Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta nemeni ba..? Toh sai ma kallon rainin data bini dashi da ƙyar ta iya cemin ina kwana, fisabillahi wannan wace irin rayuwa ce? Duk haƙurinka sai an ƙureka.." Ya faɗa yana dafe kanshi. Ishaq dake kallonsa cike da tausayinshi tsam ya miƙe ya zagayo gabanshi yasaka hannu ya dafa kafaɗarsa yana faɗin "Is Ok...Ya isa haka Tahir maganar duk bashi da amafani tunda ba ji zatayi ba, ni narasa wane irin taurin kai ne Farida ke dashi ko Aliya fa tayi tayi da ita amma ƙarshenta ma yanzu sama sama take mata magana bazata chanza ba, haƙuri zaka ƙara da kuma tausan Goggo Abu har ta amince maka ka sanar da Hakimi kana buƙatar ƙara aure..."

Tahir baiyi magana ba illah sauke ƙananun ajiyar zuciya dayakeyi kafin ya miƙe yana sauke jannun Ishaq dake kafaɗars bai bari sun haɗa ido ba sai ma ƙoƙarin duba agogon hannunshi da yayi lokaci ɗaya yana faɗin "Ishaq zamu makara fa, muyi alwala mu isa masallaci.." Ya faɗa yana kama hanyar ficewa, ajiyar zuciya Ishaq ya sauke kafin yace "Ok..." Daidai lokacin da Tahir ya fice daga Office d'in shima bai zauna ba wayarsa ya ɗauka ya tura cikin aljihu yabi bayan Tahir ɗin da sassarfa.

Farida ko tun bayan fitansu take zaune a falo tana latse latsen waya, sai da ta gaji taga dama kana ta tashi ta nufi dining tayi breakfast ta gama kenan sai ga iya ta fito ɗauke da Naila wacce ta tashi daga barci Iya tayi mata wanka ta saka mata wata riga doguwa bulawus mai kyau rigima takeji don yau ko madarar nata data dama mata bata sha ba, shine ta fito da ita zuwa wajen Farida karɓan ta tayi ta cilla ta sama alamar wasa duk yadda Naila keson wasa yau bata nuna ba don kuka ta saka mata tana binta da kallo, Farida ta kyaɓe fuska tana faɗin "Meya sameta ne Iya..? Baki bata madararta bane..?"

Iya tace "Na bata ta ƙi karɓa Hajiya gwada bata nono ƙila shi takema kewa.." Dariya Farida tayi tana shafa kumatun Naila tace "Wannan babbar yarinyar? Ai tayi girma da shan nono, kinga ina ɗaukanta ina haki shiyasa nake jinjina ma Mufeeda don tana ƙoƙarin ɗaukan Naila, tunda naga tafi sabawa da madararta na yayeta domin bazan iya ma tuna rabon da na bata nono ba gaskiya.."

Iya tayi galala da baki kafin tace "Haba Hajiya Naila fa yarinyace ƙarama har yanzu ko shekara bata rufe ba fa.? Gaskiya bai kyautu ki yayeta tun yanzu ba, don Allah ki barta ko wata sha takwas tayi in bazaki barta ta cike biyu ba..." Tun kafin Iya ta ƙarasa Farida ke jifanta da wani banzan kallo batayi magana ba sai da ta miƙe ta miƙama Iya Naila kafin ta ɗauki wayarta tana fadin "Iya ki kama bakinki, ina ruwanki da hukuncin dana yanke? Ai nima nasan ciwon kaina ko..? So plz ki tsaya iya matsayinki bana so kina shiga hurumin da banaki ba.."

Iya ta rausayar da kai tana ƙara riƙe Naila dake rigima tace "Allah ya baki haƙuri Hajiya.." Bata bi ta kanta ba ta haura sama ta amsa kira, da kallon kaiconki Iya ta bita kafin ta kaɗa kai ta koma ɗakin Mufeeda da Naila da ƙyar ta lallasheta ta sha madararta kuma ma harda rigimar bata ga Mufeeda ba goyata tayi kafin ta fito falo ta fara tsabataceshi, bata gama ba Naila tayi barci sai ta maidata ɗaki ta kwantar ita kuma tazo ta cigaba da aikinta lokaci bayan lokaci tana leƙa Naila acikin ranta kuma tana fatan Allah ya kawoma Alhaji mafita amma tabbas baiyi dacen abokiyar arziki ta gari ba duk da ba Alhaji ya kawota gidan ba amma kuma kyawawan halayyarshi da kyautatarwarshi garesu yasa take ganin girmanshi da darajanshi kuma take zaune dasu da zuciya ɗaya.

******

*BAYAN KWANA UKU*

Duk tsawon wannan kwanakin zaman doya da manja ke gudana tsakanin ma'auratan, shi Tahir ya riga daya fita sha'anin Farida sam domin yana ganin yana gaba da ita amma baida daraja da arzikin da Farida zata nemeshi, shiyasa yayi burus da ita dagashi sai 'ya'yanshi suke harkar rayuwarsu ko alama bai sakama ranshi yana da wata mata agidan, toh itama Farida bata damu dashi ba, hakan da yayi ma yayi mata daɗi domin batason fitinar Tahir sam gani take da zarar ta nemeshi fitinarshi zata tashi shiyasa ta shareshi a zuwan in ya gaji zai nemeta lokacin ya huce sai su daidaita.
 
Kwana biyu ne da dawowarta bata fita ba saboda gajiyar dake jikinta, ranar data kwana uku bata wuni a gida ba, baima san ta fita ba, sai da ya dawo gidan wajen 6 na yamma Iya ke sanar dashi Farida bata gida ƙoƙarin ɓoye damuwarsa yayi amma na yau kam Farida takaishi bango sosai. Garzali yaje ɗauko su Basma daga Islamiya sama ya haura ɗauke da Naila wacce ya amsheta hannu Iya har ya shiga wanka ya fito zuciyarsa tafasa take, koda ya fito Naila tayi barci dama ita rigimarta kaɗan ce dan dataji taushi da iska sai barci yana ƙoƙarin zura jallabiyarsa ne yaji ƙarar buɗe gate alamun Garzali ya dawo daga ɗauko su Mufeeda, carbinsa ya ɗauka ya fito kansa na ɗigar da ruwa kaɗan, dasu ya cikaro duk suka gaisheshi ya amsa fuskarsa ba walwala kafin ya kalli Bassam yana faɗin "Oya shiga ka fito mu tafi Masjid.." Kada kai yayi kafin ya shiga ɗakinsa agurguje Bassam ya ɗauro alwala ya fito Tahir ya kama hannunshi suka fice zuwa masallacin dake kusa dasu yayinda Mufeeda da Basma kowacce tayi ɗakinta domin ɗaura alwala tunda wasu masallatan ma sun riga sun tada Sallarsu.

A ƙa'idar Tahir baya baro masallaci sai an idar da sallar Isha'i yau ma ɗin hakane ta kasance riƙe da hannun Bassam kamar koda yaushe suka shigo gidan megadi na musu barka da zuwa basu kai ga isa ƙofar da zata sadasu da babban falon gidan ba horn d'in motar Farida yayi musu maraba da hanzari megadi ya wangale mata gate ta sako hancin motarta cikin gidan, cak Tahir ya tsaya ya waigo yana kallonta tana ƙoƙarin faka motar a parking spaces, ta cikin motar itama take kallonsa ganin yadda yake mata wani kallo ne yasa tasha jinin jikinta sosai tana ƙoƙarin fitowa daga motar ne nepa suka ɗauke wuta wajen yayi duhu shi ya taimaketa don Tahir hannun Bassam yasaki yace mai ya shiga cikin gida shi kuma ya nufi wajen Garzali yana sanar dashi ya duba Genaretor ɗin Allah yasa akwai diseal, lokacin ne Farida ta samu sa'a tayi wuf ta fada cikin falon, yana ganin haka shima ya juya ya take mata baya tana ƙoƙarin haura steps d'in benen ne taji kakkausar muryanshi yana faɗin

 

  "Da zinin wa kika fita Farida....?" Muryansa cike da amon sauti mai cike da tsantsar ɓacin rai, rass gabanta ya faɗi sai ta kasa juyowa don muryansa kaɗai ta isa ta bayyana mata yau Tahir ya gama haƙuri da ita, bata samu zarafin juyowa ba ya sake daka mata wata uwar tsawar data gigita ta, bama ita kaɗai ba hatta su Basma da Bassam da Mufeeda da Iya dake ɗakunansu sai da suka firgita suka fito falon da sauri daidai lokacin da aka kunna Genaretor haske ya gauaraye ko'ina.

"Nace da izinin wa kika fita Farida...? Saboda raini kina jina ina magana kina min banza..?" Ya faɗa yana tattare naman goshinsa saboda fushi, Farida ta juyo a hankali tana kallonshi tana kuma ƙoƙarin ɓoye razanarta haɗe fuska tayi kafin tace "Dama na saba tambayar izininka ne idan zan fita...? Na ɗauka nida kai mun wuce wannan ƙarnin..." Ta faɗa tana kaɗa key ɗin motar dake hannunta ba tare data jira komai ba ta kaɗa kai ta juya ta cigaba da taka steps d'in cikin halin ko in kula wani ɓacin rai mai zafi ya ziyarci zuciyar Tahir ko gani bayayi yayi kukan kura ya bi bayanta a harzuƙe kafin ma ta ankara ya cimmata sai ji tayi ya jawota baya da sauri ƙiiiiii.....kamar wata kayan wanki, bai direta ko'ina ba sai tsakiyar falon bayan ya ingizata baya tayi taga taga zata faɗi, ba domin Allah ya taimaketa ta daddage ta riƙe kujeran dake falon ba da sai ta faɗi ƙasa..

Cike da mamaki take binsa da kallo kafin ta buɗe baki tace "Tahir...Lafiyanka ƙalau kuwa..? Ta faɗa tana binsa da kallo ganin yanda yake huci bai bata amsa ba illah cewar daya ƙarayi "Nace da izinin ubanwa kika fita Farida...?" Baki buɗe take kallonshi kamar yadda Basma da Bassam suka zura musu ido, cike da wani yanayi hakama Mufeeda, Iya ce dake tsaye ranta duk ba daɗi tunda suke da Alhaji basu taɓa ganinshi cikin fushi hakaba tana ƙoƙarin isa gareshi Farida tace "Kace da izinin ubanwa na fita ko..? Toh da izinin ubana ko..." Ai bata ƙarasa ba taji Tas! Tas! Maruka biyu kyawawa Tahir ya wanke fuskar Farida dama da hauni lokaci ɗaya, kamar walƙiya taji marukan saboda azaba sai gata zaune daɓas da ɗuwawunta akasan cafet ɗin falon hannayenta dafe da kuncinta tana bin Tahir da kallo hawayenta na sauka kamar an buɗe famfo.

Ba Farida kaɗai ba hatta Basma da Bassam saboda razana sai da ya ƙanƙame Basma suna rawar jiki a tare lokaci ɗaya suka fashe da kuka, hakama Mufeeda da ta maƙale jikin ƙofa tana rawar jiki, Iya ko ƙirji ta dafe tana faɗin "Innalillahi Wa'inna Ilaihirraju'un...Alhaji mezan gani jaka..? Ashsha abu baiyi daɗi ba.." Ta fada cike da damuwa.

Ko sauraranta baiyi ba ya kalli Farida yana nuna ta da yatsa kafin ya fara faɗin "Wannan ne na farko kuma na ƙarshe... wallahi in kika ƙara fita bada izina na ba Farida daga ranar zaki tabbatar da babu wani amfanin da kike dashi a cikin rayuwar Tahir..." Ya faɗa cikin kakkausar murya, kuka Farida ta fashe dashi bilhaƙƙi da gaskiya kafin ta miƙe cikin kuka tana faɗin "And So What...Nima ai baka da wani amfani a wajena, waye kai awajen Farida? Ka sakeni in ka isa tunda bani da amfani juz Tahir ka sakeni ka gani in rayuwata zata yanke ko ta wulaƙanta daga yau ka sakeni don Allah..." Ta faɗa tana hargowa cikin kuka.

Basma ce ta saki ihu tana faɗin "No..Momy Daddy Stop plz..." Ta faɗa tana duƙawa haka shima Bassam yayi suna kuka suna faɗin "Plz Daddy Momy don Allah ku bari kuna sakamu muna jin ba daɗi..." Suna faɗa suna kuka, Mufeeda ma kukan take, da kallo Tahir ya bisu lokaci ɗaya kuma sai jikinsa yayi sanyi sosai idanuwansa sunyi jawur kai kawai ya kaɗa kafin ya wucesu da sauri ya haura sama cikin sassarfa, ganin haka yasa Farida tabi bayanshi da sauri tana kuka sai dai kafin ta ƙarasa ya shige bedroom ɗinsa ya banko ƙofa a ƙofar ɗakin ta tsaya tana kuka tana faɗin "In ya isa ya fito ya saketa dama ita tagaji da aurensa..." yana jinta ya mata banza kan gadonsa ya hau ya saka kanshi cikin gwiwoyinsa yana ƙoƙarin daidaita numfashinsa.

Basma da Bassam ko kuka suke sosai na ganin abunda ke faruwa tsakanin iyayensu wanda basu taɓa gani ba da ƙyar Iya ta lallashesu kowanne ya nufi ɗakinsa cikin damuwa, haka ma Mufeeda ta koma ɗakinta ta faɗa bisa gado tana kuka, wanda tarasa dalilinshi, ranar dai gaba ɗaya gidan ba wanda ya yi dinner haka kuma barci sai dai sama sama, daga Tahir ɗin har Farida barci ɓarawo ne ya ɗaukesu balle su Basma da suka tashi fuskokinsu duk a kumbure saboda kuka.





*Janafty..*
*Aisha Alto.*
*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Alkaluman:*✍️

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty*💕

_Don't Forget to Vote us on Wattpad:Janafnancy13 or Aisha Alto alto_


_*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_

*BISMILLAHIR RAHAMIR RAHIM*

       *BABI NA BAKWAI*

....Duk da yaran Sun Tashi Zuciyarsu ba Dadi bai Hanasu Shirin Tafiya mkaaranta ba,Suna bisa Dinning Suna Breafsat,Kowa ka gani Fuska ba Walwala Don Daga Tahir din Har Faridan ba Wanda Sukaji Motsinsa Har Gwarashi yazo da Asuba ya Tashi Bassam sun Tafi masallaci.

Batare da Sun saka iyayen nasu a ido ba garzali ya Kwashesu Zuwa Mkranta Naila Kuma dama Wajen Tahir Ta Kwana,Sun Fita ba Dadewa Farida ta fito Daga Cikin Bedroom Dinta Dauke da karamar Trolly dinta Fuskarta ta Kumbura Idanuwanta Sun Chanza kala Saboda Kuka Tana Sanye da Riga da Sikat na Wata Atamfa Holland,Daurin Dankwalin dai gashi ga kamarshi,sai karamin Gyale Vail Data Yafo Bisa kafadarta,karamar Jakarta na Hannunta Hade da Wayarta sai Key din motarta Dake Hannunta.

    Ahaka ta Sauko Har Zuwa Main Falo din Tana Tafiya tana Share Hanci da Iya taci karo Wacce Tafito Daga Kichen,cikin mamaki Take kallonta kafin Tace"Hajiya lafiya Kuwa..? Wata Uwar Harara Ta maka mata kafin Ta Saki Tsaki takama Hanyar Fita Daga Falon,iya bata Dandara ba Tace"Haba Hajiya gaskiya Wannnan ba girmanki bane,Ina Zaki Tafi ki bar mijinki da ya"yanki Kefa ba yarinya bace Yaji bai kamace ki ba,kin kai Munzalin Da Zaki ma Wata Fada bama Kanki ba..."Tafada Cikin Nuna Alamun Abun bai mata Dadi ba.

Juyowa Farida Tayi Afusace kafin Tace"Wlh iya sai na Tafi nagaji da Irin Tozartanin Da Tahir yake yi nagaji..!kina gani Jiya gabanku gaban ya"yana Ya Tsinkeni da maruka har biyu Saboda ga baiwarsa ko,Allah sai na Tafi Sai ya Zauna Shi kadai.."Tafada Tana Sharbe Kwallah kamar Wata yarinya.

Iya tayi kasake kafin Tace"Hakuri Ake Hajiya,Kowa fa kikagani yana Zama lafiya agidan Mijinshi karki Tambayeshi Hakuri,Kema Kiyi Hakuri Don Allah In kika Tafi Gida Kicema su Umma Mene Don Allah.."?Tana Sharan Ido Tace"Ai ba Kano Zani ba Danbatta zani Wajen Goggo Abu taga Shaidan Yatsun Tahir Akan Fuskata..."Tafada Tana juyawa da Sauri Ta Fice Daga Falon Tana kara Rike zaman karamin Akwatin Dake Hannunta Iya Dake Tsaye ta Yunkura Zata Bita sai Taji Muryan Tahir Daga Sama yana Fadin"kyaleta iya..."yafada Cikin Halin ko Inkula

Iya ta Waigo Jiki asanyaye kafin Ta Rusuna Tana gaisheshi,Shiko yana Daga saman Benen ya amsa mata Fuskarsa na Nuna Alamun baida Damuwa yana Sanye da Amarican Suit,Ash colour,Yar jakar Briefcase dinsa ne Ahannunshi da alamun Fita Zaiyi Tana Kokarin Barin Falon ya Karisa Saukowa yana Fadin"Naila tana Room Dina iya Ta Koma barci plz ki Haura ki Daukota Ta Zauna Kusa dake.."Ya Fada yanq Nufar hanyar da Zai Sadashi da Haraban Gidan Lokaci Daya yana kallon Agogon Fatan Dake Hannunshi.

Iya tabi bayanshi da kallon Tsausayi kafin Tace"Insha Allahu Adawo lafiya Alhaji.."Bai Jita ba Don ya Riga yaFita Daidai Lokacin Kuma Garzali ya Sawo kan Motar Cikin gidan ya Dawo Daga kai Su Basma mkranta batare da bata Lokaci ba ya Shiga ya Juya Dashi Zuwa Office don Ya Makara gashi Kuma Meeting garesu Suna Tafe yana kallon Agogon Dake Tsitsiyan Hanmunshi kafin Wayarsa kirar iphone 11 promo,tadauki Tsuwa Sunan Ishaq ya Fito baro baro Afuskar Wayar Dauka yayi Da Hanzari suka gaisa kafin Su Cigaba da mgana Cikin Kulawa da Tsantsan Ilimi.

********

*D'ANBATTA*

Goggo Abu Sai Dai Taga Farida Kwatsam Tazo Tana Mata Kuka Wiwi kamar Wacce Aka yanka Ko Akace Uwarta ta Mutu Lokacin Data Iso Ashe na gidan,nan Goggo Abu Ta Rude Ta Shiga Tambayanta Abun ya Faru,Farida na Kuka tana Zayyanama Goggo Wai Tahir ya mareta Har guda hudu Dukkanta ma yaso yi sai da iya mai aikinsu Ta Shiga Tsakani Farida na Kuka Tanama Goggo Abu Rantsen Rantsen Cewa Tahir yace ma bata da Wani Amfani Acikin Rayuwarshi.

Ran goggo Abu ya baci Ta Dinga Sauke Numfashi Takaichi Attahiru na Damunta Ashe ce Tace"goggo Kada ki yanke Hukunci Cikin Fushi yakamata Shima yayan Ki kirashi ki Fara jin Ta Bakinshi Tukunah.."Tafada Da Sigar Lallashi,Cikin Kuluwa Farida Ta Dago Tana Hararan Ashe kafin tace"Eh mana Akirashi mana ai ba karya namai ba Jiya agaban ya'yana Da yan Aiki ya Tozartani nidai kam goggo Ki kirashi na Gama zama da Tahir kamar yadda yace banda Wani Amfani Acikin Rayuwarshi Nima Tahir baida Amfani Awajena ya"yana yaje ya Rike na barmai Dama badasu nazo ba..."Tafada Tana Shesshekan Kuka Lokaci Daya Tana Hararan Ashe din Domin Dama Jininsu baizo Daya Saboda yadda Tahir yake matukar ji da Ashe Ita Kuma Duk Abunda ya Shafi Dan"uwanta bata Wasa Dashi.

Ashe bata mata mgana ba illah kallon Goggo Abu Datakeyi kafin Tace"Kinji goggo Don Allah Kifara Kiranshi Tukunnah.."Jin Haka yasa goggo Ta Mike Ta Shiga Ciki Ta bar Ashe da Farida Anan Cikin Falonta Kowa na kallon Kowa Cike da Takaichi Mikewa Ashe tayi ta Fice Zuwa Shashen Innaro Tana Fadin"Allah ya kawo maka mafita Dan"uwana..."Tafada Cike da Habaici da Kuluwa,Da Ido Farida Ta Bita kafin Ta Rakata da Tsaki Tana Share Kwallah.

Fitowarsu kenan Daga Meeting yana Hanyar Komawa Office ya Fito da Wayarshi Wacce Tun Shigansu meeting din ya sakata A Silent Hankalinsa ne ya Tashi Ganin Misseds Rututu Na goggo Abu gabansa sai dai ya Fadi yana Bude Kofar Office din ya Na Kokarin Kiranta gabda zata Katse Ta Dauka yana Kokarin gaisheta ta katseshi A Fusace Tana Fadin"Dagata min Attahiru Nagode da Abunda Kamin in Har na Isa dakai kazo gida yanzu ka sameni mutumin banza kawai..."Tafada Cikin Fushi kafin ta yanke Kiran,Dafe kai yayi yana salallami,Domin yasan Cewa Farida Tagama Hadama goggo Abu Famfo shi bama Wannan ya Dameshi ba Irin yadda Ta Dau Zafi Dashi Allah ne kadai Zai Kwaceshi.

   Office din Ishaq ya Tafi Agurguje Sukayi mgana Sama sama Kafin Suyi sallama ya Fito bai Tsaya bata Lokaci ba yace ma garzali Su kama Hanyar Danbatta sai da Sukayi Nisa ne Garzali ke Tunamai dasu basma Ba Wanda Zai Daukosu Daga Sch,Dafe kai yayi yana Salati kafin ya Dauki Wayanshi Shugaban mkrantan Su Basma ya Fara Kira inda yabada Umarnin Indan Antashi Daga Mkranta Basma da Bassam Su bi Sch Bus Su Dawo gida Saboda Dukkansu basunan bamai Zuwa ya Daukesu,Daganan sai Shugaban Mkrantar su Mufeeda Itama Abunda yace Kenan Kafin ya Katse Kiran,yana Sakin Numfashi kadan yasan yau sai sunyi Rashin Islamiya Saboda baita yarda Sun Fita Waje Su kadai ba Duk inda Zasu sai dai garzali ya kaisu Kuma yana Da Tabbatacin Tunda Sukaga babu mai Kaisu bazasuyi gangancin Fita ba.

Wajen 2pm suka iso Kofar gidan Hakimi,Shikanshi Hakimi da Jama"arsa Sunyi mamakin ganinshi don Akasari bai Cika Zuwa Cikin Sati ba Sai karshen Sati,Hakimi bai yi mamaki Sosai ba Saboda yaga Zuwan Farida Hartazo ta gaisheshi Yaga Fuskarta ta Chanza kamar tayi Kuka Daya Tambayeta sai tace bakomai tatashi Ta Shiga To Tunda yaga Zuwan Tahir sai yasha Jinin Jikinsa Ammh Dayake yana da Miskilanci sai bai Nunama Tahir din Komai ba Wanda Sai da yagama gaisawa da Jama"ar Wajen kafin ya Karisa garesa yana Kwasan gaisuwa,bayan Tambayi Aiki da yara,bai Zauna ba ya Mike yacemai Zai Shiga Cikin gida,Hakimi yayi Mirmishin su na manya kafin ya kalli Tahir din yana Fadin"Attahiru yau kazama Mara Hakuri ko...? Akullum ina maka Nasihan ka Rika kai Zuciyarka Nesa Domin Akasari mata akarkarce suke Kana Kokarin Daidatasu Suna kara famdarewa ne,Toh Dole sai munyi Hakuri Dasu kaji...?"Yafada kasa kasa Wanda Inba Tahir din ba Wanda yakejin meyake Fada,Sadda kanshi yayi kasa yana Fadin"Naji Hakimi Insha Allahu Zan Kiyaye.."Kai ya gyada kafin yace"Tashi ka Shiga Ciki Allah yayi maka albarka.."Da Ameen ya amsa kafin ya Wuce Zuwa Cikin Gidan...

Sheshen Innaro ya Wuce Direct nan Suka Ci karo da Inna Fulera ta Zube Tana gaisheshi ya amsa Cikin sakin Fuska Kafin ya Wuce Zuwa Babban Falon Innaro Dake Shashenta,Nan ya iske Innaro da Ashe Suna Hira,Ashe Dataji Dadin ganin Dan"uwanta sai da tatashi ta Fada Jikinsa Tanamai Oyoyo Riketa yayi yana Dariya Lokaci Daya yana Shafa Kanta,Tare Suka Zauna gaban Innaro,Tahir yafara gaisheta ta amsa Cikin Sakin Fuska da Fara"a Tana Tambayanshi su Basma ya amsa da Suna Mkranta,Yadade Awajenta Suna gaiswa da Hira kafin ya barota Zuwa Shashen Goggo Abu Ashe bata biyoshi ba Saboda tasan Goggo Abu Korarta Zatayi.

Lokacin Daya Sawo kanshi Falon goggo Abu Da sallama Abakinshi da Farida yaci karo Tayi Rashe Rashe Atsakiyar Falon Tana Shan Fura,Suka Hada Ido,Daure Fuska yayi kamar bai Taba Dariya ba yana karisowa Cikin Falon Goggo Abu Tana Fitowa Daga Uwar Dakinta Suka Ci karo,Takalmin kafarsa yacire kafin ya Zauna yana gaishe da goggo Abu Wacce Ke Dankaramai Harara kafin Tace"Tashi Tsaye bana Bukatar gaisuwaarka Attahiru,domin ka gama Nunamin Iyakata..."Tafada Cikin Kakkausan Murya.

Kasa yayi Dakai yana Jin Wani Daci Acikin Ransa,Dagowa yayi yana Kallon Farida Wacce Ke kallonshi gabanta ne yafadi ganin Irin Kallon Dayake Jifanta Dashi bai iya mgana baa,sai ma Sauraran Goggo Abu Dayayi Tayi Ta Inda Take Shiga batanan Take Fita ba Sai da Tagama Wanke shi Tas Kamar Zata Dakeshi Ta Koma Gefe Tana Haki,sai da yaga Ta gama kana ya Dago yana kallon Goggo Abu kamar yayi kuka yana Fadin"Goggo Ta Fada miki Fita Take bada Izinina ba,Ta sanar dake batamin Kallon Mijinta Dauka na Take tamkar Wani yaronta ko Ma"aikacinta Ta gayamiki Wannan Ko bata gayamiki ba.."?Yafada kamar Zai Fashe da Kuka.

Daga Farida Har Goggo Abu Jikinsu yayi Sanyi Saboda yadda Tahir din yayi mganar,Sai goggo Abu Ta Koma Da Kallonta kan Farida tana Fadin"Kinji Abunda Mijinki yace In Hakane To Tabbas baki kyauta ba,Taya zaki Dinga Fita bada Izininsa ba Ai ba Zaman kanki kikeyi ba Ko Farida,Gaskiya ki gyara Kina Cikin Fushin Allah da Tsinuwar mala"iku matukar baki Roke Mijinki Gafara ba.."

Farida ta kanta ke kasa ta Fashe da Kuka,Jawota Jikinta goggo Abu Tayi Tana lallashinta Lokaci Daya Tana Fadin"Yi Shuru kibar Kuka,Ki bama Mijinki Hakuri Kune mi gafaran Juna Don Allah bana Jin Dadin Wannam Rashin Jituwar naku,kufa ba yara bane Kune fa Kuke da yara kamar basma da bassam Haba Don Allah Farida Don Allah Ku Sansanta kanku.."Tafada Cikin Sanyi Dagowa Farida Tayi Tana Share Kwallah kafin tace"Toh Goggo.. "Muryanta ta Dishe Sosai...

  Mirmishi goggo Abu Tayi kafin Ta Mike tana Fadin"Yauwa Naji Dadi bari naje na Karboma Atrahiru Fura Wajen Innaro yanzu zan Komo ."Tafada Tana Ficewa Don ta basu Waje bayan Fitanta Falo ya Dade Shuru kafin Farida ta yanke Shurun bayan Ta Dago Tana kallon Tahir Daya Tsurama Cafet din Goggo Abu Ido Fuskarsa ba Annuri ko Kadan Duk da gabanta na Fadi hakanan ta Daure Ta Furta.."Srry...'Tafada Muryanta na Rawa Ko kallonta baiyi ba,ganin Haka yasa sai Jikinta yayi sanyi Tatashi Ta Koma Side din daya ke kallo Ta Sake Furta"Am Srry..."Kauda kai yayi Yana Neman Tashi sai Ta Riko Hanmunshi Da Sauri ta Fashemai da Kuka bayan ta Dora kanta bisa  Cinyarsa,tsayawa yayi yana Kallonta Kukanta na Dakarmai Zuciya,Runtse ido yayi kafin ya Dora Hannunshi bisa kanta yana Tapping cikin Ajiyar Zuciya yake Fadin"Shiii...is ok.."..

Jin Abunda yace ne yasa Ta Dago Da Sauri Fuskarta Jage jage da Hawaye,tana kallonshi Mirmishi ya sakarmata kafin ya Zaro Wani Farin Hankey Daga Aljihunsa,yana Share mata Hawaye yana Fadin"Nace komai ya Wuce ko..? Kece fa kike ja muna Fada Farida,in da bakiyi Saurin Zuwa Wajen goggo Abu banayii Regreating din marin da nayi miki zan baki Hakuri,plz Farida..."Bai karisa ba goggo Abu Ta Shigo Dole yayi Shuru ganinsu haka sai ya sanyayamata Rai,Furar ta mikamai ta sake Ficewa,yana kallon Farida kasa kasa yafara Shan Furarsa,yana gamawa ana Kiran sallar La"asar nan yafice Zuwa Msallaci Ita Kuma goggo Abu Ta Dingama Faridar Nasihan bayan Suma Sun Idar da Sallar.

Bai komo dakin Goggo Abu ba sai da ya sallami kanwarsa Ashe,Har gida ya karata akafa suna Tafe Suna Hiransu gwanin ban Sha"awa,sai da ya Dawo ya Shigo bangaren Goggo Abu yace Farida tataso Su Tafi,nan ma goggo Abu Hadasu Tayi tana musu nasiha Sosai kafin Su mata sallama Shashen Innaro Suka Koma Suka mata sallama nan Tabada Sakon Fura mai Dadi Tace akaima basma da Bassam,Awajema Sallama Suka ma Hakimi ya bisu Shima da Sanya albarka.

Tahir shi ya Tukasu Shida Farida Acikin Motarta Shi Kuma garzali ya Tuko ta Tahir,acikin Motan Ma Hannunshi Farida Ta Damke tana Fadin"Shine ni baka bani Hakuri ba.."Tafada Cike da Shagwaba,Hankalinsa na Wajen Tuki ya Waigo yana Fadin"Ah...Waht Are u Eating na baka is Fooling Down,Zan baki mana ammh ai kinsa nawa Is so Special ko.."Yafada yana kallonta Lokaci Daya yana Kashe mata ido,Dariya tayi tana Kwantar da kanta Cikin kujeran Mota batace komau ba Ammh Hannayesu Sarke da Juna Jefi Jefi suna Hira Har Suka Kariso gida.

  Abun mamaki Haka yaran Suka ga Iyayen nasu Sun Shigo Hannuwansu Sarke da Juna,Saboda Jin Dadi basma da bassam Suka Ruga suka Rumgumesu suna Ihun Oyoyo momy da Daddy,Hatta Iya da Mufeeda Sunji Dadin ganin Farida da Tahir Da Alamun Komai ya Wuce,Ranar

Please Login or Register in order to submit comment