Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abin n'a damu n'a, tsintar kaina nake ana bani Umarni dan in dinga wulakanta ki, dan Allah gani gaban ki duke ki yafe min, ki taimaki Rayuwa ta ki yarda n'a nuna miki so da tatali,I love you Kamrina."

Sai yanzu yake jin radadin cin mutuncin da ya mata hawaye masu zafi ne suke zubo masa duk tana kalon sa a yar huda Dan ta daina kukan kuma tana sauraran sa, share hawayen sa yayi yasa kayan sa, yabar mata d'akin, tashi Kamrina tayi har yanzu bata yarda da kalaman sa ba a ganin ta dadin baki ne .duk ta luluba da bargo kanta kawai kake gani.

"Assalamu Aleykum Kawa ta "taji an fada daga jikin bango, dan murmushi tayi dan tasan mai muryar bata huce ta kawar ta Aljana fatima.



Amsa salamar tayi ta daga idanun ta aiko ita kin ce, nan ta kara so ta zauna kusa da Kamrina ta dafa ta tace "nasan matsalar ki da abinda ya haifar kiyayar da mijin ki da ya miki à baya, zan fada miki ne badan wani abu ba saidan ki daina hukunta mijin ki kina azabtar dashi à bisa rashin Sani, dago kai Kamrina tayi tana mata kalon mamaki, Fatima ta kada mata kai alamun tabatar wa., sanan taci gaba da cewa Kamrina tun farko n'a barki ne da mijin ki saboda mu bama shiga harkar miji da mata, anma hakan ba wai zai hana bana bibiyar lamarin rayuwa ki bane, ke amana ce a gu n'a tun kina jaririyar ki, duk abinda mijin ki ke miki n'a tsangwama ba yin kansa bane, bara kiga wanda sukayi abun, wani abu tayi take wasu halita Suka fito à bango anma gajeru anma ba kalar tsoro suka fito ba, da yake Kamrina batada tsoro Dan haka ta tsaya kalon su.

Ran Fatima à bace ta kale su tace "dan ubanku ku fadi abinda kuka yi ,nan dayan yace "mu aiko mu akayi mu ma kishiyar ki aiki,ni n'a shiga kan mijin ki Kumar ina sa masa tunani daban daban wanda zai Dinga baki wahala", dayan yace "ni kuma nine n'a shiga zuciyar sa nake taushe Son da yake miki ina sa masa kiyayar ki da k'arfi, duk cin mutuncin da yake miki sai mun juyar masa da hankali tukon mu ke miki rashin mutunci, k'arfin addou'a ne ya kore mu a jikin sa, da.kuma rashin cika Alkawari irin n'a kishiyar ki, tunda gimbiya fatima ta gane da mu ne muka cutar da ku take gana mana azaba dan Allah ki yafe mana,mijin ki bashida laifi,'.





Wani abu Fatima tayi take suka bace.



Ta dawo wajen Kamrina dake kuka ta dafa ta tace "kawata kiyi hakuri in Allah ya yarda kin cinye jarabawar ki dan nan gaba zaki zama yar gata, ki zama abin so n'a barki lafiya ."



Bat ta bace .




Kamrina tasha kuka, ashe Kumar ba yin kansa bane ashe gaskiya yake fada ji tayi zuciyar ta tayi sanyi tashi tayi ta ta koma tayi Wanka ta shafa mai ta shirya, yau kam mulki ya tashi, doguwar riga tasa sanan tasa Alkyaba, tayi kwaliya simple tasha kyau sosai .




Acan anyi ma su Sarauniya Fatima iso har fada bayan Sun gaisa da sarki , sosai ya rude ganin kamanin Kamrina à wanan family, anma yaji dadin abinda suka zo dashi, da murnar sa harda shi aka isa b'angaren Fulani, itama yau ta shirya cikin Alkyaba, Fulani kam gaban ta faduwa yayi itama, ganin mai kama da mahaifiyar ta da kuma mai kama da Kamrina, bayan an zazauna, Fatima sarauniya hawaye ya fara zubowa à idanun ta ta matsa kusa da Fulani ta rungume ta tana hawaye tace "ko ba'a fada ba kece yar uwa ta, daidai Kumar yayi Salama shima ya shigo.






Kuyi hakuri Next page Kamrina zata hadu da yan uwan ta insha Allah.







Aci gaba da gashi🍇

Maimou Love😘🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
*WACECE NI KAMRINA*
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀






*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM*💋








*PAGE 75-76*






Fulani ma kuka take bayan ta rungume Fatima, dan tana zuwa taji wani feling na yan uwan taka,a tsakanin su, nan Fatima ta fada mata ita wacece da komai na tarihin su, Sosai suka kara rungumar junan su, Fulani tace " ashe nima inada yar uwa ban sani ba, anma kaka ta cuceni, sarki ma murmushi yayi cikin farin ciki, yana godiya ga Allah. yayin da Kumar ma suke cikin farin ciki, wata irin zabura Kumar yayi lokacin da yayi Arba da Kamrina karama yar kimanin shekaru goma sha biyar sak komai nata irin n'a Kamrina ne,da k'arfi ya furta Kamrina, wanan ai kowa ya ganta yasan Kamrina n'a tace Fulani ma cikin rudu tace "tabas Kumar nima da suka shigo nayi mamaki wanda har yanzu ina cikin rudu, mai martaba ma abinda yace kenan, Ibrahim da Sarauniya suma tashi sukayi bakin su har zanzana yake , Fatima tace " Dan dan Allah ku nuna min wanan Kamrina ba tantama ya ta Ce 😭

Salama Kamrina ce ta katse su yayin da duka suka juyo suka zuba ma Kamrina ido Fatima n'a ganin ta take à gurin ta some, yayin da Ibrahim da Kamrina karama suke hawaye, Dan ba ko tantama wanan Kamrina su Ce.itama kusan hakan taji suman tsaye tayi lokacin da tayi arba da mai kama da ita....


Ruwa aka zuba ma Fatima ta tashi, tana hawaye ta buda ma Kamrina hanu wada take tsaye kamar statut Fatima n'a kuka tace "Alhamdulillah ashe zanga wanan ranar ,ranar da Zanga ya ta da da yar uwa ta, shekara da shekaru ina kukan rashin ta, à hankali Kamrina ta karaso tana kuka, domin itama taji à. Jikin ta cewar wanan ahalin ta ne, rungume ta Fatima tayi tsam kamar zata maida ta cikin ciki, Ibrahim ma da Kamrina karama da sauri suka zo suka rungume ta, take ran Kumar ya baci ganin wani gardi n'a rungume da matar sa, runtse idanu yayi.





Nan suke kuka, sai sanan Fulani ta samu k'arfin halin magana tace "à'a ya haka, Ya ta Kamrina ki warware min wanan kulin, hawaye ne tantsam à idanun Kamrina, ta tashi tsaye tace ina zuwa,kalo suka bita dashi, ba kamar Fatima da take ganin kamar zata kara rasa yar ta ne.



Mota ta higa sai b'angaren su tana kuka da gudu ta fido kayan da Apou ya baya wanda yace dasu ya tsince ta, ta fido ledar da sauri ta koma mota ta figa sai wajen fulani ko ida rufe k'ofa bata yi ba ta shigo kayan ta fido à leda, tana kuka tace.



"wanan sune kayan da mariki na yace ya tsince ni dasu, da sauri Fatima ta tashi tana zanzana, ta amshi kayan, kuka kuka dariya dariya take, tace wly wanan sune kayan, Ibrahim ka tuna su,


Shima yana hawaye yace "Mama wly sune n'a gane su, wanan yar uwa ta Ce, kanwata...




Waya ya d'auka ya kira mahaifin sa mai martaba, yace "Dad idan da Hali kazo kasar bagadur yau Dinan, ya Kashe Fulani ma kiran Momy tayi cewa tazo yau tahau jirgi tazo. 🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
*WACECE NI KAMRINA*
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀






*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM*💋








*PAGE 77-78*







_Mistake à wacan Karon Ibrahim yace kasar bagadur, zance k'asar Rajugur ne ba bagadur ba_







Kasancewar Sarki Abdullah baya sanya à Al'amarin iyalan sa, hakan yasa ya aje komai suka hau jirgi Dan zuwa Rajugur da shi da kuma waziri, da dogarai..



Haka Fulani ma cikin d'aurewar kai abinda amiyar ta ta mata ta kira ta ta sanar da Momy cewar tayi gagawar d'aukan jirgi tazo yau, ba wani Bata lokaci itama Momy tahau jirgi sai k'asar Ratifié cik'e da fargaba, tare da tsoro .




Kilishi da hafsa zaune, wada tasha kitson atashmn sanye take cikin pakistan riga da wondo, ta kali mahaifiyar ta, ta yamutse fuska tace "gaskiya Momy ni zanje naga abinda ke wakana wancan b'angaren kar ayi bani."


Wata uwar harara kilishi ta watsa mata tace "ce miki akayi ni bazan je ba, maza tashi, haka suka tashi suka nufi b'angaren Fulani, haka kawai itama Princesse yau tayi sha'awar zuwa b'angaren Fulani, taga wai mai yarinyar nan Kamrina take yi kulum tana cikin zuwa b'angaren, dan haka itama mota ta shiga tayi b'angaren, kusan à tatare suka iso ita da kilishi da Hafsa, ko kalo basu isheta ba, itama haka hafsa harara ta banka ma Princesse, kwafa Princesse tayi bata ce komai ba anma da da hanya da taci uwar Hafsa, Dan à. Kufule take, anma ba komai Allah kai damo ga harawa .





Suma salama sukayi suka gaida mutanen, cike da mamakin Kamrina da sukayi rungume jikin wata mata wada suke matukar kama, zama sukayi suma aka tashi baki daya aka ci abinci tare da yin Sallah, Princesse tasha jinin jikin ta yayin da ta d'auke wuta ganin wanan matar mai cike da mulki rungume da Kamrina,bayan haka ga da take yi da ita da yayan ta, dukan su kanun su a kule yake jiran mai martaba kawai ake yayin da sarki da Kumar da Ibrahim suka fita dan zuwa Sallah .Rukayya da take zabga barci bayan ta gama kwaliyar ta tasha maganin mura dake damun ta hakan yasa barci yayi awon gaba da ita bata sani ba......



D'akyar Fatima ta bar Kamrina sukayi Sallah, daga kilishi har Princesse sudai kalon ikon Allah suke, dan sunyi matukar shan jinin jikin su, jin su waye Asalin ahalin Kamrina.




.



Awani uku saiga mai Martaba sarki Abdullah kusan kamar hadin baki tare suka iso da Momy, Mai martaba Daddyn Kumar yayi matukar farin ciki da zuwan wanan Sarki, bayan an kaisu masauki aka aje musu abin motsa baki, Sarki Abdullah cikin fara'a bayan an gaisa yake cewa à kaisa ga iyalan sa, ba musu suka tarkata suka tafi, yayin da Kumar yake kara jinjina girma irin n'a daddyn Kamrina.


Dama shi Allah ya hada jinin sa da na Sarki Abdullah, anma iyakaci in ana taro n'a sarakai, yasha zuwa ya zauna kusa da Sarki Abdullah lokacin yana Karami.shima sarki yana Son sa, to da ya girma ne sai ya daina zuwa wurin sa.



Momy ce ta fara shigowa tayi arba da Kamrina da Fatima rungume da ita ,gaban ta ne ya bada dum dan ba makawa asirin su ya tonu ,da fara'a fulani ta tare ta. itama tana hawaye ta taso daga jikin mahaifiyar ta tazo ta rungume Momy, itama rungume ta tayi tana dadaba bayan ta alamun rarashi, bafade ne ya sanar da shigowar mai martaba, nan kowa ya nutsu aka zuba ma k'ofa ido, sai gasu sun shingo, kowa ya kwashi gaisuwa, yana amsawa cikin fara'a, yayin da Idanun sa ke kan abin kaunar sa, hankalin sa duk à tashe ganin kukan da take, itama fatima murmushi tayi tace "ranka ya dade ashe abinda kake fadi zai tabata, ashe akoi irin wanan ranar ta farin ciki, da zanga jini n'a biyu à lokaci daya ,mai martaba bai gane komai ba, nan ta nuna masa da hanun ta inda Kamrina ke zaune itama ta kure mahaifin ta da kalo, akoi yar kama, firgigit Sarki yayi wata irin zabura, yayin da yake murje idanun sa ya gani shin da gaske abinda ya gani kalon sa yakai ga Kamrina karama dake kusan sa tana masa murmushi ya tabatar ko ita ce,tafiya ya fara yi bayan ya tabatar da zargin sa, yace "wanan ya ta ce Kamrina take hawaye suka zubo masa, tashi Kamrina tayi ya rungume ta tsam, wani irin farin ciki ke shigar sa wanda ya jima baiyi makamancin sa ba. Kara rungume yar yake tsam, hawaye n'a zuba n'a farin ciki, yace "ashe mafarki na zai zama gaskiya, yau shekaru ashrin da uku, da kwana takwas, da awa biyu da rabi da batan ki ya ta, yau Allah ya bayana min farin ciki na, sabatu kawai mai martaba yake, d'akyar aka samu yayi shiru Anma yana rike da yar sa, bayan an zauna, Fulani ta goge digon hawayen ta ta dubi Momy tace "yanzu ke kadai zaki mana bayani ta ya akayi kika samu Kamrina.


Kamrina ce ta katse zancan da cewa ni zan fada muku komai, nan kowa ya tsura mata ido, hawaye ta share nan ta fara basu labarin rayuwar ta tun tasowar ta da wanda ya rike ta, jama'a da dama sunyi matukar girgiza dajin labarin yayin da suka tausaya mata, ana koke koke, .....



Sarki Abdullah ne yayi gyaran murya, yace "kwarai inada masaniya cewar akoi wanda zai Bata à cikin yaya n'a, kowa ya kuro masa idanu cikin mamaki, yace "tun ina karami rahaunin baba na wanda n'a gado ne suma kuma musulmai ne, suna bamu kariya ga duk cutar da Za'a mana, anma mu munce Allah ne mai bamu kariyar domin shi ya halice mu kuma shi aiko su, dan haka kariya tana gare sa, duk wata cuta in ta danganci family din mu ne basu bari à cuce mu, à haka har n'a girma bayan mahaifi n'a ya rasu n'a amshi sarauta suka dawo gareni, sukan yawan zuwar min fira bayan n'a kwanta barci, ba wasu bane ila Aljanna Fatima, sai mijin ta Abubacar, sukan zuwa muyita fira dasu, sunsha cemin nan gaba zanyi kuka domin kadara ta ce, haka n'a auri fatima har n'a haifi ibrahim, sanan n'a haifi Kamrina yarinyar da nafi so à rayuwa ta ,zan iya komai à kanta, kwatsam bayan an haife ta sa sati uku nayi mafarkin rafanai n'a kamar yanda nake n'a gansu ransu duk ba dadi kamar su min kuka, sukace tabas abinda muka jima muna fada ma yazo, zakayi kuka, à cikin yayan ka akoi wanda za'a d'auke, domin in ba'ayi haka ba to tabas makiyan ka dap suke da su raba ka da daya daga cikin yayan ka har abada, dan haka duk abinda ka gani ka d'auka kadarar ka ce, kuma insha Allah abinda aka d'auke ma zai dawo,komin jimawa Allah zai kare sa kuma muma muna tare dashi, yayin da Fatima matar sa tace "ni n'a d'au Alkawari zan kula da ko waye à yayan ka har karshan numfashi n'a ina kuka suka bace, na farka naci gaba da kuka n'a, tun à lokacin n'a kara kusanta da yaya n'a ina rungume da su har fada bana Son abinda zai raba ni dasu, ba kamar jaririyar Allah Kamrina, kwatsam ranar ina fada aka zo min da mumunan labarin batan Ya ta Kamrina, naci kuka kamar raina, da na tuna abinda suka ce,......... "



Mai martaba ya kali Fatima yace wanan shine asalin abinda baku sani ba.....



Salama ce akayi ta k'ofa mace da namiji ne farare kar dasu, saurayi da budurwa, Kamrina n'a ganin budurwar ta tashi zurmut bakin ta har yana rawa tace "Fatima, rungume ta budurwar da aka kira fatima tayi suka nemi guri suka zauna, suna murmushi,suka kali Fatima suka ce "Kamrina barka muna miki murnar saduwa da familyn ki bayan shekaru da dama, kowa kalon su yake a tsorace, Mai martaba Abdullah yayi murmushi ...



Yace "duk da baku taba zuwan min à haka ba na gane ku....



Nan sarki ya gabatar ma da mutanen wajen Fatima da Aboubacar.......



Take kowa ya fara matsawa cikin tsoro jin wanda suka zo gurin ba mutane bane.. .




Aboubacar yace "à wanan zamani akoi wani sarki da kuka taba samun sabani dashi, yayi alkawari sai ya dau fansa, Dan haka yayi Alkawari sai ya raba ka da abinda kafi so à rayuwar ka ,domin bokan sa yace "masa da sa hanun ka à rashin haihuwar sa, in baka manta ba lokacin kai baban abokin sa né, kun shaku sosai tun kuna yara, anma ta wanan karyar da bokan sa yayi ya daina hulda dakai, duk da kai har cikin ranka da zuciya daya kake tare dashi, sanan baka taba yi masa wani abu ba, à bayane, à fili anma shi da yake yana hulda da irin malaman tsubu sai ya yarda.

Kwatsam suna shirin yanda za'ayi su raba ka da danka Ibrahim basu samu nasara ba har Allah ya azurta ka da samun haihuwar Kamrina da sukaji irin Son da kake mata suka hada plan zasu sace ta sanan à kashe ta, tunda kafi son ta shine ni kuma na tura Fatima ta d'auko ta, tana d'auko ta ta aje ta a wani daji nesa da garin, à nan ta tsaya gadin ta har wanan maharbin yazo ya d'auke ta, Fatima ta bisa taga inda yake zaune,tun daga lokacin take gewayo wa tana duba lfy Kamrina har ta fara girma.
Anma ita Kamrina bata santa ba saida takai shekaru bakway à duniya. "




Hawaye ne ya zuba à idanun Mai Martaba sarki Abdullah, ya runtse idanu ,yace yanzu da Sarki Raiyan ne ya hana ni farin ciki, yayi sanadiyar nesanta ni da jini n'a, Alhalin ban masa , komai ba zargi ne, mai zai kaini ga masa abinda yake tunani, duk Son da nake masa, n'a d'auke sa tamkar dan uwa n'a, lokaci guda ya yanke zumunci dani har yanzu inajin zafin abun."😓




Princesse da tunda taji sunan mahaifin ta da abinda yayi, ta sulala tabar gurin hankalin ta tashe.




Kilishi ma da hafsat cikin bakin ciki suka bar gurin, yayin da Abubacar da Fatima suka masu salama suka tafi.
Sarki yayi matukar yima su Momy godiya tare da Fulani da suka rike masa ya tsakani da Allah, sanan aka gabatar masa da Kumar à matsayin surukin sa, nan ma yayi murna sosai, yace "ashe dan gida n'a ne akayi dariya, Fatima ma tasha musu godiya, sanan Sarki yaba Momy mayan gidaje biyu da ake ji dasu à kasar Rajugur ita daya Daddy daya, Suraya ma aka bata Baban gida à kasar da take, da mota guda uku, Umar sanda ma an masa kyautar gida da mota, yayin da Sarauniya Fatima ta ma Suraya kyautar sarkokin Diamond da na zinari. 💎




Kumar kam kyautar wanan doguwar mota aka masa wada take miliyoyi, tare da kyautar manyan kamfanoni guda uku, da manyan gidaje guda biyar, Sarki baban Raiyan
Kuma aka kara basa kasa goma acikin nasa wanda zasu kara zama à karkashi mulkin sa.




Fulani kam dakatar dasu tayi tace tunda taga yar uwar ta babar kyau ta ce, suma sauran dakyar suka amsa suna godiya, bayan wanan kyautar harda zunzurutun kudi, Momy kam tasha kukan farin ciki, b'angaren kilishi naira millions biyar biyar aka basu, ba kumya suka amsa Anma cike da kyashi.


Sarki saida sukayi kwana biyu suka tarkata Suka tafi harda Kamrina da Fulani da Momy, Kumar ma da Princesse da ta matsa sai taje ganin kwam ba'a barsu à baya ba, kai harda Rukayya wada tunda taga Ibrahim taji Son sa ya shige ta farat daya, anma Sam bata nuna ba, yayin da shi kuma Ibrahim Da yake miskili ne bai ma nuna ya san da ita ba. domin biki ne baba za'a shirya ma Kamrina.

Har Kilishi da Hafsat sunzo.

Kai Kamrina taga gata ba kadan ba.....
.




Suna zuwa, ko wanen su ya d'auke wuta da suka ga kyau da tsari irin n'a gidan Sarki Abdullah abin kalo ne. Kumar kam ya tsure da irin daular gidan, D'akin Kamrina aka bud'e mata Wanda kulum yake kule bayan amintatun bayi suna gyara sa kulum. D'aki ne da gadon ta ma na zinari ne, wanda nidai ban taba ganin irin sa ba, akwatinan kayan ta ma na zinari ne, kai ko mai zaka duba to n'a zinari ne, wayo Allah Princesse da Rukayya da hafsa da Momy da kilishi kusan suman tsaye sukayi .






Aci gaba da gashi 🍇
Maimou Love😘







Kuyi hakuri da wanan🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
*WACECE NI KAMRINA*
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀






*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM*💋







*Yar daki na Kellu, wanan book gadaya sadaukarwa ne gare ki, godiya ta bazata isa ba*



*Ina matukar godiya gareku ,har abada bazan manta karamcin ku gare ni, nagode nagode, yan groupe Maimouna M Abdoul 3 Novel, wly ina Alfahari daku kune kamar haka*
👇👇👇



*My yar daki*
*Kellu*
*Aisha Aminu*
*Hajiya Wasila*
*Maman Ummi*
*Aysha Naseer*
*Maryam Kolo*
*Zainab K/Bai*
*Hassana Ado*
*Halimatu Sadiya(Maman Khadijah*)
*Fatima Zarat Azare*
*Bilkissu Abdoulahi*
*Rashida Abubacar*
*Firdaussi Ibrahim*
*Rukaya M Adam (Maman husna*)
*Aishantyna*
*Limat Aliyu*
*Israt Nasir*
*Maryam K Abdoul*
*Az Zahra*
*Fatima Bello*




_Nagode matuka, tataunawar ku akan novel dina ya sani nishadi, da farin ciki marar misaltuwa, Allah sa ku dore haka n'a dinga jin dadi na_😍😍😍😍😍😘 .



*Dedicated to Fatima Kelu*






*Page 79-80*





Princesse ji tayi ya ta mutu dan bakin ciki, wai ace kishiyar ta tafi ta, tayi da na sanin biyo su, kilishi ma da hafsa tabe baki kawai sukayi, anma sosai sukayi mamakin, irin daula ta wanan gida.

Kumar d'akin su daya da Ibrahim, dan Ibrahim yace tare zasu kwanta, Kamrina kam sarauniya Fatima tace tare zasu zauna, yayin da Kamrina karama ta marairaice tace "Anmi ni kin yaye ni ko "
Da yake haka take kiran sunan mahaifiyar ta, kowa dariya yake yayin da Kamrina ta mata gwalo, tace "ai ke kin jima ni kuma ana ramamin n'a shekaru na ne, saida Fatima tayi kwala , Dan Kamrina ta bata tausayi, raba da da uwar sa tun yana yaro.
Yau kwana daya kenan da zuwan su,
Kumar ne d'akin Ibrahim ,sanye yake da kananan kaya yayi kyau ya hadu har ya gaji.

Tunanin Kamrina ne da son ta suka baibaye zuciyar sa,yayi nisa cikin tunanin Ibrahim sai zance yake masa anma ina yayi nisa, Princesse tifa ce tayi salama ta shigo, Ibrahim ya ganta suka gaisa sama sama ya fice daga d'akin, tsaye tayi ta rike kugu tana rike da kugu, sai jijiga take, yayin Da kumatun ta da tumbi suma suke rawa, sai cika take tana batsewa, tace "kai ,kai malam ni ka tashi kawai mu koma meye abin tsayawa kuma."
Jin yanda aka cika masa kune da ihu yasa ya dawo daga hayacin sa, kalon ta Kumar yayi n'a yan wasu seconde sanan daga baya à hankali ya budi baki yace "ina zamu kuma.?


"gida ta amsa masa kai tsaye,."


Kalon ta yayi dakyau, yace "dama kinzo ne dan ki takura min, naga ke kika matsa sai kinzo, kuma kinzo to meye n'a matsa min "

"au ai dama kace haka tunda kabi ka nace ma wacan kodadar, an wanke an baka kasha, mtssss, to in kai an shanye ka ni ba'a shanye ni ba, kuma bara kaji ni bazan zauna gidan su kushiya ba, inda ake ma mahaifi n'a shairi ba. ."
🤷‍♂fine ga hanya nan zaki iya tafiya
Ba Wanda ya rike ki. " ...
"au haka kace ko, to ai banyi mamaki ba dan an gama da kai mtsss. "
Tana gama fadar haka tayi ficewar ta, shi dariya ma ta basa, komawa yayi yaci gaba da tunanin sa, Kamrina ce tasha shiri cikin alkyabar ta, yayin daga ciki tasa riga da wondo n'a englishe wears daga bisani tasa bakar alkyaba, ita kadai take yawace filin gidan tana kara yaba tsaruwar gidan nasu.

Tayi kyau sosai, yyin da Kamrina karama take tare da Rukayya harda hafsa à garden wanda ya hadu iya haduwa,sam.Kamrina bata san Suna fita ba ai da bazasu barta ba. .


Kamrina duk inda ta huce sai fadawa ko kunyangi Sun gaishe ta.tana amsa musu cikin fara'a, direct part din yayan ta Ibrahim tayi,

Please Login or Register in order to submit comment