Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duka saboda takaicinta, ita ko Farida wani bala'in haushin Bilkisu ta ƙara ji a zuciyarta, take wasu hawaye suka fara zubowa daga cikin idanunta Umma na kallonta tace "Ai kuka kam yanzu kika farashi Farida..tunda dai kince ke ba mai hankali da tunani bace balle kisan ya kamata, na ɗauka zaki yi nadama ne saboda abinda sakacinki da toshewar tunaninki ya janyo muku ke da mijinki, ashe ba haka bane, ke inda tunaninki yake daban, abinda kika ɗaukarwa zuciyarki tun farko shi zaki ci gaba da yi. To kiyi Farida, bance ki  fasa ba kici gaba..." Haka Umma tai tawa Farida faɗa, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, Farida kuwa in banda kuka ba abinda take yi har da shassheƙa, sai yanzu ne ita da kanta take ganin aibun abunda tayi a rayuwarta, bata kyautawa kanta da 'ya'yanta ba, uwa uba kuma mijinta, bata tashi sanin babban kuskuren data tafkawa rayuwarta ba, sai data je gidan Bilkisu taga yanda take yiwa mijinta take kaffa kaffa dashi, bata haɗa komai da mijinta ba. Ita yanzu wace riba zata ce taci na irin halayen dasu Bilkisu suka dinga zigata suna ɗorata akai kuma tana bi...?

Umma ce ta katse mata tunanin da take da faɗin "Yanzu a irin waɗannan abubuwan da kike yi wace riba kika samu? Me kuma zaki ɗorar? Miji ya gaji da halinki, har ya daina damuwa da duk wasu lamura da suka shafeki, kin kaisa bango halayenki sun gama isarsa, kin tafi kin bar gidan mijinki da 'ya'yanki kin tafi gidan ƙawa kin zauna har tsawon kwanaki, kin gama fallasa kanki da zuri'arki a gaban ƙawayenki, sirrin gidanki da komu bai kamata mujishi ba kin gama tallatashi a titi ga wasu can kinyi terere da mijinki, don nasan sai kin gaya musu duk abinda yake faruwa, tunda tunaninki ya gama toshewa..." Ta faɗa tana murmushin takaici, wani kukan baƙin ciki Farida ta fashe dashi tana girgiza kanta, kafin ta ɗago hawaye na tsirarowa daga cikin idanunta tace "Umma don girman Allah..." Sake dakatar da ita Umma tayi da faɗin "Komai kika yi fa kanki kika yiwa, nidai zanci gaba da tayaki addu'a Allah ya shiryeki yasa ki gane gaskiya. Don haka maza ki tashi kije ki yiwa Mufeeda gaisuwa..." Ta faɗa tare da miƙewa, itama Faridan tashi tayi tana share hawayen fuskarta tabi bayan Umma suka fito falo, inda Goggo Abu da Mufeeda suke sai Nailah da Iya da Maman Lantana, Umma zama tayi a kusa da Mufeeda tana kallon Farida da tayi tsaye tana kallon Mufeeda a sace tana turo baki alamar bazata iya ba an takura mata, wani kallo Umma ta watsa mata ba shiri ta dubi Mufeedan data sunkuyar da kai ƙasa tana wasa da bakin hijabinta, sai data zabga mata uwar harara kafin ta ɗauke kai tana faɗin "Ya ƙarin haƙuri...Allah ya jiƙanta ya gafarta mata.." Ta faɗa a tare tana zama a kujerar dake falon.

A hankali Mufeeda ta ɗago ba tare da data kalli inda take ba tace "Alhamdulillahi...Momy mun gode Allah, Ameen na gode.." Ta faɗa ƙwalla na taruwa a cikin idanunta, janyota Goggo Abu tayi jikinta tana share mata hawaye, taɓe baki Farida tayi tana kallonsu kafin ta ɗauke kai tana sakin siririn tsaki.

Ranar a nan Umma ta kwana yayinda Abba kuma suka juya shida direba suka koma wanda sai ranar addu'an uku sannan zai dawo bayan anyi addu'an uku da safe sai su koma tare da Umma.

************

Yau akayi addu'an ukun Inna Fulera, bayan mutane duk sun watse yayi saura sai yasu yasu a gidan, suka taru dukkansu da Baba Hakimi da Goggo Abu da Innaro da Tahir da Ashe dasu Basma da Bassam sai Farida da Mufeeda da Umma da Abba.Sai Ishaq da Zahra da Suka zo Suma, Sai da suka haɗu gaba ɗayansu kafin Baba Hakimi yasa Tahir yayi addu'a aka shafa, sannan ya fuskanci Mufeeda wacce ke zaune a ƙasa ta duƙar da kanta ƙwalla na zubo mata, nan ya shiga yi mata nasiha sosai da nuna mata ta dinga yiwa mahaifiyarta addu'a ta daina mata kuka, kanta ta gyaɗa masa kafin ta ɗago tana share ƙwallar tausayin kanta.

Umma ce ta gyara zamanta tana kallon Abba take faɗin "Gata nan Alhaji ka tambayeta inda ta tafi tabar gidan mijinta da 'ya'yanta tsawon kwanaki bata gidan aurenta...ba tare da tazo gida ba, ba kuma tazo nan Ɗanbatta ba..." Ta faɗa tare da nuna masa Farida da tayi tsuru tsuru tana raba idanu, wani kallo Abba yayi mata yana faɗin "Au wato bayan mun tafi shine tabar gidan tayi wani guri, saboda bata ji maganar da mukayi mata ba..?" Gyaɗa kai Umma tayi tace "Ai kuwa babu abinda ta ɗauka a faɗan da akayi mata.." Ta faɗa tana kallon Farida.

Gizgiza kai Baba Hakimi yayi yana faɗin "A'a bafa kusan dalilinta na barin gidan ba, ƙila dai akwai abinda shi Attahirun yayi mata ne..." Da sauri Abba ya katseshi da faɗin "A'a Mansur, karka ce haka, ai yana gaba da ita, kuma ko ba haka ba ai mijinta ne shi, kuma kome zaice mata ai bai kamata ace tayi fushi tabar gidan ta tafi wani guri daban inda ba'a sani ba..."

Baba Hakimi na kallon Abba yace "Ka bari muji abinda ya faru a bakinta tukunna..ke Farida faɗa mana abinda Attahiru yayi miki da yasa kika bar gida..?" Ya faɗa yana kallonta, ƙara sunkuyar da kai tayi ta shiga rattabo abinda ya faru ranar bayan tafiyarsu tana haɗawa har da sharri tana ƙullawa, tunda ta fara maganar kawai Tahir ya girgiza kai yana sakin murmushi bai ce komai ba, har ta dasa aya...

A harzuƙe Abba yace "Wato a ranar da muka gama magana akai miki faɗa a ranar kika sake shuka wata tsiyar ko Farida..? To ki sani wallahi tallahi babu inda Mufeeda zataje tana nan zaune daram a gidan anan zata zauna ta haihu, sai dai ke kibar gidan don ubanki kije duk gidan ubanda zaki amma banda gidana, kuma wallahi duk ranar da kika sake fita kika je wani waje bada yawun mijinki ba ko kika fita saboda nuna kinfi ƙarfinsa Allah ya isa bamu yafe miki ba, tunda ke bazaki taɓa yin hankali ba..." Ya faɗa a zafafe yana sauke numfashi, sake rushewa da kuka Farida tayi har tana jan numfashi kamar zata shiɗe saboda baƙin ciki, nan Umma ma ta ƙara dasawa sukayi mata tass, abin mamaki Goggo Abu na zaune tayi laƙwas sai bin kowa da kallo kawai take ta kasa magana.

Baba Hakimi ma yayi mata faɗa sosai sannan ya haɗa har da Tahir shima yayi musu faɗa kafin ya ɗora da faɗin "Kiyi haƙuri Farida ki rungumi Mufeeda ki tausayawa rayuwarta, ki zauna da ita lafiya kinga marainiyace, ki ƙara riƙeta kamar yanda kika fara riƙeta ada..idan cikinta ya isa haihuwa watan ya tsaya Innaro zata zo can gidan naku ta zauna don ta riƙa kula da ita har ta haihu.." Ya faɗa yana ƙara lallashin Farida kan ta zauna lafiya da mijinta ta kula da 'ya'yanta.
Daga ƙarshe dai Baba Hakimi ya saka musu albarka tare da yi musu fatan alkhairi da gamawa lafiya dukkansu.

Nan Tahir ya matso gaban Abba ya duƙar da kai bai ce komai ba, lura da hakan da Abba yayi yasa yace "Me yake faruwa ne Tahir.? Ko akwai wata matsala ne kuma...?" Jinjina kai Tahir yayi alamar Eh.. Abba na gyara zama yace "Ka faɗa min ko mene ne Tahir insha Allahu indai inada dama Allah ya bani iko zanyi maka maganinsa..." Cikin jin daɗi Tahir ya ɗago yana faɗin "Dama Abba inaso ne ka roƙi Baba ya yafewa Goggo Abu.." Ya faɗa yana jin ƙwalla na taruwa a cikin idanunsa, saurin ɗagowa Abba yayi yana kallon Baba Hakimi, kafin yayi magana Baba Hakimi ya rigasa yana murmushi yace "Na riga na yafe mata duniya da lahira, Allah kuma ya yafe mana baki ɗaya ya kiyaye gaba.." Da Ameen duk suka amsa, kafin Tahir ya fara miƙewa Shida Ishaq  suka  fita daga ɗakin suka nufi ƙofar gida gurin Sauran Jama"an Dake Wajen Wadanda Suka zo Addu"arku Uku ba Dadewa sai ga Su Abba Suma Sun Fito Suna Tattaunawa shida Baba Hakimi.

A ranar Umma da Abba suka koma Kano, da yamma suma su Tahir da Farida da Iya da Mufeeda da yara duk suka tattara suka yi shirin komawa Kaduna, mota biyu sukayi Tahir da Farida da Mufeeda suka shiga motar Ishaq, su kuma Basma da Bassam suka shiga motar Tahir da Garzali ya tuƙo suka ɗauki hanya, bayan sun bar motar Farida a nan gidan Baba Hakimi akan washegari Garzali zai dawo ya ɗauka.

******

A hankali abubuwa suka fara daidaita, sai dai Farida tana tsananin kishin Mufeeda, amma tana ƙoƙarin dannewa bata son a gane, don irin tsantsar kulawar da Tahir ke nuna mata kwata kwata bata so, amma tana yi tana dannewa, bata so a gane tana jin haushi.

Haka a ɓangaren Tahir shima kwata kwata baya ganin hasken Farida, don ta gama sire masa gaba ɗaya a ransa, daurewa kawai yake yana nuna kulawarsa a kanta, kuma yana ƙoƙarin sauke hakkinta dake rataye a wuyansa, amma duk ɓoyewarsa sai data gane, don a komai ya ƙara canza mata sosai, kusan rabin kulawarsa gabaki ɗaya yanzu duk ya ɗorata akan Mufeeda ne.

A lokacin ne kuma su Mufeeda suka shiga Jss2 suna ci gaba da karatunsu, bata da matsalar komai ta ƙara wani kyau da haske, sai dai kusan kullum kafin tayi barci sai ta tuna da Innarta, idan tai kuka sai ta share hawayenta kuma tayi mata addu'a.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya wani lokaci aji daɗi wani lokacin kuma aji akasin haka,Farida Bata Kaunar Ta Bude Ido Taga Mufeeda da Ciki Acikin gidannan Tsoronta Daya ne Abba da Umma Tasan yanzu Abu kadan Zatayi Suyi Fushi da Ita Sosai,Abunda kuma ke karamata Kishin Mufeeda Shine ganin yadda Tahir ya Watsar da al"amarinta bai Cika damuwa da Al"amarinta ba,gasu Bassam Sun ki marata baya Sun bi Bayan Mahaifinsu,Haka Suke Kafa kafa da Mudeeda kamar su lasheta komai take bukata tana samu Koda yaushe Cikin Tallalinta Sukeyi.

Tuni Farida ta Watsar Da Shawaran Kawayen banza,Tunda Agroup Dinsu Billy Taje Tana bada Lbrin Zata kwatar mata yanci Ta gayamata mgana Ranta ya baci,ta Shiga group din Ta maida mata martani Tamata Wankan Tsaki Billy Tasan bata da gaskiya Sai ta kama kame kame,anan Akayita bata Hakuri Daga karshe Fitama Farida Tayi Daga Group Wasu Dadama Sun Bita Suna bata Hakuri Suna Fadamata Kowa Data gani Anan yana lallaba Aurensa ne,ba wani mai Sakaci,sai Lokacin Farida Tagane tayi Wauta babba..Wato Duk Acikinsu itace Sakarya Tayi Kuka Sosai kamar Ranta zai Fita Tayi Nadama sanda bashi da amfani,Tadaina Fita kwata kwata Wanda Ta gyara Domin Shi ko kallo bata Isheshi Ba Domin yafi Nuna kalawarsa Akan Mufeeda Fiye Da Ita,Abunda yasa Farida Rama kenan Atsaye Duk tayi Wani Zuruzuru Da Ita.

***********

   *BAYAN WATA SHIDA*

Cikin Mufeeda ya ƙara fitowa sosai yayi girma gwanin ban tausayi, Tun yana Wata Hufu Tafara Zuwa Awo Anan Iyali Hospital,kuma shi yake kaita watarana In yana da Lokaci Ranar dai bai samu Zuwa ba sai Garzali ya kaita ita da Innaro,tsufan cikin nata ne, yasa Tahir ya hanata zuwa islamiya yace ta riƙa zama a gida makarantar boko zata rinƙa zuwa kaɗai, duk ranar da ba makaranta tana zaune a gida, hakan yana ƙona ran Farida sosai ya baƙanta mata zuciya, don ta tsani ganin cikin bata ƙaunar tayi tozali dashi kwata kwata a rayuwarta, jira take kawai Mufeedan ta haihu Tahir ɗin yasan nayi da ita.

Baba Hakimi ya cika alƙawari Tahir na sanar Dashi Cikin Mufeeda ya Cika Wata Tara yace ya Aiko Garzali ya Ɗauketa, nan da nan kuwa ya aikashi sai ga Innaro Ta Iso Abunda ya ƙara baƙantama Farida rai ganin Ɗakin Mufeeda Tahir yace A sauketa Suna Murna kamar ba Ɗan Shege za'a Haifa ba, Haka Tazo da Jiƙe jiƙe Saboda Maganin sanyi, Take Ta bama Mufeedan Ita da Iya ba'a san Wanda yafi Wani kula da Mufeedan ba, Goggo Abu kuwa Batama ta Farida yanzu Domin Da ƙyar ta samu bayan Abba ya saka Baki Hakimi ke Kulata Ko a hakan ba kamar baya ba, Shiyasa Take ƙoƙarin gyara Kuskuranta ta kuma Ƙudirci Wani Abu A ranta Jira kawai Take Allah ya Sauke Mufeedan lafiya Ta Aiwartar da Ƙudirinta Domin yanzu Tausayin Mufeedan Take Kullum Cikin Kira Take awayar Innaro Ana bama Mufeeda Tana Tambayanta Me take ji..? Wani Lokacin Dariya kawai Mufeeda keyi bata cewa komai Domin Yawanci Tambayan Tahir kenan Inya Shigo Dubata da Safe da Kuma bayan Ya Dawo ko Shi bata bashi Amsa sai dai ta Sunkuyar Da kai Aranta Tana Jin Daɗin yadda Daddy ya fara maida Jikinshi ba kamar Farkon Al'amarin ba.



*Anitha...*
*Aisha Alto...*
*NANNY...!*
      (Mai Reno..)

*Alƙaluman:*✍🏻

*AISHA ALTO💞*
*JAMILA UMAR (Janafty💕*


_Don't Forget to Follow us On Wattpad: Janafnancy13 or Aisha Alto Alto_


*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔*
*KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

       *BABI NA ASHIRIN*

""Ɓangaren Kayan Haihuwa Kuwa Babu Abunda Tahir bai gama Siya ba Kuɗi masu yawa ya Ware ya bama Matar Ishaq Zahra ta sayo komai da komai Kayan jariri kuwa komai Biyu ta Siyo na Mace Dana Namiji Tace Saboda Tahir bai yarda an mata Scanning ba, balle aga mai Zata Haifa.

Kuma Zahran Da kanta ta kawo Kayan Gidan, Abunda Ya ƙarama Farida Ciwo yanzu Har Takai matsayin da Bata da Wani amfani Wajen Tahir, ya maida kanshi dashi da 'yan'uwansa da Iyayensa Wajen Tattalin Mufeeda, Sai dai Tayi Wuni Cikin Ɗakinta Taita kuka bamai lallashinta Ita baga kulawan Miji ba Haka Zalika ma Su Bassam banda Gaisuwa babu Abunda Ke Haɗasu Koda yaushe Suna Ɗakin Mufeeda suda Iya da Innaro Wani Lokacin Tana Falo sai dai Tajiyo hirarsu Da Dariyansu Mufeeda kuwa Ko ta ganta ta gaisheta Farida bata amsawa Sai dai Ta bi Cikin Jikinta da kallo Cike Da Kishi ganin yadda yayi Girma yana Neman Rinjiyan Mufeedan, Burinta da Fatanta Allah Ya Sauke Mufeedan Lafiya ta ƙara gaba Allah barshi abunda Zata Haifa In Ta gama Shayarwa akaisa gidan Marayu Domin ba Wanda Zai Gurɓata mata 'ya'ya dana Shege

******

Yau ɗin takama Jumma'atu Babban Rana ce, Misalin ƙarfe 9 na Safe Duka suna Zaune A falo Suna Hira Innaro, Iya da Basma sai Bassam Dake wasa da Naila Wacce Take Tafiyanta yanzu Sai Mufeeda dake Zaune kasan Cafet Ta Buɗe ƙafa Hannayenta na Baya ta Dafa ƙasa Ga Cikinta nan Wani Randa guda yayi girma sosai har yayi ƙasa, Ta kumbura Ko'ina na Jikinta ya Buɗe ya ƙara Girma, In ka kalleta Farat Ɗaya kamar ba Mufeeda ba Domin Ta Cika Ciki ya sakata tazama ƙatuwa, su Basma suna Hutun Ƙarshen Shekara in suka koma zasu Shiga jss3 hadda kawai Suke Zuwa yanzu da Islamiya.

Aya ce agabanta Tana ci Tana Dariyan Labarin da Iya ke basu na Matar ƙaninta da Ta faɗa masai, Basma Saboda Dariya Harda Riƙe Ciki, Mufeeda ma Dariyan Take lokaci Ɗaya tana Cin Ayanta, Farida Data Sauko Daga Sama ta bisu da kallon Takaichi Da ƙyar ta iya Buɗe baki Ta gaida Innaro, Iya ta gaidata Hakama Su Basma Duk ta amsa amma Mufeeda na Gaisheta tayi kamar bata jiba ta Shige Kichen Abunta Mufeeda bata damu ba Domin Inda Sabo ta Saba da Hallayar Farida.

Ruwa ta Ɗauko Kafin Ta sake Haurawa Sama Ƙofar Bedroom D'in Tahir Tabi da kallo, Tun Jiya Daya Dawo Daga Lagos bai sake Fitowa ba, Buɗe Ƙofar tayi Ta Shiga ta Iskeshi kwance Cikin Bargo yana barci Ƙyalesa Tayi Ta Fito Daga Ɗakin Tana Tunanin gajiyace Domin Wajen Satinsu Daya achan Shida Ishaq ne Suka Tafi Taran Sabbin Motocinsu da Zasu zo ta Jirgin Ƙasa, Toh basu iso ba Sai Shekaran jiya Da Daddare Su kuma jiya suka taho Zuwa Kaduna.

Ɗakinta ta koma ta Sha Ruwa kana Ta Koma ta kwanta Tana Tunanin Da Zarar Mufeeda Ta Haihu Ta bar mata gida Zata gyara Duka mu'amalanta da Mijinta Harda 'ya'yanta Batasan Cewa Lokaci Tuni ya Ƙure mata ba.

Mufeeda Dake Dariya Ƙasa ƙasa, Taji kamar bayanta ya amsa Da Sauri ta gimtse Dariyan Tana jin Lokaci Ɗaya maranta ya Ƙulle, Cije baki tayi ganin ba Wanda ya lura da Halin Data ke ciki Ta Dafa Kujeran Ta Miƙe A hankali Tana Cije baki Lokaci Ɗaya Innaro da Iya Suka kalleta kafin Innaro taceb"Mufeeda lafiya..? Ina zaki Haka..?"

Saurin Sakin Murmushi Tayi kafin tace "Bakomai Innaro Toilet zan Shiga.." Innaro tace "Ayyah..Jeki Dawo.." Ta faɗa Tana kallonta da Sauri Mufeeda ta Fara Taku Zuwa Ɗakinta Tana Daurewa amma Fa Cijewa kawai take saboda yadda Ƙugunta ya Riƙe ga Maranta ta Ƙulle Waje Ɗaya,bHar ta Shige Ɗakinta Innaro na Binta da kallo kamar tana so Ta Ɗago Wani Abu...

Mufeeda Da ƙyar Ta iya kai kanta Tsakiyar Ɗakinta kafin ta Durƙushe Tana Riƙe gadon Hannu Biyu Jin Ƙugunta kamar zai Tsage gida Biyu, Zufa ce ke Keto mata kamar Wacce Ake Gasawa Salati Mufeeda ke Saki Cikin Ranta Lokaci Ɗaya Hawaye na Wanke mata Fuska ko Bata sani ba Wannan Azaban Data keji Ta Gane Naƙuda ce, Tun Abun na Ƙasa ƙasa Har ya gagari Tunanin Mufeeda Kuka Take Wurjajan da Majina Domin Tagama Yanke Kauna wallahi Mutuwa Zatayi domin Wannan Azaba Ta mutuwa ce.

Innaro ce Taga Shirun na Mufeeda Yayi yasa Ta kalli Basma Tana Faɗin "Ke Basma Maza Tashi ki Dubo min Mufeeda najita Shiru ne.." Da Hanzari Basma Ta Miƙe Ta Nufi Ɗakin Mufeeda Halin Data Tarar da ita ya bata Tsoro Cikin Firgici Tace "Innaro kuzo kuga Mufeeda.." Ta fada da Ƙarfi Jin Haka yasa Innaro da Iya Suka fara Rige Rigen Shiga Ɗakin Mufeeda Hankalinsu a Tashe, Bassam Dai Naila ya Ɗauka Wacce Ta Fashe da Kuka lokaci Ɗaya bai bisu Ɗakin ba ya dai Tsaya A falon yana Tunanin ko lafiya...

Kallo Ɗaya Innaro Tama Mufeeda Ta Fahimci Tana kan Gwiwa Basma Ta kallah Wacce Har Ta fara Hawayen Tausayin Mufeeda tace "Maza kije ki kira min Daddynki.." Da gudu Basma Ta Fita ta Haura sama Tahir na kwance Cikin Barci Yaji Basma na Faɗin "Daddy Daddy...Ka Tashi Innaro na Kira Mufeeda Zata Haihu Tana ta kuka.." Take Faɗa Tana Kuka Itama.

Zumbur ya Miƙe Daga Kwancen Yana Kallon Basma Ido ya Zaro yana Faɗin "Zata Haihu kika ce Basma..?" Kai ta gyaɗa mai tana Share Ƙwallah da Hanzari ya Dirko Daga kan gadon Da gashi sai Dogon Wando Jallabiyansa ya Laluba ya saka ya zari Key ɗin Mota ya Fita Da Sauri Basma Tabi Bayanshi Fitowarsu Da Hanzari ya Fito Da Farida Daga Ɗaki Ganin Tahir da gudu ya Sauka Ƙasa yasa Itama Tabi Bayansu da Sauri Tana mamakin Me ya Razana Tahir Lokaci Ɗaya Haka..?

Tahir ko na Shiga Ɗakin Mufeeda Yaga ba yarda Take Innaro na mai magana bai Saurareta ba kawai ya Cicciɓi Mufeeda Zuwa Waje yana Faɗin "Innaro ki Ɗauki Mayafi mutafi Asibiti.." Farida Dake Ƙoƙarin Shiga Ɗakin Mufeeda Tayi Baya ganin Tahir ya Ɗauko Mufeeda Tana Faman kuka tana Yarfa Hannu, suman Tsaye Tayi Cike Da Takaichi da Kishi Wai Tahir ne ya Ɗauki Mufeeda da Hannunsa Niko Nace Yamata Cikin ma balle Ɗauka.

Bata gama Mamaki ba Iya da Innaro Da Suka Rufa mai baya Da Gudu Mayafai A hannu Saboda Zullumi sai ga Basma Ita ma da Hijabi Ta Runtuma tabi Bayansu, baki ta Riƙe Cike da Baƙin ciki Lokaci Ɗaya kuma Falon ya ƙara Ɗaukan Kukan Naila, Daga Nailan Har Bassam D'in Da Harara Ta Bisu kafin Ta Saki Tsaki ta koma Sama Tana Ƙunƙuni Ita kaɗai.

Tahir ko Garzali bai Saurara ba ya Kai Mufeeda Bayan Mota, Ya Dawo Gidan Gaba Mazaunin Direba ko Su Innaro Dake Fitowa Haraban Gidan bai Jira ba ya Kunna Mota yayi Reverse da Ƙarfi lokaci Ɗaya ya saki Hon ya Fice Da Gudu, Su Innaro basu Tsaya ba Suka Faɗa Mota Basma Ta Shiga Gaba Innaro Tace "Garzali bi mana bayan Attahiru..." Cikin Bin Umarni Garzali yaja mota Yabi Bayan Tahir Daya Nufi Asibitin Iyali Hospital Dake Kusa Dasu.

****
Koda Tahir ya gama Faka Motarsa Cikin Haraban Asibitin Bai Jira Wani ba, Ya Fito Daga Mota ya Buɗe Baya ya Cicciɓo Mufeeda Dake kuka Wurjajan Lokaci Ɗaya Da Salati Domin Ji Take kamar Zata mutu da Gudu ya Nufi Cikin Asibitin Da Ita ganinshi Haka ne ya saka Nurses Da Gudu suka gungoro Gadon Ɗaukan Marasa Lafiya Zuwa Gareshi ganin kamar ya Fita Daga Hayyacinsa yana Kiran Likita.

Kan Gadon ya Ɗora ta da Hanzari Suka Shiga Turata yana Bin Bayansu cikin Tashin Hankali Labour Room Suka Shiga da Ita Suka Rufo ƙofa Dole Tahir ya Tsaya Awaje yana Safa da Marwa sai ga Su Innaro Sun Shigo Asibitin Hankalinsu Tashe Cikin Fargici Innaro Tace "Attahiru Ya Ake Ciki...?" Numfashi ya Sauke yana Faɗin "Bansani ba Innaro Sun Dai Shiga da Ita Ciki..." Gefe Suka Koma kowa na Addu'a Cikin Ransa Basma ko Hawaye Take Sharewa Suna nan Tsaye Wata Nurse Ta fito da Gudu Ta Wuce Office d'in Likita, Sai gashi Sun Fito A tare Cikin Hanzari Sun Koma Cikin Ɗakin Daga Wajen Suna Jin Salatin Mufeeda Da Kukanta Lokaci Ɗaya Tahir yaji Jikinsa ya Saki Ƙwalla Ta Cika mai ido yana Fatan Allah ya Sauki Yarinyar nan lafiya kada ta Mutu Da Cikin nan ya Shiga Uku.

Tsawon Awa Ɗaya Likitoci na Shige da Fice kan Mufeeda Haihuwa Shiru nan da nan Suka mata Scanning Nan Suka gano yan Biyu ne A cikinta amma Sun Galabaita, yunƙurin Fitowarsu da kansu Matsala ne, Nan da nan Wani Likita ya Fito Yana Faɗin "Ina Mijinta...?" Da Hanzari Tahir ya Isa Gabanshi yana Faɗin "Gani Dr..Hop ta Sauka lafiya.." Kai ya girgiza mai kafin yace "Biyoni Office da Sauri bamu da Lokaci.." Jin Haka yasa ya bishi da Hanzari, Zuwa Cikin Office Ɗinshi Suna Shiga Ciki ko zama baiyi ba ya Miƙa mai Wata Takarda yana Faɗin "Muna Buƙatar saka Hannunka anan, zamu Shiga da Ita Aiki ne yanzu Domin Ceto Rayuwarta data yaran Dake Cikinta.." Tahir na Zufa ya karɓa Takardan Haɗe da Biron ya Rattaba Hannu, kafin Likitan ya karɓa yana miƙa mai Wata ƙaramar Takarda yana Faɗin "Ka biya Kuɗin Aiki yanzu..." Tahir bai Tsaya ba ya Fito da Sauri su Innaro Dake Zaune Suka miƙe Suna kallonshi Kanshi ya Shafa yana Faɗin "Sun ce aiki zasu mata yanzu...Ku zauna anan Bari naje na Biya Kuɗin Aikin Na Dawo.." Innaro tace "Toh kana da Kuɗi A hannunka..?"

Yana Tafiya yake Faɗin "A'a Sai dai Atm ɗina zanyi Amfani Dashi.." Ya faɗa yana Ƙara Sauri Cikin Minti goma Sai gashi ya Dawo da Resit ya Riga ya Biya Kuɗin Aikin bai Daɗe da Isowa Wajen ba Sai ga Mufeeda An Gungurota Zuwa Ɗakin Tiyata an Chanza mata kaya, Kuka Take da Salati Lokaci Ɗaya Suna kallo Aka Shiga Da Ita Gefe Suka koma Kowa Da kalan Addu'an Dake Ranshi barin ma Tahir da Abun Duniya Suka Taru Suka mai yawa...

Shuɗewar Awa Biyu Kafin wasu Nurses Guda Biyu Su Fito Daga Ɗakin Tiyatan Ɗauke da Yara Guda Biyu Cikin Wasu Showels, da Hanzari Suka miƙe Suna kallonsu Cikin Fara'a Ɗaya Tace "Congratulation ta Sauka An Samu Twins, mace da Namiji..." Gaba ɗayansu Suka Haɗa baki Wajen Faɗin "Alhamdulillah." Innaro Ta karɓi Namijin Iya kuma Ta karɓi Macen Dukkansu bakinsu yaƙi Rufuwa Shiko Tahir Hamdala yake Acikin Ranshi kafin yace "Ina ita Maman Yaran..?" hope tana lafiya.." Ɗayar tace "Eh ana gyarata ne da Zarar an kammalah zamu maidata Ɗakin Hutu.." Daga Haka Suka Wuce, Chan sai ga Likitocin Suma Sun Fito Suna Cire Safan Hannu, Musabaha sukayi da Tahir Suna mai Murna, Bakin kowa yaƙi Rufuwa, Bai Ɗauki yaran ba Domin Wani Tausayinsu ne ya Tsirga mai na Ya samar Dasu Ta Hanyar da bai dace ba, Ashe Dalilin Daya sa ya Afkama Mufeeda Kenan Rabon samun Waɗannan ne ya Kawo Haka.

Ba ɓata Lokaci aka Gunguro Mufeeda Zuwa Ɗaki na Mussaman Domin Hutu, Suka ce Kar wanda ya Shiga Inda Take Sai ta Farfaɗo bayan Awa biyu da wani Abu, Yanzu aje azo da kayan Jarirai da Kayan Tea d'in da Mai Jego zata Buƙata in ta Farfaɗo, Tahir ne ya barsu anan ya Koma gida, Farida na Jin Dirin Mota ta Zabura ta Fito Falo Suka Ci karo da Tahir Cikin Rawan Baki Tace "Ta Haihu..?"

Bai kalleta ba yace "Eh amma C.s Aka mata an Ciro 'Yara Biyu mace

Please Login or Register in order to submit comment