Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mufeeda..amma karki dubi munin abunda nayi miki ki dubi girman alkhairina agareki ki yafe min kuskurena..nasan na cutar dake sakacina ya jefaki cikin wani yanayi, na cuci rayuwarki...Kuka ya hanata ƙarasawa. Da sauri Mufeeda ta faɗa jikinta itama ta fashe da kuka tana faɗin "Bakiyi min komai ba Momy..kuma duk abunda ya faru dani daga Allah ne dama dole sai ya faru dani ban isa na kauce masa ba, kuma na ɗauki hakan a matsayin ƙaddarata, don haka ki daina cewa na yafe miki bakiyi min komai ba, nice ma zan roƙeki yafiya...Don Allah ki yafe min, kuma duk abunda kika yi min wanda na sani da wanda ma ban sani ba duka na yafe miki..." Ta faɗa tana ƙara ƙanƙame Faridan a jikinta, ƙara rungumeta Faridan tayi itama suna sharɓan kuka, Tahir dai na tsaye yana kallonsu jikinsa duk yayi sanyi, a hankali Farida ta janye Mufeeda a jikinta ta durƙusa agaban Iya itama ta roƙeta ta yafe mata sannan ta durƙusa agaban Innaro itama ta yafe mata sannan Basma da Bassam suma duk suka yafe mata. Nan take taji ta fayau zuciyarta tayi mata wasai taji kanta kamar an sauke mata wasu tulin kaya.

Haka a ɓangaren Tahir yaji daɗin abunda Faridan tayi sosai a ransa har hakan ya nuna a fuskarsa kuma yana fatan Allah yasa hakan ya zama gaskiya har a zuciyarta tayi tuban ba tuban muzuru ba.

Miƙewa tayi a hankali ta ƙarasa inda gadon jariran yake inda suke ciki a kwance luf abinsu ta tsaya tana murmushi ƙwallah na taruwa a cikin idanunta ta buɗe ta ɗauko macen ta riƙe sannan ta ɗauki namijin shima ta haɗasu ta rungume a jikinta tana jijjigasu kafin kuma ta cirosu daga jikinta ta tsura musu ido tana kallonsu har bata san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba, ƙarasa tayi gaban Tahir da fara'a a fuskarta tana faɗin "Abban Basma zoka gani, wallahi yaran nan tamkar Basma da Bassam lokacin dana haifesu suna jarirai.." Ta faɗa tana ƙarasawa gabansa, yana dariya ya karɓi namijin a hannunta yana kallonsa yace "Wallahi haka nace nima.." Innaro tace "Nima dai haka nace.."
Tahir yana murmushi yace "Ai kamarsu da 'yan uwansu ce ta fito sosai." Ya faɗa yana miƙa mata yaron. Karɓarsa tayi ta miƙa masa macen tana faɗin "Yanzu da wane suna za'a dinga kiransu kenan..?" Ta faɗa tana kallonsa, yana dariya yace "Mufeeda wane suna za'a dinga ce musu..?" Ƙara sunkuyar da kanta ƙasa tayi cike da kunya tana faɗin "Duk abunda kuka zaɓa yayi Momy.." Ta faɗa tana murmushi. Farida tace "To shikenan, namijin zamu dinga kiransa da Ayman macen kuma mu ce mata Airah.." Da murna Basma tace "Yauwa Momy...Wallahi sunan yayi mana daɗi sosai..kuma ya dace dasu..Allah ya raya mana ƙannen mu.." Da Ameen duk suka amsa, kafin daga nan suka shiga hirar yanda taron suna da bikin tariyar zata kasance, kowa ka gani fuskarsa cike da fara'a da farin ciki take, har ta su Basma da Bassam ma walwalarsu ta ƙaru a wannan daren, sai farin ciki da annashuwa suke.

Sun daɗe sosai a ɗakin suna hira har ƙarfe 10:30pm kafin Tahir da Farida sukama su Innaro da Iya da ita kanta Mufeedan data fara barci sallama suka fice tare dasu Basma da Bassam kowa ya shige ɗakinsa bayan sun musu sallama suma, suka nufi bedroom ɗin Tahir.

Suna shiga ciki ta janyosa jikinta ta rungumeshi ta baya ta zagaya hannayenta a saman cikinsa tana shafo ƙirjinsa a hankali cike da wani irin salo, juyo da ita yayi gabansa ya tsura mata idonsa, kasa jurar irin kallon da yake mata tayi ta zame hannunta ta faɗa jikinsa ta ƙanƙamesa ta fashe da kuka mai tsuma rai da zuciya tana ƙara bashi haƙuri.

A hankali ya fara shafa bayanta alamar lallashi yana hura mata iskar bakinsa a cikin kunnenta cike da wani irin salo mai tafiyar da ruhi haɗe da zuciya mai ƙara azalzala wutar ƙauna, ƙara shigewa jikinsa tayi ta lafe tana karɓar saƙonsa, a hankali ya fara tafiya da ita zuwa gurin gadon dake ɗakin tana jikinsa a narke tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa mai sanyaya zuciya, a haka suka isa gaban gadon, cike da shauki ya ɗagata cak ya ɗorata a saman gadon ya kwantar da ita flat, sannan ya hau kai shima bayan ya zare rigar shadda dake jikinsa yayi saura daga shi sai dogon wandon kayan.

Wani irin shauki da tsantsar soyayyar mijinta Farida taji tana ƙara kamata, tana daga kwancen tana kallonsa ya hayo saman gadon ya fara ƙoƙarin zare mata rigar jikinta, wani irin daɗi da farin ciki mara misaltuwa Farida taji sun kamata lokaci ɗaya daɗi ya baibayeta ta ɗago ta faɗa jikinsa tana ji a ranta yau zata gwada masa tsantsar ƙauna wacce bata taɓa nuna masa ba, zata nuna masa tsabtatacciyar ƙauna mara iyaka wacce babu algus a cikinta, zata sa yayi alfahari da ita ta tsaya a ransa ya kasa gogeta a zuciyarsa. Cike da salo ta jawo makunnin wuta ta kashe wutar ɗakin, ɗakin yayi duhu kaɗan ta miƙe ta sauka daga kan gadon ta cire rigar da kanta yayi saura daga ita sai pant da bra suma a hankali ta zaresu ta koma saman gadon ta haye jikin Tahir dake zaune mamaki ya gama cikasa ya zuba mata ido kawai yana kallonta, ganin irin kallon da yake mata mai cike da mamaki yasa ta ƙara zagewa ta jawosa jikinta ta haye saman cinyarsa a hankali ta fara shafo fuskarsa zuwa leɓensa da wani irin salo kafin ta ɗago haɓarsa tana kallon cikin ƙwayar idanunsa ta haɗa bakinsa da nata, wani irin lumshe idanu Tahir yayi cike da jin daɗi ya ƙara matso da ita jikinsa sosai ya kamo tattausan harshenta ya fara mata wani irin tsotsa mai tayar da hankali dasa mutum mantar dashi kansa waye.

Sake zagewa Farida tayi sosai ta kamo harshensa ta shiga aika masa da wani lafiyayyen kiss mai kashe jiki da zuciya, Tana yi tana shafar sumar kansa tana tura yatsunta ciki tana masa wani irin salo kamar tafiyar tsutsa, a haka ta sauka har kan gadon bayansa tana shafa bayan tana masa tafiyar tsutsa kamar tana masa susa, idan ta ja har tsakiyar bayansa sai ya gantsare ta dawo da hannunta sama tana shafo ƙeyarsa, in banda sauke numfashi da gurnani babu abunda Tahir ke yi, hakan ya ƙara mata ƙwarin gwiwa ta zage sosai ta dage ta shiga nuna masa tsantsar ƙauna mai cike da nuna tattali da tsantsar so mai tsayawa a zuciya.

Duk wani salo mai kashe zuciya da saka rai cikin tsantsar buƙatuwa, sai da Farida tayi amfani dasu gurin kashe jikin Tahir ta mantar dashi kowa da komai a wannan dare, ta zage ta nuna masa cikakkiyar kulawa da tattali.

Wani al'ajabi da mamakin Farida ne ya kama Tahir, sagale ya tsaya kawai yana kallonta a ransa yana tambayar kansa dama kenan ta iya komai take tsaya masa kamar gunki ta barsa yayi kiɗinsa yayi rawarsa? Ko ta nuna masa bata son komai da yake mata ita ta gaji bata iya ɗaukar lalurarsa? Lallai Farida yau ta bashi matuƙar mamaki, kuma yaji kimarta da darajarta sun fara dawowa a zuciyarsa.

Sosai Farida ta zage ta kafa tarihi mai tsayawa a zuciyar Tahir a wannan dare, tayi duk abunda tasan zai faranta ransa ya manta da komai da kowa sai ita. A ɓangaren Tahir kuwa shima tsayawa yayi tsam ya nuna mata tsantsar kulawa mai dasa farin ciki mara gushewa da walwala mai matuƙar tasiri a zuciyar duk wasu ma'aurata masu so da ƙaunar junansu.


Washegari da sassafe Farida ta tashi bayan sunyi wanka da Asuba sunyi sallah Tahir ya koma barci ta fice ta nufi ɗakin Mufeeda, lokacin ko tashi Mufeedan bata yi ba tana ta sharar barci abinta, sai Innaro dake zaune akan darduma tana lazumi Iya kuma na kichen zata dafa ruwan wanka, bayan sun gaisa da Innaro ne ta fice taje ta haɗo ruwan zafi a babban robar wanka, Innaro tace ta bari za suyi musu wankan taje ta kula da mijinta, amma Farida tace A'a su bari ita zata wanke 'ya'yanta tas. Haka kuwa akayi ta ɗauko jariran a cikin gadonsu ta fara yiwa Ayman sannan ta yiwa Airah itama, ta shiryasu tsab cikin lafiyayyun kayan sanyinsu masu kyau da tsada, Innaro na zaune tana kallonta gwanin sha'awa. Sai data gama musu sannan ta fesa musu turare mai sanyin ƙamshi ta sakasu a cikin shawul ta miƙawa Innaro su sannan ta miƙe ta ɗauke robar ta kai Toilet d'in Mufeeda ta zubar da ruwan ciki, sannan ta sake haɗawa Mufeeda ruwan wankan itama ta fito ta tasheta, ta cire kayanta suka shiga toilet. Farida Ita ta taimakawa Mufeeda tayi mata wankan jego tsab ta gasata sosai Mufeedan sai sunkuyar da kai take tana jin kunya amma ita Farida ko a jikinta ta zage ta gyarata tas ta rufa mata babban tawul suka fito..Suna fitowa ta zaunar da ita a bakin gado ta ɗauko mai ta bata ta shafa kafin ta buɗe akwatinta ta ciro mata wata atamfa riga da zani ta ajiye mata, ta koma ta ɗauko humra da kulacca da Innaro tazo mata dasu ta bata ta shasshafa a jikinta sannan ta saka kayan ta zauna ita kuma Farida ta fita. Bata jima da fita ba ta dawo ɗauke da babban kofi da kayan tea a hannunta, Mufeeda dai sai binta da kallo kawai take tana jin tsananin farin ciki a ranta, Farida kuwa tana jin bala'in kishin Mufeeda a ranta amma tana dannewa kada a gane, a haka ta haɗa mata tea mai kauri ta miƙa mata ta tura mata bread da filet ɗin soyayyen kwai ta tasata gaba sai da taci tayi dam zufa sai keto mata take, haɗa kayan Farida tayi ta fitar dasu ta kai kichen sannan ta dawo ta haɗa kayan da Mufeedan ta cire da waɗanda ta cirewa jariran ta fita dasu can bayan gidan ta wankesu tsab ta shanya sannan ta dawo lokacin ƙarfe 8:20am tace Mufeedan ta koma ta kwanta ta huta bari taje su gama haɗa breakfast da Iya, Innaro ta amsa tana sa mata albarka ta fita a ɗakin ta nufi kichen.


Lallai Farida ta sauya sosai kuma duk wanda ya santa a ranar ya ganta dole zai gane hakan, Iya ma sai kallonta take suna aiki, tare suka gama haɗa komai suka jera a dinning table kafin ta nufi bedroom, tana shiga ta samu Tahir ya tashi yana Toilet yana wanka. Tuɓe kayan jikinta tayi itama ta shige toilet d'in don suyi wankan tare.

Mintuna talatin suka ɗauka a toilet d'in sannan suka fito ɗaure da tawul a jikinsu suna rungume da juna suna dariya, ita ta shafa masa mai ta shiryashi tsab sannan shima ya tayata ta shirya ta feshesu da turarensa mai daɗi da sanyaya zuciya ta ɗauko hularsa zanna bukar ta kafa masa yayi kyau sosai tana kallonsa tana jin wani kishi na taso mata tayi saurin kawar dashi ta riƙo hannunsa tana murzawa a nata cikin kwantar da murya ta fara faɗin "Abban Basma ya kamata fa a siyo kayayyakin da Mufeeda zata saka tunda tare za'a haɗa da taron suna da fitar biki..." Ta faɗa tana sumbatar tsakiyar tafin hannunsa, lumshe idonsa yayi ya kamota jikinsa yana faɗin "To shikenan, zan turo miki kuɗi ta account ɗinki sai ku sayi abunda ya dace.." Ya faɗa yana sakar mata kiss a goshinta, tana murmushi ta kama hannunsa suka fice daga ɗakin suka sauka ƙasa.

Sai da suka shiga ɗakin Mufeeda ya dubasu ita da yara suna ta barci suka gaisa da Innaro da Iya dake shirya Naila kafin suka fice bayan Farida ta ɗauki Naila tace su Innaro su fito Dinning suci abinci, suna fitowa daga ɗakin suka samu Basma da Bassam sun fito daga ɗakinsu wanda da alama sun shiga su gaishesu ne basu samesu ba, da murna suka nufesu suka faɗa jikinsu, Tahir ya ɗago Basma daga jikinsa yana murmushi yake faɗin "Karki kayar da Daddy mana..ko bakisan kin girma bane..?" Ya faɗa yana jan kumatunta, turo baki tayi ta duƙa ta gaisheshi ya amsa cikin sakin fuska tare da shafa kanta, sannan ta juya ta gaishe da Farida dake kallonsu tana murmushin jin daɗin gyara rayuwarta da tayi, shima Bassam ya gaishesu kafin Tahir ya kama hannunsu yace suje Dinning su karya, da sauri Basma ta zame hannunta tana faɗin "Zanje na ga ƙannena da Aunty Mufeey tunkunna Daddy.." Ta faɗa tare da ƙoƙarin rugawa da gudu, saurin kamota Farida tayi tana harararta tace "To barci suke yi..baza kije ki tashesu ba.." Ta faɗa tana nufar dinning, ba don Basma taso ba tabi bayanta tana turo baki, Tahir dai na kallonsu yana murmushi bai ce komai ba.

Sai da suka gama karyawa sannan Farida ta rakashi harabar gidan ya shiga mota Garzali yaja har suka fice tana ɗaga masa hannu kafin ta koma cikin gida ta shiga bedroom ɗinsa ta gyarashi tsab ta fesa room freshener mai ƙamshi ta saka turaren wuta mai daɗi ta janyo ƙofar ɗakin ta fice..tana saukowa taji alert ya shigo wayarta tana dubawa taga transfern kuɗi ne masu yawa Tahir yayo mata tana murmushi ta nufi ɗakin Mufeeda tace Innaro ta shirya zasu fita kasuwa.

Haka kuwa akayi ita da Innaro suka je kasuwa ta narkowa Mufeeda siyayya sosai ita da jariranta ta haɗo musu kaya masu kyau da tsada, a nan kasuwar ta samu haɗaɗɗen shagon ɗinki ta bada kayan Mufeeda ta zaɓar mata ɗinkuna masu kyau da ɗaukar hankali, bayan ta biya kuɗin ya faɗa mata ranar da zata zo karɓa suka dawo gida.

Duk waɗannan abubuwan da Farida take yi kawai tana daurewa ne don tayi alƙawarin ta gyara halayenta, bazata ƙara yin abunda tasan zai sa wani yaga baƙinta ba balle mijinta da iyayenta da 'ya'yanta su tsaneta su dinga jin haushinta ba, saboda haka ma duk wasu ƙawayen banza tayi watsi dasu ta daina bi ta kansu, yanzu ta gyara rayuwarta zata tsaya ta kula da mijinta da 'ya'yanta.


Bayan kwana biyu da haihuwa Goggo Abu tazo duba Mufeeda da yaran taji daɗin yanda ta ga Farida ta koma ta saki jikinta tana ta kula da Mufeeda da yaranta nan ta tarasu tayi musu nasiha sosai mai ratsa jiki da zuciya.


*BAYAN SATI ƊAYA...*


Ana gobe taron suna da yamma Farida ta ɗauki Mufeeda suka tafi cikin gari ta kaita wani haɗaɗɗen Saloon inda take zuwa aka tsantsara mata ƙunshi da kitso ta biya kuɗin suka dawo gida. Suna zuwa suka tarda Ashe dasu Muda da Laila sun zo, nan Ashe tayi ta yaba kyaun da Mufeedan tayi, ita dai Farida sai dai tayi dariyar yaƙe kawai tana ƙoƙarin danne abun data ji yana taso mata.

Washegari tunda sassafe Zahra matar Ishaq da 'ya'yanta suka zo. Nan suka haɗu dasu Innaro da Iya da Farida da Ashe suka shiga aiki baji ba gani, don ba wani taro za'ayi sosai ba, iya yasu yasu ne kawai suka cika gidan.
Farida da kanta ta kira mai kwalliya tazo har gida ta tsantsarawa Mufeeda kwalliyar data ƙara fito da ita tayi kyau sosai, ta ɗauko mata wani haɗaɗɗen leshi blue mai adon stones cikin waɗanda aka ɗinko mata ta bata ta saka tayi cacas a ciki, nan kyaun Mufeeda ya ƙara fitowa sosai ita da kanta Farida sai da ta kalleta ta ƙara kallonta don gani take kamar ba Mufeedan data sani bace a gabanta, Farida da kanta tayi mata lafiyayyen ɗaurin ɗankwalin daya sake fito da kyawun fuskarta tayi fayau abinta sai ɗaukar ido take tana ƙyalli. Haka jariran suma expensive kaya aka saka musu haɗaɗɗu masu kyau da tsada sai ƙamshi suke suna walwali abinsu, Basma da Bassam ma da Naila sunyi gayu abinsu sun sha kyau suna rungume da ƙannensu Ayman da Airah sun hana kowa ɗaukarsu sai dai ka gansu a hannayensu duk inda sukai dasu Naila na nan nane dasu itama.

Taro yayi taro an gama lafiya an tashi lafiya, sai dare Ishaq yazo ya ɗauki Zahra da 'ya'yansa bayan Farida ta haɗa musu kayan suna cike da leda ta rakasu har gurin mota sukayi sallama ta koma cikin gida, don yau duk a gajiye take ko hirar dare da suka saba yi a ɗakin Mufeeda bazata tsaya yau ayi da ita ba, wanka kawai zatayi ta haye gado kafin kuma uban gayyar shima ya dawo.


Washegari Ashe dasu Muda da Laila suka koma Ɗanbatta suma, nan Innaro da Farida da Iya suka cigaba da kula da Mufeeda da yaranta, Basma da Bassam kuwa indai suna gida kullum suna nan liƙe da ƙannensu haka Naila sai tasa rigima itama sai ta ɗaukesu.

Wannan kulawar da Farida ta gani kowa na ba Mufeeda shiya ƙara saka mata kwaɗayin son taga ta sake haihuwa itama, don taga duk wata kulawar Tahir da tattalinshi ya ɗorasu duka ne akan Mufeeda da 'ya'yanta.

Ranar da Mufeeda tayi arba'in a ranar Innaro tace bazata ƙara kwana a Kaduna ba, itama Ɗanbatta zata koma, haka kuwa akayi Tahir da Farida suka haɗa mata sha tara ta arziki da kaya niki niki Garzali ya maidata.




*Anitha...*
*Aisha Alto...*
*NANNY...!*
      (Mai Reno..)

*Alƙaluman:*✍🏻

*AISHA ALTO💞*
*JAMILA UMAR (Janafty💕*

_Don't Forget to Follow us On Wattpad: Janafnancy13 or Aisha Alto Alto_


*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔*
*KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*

      *BABI NA ASHIRIN DA UKU*

Ranar da Innaro ta tafi Farida ta samu Mufeeda a cikin Ɗakinta tana bama Ayman Nono Domin shiyafi Airah rigima, Gefenta ta Zauna Tana Faɗin "Kina nan Ashe..? Ina Airah take ne..?

Mufeeda tace "Wlh Ayman ya tashi Da Rigima ni nagaji da Tsotsan nan nashi Momy.." Hararanta tayi kafin tace "Kin me..? Lallai Awo ki Yarinya don sai sun Shekara 2 zaki yayemin yara.." Shagwaɓe Fuska tayi tana Faɗin "Kai Momy.."

Bata bi ta kanta ba ta fara faɗin "Kinsan Abunda Nake so Dake..? Mufeeda ta girgiza kai Farida ta cigaba da Faɗin "Yau zaki karɓi girki ma'ana Yau kece keda Abban Basma.." Ido Mufeeda ta Zaro gabanta na Faɗuwa Kallonta Farida tayi tana Faɗin "Eh Sai ki Shirya, yanzu tashi zakiyi mu shiga Kichen tare muyi Dinner, kinga ya kamata ace mun gyara komai bai dace ace yana da mata har guda biyu ba amma ace kullum Sai dai Iya ta girka ta bashi yaci ba sai na yanke Shawaran Duk wacce keda miji Ranar toh zamu Shiga kichen tare mu taimakama juna ko ya kika gani..?

Mufeeda ta Sadda kai ƙasa Tana Faɗin "Duk Abunda kika yanke Dai-dai ne Momy.." Kafaɗarta ta Dafa tana Faɗin "A'a karki ce Haka kema fa matar gidan nan ce kina da Hakki kan komai.." Mufeeda batayi magana ba Farida ta cigaba da Faɗin "Iya zata shi ci gaba da taimaka mana wajen kula da Airah da dai Sauransu.." Kai Mufeeda ta gyaɗa tana Faɗin "Hakan yayi Momy.." Sun daɗe suna hira kafin Ayman ya gama shan Nono Farida ta ɗaukeshi su Fito Falo, Su miƙawa Iya wacce ke goye da Airah tayi barci an samu 'yar Rigima Naila an tafi islamiya, Farida ce ta miƙa ma Iya Ayman ta faɗa mata Shawaran da suka yanke taji Daɗi sosai, Ko babu komai yanzu Tahir zai Fara Ɗanɗanan daɗin Aure.

Farida da Mufeeda Haka suka Zage suka Shiga Sukayi girki mai rai da lafiya, Tuwon Shinkafa suka yi miyar Agushi saboda Tahir yana bala'in son Tuwo ga miyar taji man Shanu da naman rago zuƙu-zuƙu, Zobo suka haɗa suka sanyashi cikin Fridge, Dai-dai Dawowarsu Basma Daga Makaranta suka gama komai har gyara kichen ɗin Farida ta Fita ta bar Mufeeda na wanke wanke Abun da suka ɓata, Su kansu yaran sunyi matuƙar mamaki ganin Duka iyayen nasu acikin kichen suma sun Nuna murnansu suna tsalle Cewa yau zasu ci girkin Momy dana Aunty Mufeeda.

Farida ta matsama Mufeeda taje tayi wanka itama Sama ta Haura ta Shiga wankan, Bayan ta Fito tayi sallar Magriba ta Shirya cikin wani ubansun Leshi Riga da zani batayi kwalliya ba amma Tayi kyau sosai Tana Fesa Turare taji Ihun yaran suna Faɗin Daddy oyoyo Murmushi tayi tana Ƙoƙarin Ɓoye Abunda ke Taso mata acikin ƙasan Ranta ta Fito Tun daga saman Steps d'in yake kallonta yana Riƙe da Naila harta ƙaraso tana Faɗin "Sannu da zuwa Abban Basma.."

Murmushi ya sakar mata yana Faɗin "Yauwa Umm Airah ko..? 'yar Dariya tayi Briefcase ɗinsa ya Miƙa mata ta maƙale kafaɗa tana Faɗin "Yau bani keda kai ba Mufeeda ce.." Duk da acikin Ranshi yaji daɗi domin wajen Wata goma kenan yana Fatan sake komawa wannan ƙorama amma sai bai nuna ba yawani Ware ido yana Faɗin "Bangane ba..? Baki ta murguɗa mai tana Faɗin "Baka gane ba ko..? Zaka gane anjima.." Dariya yayi yana kallonta saboda yarda tayi magana su Basma kuwa Tuni sun Wuce ɗakunansu, Farida ce ta Ɗaga Murya tana Faɗin "Mufee...Wai me kikeyi ne Haka bakiji Shigowar Megidan naki bane...? Ta faɗa tana Murmushi..

Mufeeda Dake laɓe Tun Ɗazu ta kasa Fitowa saboda kunya ta Fito kanta Sunkuye tana Faɗin "Gani Momy sallah na idar..." Ajiyar Zuciya Tahir ya sauke yana kallonta ƙasa ƙasa Tana Sanye cikin Riga da Siket na wata atamfa wanda yasan Mufeeda abaya ba wanda zai ce itace yanzu domin Mufeeda yanzu haihuwa da Namiji Sun Buɗata tayi kiɓa kamar ba ita ba hips da nonuwa kuwa sun cika ko'ina, ƙarasowan tayi ta ranƙwafa tana faɗin "Sannu da zuwa Daddy." Amsawa yayi yana kallon Fuskarta ido cikin ido Farida Dataga Haka sai ta wuce kichen tana Faɗin "Ki bishi Sama ki Taimaka mai yayi wanka Mufee, kafin ku Fito na Shirya Tebur.." Ta faɗa tana Shigewa kichen da Sauri kamar zata faɗi Domin bazata iya jurar irin wannan kallon Sha'awan da Tahir ke bin Mufeeda dashi ba.

Ganin ta tsaya tana Wasa da Hannunta yasa kawai ya juya ya fara Haura step Naila kuma Tun ɗazu ta sauka Daga hannunsa tabi Basma Ɗakinta cikin Sanyi jiki tabi bayansa yana jin takunta ya mata banza Har Suka Shiga bedroom ɗinsa, ko kallonta baiyi ba ya ijiye Jakar Briecafe ɗinsa da wayarsa ya Buɗe Ƙofar Toilet ya Shiga Haushinsa Ɗaya da Mufeeda Yadda komai wai sai Farida tace mata tayi Zatayi alhalin yana da tabbacin Daga Iya har Innaro basu barta Haka ba.

Kuma yayi gaskiya domin Innaro ta mata nasihan ta kuma ta bata wasu Shawarwarin, ƙara zama da Miji, Harda gyaran Jego Haka Innaro ta Tiƙe ta ma Mufeeda, kayan lambun nan Duk matsa mata take tana Sha Tsarki da ruwan zafi mai bagaruwa, shan madara da Zuma, kuma kafin ta tafi ta tarasu ita da Farida ta sake musu nasihan Zama lafiya, Amma Duk mufeeda tayi biris tana jiran komai sai Farida tace tayi kana zata Da Haushin Abun ya gama wanka ya Ɗauro alwala ya Fito Kansa Ɗaure da karamin Towel yana goge kansa Jikinsa kuma sanye da wani baƙin dogon wando Tana nan tsaye inda ya barta yana ganin Haka yace "Kinga ki Tafi kawai Nagode.." faɗin haka da yayi yasa ta Ɗago kanta suka Haɗa ido saurin kauda kai tayi ganin Ƙirjinsa yana waje ga gashi Duk ya kwanta cikin kasala ta ƙarasa kusa dashi tana Faɗin "Kayi haƙuri Daddy..."

Kallonta yayi yana Faɗin "Baki man komai ba Mufeeda Abu Ɗaya nake so ki gane yadda nake Mijin Farida haka kema nake Mijinki.." Gyaɗa kai tayi kanta na ƙasa tace "Bazan ƙara ba.." Ta faɗa Muryanta na rawa ganin Haka yasa ya Riƙo kafaɗunta yana Faɗin "Meye Abun kuka..? Kinga Zauna na gama Shiryawa mu sauka tare.." Ya faɗa yana Zaunar da ita Kan gado shi kuma ya juya yana neman kayan da zai saka Wasu Riga da wando ya saka ƙirar Armani ya Taje kansa sai gashi ya fito kamar ɗan Saurayi dan Shekara Talatin da Biyar, Tana ta satar kallonsa bai nata magana ba, sai da ya gama kana ya Riƙo Hannunta ya miƙar da Ita yana Faɗin "Muje ko.."

Kasa kallonshi tayi ta sadda kanta ƙasa, har suka Fito Daga Bedroom Farida na Saman Dining bayan ta gama Shirya komai ita da Basma da Bassam da Naila da Iya, Hangosun da yayi yasa ya saki hannun Mufeeda saboda idanuwan yaran, Farida ko Sau Ɗaya ta kallesu bata ƙara ba Har suka ƙarasa Saukowa, Farida Jikinta na rawa Ta ja musu kujeru suka Zauna yana amsa gaisuwan iya Cikin Fara'a yace "Ina su Airah...? Farida Tace "Har sunyi  barci kasan su Da sunji Ruwan zafi

Please Login or Register in order to submit comment