Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata da maganar tana dakatar dashi, saboda dalilinta na kada azo ayi abunda zai lalata zumuncinsu, abun na damun Tahir amma haƙurinsa da kuma kawaicinsa yasa ba'a gane halin dayake ciki banda abokinshi kuma amininshi Ishaq.


Wannan kenan.


******

*Kano*

_Tarauni Gra_


Ƙudundune take a cikin lallausan bargo tana sharar barcinta hankalinta kwance Umma ce ta shigo cikin bedroom ɗin tana bin Faridan da kallo lokaci ɗaya tana duba agogon bangon daya ƙawata bedroom d'in ƙarfe 12 daidai kai ta girgiza kafin ta ƙarasa kusa da Farida gefenta ta zauna tana ƙara gyara zaman doguwar rigar leshin dake jikinta matashiyar dattijuwa ce fara mai yalwar fara'a kallo ɗaya zaka mata ka fahimci hutu da jin daɗi sun zauna mata fuskarta kuwa ɗauke da kwalliyarta don Hajiya Aliya bata yarda da zama haka ko kuma girma ya cuceta ba a'a tafi kowa kula da mijinta da tattalinshi, inda ace Farida tana lura da yanayin rayuwar iyayen nata da har abada Tahir bai taɓa complain akanta ba.


Bargon ta yaye kafin ta fara buga ƙafarta tana faɗin "Farida...Ke Farida..." Miƙa tayi tana wani ƙara narkewa bargon take ƙoƙarin ƙara ja, da sauri Umma ta fizge tana faɗin "Wai miye haka..? Tun jiya da kika iso kike kwance kina wannan barcin, bazaki tashi kiyi ƙoƙarin komawa gidanki ba baki tunanin wani hali mijinki ke ciki da 'ya'yanki balle ma ki riƙa tuna ƙaramarsu Naila mai shan nono..."

Ta fada cikin damuwa, miƙa Farida tayi tana turo baki kafin ta miƙe da ƙyar tana gyara gashin kanta wanda duk ya baje saboda barci, fuska ta yamutsa kafin tace "Toh Umma me zai samesu..? Lafiyansu ƙalau su fa, Basma ba yara bane, Tahir ma haka Naila kuma Mufeeda na kula da ita, in ma ta tafi makaranta iya na gida zata kula da ita.." Ta faɗa tana zuro ƙafarta ƙasa, kallonta Umma tayi kafin ta dafa kafaɗarta tana faɗin "Toh naji tashi dai ki yi wanka ki shirya ki fito ki karya ki yi haraman tafiya kinji Faridata..?" Ta faɗa da sigar lallashi da lalama, miƙewa Farida tayi bayan ta zura wani takalmi mai taushi tace "Umma ina Abba..?

Miƙewa itama tayi tana faɗin "Abbanki ya fita tun safe yana da baƙi, amma ya bar sallahu direba ya tuƙa ki zuwa Kaduna yace bayason kina doguwar tafiya ke kaɗai.." Murmushi ta saki kafin tace "Abbana kenan toh me zai sameni nifa ko achan Kaduna Tahir baya tuƙani duk inda zani da motata nake zuwa har Ɗanbatta in kinga direba ya tuƙamu tare ƙila tafiyar tazo ɗaya ne.." Murmushi Umma tayi kafin tace "Hakane, toh kindai ji sakonsa ko..? Toh kiyi maza ki shirya ki fito.." ta faɗa tana kama hanyar ficewa, ƙara tura baki Farida tayi kafin tace "Kai Umma sai wani koro na kikeyi.." Ta faɗa tana tura ƙofar toilet Umma bata ba zancenta muhimmamci ba tace "Eh saboda baki da gatan daya wuce gidan mijinki da 'ya'yanki.." Faridar na jinta daga bayi sai ma ta kyaɓe baki don ita basu dameta ba gani take da ƙafarsu da lafiyansu sai ta zauna ta ƙoƙarin ƙare rayuwarta akansu.


Sai da Farida ta shafe wajen awa ɗaya kana ta fito daga cikin bedroom ɗinta na gidan iyayenta, sanye da wata irin shadda Gezner mai ruwan brown ɗinkin doguwar riga, sai ɗaurin Maryam Babangida data cukashi, fuskarta ba kwalliya amma kuma kallon farko zaka mata ka fahimci bata da wata damuwa, vail ne yafe akanta sai ƙaramar jakarta Umma ta tarar akan dining tana breakfast cikin yanga ta ƙarasa itama taja kujera ta zauna tea kad'ai tasha sai ferfesun kayan cikin ta miƙe tana share bakinta da tissue, kallonta Umma tayi kafin tace "Don Allah Farida ki dinga zama agidanki ba don niba sai don ki girmama darajan aure ki kuma girmama haƙurin mijinki akanki plz.."

Rausayar dakai tayi kafin tace "Umma kenan Tahir ya gama shanye ku kuma, kamar yadda ya gama da iyayenshi, shikenan kuma ni ban san ciwon kaina ba Umma nafa girma nima daidai gwargwado na mallaki hankalin kaina ai nasan me nakeyi, bikin fa ƙanwar Beauty akayi fa Umma kuma kinsan yadda muke da Beauty tun muna makaranta, kawai shegen ƙorafin shi ne yayi yawa..." Ta faɗa tana ɓata fuska kafin ta wuce ta koma cikin bedroom ɗinta ta ɗauko ƙaramar trolley ɗinta ta fito tana faɗin "Umma zan tafi sai munyi waya.."

Umma ta bita har waje inda direba ke jiranta trolley d'in direban ya karɓa ya saka cikin wata baƙar Venz ɗin Farida, kafin ya buɗe mata gidan baya sai da ta shiga kana ta leƙa tana fadin "Umma zan bashi kuɗi ya shiga motar haya in mun isa, ki gaida Abba..." Kai Umma ta gyada tana faɗin "Allah ya kiyaye hanya kar dai naji kin sake fita har zuwa nan da sati biyu Allah kuwa.." Dariya Farida ta saki har haƙorin Makkanta sai da ya bayyana kallonta Umma tayi kafin tace "Kinji ni ko baki ji ba..?"

Kai ta gyaɗa kawai batayi magana ba amma acikin ranta tana tunanin irin shagalin da suke dashi ranar sati anan Kaduna, ƙanin Bilkisu zai yi aure dole suje su raƙashe, har motarsu ta fice daga haraban gidan Umma na ɗaga musu hannu ita kuma Farida sai ta ƙara gyara zama ta jingina kanta jikin kujera ta fito da wayarta ta fara latsawa tana sakin murmushi lokacin data shiga WattsApp, inda taga group ɗinsu na Classes Bbys na waɗanɗa sukayi makaranta tare ya cika da massagea tasan ƙila maganar yadda bikin ƙanin Bilkisu zai gudana ne jiki na rawa ta shiga ta fara bin Chat ɗin cike da farin ciki.






*Aisha Alto*
*Shakira*
*NANNY...!*
     (Mai Reno..)

*Alƙaluman:✍🏻*

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR (Janafty*💕

*Wattpad: Janafnancy13 or Aisha Alto Alto*

*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI*💔
*KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM*💘

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

        *BABI NA BIYAR*

Ƙarfe 3:30pm. Suka shigo garin Kaduna direct suka nufi Unguwar Rimi GRA suna zuwa maigadi ya buɗe tangamemen gate ɗin gidan direba ya sulala motar ciki ya yi parking ya fito da sauri ya buɗewa Farida ta ziro ƙafafuwanta waje sannan ta fito riƙe da wayarta da ƙaramar jaka a hannunta ta buɗe jakar ta ɗebo kuɗi ta miƙa masa "Gashi kaje tasha ka shiga motar haya ka koma gida. Allah ya tsare." Cike da ladabi ya karɓa yana mata godiya, hannu kawai ta ɗaga masa ta juya ta ɗauki ɗan ƙaramin akwatinta ta shige cikin gidan, direban ya juya shima ya fice daga gidan.

Falon tsit yake babu kowa a ciki da alamu yara basu riga sun dawo daga makaranta ba, a gajiye take dan haka bata bi takan komai ba ta nufi ɗakinta, tana gab da shiga ɗakinta ta tsinkayo muryar Iya cike da murna tana faɗin "Sannu da zuwa Hajiya, ashe kece? Ina kichin zan haɗawa Naila madararta na jiyo motsin shigowa..sannu da dawowa." Iya ta faɗa fuskarta cike da fara'a tana tahowa inda Farida take tsaye da Naila riƙe a hannunta tana murmushi.
Murmushin itama Faridan tayi ta aje ɗan akwatin hannunta ta miƙa hannu ta karɓi Naila ta ɗagata sama ta sumbaci goshinta ta shafa kanta sannan ta miƙawa Iya ita ta ɗauki akwatinta tace "Sannunku da gida Iya." Ta faɗa kawai tare da shigewa ɗakinta, turus iya ta tsaya tana bin bayanta da kallo kafin ta girgiza kai kawai ta juya ta koma kichin dan cigaba da abinda take yi, dan in dai halin Farida ne na nuna halin ko in kula da 'ya'yanta da duk wani abun daya shafi gidan aurenta yaci ace zuwa yanzu duk sun saba dashi, bai kamata a kullum ya zama wani sabon abu ko baƙon abu a gurinsu ba.
Kwana da kwanaki bata gida bata tare da 'ya'yanta da mijinta ga yarinya ƙarama mai shan nono wacce ko yayeta bata yi ba amma ta dawo ko ta tsaya ta tambayi yanda suke balle ta ji ina suke da bata samesu a gida ba, gashi ko ƙaramar 'yarta mai shan nonon ma bata wani damu da ita ba ko ta nuna kulawarta a kanta ba, shiyasa itama 'yar ko murna da ganin uwar tata bata yi ba sai kallonta kawai da take kamar wata baƙuwa.

Tana shiga bedroom ɗinta ta zube wayarta da jakarta ta tuɓe kayan jikinta ta jawo tawul ta ɗaura ta faɗa toilet, bata wani daɗe sosai ba ta watsa ruwa ta fito ta faɗa gado tai kwanciyarta abinta saboda wani irin bacci take ji duk ta gaji jikinta sai ciwo yake mata.

Ƙarfe 4pm. Bassam da Basma suka dawo daga makaranta, suna shigowa suka tarda Iya na bawa Naila madara a falo a gajiye duk suka zube saman kujera suna maida numfashi, Iya ta ɗago tana kallonsu da murmushi akan fuskarta tace "Sannunku da dawowa ya makarantan?" Basma na turo baki tace "Ba daɗi Iya, yau munsha wuya ga rana ga zafi." Dariya Iya tayi tana kallonta tace "To Mummy dai ta dawo..." Da murna duk suka miƙe suka kwasa da gudu suka nufi ɗakinta tana kwance suka shigo cike da farin cikin ganin mahaifiyarsu suka faɗa kanta da gudu suna murna suke faɗin "Oyoyo Mummy..!"
haɗe rai tayi ta yatsine fuskarta ta tashi zaune haɗe da janyesu a jikinta ta ɗaure fuska tace "Please kuje waje ina so zan huta ne, idan na tashi zan nemeku.." ta faɗa tare da janye hannunta ana Basma tana nuna musu ƙofar fita, a sanyaye yaran ke kallonta kafin su juya a hankali suka fice daga ɗakin suna waigenta, ƙaramin tsaki taja ba tare da tunanin komai ba ta gyara kwanciyarta abinta ta lumshe idonta tana jira bacci ya ɗauketa.

Yanda Iya taga sun fito daga ɗakin jikinsu a sanyaye yasa ta miƙe da Naila dake bacci a hannunta ta nufesu ta kamo hannun Basma tana ɗan murmushi tace "Kuje ku cire kayan makarantan kuyi wanka sai ku fito ku ci abinci, kafin nan Mufeeda ta dawo itama sai ku shirya ku wuce islamiyya.." gyaɗa mata kai suka yi kafin kowa ya nufi ɗakinsa, itama ta juya ta nufi ɗakin Mufeeda ta kwantar da Naila ta fito.

Sai da sukayi wanka sukayi sallar La'asar sannan suka fito falo cikin shirinsu na tafiya islamiyya, lokacin itama Mufeeda ta dawo har tayi wanka ta saka uniform irin nasu tayi shirin islamiyya.
A dinning suka haɗu suka ci abinci kafin da suka gama suka ɗauki jakunkunansu suka fice Garzali ya kwashesu zuwa islamiyya.

Ƙarfe 6:20pm. Suka dawo suna shiga falon kowa ya nufi hanyar ɗakinsa.
Suna shiga falon motar Tahir na shigowa cikin gidan dawowarsa kenan, bayan yayi parking ya buɗe motar ya ɗauki wayoyinsa da rigar suit ɗinsa daya cire ta saman yabar ta cikin a jikinsa ya kulle motar ya nufi cikin gidan da takunsa mai cike da kuzari da izza ya shiga falon da sallama, da gudu Basma da Bassam da suka buɗe ɗakunansu zasu shiga suka rugo gurinsa suka faɗa jikinsa tare da ƙanƙamesa suna masa barka da zuwa, yana murmushi ya riƙe hannun Basma yayinda shi kuma Bassam ya karɓi rigarsa da makullin mota ya riƙe fuskarsa cike da fara'a da murna yace "Daddy Mummy ta dawo tana ɗakinta.." ɗif Tahir yayi ya gimtse fuskarsa yay kamar baiji abunda Bassam yake cewa ba, kallon juna suka yi da Basma kafin Bassam ya ƙara kallonsa yace "Daddy Mummy fa ta dawo.." karɓar rigarsa da makullin motarsa kawai yayi a hannunsa yace "Maza kuje ɗaki ku cire uniform ku canza kaya, sai kuyi alwala ka fito muje masallaci an kusa kiran sallah." Yana faɗa ya saki hannun Basma suka nufi ɗakunansu shima ya juya ya nufi bedroom ɗinsa yana jin wani takaici da ɓacin rai a zuciyarsa.

Yana shiga ya tuɓe kayan jikinsa ya shige toilet a gurguje ya watso ruwa ya haɗo da alwala ya fito ya zira jallabiya ya fesa turare ya ɗauki casbaha ya fice daga ɗakin yana fita ya samu Bassam da Mufeeda zaune a falo, tana ganinsa ta miƙe ta ɗan rusuna ta gaishesa ya amsa yana kallonta kafin ya kama hannun Bassam suka fice zuwa masallaci itama Mufeeda ta nufi ɗakinta don gabatar da sallar Magriba da ake kira.

  Basu dawo ba sai da suka sallaci sallar Isha'i kana wajen after 8 suka shigo gidan, suna shigowa suka iske Mufeeda da Basma suna taya Iya jera warmers akan dinining, kallo ɗaya yayi musu sanda Mufeeda da Basma suke mishi sannu da suwa kai ya gyaɗa ba tare da yayi magana ba ya fara haura step Mufeeda ta bishi da kallo asace tana so ta karanci yanayinsa, karaf ya waigo suka haɗa ido gabanta ne ya faɗi tayi saurin sadda kai jikinta ya fara rawa ganin yadda ya sakar mata ido Basma ce ta lura da tsayuwarshi idonshi na kallon Mufeeda amma bai bari kowa ya fahimta ba cikin kulawa Basma tace "Daddy plz kai da Momy ku fito muyi taking dinner tare tunda all of u yau kuna gida.."

Bassam dake zaune kan ɗaya daga cikin kujerun falon tun bayan shigowarsu shida Tahir yace "Eh mana Daddy plz...We miss u.." Ya faɗa cikin muryan taausayi wani haushin Farida ya ƙara kamasa, amma bai nuna ba sai ma ya murmusa yana fadin "Mufee Naila tayi barci ne...?" Kanta na ƙasa tace "Eh Daddy tun ɗazu dana bata madararta na goyata tayi barci.." Gyaɗa kai yayi kafin ya juya yana faɗin "Gud.." Bai ko ƙara kallon su Basma ba waɗanda suka sakamai ido ganin yana neman haurawa sama ne yasa Basma ta ɗaga murya tana faɗin "Daddy...." Juyowa yayi cike da wani fushi yana kallonta baya taja ganin yadda fuskarsa ta chanza cikin rawar murya tace "Am Sorry Daddy...I didn't mean to hurt u..." Ta faɗa kamar zatayi kuka Mufeeda ma dake gefe yanayin Tahir ɗin yasakata sanyin jiki balle Bassam dayayi tsam a saman kujera yana bin Daddynsu da kallo a tsume.

Ganin yadda duk sukayi ne yasa tausayinsu ya kamashi sai ya ƙaƙalo murmushin dole yana faɗin "It's Ok, don't worry kuyi taking dinner ɗinku me am ok, na biya wajen Ishaq naci abinci ok..?" A sanyaye Basma ta ɗaga kai kafin tace "What abount Momy...?" Atsume ya kalleta kafin ya bi ƙofar bedroom ɗin Faridan da kallo daga inda yake yana jiyo sautin dariyarta da alamu waya take bai  bama takaichinsa muhimmanci ba yace akausashe "Basma kuje kuci abincinku ku shiga ciki ku kwanta u know tomorrow akwai school ko..?" Gyaɗa kai tayi kafin yace "Oya bana son wata magana kuma, ita Momyntaku ai ta fiku sanin cikinta in tana buƙata zata fito taci, saboda haka kuci abincinku kowannenku ya tafi ɗakinsa ya kwanta and don't forget kowannenku yayi Assigment ɗinsa Basma Bassam Mufeeda am i clear..?" Ya faɗa cikin bada umarni.

Gaba ɗayansu suka amsa da yes Daddy, gyaɗa kai yayi kafin ya juya ya ƙarashe hayewa steps d'in ko kallon ɗakin Farida baiyi ba ya tura ƙofar ɗakinshi ya shiga yana sakin siririyar ajiyar zuciya yana ƙoƙarin danne fushinsa yana ƙara tunanin wani irin raini Farida tamai da zata fi kwana biyar bata gida kuma ta dawo gidan bayanan, bayan ya dawo kuma ta kasa fitowa ko sannu da zuwa tamai alhalin yasan ta ji dawowarshi? Tsaki yaja yana ƙoƙarin zama gefen gadonshi lokaci ɗaya zuciyarsa na zafi duk da haƙurinsa wannan karon Farida ta ƙureshi, bai ƙara ƙoƙarin saka ɓacin ranta a cikin ranshi ba ya cire jallabiyar jikinsa ya haye gadonsa daga shi sai dogon wando baƙi duka zatinsa da kwantaccen baƙin gashin ƙirjinsa ya bayyana ƙaramin Qur'aninsa ya ɗauka ya buɗe ya fara karantawa cikin natsuwa lokaci ɗaya ya nemi ɓacin ran Farida ya rasa duk ya gushe acikin ranshi, a hankali ya cigaba da karatunsa cikin jin daɗi da shaukin abun.

Suko su Bassam duk da zuciyarsu ba daɗi da yanayin halayen Momynsu da Daddynsu hakan bai hanasu zama suci abinci ba hatta Mufeedan itama jikinta yayi sanyi, su Basma kuwa ba Momynsu tafi damunsu ba a'a  Daddynsu wanda sun lura indai Farida na gidan bashi da walwala koda yaushe cikin ɓata mishi rai take, kuma abunda yaran suka lura dashi yadda uwar tasu bata damu da rayuwarsu ba hakama bata damu dana Daddynsu ba, abun baya musu daɗi domin sun fi shaƙuwa dashi sosai akanta, shine yake zama dasu ya kuma jasu ajikinshi yaji damuwarsu kuma shine ginshiƙin tarbiyarsu shiyasa in suka ganshi cikin damuwa suke shiga damuwa shiyasa wani lokacin sunfi sakewa in Farida bata gidan haka dai kowa ya tsakuri abincin ya tashi yau Iyar ma datake jansu da hiran ban dariya tunda ta fara taga sunƙi sakin fuska sai ta ƙyalesu Bassam ne ya fara tashi sai Basma dukkansu ba wanda suka ma magana kowanne ya nufi ɗakinsa domin cika umarnin mahaifinsu. Mufeeda bata ci abincin sosai ba itama ta tashi Iya bata damu ba domin indai yanayin gidan Tahir ne ya riga ya zame ma kowa jiki, yau daɗi gobe akasin haka, itama tattara komai tayi zuwa kichen kafin ta shige ɗakinta, hakama Mufeeda ta shige ɗakinta ta kulle wanka tayi kafin ta saka kayan barcinta ta kwanta kusa da Naila bayan ta cika umarnin Tahir tayi Assigiment ɗinta ta rungume Naila a ranta tana tausayin Tahir tana kuma ganin Farida a muguwa tana muzguna ma mutum mai haƙuri da kawaichi kamar Tahir, wani lokacin kamar tamai ƙwalla takeji domin tun zuwanta gidan ta fahimci Tahir da Farida are different sam basu dace da juna ba, akwai abunda Allah ya tsara ne a tsakaninsu amma zamansu waje ɗaya kwata kwata baiyi ba.

*****

Washegari ƙarfe 7 da wani abu Tahir ya fito daga ɗakinshi cikin shirin fita yau ɗin shigar manyan kaya yayi saboda juma'a ce, wata farar Gezner ce mai maiƙo da yarari ajikinsa ɗinkin matasa ne da samari masu jin kansu wato ɗinkin Muhammed, kansa sanye da hula Zanna Bukar mai kalar blue irin aikin jikin shaddar sai agogon fatar dake hannunsa na kamfanin Rado ne, ƙafarsa sanye da buɗaɗɗen takalmi na fatar damisa.

A kallon farko in kamai zaka fahimci tsantsar zatinsa da haibarsa uwa uba kyau da nasaba ga ƙwarjini, fuskarsa na fitar da annuri amma kuma zuciyarsa tana ɓoye ɓacin ransa daidai lokacin daya fito yana ƙoƙarin gyara zaman hulan kansa sai ga Farida itama ta fito daga cikin bedroom ɗinta suka kusa bangazan juna shi yana sauri ya sauka ƙasa zashi Office suna da baƙi daga Lagos ita kuma ta fito sanye da wata doguwar riga ƙirar Armani baƙa sai wani jan vail data naɗa akanta hankalinta na kan wayarta amma kuma ƙamshin turaranshi shiya sanar da ita Tahir is here.

Cak ta tsaya tana binshi da kallo, shima kallonta yayi amma kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai lokaci ɗaya yana ƙara haɗe ransa itama sai ta kauda kai tana wani basarwa saboda kada ya kawo mata wata mgana cikin dakewa ta furta "Good morning Abban Basma.." Kamar bazai yi magana ba sai da ya raɓata ya fara saukowa daga steps kafin ya amsa da cewa "Morning..." Daga haka bai ƙara mata magana ba ya sauko falo da hanzari inda Mufeeda da Basma da Bassam ke zaune kowanne da uniform ajikinsa suna karyawa, suna ganinshi dukkansu suka miƙe suna faɗin "Good morning Daddy..." Yana sakin murmushi ya ƙaraso yana dafa kan Basma da Bassam harda Mufeedan kafin yace "Morning how are u...?" A tare suka amsa da "We are fine Daddy.."

Fuskarsa na kallon Mufeeda yace "Mufee ya kwanan Naila..?" Tana wasa da gefen hijabinta tace "Ta koma barci Daddy tana tare da Iya.." Gyaɗa kai yayi daidai lokacin da Farida ta ƙaraso falon shi kuma ya juya yana faɗin "Bassam hau sama ka ɗaukomin briefcase ɗina, idan kun shirya kuzo mu ajiyeku kafin mu wuce in kuma yaje ya kaini ne ya dawo toh.." Da sauri Bassam ya miƙe yana faɗin "No Daddy zamu bika.." Ya faɗa yana isa gaban Farida kafin ya ranƙwafa yana gaisheta ta amsa tana shafa kanshi kafin ya nufi upstairs da sauri hakama Basma ta taso ta rungume Farida tana gaisheta Mufeeda dai sai da ta koma ɗaki ta ɗauko ƙatuwar jakarta ta fito kana ta durƙusa tana gaida Farida ta amsa ba yabo ba fallasa Tahir na gefe hannunsa na harɗe kan ƙirjinsa yana kallonta cike da mamaki tana ɗagowa suka haɗa ido sai ta wani ƙara haɗe rai kafin ta koma kan ɗaya daga cikin kujerun falon ta zauna tana wani tamke fuska.

Takaichinta yasa ya fice daga falon har yana jan siririn tsaki da kallo ta bishi kafin tace a fili.. "Fitinanne, nema na kake da fitinarka niko bazan biye maka ba.." Tsaki taja daidai lokacin dasu Bassam ya ƙaraso ɗakinsa ya koma shima ya ɗauko jakarsa suka fito Basma ta rigasu ficewa kafin Mufeeda da Bassam su fice suna ma Faridan sallama ko ɗaga kai batayi ba hannu kawai ta daga musu.

Sai da aka fara kaisu Basma School ɗinsu kafin akai Mufeeda har suka ajiyeta tana satan kallon Tahir tausayinshi na ratsata domin agabanta Farida ta faɗi maganar ɗazu ranta bai mata daɗi ba duk da ƙarancin shekarunta tasan hakan bai dace ba, ranar dukuku ta isa ajinsu duk zuciyarta da ranta ba daɗi Tahir ke cikin ranta tana matuƙar tausayama rayuwar mutum mai nagarta da kamala kamarshi.






*Aisha Alto*
*Anitha..*
*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Alkaluman:*✍️

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty*💕

*Wattpad: Janafnancy13 or Aisha Alto Alto*

_*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_

*BISMILLAHIR RAHAMIR RAHIM*

       *BABI NA SHIDDA*

......Har ya isa Office fuskarshi ba annuri, har suka gama sallamar baƙinsu waɗanda abokan harkarsu ne daga Lagos, office d'in Ishaq suka wuce suna cigaba da tattauna abunda ya shafi kasuwancinsu, suna shiga Tahir ya nufi ɗan ƙaramin fridge d'in dake Office d'in ya buɗe ya ɗauko musu ruwa guda ɗaya bayan ya ɗauko wasu ƙananan kofuna guda biyu kai tsaye bisa kujeran dake fuskartar wacce Ishaq ya zauna shima ya zauna ya ajiye kofunan bisa teburin dake gabansa batare da yace komai ba ya tsiyayama Ishaq ya miƙa mai ya karɓa da murmushi kafin yace "Thanks."

Bai yi magana ba illah murmusawa kawai da yayi kafin shima ya tsiyayama kanshi ya kafa kai yana sha, dukkansu atare ko wannen su ya ajiye kofin ruwan kuma suka sakarma juna murmushi alokaci ɗaya, ajiyar zuciya Tahir ya sauke yana wani lumshe ido kansa ya jingina jikin kujera yana ƙara takure fuska kafin ya sanya hannu yana taɓa naman goshinsa daya tattare, Ishaq na lura dashi ganin yadda yake yamutsa fuskane yasa ya gane akwai matsala sosai.

Gyara zama yayi kafin yace "Uhm..Tahir meke damunka ne..? Tun shigowarka Company na lura baka cikin walwalarka..?" Bai ɗago ba illah sauke hannunshi dayayi yana ƙara lumshe dara daran idanuwansa har Ishaq ya fidda rai da zai yi magana sai chan yaji ya furta.."Kai ma da neman magana kake, a duk duniya ni Tahir ina da wata damuwa ne bayan damuwar Farida..? Bani da ita komai na duniyar nan na mallakeshi Ishaq sa'ar mace tagari ne kaɗai banyi ba, shi kaɗai ne matsalata a yanzu da damuwata Ishaq..wallahi halin Farida ya isheni, na kai maƙura..."

Ishaq ya saki ajiyar zuciya kafin yace "Nasani Tahir buh ya maganar da mukayi dakai last week da kaje Ɗanbatta baka ƙara ma Goggo Abu maganar auren naka bane..?" Sai lokacin Tahir ya miƙe daga kishingiɗan dayayi yana faɗin "Hmmm bari kawai Ishaq, narasa me Farida tama Goggo Abu da take gudun ɓacin ranta, amma ni take ƙoƙarin danne min hakki wallahi ko wannan zuwan taƙi kuma tace zata saɓamin in na sake na tunkari Hakimi da maganar, wai zata ƙara ma Farida magana in sunyi waya.." Tsaki Ishaq yaja kafin yace "Wallahi baji zatayi ba, ai da tana jin magana dataji tasu Alhaji, gaskiya in na samu lokaci zanje ƙauye nama Goggon bayanin za'a cutar dakai kuma Farida bata da asara." Murmushin dayafi kuka ciwo Tahir yayi kafin yace "Kadama ka wahalar da kanka Ishaq, domin Goggo bazata taɓa sauraranka ba daga ƙarshema zatace haɗa baki mukayi na turo mata kai. Kawai nidai yanzu na cire lamarin Farida araina ina ta addu'a amma tabbas Ishaq na kai maƙura nifa mutum ne mai lafiya ba dutse ba ina buƙatar macen da zan dinga samun natsuwa awajenta.." Saurarawa yayi yana maida numfashi cike da ɓacin rai kafin ya cigaba da faɗin "Ko bama haka ba Ishaq ina buƙatar macen da zata kula dani nima, taji dani nima ina so naga ana bani girma amatsayina na namiji, yanzu ka duba kagani Ishaq rainin da Farida tamin har yakai ta tafi tsawon kwana biyar bata agida, amma jiya data dawo basai

Please Login or Register in order to submit comment