Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya Faru ba laifina bane Laifin Farida ne Ita ce Sanadiyar Jefani Cikin Halaka amma Wallahi bayan Matata Farida ban taɓa Keta Gonar da ba Tawa ba sai akan Mufeeda Wacce Ƙaddara ta Hau kanmu.." Ya ƙarashe Faɗa Cikin Muryan Kuka, Miƙewa Aliyu yayi yana Faɗin "Ashsha Kaji ko..? Abu baiyi Daɗi ba.."

Tahir bai bashi Zarafin ƙara magana ba, ya Shiga bashi Labarin irin zaman Wulaƙancin Dayayi da Farida da yadda ta banzatar da Rayuwarsa da Ƙoƙarinsa na ƙara Aure da yadda Goggo Take Dakatar dashi har Zuwa Faruwan komai Ya ƙarashe yana Faɗin "Wallahi Tallahi..Farida Ta Cutar dani Cutar da Allah ne kaɗai zai sakamin, Sai Farida tayi Wata Huɗu bata kalleni A shimfiɗa ba, Ku gayamin Ni Dutse ne ko Gunki da bazan Buƙaci mace ba..?" Ya faɗa lokaci Ɗaya yana Juyo da Fuskarsa Wacce Hawaye suka Wanke mishi ita.

Daga Ishaq Har Aliyu Jikinsu yayi Sanyi Sosai Aliyu ne ya ƙarasa Kusa Dashi ya Dafa Kafaɗarshi yana Faɗin "Cool Down Ka daina Kuka, Haƙiƙa Wannan Abun da ya faru ƙaddara ne ko Kuma nace Darasi ne ga Farida da Goggo, Amma fa maganar gaskiya kana da babban Laifi Tahir na yarda kabar Farida ta Rainaka take yarda taga Dama bayan Kai kake Aurenta aiko Min gatan da iyayenta Suka bata Tunda tabar Gabansu Ta Dawo ƙarƙashin Ikonka ya kamata ka Nuna mata ƙwanjinka na Mulkinka Amatsayinka na Namiji mai Cikakken Iko Agidanshi.. Maganar gaskiya kayi Kuskure.." Ya faɗa yana Murza Kafaɗarsa.

Numfashi Tahir ya Sauke kafin yace "Tabbas maganarka Hakane... Haƙurina da girman Iyayenta Danake gani Da kuma Nasihan Goggo Akaina da Kuma 'ya'yan Dake Tsakanina da Farida yasanya Bana iya Mata Wani abu, In tayi ba Daidai ba Shine Kuskure na barta ta saba da Komai tayi Daidai ne Tabbas nima ina da Laifi ba komai Ake ma Haƙuri ba Gashi Haƙurina yajamin naje na Afkama Marainiyar Allah Daga Ƙarshe na zama Abun YaɗaWar Farida Kamar bamu Haɗa komai da Ita ba, ba komai...Haka Allah ya Tsara min.." Ya faɗa yana Share Hanci kamar Wani yaro.

Kafaɗarsa Aliyu ya Daka kafin yace "Kazama namiji Abokina ka ganni nan bana ma Bilkisu da Wasa Tunda na Lura tana da Rawar kai Ubanta Nakeci tasan Halina ko yanzu ɗin ma ina komawa zan Koro Faridan Dole ta Dawo Tunda bata da Wajen Zuwa..."

Da Sauri Tahir yace "No..no plz ka ƙyaleta Ka barta ta Zauna Da kanta zata Dawo ba sai kamata magana ba ai zataga Abunda saɓanin Shi Suke gaya mata zata ma kanta Faɗa Tun kafin Wani ya mata.." Ishaq yace "Shawara mai kyau Tahir..."

Aliyu ya Saki Hannu yana Faɗin "While Tunda kace Haka zan saka musu ido.. Amma True Tak, Yarinyar nan ta Haihu ka Aureta Wallahi Sweet Sixtyn suna da Daɗin Sha'ani, Tuni Farida zata Rena kanta Ta Dawo Tana begenka Lokacin Da ka mata Nisa.." Dariya Ishaq ya saka kafin yace "Shawara mai kyau..Dama Shi ya Chanchanta yayi Wuf da Ita.." Hararanshi Tahir yayi Bai yi Magana ba, Shima Aliyu Dariya yake kafin su Cigaba da Tattauna maganar Tare Suka Fito Sai da Sukayi sallar La'asar Cikin Jam'i kana suka Rako Aliyu ya Hau Motarsa Zuwa gida, su kuma suka koma Office d'in Tahir Ishaq bai Dawo da Maganar ba ganin Tahir ya basar da Zancen ya Ɗauko Lissafinsu suka cigaba dayi amma Cikin Ran Tahir Tsanar Farida ce ke ƙara Ninkuwa in ya Tuna Tana chan tana Yawo Dashi Acikin Duniya kamar babu Igiyan Aurenshi Akanta.


******

*BAYAN SATI ƊAYA*

Lokacin Tuni Har Su Basma Sun koma Makaranta Hadda Itama Mufeedan Don Da Tahir ya nuna kamar Ta Haƙura da Karatun Saboda Gujema idon Mutane sai Ta Fara Share Ƙwallah Shi kuma ƙwallar Mufeeda kamar dalma yake Acikin Ranshi, dole ya barta ta cigaba da Zuwa Makaranta amma bayan yaje yama Shugaban makarantan Bayanin Cewa Mufeeda matar Aure ce, Kuma tana Ɗauke da Juna biyu So School Authority Su kula da Ita, basu Tsaya Tambayan Waye Mijin Ba Illah Suka yarda da maganar Tahir Suka kuma Rubuta Cikin Record Book.

Hatta da Islamiyya ta koma Abunta kamar ba Ita ba, sai dai Tayi Kiɓa Sosai, Ta ƙara Fari ta Cika ta Ko'ina Saboda tana samun Abunda Take so Abincinta Dama Shine Faten Wake, sai ƙosai da Koko sai kayan kwaɗayi Irinsu Goriba, yalo Sai Ice cream Wanda In Mufeeda bata Sha ba kamar Cikin zai ɓare, Shiyasa Tahir kullum zai Dawo sai ya Shigo mata Dashi, Ba laifi Iya na Kula da Ita sosai su Basma ba'a barsu Abaya ba Lokaci kaɗan Mufeedan Ta Saki Ranta sai dai Tunanin Innarta Dayaki barin Ranta.

Ɓangaren Su Goggo Abu kuwa ba Wani Cigaba, Tahir Sau Ɗaya ya Kira Baba Hakimi Awaya Tunda yaji ya fara mai maganan Goggo Abu ya Datse Kiran, Tun daga Ranar ko ya Kirashi baya Ɗauka Dole ya Haƙura sai dai yana Kiran Goggo Akai akai Yana ƙara bata Haƙuri amma ya Ɓoye mata Shima Saboda Ita Baba Hakimi ya Daina ɗaga Wayarsa sai dai ya Dinga Nuna mata ta kwantar da Hankali komai xai Daidaita.

*******

Yana Toilet yana Wanka, Akayi ta Kiran Wayarsa bai ji ba sai da ya gama Wanka ya ɗauro Alwala ya Fito Ɗaure da Towel A ƙungunsa Ƙaramin na Saman kansa yana Tsane Ruwan Jikinsa, Yaji Kiran Wayarsa Cikin Sassarfa ya isa Kusa da Wayar, Abunda ya bashi tsoro ganin Kiran Baba Hakimi, Da Asuban Fari Domin Lokacin Wajen ƙarfe 4:43am ne.

Cikin Firgici Da Tsoro ya ɗaga Kiran yana Faɗin "Salamu Alaikum Baba..?" Ya faɗa Cikin Rawan Murya banji me akace ba Sai dai naji Tahir ya saki Salati yana Faɗin "Innalillahi Wa'inna Alaihirraju'un..Allah ya Jiƙanta da Rahma Allah yasa ta Huta..."

Ya faɗa kafin ya Ɗauke Wayar A kunnensa Cikin Mutuwar Jiki ya Faɗa gefen gado yana Dafe kanshi Ko'ina na Jikinsa na Rawa, lokaci ɗaya Yaji Hawaye Sun Cika mai ido Har Sun Fara gangarowa.





*Shakira*
*Aisha Alto*
*NANNY...!*
      (Mai Reno..)

*Alƙaluman:*✍🏻

*AISHA ALTO💞*
*JAMILA UMAR (Janafty💕*


_Don't Forget to Follow us On Wattpad: Janafnancy13 or Aisha Alto Alto_


*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔*
*KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

      *BABI NA GOMA SHA TAKWAS*

........Ya Daɗe Zaune a gefen Gado yana Dafe da kanshi yana Jimamin Abunda Baba Hakimi ya Sanar Dashi, Tausayin Mufeeda na Ƙara Cika masa Zuciya. Rashin Mahaifiya Akwai Ciwo balle Ita Daba Uwa ba uba..

Ya daɗe Zaune Baisan Iya Adadin Lokacin Daya Ɗiba yana Tunani da Kuma Tausayin Mufeeda ba, Kiran Sallah ya ƙara Jiyowa Daga Masallatan Dake Kusa Dasu Zabura yayi ya Miƙe Lokaci Ɗaya yana Duba agogon Wayarsa yaga 5:10am Da Sauri Ya Nufi Wardrope ɗinshi ya Buɗe ya Ɗauko Wata Jallabiya mai Ruwan Toka ya Zura Hula ya sanya kafin ya Ɗauki Carbin sa ya Fice Daga Ɗakin.

Ƙasa ya Sauko Zuwa Ɗakin Bassam Shi ya kuma Tashi Su Basma, Iya kuma Koda ya Leƙa Ɗakinta Ta tashi sai yace Ta tashi Mufeeda Lokacin Sallah yayi, Daga nan Suka Wuce Masallaci Shida Bassam sai Wajen Bakwai Saura Suka Dawo Suna Shigowa Falon Suka Iske Basma Tsaye da Uniform A jikinta Cikin Girmamawa Ta Duƙa ta gaishe da Tahir, Cikin kallonta yake amsawa yana Faɗin "Ku Saka kayan gida ne Basma Gaba ɗayanmu yau Ɗanbatta zamu.." Tare da Bassam Suka Kalleshi Cikin Murna Suka ce "Da gaske Daddy..?" Kai ya gyaɗa musu alaman Hakane Tsalle Suka Farayi alamar Murna Cikin Dakewa yace "Ku ɗiba kayanku koda Kala Uku uku ne sai bayan Kwana Uku zaku Dawo.." Jin Haka yasa Suka Zura da Gudu Zuwa Ɗakunansu da Kallo ya bisu Acikin Ranshi yana Faɗin Kurucci Dangin Hauka.

Yana Shirin Haurawa Sama Iya ta Fito Daga Kichen ganinshi yasa Ta saki Fuska Tana Faɗin "Ah...Alhaji Barka da Safiya.." Cikin Sanyi ya waigo yana Faɗin "Ina kwana Iya..?" Ta amsa da lafiya lau bai bata Zarafin magana ba yace "Ahm Iya Ki Shirya kayanki ki kuma Saka Mufeeda Ta Shirya Kayanta Ɗanbatta zamu yanzu da Safen nan." Iya ta Ji Zuciyarta ta Tsinke da Sauri Tace "Ɗanbatta kuma Alhaji..? Allah sa lafiya..?"

Shiru yayi kafin yace A hankali.. "Mahaifiyar Mufeeda ce Allah yama Rasuwa Jiya da Daddare yanzu Baba Hakimi ya Kirani yake Faɗa min.." Dafe Kirki Iya Tayi kafin tace "Innalillahi Wa'inna Alaihirraju'un..." Ciwo Tayi Alhaji..?"

Kai ya gyaɗa mata kafin yace "Eh har ta kwanta Asibiti ma, Ki Taimakama Mufeeda Don Allah Iya, Kuma karki Sanar da Ita Domin batasan Halin Da'ake Ciki ba.."Jinjina kai Iya Tayi Tana Faɗin "Allah Sarki Haƙiƙa Mufeeda Tayi Rashi babba..Allah Ya Jiƙan Inna Fulera, Insha Allahu Alhaji yanzu zamu Shirya.." Ta faɗa Cike da Tausayawa.

Gyaɗa mai kai yayi kafin ya Haura sama Ita kuma ta Koma Kichen Ta Cigaba da Soya Dankali, cikin Jimami da Tausayin Mufeeda sai da Ta kammalah Duka Abun karyawan Ta kwaso Zuwa Dininng kana Ta Shiga Ɗakin Mufeeda Ta Isketa Tayi Wanka Har ta shirya Cikin Uniform ɗinta Naila ma Ta mata Wanka Ta Shiryata Cikin Riga da Wando, Tana gefen Gadon Tana Riƙe da Hannun Naila wacce Ke Tata tan Tafiya, cike da Tausayin Mufeeda Iya ta Shigo Ɗakin Tana Faɗin "Mufeeda Ki Cire kayan Makarantar ki saka na gida kuma ki Haɗa kayanki Cikin Akwati Naki dana Naila yanzu Alhaji ke gayamin Ɗanbatta zamu Tafi Dukkanmu sai mun kwana Biyu A chan.."

Da Sauri Mufeeda Ta Ɗago Tana kallon Iya Cikin Fitar Magana tace "Ɗanbatta kuma iiya..? Na Shiga Uku ko Gida Daddy zai maidani..?" Ta faɗa Idanuwanta na Cikowa da Ƙwallah Saurin girgiza kai Iya Tayi Tana Faɗin "Ko Ɗaya inaga dai Hutu Alhaji ya samu yakeso muje chan Muyi Hutun.." Ta faɗa Tana Ƙara Jin Tausayin Mufeedan, jin Haka ya saka Mufeeda Ta Washe baki Tana Faɗin "Da gaske Iya..? Yau zan kwana A ƙirjin Innata.." Ta faɗa Cikin Farin ciki Lokaci Ɗaya Tana Ijiye Naila kan gado ta isa Wajen Akwatinta ta Ɗauko, Iya Fita tayi Tana Sharan Ƙwallar Tausayin Mufeeda.

Shiko Tahir kafin ya Shirya sai da ya Kira Ishaq ya Sanar Dashi Cikin Tausayawa Ishaq yace Ya Jirashi gashinan Zuwa Su Tafi Tare Haka ko Akayi, ƙarfe 8am da 'yan Mintina Gaba daya Sun gama Shirinsu Sun karya Tahir ne ma bai Karya ba, Lokacin da Suka Fito sai ga Ishaq ya ƙaraso, musabaha Sukayi da Tahir Su Basma kuma Suka Ranƙwafa Suna gaisheshi ya amsa yana Shafa kansu, Nan da nan Suka Shiga Mota bayan Garzali ya Zuba kayansu Cikin Booth d'in Motar, Harda Tahir Shima da Jakar kayansa, Cikin gida kuwa Iya sai da ta kashe komai na Wuta Kana Suka Fito, Motar Garzali Su Iya da Basma da Bassam da Mufeeda Suka Shiga Tahir  wanda ya ke Riƙe da Naila, da ishaq suka Shiga Motar Ishaq ɗin, Tara da Wani Abu na Safe Suka Ɗauki Hanya bayan Tahir ya Kira Baba Hakimi yace Atsahirta da Jana'izar Inna Fuleran Har su Iso ko Mufeeda ta samu ganin gawar Mahaifiyarta Suna Tafe Suna Janjanta Abun Shida Ishaq, Lokaci Ɗaya kuma suna Gudu ba Sosai ba.

******

Ƙarfe 11 da 'yan Mintuna Motocinsu Suka Yada zango A ƙofar Gidan mai girma Hakimin Ɗanbatta Inda Suka Tarar da Al'umma Tsaye, wasu kuma Suna Zaune da alaman dai Isohuwarsu Ake jira, Mufeeda Kuwa Tunda Suka Shigo garin Ɗanbatta gabanta ke Faɗuwa Zuciyarta bata Tsinke ba Sai da Suka Tsaya A ƙofar Gidan Duk da Ƙofar Gidan Hakimi ba'a Rabashi da Jama'a amma na Yau Daban ne, Sukansu su Basma Sunyi Wani Iri balle da Suka Firfito Daga mota Sunji Ana gaisawa da Tahir Ana mai gaisuwa, Umarni ya basu kan Su Shiga Cikin Gida, Shi kuma Idanuwansa na kan Mufeeda bayan ya Miƙawa Iya Naila.

A cikin gidan ma Cike yake da Mata Tunda nan Aka kawo gawar Inna Fuleran Bayan ta cika Akayi mata Wanka da Suturu Tunda Suka Shiga gidan Mufeeda ke Jan Ƙafa, kamar Mara Lafiya, barinma yadda jama"a ke Binta da kallon Tausayi Basu Dai Tsaya ba sai da Suka Shiga Falon Goggo Abu Inda Suka Iske Goggo Abu zaune da Hijabi Da Carbi Ahannunta gefenta kuma Innaro ce sai Ashe da Maman Lantana Dake gafe Daga Tsakiyarsu kuma gawar Inna Fulera ce Lulluɓe Cikin Likkafani Tunda Suka Shigo Ɗakin Maman Lantana Ta ɗago Tana Kallon Mufeeda Idanuwanta na Zubar da Ƙwallah Tun daga Lokacin Jikin Mufeeda ya fara Rawa Saboda yadda gabanta ya fara Tsinkewa Lokaci Ɗaya.

Basma ganin gawa ne yasa Ta koma bayan iya Tana Rawar Jiki Ita ko Mufeeda Maman Lantana ta Nufa Tana Faɗin"Maman Lantana lafiya naga kina kuka..? Waye nan kwance ya Rasu..? Ina Innata naga banganta bane.." Ta ƙarashe Faɗa Cikin Fitan Hayyaci Hannunta Mama Lantana Ta Rik'e kafin Tajata har gaban gawan Inna Fulera ta saka Hannu ta yaye Farin likafanin Da'aka Lulluɓeta Dashi Dayake Tana Cikin Makara ne, Fuskar Inna Fulera Ta bayyana Kwance Bata Numfashi.

Daskarewa Mufeeda Tayi Tana bin gawar da kallo Cikin Rashin Hayyaci Kafin Ta Sulale ƙasa Ta Duƙe Gaban Gawar bakinta na Rawa Muryanta na Tsinkewa Take Faɗin "Inn... Innata..Ta..na barci ne ko..?" Ta faɗa Lokaci Ɗaya Ta Ɗago kai Suka Haɗa ido da Maman Lantana Hawaye Sun Fara Wanke mata Fuska Jikinta na Rawa ganin Tana Taɓa Inna Fulera ba motsi gashi Duk An Nannaɗeta Ciki Likafani Zuciyarta Ta Tabbatar mata da Sai Mutum ya Mutu Za'ayi mai Haka Kenan Innarta Ta Rasu..? Zuciyarta ce ta karye Ta Faɗa jikin Gawan Tana Faɗin "Innata ki Tashi...Nasan kina Jina..? Nice 'Yarki Mufeeda ki Tashi ki ganni nasan Wasa Kike man baki Mutu ba.." Ta Faɗa Tana Kuka Wurjajan Su Goggo Abu Saboda Tausayi Sai Sharan Ƙwallah Suke na Tausayin Mufeeda Maman Lantana ne ta ƙaraso kusa Da Ita ta Riƙota Tana Kuka Take Faɗin "Bar Kuka Saman gawa Mufeeda Fulera ta tafi..Sai dai muyi mata Fatan Dacewa Ta Cika Da Kalmar Sunanki Abakinta bayan Ta Jaddada albarka agareki.." Ƙyam Mufeeda Ta Tsaya Da Kukanta Tana kallon Maman Lantana Cikin Fitan Hayyaci Take Faɗin "Da gaske ne dama Inna ba barci Take ba..? Innata fa Ta Rasu kika ce..?" Na Shiga uku ni Mufeeda ina zan Saka kaina..?" Ta faɗa Tana Sakin Wani Marayan Kuka, kamar zata Shiɗe Lokaci Ɗaya Tana ƙara Sulalewa kan gawar Iya da Basma na waje Ɗaya Suna Sharan Ƙwallah Hatta Naila Datake yarinya Ganin Mufeeda na Kuka Itama sai Ta Fashe da Kuka ganin Yadda Mufeeda ke ƙanƙame gawar Inna Fulera ne Tana Kuka Tana Faɗin Inna Ki Tashi ya sanya Innaro Tashi Ta Riƙota da Ƙarfi Cike da Tausayi amma sai Mufeeda Ta Turje domin Wani ƙarfi ne yazo mata ta ƙwace kanta ta koma ta ƙara kwanciya kan gawar Inna Fulera Tana Kuka Daidai lokaci kuma Su Tahir Suka Shigo Dashi da Ishaq da Wasu mutane su Shida Sunzo Daukan Gawar, Tun Shigowar su Mufeeda Cikin gidan Tahir ke Cikin Zullumi yanzu ma yana Shigowa Idanuwanshi na kanta Gaba ɗaya Jikinshi na ƙara Sanyi Kusa da Ita Suka Isa kafin ya Sanya Hannu ya Dafa kafaɗarta yana Faɗin "Mufeeda..." Ya faɗa Cike da Rauni.

Jin Muryansa yasa ta Ɗago da Sauri Ganinshi yasa Kawai Tayo Rimi ta afka mai Har sai da ya zauna kan Cafet ɗin bayan yayi Saurin Riƙeta Cikin Kuka Take Faɗin "Kagani Wai Daga Innata na barci suna cewa ta mutu, Zata Tashi ko Daddy kace mata Ta tashi gani nazo.." Ta faɗa Tana Zubar Hawaye Zuru yayi mata da Ido kamar ya Fashe mata da Kuka Cikin Fitar magana yace "Kinga Kwantar Da Hankalinki, kinji ko..? Kin Taɓa ganin Wanda ya Mutu ya Dawo..?" Girgiza kai tayi kafin ya cigaba da Faɗin "Toh ki saka Aranki Inna ta tafi bazata Taɓa Dawowa ba...Yanzu Addu'arki kaɗai Take buƙata ba Kukanki ba.." Tsuru tamai da Ido Hawaye na Zuba mata Shar kafin tace "Bani da Kowa...Inna itace gata na...Ya zanyi na Shiga Uku.." Baki ya Rufe mata yana Faɗin "A'ah kina damu...Mune gatanki Mufeeda nayi ma Inna Alƙawarin zan zamo garkuwarki Har Ƙarshen Rayuwarki ki daina Kuka Tashi ki bari Aɗauki gawarta Amata Sallah zamu kaita gidanta na gaskiya.." Ya faɗa yana Ɗagota Tsaye kafin yama Su Ishaq alama da Ido kan Su Ɗaga gawan Gaba ɗaya Falon ko Mamakin yadda Tahir ya Iya Shawo kan Mufeeda Akeyi, wacce Tun Taga Da Gaske za"a Fita da Gawan Inna Fulera sai ta ƙara Tuburewa Tana Kuka Tana Ƙoƙarin Ƙwace kanta Tana Faɗin "Wayyo ku Dawo min da Innata Ku Dawo min da Ita.." Take Faɗa Tana kuka Tana miƙa Hannu Har Aka Fice da Ita Agaban Idanuwanta Luu kawai Tayi Ajikin Tahir alamun Ta Sume, Fuskarta yake Shafawa yana Kiran Sunanta, Innaro da Ashe Suka Taso da Sauri Suka Riƙota Suka Shiga da Ita Uwar Ɗakin Goggo Abu Mama lantana kuma Ta bisu da Ruwa Shi kuma Tahir Da Sauri ya Fice yana Ji kamar Shima ya share Ƙwallar, Da kallon Tausayi Goggo Abu Ta Bishi Itama Ƙwallar Take Sharewa Domin Har yanzu bata Ishi Baba Hakimi kallo ba.

Har Aka kai Inna Fulera gidanta na Gaskiya Mufeeda bata ƙara magana ba Bayan Ta Farfaɗo Tana dai Zaune Zuru Hawaye na Zubar mata Kowa yazo ita yake Tausayi ba Uwa ba Uwa Gashi ba wani ƙwaƙƙwaran Dangi, Mutane sai magana Suke Wasu na Faɗin Ai Taimakonta Ma gidan su Hakimi, Sune gatanta, gida ya cika da 'yan Zaman Makoki Hakama Ƙofar Gida Cike da Mutane Ciki Harda Su Tahir da Ishaq Harda Garzali Direba Wanda Tahir yace ya Koma gida yace ya barshi ya samu Jana'iza Mutane da Kuma alhinin Mutuwa ya saka ba Wanda Ya Lura ba Farida balle Har Ya Tambayeta Goggo Abu ne ke Damuwa Da Ita, Toh Itama Tana Ta kanta ne Ba wanda Ya Tuna Da Ita sai Washegari Da Umma Suka zo gaisuwa Ita da Abba,Tun Ajiya Ishaq ya koma Shida Garzali inda Tahir yace Ranar Uku ya Dawo ya Ɗaukesu.

Tahir ya Shiga Cikin Gida Da Rana gaida Umma Naila na Hannunsa bayan Tagama ma Tahir gaisuwa Shiko Rabin Hankalinsa naga Mufeeda Wadda Cikin Kwana Ɗaya Ta Fita Hayyacinta Kukan Zucci Take Wanda Sai dai Aga Hawaye na Zubo mata Ta fita Kamanninta Fuskarta Ta Kumbura Idanuwanta Sunyi Jawur Tana Kusa Da Goggo Zaune ta Tsurama Cafet Ɗinta ido Yana Nazarinta ne Umma Tace "Wai ni kam Ina Farida ne Tunda na Shigo ban Ganta bane ko Tana Shashen Innaro ne..?"

Gaba ɗaya wajen Aka Zuba ma Tahir Ido, dama Cikin Uwar Ɗakin Goggo Abu ne, Daga Umma sai Mufeeda sai Goggo Abu Innaro ma Tana Falo Ita Da Ashe da Sauran Jama'a Cikin Dakewa Da Rashin Damuwa Tahir yace "A'ah Umma bata zo ba.." Cikin mamaki Take Faɗin "Bangane bata zo ba? Tahir Mutuwa fa Akayi Shine ka ƙyaleta Taƙi Zuwa..?"

Murmushi yayi kafin Yace "Nifa Umma Tun Washegarin Tafiyarku Farida ta saka ƙafa Ta bar gidan Batare Dana san Inda Taje ba.." Salati Umma ta Saki Kafin Tace "Na shiga uku ni Aliya Farida Zata Kasheni Lokacina bai ƙare ba Haba Tahir Shine Duk Tsawon Wannan Lokacin Baka Taɓa Sanar damu ba..?" Kansa ya Sunkuyar batare Daya ce komai ba Mamakin Goggo Abu yake Yadda Ko ƙanzil batace ba Lalle Goggo Taga Rayuwa.

Cikin Ɓacin Rai Umma Ta Ciro Waya Ta Dokawa Farida Kira, lokacin da Kiran Umma ya Shigo Tana Zaune Afalon Na Billy Tana kallon Ikon Allah, domin Abban Su Walida ne yayi Tafiya yau zai Dawo Shine Billy Ta kasa Sukuni da Zama Tsakanin Kicthen da Falon ƙayataccen Girki Take mai Tana Rawan Jiki, Farida Abun na bata mamaki In Taga Abunda Billy ke Aikatawa kamar ba da ita Cikin masu Zugata kan ba'a Sakarma namiji Fuska Balle kai mai Rawan Jiki Itako Tunda Tazo Gidan Matuƙar Taga Billy Afalo Toh Abban Walida ya Fita ne In ko yana nan bata da Lokacin kowa bayan An Chaɓa Ado An Shiga Kichen Anyi Girki Ta Tuna Sanda Billy ke Bata Shawaran Ta Ɗauko mai aiki Kada ta zama baiwa mai abinci, Abun bai ƙara Ɗaure mata kai ba, sai da taga yadda Billy ke Rawan Jiki ko Muryan Abban Walida Taji, kenan Itace Suka Maida Sakarya da Suke Sanar Da Ita Tsakaninta da Namiji bawani Ragowa in Tanaso ta ƙwaci 'Yancinta..?

Tana Cikin Wannan Tunanin Wayarta Ta Shiga Tsuwa, ganin Sunan Umma sai da gabanta ya amsa Tana Ɗagawa Umma tace "Kinci Ubanki Farida.." Cikin Mamaki Farida Tace "Kai Umma me nayi kuma..?" Umma tace "Ubanki kikayi Nace Ubanki kikayi..Ashe Farida Baki da Mutumci bansani ba? Kina gidan Uban waye Bayan kinbar gidan Mijinki...?" Tura Baki Farida Tayi kafin Tace "Umma ina gidan Billy...."
"Billyn ubanki Sakarya mara Tunani Wato ita Tana Gidan Aurenta Ke kuma Ta barki ki Zauna Tunda baki da mafaɗi, Toh maza ki Haɗo Yanaki yanaki Kizo Ɗanbatta yau ɗin nan muna Jiranki Nida Abbanki munzo Gaisuwar Rasuwar Mahafiyar Mufeeda.." Daga Haka Umma Ta Katse Kiran.

Sororo Farida Tayi Ranta na ƙuna da Sunan Mufeedan Da'a Aka Ambata Amma Haka Ta tashi ko kallon Ɓarayin da Billy Take bata yi ba Wacce ke Jera Kuloli bisa Dinning Ɗakin Da'a Aka Sauketa ta Shiga Tana Hawaye Ta Haɗa kayanta Tsab Ta Ɗauko Mayafinta da Akwatinta ta Fito, A falo Suka ci karo da Billy Cikin mamaki tace "Ah Farida Ina Zuwa naganki da Akwati Haka..?"

Kai Tsaye Farida tace "Ɗanbatta zani..." Sheƙeƙe Billy ke Binta da kallo kafin tace "Wai koma ma Tahir ɗin zakiyi Don Rashin Zuciya..?" Cike da Haushinta Farida Tace "Eh zan koma ma Mijina Tunda na lura masu bani Shawaran yadda zan Tafi da gida Su basu amfani da Shawaran ko Kaɗan.." Sororo Billy Tayi Domin Tagane magana Farida ta yaɓa Mata, Ɗaure Fuska Tayi kafin tace "Au Haka zaki ce...? Ke kika sani Ai 'yanci Ake Neman ƙwatar miki Mutumin daya Tozartaki yama 'Yar aikinki ciki ai magana ta ƙare.."

Farida Takama Hanyar Fita Take bama Billy Amsa Cikin Dakewa tace "Eh 'Yanci Abarni na ƙwatarma kaina kamar yadda Kuma naga kuna Ƙwatarma kanku, kuma maganar yama 'Yar Aikina ciki Gwarashi nashi ya bayyana Mijin Wata Fa.? Uban wa yasan Wani Ta'asan yake Aikatawa Adai yi Sha'ani.." Baki Billy Ta kama kafin tace "Kambu...! Amma kafin ta Sake Wata Magana Farida Ta Fice da Kallon Mamaki Ta Bita Kafin Ta taɓe baki tace A fili.. "banza.Allah sa Kin Fara Wayau kenan.."

Itako Farida Motar Ta ta Ta Shiga Taba ta Wuta sai da Ta Fahimci Lafiyarta kana Ta saki Hon Megadi ya Buɗe mata Ƙofa ta Fice da Gudu Cikin Lokaci kaɗan Ta Ɗauki Hanyar Ɗanbatta Zuciyarta Cike da Fargaban Wani Irin Hukunci Zata karɓa Wajen Umma da Abba.



*Aisha Alto*
*Shakira*
*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Alkaluman:*✍️

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty)*💕

_Don't Forget to Follow us on Wattpad: Janafnancy13 or Aisha Alto Alto_

_*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_

       *BABI NA GOMA SHA TARA*

Ƙarfe 2:40pm. Ta isa Ɗanbatta, Tahir da Hakimi da sauran mutane suna zaune a ƙofar gidan suna karɓar gaisuwa gurin jama'a masu zuwa musu ta'aziyya, haka ta ratsa tana sunne kai ta shige cikin gidan, tana shiga direct ɗakin Goggo Abu ta dosa.

Tana shiga da Umma suka fara haɗa ido, rass taji gabanta ya faɗi tana turo baki ta ƙarasa ciki ta zauna a kusa da Goggo Abu ta duƙar da kai taƙi kallon kowa dake ɗakin, Mufeeda kuwa tana ganin Farida ta shigo tayi maza ta miƙe ta fita falon Goggo ta zauna, don bata son abinda zai haɗasu da Farida guri ɗaya, gani take zata iya rufeta da duka don haka take jin tsoronta.

Miƙewa Goggo Abu tayi itama ta fito falo gurin Mufeeda ta zauna akabar Umma da Farida kaɗai a cikin uwar ɗakin, ɗagowa Farida tayi tana kallon Umma tace "Umm..." Da sauri Umma ta dakatar da ita tana watsa mata harara take faɗin "Uban me ya kai ki gidan Bilkisu Farida...? Wato dai ke har yanzu bazaki natsu kiyi hankali da duniya kisan me take ciki ba ko Farida.? Yanzu da kika je gidan Bilkisun uban me kikaje tayi miki? Me ma yasa kika saka ƙafa wai kika bar gidan mijinki da 'ya'yanki bayan duk irin faɗan da nayi miki ranar kafin mu tafi? Wato baki ji ba shine kika shure kika tafi gidan ƙawa har na tsawon kwanaki huɗu kina can a zaune saboda gaki ballagaza ko...? To uban me kika je yi gidan aurenta tayi miki..? Tana zaune da mijinta lafiya ke da baki san mutunci da darajar naki mijin ba shine kika kwashi jiki kika tafi gidanta tayi miki maganin taki matsalar ko?" Ta faɗa a hasale tana ji aranta kamar ta tashi ta rufeta da uban

Please Login or Register in order to submit comment