Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amso duk wani abu da ya danganci gasar Kamrina, gyarar kam sun sha SΓ‘, nikam baki na yanzu bazai iya fadar kyan da su Kamrina sukayi ba,
booking din jirgi sukayi, dan saΓ­ sun kwona daya a kasar Rajugur, dan Aminiyar ta tana son ganin ta, hakan yasa saΓ­ sun sauka masarautar kafin su karasa, ga gasar saura sati daya.








Aci Gaba da gashi πŸ‡
Maimou LoveπŸ˜˜πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
*WACECE NI KAMRINA*
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€







*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*πŸ’‹






✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
πŸ’«
*🌟🌟TAURARI WRITERS ASSOCIATION*..............✍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨







*PAGE 17-18*







Su Momyn Suraya suna isowa, daya daga cikin drebobin gidan su kumar Fulani ta aiko,,,,,, yana ganin su yaje ya tarbe su ,nan suka shigo Mota saΓ­ baban gidan sarauta birnin Rajugur,baban gida ne gari guda, dan ko kuyangin gidan yan gata ne, ko wace d'akin ta da AC, fadar tsaruwar ku kanku kuyi imagine kunsan fadar tsari kyau dukiya baki kam bazai iya lisafawa ba, saide muce Masha Allah daula kam an same ta ta duniya saΓ­ kuma ta lahira .

Ko a cikin gidan doguwar tafiya suka sha a motar ma kafin sukai b'angaren Fulani, guri ne da duk yafi ko ina na gidan tsari da kyau da haduwa, saboda son da sarki yake mΓ‘ matar sa Fulani sam bai hada ta da kowa ba, ko nasa b'angaren dap yake da nata,.


Shin ban fada muku fulani nada kishiya ba, to fulani nada kishiya, sunan ta hajiya hauwa, anma suna kiran ta da kilishi....



Fulani nada son Jam'a da fara'a, tana son danta ya auri yar kworai yar da ta fito daga dangi, acewar ta sune masu tarbiya, danta zaiji dadin zama da ita.


Kilishi makirar mace, muguwa, sam batada hali mai kyau, tana da diya daya tak Hafsatu ita ta gaji halin uwar ta,yar kimanin shekaru ashrin, sai Abida yar da take riko wada taci burin ko halin yaya ne saΓ­ ta aura Prince Kumar ita ,dan tacika wani burin ta,Prince Kumar tun yana yaro take gana masa azaba taso kashe sa ta hanyar shake sa da filo, anma Allah da yayi da sauran kwonan SΓ‘ a gaba saΓ­ ya rayu, itama tana da kyau sosai anma fulani ta fita komai,sam daga sarki har fulani basu san mugun halin kilishi ba, har shi Kumar din, har yanzu ko da take zaune tasha kula ma Fulani makirci, anma da Yake ita ta rike Allah to saΓ­ abin ya koma kan kilishi.....

Wanan shine kadan daga cikin tarihin matan gidan .


Fulani a waje da dan saurin ta taje ta rungume kawar ta, nan ta kamo su suka shigo kayatacen falon dake d'auke da kujeru na Alfarma na kece raini, falon kam yaji kayan alatu..........

Bayan sun gagaisa an dan taba firar yaushe rabo, nan aka cika gaban su da kayan yayan itatuwa, su inibi, ayaba, aple lemu, da sauran su, Fulani tasa kuyangi su nuna mΓ‘ su Suraya d'akin da zasu huta, hada Kamrina wada har yanzu take sanye da nikaf, Fulani dai da kalo ta bita.

Sai daga bisani ta juyo da kalon ta ga Momyn Suraya bakin ta cike da tambayoyi, murmushi Momy tayi tace "hum mutuniyar nasan mai zaki ce, wanan wada kika gani sunan ta Kamrina, marainiya ce, uban ta dan uwa na ne, wanda tun yana karami ya bace saida ya girma yayi aure tukon asirin da kishiyar uwa ta masa ya dawo, da matar sa da ya aura a daji da ya daya wato Kamrina sunzo ne Za'a kaisu dangi su zagayo shine motar su tayi hadari daga nan duk suka mace, niko dama na d'auki Kamrina, wanan shine dalilin da yasa na rike ta taci gaba da zama wuri na, maganar rufe fuskar ta wani sirri ne, anma ke dole ki ganta da zarar sun tashi.... "
Murmushi Fulani tayi tace Allah taya ki riko wly har taban tausayi. "

Ita daΓ­ Momy dan murmusawa tayi anma bata ji dadin karyar da tayi ma amiyar ta ba, anma ba komai tayi haka ne dan tasan halin kawar ta..





Fulani tace "uhum Bazaki ki shiga ba ku gaisa da Kilishi ba."

"Ai fa saΓ­ kiyi ba inda zani wly"cewar Momy dan ita sam Kilishi bata mata ba ta tsane ta...........

Prince Kumar ne ya shigo ya duka ya gaida Momy ta amsa tana fara'a, sun dan taba hira, Fulani tace kanwar ka Suraya tazo fa, anma yanzu suna hutawa in anjima kun gaisa, dariya yayi sanan ya fita.


Garden dinsa ya nufa, wurin hutun sa, harda wankan in yana son hutu nan yake shakatawa sa....


Su Kamrina ba wani barci sosai zukayi ba suka tashi, dan ba wata gajiya suka kwoso ba, wanka sukayi suka sake kaya, yayin da Kamrina ke sanye da doguwar riga abaya fido hips dinata, sanan tasa nikaf, ta kali Suraya tace "sis nifa yanzu har na fara sabawa dasa wanan,. "


Dariya Suraya tayi tace "kawanta yanzu ai kin zama Ustaziya sai yanda Hali yayi. "

Dariya suka kwosa duka, sanan Suraya tace" kinga zo mu fita kiga tsarin gidan masarautar Rajugur ."

Haka suka fito suna yar hira, har falon da Fulani da Momy suke, samun wuri suma sukayi suka zauna,,,,,,,, bayan sun gaida su.

Momy tayi Murmushi sanan tace "ya ta Kamrina bud'e wanan nikaf din."

A hankali Kamrina ta yaye, Fulani kam har saida ta firgita, take tunani ya fado mata cewa anya ba Aljanna bace, dariya Momy tayi tace "kawa ta ya haka kuma🀣,


Fulani tace "wai kina ganin abinda nake kuwa, murmushi Momy tayi sanan tace Kamrina maida Nikaf din ki, Suraya kuje da ita ku Zagaya gidan, kuje wurin yayan ki dazu yazo kuna barci, da murna Suraya suka tashi suka bar falon, Nauyayar ajiyar zuciya Fulani ta sauke tace "Saratu wanan Yar kamar Aljana dan kyau," dariya
Tayi tace "kinsan mahaifiyar ta a daji suke, to yawanci akoi masu kyau kawai rashin kudi ke kworuwar su, ko wanan gasar da yarinyar nan take ci, ai in za'a bincika akoi wanda suka fita sosai to rashin, kinga ko ni bana da ya ta za'ayi gasar. "




Murmushin jin dadi Fulani tayi sanan tace "anma gaskiya kawa ta kin kauda min babar matsala ta, ga danki nan dama yace bazai auri wada bata kai Princess tifa kyau ba, to ga wata,dan ko makaho ya laluba yasan Kamrina tafi Primcess tifa kyau nesa ba kusa ba, kinga kenan saΓ­ ayo tuwo na maina .



Sosai Momy taji dadin wanan batun daga bisani aka ci gaba da zantawa.....



Suraya da Kamrina suna tafe cikin gidan saΓ­ Nun ma kamrina ko ina take, suna haka saΓ­ ga Hafsa yar wajen kilishi, ita da kawayen ta saΓ­ kuyangi da suke biyar bayan su, domin Hafsa akoi son nuna isa da mulki, ga girman kai da wulakanci, har saΓ­ ince ita da Princess tifa bansan wanda yafi wani ba tamaka da mulki da wulakanci ba.................


Hafsa na ganin su Suraya taja wani uban tsaki, ta banka mata harara, sanan "tace gayar munafukai ashe anzo, tana gama fadar haka suka tafa da kawayen ta suka sheke da dariyar rainin hankali,sanan suka shige Mota sukayi ficewar su....


Kamrina tace "anty meye tsakanin ki da wanan kuma?



Murmushi Suraya tayi tace " share su kawai banzaye ne........


A haka sukayi ta zagaya wa har suka zo garden da Prince Kumar ke shakatawa zaune Yake bisa dan gadon nan mai lilo, yana rike da jarida juis a gaban sa sanye yake da kaya kanana na shan iska, yayin dΓ‘ ya ba kofa baya, salama sukayi, Kamrina da tunda ta shigo gaban ta ke faduwa, wata rikitaciyar kara tayi ta duka yayi da ta yaye nikaf din ta, a rashin sani tsabar ruduwa ,da dan Sauri Kumar yayo wurin su a rude...........











Aci gaba da gashi πŸ‡
Maimou LoveπŸ˜˜πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
*WACECE NI KAMRINA*
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€






*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*πŸ’‹




✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
πŸ’«
*🌟🌟TAURARI WRITERS ASSOCIATION*..............✍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨







_My Kawa Mrs Adam yar mutan kagara, Allah kara miki lfy, yasa kafara_

wanan shafin naki ne_



_Ina kuke masoyan litatafan wanan hazikar, mai cike da kwonyar baiwa da basira, wato *yar Mutan Kagara* ku garzayo kar abaku labari, domin wanan karon ma wanan hazikar Yar Mutan Kagara tafe take da nata labarin, mai cike da darasi da nishadi da wa'azi, wanan book shi ake cema sabon salo, dan yana tafe da nasa salon,hum wai ko kar na cika ku da zance, bari na fada muku sunan book din, sunan dai shine_ *GIDAN SODJA*

_Hum koda jin Sunan kunsan zai bada kala, karku bari abaku labari 😍😘_



*Gidan Sodja*

_By_
_yar Mutan Kagara_







*DEDICATED TO MRS Adam Yar Mutan Kagara*




*page19-20





Ganin haka yasa Suraya cikin zafin nama saurin rufe ma Kamrina fuska,,,,,,,, ,,,,,,,, ,,,,,,,



Kumar yaga hakan anma bai wani damu ba, dan baiga fuskar Kamrina ba, zuwa yayi ya duka dai-dai inda Kamrina take, duk da cikin yanayin da take saida gaban ta ya fadi, Suraya ta katse mata dan tunanin da ta fara cewar, Sis bari n'a fada ma Momy Γ  kira doctor ya duba kafar ki duba sai zubar jini take........



Kumar cikin sanyi ya fara magana da zazakar muryar sa yace "kema ya akayi kika buge, anma koda yake Ai dole kinzo kinsa wanan abu Γ  fuskar ki, wanan ai na munafukai ne mtssss."


Kalon sa ya juya ga Suraya yace "kanwata tare kuke. "?

Ita dai Suraya bata samu damar magana ba sai kada kai da tayi,,,, dan hankalin ta ya tashi dan ganin yanda k'afar Kamrina ke zubar jini, waya Kumar ya d'auka, yar magana yayi daya ya kashe, sanan yace "ki d'auke ta kuje can b'angaren Momy doctor zaizo ya 'duba ta, duk kunzo kun wani bata min wuri kun tada min zuciya. "

Dago kai Kamrina tayi, ganin idanun da Kumar yayi cikin nikaf saida gaban sa ya fadi,,,,,,,itadai Kamrina tsabar haushi kasa magana tayi sai kalon Suraya da tayi tana mata alama da su tafi, ita kanta Suraya taji haushin cin fuskar da kumar yayi ma Kamrina......




Kama ta tayi suka koma, Kamrina tana dan dingishi,,,,
Kumar ya rasa abin da yasa ya tsaya yake kalon wanan yarinyar, "mtsss In kaga irin masu rufe fuskar nan ba wani kyau ne dasu ba ,anma sai wani rufe fuska, mtss ya kara tsaki............


Juyawa yayi yaci gaba da karatun jaridar sa hankali kwonce.




Su Momy na ganin yanda Suraya ta shigo suka rude, aiko ba'a jima doctor yazo ya duba k'afar ba wani jimuwa sosai ne tayi ba, kawai zubar jinin ne, ya tsayar da jinin ya bata diclo tasha dan saboda tabar jin zafin ciwon.......









.




To Suraya ta jata suka yi d'akin da aka basu, Kamrina tace "Anty wai waye wanan dan rainin wayon😏."


Murmshi Suraya tayi sanan tace "shine Prince kumar, nan fa Suraya ta bata Labarin sa harda n'a Princess Tifa,ba karamin haushin Princess Kamrina taji ba......

Γ€ haka dai basu kara fita ba, sukayi ta fira, har washe gari, suka shirya, sosai fulani taji ba dadi, saida aka kai su Momy suka gaida sarki.


Sanan aka kaisu filin jirgi, tunda Su Kamrina suka koma garin bagadur, suke shirye shirye ba zama domin aski ya zo gaban goshi.....



Yau saura kwona biyu Γ  fara gasa, gidan yau sai shirye shirye ake domin yau Daddyn su Suraya da Kuma Umar Sanda zasu zo, dan tare suka Je da daddyn sa, ita kanta Kamrina harda ita aka shiga kitcin domin tana son koyon girki ,K'arfe biyu na rana sai ga inji niya, da sauri Momy da Suraya suka fita tarbe, haka dai suka tarbo su, bayan anyi sanu da zuwa akaci abinci, suka huta, can da yanma Γ  tatare Umar Sanda da Mahaifin sa kamar hadin baki suka sauko, nan Momy tace tana son magana dasu mai mahinman ci, nan suka Bata hakalin su nan ta fada musu komai game da Kamrina.


Nisawa Dady yayi yace "anma Maman Umar kina ganin bazamu samu matsala ba daga ita yarinyar,"Murmushi Momy tayi dan dama tasan mijin ta akoi tausayi da taimako, shima Umar jiran amsar Maihaifiyar sa yake, dan shi bayada wata matsala dangane da hakan, Momy tace "Alhaji gaskiya yarinyar akoi tarbiya ,duk da tashin ta da tayi Γ  daji abu guda ne ke kule min kai da yarinyar, watarana in tana abu kamar ba a daji ta fito ba, kamar dai anma ba komai, murmushi Daddy yayi sanan yace "to Allah bamu ikon riketa da Amana, anma Γ  turo min ita na gani, Ameen suka Ce sanan aka kira Kamrina ta gaida su, ba Karya shi kanshi dady da Umar Sanda Sun girgiza da kyan Kamrina anma suka dake.

Daddy yace "diyata zo nan. "

Γ€ hankali Kamrina taje nan ya dafa kanta ya Sa mata Albarka, daga bisani aka Ci gaba da hira, Umar kansa jin ta yayi tamkar yar uwar sa Suraya ta jini, wani murmushi yayi da ya tuno kalaman Prince Kumar, "Umar bazaka gane bane, ni na tabata har abada ba Za'a taba samun wada takai Princess kyau ba, ai ba yau bane da za'a samu.


Murmushi yayi yace "Prince kenan yau dai naga wada In ta jera guri daya da Princess to baza à ga kyan Princess ba sai ma muni. 🀣




To Γ  haka dai aka zauna Familyn Kamrina ko ina tana samun kulawa daga wanan family ba abinda zata ce dasu sai Allah saka musu da gidan Aljanna......




Hum ance Rana Bata karya saide Uwar diya taji Kumya, Ayau ne za'ayi wanan gasa, Γ  inda bokan Princess yace tazo da kanta dan wanan karon ya hango matsala, anma sai tazo da kanta.


Da Rabi Kuyangar ta ta fada mata sai cewa tayi ba inda zata Je, ita Γ  matsayin ta na Princess taje gurin wani boka, in bazai iya ba ya bari kawai dan ita tasan ko ana ha maza ha mata sai taci gasar.......




Γ€ d'akunan gasa ko wace da d'akin da ake Bata, ita da masu yi mata kwoliya da sauran abubuwa, haka ko akayi kowace ta kama d'akin ta, su Suraya ma daga baya sukazo, Γ  yayin da Kamrina take lulube da abaya da kuma nikaf,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,

Kowa ya gansu sai yayi dariya ace abun kuma hada ustazai, sudai su Suraya Dariya kawai Sukayi da ita da mai kwoliyar Kamrina da kuma Zhara dan su suka san abinda suka zo dashi, Γ  hankali Princess Tifa itama tazo da makaraban ta sai tamaka take, kowace budurwa tasha jinin jikin ta, dan suma sunsan zuwa kawai sukayi anma matsawar Princess Tifa n'a nan saide su biyo bayan ta, dayawa jikin su yayi sanyi, itako sai tamaka take ana take mata baya yayin da Rabi ke mata kirari, ita ma shiga sukayi d'akin da aka basu domin kwoliyar ta da shiri, awa daya aka basu n'a shiri, yayin da mutane ke zaune Γ  kayatacen wuri, shugabanin kasashe daban daban, sarakuna, ministoci, mayan masu kudi, guri kam ya fara cika..........








Aci gaba da gashi πŸ‡
Maimou LoveπŸ˜˜πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
*WACECE NI KAMRINA*
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€






*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*πŸ’‹




✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
πŸ’«
*🌟🌟TAURARI WRITERS ASSOCIATION*...............✍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨







_Sorry Fans Γ  wacan page nayi mantuwa bansa number ba wato page 19-20.





_kuyi hakuri fans wasu na cewa na fara Jan aji a book dina, ko kadan ba abinda kuke tunani bane, wato idan oga yazo gaskiya bana typing sosai har sai ya tafi, to insha Allah yanzu zaku dinga ji na, har sai In Allah ya dawo dashi lfy, ina fatan kun fahimce ni nagode_😍









*PAGE 21-22*









Wuri daya Fulani da Momy suka zauna, da Umar sanda da kuma uban gaya wato Prince Kumar, duk ya kagu yaga Princesse din sa, dan yanzu fa yana jin Son ta har cikin bargon zuciyar sa ., sanye yake cikin kaya na Alfarma irin na gidan sarauta, wato shada ce fara kal, riga da wodo irin dinkin nan na zamani, Γ  yayin da tasha aikin maza, yasa, yayin da ya hauda alkyaba ta gidan sarauta irin ta maza kayan sun kama sa sun masa kyau sosai, agogon Zinari ne yake sanye dashi Γ  hanun sa mai d'aukan hankali, yayin da ya jera zobuna irin n'a maza, guda uku, daya n'a azurfa, biyun ko na zinari, fuskar sa tasha gyara sai kyan sa ya karu, yayi freshe dashi tamkar ango duk ya haske gurin.........


Sai wani zuba murmushi yake, kamar an masa kyauta da gidan Aljanna,,,,,,, shi kansa Umar sanye yake da manyan kaya yayi kyau sosai shima, yayin da fulani da Momy suma sunsha nasu Ado, b'angaren sarakune daban da na manyan masu kudi, kowa da nasa b'angare matan kuma duk sai suka hadu wuri daya .....



Kumar ne yakai duban sa ga Umar fuskar sa d'auke da kayatacen murmushi yace " aboki na ni da hakura sukayi da wanan gasar domin banga amfanin ta ba, saboda kowa yasan Princess zata cinye. "

Umar murmushi yayi yace "hakane anma ka sani bana ko a samu wada tafi Princess."


Musmushi Prince yayi, sanan daga bisani yace "ai banga wada zata fi Princess dita ba, dan karka manta kusan shekaru goma tayi tana ci so kawai wanan ma ita zataci. "


Shidai Umar Sanda murmushi yace "hakane. "





Acan ko Princess tifa ake ta ma gyara kamar za'a fida mata fata, anyi mata kwoliya wanda yasa ta kara kyau sosai ,wata riga baka wada tasha zubi mai wuyar fasaltuwa dan rigar ba karya ta hadu,aka sa mata tayi kyau sosai, takalman ma abin kalo ne... Um Princess tifa kam tayi kyau ba karya......

Bari n'a leka gurin su Kamrina nayo gulma......



Mai kwoliya ce ta dage take cancara ma Kamrina, duk yanda naso naga yanda ake wanan kayataciyar kwoliya ban gani ba πŸ˜”Suraya ta hana tace wai salon naje
Na fada ma Princesse tifa, nace Allah ni ta wajen su Ce, sanan ta gusa min, ya Allah nace domin tun kafin Γ  gama kwoliyar n'a tsure, kamar zan sakin fitsari ,tsabar kyau tsgworon sa da na gani, haka fa akaci gaba da kwoliya, ana gamawa aka zuba mata walkiya Γ  fuska da jiki, lokacin de ta juyo n'a kale ta saida ciki n'a ya bada kululu, domin zawo ya kusa kufce min, kyau kam ko mai mata make up din ta tsorata.......


Ana haka Suraya ta warware wata doguwar riga runwan gwold, tasha kyau duk da Simple ce batada tarkace anma fa duk wanda ya ganta yasan riga ce kuma ta hadu matuka.....




Ana sanya ma Kamrina Suraya tace "kai kanwa ta, kar fa ki birkita tunanin jama'a, dariya Kamrina tayi, aka d'auko mata takalma masu tsini, wata sarkar gwold ta indiya aka sa mata ta zubo har wajen cibiya, ,turare kam tasha sa, yan hanu da zobuna duk kalar rigar, aka zubo mata gashi har hucin gwiwar ta tayi kyau har n'a bala'i hips dinta sun fito sosai, kirar kalangu, ga boobs ga hips ga baya .....
Aka yaye fuskar ta da wani yadi n'a rigar mai matukar kyau sara sara. .


Tuni an fara gabatar da taro, wani matashi ne ya tsaya Γ  gaban wani tebur mai tsawo, laspika yakai daidai bakin sa, yayin da b'angare guda masu yanke hukunci n'a zaune sun fara dan rubuce rubucen su,inda aka shimfide dogon jan karpet ,inda yan gasar zasu dinga takawa, wurin yasha decoration mai kyau, wanan mutumin ne ya fara magana, cewa ina ma kowar barka da zuwa wanan taro, kamar yanda kuka sani ko wace shekara ana gabatar da wanan gasa to yau ma Allah ya kawo mu. Ba tarΓ© da bata lokacin ba zan fara kiran yangwon yar kasar china zata fara shigowa, masha Allah tanada kyau sosai itama tasha shirin ta, tazo da tafiyar ta ta zagaya yan kasar su sukayi kuwa aka tafa mata, ta fita yar kasar indiya ma tazo, da kayan su irin n'a indiyawa suma yan kasar su suka tafa mata , haka yar kasar larabawa tazo itama tasha shiri, itama tayi kyau sosai an tafa mata, bayan duk kowa ya shigo ya rage daga Princess tifa sai Kamrina suka rage, nan mai gabatar wa yace masha Allah kamar yanda kuka sani kowace kasa mutum daya ake d'auka, to wanan karon abin yazo da banbanci, domin kasar bagadur tazo da kyawawa guda biyu, ta farko itace Princess fatima, wada kuka sani da Princess tifa, wada ta kwoshe shekaru ita kecin gasar, sanan sai dayar da tazo itama Γ  dama da ita wato, Kamrina, dan haka kusan Γ  tare zasu fito, anma Princess tifa ta fito daga farko, kamar hadin baki, Princess tifa acikin wani abu aka d'auko ta, wanda shi kansa yasha Ado, ana zuwa da ita tsakar fili, kowa ya zuba idanu ga masu take mata Baya, ihu kawai ake, ana cewa ta cinye ta cinye, Γ  yangance ta zuro kafafun ta, mutane sai ihu suke, matasa matasa, yayin da Prince kumar keta yage baki, shima yana wani kara jin kansa na kara fadi cikin abokai shi Γ  dole ga matar sa, fitowa Princess tayi, gaba daya, waw kowa ke fada, yayin da aka d'auke wanan karagar aka barta ita kadai, sai yar tafiya take cikin rangwoda ana tafa mata, matasa cewa suke kin cinye,
Nan wanan mutumin yace sai ta k'arshe wato Kamrina, gefe akasa Princesse ta gusa,Kamrina ta dubi Suraya tace "anty anya na iya wly gaba na faduwa yake."

Murmushi Suraya tayi tace "insha Allah komai zaizo daidai zaki iya, kiyi kamar ba mutane Γ  wurin, murmushi Kamrina tayi, sai Suraya ta rufe mata fuska da wana yadi mai kyau da d'aukan ido, ta Dan rike kasan rigar Daga baya Suraya tayi kowa ya zuba ido yaga ta k'arshen nan ,kara kiran sunan Kamrina akayi, sanan Kamrina ta fito Suraya Γ  bayan ta a hankali cikin tafiyar ta mai d'auke hankali, kowa jira yake yaga abinda yake boye Γ  fuskar, ga gashi da aka saki sai reto yake a bayan ta, suna zuwa dai dai tsakiya, Suraya ta saki rigar ta koma, Γ  yayin da Kamrina ta kara so daidai k'arshen inda ake tsayawa kuma kusa da Princesse tifa Γ  hankali ta yaye wanan abin n'a fuskar ta, kayataciyar fuskar ta d'auke da Murmushi, tana ida yaye wa, Mutane dayawa dake gurin ya an masu alura suka tashi tsaye Γ  zabure, sukayi suman tsaye, aciki ko harda Prince Kumar, Princess tifa ko tanayin arba da Fuskar Kamrina sululu ta fadi some Γ  gun.......











Aci gaba da gashi πŸ‡
Maimou loveπŸ˜˜πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
*WACECE NI KAMRINA*
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€






*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*πŸ’‹




✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
πŸ’«
*🌟🌟TAURARI WRITERS ASSOCIATION*...............✍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨







_πŸ€¦β€β™€fans duk naji sakon ku, karku damu in kuna Son page diyawa to saide na dinga tsalake kwona biyu sanan zan turo, in kuma irin wanda nake yanzu ne to shi zaku iya samun kulum, saide in wani baban Uzuri ne ya hana ni, so ya kuka gani Γ  dinga maku kulum ko kuwa in dinga maku mai yauwa duk bayan kwona biyu, kuyi shawara nagode matuka yanda kuke Son wanan book ubangiji Allah barmu daku Ameen. sai naji daga gare ku 😍,😘_








*PAGE 23-24*






Ba karamin firgita Kamrina tayi ba ganin, Princess Γ  some, da sauri Momyn Princess da Kuyangi suka kwoshe ta sai d'akin da aka basu dan kwoliyar su,,,,,,,,


Mai gabatar da taro ne ya ankarar da mutanen dake tsaye dan sam ma su ba ta

Please Login or Register in order to submit comment