 9 Take kunji.." Gyaɗa kai Basma Tayi kafin Ta mike Tana Share Kwallah Hannunta Bassam ya Riƙo Kafin su Duka Dukkansu Su Sakarma Tahir kiss a Goshi, Lumshe ido yayi Idanuwansa Sun Cika da Kwallah Cikin Raunin Murya yace "Take care..." Suka Fice Suna Ɗaga mai Hannu Suka Fita Wani Kuka yazo mai ya Shige Cikin Bargo yanayi kamar ya Shiɗe Saboda Takaichi So yake ya Buɗe Ido yaga Duk Abunda ya Faru mafarki ne Amma Ina bakin Alƙalami ya Riga Daya bushe, Abunda yasa Ma ya bari su iya suka Tafi Asibitin bashi da mafita ne don ya cigaba da Hanasu Zuwa Zasu Zargi Wani Abu, shiyasa yakira Dr Hadiza da Safen nan, dayake sun karɓi Numbarn Juna, ya Roƙeta Akan Don Allah mahaifiyar Mufeeda Zatazo Dubata koda Wasa Kada Ta mata Narrated din Abunda ya Faru da Mufeeda baya son Hankalinta ya tashi Sai daga baya zai sanar da ita, jin Haka yasa Dr Hadiza ta Amince da Roƙonsa suka Rabu Akan sai Anjima zai Shigo Asibitin.

Su Basma Sun Iske Jikin Mufeeda da Sauƙi Tana ta Barci ga Nurses nata kula da Ita sai Wajen 1 ta Farka taji Daɗin ganinsu Iya dasu Basma Ta dinga Murmushi, ta daina Kukan yanzu, Tunda Ta fara jin Sauƙi Gasata Suke bana Wasa ba ga mgaunguna gashi tana samun Hutu Dr Hadiza Da Tazo da Safe Haka ta Dinga Tambyar Mufeeda ko Zata Tuna Fuskar Wanda yayi mata Wannan Aiki Ko Zata Taimakesu Su Nemar mata Hakki, Acikin Ranta Kuka Take Har Asarari, Saboda Bazata iya Buɗe baki ta Furta Wanda ya Inganta Rayuwarta ne ya Aikata mata haka Bazata iya karya Alƙawarin da tayima Daddy ba Koza'a Kasheta Akaro na Farko Zata saka mai da Abunda yayi mata Arayuwa, tana kuka take Cemata bata sani ba Dole ta kyaleta.

Sun Daɗe sai Wajen Uku Suka Tafi bayan Iya Ta Zuba mata Faten Waken Data Zo mata Dashi Abakinsu ma Takejin Wai Daddy baida lafiya, Tana Shan Faten Waken Tana Sharan Kwallah Na Tausayin kanta Dana Daddy Domin Dukkansu Sun Faɗa Cikin Wata Jarabawa, koda suka koma gida Tahir na Kwance Ba yadda yake Ishaq ne da yayi ta Kiran Wayarsa bai samu ba  yazo gidan nan ya iskeshi Kwance Zazzaɓi ya Rufeshi Batare da Tunanin Komai ba ya Taimaka mai ya Fito Suka Tafi Asibiti.

Iyali Hospital Ishaq ya kaisa Suna Zuwa Suka Riƙeshi Saboda Jikinsa ba ƙwari ga Jininsa ya Hau Gado Suka bashi bayan Sun Sakamai Drip, Ishaq kamar yama Tahir Kuka yana Tunanin Duk Damuwar Farida ce Sai da Aka gama Komai aka kawoshi Ɗakin Hutu kana ya samu Sararin Kiran Farida yana Sanar da Ita Tahir bashi da lafiya gashi Anyi Addmiting Ɗinsu, Taji ba Daɗi Sosai Ta Dingama Ishaq din kame kamen batama san Bashi da lafiya ba, Nan tace Insha Allah gobe Zata Dawo Daga Haka Suka Rabu, kafin ya kira Zahra yana Sanar da Ita ta Turo Direba da Abinci yana Asibiti Zai Kwana da Tahir, Su Basma kuwa Jin Shuru basu Dawo ba yasa Suka saka Garzali ya Kawosu Asibitin nan Suka Iske Daddynsu Kwance Kuka Sukayi Tayi Ishaq na lallashinsu bai Tashi ba Har Suka Koma gida, Iya Tayi Tagumi Tana Jimamin Wannan lamarin Gefe Ɗaya tana Tir da Halayyar Farida.

Sai Wajen yamma Farida Ta Dawo, Tun Agida ta samu labarin Itama Mufeeda na Asibiti ga Tahir Abu Lokaci Ɗaya sai ta Fara Zuwa Asibitin Inda Tahir yake Ta Dubashi, taji Tsoro Ganin yadda Tahir ya Faɗa yayi Wani Sukuku Dashi nan ta Iske Ishaq da matarshi da 'ya'yansu, Alokacin ne yake Shaida mata Likita yace Damuwace Tayi mai yawa Sosai Shine ta galabaitar dashi gashi bayason Cin Abinci, Tagumi Farida Tayi Tana kallon Tahir Cike da Tausayi, Yau ne Rana Ta Farko Dataji bata kyauta ba, Shiko Tahir bayama son ganin Fuskar Farida Saboda Duk Itace Silan Shiga Wannan Halin Shiyasa ya Kulle ido Yayi mata barcin karya, Da Farko Ta karɓi Ishaq Jinyar Shi ya Koma gida Amma Sai Tahir ya Hana yace Ta Koma gida Saboda Mufeeda Shi Ishaq ɗin ya cigaba da Zama Dashi bata da yarda Zatayi Hakan ta Haƙura suka Fito da Aliya Kowa ya Shiga Motarshi Zuwa Gida.

Bata samu Zuwa gaida Mufeeda ba sai Washegari dasu Innaro Suka zo Da Ashe da Hakimi Sun Zo Duba Tahir bayan sun Dubashi ne Farida Ta ƙarasa Dasu Suka Duba Mufeeda wacce Ta samu Sauƙi Sosai, Koda Suka Haɗu In Farida zata Lura Mufeeda bata iya kallonta Saboda gani Take kamar Zata Fahimci Abunda ya Faru, Amma ita Farida ba Wannan bane agabanta Damuwarta yadda Tahir bayason kallonta balle yimata mgana sai ya zama Dole.

Washegari ne Umma Tazo Daga Kano, itama Ta Jinjina Ramar da Tahir yayi da Zata Tafi, tayi tama Farida Faɗa lokacin Data Zo Rakata, Akan ta kula da Mijinta Taga dai Halin Dayake Ciki Haƙuri Farida tabama Umma Inda Tamata Alƙawarin gyara Kuskurenta, itama bata Wuce ba sai da ta biya ta Duba Mufeeda, kana Direba ya Wuce Da Ita Kano.

Tahir Kwana Huɗu yayi A Asibiti kafin asallameshi ya Dawo Gida, Mufeeda ko Sai da ta Kwana Takwas Cur ta Warke kamar babu Abunda ya Faru kana Dr Hadiza Tayi Discharging Ɗinsu Tahir da kanshi yaje ya Taho Da Ita Shida Farida Wacce yanzu ke Wani Rawan Jiki Dashi Shi kuwa kallonta kawai yake Acikin Ranshi yana Faɗin Lokaci ya Ƙure miki Farida, Baya son ma Haɗa Ido da Mufeeda Amma itako Tana ta Satar kallonshi ganin yadda ya rame yayi ƙasumba kamar ba Daddy Ɗan Gayu ba, ita kaɗai Tayi ta Sharɓan Kwallah Acikin Ranta Tana Faɗin Ta yafema Daddy Duniya da lahira kuma Har Abada ba Wanda Zaiji Labarin Abunda ya Faru.

Gida yayi Daɗi da Dawowar Mufeeda mussaman ma Basma da Bassam da Iya, Tahir ko yanzu kwata kwata ya daina Sakewa kamar da ko ya'yanshi Sun Fahimci Haka dama kuma baida yawan magana Amma yanzu Abun nashi yayi yawa Tun balle Farida Data zage tana Kula Dashi Amma Sai dai ya Bita da Ido Abun ya Fara bata mamaki da Tsoro ko Ta Tambayeshi sai yace mata ba komai ta bashi Haƙuri Kuma yace ba komai amma ya kasa Sakin Jiki Da Ita Babban Abunda ya bata mamaki Shine bai Nemeta ko Sau Ɗaya ba, Shi ko Gaba ɗaya Sha'awarshi bata Zuwamai Saboda baya Cikin Natsuwarsa, Abunda ma ya ɗan Lafamai Shine ganin Mufeeda ta samu lafiya ta Dawo Walwalwarta Har Ta koma School Shi kaɗai sai ya Riƙa Fita Ta Ƙofar baya Daga sama yana Hangensu in Zasu makaranta ganin Ta Saki Jikinta yasa Hankalinsa ya fara Kwanciya.

Sati biyu ya kwashe Agida yana Hutu kana ya koma Office Wanda ko Alokacin Sai Ahankali Ishaq yasha Kamashi yashiga Zurfin Tunani Akwai Ranar daya ganshi yana Kuka Abun yabashi Tsoro, yayi kuma Tambayar Duniyar nan Amma Tahir yaki Sanar dashi sai ma Murmushin Kuka Dayayi mai yana Faɗin karyayi Fatan Jin Abunda ya Aikata Domin Har shima in yaji Sai ya Tsaneshi, Abun yabashi Tsoro Sosai Sai ya Dinga Fatan Allah ya yayema Tahir Duk Abunda Ke Damunshi Tunda yaƙi Sanar dashi koma menene.

Ita kuma Farida takasa gane kan Tahir yadaina Fitowa Dining Cin Abinci sai dai takai mai Ɗaki, shima bawani ci yake Sosai ba, koda yaushe ya dawo yana Ɗakinsa yana karatun Qur'ani ko Kuma ka ganshi Zaune yayi Tagumi duk ya Chanza kamar ba Tahir ba, bashi da Wata Walwala Komai na Duniya ya Fita kanshi gani yake Watarana Za'a gane Komai yana ji Ajikinsa Asirinsa bai Rufeba Wata rana Komai Zai Fito Sarari, kowa kuma Zaiji yazaiji Da Kunyar mutane Dawani Ido Zai kalli iyayansa yace Shine da kanshi ya Aikata Wannan Aiki, Abun yana Ranshi ya Hanashi Sukuni.

*****

Yau ɗin Takama Weekend ne Sunday, Tun safe Farida ke Lura da Tahir yayi Zurfi Cikin Tunani Ko Ruwan Wanka Data Hadamai bai Shiga yayi ba, Tana Lura Dashi yayi Zaune Kawai yayi Shuru agefen Gado ya zabga Tagumi da Hannu Bibbiyu.

  Shigowarta Bedroom d'in yasa Ta Bishi da kallo kafin ta ƙarasa Kusa Dashi Zama tayi Gefenshi Kafin ta sanya Hannu Ta dafa Kafaɗarshi Tana Faɗin "Abban Basma..." Ta faɗa Lokaci Ɗaya Tana Girgiza Kafaɗarshi, Ɗagowa yayi yana kallonta Kafin ya saki Ajiyar Zuciya, yana Lumshe ido Lokaci Ɗaya yana Furzar da Iskar bakinshi, narai narai Tayi da Ido kafin tace "Meke damunka ne..? Tunda Kadawo Daga Asibiti Ka Chanza kadaina Walwala kamar baya baka sakin Jiki da Kowa, Baka da Aiki sai yawan Zama Shuru da Tunani, kuma kasan Cewa Likita yace kadaina yawan Zama Cikin Tunani Saboda Jinin Ka yayi Sama.." Ta faɗa Cike da Tausayawa.

Ƙura mata ido Yayi kafin ya saki Ajiyar Zuciya, Kawai ya Miƙe bai ce mata komai ba, sai da ya Nufi Hanyar Toilet kana ya Waigo yana Faɗin "Bafa komai Tun Ranar Nake Faɗa miki karki Damu.." Ya faɗa yana Tura Ƙofar Toilet d'in ya Shiga Da kallo Ta bishi Jikinta Duk yayi Sanyi A iya Tunaninta ta kasa gano Abunda ke Damun Tahir Ta tambayeshi ko Itace Amma yace karta damu Bakomai Amma Koda yaushe Abun nashi ƙara gaba yake ba Wani Chanji, tana nan Zaune ya Fito Wanka Ɗaure da Towel a ƙugunsa yazo ta gabanta Zai Wuce Da Hanzari Ta Miƙe ta faɗa Jikinsa Ta Rungumesa ta baya ta Fashe mai da Kuka Tana Faɗin "Nidai don Allah ka sanar dani Abunda ke Damunka..? In nice na maka laifi Tunda na Dawo nake baka Haƙuri Bai ci ka Haƙura ba? Don Allah kadaina Wannan Tunanin.." Ta faɗa tana zagayo da Hannuwanta Ta Cikinshi Runtse Ido yayi Jikinsa Duk yayi Sanyi kafin ya Buɗe ya Juyo da Farida Suna

Please Login or Register in order to submit comment