Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Namiji.." Dafe ƙirji Farida Tayi kafin Tace " 'Yan biyu fa kace...?" Ta faɗa Tana kallonsa Bai mata magana ba illah binta da Kallo Da yayi kafin yace "Eh Abunda Kunnenki ya jiye miki..." daga Haka ya Wuceta ya Barta sama ya Koma ya Ɗauko Wayarsa ya Sauko, Ɗakin Mufeeda ya Shiga Inda ya Tatarro Duka kayan Babies, Sai kuma Dogayen Riguna da Riga da Zani, ya Fito Nan ya Wuce Farida Tsakiyar Falon Tana Binshi da Kallo, Bassam ne ya Biyosa yana Tambayansa Mufeeda Ta Haihu Cike da Fara'a Tahir ya Ɗaga mai kai kafin yace "Kun samu ƙanne Bassam 'Yan'uwanku ne Twince ne Suma.." Washe Baki Bassam yayi Harda Tsalle yana Faɗin "Daddy Zan Bika.." Bai ce mai komai ba sai ma Miƙa mai Jakar Kayan Mufeeda da yayi Suka Fice Daga Falon.

Sai da Tahir ya kawo Kayan Kana Aka maida Yaran Ciki aka Sake Gyarasu aka Shiryasu Cikin kayan Sanyi pick masu kyau Ɗakin da Mufeeda Suke Suka maidasu, suka ce suma abarsu Su Huta Haka nan, Bakin Basma da Bassam yaƙi Rufuwa saboda Murna Sai Lokacin Tahir ya samu Damar Kiran Baba Hakimi yake Sanar Dashi Baba Hakimi Dake Shirin Fita Sallar Azahar ya Washe Baki yana Faɗin "Kai Masha Allahu...Allah ya inganta.." Daga nan Abba ya Kira Shima ya Sanar Dashi, Shima ya Saka albarka, Daga Abba sai ya Kira Ishaq ya Sanar mai, Wanda ke Zuba kabbara Cikin Waya kafin Kace me Haihuwan Mufeeda Ta isa Kunnan Wanda ya kamata Farin ciki kamar bata Gurɓattaciyar Hanya aka samesu ba.

****
Baba Hakimi Na gama Waya da Tahir ya Shiga Cikin Turakarsa ya Ɗauko Huhun Goro da Dabino Cikin Wata Leda Waje ya Fita Zuwa Masallacin Kusa da gidan nashi Lokacin Har An Tada Sallar Jumma'a Domin Babban Masallaci ne Wanda ke Jikin Gidan nashi Inda Suke Gudanar da Sallar Jumma'a.

Bayan An idar da Sallah Baba Hakimi Ya bada Sanarwan Akwai ɗaurin Aure nan da nan ko Kowa ya Matso kuɗi ya Fito Dashi Duba 30k ya bama Liman yana Faɗin "Ina so kazama Wakilin Ɗana Tahir, ni kuma zan zama Wakilin Mufeeda A Ɗaura musu Aure.." Liman ya Washe baki ba tare Da bata Lokaci ba nan Take Shaidu Suka Shaida Ɗaurin Auren Tahir Mansur Ɗanbatta da Mufeeda Bello Ɗanbatta, Auren Daya bama Kowa Mamaki Domin Mutane Da dama Sun san Mufeeda A matsayin Wacce ke Reno A gidan Tahir, Cikin Fari ciki Taro ya Watse bayan an Raba Goro da Dabino Baba Hakimi ya ɗibi Wasu ya Shiga Dasu Cikin Gida Har Ɗakin Goggo Abu Wacce ke Cike da Murnan Wayar Da Tahir ya mata yanzu Yana sanar da Ita Haihuwan Mufeeda, goro da Minti ya miƙa mata yana Fadin "Na Ɗaura ma Tahir Aure da Mufeeda Yanzu bayan Mun Sauko Daga Sallar Jumma'a..." Baki Goggo Ta Washe kafin tace "Mallam kamar kasan Abunda Ke Raina kenan...Allah ya basu zaman lafiya.." Da Ameen ya amsa Cikin Jin Daɗin Haɗin kanta Duk Da yasan bazai Samu Matsala ba.

******

Har Yammah Su Innaro na Asibitin Sun cika Ɗakin da Mufeeda Take bayan ta Farfaɗo, Basma da Bassam Sun ƙanƙame yara Ko Tahir basu Bari ya Ɗauka ba, sai da Innaro ta karɓe Macen Ta Hannun Basma Ta Miƙa mai ya karɓa Cikin Jin kunya Lokaci Ɗaya yana Tsurama Jaririyar Ido Sak Basma Tana Jaririya, Lokaci Guda Idanuwansa Suka kawo kwallah yayi Saurin Mayar Dasu Mufeeda Dake Jingine da Gado Tana kallonshi yana Dagowa Suka Haɗa ido sai tayi Saurin Kauda kai Murmushi yayi ya ƙarasa Kusa da Ita yana Faɗin "Mufee ya Jikin..?" Kanta na Ƙasa Tace "Da Ɗauki Daddy..." Kai ya gyaɗa kafin yace "Masha Allah...Allah ya ƙara baki lafiya.." Da Ameen Ta amsa Ƙasa ƙasa, kan Jikinta ya Ɗora mata Jaririyan Yana Faɗin "Kina Sonta...?" Kallonsa Tayi kafin tace "Kaifa kana Sonsu...?" Kai ya Gyaɗa mata kafin yace "Ina sonsu Sosai kuma Zan Cigaba da Ƙaunarsu Har Ƙarshen rayuwata.." Murmushi Ta Saki kafin tace "Nima ina sonsu...." Dariya yayi yana kallonta kafin ya Miƙa Hannu ya karɓi na Hannun Bassam ya Ɗora mata Bisa Jikinta yana Ƙoƙarin Zama Kusa Da ita Wayarsa ta Shiga Ƙara Miƙewa yayi ya Zarota Ciki Aljihu sai yaga Hakimi ne Da Hanzari ya Fice Mufeeda ta Bisa da Kallo Cikin Wani yanayi.

Fita yayi Haraban Asibitin kana Ya Ɗaga Kiran Cikin Farin ciki Baba Hakimi yace "Ya Wajen Maijegon da Sabuwar Amarya don bazan Tambayi sabon Megidan Salamatu ba Tunkafin ya Fito Duniya Take Nuna min Son kai.." Dariya Tahir yayi kafin yace "Duk Suna lafiya Ranka ya Daɗe.." Baba Hakimi yace "Madallah kafin ya Zarce da Faɗin "Attahiru na yanke Wani Hukunci ba tare Da nayi Shawara Da kai ba Domin ina ganin Hakan Shine Daidai.." Tahir ya Jinjina kai yana Faɗin "Ka isa ne Ranka ya Daɗe kowani Hukunci ne zan karɓa Hannaye Bibbiyu.." Baba Hakimi ya saki Murmushin Jin Daɗi yana Faɗin "naji Daɗin Haka ba Komai Illah Ɗazu bayan sallar Jumma'a Na Ɗaura maka Aure da Mufeeda yanzu Haka tana Matsayin Matarka ne Attahiru..Bata da wanda ya fika ku Haɗu ku Rungumi 'ya'yanku Karsu Tashi suga bakwa Tare Su Tuhume ku Wata rana.." Ajiyar Zuciya Tahir ya Sauke kafin yace "Hakane Baba...Allah ya bani ikon Adalci.." Da Ameen Baba Ya amsa kafin Su yanke Kiran Bayan Baba Hakimi ya tabbatar mai Suna Tafe ko yaushe.

Bai koma Cikin Asibitin ba yayi Tsaye yana Tunanin Wannan Al'amarin Guda Biyu Lokaci Ɗaya Haihuwa da Aure, Dafe kansa yayi yana Faɗin "Alhamdulillah...Allah ne Abun Godiya.." Yana Cikin Wannan Halin ya hangi motar Ishaq Ta Shigo Cikin Asibitin Bai Matsa daga Wajen Ba Har Suka ƙaraso Shida Zahra ta gaisheshi Bayan Ta mai barka, Shi ya musu Jagora zuwa cikin Ɗakin Suka Gaida Mufeeda Suka kuma Ɗauki Yaran Bayan Sun gaisa da su Innaro Nan Suka bar Zahra Tahir yaja Ishaq suka Fita Waje Cikin Damuwa ya labarta mai Abunda Baba Hakimi ya Kirasa ya gaya mai Baki Ishaq ya Washe kafin yace "Finally...Baba Hakimi ya gama maka Komai Friend...Mufeeda Ta Chanchanci Haka Domin Bata da Wani Gata Nan Duniya bayan kai...Gaskiya Allah sakama Baba Hakimi da alheri Yayi Abunda ya Dace.." Tahir dai Shiru yayi yana Jin Ishaq Shi kuma yana Cigaba da Bashi baki basu koma Cikin Ɗakin ba sai da Sukayi sallar Mangariba, suna komawa Tahir yace Su Basma Su Shirya su Koma gida, Harda Iya gobe da Safe sai su Dawo Innaro kaɗai Aka bari zata kwana da Mufeeda, Zahra tayi musu sallama Bayan ta ijiye musu kwandon Abincin Da tazo Dashi. Tare Suka Fita Bayan Tahir yayi musu Sai da Safe Mufeeda kuwa na Kwance Tana Binsu da kallo har Suka Fice Daga Ɗakin.



*Anitha..*
*Aisha Alto..*
*NANNY...!*
      (Mai Reno..)

*Alƙaluman:*✍🏻

*AISHA ALTO💞*
*JAMILA UMAR (Janafty💕*

_Don't Forget to Follow us On Wattpad: Janafnancy13 or Aisha Alto Alto_

*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔*
*KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*

    *BABI NA ASHIRIN DA DAYA*

"""Suna Shigowa gidan da Farida Suka ci karo tana Zaune Afalo Tana Zare ido Domin gama wayarsu kenan da Umma tana Tambayanta ya Wajen masu jego tace suna lafiya tanama Asibitin ne Tafito amsa waya ne,Umma taji Dadi tace mata suna nan Zuwa Cikin Satin nan Ita da Abbanta......

Daga Tahir har ya"yansa Babu Wanda ya Tankata Kowannensu Dakinsa ya Nufi Haka Shima Tahir ya Haura sama ya Fada Dakinsa A matukar gajiye yake Shiyasa yafada wanka,Iya ce kadai ta iya tsayawa tana gaida Faridan wacce Tabi su Basma da kallon Mamaki,Tahir ta Daina Damuwa dashi Domin baya Shiga Harkanta Tuni.

Bayan ta amsa gaisuwan Iya ne ta kalleta tana Fadin"Wai iya da gaske ne Mufeeda yan biyu ta Haifa...? Gyada mata kai Iya Tayi Lokaci Daya tana Washe baki tace"Eh Hajiya mace da Namiji yara nan kamar su Basma suna Jarirai inji innaro.."Harara Farida ta Zabgamata Lokaci Daya Tana Fadin"Kul kar na sake ji...Ni ya"yana na Sunnah ne karki kara Hadasu da Shegu wanda ba ya"yan Sunnah ba.."Cike da mamaki Iya ke kallonta bata samu Zarafin mgana sai ma gyada kai Datayi ta juya Zuwa Daki bayan ta kalli Naila dake barci kan kujera tagaji da kuka Barci ya kwasheta.

Da Harara Farida ta Bita kafin ta koma ta Zauna tana karkaɗa ƙafa, Iya tana Komawa ɗaki ta Fito ta Shiga kichen domin sama musu saukakkan Abinci da zasu ci Shiko Tahir Bayan ya Fito Wanka yayi sallar Isha'i da Shafa'i da Wuturi ya koma ya kwanta domin Haka kurum yaji Cikinsa ya Cika baya Sha'awan Cin komai kwance yake kawai yana Tunanin Wai shi yanzu mijin Mufeeda ne, Lalle Allah ne mai Tsara komai kuma ya aiwatar yana Fatan Allah yasanya alheri yabashi ikon kwatanta Adalci Domin baya ta Farida Ita yanzu bazai ƙara Ɗaukan Wani Iskancinta ba, Itama ta sani.

Da Iya ta gama Dafa musu macaroni da Kifi, Su Basma kaɗai Suka ci sai Iya ko Farida bata ci ba ɗaki ta koma tana kukan Bakin ciki da Takaichin Wai Mufeeda Ta haihu har 'ya'ya biyu lalle ma wato zata Haɗa kafaɗa da ita, ba wanda yabi ta kanta Har Washegari da Safe Tahir ya Tafi Office Su kuma Iya da Basma da Bassam da Naila data saka Rigimar sai ta tafi Tahir baima sani ba Ya bari sai zuwa yammah su koma Tunda ya tafi musu da Abun karyawan da Iya tayi musu Ashe su kuma suna Gama Dafa na Rana suka tafi dashi Keke Napep Suka Shiga Zuwa Asibitin Suka bar Farida agida tana kallon ikon Allah.

Sanda suka isa asibitin ma Sun Iske Zahra matar Ishaq itama ta kawo Abinci Mufeeda na Zaune Innaro na bata Tea abaki Taji Sauƙi ba kamar jiya ba, Namijin ne ke Hannun Zahra Shine mai Rigima macen na kwance Tana barci Naila Haka ta saka Rigiman sai an bata Ta Ɗauka ganin Su Basma Sun Ɗauka harda kukanta Su Iya na mata Dariya, cikin ikon Allah Ruwan Nonon Mufeeda ya Fara Zuwa ba laifi Tunda Dukkansu suna samu Suna Sha Duk da baya isarsu Da Safe ma da Tahir yazo Likita yamai maganar za'a Haɗa musu da madara saboda kada yunwa ta kamasu.

Kumburin Jikin Mufeeda ya Ragu amma ba Sosai ba, Sunyi Waya da Baba Hakimi da Goggo Abu Awayar Innaro Kunya Mufeeda keyi Jin Suna Tambayanta Ya Jikinta bata magana sai dai Murmushi Suna nan har Dare nan Ishaq da Tahir suka samesa bayan Sun Dubata Suka Wuce gida Gaba ɗayansu bayan ya kawo musu Kayan marmari da Nama gashasshe saboda Mufeeda Ta maida Jikinta.

Haka Suka Din gayi Har Tsawon Kwana Biyar, amma Farida bata taka Asibiti ba sai Ranar da Mufeeda ta cika kwana Shida taji Sauki ma, har ta fara Zuwa Bayi da kanta aikin ya fara Bushewa, Farida kunya taji Yasa ta Shirya taje Asibitin Aikwai Tayi Nadama Sosai Domin ba wanda ma yabi Ta kanta Bata Raina kanta ba sai da Yammah Bayan Tahir ya Shigo Asibitin yana Shigowa Ɗakin Su Basma da Iya da Innaro Suka Fice Suka barshi amma ita sai ma gyara zama Datayi kuma Abun Haushi ko Yaran bata Ɗauka ba Daga Cikin gidansu ta leƙasu Idanuwanta na kawo ƙwallah ganin Tsabar kama da Tahir da yaran Suke ko Mufeeda Da ƙyar ta iya gaisheta ta amsa itama ta kauda kai saboda Nauyi Itako Hararanta kaɗai take Acikin Ranta tana Faɗin "Kin kusa bar min gida makira.."


Bata gama Jin Nadama ba sai Dataga Tahir ya Shigo ko ɓarayin Datake bai kallah Data gaisheshi ma Kansa na gefe ya amsa, amma yana isa kusa da Mufeeda ya saki Fuska yana tambayanta ya Jikinta ita kuma Munafukar tana Sunne kai Numfashinta bai kusa Ɗaukewa ba sai taga ya zauna gefen Gado ya Duƙa yana ma yaran Wasa Mufeeda kuma na kallonsa Tana Murmushi, macen ya Ɗauko yana Faɗin "Yarinyar taso ta ɗauke ki fa Mufee..? Ya faɗa yana kallonta.

Sunne kai tayi Tana Murmushi batace komai ba, sake kallonta yayi yana kallon Jinjiran kafin yace "Kila yau ko gobe ku koma gida, in kun koma sai mu Shawaran Wasu suna zasu saka musu.." Kan Mufeeda na ƙasa tace "Basai kayi Shawara dani ba Daddy Duk Sunan da ka saka musu Dai-dai ne.." Ta faɗa tana Wasa da Hannayenta Kallonta kawai yake yi Tausayinta na ƙara Shiganshi kaɗa kai yayi yana Faɗin "A'ah...zamu magana in kun koma gida kema kina da Hakki yaranki ne.." Bata sake magana ba illah Kallonsa Datake kasan Ido bataso ya Fahimci Tana kallonshi batasan kuwa yana Kallonta ta gefen ido sai dai yayi murmushi kaɗai


Farida Dake Zaune ba tasan Sanda Ta miƙe A fusace ba tana Faɗin "Asirin mutum ya Tonu yace Ƙaddara ne, Kuma ko kunya Yazo yana Abu goɗai goɗai, Wlh mutum bai isa ba Zuwa za'ayi abar min gida Nida Mijina da 'ya'yana, bana son karuwancin Ƙauye.." Ta faɗa tana Ficewa Daga Ɗakin Daga Mufeedan Har Tahir da ido Suka bita Shiko Tahir ko Damuwa da kalamanta baiyi ba Mufeeda ce Idanuwanta Suka cika da Hawaye Tahir bai ce mata komai ba Cikin Ranshi Dariya ce Ke Cinsa na Tunanin yadda Farida zataji in Taji Mufeeda matarsa ce yanzu.

Haka ko akayi Washegari da Safe aka sallami Mufeeda suka koma gida kafin su Dawo Iya da Basma Sun riga sun gyara Ɗakin na Mufeeda suna Dawowa nan suka Sauketa ita da 'ya'yanta Aranar kuma sai ga Ashe da Tawagarta ita da Laila da Muda tazo da kayan Wanka Goggo Abu ta bata Sakon ta kawo Itama Data Ɗauki yaran Sai da tayi ƙwallar Tausayi da Jinjina ma Rabo, Nan ta kwana Washegari kuwa sai ga Baba Hakimi ya iso gidan bai jima da Zuwa ba sai ga Abba da Umma suma sun iso Tunda Farida Taga Haka Jikinta bai bata ba illai kuwa Domin Taro Aka Sake zama kamar na Farko harda Mufeedan Shiko Baba Hakimi na Rike da Jaririn Namiji Abba na Riƙe da macen Tunda Farida Taga an Kirata Gabanta ke Faɗuwa Tana Addu'an Allah yasa Tafiya da Mufeeda Zasu yi ƙauye.

Bayan Buɗe Taro da sallama da Godiya Ga Allah Baba Hakimi ya Fara Magana yana Cewa "Kowa anan yasan Abunda ya Faru Har Aka samu Waɗannan yaran Munyi Tawassali da Sunayen Allah kuma mun yarda da Ƙaddara..Gashi Ashe Rabon bana Ɗaya bane Rabon Har na 'ya'ya Biyu ne Hakan Kaɗai ya isa kowa yagane Ƙudurar Allah ne.." Kowa ya gyaɗa kai banda Farida dake kallon kowa ɗai ɗai.

Cikin Dattako Hakimi ya Cigaba da Faɗin "Magana Ɗaya zanyi Zuwa biyu dama Abunda Ya kawoni kenan, na Farko nazo ne naga Ƙaruwar Da aka samu na Biyu kuma na gabatar muku da Hukuncin Dana yanke ko nace Wanda na Zartar nasan Wasun ku sun sani kamar Kai Tahir da Ke Innaro Tare Da Aisha, toh ba wata Magana bace Illah Aranar da yarinyar ta sauka Attahiru na Kirana banyi ƙasa a Gwiwa ba na Biya Sadaki aka Ɗaura musu Aure..." Kowa maganar bata Razana Shi ba Umma da Abba da Iya Cikin Farin ciki Suke Faɗin "Masha Allah hakan yayi Dai dai.

Farida ko Kamar Saukan Aradu Haka Taji mganar Arzane ta miƙe Hannnunta Bisa Ƙirjinta tana Faɗin "Aure...? Mijin nawa kuka Aura mata kanbura uba..." Ta faɗa Tana girgiza jiki, Tahir Da yaji kamar Ta Tsikara mai allura na Zagin Data ƙunduma kafin ya Ɗauki mataki Umma ta miƙe ta Sharara mata mari tana Faɗin "Kinci Ubanki Farida Baban Mijin naki kike cema Kan Bura uba Saboda baki da Tarbiya..?" Kuka Farida ta Fashe Dashi Ta Duƙe tana Faɗin "Wayyo Allah na na Shiga uku ni Farida Ina zan saka kaina kowa baya sona." Umma ta Ɗuma mata Dundu Tana Faɗin "Eh ɗin ba'a sonki ɗin Uban waye zai soki Kina da Mugun Hali Tir Dake Farida iliminki bai miki amfani ba.." Kuka Farida take kamar Ranta Zai Fita kowa A falon yaji Daɗin Hukuncin Umma Barin ma Ashe da Haushin Farida ya cika mata Ciki Abba ko Kunyace Ta Hanashi Magana Shiko Baba Hakimi mamakin Rashin ɗa'ar Farida ne ya kamashi.

Basma da Bassam Dake gefe ko Ajikinsu basu damu da Kukan Da Farida keyi ba sai ma murnan Da Suke Daddynsu ya auri Mufeeda Zasu Dinga ganin Twince dama Fargabansu kar a ɗauke musu su suna sonsu sosai kuma suna son zama da ita.

Mufeeda kuwa kanta na Duƙe Tana Share hawaye Wai Abun Mamaki itace matar Daddy, Lalle Allah mai yarda yaso amma Maganar gaskiya ba' ajinta bane ya Fita komai da komai, Ta Daɗe tana Fatan Allah ya bata Miji Irin Daddy koda bai kaisa ba koda Rabinsa ne sai gashi shi ɗin Allah ya mallaka mata, Babu Abunda Zatama su Baba Hakimi sai godiya Domin Sun inganta Rayuwarta.

Hakimi ne ya Kaɗa kai yana Faɗin "Banzaci Haka Daga gareki ba Farida..Assha Abun bai min Daɗi ba..Karki manta Mufeeda yanzu amana take garemu, Tun mahaifiyarta na Raye take ƙarƙashin Ikon mu kuma in bai Aureta ba Alhalin Shi ya ɓata mata Rayuwa Wa kikeso ta Aura ga 'ya'ya baki Tunanin Watarana agoranta musu..? Saboda Haka Tahir shine Rufin Asirin Mufeeda Itama Shine Rufin Asirinta ina Fatan zaku zauna lafiya da Junanku Ku Rungumi ƙaddaranku Tunda Haka Allah ya Tsara muku.." Ko ɗago kai Farida batayi ba sai Gunjin kuka take Baba Hakimi bai Damu ba Illah maida kallansa Da yayi kan Mufeeda yana Faɗin "Kiyi Haƙuri Mufeeda kiyi ma Mijinki biyayyah kuma ki kula da 'ya'yanki na Tabbata Attahiru bazai barki kiyi Kukan Maraici ba.." Mufeeda kanta na ƙasa Tana Share Ƙwallah tace "Bakomai Ranka ya Daɗe...Bani da Bakin da zan mika godiyata zuwa gareku..Tun Mahaifiyata nada Rai kuke Jin ƙaina kuna Wahala dani, Daddy ya ingata Rayuwata ya Wahala dani ya Tarbiyantar dani kamar 'yar daya Haifa na yarda Ƙaddara ne ya Faɗa mana Babu Abunda zan ce muku Sai Fatan Gamawa da Duniya lafiya, Allah ya saka muku da Gidan Aljannah Firdausi.." Ta faɗa tana kuka Sosai kowa Afalon sai da kalaman Mufeesda ya Sakashi kwallah Shi kanshi kafeta da Ido yayi yana Jinjina ma Kaifin Tunanin Mufeeda Kukan kuwa kara Narkamai da Zuciya yake.


Baba Hakimi ya Jinjina kai yana Faɗin "Ameen Ameen...Allah yayi muku albarka...Allah ya albarkaci Aurenku ya kuma baku zaman lafiya.." Yake Faɗa yana Share Siririyar ƙwallar Data Zubo mai, Abba ne yayi gyaran Murya yana Faɗin "Masha Allah...Allah ya bada zaman lafiya Haƙiƙa Mansur kayi Tunani mai kyau Allah ya sanya alheri.."

Kowa ya amsa da Ameen Baba Hakimi ne ya kalli Tahir yana Faɗin "Ka sanya musu suna..?" Kai ya gyaɗa kafin yace "Eh jiya da Daddare nayi ma Namijin Huɗuba da Sunanka macen kuma na mata Huɗuba da Sunan mahaifiyar Mufeeda.." Kowa ya Washe baki yana Faɗin Masha Allah Mufeeda kuwa Ɗagowa tayi tana kallon Tahir Lokaci Ɗaya Tana Kuka tana Dariyar Farin ciki Shima Murmushin ya sakar mata.

Baba Hakimi yace "Kai...kai Naji Daɗi sosai nagode..Allah ya Raya Mansur da Hulairatu.." Kowa ya karɓa da Ameen kafin ya cigaba da Faɗin "In zaku yi taron Sunanku Ku haɗashi duka da Tarewar Mufeeda Tunda Duka gida ne, Bana son Bidi'a Komai kuyi shi Lokaci Ɗaya.." Ashe tace "Insha Allahu Baba Dama munyi magana da Yaya Tahir In Sati ya Zagayo za'a Yi Taron Suna sai A haɗa da Tarewarsa Allah ya basu zaman lafiya.."


Ta faɗa tana makama Farida Harara Wacce tabar kuka sai ajiyar Zuciya, babu wanda ma ya ƙara bi takan Farida aka Rufe Taro da Addu'a Baba Hakimi ya miƙama Innaro Takawaranshi Shi kuma Abba ya miƙawa Iya mai sunan Inna Fulera suka Fita Waje, Farida kuwa Umma ta jata ɗaki ta Zaunar da Ita tana Faɗin "Farida..Farida.Farida..!

Ta faɗa tana kallonta Cikin Muryan Ɓacin Rai tace "Farida Sau nawa na kiraki..?" Ta faɗa tana Murɗe mata kunne Cikin Hawaye tace "Sau uku Umma.." Sakin mata kunne Tayi tana Faɗin "Kinga Duk Abunda ya Faru ko..? Kinji kuma kin gani yadda kika zama bora banza a idon Mijinki da 'ya'yanki harda Dangin Mijinki...ko..?" Kai Farida Ta gyaɗa tana Kuka sosai Umma tace "Toh ya rage naki ki Zauna kima kanki karatun ta natsu In ba Haka ba Wlh Tallahi Tahir zai koreki Daga gidan nan Kina ji kina gani yarinya ƙarama ta ƙwace miki miji Tunda kin zama Sakarya Kina sane yanzu ba Da bane Wlh Tahir bazai ƙara Ɗaukan Abun da ya Ɗauka abaya ba, Ya Rage naki Farida Ki gyara Rayuwarki da Halayyarki in ba Haka ba Wlh Zaki Kwashi Nadaman Dayafi Wanda kike karɓa yanzu, Daga ƙarshe ina Fatan Allah ya Sausauta Zuciyarki ya Kori Sheɗan acikin Rayuwarki." Ta faɗa tana miƙewa kafin tace "Zamu Tafi..Sai an kwana biyu ƙila nazo Ranar Tariyan, Don Allah Farida ki maida komai ba komai ba, ki nemi Gafaran Mijinki ki kuma Rungumi 'ya'yanki Da Mufeeda Ko kimarki ta Dawo don Allah ba domin Halina ba..." Ta faɗa Tana Haɗa Hannuwanta Waje Ɗaya.

Farida ta miƙe ta Rungume Umma tana kuka take Faɗin "Insha Allahu Ummah naji maganarki...Nayi miki alƙawarin Zan Chanza Halina Umma zan Nemi gafaran Tahir dashi da Mufeeda Umma, Na gane kuma na Fahimta Duk Abunda ya Faru laifina ne.." Rungumeta Umma Tayi tana Bubbuga bayanta take Faɗin "Naji Daɗin Haka Allah yayi miki albarka.."

Ta faɗa tana Share mata ƙwallah, Har Falo ta Rakota Ta Shiga wajensu Innaro ta musu sallama ta Fice Haraban gidan inda Abba ke Jiranta Daga nan suka ma Tahir sallama suka Tafi, Baba Hakimi ko Tuni Garzali ya Miƙa Dashi Farida kuwa ɗaki ta koma tana kuka Cikin Zuciyarta tana Fatan Allah ya bata ƙarfin Gwiwan Gyara Rayuwarta.






*Anitha...*
*Aisha Alto..*
*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Alkaluman:*✍️

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty)*💕


_Don't Forget to Follow us On Wattpad: Janafnancy13 or Aisha Alto Alto_

_*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_


*BABI NA ASHIRIN DA BIYU*



_Assalamu Alaikum...Ina masoyanmu na nesa Dana kusa..Ku marmatso ga dama ta samu Kuna Buƙatar ku kece raini cikin Flat Shoes masu kyau da Tsari...Toh ga dama ta samu zaku samesu acikin Rahusa mai Sauƙi...Gamai Buƙatar Siyan Ɗaya ko Sari Zai iya Tuntuɓarmu ta wannan Nombobin kamar Haka 09069067488 ko kuma 08147672049 Mu na Maraba da masu siyan Ɗaya ko Sari zaku samesu kan Rahusa mai Sauƙi...Sai kunzo..Siyan Nagari mai da kuɗi gida...mai kasuwa kuma Shi ke da Riba..._

Sai da Farida taci uban kukanta ta gode Allah, sannan ta share hawayenta ta miƙe jiki a sanyaye ta shiga toilet tayo wanka ta fito ko mai bata tsaya shafawa ba ta zira doguwar rigar atamfa a jikinta ta zauna a bakin gado ta zabga tagumi ta tsurawa guri guda idanu tana saƙe saƙe a zuciyarta.

Bayan sallar Isha'i Tahir ya shigo gidan, tana jin motsin shigowarsa ta miƙe a sanyaye ta ɗauki hijabinta ta fice ta nufi ɗakinsa, yana ƙoƙarin shiga toilet ta shigo, kallo ɗaya yayi mata kawai ya ɗauke kansa gefe ya buɗe ƙofar toilet ɗin zai shige abinsa, da sauri ta isa gabansa ta riƙo hannunsa ƙwallah na taruwa a cikin idanunta ta marairaice gwanin tausayi tace "Don Allah don sonka da Annabin rahama kayi haƙuri kazo muje ɗakin Mufeeda...Akwai maganar sa nakeso nayi daku ne dukkanku...Don girman Allah Abban Basma kar kace a'a..." Ta faɗa da magiya ƙwallah na gangarowa daga cikin idanunta suna zubowa kan fuskarta, tsam yayi kawai ya tsura mata ido yana kallonta kamar ba zai je ba, can sai ya janye hannunsa a nata ya raɓa ta gefenta ya nufi ƙofa, da sauri tabi bayansa suka fice suka nufi ɗakin Mufeeda.

Suna shiga suka iske su Innaro da Iya dasu Basma da Bassam a ɗakin tare da Mufeedan suna hira, a hankali ta taka ta shiga tsakiyar ɗakin ta tsaya agaban Tahir daya tsaya ya zuba mata ido yana kallonta yayinda gaba ɗaya su Iya da Innaro dasu Basma suma suka zuba mata ido suna kallonta, a hankali ta durƙusa a gaban Tahir ta zube gwiwoyinta a ƙasa hawaye na zubo mata ta duƙar da kai cikin rawar murya tace "Don Allah don Annabi don girman Allah...Kayi haƙuri ka yafe min na tuba..Ka yafe min duka laifin dana aikata, bazan sake ba, na yarda nayi kuskure kuma zan gyara halayena..." Ta faɗa tare da fashewa da kuka, a hankali yace "Na yafe miki...Allah ya yafe mana baki ɗaya.." Wani sanyin daɗi taji ya ziyarci zuciyarta har sai da ta saki ƙaramin murmushi ta juya tana share hawayen fuskarta ta matsa gaban Mufeeda dake zaune ta duƙar da kanta tana wasa da farcenta, a hankali Farida ta riƙo hannunta tana kallon cikin idanunta take faɗin "Nasan nayi miki abubuwa da dama waɗanda bazasu lissafu ba

Please Login or Register in order to submit comment