Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a jami'ar BUK kafin yazo ya tafi dashi shi kanshi Mansur yaji wani iri balle Abu da Ashe da suketa kuka amma sai Alhaji Ibrahim ya lallashesu da cewa in suka samu hutun makaranta Tahir ɗin zai dinga zuwa yana gaisheshi.

Kai tsaye ya nema masa Admission bayan ya zaɓar masa course d'in da yayi wato Business Asmitration domin yana sha'awa tare da burin Tahir ya zama yayi karatu ko don ya taimakeshi bisa harkan kasuwancinsa tun bayan da mahaifansa suka rasu duka kula da kamfanin mahaifin nashi ya dawo hannunshi gashi shi kuma ɗiya mace Allah ya bashi zuwan Tahir gidan sai Farida ta samu Yaya duk lokacin tana da shekara tara da wani abu sai ya kasance shike kula da ita koda home work d'in makaranta ne shi ke mata in bai da lakca kuwa suna tare yana koya mata karatu inda bata gane ba kafin kace me shaƙuwa mai zurfi ta shiga tsakaninsu duk kuma sanda ya samu hutu zai tafi Ɗanbatta tare da Farida yake tafiya saboda bata yarda ya barta agida duk inda ya saka ƙafa anan take saka nata al'amarin daya ke ma iyayenta daɗi domin basu da abar farin ciki irin Farida shiyasa suka sangarta komai sai an mata basu la'akari da ita macece, abun na cima Tahir tuwo a kwarya yadda Farida bamai gaya mata taji tun tana ƙaramarta yarinyace mai ƙawayen bala'i da tarkace kowa nata ne ga kuma shegen zuwa gidan ƙawaye tun tana ƙaramarta jikinta rawa yake in taji labari biki kowani event da za'aje achashe sukuma iyayenta sun bata freedom wani lokacin ma Tahir ke taka mata burki taji dayake tana tsoronshi.

Yana shekarar ƙarshe a BUK Allah yama Hakimin rasuwa aka kuma naɗa mahaifinshi wato Mansur bai samu zuwa ba sai lokacin bikin mahaifinshi inda ya ƙara aure da Salamatu Innaro, lokacin ne ya daɗe agida kafin ayi posting ɗinsu su tafi service ɗinsu suna gamawa Abba Alhaji Ibrahim ya matsa mai ya tafi birnin US ya ɗora Masters ɗinshi yana chan har mahaifinshi ya ƙara aure da Binta itama irin Salamatun ne har ta shekara Allah bai bata haihuwa ba sai Hakimi Mansur ya haƙura ya fara tunanin ƙila iya ƙwanshi da zai gani a duniya kenan.

Sai da ya shekara uku kana ya dawo lokacin Farida har ta gama Secondary Sch ɗinta ta shiga BUK aji ɗaya a yayinda Ashe kuma take SS1 wanda yaje yaji wai za'a mata aure shi ya hana yace don Allah abarta ta ƙarasa toh dalilin haka aka barta sai da ta kammalah Secondry Sch ɗinta kana aka mata aure da yaron limamin garin Badamasi suna zaune anan garin Ɗanbatta.

Dawowarshi ne yasa Abba ya buɗe mai kamfani a garin Kaduna wato *IBRAHIM KWATANO AND SONS LIMITED* Wanda ya bama Tahir ragamar kula da wajen amatsayin manaja murna sosai yayi ya dingama Abba godiya haka Hakimi Mansur da yaji sai da yazo har Kano yamai godiya kowani masoyin Tahir in yaji wannan labarin sai ya tayashi murna da farin ciki, lokaci kaɗan kamfani ya fara aiki bayan an zuba ma'aikata da masu kula da abubuwa lokacin ne kuma Tahir suka haɗu da Ishaq wanda ke matsayin Accounting Manager a kamfanin, sai tasu tazo ɗaya sakamakon amana irin ta Ishaq da kuma hankali da sanin mutumcin kanshi shiyasa lokaci ɗaya abota mai ƙarfi ta shiga tsakanin Tahir ɗin da Ishaq wanda shima ɗan asalin Kaduna ne.

   A nan Kadunan Abba ya siyama Tahir gida wanda yake zaune da motar hawa mai tsada saboda taƙaita zirga zirga daga Kano zuwa Kaduna da zuwa Ɗanbatta shekara uku kamfanin yayi da buɗewa amma yayi ma saura zarra dama Tahir haka yake komai ya sama hannu sai anga albarka kafin kuma wannan shekarun abba na matuƙar alfahari da samun Tahir hakama iyayenshi don zuwa wannan lokaci hatta gidansu ya gyarashi tsab ya kuma sakama duka iyayen nashi mata ababen more rayuwa a duka shashensu daya gina musu, lokacin kuma shekara biyu da rasuwar Binta, Ashe ma sha tara na arziki yake mata bama itama kaf al'ummar Ɗanbatta suna alfahari da samun ɗa irin Tahir saboda shi baya da burin ya tara abun duniya illah yama jama'a hidima da kuma garin haihuwarsa.

 
Farida na shekarar ƙarshe a makaranta ta furtama iyayenta ƙudirinta game da Tahir na tana sonshi da aure jin haka ya daɗaɗa ran Abba da Umma sosai sukayi farin ciki domin sun fi kowa sanin samun ɗa nagari mai halin dattako irin na Tahir sai an tona ko kafin ma Tahir ɗin yaji labarin Abba ya isa Ɗanbatta ya labartama Hakimi suma achan ɓangaren shida Goggo Abu sunyi murna sosai don aganinsu su Alhaji sun ma Tahir hallacin daya kamata shima ya saka musu har Kaduna Abba yaje ya sameshi da maganar hakika ya girgiza dayaji muradin Farida amma ba ita da cewa sakamakon Abba yayi mai abunda bazai iya ƙin jininsa ba duk da ko ya gane tuntuni Farida ba irin macen data dace dashi bane, amma bai da yarda zanyi ganin iyayenshi sun kirashi sun jamai kunne kan karyama Abba gardama kan ƙudurin haɗa auren shi da Farida.

Cikin wata uku aka gudanar da bikinsu wanda yabar dimbin tarihi domin shagali akayi kamar ba gobe, bidi'a kala kala don ma shi Tahir ɗin ya doje Ɗanbatta ya tafi bai yarda ya zauna a kano ba sai ranar aure yazo shida Ishaq da tawagar Hakimi da daddare kuma akayi dinner wanda Tahir yasha mamaki uban mutanen dasu kazo wanda shi baisan ko ɗaya ba ashe duk jama'ar Farida ne, saboda tsabar zuwa bikinta har laƙabi ake mata da Farida biki-biki, abun bai bashi mamaki da saninta da uban ƙawaye da kuma son zuwa sha'ani ita ko bikin waye ko ba'a gayyaci Farida tana zuwa indai tasan cewa za'ayi Event aji daɗi ashana ta sake yadda ranta keso balle shiganta BUK ta ƙara samun ƙawaye na gari dana banza kuma ta ƙara yawo idonta ya buɗe amma bana iskanci ba na wayewa.

Washegari aka kawota Kaduna Anguwar Rimi Gra a babban gidan da Tahir ya gina da guminsa Farida taga gata gaba da baya domin da tsala tsalan motocinta biyu aka kawota gidan, ko wata ɗaya basuyi da aure ba Tahir ya fara gaya musu, saboda ko girki Farida bata iya ba ko kichen bata shiga sai dai shi in ya dawo daga Office ya zage ya shiga ya sama musu wani abun su ci, ko kuma in zai dawo yayi musu takeaway baima wahalar da bakinsa ganin bata iya ba balle tayi ganin haka yasa tama Umma magana ta kawo mata 'yar aiki itama basu daidaita ba watanta biyu ta ƙara gaba saboda halin Farida na faɗa komai aka mata ba'a mata daidai ba, watansu huɗu da aure akayi posting ɗinsu zuwa service a kuma lokacin ne ciki ya ɓulla ajikin Farida wacce ta dinga kuka wai zai hanata tafiya service Bauchi, abu har sai da iyaye suka shigo ciki Abba ne da kanshi ya mata cuku cuku ta dawo Kaduna amma ba haka ranta yaso ba ciki zai mata cikas wajen zuwa biki ko sha'anin kece raini amma bata da yarda zatayi don Tahir ya kasa ya tsare kan cikin jikinta taga ainihin kalanshi

Sai da cikinta yayi wata goma cur kana ta haihu shima C.S aka mata aka ciro 'yan biyu mace da namiji murna wajen Tahir ba'a magana, saboda shagwaɓan Farida da sangarta sai dai Tahir ya barta aka tafi da ita Kano wajen Umma, ta kula da ita yara kuma suka ci sunan Basma da Bassam, Farida bata dawo ba sai da ta kusa wata uku kana ta dawo har su Basma sun fara wayau data dawo har da 'yan aikinta guda biyu ɗaya ta kula dasu Basma ɗaya kuma tayi girki da gyaran gida, zamanta a Kaduna yasa Farida tayi ƙawaye fita biki sai wanda bata jiba Tahir kuma haƙuri gareshi, ko tayi wani abun bai cika mata magana ba saboda miskilancinsa, uwa uba kuma fifikon soyayyarta azuciyar iyayenta da kuma damar da iyayensa ke ganin taimakon mahaifinta gareshi karya wulaƙanta ta amma zamansu da Farida duka  haƙuri yafi yawa a ciki.

Haka dai rayuwa ta cigaba da gangarawa da daɗi ba daɗi Tahir dai na haƙuri da halin Farida rayuwarsu Basma da Bassam kuwa ta walagigi ce hannun 'yan aiki da kuma shi saboda in ya dawo daga Office yana zama ya kula dasu Farida kuma bakin yawo ke cinta daga yau tana wajen bikin ƙawarta sai gobe bikin ƙanwar ƙawarta gashi ita kuma bata da sha'awar yin aiki amma kuma bata iya zama agida ita kenan yawon biki, gashi shi mutum ne da bayason hayaniya da ɓacin rai ya kai ƙararta sau biyu wajen su Abba amma ba wani chanji shiyasa ya kawo ido ya sakamata yana ƙoƙarin shanye ɓacin ranshi akanta duk babu abunda zai ɗaurar na jin daɗin aure shi kam.

Matsala ta biyu kuma shine Farida tana daga cikin jerin matanan masu ƙarancin sha'awa kuma basu ba hakan muhimmanci ba balle ta nemi magunguna ko na musulunci ne saboda shi Tahir yana daga sahun maza mabuƙata, wani lokacin sai suyi sati biyu Farida bata kalleshi ba in ko ya nemeta sai ranshi ya ɓaci ya rasa meke damunta wani lokacin yana buƙatar saboda gudun ma kanshi ɓacin rai yake ƙoƙarin daurewa shiyasa koda yaushe cikin yin azumi yake koda bana ranar Litinin da Alhamis ba.

Bayan haihuwar su Basma tayi family plaining ba tare da Tahir ya sani ba shiyasa har su Basma suka kai shekara takwas bata ƙara haihuwa ba, tunda har sun shiga makaranta Commond sch Kaduna, har tuhumarta ya taɓa yi ta turje tace batayi komai ba taƙi gaya mai gaskiya haka da suka je Ɗanbatta Goggo Abu ke tambayanta Allah sa ba ƙwayoyin zamani Tahir ɗin ya ɗorata akai ba tace ba komai. Da yake ba'a ma Allah dubara cikin wannan tsukun ta samu cikin Naila wanda ya wahalar da ita shima C.S aka mata tana haihuwarta Farida tayi alƙawarin ta gama haihuwa itama wannan haihuwar gida ta koma, 'yan aikinta kuwa tuni ta sallamesu da zata dawo daga wankan Naila ne ta dawo da Iya.

Tahir ya rasa shi wani irin ƙaddaran rayuwa ce ta faɗa mai yana ganin Ishaq da matarsa Zahra gwanin ban sha'awa amma shi ƙarya ne ya dawo daga Office ya iske Farida agida ko tana gida bashi da wani matsayin da zai shigo tazo ta mai sannu da zuwa tayi kwalliya don ya gani yaji daɗi tana ciki tana waya da ƙawayenta ana tsara yadda bikin ƙanwar wanche zai kasance kullum cikin yi mata nasiha da nusassheta yake amma bataji saboda misalin dayake yawan mata da Zahra matar Ishaq ta yanke alaƙa da ita bata wani sakarmata fuska sai itama Zahran taja baya da ita.

  Goggo Abu ce kaɗai da ƙanwarsa Ashe suka san halin dayake ciki in ya gaya mata sai ta bashi haƙuri ta kuma ce zatama Faridan magana toh ko Faridan taje garin in Goggo Abu ta mata faɗa sai tace insha Allahu zata gyara kuma bata gyarawan kuma Goggo Abu ta hanashi sanarma Hakimi wai kada ya zama sanadiyyar raba amintantakar dake tsakanin Abba da Hakimi.

  Mufeeda Kuma Tahir da kanshi ya ɗauko ta faga Ɗanbatta bisa umarnin Goggo Abu bayan Ita Faridan da kanta ta Nemi Goggon data samo mata matashiyar yarinyar wacce zata tayata kula da Naila amatsayin NANNY...."





*Aisha Alto.*
*Shakira.*
*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Alkaluman:*✍️

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty*💕


*Wattpad: Janafnancy13 or Aisha Alto Alto*


_*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_

*BISMILLAHIR RAHAMIR RAHIM*

       *BABI NA HUDU*

  *MALLAM BELLO GURGUN DANBATTA* Sunan mahaifin Mufeeda wanda shima ya kasance haifaffan garin na Ɗanbatta ne gaba da baya, haka ma matarsa Inna Fulera itama haihuwan nan ce kuma tashin nan.

Sai dai kuma tun asali dukkansu biyun sun fito daga tsatson talakawa ne futuk marasa ƙarfi kuma dama auren zumunci ne tsakanin Bello da Fulera, bayan haka kuma dangin nasu basu da yawa saura sun mutu sauran kuma sun lula garuruwa neman kuɗi.

Bello gurgun Ɗanbatta ya samo asali ne da tun yana yaro ciwon daji yakamashi ahannu wanda yayi sanadiyar cire mai hannu guda ɗaya shikenan in za'a kirasa sai adinga mai in kiya da Bello gurgun Ɗanbatta, daga Malam Bello har Inna Fulera duka sun rasa iyayensu so suna zaune awani ƙuntataccen gidan ƙasa cikin matsi da wahalar rayuwa, dukkansu babu wanda yayi ilimin boko sai na allo shima ɗin sama sama don lokacin bawai sanin darajan abun sukayi ba, balle su damu dashi baida wata sana'a sai sana'ar noma kayan lambu kamarsu tumatur dasu kabeji da albasa, yana shiga cikin gari yana siyarwa da hannun nasa guda har su samu su rufama kansu asiri.

Sun shekara kusan goma da aure kafin Allah yabasu Mufeeda wanda bayan ita ta haifi 'yan biyu duka maza basu zo da rai ba daga lokacin kuma haihuwa ta tsayama Inna Fulera sai suka cigaba da rainon Mufeeda wacce suka ɗauki son duniya suka ɗora mata saboda ita kaɗai garesu itace 'yarsu kuma ahalinsu sannan abokiyar hirarsu shiyasa itama Mufeeda ta taso cikin so da ƙaunar duka iyayen nata guda biyu, duk da tazo ta iskesu cikin wahalan rayuwa amma suna iya bakin ƙoƙarinsu akanta don ita kanta Inna Fulera bata zauna ba tana saida dafaffen kabeji acikin gida ana zuwa siya ba laifi tunda tana da   tsabta...

Haka suka cigaba da gangara rayuwarsu da daɗi ko ba daɗi har lokacin da Mufeeda keda shekara goma sha uku a duniya ta girma duk wasu alamun budurci basu bayyanar mata ba sakamakon siririyace ita bata da jiki sosai, kwatsam suka tashi da wani rashi, rashi mai girma daya taɓa zuciyarsu wanda har yau suka kasa mantawa dashi na rasuwar Bello Gurgu sanadiyar faɗawa rafi ruwa ya cinyesa Inna Fulera da Mufeeda sunyi kuka kamar ransu zai fita, duk da a lokacin Mufeedan nada ƙarancin shekaru amma wannan rashin da sukayi ya tsaya mata sosai a cikin ranta.

Ko takaba Inna Fulera bata fita ba suka fara shiga tasku da wahalar rayuwa na babu sai su kwana basu ci ba, abun na damunta duba da ƙarancin shekarun ita Mufeedan shiya sanya tana gama takaba labarin neman ma'aikata daga gidan Hakimi ya sameta inda Tahir ya bada cigiyar neman waɗanda zasu dingama iyayensa hidima yana biyansu duk wata Inna Fulera batayi ƙasa agwiwa ba ta isa gidan Hakimi gaban Goggo Abu sai dai koda taje an riga angama ɗaukan adadin ma'aikatan, nan Inna Fulera ta faɗi gaban Goggo Abu tana kuka tana roƙonta data rufa mata asiri ta taimaki rayuwarta data marainiyar Allah Mufeeda toh a lokacin sai taausayin ƙarancin shekarun Mufeeda ya ɗarsu a zuciyar Goggo Abu har yayi sanadiyar data ɗauki Inna Fulera amatsayin hadimarta amma in tagama da shashenta takan shiga madafi ta taimaka duk wata 15k Tahir ke biyansu dukkansu wanda cikin lokaci kaɗan ya taimaki rayuwar mutane dadama ciki harda Inna Fulera wanda cikin haka ne ta sanya Mufeeda a makarantar Primary Ɗanbatta tana zuwa idan ta taso sai ta biyo gidan Hakimi wajen Innarta taci abinci ta ƙoshi ba shashen datake zuwa sai shashen Goggo Abu ta zauna tayi shuru dake bata da yawan magana wani lokacin in Goggo Abu ta ganta sai Tahir ya faɗo mata acikin ranta tana tunanin shigen miskilancinsa amma in ta kalli yanayin Mufeeda sai taga ta shanyeshi haka kurum take jin tausayin yarinyar shiyasa take janta ajiki sosai.

Mufeeda bata da wata ƙawa agarin sai Lantana wacce maƙotansu ne itama Mamarta tana aiki agidan Hakimi ita kaɗai ce ƙawarta kuma gashi makarantarsu ɗaya kuma ajinsu ɗaya, shiyasa sai tasu tazo ɗaya kuma in sun tashi daga makaranta tare suke wutowa gidan Hakimi wajen iyayensu, Mufeeda bata da saurayi kamar na sauran 'yanmatan ƙauye ko nace bata bi ta kansu kwata kwata saboda ita bata son auren wurin da'ake musu mutum ɗaya ne take kulawa shima sai ya dameta Iliya mai rake, tun tana ƙaramarta yake bibiyarta abokin saurayin da Lantana zata aura ne Murtala shiyasa wani lokacin in sun biyo hanyar makarantar allo in Murtala yaja Lantana gefe itama sai Iliya ya jata duk dai bata sakarmai fuska bai damu ba saboda yaci ace ya saba da yanayin rayuwar Mufeeda.

 
   Inna Fulera bata rufe shekara da samun aiki agidan Hakimi ba Farida tazo garin inda ta samu Goggo da shawaran tana buƙatar a nema mata wata yar yarinya wacce zata tafi da ita amatsayin Nanny saboda kula da Naila sai su dinga biyanta duk wata suna aikoma da iyayenta tunda ta lura duk waɗanda Umma ke samo mata daga Kano ita basu mata, Goggo Abu na jin haka sai Mufeeda ta faɗo mata arai amma sai ta fara tunanin kamar ba zata iya ba, ilai ko Faridan na ganin Mufeedan tace ko itama aka bata ta isa, Goggo Abu bata yanke hukunci ba sai da ta nemi shawaran Hakimi da Innaro suka kuma bada goyon baya Duk Da Tahir ɗansu ne amma suna da kyakkyawan sheida akanshi shi da matarshi basu wulaƙanta mutane...

Cike da ƙwarin gwiwa Goggo Abu tasa aka mata kiran Inna Fulera ta labarta mata muradinta azahirin gaskiya taji firgicin maganar duba da Mufeedan kaɗai gareta kuma ta ƙwallafa rai da ita amma kuma Goggo Abu bazata nemi alfarma taƙi mata ba, bata da yarda zatayi ta amince amma zuciyarta ba daɗi duk da ko ta tabbatar Mufeeda zata samu ingantacciyar rayuwa agidan Tahir, amincewar Inna Fulera ya sanyayama Goggo Abu rai nan ta mata alƙawarin insha Allahu bazatayi nadama ba, Farida ta koma bayan ta bar sallahun Mufeeda ta shirya sati mai zuwa direba zai zo ya ɗauketa.

Inna Fulera data koma gida tayi kuka sosai kuma bata iya sanarma da Mufeeda ba, fahimtar haka yasa Goggo Abu ta saka Inna Fuleran ta turo mata Mufeedan ta sanar da ita, wayyo gwanin ban tausayi duk da ta kasance mai rauni wajen kazar kazar ɗin rayuwa amma kukanta ya kasa ɓoyuwa tana kiran ita bazata bar Innarta ba Goggo Abu ke ta lallashinta amma taƙi yin shiru ƙarshenta ma ta tashi da gudu ta fita sai gida chan taje ta sakama Inna Fulera kukan ba inda zata tafi ta barta, kwana tayi lallashinta da bata baki amma Mufeeda taƙi yarda.

Sati kuma na cika sai ga Tahir yazo garin Garzali ya kawoshi kuma shi Farida bata sanar dashi komai ba, Goggo Abu kuma tana ganin haka sai ta zata ya sani ne shine yazo tafiya da Mufeedan nan da nan tasa aka kiramata Inna Fulera tace tayi maza taje ta shiryo Mufeeda da kayanta ga Attahiru nan yazo tafiya da ita Kaduna, Allah sarki raba uwa da 'ya sai Allah da kuka da komai Inna Fulera ta kawo Mufeeda gidan Hakimi sai lokacin ma Tahir yasan da maganar bai wani damu ba sanin dama Farida bata ɗaukeshi bakin komai ba, abun kuma yayi mai daɗi ko banza yana daraja garin haihuwarsa haka Mufeeda ke kuka Inna Fulera nayi taƙi shiga mota ta ƙanƙameta Innarta tana wani kuka mai ban tausayi tare da ƙawarta Lantana, har sai da Hakimi yace a haƙura da tafiya da Mufeedan asamu wata saboda yadda daga Mufeedan har Inna Fuleran suka bashi tausayi haka shima Tahir wanda da kanshi yaje ya riƙo hannun Mufeeda yana kallonta ƙwarjininsa ya hanata yi mishi gardama gaban Inna Fulera ya duƙa yana ƙara jaddadamata insha Allahu zai kular mata da Mufeeda kamar 'yar da ya haifa kuma alƙawari ne yayi mata zai dinga kawo Mufeeda lokaci bayan lokaci tana zuwa ganinta, wannan kalaman nashi su suka sanyaya ran Inna Fulera da kanshi ya saka Mufeeda cikin mota da ƙullin kayanta wanda ƙwarjininsa da kimarsa yasa ta kasa mishi gardama amma har motarsu ta ɗaga daga ƙofar gidan Hakimi Mufeeda na kuka tana ɗagama Inna Fulera hannu itama tana kuka tana ɗagamata Iliya ma yana laɓe daga chan yana leƙen tafiyar Mufeedan sai da ya share ƙwallah saboda an rabashi da masoyiyarsa zuwa birni shima Murtalan Lantana ke gaya mai..

  Koda Farida taga Tahir da Mufeeda bata damu ba dama tunda yace yau zashi Ɗanbatta ta sani Goggo Abu zata bada Mufeeda azo mata da ita shiyasa bata damu ba, lokacin da Mufeeda ta tsinci kanta agidan Tahir ta sani ta shiga wata sabuwar rayuwa na bambamcin komai kama daga wayewa da garin ma gaba ɗaya, da farko bata iya sakin jiki ba duk da ko ɗakinta ita kaɗai Farida ta bata bayan ta miƙa mata amanar Naila wacce lokaci ɗaya yarinyar ta shiga ranta abunda ya ƙara sanyayamata rai shine yadda ko su Basma basu nuna mata bambamci duka ɗaya suke ga Iya itama tana mata kyakyawan mu'amala ta ɗauketa kamar 'yar data haifa da cikinta, balle Farida da bakomai take bama muhimmanci ba, kuma ance mai ɗa wawa balle data lura yadda Naila ke samun kulawa sosai wajen Mufeeda cikin lokaci kaɗan tayi kiɓa ta chanza shiyasa komai nata na ɗakin Mufeedan awajenta yake kwana in ba Tahir bane ya matsa ta ɗaukota nono kuma in tana nan ne take bata in ko bata nan sai dai ta wuni shan madaran ruwa.

Farida bata da matsala ta ɓangaren ƙyashi ko wulaƙanta mutane ta fito daga gidan arziki shiyasa Allah bai ɗora mata wannan ƙyashin ba, komai zatama Basma da Bassam sai ta haɗa da Mufeeda da Iya haka ma Tahir baya nuna bambamci akan komai abinci tare suke ci, tun Mufeeda na ɗari ɗari har ta saki jiki ta saba, kuma duk wata Tahir na turama Inna Fulera 20k da farko cewa tayi bazata karɓa ba yayi yawa sai da Goggo Abu ta matsa mata.
Watanta uku da zuwa Farida tabama Tahir shawaran asanya Mufeeda a makaranta nan da nan ko ya yarda da shawaranta shima abun na ranshi cikin sati ɗaya cike cikenta ya tabbata ta samu gurbin karatu a Model School Kaduna inda ta fara daga Js1 duk da tana Primary 4 ta tsaya lamarin dayama Mufeeda daɗi sai da tayi kuka da farko ta fara samun matsala ta ɓangaren wayewa da kuma turanci, sai kuma Tahir ya sama musu Lesson Teacher ita dasu Basma yana koya musu suma kuma suna ƙoƙarin koya mata abunda bata gane ba tunda suma Js1 ɗin suke sai dai su Commond School sukeyi sai an kaisu kana direba ya wuce da ita in ta tafi makaranta sai Iya ta karɓi kula da Naila wacce tasha kuka kafin ta saba da rashin Mufeeda kafin ta dawo makaranta ta gaji da kuka ta haƙura.

  Sai da suka samu hutun farko kana ta roƙi Tahir wanda take cema Daddy don amatsayin uba ta ɗaukesa zata je Ɗanbatta direba ya kaita ta kwana biyar ta dawo saboda Naila, zuwan daya yima Inna Fulera dad'i haka suka ƙanƙame juna Lantana da wasu mutanen gari basu iya gane Mufeeda ba saboda yarda ta zama 'yar gayu tayi kyau kamar ba ita ba, hakama Iliya daya ganta sai da hankalinshi ya tashi na ganin tabbas Mufeeda tafi ƙarfinsa koda ta koma bikin Lantana ya kusa, bata saran zuwa ba amma data roƙi Mami Farida ta roƙar mata Daddy sai gashi ya barta taje ta kwana ɗaya ta dawo zuwan daya sanya ta zama zara cikin wata saboda kyanta da kuma ilimi da wayewar data samu tare da cigaban rayuwa.

Matsalar Farida da Tahir ta fara girma tunda yanzu sai ta shafe wata da watanni bata bashi hakkinshi ba, kuma shi ba dutse bane yana buƙatar wajen ɗebe kewa da damuwa, amma sam Farida hakan baya gabanta in ya nemeta tayi ra'ayi to laba'asa ne da komai ya kammala shikenan ko ajikinta, abun na damunshi kullum cikin azumi yake gashi bata zama agida abun haushi yawon gidajen ƙawaye in Farida taji biki jikinta na rawa tun ada yana ɗauka yarinta ne in taƙara girma zata bari amma ina ko raguwa baiyi ba, su Abba ko ya gaya musu suka mata faɗa zata nuna taji amma kuma ta bayan kunnanta yake wucewa haka Goggo Abu wacce ke tausanshi kada ya sanarma Hakimi halin dayake ciki, maganar ƙarin aure kuma ba ra'ayinshi bane tunda shi mutum ne mara son hayaniya gashi kuma da haƙuri amma ƙanwarsa Ashe ce ta bashi shawaran ya ƙara aure ya bar Faridan ita taje chan ta ƙarata da halinta tun bai yarda da shawaranta ba har ya fara tunanin shine mafita toh Goggo Abu ce ta takamai burki sau uku kenan yana zuwar

Please Login or Register in order to submit comment