Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Basma, Basma ce ta fara buga ƙafa tana faɗin "Plz Daddy na yau kadai...plz Don't say no..." Ƙura mata ido yayi yana kurɓan ruwan Lipton dake hannunsa kafin ya sauke yana faɗin "Ok..ok kuje ku shirya sai mu tafi.." Ya fada yana ajiye kofin ruwan lipton ɗin dake hannunsa.

Jin abunda yace ne yasa Bassam da Basma suka daka tsallen murna suka rungumeshi suna faɗin "Tanque Daddy..." A tare suka bashi peck agefen kumatunshi kafin su sakeshi kowa ya rumtuma zuwa ɗakinsa yana murna, Iya na musu dariya, Mufeeda kuwa shiru tayi ta duƙar da kai tana ƙoƙarin share ƙwallar data biyo gefen ƙunnenta, Tahir na lura da ita sai ya murmusa yace "Kema Mufee tashi kije ki shirya ki kuma shirya Naila duka mu tafi harda Iya, tunda bazamu barta ita kaɗai a gida ba.."

Mufeeda jitayi kamar an sakata agidan aljannah Firdausi haƙoranta duka awaje tace "Da gaske Daddy...?" Kai ya gyaɗa mata yana kallonta yadda jikinta yake rawa saboda murna, ga goyon Naila amma haka ta kwashi gudu ta shige ɗaki da mamaki Tahir ke kallonta ganin goyon na rinjayarta Iya kuwa miƙewa tayi tana dariya tace "Nagode Alhaji kamar kasan ko ina son komawa garin nan naku gaskiya iyayenka ko nace gidanku suna da kirki sosai..." Ɗan murmusawa yayi baiyi magana ba illah ficewa da yayi yana faɗin "In kun shirya ku sameni awaje.."

     Mintina talatin yayi musu yawa kowannensu ya shirya baki yaƙi rufuwa karma Mufeeda taji labari wacce ke ji kamar ta buɗe ido ta ganta gaban Inna Fulera saboda yadda ta zaƙu ta ganta, ta chanza kayan jikinta wannan karon less ne ajikinta riga da zani, sai hijabinta hakama Basma itama wata shadda ce ajikinta iri ɗaya dana Bassam itama hijabin ta saka don Tahir bai yarda da sanya mayafi ba kwata kwata bama ya yarda ya siyo musu ko Farida ta siyama Basma bata sakawa in Daddy na nan saboda tasan baya so, hakama Iya ta shirya itama tsab, kayan abinci Tahir yasaka aka ɗebo daga Store aka cika booth ɗin motar kafin Garzali ya shiga mazaunin direba Tahir ya shiga gaba Mufeeda da Basma da Iya da Bassam suka shiga gidan baya da yake motar nada yalwa, nan da nan yayi ma mator key ya saki horn lokaci ɗaya Megadi ya wangale musu get suka sulala waje yana musu fatan isa lafiya da kuma dawowa lafiya.

******

*ƊANBATTA*

Ƙarfe 11pm na safe motarsu ta tsaya adaidai ƙofar gidan Hakimi wanda tunda suka shigo garin Ɗanbatta yara ke bin motarsu da gudu ana faɗi ga Tahir ɗin gidan Baba Hakimi nan yazo saboda yara da manya sunsan yadda in yazo suke warkewa domin haka zai fito ƙofar gida yayi ta rabon kuɗi baya tsayawa sai ƙudin dayazo dashi duka sun ƙare, shima tunda suka shigo garin yake ta amsan gaisuwan mutane daban daban har zuwa ƙofar gidan mahaifin nashi wanda ke zaune a ƙofar gida kan wata kujera daga ƙasa kuma wata ƙatuwar tabarma ne mutane na zazzaune talakawa masu kawo ƙorafe ƙorafansu, shiko mai girma Hakimi Mansur na zaune bisa kujeran nan yana sanye da babbar riga kansa da rawani farin dattijo ne mai farin gashi da dattako, tunda motar ta tsaya farin ciki ya cikashi na zuwan ɗan nashi mafi soyuwa a cikin ranshi, nan da nan mutanen wajen suka miƙe kafin ma Garzali ya zagaya ya ɓude mai murfin motar har ansamu waɗanda suka buɗe mai suna mai barka da zuwa kamar wani babban mutum zakuyi mamakin yadda dattawa ke girmama Tahir sakamakon mutum ne nagari hankali da hikima kuma duk abokan mahaifinsa ne ya zauna cikinsu lokacin yana zaune agarin kafin ya koma cikin garin Kano domin yin makaranta sakamakon shine ɗa ƙwara ɗaya tak namiji da Allah ya bama Baba Hakimi.

  Hannu ya basu suna musabaha lokaci ɗaya yana ranƙwafawa alamar girmamawa har zuwa bisa tabarman dake wajen ya duƙe yana gaida mahaifinsa hakama Bassam yayi, miƙa masa hannu Baba Hakimi yayi yana faɗin "Yaka nan samarin birni.." Ya faɗa yana dariya tashi Bassam yayi yaje kusa da Baba Hakimi ya zauna ya miƙa mai hannu sukayi musabaha yana tambayanshi ya karatu daidai ƙarisowan su Mufeeda suma durƙusawan sukayi suna gaisheshi da mutanen dake wajen amsawa yayi cike da murna yana kallon fuskokinsu kafin yace "A'a amaryata me kika zomin dashi..?"

Basma na dariya tace "Kaji ka me nazo maka dashi ko kuwa mai ka tara min? Nazo karɓan nawa kajin ne da zabbin wannan shekarar.." Ta faɗa tana dariya gaba ɗaya wajen sai da aka murmusa ganin duka haƙoran Hakimi awaje yana dariya kafin yace "Au hakane, toh ki shiga ciki ki kama iya iyawarki, amma in Abu ta ganki ba ruwana.." Miƙewa tayi tana faɗin "Sai me..? Nida abun mijina.." Ta faɗa kamar da gaske, Dariya yayi yana kallon Mufeeda wacce ta sauko Naila data fara rigima hannu ya miƙa mata yana faɗin "A'a wanake gani kamar 'yar wajen Fulera...?" Tahir dake gefe ya taso ya karɓi Naila ya miƙa ma hakimi yana faɗin "Eh itace ranka ya daɗe.." Karɓan Naila yayi yana faɗin "Masha Allah...Allah yayi maka albarka Attahiru, kai kaga yara duk sun girma gama wata amaryar tawa inaga fa nan zan dawo.." Ya faɗa cike da barkwanci yana kallon fuskar Naila wacce ke zare ido tana bin kowa da kallo, dariya aka sakama Hakimi jin abunda yace, miƙewa su Mufeeda sukayi suka shiga cikin gidan suka bar Bassam da Tahir da Naila dake hannun Hakimi.

Gidansu Tahir babban gida ne mai ɗauke da shashe huɗu ginin bana ƙauye bane amma ginin gidan sarauta ne, duk da yanzu Tahir ya ƙara gyara gidan sosai shashen farko na Baba Hakimi ne na biyu kuma na uwargida sauratar mata wato mahaifiyar Tahir Zainabu Abu wacce suke kira Goggo, sai shashe na uku na mai bi mata ne Salamatu wacce suke kira Innaro sai shashen ƙarshe wacce na marigayiya Binta ne aka mai dashi ɓarayin 'yan aiki da kuma wajen ajiye hatsi, gidan Hakimi cike yake da al'umma daban daban kuma babu 'ya'yansa ko ɗaya sai 'ya'yan talakawa da mutanen gari da kuma masu musu hidima acikinsu harda Inna Fulera mahaifiyar Mufeeda tana ɗaya daga cikin hadiman gidan Hakimi masu dafa musu abinci.

Tun isowarsu yara suka shiga da gudu suka sanar da zuwansu toh dayake Basma ta rigasu shiga suna shiga suka isketa kwance kan ƙafar tsohuwa mai ran ƙarfe Goggo Abu kana kallonta kaga inda Tahir ya kwaso kyawawan idanuwa da dogon hanci, gashin kanta cike da furfura ta zauna bisa wani lallausar cafet daya mamaye tsakar ɗakinta mace mai kirki da sanin ya kamata suna shigowa da sallama ta ɗago tana amsawa cike da fara'a lokaci ɗaya tana yi musu maraba.

Gefenta suka zauna Iya ta fara gaisheta ta amsa cikin sakin fuska kafin Mufeeda wacce ke wulga ido tana son ganin ta inda mahaifiyarta zata ɓullo, cikin fara'a Goggo Abu tace "Mufeedan Fulera an zama 'yan mata ko..?" Ta faɗa tana dafa kanta murmushi tayi tana sadda kai kafin Iya tace "Aikam duk sun girma Goggo harda wannan lukutar banzar data haye miki ƙafa.." Ta faɗa tana zungurin Basma wacce ta tura baki tana faɗin "Kai Iya don ma ta samu na hau wannan ƙafar nata data kusa expier.." Make mata kai Goggo Abu tayi tana faɗin "Tashi ja'ira so take ta ƙarisa ni ta samu damar auren min miji ita kaɗai.." Dariya suka saka banda Mufeeda datayi shiru ganin haka yasa Goggo Abu ta tattaka ta miƙe bayan ta ture kan Basma tana faɗin "Ku tashi ku shiga shashen Innaro ku gaisheta inaga bataji zuwanku ba.." Ta faɗa tana nufar hanyar ɗakinta na ƙurya, miƙewa sukayi suka fita sai shashen Innaro ita ma falonta kamar na Goggo Abun ne durƙushewa sukayi suna gaisheta ta amsa cikin sakin fuska tana yafito Basma da hannu ta ƙariso da sauri ta kwanta ajikinta cike da shagwaɓa tana faɗa mata wai Goggo Abu ta hanata zama a cinyarta Innaro na dariya tace "Aiko zata gamu da mai girma Hakimi amarya guda ai dole mu lallaɓaki.." Ta faɗa tana dariya Iya na tayata Mufeeda ce tace "Innaro ina Innata tunda nazo ban ganta ba, ko ta koma gida ne..?" Innaro tace "A'a Innarki na madafi Mufeeda.." Jin haka yasa Mufeeda ta tashi da sauri ta fice kamar zatayi tuntuɓe su Basma suka bita da kallo Innaro tace "Yi a hankali Mufeeda karki faɗi, ina ruwan Mufeeda akwai ƙulafucin uwa ni banzaci ma zata yarda ta zauna gidan Attahiru har tayi wannan daɗewar ba.."

Iya tace "Toh ya zatayi amma fa ranar da aka tuna da Inna Fulera toh wuni za'ayi sharan ƙwallah.." Innaro ta saki murmushi kafin tace "Allah sarki ina ruwan Mufeeda haka itama uwar take sai dai dayake ita tana da kunya da kawaichi ko tana kewar ɗiyar tata bata taɓa nunawa.." Iya tace "Allah sarki..Haka abun yake bagashi yanzu tasamu kyakkyawar rayuwa ba ai wallahi babu abunda zamu ce ma Alhaji sai fatan gamawa da duniya lafiya.." Innaro ta gyaɗa kai tana faɗin "Ameen Ameen...Haka Attahiru yake kowa nashi ne, yafi son kyautatama mutane fiye da ya kyautatama kanshi.." Iya tace "Ba shakka munga zahiri muda muke zaune tare dashi.."

Mufeeda ko tana fitowa daga shashen Innaro ta nufi babban madafin gidan Hakimi nan tayi ta gamo da 'yan aikin gidan suna gaisawa kowa na mamakin ta ƙara girma gabda shiga madafin sai ga Inna Fulera ta fito da sauri domin itama ta samu labarin zuwan su Mufeedan kamar a mafarki suka ci karo ido Mufeeda ta zaro tana faɗin "Innata..." Da ƙarfi kafin ta rumgumeta cike da murna itama cikin tsantsar farin ciki ta ƙanƙameta tana murnan ganin ɗiyarta tilo ƙwara ɗaya da Allah ya bata.

Ɗagowa Mufeeda tayi tana hawayen farin ciki tace "Innata banzata zuwa ganinki ba ayau...Kina lafiya..?" Kanta Inna Fulera ta shafa kafin ta gangaro tana share mata hawayen fuskarta tace "Nima haka farin cikina, yanzu Gaje ke sanar dani zuwanku kunzo lafiya..?" Farin cikina kin ƙara girma kina jin daɗin zaman gidan Alhaji ko?" Gyaɗa kai Mufeeda tayi idanunta cike da ƙwallah tana dariya tace "Innata mu koma gida akwai labari.." Dariya Inna Fulera tayi kafin ta riƙo hannunta tana faɗin "Yanzu kuwa farin cikina, bari na barma Maman Lantana sallahu sai mu tafi.." Da sauri Mufeeda tace "Yauwa Innata Lantana fa..? Ko sun tafi birnin ita da Ladonta..?"

Inna Fulera tace "Tun yaushe bayan auren da wata biyu suka tafi can Kano gidan da yake gadi da zata tafi tazo tamin sallama tayi tacewa na gaisheki.." Kawai sai Mufeeda ta hau sharar ƙwallah tana faɗin "Allah sarki Lantana Allah sa mugana.." Murmushi Inna Fulera ta mata suna riƙe da hannun juna suka nufi madafi Mufeeda maƙale da ita tana mata surutu.

*******

Tahir ya daɗe awaje wajen Baba Hakimi da jama'ar wajen bai shigo ba sai da ya gama rabama mutanen wajen kuɗin da yazo dashi yara da manya, Bassam ya aika yace ya sanarma Goggo Abu ta dama mai fura shida Garzali, nan ya shiga ciki ya barsa toh bai shigo ba sai da yaq gama da wajen kana yama Hakimi sallama da zai shiga wajensu Goggo.

   Goggo Abu na zaune ta gama dama ma Tahir furarsa kenan ta tsiyayarma Garzali nashi cikin wani kofin silba mai kyau ta miƙama Bassam kenan yayi sallama ya shigo kafaɗarsa ɗauke da Naila wacce tayi barci hannun Hakimi, Goggo Abu ta ɗago tana amsa sallamar nashi fuskarta cike da annuri kai tsaye gabanta ya nufa yana ƙoƙarin zama ta miƙa hannu tana faɗin "Kawo ta nan dama da ita kukazo..? Ina uwarta take ne kuka zo da ita ita kaɗai..?" Ta faɗa tana karɓanta lokaci ɗaya ta miƙe ta shiga da ita ciki ta kwantar da ita shi kuma Bassam tuni ya fice zuwa waje ɗauke da fura zai kaima Garzali Allah Allah yake ya fita ko ya samu damar shiga cikin gari kafin Daddy ya farga bayanan don Bassam akwai son ƙauye musamman ma na Babansu.

   Sai da ta fito kana tazo ta zauna inda ta tashi tana turamai kwanon sha mai cike da fura da nono tana faɗin "Lafiya na ganku kamar daga sama inace shekaranjiya mukayi magana da kai sai sati na sama zaka shigo ba.." Ta faɗa tana kafeshi da ido, rausayar da kai yayi kafin yaja kwanon furan ya buɗe yana motsawa da ludayi kafin yace "Goggo Farida bata nan ta tafi bikin ƙanwar ƙawarta Abuja tun wajen kwana uku da suka wuce.."

Ya faɗa yana sadda kansa ƙasa, shiru Goggo Abu tayi kafin tace "Naji, shine dalilin zuwanka kenan ko..?" Ta faɗa fuskarta ba annuri bai ce komai ba illah maida kanshi ƙasa da yayi yana kurɓan fura itama ganin ya mata banza sai ta ƙyalesa sanin halinsa na miskilanci, bai ƙara magana ba sai da ya gama shan furan nashi kafin ya ture kwanon yaja murfi ya rufe yana faɗin "Alhamdulillah..."

Ya faɗa kafin ya gyara zama yana faɗin "Goggo ya jikin ɗan wajen Ashe..? Jiya munyi waya take sanar dani Muda ba lafiya..?

  Tana matsa ƙafanta data miƙar dasu take faɗin "Yaji sauƙi sosai ɗazu da safe nan yake.." Daga haka bata ƙara magana ba matsowa yayi yana tayata matsa ƙafar yana faɗin "Wai har yanzu ƙafar bata bar matsa miki ba Goggo..?" Bata kalleshi ba tace "Tayi sauƙi kasan jikin tsufa fa abun sai a hankali..." Ta faɗa kai tsaye murmushi yayi ganin yadda Goggo abun ke wani cin magani duk don karya mata maganar daya saba ne, amma duk da haka bai haƙura ba gyara zama yayi yana matsa mata ƙafa yana faɗin "Goggo akan maganar Farida ne, tsakani ga Allah na gaji da haƙuri da ita da kuma hallayarta nazo ne na ƙara roƙonki ki bani dama na sanar ma da Baba Hakimi zan ƙara aure..." Ya faɗa yana ƙoƙarin son su haɗa ido.

Ƙur kuwa tamai da ido kafin tace "Har sau nawa zan ce maka kabar wannan maganar Attahiru, maganar Farida nace kayi haƙuri yarinta ke damunta banaso ka yi abunda iyayenta zasu ga kamar mun ɗaure maka gindi ka tozarta musu yarinya. Cike da wani jin haushi ya marairai ce yana faɗin "Toh amma Goggo..." Kabar maganar nan nace ko Attahiru...?" Goggo Abu ta katseshi rai ɓace, kansa ya sadda a ƙasa yayi shiru yana jin kamar ya kurma ihu, ganin yadda yayi ne sai tausayinsa ya kamata ta dafa kanshi tana faɗin "Kayi haƙuri zan yi magana da ita Faridan insha Allahu kaji..." Kai kawai ya ɗaga mata idanuwansa sun canza launi saboda ɓacin rai.
 
Ya daɗe zaune shuru kafin ya saki ajiyar zuciya ya miƙe yana gyara hulan kansa yana faɗin "Bari na leƙa na gaida Innaro daga can zan gangara wajen Ashe naga jikin Mudan." Kai ta gyaɗa kafin tace "Adawo lafiya.." Jiki asanyaye ya fice ta bishi da kallo wani tausayinshi na ratsata amma kuma bazata bari ya sanar da Hakimi wannan maganar ba sai ta ƙara magana da Faridan tunda abu na zumunci ana tare tun ba'a haifesu ba bazata bari Tahir ya ruguza wannan zumuncin ba.

Koda ya shiga wajen Innaro Iya kaɗai ya gani koda ya tambayi Basma sai Innaro tace ta tafi gidan Innarsu Ashe bai daɗe ba ya fito zuwa waje ya sanya Garzali ya buɗe booth yace ya shiga da kayan ciki, shi kuma yayi sallama da Hakimi akan zai gangara gidan Ashe dayake babu nisa da ƙafa ya taka, duk inda yabi ana gaisheshi cike da girmamawa da ban sha'awa har ya isa gidan Ashe can ya iske Basma da Bassam wanda ya gansu a ƙofar gida shida Mudan wanda sa'an Bassam ɗin ne, ita kuma Basma suna cikin gida ita da Laila ƙanwar Mudan ce 'yar wajen AShe dayake tana da tsawon ƙafa har takamo girman Basma.

  Nan Mudan ya ɗuka yana gaida Kawun nashi shi kuma ya riƙoshi yana hararan Bassam da wasa shiko yana dariya riƙe da hannayensu suka shigo gidan Ashe na ganin Yayan nata ta shiga ina zata saka dashi Laila ma tazo ta gaisheshi ya riƙe hannunta yana tambayanta karatu bai wani daɗe ba ya miƙe ya mata sallama zai tafi 30k ya fito dashi daga aljihu ya bata ta karɓa tana ta godiya 5k ya bama Mudan da Laila yace su siya wani abun buƙatar nasu suna ta murna har waje suka rakosu Ashe natama Yayan nata godiya su Mudan kuwa har gidan Hakimi suka rakasu inda Tahir yace suyi haraman tafiya nan fa aka nemi Mufeeda aka rasa Goggo Abu tace yanzu haka sun koma gida ita da Inna Fulera Tahir bai damu ba yace sai su biya su ɗauketa nan ya cika Goggo Abu da Innaro da kuɗi hakama Baba Hakimi wanda ya dinga sakamai albarka tare da nasihan riƙo da gaskiya Allah ya taimakesu har sukazo tafiya Naila nata barci, wajen karfe 3 na yamma motar su tabar ƙofar gidan Hakimi bayan su Laila da Mudan sun sanar da Kawun nasu wannan hutun yasa azo aɗaukesu agidanshi zasuyi hutu yace karsu damu in sun samu hutun zai turo Garzali yazo ya tafi dasu, murna ta cikasu harda su Bassam, wadanda suka kwaso zabbi da kaji gidan Hakimi wai zasu kiwata Tahir na kallonsu ko tankasu baiyi ba bazai shiga tsakanin jikokin da Kakanninsu ba.

Daganan sai ɗan karamin gidan da Inna Fulera ke zaune suka tsaya Iya ne da Basma suka shiga basu daɗe ba sai ga Mufeeda ta fito ita da Inna Fulera ganin haka yasa Tahir ya fito yana amsa gaisuwan Inna Fulera wacce ke neman dukamai tana ta zubamai godiya harda ƙwallarta kuɗi ya ciro 20k ya bata ta kasa karɓa sai kuka take tana faɗin "Nagode Alhaji wallahi basai kabani ko sisi ba alherinka ga Mufeeda kaɗai ya isheni ka tufatar da ita ka ciyar da ita haka zalika ka ilimantar da ita kuma baka taɓa bambamceta da 'ya'yanka ba duk da ta kasance ita ɗin hadimarka ce mai renon 'ya'yanka wallahi bani da bakin gode maka sai dai nayi fatan Allah yasa kagama da duniya lafiya ya kuma sakamaka da gidan aljannah Firdausi.." Da Ameen yake ta karɓawa cike da jin nauyin godiyarta gareshi da ƙyar ta karɓi kuɗin suka rungume juna ita da Mufeeda suna kuka gwanin ban tausayi kafin su saki juna Mufeeda ta shiga mota suna dagama juna hannu har suka bar ƙofar gidan, sun fita cikin garin kenan Naila ta tashi wacce ke hannun Tahir ya waigo yana kallon Mufeeda yana faɗin "Toh Maman Naila bar kukan haka nan gashi tana kukan neman uwar ɗakinta.." Ya faɗa cikin barkwanci yana miƙa mata Naila cikin jin kunya ta share ƙwallarta ta miƙa hannu ta karɓeta nan da nan ta ɓalle jakar data zubo kayan madaranta da Flaks ɗin ruwan zafi da ƙaramin kofi da cokali ta dama mata madaranta ta shiga bata nan da nan takoshi sai kuma ta koma barci bisa kafaɗarta ta kwantar da Naila ita kuma ta jingina kanta jikin ƙofar motar tana sharae ƙwallah..

Ta madubin gaban motar yake kallonta ajiyar zuciya ya sauke kafin ya murmusa yana faɗin "Tasan kan renon yara.." Ya faɗa yana maida kanshi cikin jikin cussinon ɗin kujeran motan shi kuma Garzali ya saki kan mota yana bata wuta.


*Don"t Forget To comment,Vote and Share*


*Aisha Alto*
*Anitha..*
*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Alkaluman:*✍️

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty*💕

*Wattpad:* *Janafnancy13 or Aisha Alto Alto.*


_*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_

*BISMILLAHIR RAHAMIR RAHIM*

       *BABI NA UKU*

      *ASALIN LABARI*

 
*HAKIMI MANSUR ƊANBATTA* Shine asalin sunan mahaifin Tahir wanda gabanshi da bayanshi haifaffan garin Ɗanbattan ne kuma ya fito daga tsatson Hakimin Ɗanbatta ne daboda haka sarautar Hakimi daya samu ba haye yayi ba gadon gidansu ne.

    Tun suna samarinsu lokacin tasowarsu basuyi karatun boko ba lokacin bai yawaita ba sosai sai dai karatun allo wanda yabi gari lokacin inda ake ɗaukan yara dawaya daga kowane yanki suna zuwa karatun allo cikin Kano da sauraran garuruwa basu dawowa har sai sun sauke alqur'ani wasun suma har sai sun fara sana'a, sunyi ƙarfi kafin su waiwayi gida, toh hakan ne ta faru da Mansur wanda ɗane ga mai garin Ɗanbatta, lokacin dayake da shekara tara a duniya aka tafi dashi cikin garin Kano aka damƙashi hannun wani malamin addini mai suna Malam Haruna wanda amini ne yake ga Hakimi Hayatu.

A lokacin ba dan talaka ko ɗan mai kuɗi ba ko yaron gidan sarauta a'a lokacin ilimi bai yawaita kamar yanzu ba shiyasa zaka samu yara daga mabambantan garuruwa ankawosu wajen Malam Haruna karatun allo duk kuma daya ke iyayen yara a lokacin basu sake kamar na yanzu da in suka kawo yaro sai sun manta dashi a'a su kowane bayan wattanni suna zuwa ganin 'ya'yan nasu kuma suna musu aike akai-akai.

Wannan shine dalilin haɗuwar amintakan Hakimi Mansur da kuma Alhaji Ibrahim Kwatano wanda shima iyayensa suna da hali suka kawoshi nan makarantar Malam Haruna domin ya sauke Qur'ani lokaci ɗaya haɗuwar jini da abota mai ƙarfi ta haɗasu kuma Allah yayisu hazikai masu kaifin ilimi wanda har iyayensu duka suka shaida amintarsu ahaka suka shafe shekara bakwai kafin suyi sauka murna ba'a magana Malam Haruna ya shirya musu walima duka iyayensu suka zo suka tayasu murna, kafin kowa iyayenshi su tafi dashi gida.

Ibrahim yayi sa'a dama already kafin yazo makarantar allon ya gama Primary Sch ɗinshi suna komawa gida iyayensa suka mai cuku-cuku ya koma makarantar SS1, ayayinda shi kuma Hakimi Mansur koda ya koma sai ya fara daga Primary 1 duk da lokacin yana da shekara goma sha biyar ne toh kafin ya gama Secondry tuni Ibrahim yana BUK inda yake karantar Business Admistration, shi kuma Mansur yana gama Secondry karatunsa ya tsaya saboda rasuwar Hakimi Hayatu wanda dama Mansur ne kaɗai ɗansa namiji sauran duk mata ne so sai aka ɗaura ƙaninshi ya cigaba da riƙon sarautar maigari.

Mansur da Ibrahim suna ƙoƙarin ziyarar juna duk wanda ya samu dama Ibrahim na shekarar ƙarshe mahaifiyar Mansur ta matsa mai sai yayi aure kafin ta mutu taga kwanshi aduniya shine dalilin daya sanya ta nema mai auren ɗiyar ƙanin mahaifinshi Zainabu Abu, wanda cikin lokaci akayi komai aka gama akayi biki lafiya sai bayan bikin ne Ibrahim ya tafi service shi kuma Mansur yana zaune agidansu ɓarayin gadon mahaifinsa shida matarshi Zainabu Abu mai kunya da kawaichi shekararsu ɗaya da rabi da aure ta haifi kyakkyawan ɗanta mai kama da ubansa sak aka sanya masa suna Tahir to bayanshi ta yi haihuwa biyu duka basu zo da rai ba, lokacin ne kuma itama mahaifiyar mansur Allah yayi mata cikawa, wanda har iyayen Ibrahim sunzo gaisuwa shi baya ƙasar yana  ƙasar Ughanda yatafi haɗa Masters ɗinshi, tun kuma bayan rasuwarta sai Abu ta shiga ɓari data samu ciki baya zama sai tayi barinshi kamar bazata rayu ba abunda ya fara damunsu har suka fara neman mata magani amma kuma sai cikin yayi kamar zai zauna sai kuma tayi ɓarinshi.

   Sai da Tahir ya shekara 9 aduniya kana Ibrahim yayi aure bayan ya daɗe da dawowa ya haɗa Masters ɗinshi Babanshi ya bashi kuɗi sosai ya ɗorashi kan kasuwancinsa dayake dama shi ɗin motoci yake saidawa 'yan kwatano shiyasa yake amsa wannan laƙabi bikin da Zainabu Abu ita da Mansur da Tahir sukaje suka kwana uku suka dawo domin Mansur da Ibrahim basu yarda zumunci ba.

Matar Ibrahim Aliya itama 'yar gidan masu dashi ne irin yaran nan da jin daɗi yayi musu yawa, shekaransu ɗaya da aure ta haifi yarta mace wacce aka sakama suna Farida, yarinyar data ga gatan duniya sosai daga ɓangaren iyayenta zuwa na kakanninta kuma tunda ga ita Allah bai ƙara basu haihuwa ba.

Tahir nada shekara sha uku aduniya lokacin har ya kammalah zana jarabawarsa na Primary, Abu ta haifi 'yarta mace mai suna Aisha suna kiranta Ashe wacce Tahir yafi ma iyayensu murna da ɗokin haihuwar Ashe tafi tafi rayuwa na nisa har zuwa lokacin da Tahir ya kammalah Secodary School ɗinsa acikin makarantar Secondry dake garin Ɗanbatta.

Tahir tun yana ƙaraminsa yaro ne mai son yayi karatu shima ya zama wani abu ya taimaki iyayensa da garinsa na haihuwa wannan dalilin ne yasa wani ziyara da Alhaji Ibrahim Kwatano ya kawo mai suka tattauna batun Tahir ɗin shikuma yayi mai alƙawarin zai tafi da Tahir domin ya inganta rayuwarsa labarin dayayima Tahir dadi sosai bai tafi dashi a lokacin ba sai da ya karɓi takardunsa ya tafi dashi ya nema mai gurbin karatu

Please Login or Register in order to submit comment