Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

domin tun jiya aka nuna mata part din, ta tafi domin suyi fira da dan uwan ta, sai murmushi take, hada hawaye ke zubo mata na farin ciki, à cikin ranta take cewa yanzu nima ashe inada yan uwa masu so na, ashe nima zanga wanan ranar, yanzu wanan gida da daula duk ta gidan mu Ce, hum duniya Kenan mahakurci mawadaci., à haka take zancan zuci har ta karasa part dinsa tana yaba haduwar b'angaren, shiga tayi da salama, tana kiran bro bro kana ina kazo muyi fira, kaga Rukayya da Auta sun tafi sun barni ni kuma bansan inda sukayi ba, ta karasa fada cikin shagwaba, duk à tunanin ta yayan ta ne kwance, da taga Kumar, shiko Kumar sai wani lumshe idanu yake, yana kara jin wani irin à ransa, domin tun a k'ofa sanyayan kamshin turaren ta da yaji ya tabatar masa da ita ce, jin muryar ta kadai tada masa sha'awar sa yake, bare kuma ya ganta, bai taba tunanin yana Son ta har haka ba, wani irin nishadi yake ji d'à yaji ta, dama idanun sa gangar jikin sa ita kawai suke bukatar gani.



Kamrina nata sambatu har ta karaso gap da gadon ,saida ta daga kai taga wanda ke gurin ,take ta rikice ta rude, cikin i ina tace so so sorry, nayi tunanin yaya Ibrahim ne, juyawa tayi zata fita, taji an kamo hanun ta cikin zafin nama.
Cik'e da tsiwa ta juyo tace "yadai ?


Lumshe idanu Kumar yayi, ganin komai tayi kyau yake mata, ga wani kyau da ta kara,a hankali cikin muryar sa mai dadin sauraro yace "ke haka ake zaman aure ina matsayin mijin ki ,kuma yaya à gun ki anma baki san ki gaida ni ba, ko banci darajar miji ba, ai naci darajar yan uwantaka.



Da zata masa masifa Anma da taji ya ambaci yan uwa sai tayi sanyi, ko ba komai ai yaci darajar yan uwan taka, à hankali tace "kayi hakuri, ina kwana."

Wani sanyi yaji, ko ba komai ya samu lagwanta. murza yatsun ta yayi à hankali saida tsigar jikin ta ya tashi ,juyowa tayi tace "sakar min hanu n'a zan tafi ."


"haba my love kiji tausayi na ki yafe min mana"


"Look, yaya Kumar ni na riga da na yafe ma, hakan kuma ba wai yana nufin da ina sonka ba,."

Matsowa yayi zai rungume ta, tun k'arfin ta tasa hanu ta tura sa sai ga kumar yana neman faduwa dakyar ya tsaida kansa, ranta à bace ta nuna sa da dan yatsa, tace "kar ka sake gangancin taba jiki n'a, sam babu dugon Son ka à raina dan ni da zaka taimake ni da ka sake ni wly ."

Tana gama magana da gudu tabar sashen.



.


Buga hanun sa yayi jinkin gado hanun sa saida yayi jini ran yan maza ya baci yau ,shi kam ya gaji, da wahalar da matan sa suke basa Dan haka aure kawai zai kara ,in ba so ake sha'awa ya kashe sa ba, har su koma gida zai ma mahaifin sa magana.

Princesse ko kasa tafiya tayi, Dan kanta da yake sara mata. Gagarumin taro aka hada wanda ba'a taba yin irin sa ba, yan uwa n'a nesa da na kusa duk sunzo, kuma sunyi murnar ganin yar su ,sosai aka kayata taro, Fulani ma taga sauran dangin ta na uwa anyi kukan farin ciki, Kumar ma ya halaci taron anma ransa ba fara'a, itakam Kamrina ko à kwalar rigar ta.



Bayan kwana biyu jama'a an watse, Princesse ta fara wani matsanan cin ciwon ciki, hankalin su Fulani à tashe ,Kumar ma haka, aka kira doctor, yayi yan gwaje gawajen sa bayan yan mitintuna ya tabatar musu da ciki ne da ita wata biyu.


Wayo kuzo kuga farin ciki wurin family, ba kamar uban gaya kumar har sujada yayi ya gode ma Allah, dama kulum addou'a da yake kenan Allah basa haihuwa, Kamrina ma tayi matukar farin ciki domin ita mutum ce mai Son yara. Kowa yayi farin ciki, nan aka bata magani tasha.kumar ba kumya ya rungume ta.


Kichen Kamrina ta shiga ta fada ma masu aiki duk wani ganyen da za'a hada mata suka hada da kanta ta zauna ta hada juis n'a masu ciki masu kara musu lafiya, kilishi ta hadu da ita zata shiga kichen , domin ita kilishi tana ganin wanan itace dama ta d'aukan fansa, tace " à ya ta mai kike à kichen kuma ?

Da fara'a Kamrina tace "wly wani juis ne mai kara lfy nake hada ma Princesse. "

Dariya kilishi tayi tace "kin kyauta ai ko, bari na Dan zaga. "


"OK Kamrina tace bata kawo komai à ranta ba ta shiga d'akin ta, d'auko wani mahadin.


Da sauri Kilishi ta shiga kichen Din, yan aiki tayi sa'a suna ayukan su basu ma lura da ita ba, can inda taga wayar Kamrina nan ya tabatar mata da ita ke gurin, à hankali ta bude wata leda, ta zuba magani à cikin mahadin da Kamrina tayi ma Princesse, tayi saurin fita .


Kamrina n'a komawa ta gama hada juis din ta fito falo à lokacin daga hafsa sai Rukayya da Fulani sai Kamrina karama, sai kuma Princesse da take jikin Kumar, da fara'a Kamrina ta karasa ta mika mata cup din tace "gashi kisha zai kara miki lfy da abinda ke cikin ki. "



Princesse ta kali Kumar ya daga mata gira alamun ta amsa, itama bata kawo komai ba, ita dai burin ta ta samu k'arfin jiki, nan ta kafa kai tashanye duka, Dan taji dadin abun .







Aci gaba da fashion🍇
Maimou love 😘🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
*WACECE NI KAMRINA*
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀






*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM*💋









*Page 81-82*







Princesse nashan abinda Kamrina ta bata ta samu yin barci À jikin Kumar, gefe daya Kamrina da Rukayya zaune suna buga game à waya, kadan kadan tana satar kalon su Kumar wani bakon abu take ji in taga yanda Kumar ke shafa jikin Princesse, wata irin kara Princesse tayi wanda yaja hankalin mutane ba kamar Kumar da yafi kowa rudewa, hanun princesse rike da Ciki yayin da take nukurkusu, jini ne ya bale mata, ganin haka Kumar ba karamin ruduwa yayi ba.


Idanun sa sunyi jawur ya ma kasa magana, take mutanen gidan suka fito, harda Kilishi, Anmi ce wato Fatima cikin ruduwa ta kira doctor, Princesse ko sai kuka take, domin azaba take sha, à rikice Kamrina itama take dan ta rasa wani taimako zata bada, ta rude sosai, doctor n'a zuwa yaga halin da Princesse take, yace maza à d'auke ta suje asibitin cikin gidan domin baida isasun kayan aiki à gun sa, Kumar ne ya sungume ta, suma suka mara masu baya.

.


À mota suka isa asibitin cikin gidan, nan aka shiga da Princesse, doctor sunyi iya kokarin ganin sun ceto cikin jikin Princesse anma Allah baiyi ba, ciki ya zube, nan suka gano tasha wani maganin zubar da ciki ne.



Bayan awa daya doctor ya fito yace Kumar ya same sa Office, Kumar kamar yayi kuka ya bisa, su Fulani ma hankulan su duk à tashe.




Guri Doct ya nuna ma Kumar ya zauna, ba musu Prince ya zauna.

Doct yace "Ranka ya dade saide kayi hakuri, akoi matsala,yana fadar haka yayi shiru, waro idanu Kumar yayi duk ya rikice, yace "doct karka ce min ciki na ya samu matsala plz😭domin wly bazan iya d'auka ba."

Dr ko ya girgiza ganin yanda Kumar ke kuka, anma ya ya iya dole ya fada masa, domin shi yafi kowa cancanta da ya ji.


Nisawa Dr yayi yace "plz kayi hakuri, duk abinda kaga ya faru rubutace ne, cikin matar ka ya zube wato tayi bari ,sakamakon wani magani da tasha cikin wani juis ko wani abu dai mai kalar juis.
Kuma shine abu na k'arshe da tasha.

Tunda Dr ya fara ma Kumar zancan ciki ya zube, yake juya kai cikin takaici, yayin da idanun sa suka kada, jijiyoyin kan sa na tashi, anma yana fadin abinda tasha n'a k'arshe, ran Kumar yayi kololuwa wajen tashi..


Wani irin fita yayi kamar zai tashi sama, zan iya cewa tunda nake ban taba ganin bacin rai irin na yau ba a fuskar Kumar, fita yayi à harabar wajen asibitin kowa n'a gurin banda mai Martaba da yake gurin wani taro.


Wurin Kamrina ya nufa, kowa n'a gurin ya tsorata ganin yanayin sa, yana isa baiyi wata wata ba ya zabga ma Kamrina mari, wanda kowa saida yaji Marin, Fulani à fusace itama ta tafo ta mare sa, rai a bace tace "kanada hankali ko kana hauka ne zaka.


"Eh ina hauka ne,cewar Kumar da ya amsa ma Fulani, kowa na gurin ya tsorata da kalaman sa, à hasale yayi gurin sarauniya Fatima ya duka yana kuka ya rungume kafafun ta, yace "Anmi kinga abinda Kamrina tayi min matata kuma yar uwa ta dan ta tsane ni ta zubda min ciki ,maman dan kawai d'aukan fansa abinda n'a mata, wanda koda za'a kashe ni bansan nayi hakan ba, nan ya zayana musu zaman su da Kamrina da komai sanan ya fada masu zubar masa da cikin mata da tayi, kowa ya girgiza aka koma kalon Kamrina domin duk sunsan itace mutum ta k'arshe da ta ba Princesse abu tasha. itama à rikice take ta ma rasa bakin kare kanta jin shairin da aka mata, ganin shirun yayi yawa yasa kowa gaskatawa, cikin wani irin rudu Kumar yace "jini na kika zubar akan kin tsane ni, to yau zan kawo k'arshen kiyaya, office din doctor yaje ya samu biro da takarda, yayi rubutu ya fito, yakai duban sa ga Rukaya yace "yar uwa ki kular min da Princesse, sanan ya kai duban sa ga Fatima Anmi, yace "ki yafe ni Anmi nasan ke zaki yi min adalci, takarda ya ba Kamrina yace "kije n'a sake ki saki daya, yana gama fadar haka yabar asibitin cikin matsiyacin gudu,dan kar ma Fulani tayi gangancin tsayar dashi, baisan Fulani ta ma shiga chok ba bata ma iya magana. filin jirgi yaje ya ciri ticket n'a zuwa US.yayi sa'a ya samu, jirgin k'arfe shida n'a safen gobe, Hôtel yaje ya d'auki d'aki daya ya kwana zuwa gobe.









Aci gaba da gashi🍇

Maimou Love😘🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
*WACECE NI KAMRINA*
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀






*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM*💋







*duba ga yanda kuka damu da Son yau nayi muku typing din Kamrina shi yasa nayi, domin yau Aï ce ya kamata ta fafata, anma kun amshe mata wuri ,ba ruwa na zata iske ku*🤣







*PAGE 83-84*






Tunda Kumar yaje hôtel, ya shiga d'aki, ya fara kuka ,kuka yake sosai matuka, wanda tunda uwar sa ta haife sa bai taba irin wanan kuka ba, kuma shi kukan sa da biyu, na bakin cikin tsanar da Kamrina tayi masa har zata iya,raba sa da jinin sa, cikin da ya dau shekaru yana rokon Allah ya basa da sai yanzu yaga samu kuma yaga rashi, why why Kamrina me yasa zakiyi abinda zaisa ma zuciya ta tsanar ki me yasa, kinsan à duniya kece mutum ta uku da nafi so à rayuwa n'a daga iyaye n'a sai ke me yasa me yasa."

Ya jima yana wanan sabatun dakyar ya samu yayi barci...




B'angaren su Fulani saida Kumar ya fita daga harabar asibitin ta ankara Cikin fushi zataje ta masa magana Ànmi ta rike ta, ta girgiza mata kai.



Kamrina kam tunda ya bata takarda ta kasa motsi, takai minti goma à tsaye Rukaya ce ta taba ta ta riko ta,sai ji sukayi Kamrina tayi suuuu ta fadi kasa sume, hankula suka tashi, aka d'auke ta sai wani d'aki aka kwantar da ita, taimakon gagawa aka Bata, anan Fulani Momy da Anmi suka kara tabatarwa cewar akoi boyeyen Al'amari akan zubar da cikin nan duba ga yanda Kamrina ta kasa magana da mamakin zubar da cikin da akace tayi, wanda bata aikata ba.


D'akyar aka samu Kan Kamrina ta farfado, koda ta farfado ma kasa magana tayi sai idanu da take bin kowa dashi....



Fulani n'a kuka tazo ta kama hanun Kamrina tace " ya ta kiyi hakuri nasan bazaki iya kashe ko dan tsako ba bare ki raba uwa da cikin ta ba,nasan da wata kasa. "



Kilishi ranta ya dan sosu tace "haba Fulani à gaban ki dai kinji abinda dan nan ya fada, ya kamata in yaro yayi ba daidai ba a dinga tsawatar masa anma ba wai à dinga basa goyan baya ba ana yarda da abinda yace. "


Tunda Kilishi ta fara magana Kamrina tayi kur ta kure ta da idanu, kamar tana nazarin wani abu anma ganin haka da Kilishi tayi saida cikin ta ya bada kululu, tsoro ya kama ta kardai ace yarinyar nan ta fara gano ni. "


Kilishi tace cikin ranta, tsab kilishi taja Hafsa à zuwan zasu je ganin jikin Princesse.




Kamrina kam ta kasa cewa komai da ta kali fuskar Anmi ta sai taji ba dadi ganin tana fushi da ita, itakam meye ke shirin faruwa
Da ita ne,ga wani daci da zuciyar ta ke mata na sakin da Kumar yayi mata, wani abu ya tsaya mata a wuya mai daci, wanda shi ya hana mata magana sam ya tokare mata makoshi.



Ga bakon al'mari da ke shigar ta, ya akayi ita da ya kamata tayi farin cikin sakin anma take bakin ciki. Yau ta kasance rana mafi muni à rayuwar ta, me yasa kumar zai mata haka, me yasa zai yanke tsatsauran hukunci à kanta ba tare da yayi bincik'e ba, wata irin kara tayi mai cike da razanarwa Wanda ya tada hankalin jama'a gurin....


Da sauri suka nufo ta, ihu kawai Kamrina keyi kamar mai iskoki, can kuma ta kece da wani matsanancin kuka, ta Rude Rukayya da itama hawaye take, Rukaya ta kali Fulani tace"Fulani wly ni nasan akoi wata à kasa ni na zauna da ita nasan ko daba bazata iya kashewa ba bare zubar da ciki , akoi lokacin da tazo tana kuka n'a tambaye ta tace wata yar classe dinsu ce sunje asibiti koyon aiki wato stage akace tayi ma wata mai ciki alura ciki'n matar wata biyu Anma sai ta hada wata alura ta mata sakamakon ta manta Wada akace ta mata, ashe ta zubar
Da ciki ta mata .shine Kamrina tazo gida takai kwana biyu tana kuka wai kawar ta ta kashe rai.

Hum abinda yanzu daga likitoci har stagiaire wato masu koyan aiki suna wanan gangancin.




Wai sai kaga ke stagiaire kinzo koyon aiki asibiti maimakon ki aje hankali ki koya, ko in baki iya abu ba ki tambayi n'a saman ki wanda ya iya ya nuna miki à'a sai kuga tasa girman kai ita tafi karfin ta tambayi n'a kasa da ita ko na sama da ita, sai kaga tayi abinda bashi ba, Bata bin ka'ida maimakon tayi abu kaza sai tayi wani daban, kamar ace tayi alura kaza, bata san ta ina zatayi alura ba ta hanu ne ko jijiya, ko ta bayan duwawu, ko ta cinya, sai kawai ta tsula ta inda taga dama, kuma baza'ayi ta daidai ba saide ayita wani gurin daga nan sai à maida mutum gurgu ko wani daban, to wly har ma'aikatan Wanda basu san aikin su ba hakan suke, dan Allah yan uwa à dinga aje hanakali ana koyan aiki, in kaga abinda yayi k'arfin ka à matsayin ka na likita ko mai koyo, kai tsaye kace baka iya ba, ko kuma ka tambaya hakan ba matsala bane.


Sanan kuma masu karatun ku tsaya ku aje hankali ku iya pratique ku iya théorie, kuda kanku zaku ji dadi in kun iya aikin ku.




To yanzu Fulani wada take wanan kukan kwana biyu akan abinda ba ma ita tayi ba ya zata iya yin wanan danyan Aikin.

Fatima wada yanzu take Anmi, tace "hum to Rukayya yanzu kowa zai iya bacewa, wata kila.


Hakan ce ta faru ga yar uwar ki, kinsan kowa n'a iya kuskure kuma dan Adam kan iya canzawa à ko wane irin lokaci .


Wata kila itama hakan ce ta faru da ita, tunda ta kasa kwantar ma da mijin ta hankali ta kasa biyaya ai zata iya komai ma. "

"Ya isa !

Fulani ta daka ma Anmi tsawa, meye haka diyar ki ta cikin ki, keda ya kamata ace kin lalaba ta nayi imani cewar Kamrina bazata iya Aikata abinda ake zargin ta dashi ba."


Sanyi Anmi tayi dan itama tasan ba yar ta bace, anma ya ta iya ko ba ita bace dole à nuna mata kuskuren ta na abinda tayi ma mijin ta.



Wayar Anmi ce tayi kara ta fita daga asibitin, Kumar ne t'a daga ya gaida ta, ta amsa cikin farin ciki, tace da na kana lfy ko ? "Eh Anmi dan Allah kuyi hakuri abinda nayi ma yar uwa ta, à kula da ita Yar fira suka dan yi nan yake shaida mata zai bar kasar anma dan Allah kar ta fada ma kowa inda yake hakuri ta kara basa sukayi Salama, sosai take son Kumar ya ita ta haife sa.



Can b'angaren Momy ta rungume Kamrina tana lalaba ta.




Washe gari jirgin su Kumar ya tashi sai US, yayin da ya karye duk wani layi da Za'a same sa dashi.


A ranar kuma Aka Salami su Princesse, taji duk abinda Kamrina tayi mata a bakin Kilishi, duk da dama tasha zubar da cikin Kumar dan ko kadan bata sha'awar Yaya, anma wanan taci buri à kansa sakamakon shawara da rabi ta bata kan cewa ta samar ma Kumar magaji ta yanda danta ne zai gaji uban sa, ba dan wata ba, da wanan shawarar ta bar shan komai na hana d'aukan ciki, har ta samu wanan kuma Kamrina ta zubar mata, duk da taji an sake ta tayi murna sosai anma ta d'au Alkawarin sai ta rama sai ta kuntata ma Kamrina. À ranar ta matsa lalai sai an kaita gida wajen iyayen ta, ba yanda Fulani Suka iya haka aka mata komai jirgi ya d'auke ta sai kasar Bagadur, kasar ta asali.








Aci gaba da gashi 🍇
Maimou Love😘🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
*WACECE NI KAMRINA*
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀






*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM*💋









*PAGE 85-86*






Yau kwana biyu da saki Kamrina su Fulani Sun hana à fada ma sarki Abdullah sakin Kamrina, Anmi ta yarda ne ba tare da wani damuwa ba, ita kadai ta barma kanta sani, Su Fulani sunyi salama zasu koma gida, Kamrina kam ya ta kwala ihu domin tafi sabawa da su Fulani, suma su Fulani sunso tafiya da ita anma ganin yanayin da ita Kamrina ke ciki sai suka Barta tana kuka suma haka suka Tafi cike da kewa. .......





Tunda suka tafi gabadaya abu ya kara rikice ma Kamrina batada wani muradi yanzu da ya huce taga Kumar ji take ya tayi hauka.



Zaune take ita daya tayi zugum yau kwana daya kenan da tafiyar su Fulani Anma ta kasa sakewa, zaune take ita kadai ta zuba ma TV idanu kamar
Tana jin mai ake cewa ànma sam bata ma San tsiyar da ake yi à TV ba, tunanin Kumar ne take yanda yake Romancing dinta, murmushi take har tana dan boye fuska kamar yanzu abin ya faru, ko yana ganin ta, tuna yanda yake rudewa in yana wasa da jikin ta tun bai je ga baban ba, wani abu taji kasan ta ta taba, ji tayi duk ta jike à kasan ta, Anmi Fatima ce ta fito ita da Kamrina karama suka zauna kusa da ita, Anmi ta lura diyar tata ta rame à yan kwanakin nan, dafa ta tayi firgigit sai gata ta dawo hayacin ta, Murmushi Anmi tayi tace "rabuwa da miji koda baka Son sa Akoi ciwo, yanzu wa gari ya waya, ya miki laifi ya baki hakuri ya zubda girma da kima irin tasa ta namiji ya baki hakuri anma da yake ke k'afafar zuciya gare ki saida kika raba sa da jinin sa. "


"Kuka Kamrina ta kece dashi "ciki'n hawaye tace "Anmi ki yarda dani ba ni na zubar da cikin matar sa ba, Allah ya sani ni Kamrina ba haka nake ba, na tabatar da apou n'a da rai shi kadai yasan wacece ni, yasan ba ni bace .

Na yarda nayi ma miji n'a laifi à baya à bisa rashin sani anma banda wanan da ake zargi n'a "



Tabas taba Anmi da Kamrina tausayi, Kamrina tace "na rantse da Allah banida hanu à zubda cikin nan. '


Nan ta fashe da kuka.

Tsinkayar muryar Ànmi tayi tana rarashin ta cikin tausayawa, itama tace "nima nasan ba ke bace ya ta, duk da baki tashi hanun mu ba Anma nasan jini n'a bazai aikata hakan ba,ina so ki fada min tsakani da Allah kina son mijin ki ko kuwa ?



Sune kai kasa Kamrina tayi tana Dan murmushi tace "Anmi wly yanzu ina son sa. "



Murmushi Anmi tayi takai mata dukan wasa tace "ja'ira kawai ."



Kamrina karama ma dariya tayi, tun daga lokacin Anmi da kanta take gairan Kamrina .



B'angaren Ibrahim yayan Kamrina baya kasar anma gabadaya ya susuce Sam bai san Son Rukaya ya shige sa haka ba, dan Allah Allah yake ya gama abinda yake ya dawo gida ya sanar ma da iyayen sa.


Itama Rukaya tana can da ciwon so an kasa gane kanta.


B'angaren kilishi komai ya rikice tunda suka koma gida kulum dadare sai anyita zabgar ta da bulalar da bata san daga ina take fitowa ba yayin da kananun halitu masu muni ke fito mata suna bata tsoro, yanzu kulum dare sai ta wahala, abun ya ishe ta domin duk kamanin ta ya tsanza ita kadai tasan abinda take ji, ga hafsa ta rikice mata lalai ita Ibrahim take so yayan Kamrina In ko bata sâme. Sa.ba ta shiga duniya, saida kilishi tayi sati tana shan wuya tukon aka sarara mata, anma Sam ba alamun nadama.

Tunda Princesse tifa ta sauka gidan su tana kuka ta fada ma uwar abinda Kamrina tayi mata, mahaifiyar ta taji ciwon abun sosai, ai kuwa washe gari tace "maza suje wurin boka, boka yana jin bayanin su yace "lalai Aiki ne baba, dan haka Princesse ta dawo dadare, aiko Princesse na dawo Wa boka yace "yanzu mai kike so à miki ne ?

"boka so nake à kara sa ma miji n'a tsanar Kamrina kar ya maida ta har abada sanan asa masa matsanancin so na ta yanda zaifi jin magana ta fiye da ta uwar sa. "




Wata dariya boka ya kece da ita, yace "an gama anma wanan aiki dole sai aljani tsigu ya kwona dake, za'ayi aiki da sperm dinsa da naki za'a hada da maganin da zaki sa ma mijin ki à abinci yana Ci an gama ko uwar sa kika sa ya zaga zai aikata ba tare da shayin komai ba. "



Ba wani bata lokaci Princesse ta yarda duk da tuna wahalar da tasha àcan baya da tayi, Anma da ta tuna biyan bukata tafi komai aiko ta yarda....
.



Boka harda lashe baki, sa

Please Login or Register in order to submit comment