Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zata kori Mufeeda Daga gidan.."Ido Ishaq ya zaro yana Fadin"Kabari don Allah...? Tahir ya kariso Kusa da Ishaq ya zauna yana Fadin"Wlh Allah ina gayamaka tana Kuka Wai Tana Fadin Ta Cuceta Ishaq can u juz imaging Wai Farida na Kuka saboda ni Tahir na Ma Mufeeda ciki.."Ishaq ya saki Dariya ahankali yace"Dama tana Sonka Tsabar Iskanci ne ke Cinta nayi Takaichin Abunda ya Faru Tahir Duk da bawa bai isa ya Gujema kaddaransa ammh Ta wani Fanni naji Dadi ko banza Lokaci yayi da Farida zata girbi Abunda ta Shuka.."

Tahir ya kuramai ido yana kallonsa kafin yace"Kamar yafa..? Bangane ba..? Tashi Ishaq yayi kafin ya Sakala Duka Hannuwansa Akirjinsa kafin ya Fuskanci Tahir yana Fadin"Eh mana Ai ada Tana ganin baka da Wani amfani Awajenta,Tana ganin ka Daga Ita sai kai yanzu kuwa Dole zata Shiga damuwa Domin Tana Sonka auren Soyayyah Kukayi bana Kiyayyah ba So Dole Farida tayi kuka Kishinka Take Tahir.."Shuru Tahir yayi kafin ya Jinjina kai yace"Hakane..,? Toh ai Ta makara Sai dai komai yagama lalacewa.."Ishaq yace"Shine ake Jiyemata Tun Farko Kada tayi Nadamar Dole Wacce bata da Wani Amfani.."

Mikewa Tahir yayi kafin yace"Wannan ya Rage nata Ishaq Abunda na sani Shine Matukar Farida tace zata matsama Mufeeda Wlh Itama zata Shiga mtsala na Fadamata in batason ganin Mufeedan agidan zata iya komawa gidansu ban Hanata ba ."Ishaq yace"Ina bayanka Wlh gwara ka Nuna mata Kuskuranta Tun yanzu.."

Tahir yace"Uhm,Kabari kawai Ishaq Zata ga ainihin kalata Wlh.."Ishaq yace"Asaussauta mata Alhaji Abarta taji Da Daya..Yafada yana yar Dariya Shima Tahir Dariyan yayi kafin yace"Yau da Safe Goggo Ta Kirani Tana Kuka Tana Fadamin Tunda Suka Dawo Baba Hakimi baya kulata nadai lallasheta nace Tabari Ranar sati zan Shigo D'anbatan,Duk da ina jin kunya Ishaq sai nake ganin kamar kowa yasan Abunda na aikata.."

Kusa dashi Ishaq yazo Lokaci Daya yana Dafa kafadarsa Cikin Sigan lallashi yace"Daga goggo Har Farida nasan Haka zata Faru dasu kayi Hakuri zasu Daidaita ammh kaima kasan Dole Baba Hakimi yayi Fushi mganar Kunya kuma Don Allah ka saki Jikinka ba Wanda zai san Wannan Mganar bayan mu da muka sani kuma ko Ansani Bafa laifinka bane Kaddara ne kuma Bawa bai isa ya kaucemata ba.."Ajiyar Zuciya Tahir ya Sauke kafin yave"Hakane Nagode Sosai Ishaq Da bansamu Amini kamar ka ba Dabansan Wani Hali zan Shiga ba.."Mirmishi Ishaq yayi kafin yace"Nima Haka da Ban Hadu da Amini kamar ka da na Tafka Asara.."Atare Suka saka Dariya kafin Ishaq yace"Allah ya Sauki Mufeeda Lafiya,Ammh sai nake ganin kamar yarinyar tayi kankanta da Haihuwa fa.."Wani kallo Tahir yayi mai kafin yace"Nima fa ina Mamaki kaduba kagani yarinyarnan kamar kara ammh Ta iya Daukeni Tsaf.."Ishaq ya Buga Kafadarsa yana Fadin"Bugu Daya ko Mallam Kasaka Kwallo Araga.."Ture Hannunshi Tahir yayi yana Fadin"kaifa Dan Iska ne Zahra ta bata ka.."

Ishaq na Dariya yana Fadin"Yan Iska dai Mallam kadinga saka Mun jaye.."Shuru Tahir yayi kafin yace"Wani Hanzari ba Gudu ba,ya Zan yi da Mufeeda bayan Ta Haihu..? Ishaq yayi Shuru Shima yana Wani Tunani kafin yace"Mubar Wannan Mganar Fatarmu dai Allah ya Sauketa lafiya Insha Allahu bazai gagaraba."gyada kai Tahir yayi kafin Ishaq yace"Bari na Kira Zahra ta saka Direba ya kawoma Abincin nan kawai sai muci ko..?

Tahir na Shafa Cikinsa yace"Daka Agaza kuwa Domin nafara ganin Hazo hazo.."Dariya Ishaq ya saka kafin ya fice yana Laluban Zahra ta Waya Shiko Tahir komawa yayi yazauna yana Auna Mganar Yadda zai yi da Mufeeda bayan Ta Haihu..? Wata Zuciyar tace In ta yaye Abunda Ta Haifa sai ka mata Aure ka bata jari..,Toh wazai Aureta bayan Ta Haihu..? Babu Wanda ya chanchanta ya Aureta sai kai Tahir.."Wata Zuciya ta karantamai da Sauri yace"A"a Bazai Yuyu ba Naso kaina Dayawa bayan na lalata mata Rayuwa kuma na Tursasamata zama dani Tana karamar yarinya bazan yi Haka ba.."Yafada Afili Cikin Karayar Zuciya Lokaci Daya Tsausayin Mufeeda na Ratsashi Runtse Ido yayi Yana Tunanin Wani kariya zai Bata saboda Farida Domin yadda ya Zuciya da Farida indai Tace zata Takura Ma Mufeeda Zasu samu babban Mtsala.

****
 
Farida Kuwa Tunda Ta Shiga Daki Tafada Bisa gado Tana Gunjin kuka kamar Zatayi Hauka Gabadaya ta Birkice Haka take Buga kanta bisa katifa Tana Kuka Hannuwanta Dafe da kanta bayan Ta Barbaja Gashin kanta Ya Watse kamar Wata Kamun Hauka Cikin Ranta da Zuciyarta kamar Ta Buga Saboda Kunci Da bakinciki.

Duk bayan Kowacce Dakika sai kalaman Tahir Sun Fado mata arai Wani Jiri take gani Idanuwanta Sun kode Saboda Kuka Tana ji acikinta Ranta Tahir ya gama da Ita Tuni Shedan yamata Zugan dama Duk karya ne plan ne Tahir ya Shirya dama Sun Dade Suna Cin Amanarta Shida Mufeeda munafukar Allah,Ji Takeyi ayanzu Duk Duniya bata da wata makiyiya kamar Mufeeda Tanajin bazata iya Rayuwa acikin gidan Nan Tana kallon Mufeeda da Cikin Tahir ba Watarana Bakinciki zasu Sa Zuciyarta ta buga Ta Fadi ta Mutu .

Cikin Hanzari ta Mike Daga kan Gadon Wajen Jerin Akwatunanta Karamin Ciki Ta Dauko Ta Budeshi Bisa gado kafin Ta Bude Wardrope dinta Tana Debo kayanta tana Sakawa Gefe Daya kuma Tanayi Tana Share Kwallah,Sai da Cikata kafin ta maidata ta Rufe Tana kuka Ta Dauki Wani Hijabin Data Cire Wanda Ke Jikinta Duk gayun Farida Yau batama Tuna da Wani Abu ba Waishi Wanka balle Kwalliya,ta dauko Akwatin kenan Wata Zuciya tace"Farida ina zaki..? Kawai Taji bakinta ya Furta Kano lokaci Daya kuma kalaman Abbanta ya Fado mata Kuka Takara sakawa Kafin Ta koma Bakin gado ta Zauna Tana Faman Sharan Kwallah Cikin Ranta Tana Tunanin bayan Kano bata inda zataje kuma,Danbatta..? Kai ina..? Bazai Yuyu ba Ko Naje chan Duk Daya ne Goyon bayan Dansu zasu yi Toh ina yakamata Naje..? Kai Tsaye Wata Zuciyar Tace"gidan Bilkisu..."

Tuna Haka yasa Ta saki Mirmishin Karfin Hali kafin Ta mike Har Ta kusa Ficewa Ta Tuna Da Wayarta tazo Ta Dauka Ta Fice Cikin kunar Rai Take Saukowa Daga Stairs tana Bin Dakin Mufeeda Dawani kallo har ta kariso Tsakiyar Falon kenan Sai ga Laila da Basma Sun Fito Daga Kichen Laila na goye da Naila Ita kuma Basma na Dauke da Wani Jug ahanunta Da alama Lunching Suke Shiryawa bayan su Kuma Iya ne Dauke da Wasu Manyan Food Flaks kallo Daya Farida Tayi musu Ta Dauke kai bata kara kallonsu ba Ta Nufi Hanyar Ficewa...
.

Cike da Mamaki Basma ke Fadin"Mommy ina zaki..? Afusace Farida ta Waigo Tana Watsama Basma Harara kafin Tace"Inda Ubanki Tahir ya aikeni zani Don Kakarki Goggo Abu.."tafada Idanuwanta Sun kada Sunji Jajir Daga Basma Har laila balle iya baki Suka Rike Suna salati acikin Ransu Iya ce Tayi Saurin Cewa"Subhanallah...Haba Hajiya Wannan zagin bai kama..."Dallah Malama ki Rufan baki Tsohuwar Munafuka.."Farida ta katse Iya Tana Fadin Haka ..

Ido kawai iya ta sakamata batare Datace komai ba,Baya Farida ta Dawo Tana Nuna Iya da Yatsa Kafin tace"Nasan Duk Abunda Tahir da Mufeeda Suka Taru Suka aikata kina sane ammh Dayake ke Tsohuwar Munafukace Shine kika munafunceni ko .? Toh kema kinsan Da sani Karshen Aikin ki yazo Acikin gidan,Zan Tafi na barma Tahir gidan Tunda Dama Burinku kenan Daga ke Har Mufeedan In Kinji ko kuma In kun Burgeni ku Maye masa Gurbina da Mufeeda kodon Taimakon Shegun ya"yan dazasuyi Ta Haifa.."Tafada Tana Watsama Iyan Wani kallo Lokaci Daya da Mufeeda Wacce Taji Mganar Faridan Ta Fito tana Tsaye Kofar Dakinta tana Kuka..

Wani Mirmishin Kuka Farida Tayi kafin ta Dauki Akwatunta ta Fice da Sauri Su Iya Suka Marata baya,Basma ce tafara Juyawa Zuwa Saman Dining ta iJiye Abunda Ke Hannunta da Gudu Ta Nufi Hanyar Dakinta tana Kuka Laila ta marata Baya Cike da Tsausayi Iya Kuwa Jikinta Asanyaye ta Karisa Jera Kololin Abincin Bisa Dining kafin Ta Waigo Tana kallon Mufeeda Cikin Kulawa tace"Kidaina yawan Kuka Mufeeda bashi da Alheri..Kiyi Hakuri Daman Dole zaki Fuskanci Haka Allah ya baki Ikon Karban Kaddaranki Hannun Bibbiyu.."Daga Haka Ta Shige Kichen Tana Shara Kwallah Aranta Tana Ji ko Farida bata Koreta ba ita da kanta zata Tafi Tunda Gidan ya Rikice komai Babu Dadi,Dama Babu Abunda Ta Nema Rasa na Rayuwa Domin Danta ya samu Aiki Ta Dalilin Tahir Kawai Karamcinene da Mutumcin shi yasa Take Zaune Dasu Haryanzu Ammh Lokaci Yayi da zata koma gida...

******

_Anguwan SARKI_

Bilkisu Kawar Farida ce Wacce Sukayi Mkranta Tundaga Secondry Har Zuwa Buk,Course Daya Suka karanta kuma Suka zo Sukayi Aure A kaduna sai dai Ita Bilkisu Ta Riga Farida Aure da Wajen Shekara Daya da Rabi,Tana Cikin Wadanda Suke Zuga Farida acikin Kawayensu Duk da ko Ita ba Haka take Tafiyar da Gidanta ba Ko yar Aiki bata Dashi sai Wata Tsohuwa mai Zuwa tana mata Wanke Wanke da Wanki Shima Sai Mijinta ya Fita tazo Tagama aikinta ta tafi ya"yanta Hudu yanzu Haka kuma bata Tsaida Haihuwa ba Ammh Tana Daga Cikin Wanda Suka Zuga Farida kan Ta Tsaida Haihuwa Hakannan Dama Duk Inda ka zama Sakarai sai Ana nuna maka Hanyar da zaka sake bi ka kara Sakarcewa.

Farida da Motar Ta Fita Zuwa Gidan Bilkisu Tana Driving Tana Kuka Lokacin Data Shigo Babban Falon Gidan Bilkisu Tana Zaune kan Kujera Tana Waya da kaninta Wanda zai yi Aure Sai ga Farida ta Shigo Tana kuka Abun yabata Tsoro da Hanzari ta yanke Kiran Ta Mike Tana Fadin"Fari Mezan gani Haka..? Mutuwa Akayi..? Farida bata samu zarafin mgana ba Illa Zubewa datayi jikin Bilkisu Ta saki kukan Datake yinshi Acikin Zuciya

Riketa Bilkisu Tayi Cikin Tashin Hankali Take Fadin"Na Shiga Uku Fari wai meya Faru..? Basma ce Ta Rasu ko Shi kanshi Tahir din ne Wani Abu ya sameshi Kaina ya Kulle Don Allah ki gayamin Abunda Ke Faruwa...? Farida Ta Dago Daga Jikin Bilkisu Tana Fadin"Billy Tahir ya Cuceni...Tahir ya gama Dani Billy Shida Mufeeda Sunci Amanata..."Take Fada Hawayenta Suna Kwararowa

Bilkisu Tace"Tahir da Mufeeda Kuwa Me Sukayi Kuma...? Tafada Cike da Mamaki,Kan Kujera Farida Ta Fada Tana Dafe kai kafin Tace,"Billy..." Bilkisu tace"Na'am...Farida.." Farida Ta Runtse Ido kafin Tace"Ciki Tahir yayi ma Mufeeda Mai Renon Naila.."Wani Zabura Bilkisu Tayi baya sai gata zaune gaban Farida Duka Hannuwanta akai kafin Tace"Kibari don Allah Farida..! Wani Tahir din Wai Abbansu Basma kikeso kice yayima yarinya Dakuka Daukota Daga Kauyensu Ciki...? Tafada Duka Idanuwanta Awaje.

Idanuwan Farida na Runtse Hawaye Suka kara Kwaranyomata kafin ta Gyada kai Cikin Kuka tace"Kwarai Da Gaske..."Nan ta Shiga labartamata Abunda ya Faru Tundaga Farko Har Karshe Ai sai Bilkisu Ta Mike Tana Fadin"Kutumar Uba..Lalle Tahir Mugun dan Wasa ne Wato Fyade yayimata baya Cikin Hayyacinsa Kajimin Matsiyacin Mara Mutumci da Kima Wato Shine Iyayensa Suka Taru Suka Marama Dansu baya Saboda Tacewa Ke kuma gaki banza Sakarya sai ki zauna  Araini Cikin Shege agabanki ko..? Farida na Share Hanci Tace"Abunda ke sakani Kuka kenan Billy Bansan Iya Adadin Tarayyar da Tahir yayi da Mufeeda Ba Bilkisu ammh Duk da An batamin ba Wanda yaga laifinshi sai ma laifina ake gani Daga Karshe Cemin yayi Mufeeda bazata bar Gidan ba Sai dai ni in nagaji na kara gaba."

Billy tace"Jar Uba..!Lalle Tahir Mugun Dan Iska ne,Haka yace...? Tafada Tana Girgixa Jiki batai Tunanin Magidanci kamar Tahir Tana Surfamai Zagi,Farida ta gyada kai kafin tace"Shine Dalilin Dayasa na Taho Tunda Umma da Abba ya mallakesu ko na Koma Bazasu Taba Saurarana ba Kirufamin Asiri ki barni na zauna Awajenki Har Tahir yagane Kuskuransa.."

Bikisu Tayi Shuru Cikin Nazari Farida Ta kalleta Tana Share Kwalla tace"Ko da kwai Mtsala ne..? Ajiyar Zuciya Bilkisu ta Sauke kafin Tace"Ba mtsala in ma Dashi Abban Su Walida ne,ammh komai ke zanyi mgana Dashi in ya Shigo Tashi na rakaki Dakin da zaki Sauka bazan bari ki koma gidan Tahir ba Domin Cuta kam an Cuceki Wlh Cikin Shege Acikin gidanki don Wulakanci ma Mafi kaskanci Mai Renon Yarku Gaskiya Tahir ya bata Wayonsa Kuma girmansa ya Zube Acikin Idanuwata.."Tafada Tana Daukan Akwatin Farida Tatashi Suka nufi Wani Korido Suna Tafe Billy na Tsinema Tahir Wanda Har Azuciyar Farida Tana Jin Zafi ammh bata da yarda zatayi Tunda Ita ta Tona ma kanta Asiri.

Daki ne Mai Dauke Da gado da Wardrope sai Madubi da Tiolet ba laifi ko"ina Tsab Tsab nan Bilkisu Ta Fita ta barta Zuwa Kichen Ta Zubomata abinci Domin Duka yaran nata Suna Islamiya Fargaban Bilkisu Daya Megidanta Wanda yake da Zafi Sosai In Har yaga Farida tadawo Gidan sai yaji Dalili Kuma Akwai sanayyah Sosai Tsakaninshi Da Farida Har da Shi kanshi Tahir din Ita kuma bataso ma Tahir yasan Farida na gidanta sai yagama Wahalan Nemanta tukunna Hardai ta Zuboma Farida Abinci bata samu Mafita ba Tana ta Dai Tufka tana Warwara Tsoro ya cika Ranta Saboda Tasan Abban Walida bai da Wasa.

****

Tahir kuwa bai da lbrin Farida bata gidan Domin Bai Dawo Daga Office ba sai bayan Isha"i Suna Zauna Suna Duba sakon Wasu Sabbin Samfur din Motoci Cikin Laptop din Tahir din Shida Ishaq basu ma gama ba Suka Rabu Akan Tahir zai karisa Komai kafin gobe koda ya Dawo ya Biya ya Siyo Furanshi yana Shigowa,kafin ya Shiga Dakinsa ya Fara Biyawa Dakin Su basma ya Tarar dasu suna kallon Cartoon Oyoyo Sukayimai ya Rumgumesu yana Tambayansu ko Sunci Abinci Tsaraban Furan Daya Siyo ya basu kulli Daya kafin yayi musu Saida Safe Daganan ya Shiga Wajen Su bassam ya samesu Shida Muda Suna buga Game,nan Suma Suka Tashi Suna mai oyoyo Shafa kansu yayi yana Tambayansu lafiyansu Suma Furan Guda Daya ya basu kafin Daganan ya Fito yaja musu kofa,Dakin Mufeeda ya kallah har zai Wuce sai kuma ya kasa Cikin Sanyin Jiki yanufi Dakin Nata yana Tura Kofar yaganta Kwance Kundundune chan Tsakiyar gado Cikin bargo Tana barci Bai Shigo ba Daga Kofar Dakin ya Tsuramata ido yana kallon Karamar Fuskarta Cike da Tsausayi Wani Abu na Tasomai Daga Kasan Zuciyarsa Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin ya koma Da baya ya jamata Kofar.

Yana Shirin barin Falon ne yaji Muryan Iya na Gaisheshi Da Sauri ya Waigo yana amsawa Cikin Sanyin Murya Iya tace"Alhaji Naila na Wajena Saboda ganin yanayin Mufeedam.."Gyada kai kafin yace"Bakomai kin kyauta.."Har ya Juya ta Sake Fadin"Amh Alhaji dama Ina son mgana dakai in ba Damuwa.."Cikin mamaki Tahir ya Waigo kafin yace"Mgana kuma...? Toh Shikenan iya Kibari da Safe kafin na Fita Ki Tunamin yanzu Dare yayi.."Jinjina kai Tayi kafin Tace"Shikenan Allah ya Tashe mu lafiya.."Da Ameen Ta amsa Har ta Juya zata Tafi ya Kirata ta Waigo ya mikamata Fura guda Daya karba Tayi tana mai Godiya Daganan ya mata sai da Safe ya Haura sama ko kallon Dakin Farida baiyi ba.

Sai da yagama Duka al"adansa na Kwanciya kafin ya Dauko Laptop dinsa  ya Dora Bisa Gado ya Haye Tsakiyar gadon ya Cigaba da aikinsa Lokaci bayan Lokaci yana Kurban Furar Daya Tsiyaya Cikin karamin Kofin glass bai kwanta ba sai Wajen 1pm kana ya Kashe komai ya koma ya Kwanta bayan yayi Addu"ar barci.



*Don"t Forget to Vote,Share,comments and like..*


*SHAKIRA*
A.ALTO*
*NANNY...!*
      (Mai Reno..)

*Alƙaluman:*✍🏻

*AISHA ALTO💞*
*JAMILA UMAR (Janafty💕*

_Don"t Forget to Follow us on Wattpad:Janafnancy13 or Aisha Alto Alto_

*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔*
*KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*

      *BABI NA GOMA SHA SHIDDA*

"""Tahir Ya Fito Cikin Fitanshi na Zuwa Office yana Sanye Cikin American Suit Dinsa,Black and White ya matse Wuyansa da Tie yana Dauke da Brifcase Dinsa Lokacin daya Sauko Kasan Falo Ya Iske Basma da Laila da Bassam da Mudu suna zaune Bisa Dinining Suna Breafsat Suna ganinshi Kowanne ya Washe baki Suna Fadin"Daddy gud Mrning...?

Karisowa yayi yana Fadin"Mrning my Childreen How was Ur Nite.."Suka amsa da Fine Kan Basma da Laila ya Dafa kafin yace"Laila da Mudan Hutunku ya kare Fa Tun last Week ko .? Kai Suka gyadamai alamar Hakane Numfashi ya Sauke kafin yace"Ok Bari na Dawo Kila ko Zuwa Gobe Ko Jibi Saturday Sai mu maida ku gida ko..? Kallon Junansu Sukayi kafin Suce"Toh Daddy.."Suka Fada Suna Dariya Jin Harda Bassam zasu Rakasu gida.

Teburin yabi da Kallo kafin yace"Ina iya da Mufeeda Bazasu karya bane..'Basma ce tace"Bamu sani ba Daddy ammh iya Ta Dibarma Mufeeda Ta kaimata Daki Tundaga nan Data Fito sai Ta Koma Dakinta Bamusan Abunda Ya Faru ba.."Basma Taa Fada Tana kallon Tahir din Kafin ya samu Zarafin Mgana Bassam ya karbe da Cewa"Eh mana Daddy Gidan Duk ba Dadi Mufeeda bata Fitowa yanzu Iya ma kamar Akwai Abunda ke Damunta yau Duk kamar ba Ita ba.."Yafada cike da Kewa Irin Abun bayamai Dadi.

Shuru Tahir yayi kafin ya saki Ajiyar Zuciya yace"Ikon Allah Meyafaru ne..? Basma tace"Bamu sani ba Daddy Kila Ita da Momy ne kafin Tatafi.."Da kallo yabi Basma Baki bude kafin Yace"Tatafi..? Faridar bata nan ne..? Ina taje..? Ya jero musu Tambaya Lokaci Daya.

Basma ta Zakuda kafada kafin Tace"Bamu sani ba Daddy Tadai Tafi Har iya ta mata mgana Ta kusa Zaginta.."Ido ya zaro yana kallonta ganin Haka yasa ta Shiga maidamai Abunda ya Faru,Jinjina kai ya Hau yana Jin Wani Bakinciki na Ratsashi,Wato Duk Bayan Rusamai Rayuwa da Farida Tayi bai Isheta ba sai Tabi gari Ta gama Tonamai Asiri ko..? Domin yana da Tabbatacin Bata je Kano Domin bada Safenan ya samu Wayar Umma,bayan Sun gaisa Ta kara bashi hakuri game da Farida Tare da Fatan zasu zauna Su Rungumi kaddaransu kuma yanzu bads Dadewa ba Suka kara Mgana Da Abba duk da Mganar Business ne ammh da Farida Taje kano Jiya Dayaji lbri,Shi ba Wannan bama Damuwarshi naga Goggo Abu Domin Innaro da Ashe Sun Kirashi Awaya Suna Sanar Dashi ya Kokarta yazo Domin Baba Hakimi yayi mugun Fushi da goggo Abu baya Shiga Dakinta kuma yahanata Shigowa Turakarsa kuma Baya Shiga Sabgarta Tayi kuka Tanuna Nadamarta Ammh Baba Hakimi yayi Burus Da Ita Innaro ma Data Nemi Shiga Mganar Hakimi yaja mata Kunni da Kakkausan Muryan Kan in Ta sake ta Kara Shiga Mganar Itama zai Jingine ta Gefe Kamar yadda ya Jingine Goggo Abu..

Jin Haka yasanya Goggo Abu Ta Rikice sai Zazzabi da Ciwon kai Kafin kace kwabo ta Kwanta Ciwo koda Likita yazo Dubata sai Iske Jininta yayi bala"in Hawa nan Dai ya Dubata ya bata Mgunguna,ammh Duk da Haka Baba Hakimi bai Sakin ma Ra"ayinshi ba Koda ma akayi Haka ko Shashen Goggon Abu bai leka Ba gefe Daya kuma Inna Fulera na gida kwance ba lafiya Tun bayan Dawowarsu Hakimi ne Dayaji Lbri yasa Innaro da Ashe Suka Tafi Suka Dubata itama nan Suka Isketa jiiki yayi Zafi Maman lantana ke Kula da Ita Koda Suka zo suka Fada Hakimi bai Bata Lokaci ba ya Saka Aka kaita Asibitin garin Danbatta,Itama dai Damuwar ne ya Rafketa Hawan Jininta ya Tashi Gado Aka bata sai da ta Kwana Daya da Wuni kana aka sallameta Saboda Haka gabadaya Hankalinshi ba"a Kwance yake ba yana Jin Damuwarsa na Saka Ahali Dadama Damuwa gashi ya Lalatama Mufeeda Rayuwa da Farincikinta Gabadaya Saboda Shi bata da Sakewa kamar baya.

Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin yace"Umh..Bari nayi mgana da Iya Tukunnah.."Yafada yana Sauke kanshi kasa Cike da bakinciki mai yawa yakama Hanyar Dakin Iya kenan Basma tace"Daddy..." Ya waigo yana kallonta cikin Dankwabe kai da Marairaicewa Tace"Ka fara Shiga Wajen Mufeeda First Daddy..."Tafada Tana Hada Hannuwanta alaman Roko..

  Tsam yayi yana kallonta Cike da Mamaki kafin yace"Alright..."Juyawa yayi zuwa Dakin Mufeeda ammah Kuma Acikin gangar Jikinsa babu karfin Gwiwa Turo kofar yayi Ya Shiga da Siririyar sallama bata Jishi ba Tana Zaune Dirshan Akan gado Naila na kan Cinyarta Kanta ba Dankwali sai Kitson Shikon Dake kanta Wata doguwar Rigar Roba ce ke Jikinta Kirar Bhrain,Kofin Shayi ne Ahannunta Tana Sha gefenta kuma Farantin Silba ne Cike da Kwai da Dankwalin Turawa Wanda Iya ta Kawomata Naila ce ke mika hannu Tana yafiton kofin Shayin Cikin Sanyin muryanta tace"Nailata zaki Sha Shayi ne.."Kamar tasani ko Ta daga kai Dariya Tayi Har Fararen Hokoranta Suka bayyana Kofin takafa mata abaki Tana bata kadan Kadan Tana Sha,Gefe Daya kuma tana gutsurin kwan Tana bata Tana Fadin"Zan Cigaba da baki Abincin aboye Nailata bana so kiyi Rama.."Itako Naila batamin Jinta malulan kwanta Take Cike da Jin Dadi.

Tahir Dake Tsaye bakin Kofa ya saki baki da Hanci yana Kallonsu Gefe Daya Wani Tsausayin Mufeeda ke kara Tasiri Acikin Ranshi ga Naila Wacce in ya kalleta sai yaga ko Hakkinta Allah ya kama Farida dashi bazata Taba Jin Dadin Duniya ba,Ganin Basuji Shigowarsu ba ya Sanya yayi gyaran Murya da Sauri Mufeeda Ta Dago Daga bama Nailan kwai abaki ganin Tahir Tsaye sai ya kara Rikita ta Rude,Ta Riko Naila Lokaci Daya Tana Kokarin Ijiye Kofin Shayi bisa Side Drower sai bai zauna Dakyau ba Da Hanzari Tahir ya Isa Wajen ya Rike Kofin Lokaci Daya yana Dauke Farantin kwan Tsurama Mufeeda ido Cikin Cikin Sanyinsa yace"Shiii..Is ok..Relax.."

  Ya Fada yana Daidaita Natsuwarsa yana kuma kara gyara zaman Brifcase dinsa Dake Hannunsa,Cikin Kunya da Wani Nauyi Mufeeda ta sadda kai Tana Fadin"Ina..ina kwana Daddy..."

Bai amsa ba sai da ya Ijiye Brifcase dinsa gefen gadon Mufeeda ya mika Hannu ya Dauki Naila Wacce Tunda ya Shigo Take mikomai Hannu kafin ya amsa yana Fadin"Lafiya lau kin Tashi lafiya..? Ya fada cikin Kunya kadan Domin bayason ma yana kallon Kwayan Idanuwanta.

Itama Kunyar Takeji Shiyasa Bata Dago ba tace"Lafiya lau.."Shuru ya biyo bayan Mganar Mufeeda,Wacce kanta ke Kasa Duk kunya Ta gama kamata na Halin da Tahir ya Isketa Wata Zuciya tace"Me zaki boye Abunda Yagama Dake.."Dam Take taji Hawaye Sun Cikamata ido Shi kuma cikin Nazarinta ya Furta"Ya Jikin ki..? Kina jin Wani Ciwo Acikin jikinki..?

Shuru Tayi kafin ta girgiza mai Batayi mgana Illah Hawayen Data Rikewa ne Suka zubomata,Tsam yayi yana kallonta tana Share Kwallah cikin Tsausayawa ya Durkusa kan Gwiwoyinsa yana Rike da Naila yace"Don Allah kiyi Hakuri mufeeda kiyafemin laifin Dana aikata agareki Hakika na zama azzalumi Kuma naci Amana,Ina Jin kunyar kaina Mufeeda.."Yafada Cikin Rawan Murya.

Dagowa Tayi ganinshi Durkushe agabatan Yasa Tace Da Sauri."A"ah Daddy Meye Haka..? Don Allah katashi Ni Tun Daren da Abunda ya Faru Zuciyata ta yafemaka bayan ta tabbatar bazaka Taba aikata Haka da gangan ba.."Tafada kai Tsaye Tana Dauke Hawayenta Mikewa yayi Jikinsa Asanyaye kafin yace"Nagode Mufeeda,Ki sanar da Iya duk sanda Kikaji Wani Chanji Ajikin ki kinji ko .? Cikin Ladabi Ta Daga kai Da cewa"Toh Daddy.."Dan Mirmishi yayi kafin yace"Gud gal..Kuma kiyimin Alfarma zaki saki Jiki kamar baya,Kinga su Basma basajin Dadin ganinki Haka.."Kanta na Kasa Ta Dago da Niyyar mgana Suka Hada ido yadda idanuwansa ke Narkar da Zuciyarta yasa Tayi Saurin Sadda kai Tana Fadin"Insha Allahu Daddy.."

Mganarta Tamai Dadi Cikin Farinciki ya Furta.."Allah yayi miki albarka,ga Diyarki zan Fita aiki kada na Mkara.."Yafada yana  mika mata Naila Wajen saka Hannuwanta ta karba Hannuwansu Suka Hadu Waje Daya Wanda Dukkansu sai da Sukaji Wani Shock Atare,Mufeeda Tayi Saurin Jan Hannunta Tana barin Jiki Shi kuma yayi Saurin Doramata Naila kan Cinyarta,Lokaci Daya yana Daukan Brifcase dinsa ya Fice Daga Dakin da Sauri da Kallo Mufeeda ta bishi Zuciyarta na Bugawa batasan Dalili ba Tun Zuwanta gida nan Indai zata ga Daddy Toh Zuciyarta Ta hau buguwa kenan da Sauri Sauri kamar Wacce Tayi Gudun Tsere..

Yana Fitowa yaci karo da Iya Dauke da Ghana must go Cike da Kaya Su basma na Tambayata ina Zata,taci ko Lullubinta Cikin Mamaki ya Karisa Kusa Dasu sai Dai Sukaji Muryanshi yana Fadin"Iya lafiya kuwa..? Ina zaki da Wannan kayan..?

Jin Muryansa yasa Iya Ta Durkushe Kasa Tana Fadin"Alhaji kayi Hakuri da Abunda zan Fadamaka,Na yanke Shawaran zan bar aiki agidan nan bawai Dom kun Saba min ba ko kuma kuna min Wani abu A"ah sai domin Tsira da Mutumcina.."Cikin Wani Haushi Tahir ya Furta.."Kan Issues din Farida ne ko..? Yafada Cikin bacin Rai bai bama iya Zarafin mgana ba yace"Tunda Muke Zaune Dake Acikin Gidan nan Iya na Taba Saba Miki..? Iya ta Girgiza kai Tana Sharan Kwallah Ya cigaba da Fadin"Su basma fa..? Nan ma ta girgiza kai ya kada kai yana Fadin"Toh Tunda babu Daya iya babu Inda zakije matukar Ni Tahir Mansur Danbatta ina Raye,Koda Farida Take Takama Ta Dalilinta Kikazo Gidan nan bata da Ikon Koranki Saboda Nima karkashin Ikona Take,saboda Haka mganar Gaskiya babu Inda zakije kina Tare damu Mudin Rai.."Yafada kai Tsaye kafin yace"Basma,Laila ku kama Jakar iya ku maida mata Ciki ni na Fita sai na Dawo .'Yafada kai Tsaye yana Wucewa Cike da Haushin Farida ji yake kamar ya yanke Duka alakan Dake Tsakaninsu Wata Zuciya tace"Not Now Tahir..Juz leave her to pay Wht She Didt For u.

Iyya bata da yadda

Please Login or Register in order to submit comment